Hausa

Page 1

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugaban Annabawa da Manzanni, tare da Iyalen gidansa tsarkaka. Gaisuwa da sallama ta kauna da girmamawa a gare ku, Ya ku wadanda suka sami dacen amsa kirar Alkur’ani da samun daukakar bakuncin Dakin Allah. Abu na farko shi ne wajibi ku girmama wannan babbar ni’ima (da kuka samu), sannan kuma ku yi amfani da ita, ta hanyar dubi da tunani cikin bangarori na daidaiku da zamantakewa da kasa da kasa na wannan dama maras tamka, wajen kokarin kusato da manufofin aikin hajjin da kuma neman taimakon Allah Mai Rahama da karfi ta hanyar wannan bakunci. Ni da ku muna rokon Allah Mai rahama da gafara da ya cika muku ni’imarsa; haka nan kamar yadda ya ba ku dacewar tafiya hajji, ya ba ku dacewar gudanar da cikakken aikin hajji karbabbe, sannan kuma ya ba ku nasarar dawowa gida hannu cike cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali, insha Allah. A lokaci aikin Hajji, baya ga tsarki da gyara kai da ruhi wanda shi ne mafi girma da daukakar nasarar da ake samu a lokacin aikin hajji, har ila yau kuma tunani da kuma dubi cikin batutuwa mafi muhimmanci da suka shafi duniyar musulmi da al’ummar musulmi, suna daga cikin manyan ayyuka da ladubba da ke wuyan Alhazai. A halin yanzu daya daga cikin batutuwa masu muhimmanci kana kuma suke a sahun gaba-gaba, shi ne batun hadin kai tsakanin musulmi da kunce dukkanin kullin da ke haifar da tazara da rarrabuwar kai tsakaninsu. Aikin hajji alama ce ta hadin kai da ‘yan’uwantaka da aiki tare. A lokacin aikin hajji, wajibi ne a yi riko da abubuwan da aka yi tarayya cikinsu da kuma yin watsi da wadanda ake da sabani kansu. Shekaru aru-aru kenan ‘yan mulkin mallaka suka ba da himma wajen rarraba kan musulmi don cimma bakaken manufofinsu. To amma a halin yanzu albarkacin farkawa ta Musulunci da kuma irin fahimtar makiya ma’abota girman kai da sahyoniyawa da al’ummar musulmi suka yi da kyau da kuma tinkararsu, hakan ya sanya su kara kaimin wannan makirci na su na rarraba kan musulmi. Manufar wadannan makiran makiyan ita ce ruruta wutar yakin basasa tsakanin musulmi, kawar da duk wani kumaji na gwagwarmaya da jihadi daga gare su da kuma tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin haramtacciyar kasar Isra’ila da ma’abota girman kai, wadanda su ne asalin makiyan (al’umma). Wannan bakar siyasa ta kiyayya ita ce ummul haba’isin din kirkiro kungiyoyin ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi da makamantansu a kasashen yammacin Asiya. A saboda haka wajibi ne a gare mu, mu sanya batun hadin kai a tsakanin musulmi a matsayin mafi muhimmancin nauyi na kasa da duniya da ke wuyanmu. Wani batu mai muhimmancin kuma shi ne lamarin Palastinu. Bayan shekaru 65 da kafa wannan haramtacciyar kasa ta sahyoniyawa abubuwa daban-daban sun faru musamman zubar da jini na baya-bayan nan da ya faru, wadanda suka bayyanar da wasu lamurra guda biyu a fili: Na farko shi ne cewa haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa da masu goya mata baya mashaya jini, babu ruwansu da duk wata doka ko kan iyaka ta dan’adamtaka ko kyawawan halaye a yayin da suke aiwatar da ayyukansu na dabbanci da rashin imani. Suna halalta zalunci, kisan kiyashi, ruguza gidaje, kashe kananan yara da mata da marasa mafaka da kuma duk wani danyen aikin da za su iya, kai suna ma alfahari da hakan. Ayyukan dabbanci da ban haushin da ya faru a yayin yakin kwanaki hamsin na bayabayan nan a Gaza, misali ne na baya-bayan na irin wannan halin dabbanci, duk kuwa da cewa tsawon rabin karnin baya-bayan sun sha aikata hakan. Hakika ta biyu ita ce cewa wannan zubar da jini da danyen aiki (da suke yi) sun gaza wajen tabbatar da manufar jagorori da masu goya wa wannan haramtacciya kasa. Sabanin fata na wauta da rashin mafadi da wadannan lalatattun ‘yan siyasan sahyoniyawa suke da shi na karfafawa da kuma tabbatar da ita, a halin yanzu a kullum sai kusatar lokacin rugujewarta take yi. Tsayin daka na kwanaki hamsin da al’ummar Gaza marasa kariya suka yi a


gaban wadannan ayyukan dabbanci da nuna karfi na haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa, a bangare guda da kuma gazawar da sahyoniyawan suka nuna bugu da kari kan mika wuya ga sharuddan da ‘yan gwagwarmaya suka gindaya musu, wata bayyananniyar alama ce da ke nuni da irin wannan rauni da gazawa da haramtacciyar kasar sahyoniyawa take fuskanta. Don haka wajibi ne al’ummar Palastinu su kara fata da suke da shi (na ‘yanto kasarsu) sama da wanda suke da shi a baya, sannan kuma wajibi ne mujahidan kungiyoyin Jihad da Hamas su kara kokari da kaimi da azama da himmarsu. Shi ma yankin Yammacin kogin Jordan wajibi ne yayi riko da wannan tafarki abin alfahari da dukkanin karfinsa, kamar yadda kuma wajibi ne al’ummomin musulmi su bukaci gwamnatocinsu da su goyi baya da kuma taimakawa al’ummar Palastinu, taimako da goyon baya na hakika; su kuma gwamnatocin kasashen musulmi wajibi ne su riki wannan tafarki cikin gaskiya. Batu na uku mai muhimmancin gaske shi ne cewa wajibi ne masana masu kishin duniya musulmi na hakika su kalli bambancin da ke tsakanin Musulunci na hakika na Annabi Muhammadu da kuma Musulunci samfurin Amurka da idon basira, sannan kuma su tsamar da kansu da kuma wasunsu daga fadawa tarko kuskuren fahimtar wadannan hanyoyi biyu. A karon farko marigayi Imaminmu mai girma (Imam Khumaini) ne yayi bayanin wadannan ma’anoni guda biyu da kuma shigar da su cikin kamusin siyasar duniyar musulmi. Musulunci na hakika, shi ne tsarkakakken musulmi, Musuluncin gaskiya mai nagarta da kuma girmama ra’ayin mutane, Musuluncin “masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu”. Musulunci samfurin Amurka kuwa, Musulunci ne wanda ya sanya tufafin Musulunci don mika kai ga ‘yan kasashen waje da kuma kiyayya da al’ummar musulmi. Musuluncin da ya dana kunamar rura wutar rarrabuwan kai tsakanin musulmi, wanda maimakon yarda da kuma dogaro da alkawarin Allah, ya ke kira zuwa ga dogaro da makiyan Allah, wanda maimakon sanya wa musulmi ruhin fada da sahyoniyanci da ma’abota girman kai, yana sanya musulmi yakar junansu ne da hada kai da Amurka ma’abociyar girman kai wajen yakar al’ummarsu ko kuma wata al’ummar ta daban. Irin wannan Musulunci, ba Musulunci ba ne; munafunci ne mai hatsarin gaske da kuma halakarwa wanda wajibi ne kowane musulmin gaskiya ya yi fada da shi. Kallo da idon basira da kuma zurfin tunani, ko shakka babu zai bayyanar da wannan hakikar da kuma sauran batutuwa masu muhimmanci na duniyar musulmi ga duk wani mai neman gaskiya, sannan da kuma ayyana masa nauyin da ke wuyansa ba tare da wata kumbiya-kumbiya ba. Ko shakka babu aikin hajji wata babbar dama ce ta samun irin wannan basirar. Fatan da ake da shi, shi ne cewa ku din nan da kuka sami wannan falala ta sauke faralin hajji za ku yi kyakkyawar amfanuwa da wannan kyauta da ni’ima ta Ubangiji. Ina roka muku Allah Madaukakin Sarki da ya karbi wannan kokari na ku. Wassalamu alaikum wa rahamatullah Sayyid Ali Khamenei 5 ga watan Zul Hajj, 1435 wanda ya yi daidai da 8 ga watan Mehr, 1393.


Turn static files into dynamic content formats.

Create a flipbook
Issuu converts static files into: digital portfolios, online yearbooks, online catalogs, digital photo albums and more. Sign up and create your flipbook.