SiraÉ—in So Da Lafazin Soyayyah 2
SHARAHBIL MUHAMMAD SANI (Sharhamak) Website: www.sharhamakinfo.tk E-mail: sharhamak@yahoo.com 2|Page
Tel: 08103139272 Copyright © 2015-11-02 Sharahbil Muhammad Sani Maƙera Hakkin Mallaka © 2015-11-02 Sharahbil Muhammad Sani Maƙera DOKA An yarda ayi amfani da wannan littafi ko wani sashe daga cikinsa amma tare da kafa hujja dashi, tako wace hanya.
PUBLISHED IN NIGERIA BY SIGNTECH DIGITAL PRESS LIMITED No: 66/67 Beside Nagari Science College Birnin Kebbi, Kebbi State, Nigeria Website: www.signtechdp.com E-mail: info@signtechdp.com BOOK SETTING/COVER DESIGN BY SHARAHBIL MUHAMMAD SANI MAKERA Website: www.sharhamakinfo.tk E-mail: sharhamak@yahoo.com 3|Page
Tel/WhatsApp: 08103139272
4|Page
GODIYA Dukkan yabo da godiya sun tabbatarma Allah Madaukaki, mai kowa mai komai, wanda Ya sanya soyayya a tsakanin jinsi biyu na halittarSa. Allah Ka yi dadin tsira ga Shugaban Halitta, Shugaban Annabawa da Manzanni, Muhammad Dan Abdallah (S.A.W) tsira da aminci su kara tabbata a gareshi tare da Iyalan gidansa da Sahabbansa da kuma masu bin tafarkinsa har izuwa ranar karshe. SADAUKARWA Ga masoya na nakusa da na nesa. Ina rokon Allah da Ya kareku daga sharrin makiya Ya kuma kara kulla soyayya tare da nasara mai dorewa, amin. JINJINA Gare ku masoya na makaranta littafai na da fatar zaku kasance a tare dani a koda yaushe. Ina jinjina muku da irin kokarin da kuke da goyon bayan da nake samu daga gareku ta hanyar kira da aiko sako na fatan alkhairi da nake samu daga gareku, na gode. Na ku har kullum Sharahbil Muhammad Sani Makera (Sharha Mak)
5|Page
SiraÉ—in So NA AMINTA DA SOYAYYA Na aminta da soyayya Kaunar ki ce nayo niyya Ke ce wacce nasa zuciya ta
Kaunarki ta zamto sarkakkiya Rayuwa ta sa tayo farfadiya Na rasa inda ni zan tsaya da kaunar ta
Rayuwa tamkar darbejiya Da daci take tafi madacciya Ya ki zo kice dani kin aminta
Zo kar kice dani kin kiya In kinyi haka zan sakaya Hankali zai gushe kanki masoyiya ta 6|Page
A kaunar ki ni nake yin zabarbiya Sauri nake yi bani gajjiya Saboda son gimbiyar mata
Na aminta da soyayya Kaunarki ni yau nai niyya Ya ki yan mata
Na shiga rauni da zuciya Amma na kasa tirjiya Kaunarki ce ta sa ni gajjiya zo kice kin aminta
Sahiba ta zo ki bani soyayya Aminiya ta kan ki bani alkunya Sarauniya zo kice na aminta
SIRRIN ZUCIYA Yau zan bayyana sirrin zuciya Kaunarki ta sani hajijiya Yaki kiban so kinjiya Ke zaki barni na tsallake tsiradin zuciya
7|Page
Gani gaban ki ina juyayi Kaunarki ta sa ni nake juyayi Lallai yau zan bayyana sirrin nadai na boyoyi yau gani na zo da sirrin zuciya me sayasa a so na kasa yin tayi kullum idan na ganki sai nai ta juyayi kaunarki ta sa ni cikin juyayi yaki amince da ni masoyiya kullum idan na zo gidan ku sai na kasa tayi kallun idon ki dai nai tsayi kyakkyawar fuskarki ta sa ni tsayi ina son ki yan mata amince da soyayya kullum idaniya ta ke suke gani sun makanta a mata basu gani nayi nisa a soyayarki kizo ki gani amince da ni kar kice baki so na masoyiya kunnuwa na sun kurumta 8|Page
basajin kira bale a furta idanuwa ko sun azabata da soyayyarki wata basu gani sai ke aminiya kauna na bani kizo ki karba yafi a ce dake kizo sharba soyayyarki ce tasa ni nai ta kirba bani son ace dani zan rasaki a soyayya sirrin zuciya a yau na shaida a zuciya ta babu tsida gun wasu matan tayi tsada ke kadaice zaki taya aminiya
9|Page
SIRADIN KAUNA Siradin kaunarki zan tsallaka Masoyiya ta zo ki taimaka Ke kadai ce zan kusanta Ina tunani a zuciya ta Kaunarki lallai ta samu gata 10 | P a g e
Ke kadaice kauna na furta Zo ki yarda dani aminiya Kauna muyu da ke zo sarauniya Tunani na bani da tamka ni na furta Sanadin kaunarki na zama jarumi kauye da birni A sonki na yi suna duniya anka sanni Na samu masoya masu fata da alkhairi ni na furta Amma gani yau siradin na kasa tsallakawa Sai na fada don gazawa Shin laifi na ne ko kuwa al’adar so tambaya ta Nayi bincike kanki kuma na gane Cewa ke ce wacce ta dace kuma na gane Koda najje nai magana iyaye miji sunka mata Nayi kuka idaniya sun gajarta Zuciya ta sai faman bugawa kamar ta busta Na kasa hakuri amma can sai sunka furta 11 | P a g e
Sun bani kauwar ta don ita an rigani Nace zanyi shawara zaku jini Da naje gida na bacci yaki zowa gareni, aminiya so zoki furta Idan ka duba hannu na sunanta shine Kullun itace abin tunawa, tunaninta shine Abinyi gareni don na yi nisa a so ne zo na baki gata Ina neman shawarar yan dandalina Me zance gun mahaifanta don na nuna Karfin soyayya ta gareta ko zasu gane zan bata gata Wannan shawara ce ni na nema naji ta babba Gunku masoya ni bani zamba Ina sonta amma basu banba, aminiya zo na baki zuciya ta Siradin kaunarki zan tsallaka Masoyiya ta zo ki taimaka Ke kadai ce zan kusanta 12 | P a g e
Ina tunani a zuciya ta Kaunarki lallai ta samu gata Ke kadaice kauna na furta
‌BURINA Bani sake soyayya Bani sakara lobayya Yau na juya baya Na rasa farin ciki na Mai haskaka ruhina Mai tausayi ga kalbi na 13 | P a g e
Na zasa mai so na Mun dade da son juna Gashi yau iyaye sun raba mu da juna Ni fa kece burina Ke naso ace zan nuna Surruka ga ummana Meyasa kuke jifa na Kuka nake kan kauna Na rasa zabin kalbina Masoyayi kizo zo guna Zo kice kina burina Aure muyoshi da juna Zan rike amanar kauna Zan tsare hakken mai sona Ke ce muradin raina
14 | P a g e
Kaunarki ce burina Kaunarki ta ratsan raina In babu ke an barna Farin ciki babu araina Ya ke abin alfahari na Zo nan kizo muyi kauna
15 | P a g e
‌MANUFATA Sadiyya ke nake ta fata Rayuwa ta duniya ke ce manuffata Ina ta son su gane suna ta tsarguwa ta Yaki zo mu zauna ki zam garkuwa gareni Me yasa suka ce bazasu bani Kudi, ilimi, nasaba duk suna gareni Rikon da addini kuma dole gareni 16 | P a g e
Cikin masu hikkima dole ne a aganni Na fahimta Na aminta Na karimta Duniya ta sanni Zainab ki ce ni Zo muje ki bini Muyi aure a birni Na zo ki ganni
17 | P a g e
OYOYO MASOYIYA TA Oyoyo masoyiya ta Oyoyo zan baki gata Oyoyo kaunar ki jata Kaunar ki ta zama tsarin zuciya ta Ke ce wacce na baiwa raggamata Zo gani ki bani gata Oyoyo sai na yaba ta Kaunarki ce abin fadata Sadiya kin basu rata Yau gani ina ta fata Na so ace kudduri da fata Sun cika yau na bata gata Me yasa so yake da sata Nan take zuciya ya sata Yabi jini da jijiya ta 18 | P a g e
Gaki fara kuma kina da tsafta Doguwa ce ga ido an bata Tafiyar ta tafi ta, ai ta tsere mata Ina sonki ya masoyiya ta Kaunarki tana a zuciya ta Zo gani ki bani gata Sadiya ce masoyiya ta Kaunarki ina fadarta A zuci kuma baki ya furta Na aminta da son tauraruwa ta Mai tsari irin na mata Kizo gani ki bani gata
19 | P a g e
Soyayya! Soyayyah! Soyayyah! Har yanzo ban dainaba Kaunar ki ban fasa ba Ni ke nasanya a rai duba Ko zaki ce kina so na Eh! Nayi tunani na duba Kaunarki ta samin haiba Kwarjini a cikin hubba Har wayau ni ban daina ba Har yanzo ban daina ba Wayyo raina kaunarki ban daina ba Tunanin ki shine abin yi duba Hatsari na shiga kan soyayyar yar baba Zuciya sai faman bugawa take zo duba Na rasa sukuni kan sonki akwana ban runtsaba Safiya da rana duk daya ne guna basa gaba Me yasa suke tunanin da ba’a karba 20 | P a g e
Sirrin Zuciya Ke na baiwa sirrin zuciya Kaunarki ta sani hajijiya Tunaninki abinyi aminiya Zo yaki yan mata zo Sadiya Kaunarki nai fata muje saudiya Aure da ke nai fata masoyiya 21 | P a g e
Dare da rana kece tunanin zuciya Har abada kece a zuciya Idaniya na kuka kan masoyiya Rabuwa ni da ke ban fata sarauniya Ni bani zaton wai zamu rabu da taurariya Tunani na ke nai duba a zuciya Kina da kyan siffa ko ba kwalliya Gaki fara, a sura sililiya Iya tafiya kuma waye ba indiya Tattausan lafazi
FIYA – FIYA 22 | P a g e
Sako daga Dan Kebbi Agaida fiya fiya ka gama arna
-
kurungus angama da arna
Wa ye taure ya fada giwa
-
kurungus angama da arna
Sun razana naga basu ima
-
kurungus angama da arna
Kai har sun hankura sunga basu suna
kurungus angama da arna
Watturo taure ya fada giwa
-
kurungus angama da arna
Kanata hawa kana da girma
-
kurungus angama da arna
Kai ka kara hawa kana da girma
-
kurungus angama da arna
Sai dai gangara gwani na
-
kurungus angama da arna
Kai dai sai dai gangara ubana
-
kurungus angama da arna
Gwarzo na Sadiya basu cimma
-
kurungus angama da arna
Sharha Muhammad a gaida giwa
-
kurungus angama da arna
Dan bubawanga bashi ima
-
kurungus angama da arna
kurungus mungama da arna
-
kurungus angama da arna
Sharha Muhammad kana da girma
-
kurungus angama da arna
Kai ga dan kasuwa tsayayye
-
kurungus angama da arna
Rana ta karo a baiwa giwa
-
kurungus angama da arna
Wa yaro ya farma giwa
-
kurungus angama da arna
Yanzu karonga basu ima
-
kurungus angama da arna
Sharha Muhammad Allah daukaka ka
kurungus angama da arna
23 | P a g e
Sai dai Sharha na Makera ka gama da arna kurungus angama da arna Sannu fiya fiya ka gama da arna Gaba dai Sharha Muhammad dan kasuwa ka darasu suna Tafi dai tafi dai giwa haryanzu da kai mukai gwani na
Sannu fiya fiya ka gama da arna Gaba dai Sharha Muhammad dan kasuwa ka darasu suna Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani na Bisimilla gwani ahadun sarki na mai dare da rana
-
Eh lallai
Shi yanda yaso yakai Allah na kar ka sani kuna
-
Eh lallai
DK mai waka a jahar Kebbi zan buga tambari na
-
Eh lallai
A wajen gwarzon namiji Sharha Muhammad ubangidana Sannu fiya fiya ka gama da arna Muje Sharha Muhammad dan kasuwa ka darasu suna Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani na
24 | P a g e
Salati dubu jimla zanyo gun annabi manzo na
-
Eh lallai
Manzon Allah kunsan ya daukaka girma da suna
-
Eh lallai
Alihi da sahabai munsa suma sun daukaka da suna
-
Eh lallai
Ni dai manzon Allah kai dai ka kwanta zuciya na Sannu fiya fiya ka gama da arna Muje Sharha Muhammad dan kasuwa ka darasu suna Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani na Muna maganar Sharha Muhammad munsan kana da girma
-
Eh lallai
Kai ke bida maza Sharha Muh’d kanen Saratu uwa ta girma
-
Eh lallai
Karya yaro yashsha ya dangana don yaga bashi ima
-
Eh lallai
Dan kasuwa mai kima ka zama fiya fiya na arna
Sannu fiya fiya ka gama da arna Muje Sharha Muhammad dan kasuwa ka darasu suna 25 | P a g e
Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani na Abin mamaki ga dan taure na fada da kura
-
Eh lallai
Yaja damara ya nade hannu ku kyale saura
-
Eh lallai
Kare a cikin jeji ku kunsan bai fada da kura
-
Eh lallai
Ga Sharhabilu Muhammadu ya kira su sauna Sannu fiya fiya ka gama da arna Muje Sharha Muhammad dan kasuwa ka darasu suna Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani na Gaba gwarzo mai Allah magauta ka sakasu kuka gwani na
-
Eh lallai
To yaya zasuyi ne ka gagara ka hanasu suna
-
Eh lallai
Jirgi uban tafiya gwarzo na Sadiya bashi sanya gwani na
-
Eh lallai
Sharha Muhammad ka daukaka ba’aja da maigidana Sannu fiya fiya ka gama da arna Muje Sharha Muhammad dan kasuwa ka darasu suna Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani na Ango ga Sadiya gwani giwa kake masu kalle taru
-
Eh lallai
Gona mai taki can naffi zuwa na dinga lura
-
Eh lallai 26 | P a g e
Ganda duk yayi noma fatan da yakai ga kwara
-
Eh lallai
Har ya kai ga girbi gonar wani bata gaba nai
Sannu fiya fiya ka gama da arna Muje Sharha Muhammad dan kasuwa ka darasu suna Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani na Gaba dai sharha jan zaki ka hana suna
-
Eh lallai
Dotse mai nauyi kowaddauka shina da fama
-
Eh lallai
Ya maliya tayi ruwa kai kogi saika ja da baya
-
Eh lallai
Na sadiya ruwan malka kai muke so muke ta kauna Sannu fiya fiya ka gama da arna Muje Sharha Muhammad dan kasuwa ka darasu suna Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani na
27 | P a g e
Kwaro yaja baya ya hangi fiya fiya makashi nai
-
Eh lallai
Shi ke karya maza ciwon ciki ka gama da irna
-
Eh lallai
Masaki ke karya kada kasu surazana ubana
-
Eh lallai
Mai ilimin boko ga arbiya ina gwani na girma
-
Eh lallai
Ka fisu ado ka girmama naga basu cimma
-
Eh lallai
Kafisu gida ka girmama naga basu ima
-
Eh lallai
Kai nakawa waka banwa wawan da baida suna
Dan kasuwa sharha kai munkafi so kai muka kauna
28 | P a g e
KARSHEN ZANCE!!! Ashe waiwaye adon tafiya ne yau ga masoyiya yar mama Sadiya ce yar mama nake nunawa Yaki yar fara agaidake yar manya Sadiya ce yar Muhammad Usmanu karshen zance
Gaisuwa uwar tawaga sahiba ta ke zan yaba a yau yar girma Na gaisheki sahiba takunki lafiya dai-dai-dai gaisuwa nake yi ta miki yar girma
Bisimilla sarki Allah wanda ya zamo gatana Rabbana ka kara tsareni ya ubangiji sarki na Zani na wurin sadiya gimbiyar yan mata, takon ki lafiya kin zam sarauniya yar girma
Ga salati gun manzon Allah don fa shi yazam gatana
Alihi, asahabatu na sanya kwarrike su bai koka ba Tabi’ai waliya na sanya na rikesu ba sanya ba
29 | P a g e
Yanzu sharha zan dau hanya inje in iske giwar mata
Sha tankade da sabon kwarya!!! Tasha ruwa da sabon muda.. Sadiya ta zamo sai gada‌ Maki gani ya runtse idanu na furta jinjina ga yar girma
Gimbiya Sadiya, sannunki Sadiya giwar mata Ke alafiya kin tashi kwananki lafiya giwata Sadiya sannu hasken mata hasken ki ya wuce infurta Gani naki Sadiya tattaka a lafiya yar girma
Dukkaninku sai kunkai a kasa in kunga sadiya ta Sadiya yar gidan alfarma sannu sarauniyar mata Akyau kin cire ta tutar nan ko wa biki sai yai rata Gani sharha daga makera nazo wurin ki, kimin gata
Ke gadi girma kuma kin saba a gidanku ba karya ba Ke gadi girma yar girma tun gidanku ba sanya ba Maliya yau ta bamu ruwa tulu aja jiki can baya 30 | P a g e
In ana bayanin Sadiya mata kuje kasa kuyi ban girma
Mata suka ce ga sako na jinjinar ban girma Matan Kebbi sunke ga tasu jinjinar alfarma Sakwkwato ma sunka ce in gaida sahiba yar girma Yan yobe sun fada sun gaida yar gidan alfarma
Matan Abuja ma sunke sun gaida sarauniya yar girma Matan adamawa suna kasa sunce a gaida ke maigirma Matan Damaturu ma sunce ingaida yar gidan girma Matan Sadiya ma sunce sun gaida habibiyar alfarma
Sharahbilu jan karfe sararka anyi wasar banza Kainuwa dashen Allah ne mai kinsa yayi shirmen banza
Sannu sannu manyan haraka taka a lafiya dan girma Yau muna yabon Sadiya dole ne muzo muyu ban girma
Ke fa sharha ya shedeki kin kara daukaka yar girma Tunda sharha ya shedeki kin dinga daukaka yar girma 31 | P a g e
Ruwanki sun cika kofi kingi a barsu bakin kofa Ta sharha kin gawurta wa zayaja da ke yar girma
Zo ki bashi kyautar zuciya don shi muke jira yar gata Ni dan Muhammadu na roka zo aminta yar alfarma
Mugaida Zainaba yaya ga Sadiya yar girma Ita sarauniya Sadiya naso na ganki inyi bangirma Mata ga sharha kece fa shimfidar yan mata Duk wanda ya ce zaija dake nasheda ba zaisha ba
Ke Sadiya na gaisheki tunda kin gaida gimbiyar yan mata Ke Sadiya ikon Allah wa zayaja dake cikin mata? Ke wucesu sun lamunta sun jinjina ga reki a girma Kai a karonga sai na leka inganki sahibar yan mata
A gaida Aisha yar Sokoto na so na gaidake kin hidima Hajiya Aisha Kano na gaisheki jinjina nake kin sha fama Amina Yola ke ce jagora dole a gaidake yar girma Zainab Kaduna a gaisheki ke ma nayo jinjinar girma 32 | P a g e
Lubabatu Kano na gaisheki kema kinyi kokari yar girma Ina kike Zainab dole naje kano ban girma Ina Sadiyar Abuja kinsha fama Har wayau ina gaisheki Safiya a Abuja kinsha girma
Hakama balki na gaisheki yau har Kaduna zan ban girma Saratu ma na gaisheki don kinyi hiddima yar girma Habiba ma na gaisheki don kinyi kokarin bangirma
Go slow a sako a huta na dinga jinjina yan mata Na gaidake yar girma don na sanki ba sanin banza ba Amira kin sha hidima dole in hada da sandar girma Hindatu Turaki a gaisheki dole ingaida ke yar girma
Gaisuwa uwar tawaga sahiba ta ke zan yaba a yau yar girma Na gaisheki sahiba takunki lafiya dai-dai-dai gaisuwa nake yi ta miki yar girma Rubutawa Dan Muhammad Birnin Kebbi
33 | P a g e
KO KA/Ki NA JiNDADIN AYUKAN DA MUKE GUDANARWA? Ga duk mai Sha’awar aiko da wani sako/abu da yake bukatar a saka masa a wannan shafi a matsayin nashi gudunmawa kai tsayi sai ya aiko mana sako ta wannan adireshin i-mel sharha089@gmail.com ko ya aiko sakonsa ta wannan lamba 08103139272, 0811377717.
34 | P a g e