09.4.18
AyAU LEADERSHIP
Litinin
Don Allah Da Kishin Qasa
JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA
www.leadershipayau.com Leadership A Yau
9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
No: 120
LeadershipAyau
N150
Duk Varagurbin PDP Sun Koma Wasu Jam’iyyu —Makarfi Daga Umar A. Hunkuyi
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na qasa, Ahmed Maqarfi, ya yi iqirarin cewa, xaukacin baragurbin da suka nemi su vatawa Jam’iyyar ta PDP suna a baya, yanzun duk sun tattara komatsansu sun bar Jam’iyyar ta PDP
sun koma cikin wasu Jam’iyyun. “Yanzun mutanan kirki ma su gaskiya da kishin qasa ne kaxai suka saura a cikin Jam’iyyar mu. “Ina ba ku tabbacin, in har Allah Ya mallaka mana mulki a 2019, za mu yi duk abin da ya dace mu kyautata rayuwar mutanan Nijeriya,” in ji
Boko Haram:
Maqarfi. Maqarfi, ya yi waxannan bayanan ne ranar Asabar wajen gangamin Jam’iyyar ta PDP, na shiyyar Arewa maso yamma da ya gudana a Katsina. A wajen taron dai, tsohon gwamanan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya nemi ‘yan Nijeriya da kowa ya
tabbatar da ya mallaki katin sa na jefa quri’a, domin kowa ya zavi Shugaban da ya fi dace masa a zave mai zuwa na shekarar 2019. “Ko ma dai wa ka ke son ka zava, matuqar ba ka da katin jefa quri’ar ba za ka iya zaven sa ba, in ji Shekarau.
>Ci gaba a shafi na 2
Sojoji Sun Ceto Mutum 149 A Borno 4
• Daga dama zuwa hagu: Shugaban Qasa Muhammadu Buhari; Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Qasa, Abba Kyari; Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Muhammad Musa Bello tare da Babban Sufeton ’Yan Sanda, Ibrahim Idris jiya a yayin da Shugaban Qasan ya sauka a Abuja bayan ya dawo daga Daura wurin ta’aziyyar rasuwar Sanata Mustafa Bukar
Xan Shekara 12 Ya Lashe Harin Offa: Saraki Ya Nemi A Qara Inganta Fannin Tsaro Gasar Lissafi Ta Qasa > Shafi na 5
> Shafi na 2
2 RAHOTANNI
A Yau
Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Harin Offa: Saraki Ya Nemi A Qara Inganta Fannin Tsaro Daga Umar A Hunkuyi
A jiya ne,Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Bukola Saraki, ya yi kira da a inganta kayayyakin aikin tsaro na qasarnan, inda ya alaqanta matsalar tsaron da Nijeriya ke fuskanta da rashin kayan tsaron da suka dace, ta yadda qasar ba ta iya fuskantar matsalolin na tsaro yadda ya dace. Saraki, ya faxi hakan ne a garin Offa, ta Jihar Kwara, lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga Olofa na Offa, Oba Mohammed Muftau Gbadamosi, dangane da harin kwanan nan da ‘yan fashi da makami suka kai a garin. A ranar Alhamis ne wasu bijirarrun ‘yan fashi suka kai farmaki Bankuna biyar da kuma Ofishin ‘yan sanda na garin,inda suka kashe mutane sama da 20. “Matsalar ita ce, ta yadda za mu inganta kayan aikin Jami’an tsaron mu ne. A sarari yake, ba ma iya tunkarar duk wata matsalar tsaro yadda ya dace. Hakan ne ya sanya muka shirya wani taro kan sha’anin na tsaro akwanakin baya, domin nemo hanyar magance lamarin, mu haxa kai da sashen gwamnati domin neman mafita ga matsalar tsaro na qasarnan. “Mu a sashen Majalisa a shirye muke mu zo da shirin da ya dace da zai inganta tsaro a qasarnan, ta fuskacin samar da Jami’an tsaron da suka dace, kayan aikin su da suka shafi kuxaxe da kuma tsari. Akwai ma maganan yin haqiqanin abin da ya dace a hukumar ‘yan sanda. “Wannan matsalar tana bukatar a tashi mata tsaye
ne sosai. Matuqar ba mu yi hakan ba, za mu ci gaba da gamuwa da faruwar kwatankwacin wannan abin takaicin ne, inda za a sami wasu vatagari,su killace gari sukutum da guda, suna ta aiwatar da aika-aika har na tsawon awanni biyu. Ba wata al’umman da ta san ciwon kanta da za ta yi sake hakan na faruwa.” “Muna ta’aziyya ga iyalan waxanda suka rasa rayukan su, daga fararen hula da kuma jami’an tsaro, a wannan haxarin da ya faru. A babban gari kuma cibiyan kasuwanci kamar Offa, ya zama tilas mu fuskanci matsalar tsaro yadda ya dace, don mutane su ci gaba da gudanar da ayyuikan su.” “Tilas ne hukumar ‘yan sanda ta xauki faruwan hakan a matsayin qalubale a gare ta. Mu a namu vangaren na Majalisa, a shirye muke da mu ba su dukkanin goyon bayan da zai qarfafe su,” in ji Saraki. Kan batun ko a nemi rundunar Soji ta qasa ne da ta taimaka wa hukumar ta ‘yan sanda, Shugaban Majalisar ya ce, ba wata al’umma da ta san ciwon kanta da za ta sanya rundunan Sojin ta su riqa yin aikin ‘yan sanda. Saboda hakan yana da na shi matsalar ta daban, Sojojin ma ba su da yawan da ya dace. Sannan ga shi Jihohin qasarnan su na da yawa.Wannan ya sanya yana da wuya su iya kare xaukacin kan iyakokin qasarnan.” A na shi jawabin, Oba Gbadamosi, ya sabunta kiran da wasu ke yi ne na samar da ‘yan sandan Jihohi. “Zai fi kyau gwamnatin tarayya ta kafa rundunar ‘yan sandan Jihohi. In an
yi hakan, zai sanya su fi kusanci ga jama’a, da kuma gwamnatocin Jihohin. Wannan shi ne karo na huxu da ake yi mana shigen wannan aika-aikan a cikin shekaru goma. “Xaya daga cikin matsalolin da ke guskantar hukumar ta ‘yan sanda, shi ne qarancin jami’anta. Mun gano cewa, a xaukacin Qaramar Hukumar Offa bakixayanta, Jami’an ‘yan sandan da ke nan ba su kai hamsin ba. A duk lokacin da wani abu makamancin hakan ya ta so, ba inda muke samun wani xauki. Don haka muna fatan samun qarin Jami’an ‘yan sanda. Gwamnatin Jiha za ta iya samar mana da kayan aiki, za kuma ta iya gina mana sabbin Ofisoshin ‘yan sanda, to amma ina jami’an ‘yan sandan suke, ba su da yawa. “Kamata ya yi gwamnatin tarayya ta xauki tulin xaliban da suka kammala karatun su na digiri amma babu ayyukan yi, a aikin na ‘yan sanda, Sojin qasa, Sojin sama da ma Sojin ruwa. Akwai tulin matasanmu da suka gama karatun su na digiri amma ba su da aikin yi, kuma a shirye suke da su shiga ayyukan na Jami’an tsaron.” “Sam babu tsaro a wannan qasar. Idan da a ce kana nan a ranar da abin ya faru, da ka fahimci abin da nake cewa. “Ni ba na son na yarda da cewa, wai ba manyan makamai ne na zamani, maganan ita ce, ba za mu iya tunkarar su ba, domin ba mu da yawan da ya dace. Duk makamin da ke hannun su, Sojinmu da ‘yan sandan mu suna da su, amma in sun fi ‘yan sandan namu yawa fa,me ‘yan sandan za su iya
•Sanata Bukola Saraki
yi.” “Mun saba muna gayyatan agajin ‘yan banga, amma ka san waxannan ‘yan fashin sukan faxowa mutane ne ba tare da sun shirya ba. Akwai kuma haxarin amfani da ‘yan banga xin, domin da zaran mun sanya su aikin, watarana kuma sai ‘yan sanda su kama su, su ce suna xauke da makamai.” Xan Majalisar ta Dattawa mai wakiltar mazavar ta Offa da Irepodun, Sanata Rafiu Ibrahim, cewa ya yi, wannan harin da aka kai, ya nu na
gazawar sashen na jami’an tsaro ne, don haka ya yi kira da a sake fasalin sashen na jami’an tsaron. “Irin wannan abin takaicin yana iya faruwa a ko’ina, ya sanya zaman makoki a cikin garin. Zan yi kira ga Jami’an tsaron mu da su qara yawan jami’an tsaron da ke nan Offa da kewaye. Hakan kuma ya nu na cewa, muna da bukatar a kafa mana barikin Soji a nan Offa da kewaye, da za su iya taimakawa ‘yan sanda a irin wannan lokacin,” in ji Ibrahim.
2019: Bafarawa, Fayose Da Shema Sun Halarci Taron PDP A Katsina Daga Umar A Hunkuyi
Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya shawarci magoya bayan Jam’iyyar PDP, da su dage da addu’a da kuma neman gafarar Ubangiji. “Allah Yana horon ‘ya’yan Jam’iyyar ta PDP ne sabili da zunuban da suka aikata. “Allah Ba Ya yin kuskure, hakan ne ya sanya da ‘ya’yan
Jam’iyyar PDP suka yi ma shi laifi, sai Ya karve mulki daga hannun su ya baiwa APC, “ Bafarawa ya faxi hakan ne a wajen taron shiyya na Jam’iyyar ta PDP, ranar Asabar a Katsina. Shi ma Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Xanqwambo, ya nemi ‘yan Nijeriya ne da su guji aikata duk wani abu da zai iya karya tattalin arzikin qasarnan kamar na cin hanci
da rashawa da makamantan hakan. A na shi jawabin, tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya goyi bayan sake fasalin qasarnan ne, inda ya ce, hakan zai kawo ma qasar ci gaba a cikin hanzari. Ya ce, musamman sashen Bankunanmu da na siyasa suna bukatar sake masu fasali, domin qarfafawa xaukacin ‘yan qasa gwiwa su
shiga a dama da su. Shema, ya qarfafi ‘yan Nijeriya da su daina firgita da kiran da wasu masu nufin alheri ke yi na a sake fasalin qasarnan. A na shi taqaitaccen jawabin, tsohon gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, shawartan magoya bayan PDP xin ya yi da su manta da bambance-bambance su haxa kai su yi aiki tare domin cin
nasarar Jam’iyyar a zaven 2019. Shugaban Jam’iyyar na qasa, Uche Sekondus, Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, Tsaffin gwamnoni, Sule Lamixo, Ahmed Maqarfi, Ramalan Yero, Ibrahim Shekarau da kuma Muntari Shagari da Aminu Wali, duk suna cikin manyan baqin da suka halarci taron.
3
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
ra’ayinmu
Matsalar Shaye-Shaye A Tsakanin Matasa A farkon wannan watan ne qungiyar Gwamnonin Arewa ta yi kira na musamman ga gwamnatin tarayya da ta kafa dokar ta vaci a kan matsalar yawaitan shaye-shayen kayan maye a cikin qasarnan. Sun kuma yanke wannan shawarar ne, a bisa ganin yadda matsalar ta shaye-shayen kayan mayen ke ta qara yaxuwa a tsakanin matasa, musamman ma a nan Arewacin qasar da ma qasar bakixayanta. Gwamnonin na Arewa, sun yi wannan kiran ga gwamnatin na tarayya ne, jim kaxan da fitowarsu daga wani taro da suka yi a Kaduna, inda suka nu na matuqar damuwarsu a kan yadda matsalar ta shaye-shayen kayan mayen ke qara tambatsa tana zama tamkar wani abin ado ga matasan duk da irin illa da kuma cutuka gami da naqasan da kayan mayen ke haddasa wa matasan, lamarin sai qara tavarvara yake yi a tsakanin matasan, duk da matakan da gwamnatocin yankin ke xauka na daqile matsalar shaye-shayen. Gwamnonin sun nu na matuqar damuwarsu da ganin yadda tu’ammuli da muggan qwayoyin da matasan ke yi yake saurin lalata rayuwar matasan bakixayanta. Kwankwaxar ababen sa maye kamar su, ‘amphetamine’ da sauran ababen da ke haddasa jirkitar da hankali idan an sha su ba bisa qa’ida ba, na narcotic, irin su, codeine, tramadol da ireiren su, hanya ce kai tsaye mai saurin lalata hanta, sanya hauhawan jini, ciwon daji da sauran cututtukan jiki waxanda ke haddasa gaggautowan mutuwa. Rahotannin da aka samu a wannan shekarar kaxai, masu nu ni da yadda matasa suka riqa sheqawa lahira tun da quruciyarsu a sabili da matsalar ta shaye-shayen kayan mayen abin akwai ban tsoro saboda yawaitan su. Kwanan baya kaxan aka shelanta mutuwar wani matashin da ya sha kayan mayen har su ka yi ma shi karo ya kuma sheqa lahira tun da sauran kwanansa a garin Abraka, da ke {aramar Hukumar Ethiope ta gabas, a Jihar Delta. A dai Jihar ta Delta, wani matashi xan makarantar Sakandare ta, ‘Army Day Secondary School,’ da ke garin, Effurun, ta {aramar Hukumar Uvwie, shi ma hakanan kawai aka gan shi yana tangal-tangal a cikin aji, nan take kuma sai aka ga ya faxi qasa matacce ba rai. Ko da aka kai gawarsa xakin bincike, sai aka taras ya kwashi Tramadol ne har ya yi ma shi karo ya mutu. Mista Akindele Akingbade, Kwamandan Hukumar yaqi da shan muggan qwayoyi ta Jihar Abiya, a kwanakin baya ne ya shelanta mutuwar wani xalibin qaramar Sakandare a {aramar Hukumar Ohafia, ta Jihar ta Abiya, wanda shi ma ya sheqa lahira babu shiri bayan da ya haxiyi qwayar ta tramadol har guda 10, wanda aka ce wai ya sha ne domin ya sami qarin qwazo a gasar wasanni da ake yi a makarantar na su. Ainihin ita wannan qwaya ta, tramadol, an qirqirota ne domin ta kasance maganin da ke rage raxaxin ciwo ko kuma ya rage zafin jikin da ya tsananta. Amma a savanin hakan, sai matasan suka samo wata hanyar yin amfani da shi ta daban wacce ta kauce wa qa’idar amfani da shi xin, ta hanyar shan sa da yawa fiye da qa’ida. Matasan, sun ma yi iqirarin cewa wai shan qwayar ba bisa qa’ida ba, yana qara ma su qarfi, musamman a wajen jima’i. Duk da
cewa, akwai dokoki a qasarnan waxanda suka yi hani da yin tu’ammali da shigen waxannan qwayoyin kamar qwayar ta tramadol, da amphetamine, sai dai abin da aka rasa shi ne, tabbatar da yin aiki da dokokin. Kasantuwan yanda ake yawan shan ababen sa mayen, a yanzun haka, diloli da masu sayar da kayan mayen sun zama hanshaqan ‘yan kasuwa. A wannan satin kaxai, hukumar ta hana yin tu’ammali da kayan mayen, NDLEA, ta bayyana cewa, ta qwace qwayoyin na tramadol har milyan 159 a tashar jiragen ruwa ta Apapa, da ke Legas. Daraktan hukumar ne ta, NDLEA, mai gudanar da bincike, Mista
Femi Oluruntoba, ya bayyana hakan, a wani zama na musamman da Majalisar Dattawa ta gayyace shi domin ya yi bayani kan illoli da kuma rawar da hukumar na shi ke takawa wajen hana shan muggan qwayoyin. Ya ma qara da bayyana cewa, a kwanan nan a Kano kaxai, hukumar na shi ta lalata sama da Tan 50 na qwayar ta tramadol. Ya kuma yi nu ni da cewa, baya ga qwayar ta tramadol, akwai sama da ababen sa maye 31 da ake haxiya ko kwankwaxa domin jirkitar da hankali tun daga shekarar 2016. Matsalolin kan iyakan qasarmu, da kuma zafafan dokokin da suka haramtawa
EDITA Sulaiman Bala Idris
MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama
MATAIMAKIN EDITA Bello Hamza
DARAKTAN SASHE Mubarak Umar
RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah
BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John
manufarmu
LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!
hukumar lura da lafiyar abinci da magunguna, NAFDAC, gudanar da ayyukansu a tashoshin jiragen ruwan qasarnan, sun qara taimakawa wajen yaxuwar haramtattun kayan maye a cikin qasarnan. Wani bincike da kamfanin nan na, NoI Polls Limited, ya gudanar a ranar 1 ga watan Yuli 2013, ya yi nu ni da yadda qaruwan tu’ammuli da kayan mayen a cikin qasarnan ke qara janyo mana mugun talauci da rashin aikin yi. Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, a wani zama na musamman da Majalisar ta Dattawa ta yi kan matsalar shaye-shayen kayan mayen, ya yi nu ni da cewa, shaye-shayen, su ke haddasa yawaitan ayyukan masha’a, kamar su, fashi da makami, garkuwa da mutane, ta’addanci da saura ayyukan laifuka makamantan su, da suke barazana da sha’anin tsaro na cikin qasarnan. Sannan kuma abin takaicin, in ji Shugaban Majalisar ta Dattawa, da yawa daga cikin matasanmu, waxanda ake sa ran su zama shugabannin gobe duk sun rungumi wannan muguwar xabi’ar ta shaye-shayen na kayan maye. Wanda hakan a cewar shi, barazana ne ga lafiyarsu da rayuwar su ma bakixayanta, sannan kuma barazana ce ga iyalansu, don haka tilas ne mu tashi tsaye haiqan wajen yaqar wannan xabi’ar ta shaye-shayen na kayan maye, in ji Saraki. Matsalar ta shaye-shayen kayan maye a tsakanin matasan namu, da suka haxa da, shaqan sholisho da dangogin ta, da kuma ababen da ake sha daban-daban, da suka haxa da tabar wiwi, shaqan masai da makamantan su, waxanda suka zama ruwan dare musamman a nan arewacin Nijeriya. {warraru sun tabbatar da cewa, iyaye suna da mahimmiyar rawar da ya kamata su taka wajen duba halayyar ‘ya’yayen na su dangane da matsalar ta shaye-shaye. Kan haka, suka bayar da shawarar cewa, ya kamata iyaye su riqa duba ‘ya’yayen na su, musamman waxanda suka fara tasowa, ta hanyar duba idanuwansu a kai a kai, numfashinsu da ma yanayin warin jikinsu, gami da lura sosai a kan yanayin xabi’o’in su, na maganganu, hulxansu da kuma yadda halayyarsu ke canzawa. Da zaran an lura da wani baqon abu kan waxanda muka lissafta xin nan, sai a gaggauta xaukan mataki. Dangane da hukuma kuma, qungiyar masu haxa magunguna ta qasa, (PSN), ta kawo shawarar da a sanya dokar rubuta magunguna a qasarnan, wacce za ta baiwa qungiyar ta PSN, damar sanin ko wa da wane ne ke yin abu kaza a kowane waje, da ya shafi bayar da magungunan. Sannan kuma gwamnonin arewa, sun bayar da shawarar dukkanin gwamnatocin Jihohi su kafa wani kwamiti na musamman da zai tabbatar da ana aiki da dokokin hana safara da shan kayan mayen, a qarqashin ko dai mataimakin gwamna ko kuma Sakataren Jiha. Sun kuma bukaci Ma’aikatun kula da harkokin mata da matasa da su qara qaimi wajen shirye-shiryen wayar da kai kan haxarin da ke tattare da shan kayan mayen. A nan arewa kuma, gwamnonin sun shawarta kafa wata doka ta musamman da za ta yaqi safara da shan kayan mayen a yankin na su na arewa.
4 LABARAI
A Yau
Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Boko Haram: Sojoji Sun Ceto Mutum 149 A Borno Daga Muhammed Maitela, Borno
Sojojin Nijeriya a qarqashin rundunar ‘Lafiya Dole’, wadda ke yaqi da yan qungiyar Boko Haram a jihar Borno, sun bayyana cewa sun qwato mutane 149 waxanda qungiyar ke garkuwa dasu. Baya ga haka kuma, rundunar ta ce ta samu sa’ar kama mayaqan qungiyar har guda biyar a cikin wani samame da kai a mavoyar mayaqan. Bayanin hakan yana qunshe ne a cikin sanarwar da rundunar ta fitar a ta hannun mataimakin jami’im hulxa da jama’a na rundunar Lafiya DoleKanal Onyema Nwachukwu, inda ya fara da bayyana cewa rundunar ta kai samamen ne a mavoyar mayaqan Boko Haram da ke Yerimari Kura a jihar Borno, wanda a ciki ta samu nasarar kuvutar da jama’ar da mayaqan ke riqe dasu a mavoyar su. “a cikin xauki-ba-daxin ne, sojan Nijeriya suka
hallaka yan qungiyar Boko Haram guda uku tare da cafke biyar daga cikin su. Haka kuma, mun yi nasarar tseratar da mata 54 tare da qananan yara 95, waxanda mayaqan ke riqe dasu a hannun su. Sannan kuma zaratan sojojin namu sun tarwatsa kayayyaki da dama, mallakin mayaqanwaxanda suke amfani dasu”. Inji sanarwar “A halin da ake ciki yanzu, jama’ar da muka kuvutar xin suna samun cikakkiyar kula ta abinda ya shafi magunguna a cibiyar kula da maras lafiya, a 21 Brigade Medical Center, kuma za a miqa su ga iyalan su bayan an kammala yi musu gwaje-gwajen likita”. Bugu da qari kuma, a cikin wani samamen da sojojin rundunar Lafiya Dole ta kai a Konduga, sun yi nasarar daqile yunqurin wasu yan qunar baqinwake guda biyu, a sa’ilin da suke yunqurin kutsa kai a qauyen Mandanari na qaramar hukumar
•Wasu daga jerin mutanen da sojojin suka ceto
Konduga, a jihar Borno. “waxannan yan qunar baqin-waken su biyu, waxanda suka yi qoqarin yin sanxa da layar zana wajen shiga garin da nufin tayar da abubuwa masu fashewar, da kimanin qarfe
8:00 na dare, wanda kan ka ce kwabo sojoji masu kula da tsaro a lokacin sun gano su tare da taka musu birki”. “inda hakan ya tilasta yan qunar baqin waken canja akala tare da ranta cikin na kare, lamarin da
ya jawo ababen fashewar da ke jikin su tarwatse wa dasu. Wanda yan qunar baqin waken ne kaxai suka hallaka, inda kuma mutane uku suka samu qananan raunuka wanda yanzu haka suka samun kular likitoci”.
Sanata Hunkuyi Ya Qaryata Zargin Quntata Wa Naqasassu Daga Bello Hamza
Babban daraktan yaqin neman zaven Sanata Suleiman Hunkuyi kuma mai kula harkokin gangamin yaqin neman zavensa Alhaji Abubakar Musa Yariman Bomo ya qaryata zargin da ake yaxawa cewa, Sanata ya kori wasu gungun naqasassu dake zaune a wani gidansa dake garin Hunkuyi ta qaramar hukumar Kudan ta jihar Kaduna. Yariman Bomo ya mayar da wannan martanin ne tare da qaryata zargin a tattaunawarsa da wakilain kafafen watsa labarai ciki harda Leadership A Yau a ofishinsa dake MTD Zariya. In da ya bayyana cewa, “ Fiye da shekara 30 da suka
wuce ne Sanata Suleiman ya sayi filin ya kuma bar wasu naqasassu suka zauna a filin saboda bai tashi amfani da filin ba, ta haka ne filin ya zama kamar wani mattatarar naqasassu a garin” Yariman Bomo ya kuma qara bayyana cewa, “A halin yanzu waxanda suka fara zama a filin duk sun riga mu gidan gaskiya, basu kuma bar wasu zuri’a ba, waxanda suke zaune a wurin a halin yanzu yawancin su sun mayar da gidan kamar wani masaukin wucin gadi inda matafiya da ‘yan ci rani ke ya da zango” Inji shi. “Abin dake faruwa a halin yanzu shi ne aikin gina masallacin jumma’a da Sanata ya fara wannda aikin
gina masallacin ya yi matuqar nisa, hakan ya sa Sanata ya nemi waxanda suka fi daxewa cikin mazaunan gidan ya basu kuxaxe fiye da Naira 300,000 domin su nemi wani wuri su kama haya su ci gaba da harkokin rasuwarsu, wannan ne abokan hamayyarmu na siyasa suke amfani da shi wajen tara vatanci da yarfen siyass” Inji Yariman na Bomo ya ce, Sanata Suleiman Hunkuyi ya mahimmantar da gina wannan masallacin ne saboda yana cikin wasiyar da mahaifiyarsa ta ba shi kafin rasuwar ta, inda ta buqaci a gina masallaci da sunan ta, “ Yana fatan masallacin da ibadun da za a gudanar a cikin masallacin
su zama sadakatul jariya ga mahaifiyarsa”. Daga nan Yariman Bomo ya yi kira ga ‘yan siyasa dasu riqi gaskiya su kuma ji tsoron Allah wajen gudanar da harkokin su na siyasa, su kuma guji qage da sharri da qarya wajen cimma burinsu na siyasa. “ Gaskiya da riqon amanar jama’a ne ya sa harkokin siyasar Sanata Suleiman Hunkuyi yake ta samun bunqasa, farin jininsa kuma sai qaruwa yake yi a faxin jihar Kaduna dama Nijeriya baki xaya” Daga nan ya yi kira ga alummar jihar Kaduna da su jajirce wajen tattalin zaman lafiya tare da ba wa jami’an tsaro dukkan haxin kan daya kamata su kuma fallasa
Alhaji Abubakar Musa Yariman Bomo
harkoki da mavuyar vata gari a ko’ina suke a faxin jihar.
Shugabancin APC: Wata Qungiya Ta Nuna Muradin Oshiomhole Ya Yi Takara Daga Wakilinmu
Wata qungiyar jam’iyyar APC mai suna ‘APC Support Group’ ta ayyana muradinta ga tsohon gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole da ya tsaya takarar shugabancin jam’iyyar APC a babban taron
jam’iyyar da za a gabatar. Qungiyar ta bayyana haka ne a wata takardar manema labarai da ta sake jiya a Babban Birnin Tarayya Abuja. Takardar wacce ta samu sa hannun Sakataren Qungiyar, Dele Fulani da Bashir Saba, ta ambaci tsohon gwamnan
Edon da cewa, shi ne mafi cancanta da dacewa da shugabancin jam’iyyar ta APC. “Jam’iyyarmu mai girma ta havvaka. a shekarar 2015 ne Allah ya cika mana burinmu na amsar mulkin qasa, yayin da ‘yan Nijeriya suka gaji da
duk wani tsarin mulki, suka kuma nemi a samar da chanji. “Kamar yadda a yanzun ma muke tunkarar wani babban zaven, jam’iyyar mu ta APC na buqatar sabbin shugabanni masu hangen nesa da kaifin basira wurin kai mu ci gaba.
“A dalilin wannan ne muke kira ga Adams Oshiomhole xin da ya yi takarar shugabancin jam’iyyar a bisa la’akari da qwarewarsa da irin gudummawar da bayar tun daga qungiyar qwadago har kasantuwarsa gwamnan jihar Edo.”inji qungiyar.
LABARAI 5
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Buhari Ya Yaba Wa Sanatoci Da Irin Zumuncin Da Suka Nuna Wa Al’ummar Katsina Daga Umar A Hunkuyi
Shugaba Muhammadu Buhari, ya gode wa wakilan Majalisar Dattawa kan irin goyon bayan da suka nu na wa al’umman mazavar Katsina ta Arewa, bayan rasuwar wakilin mazavar, Sanata Mustapha Bukar. Babban mai taimakawa Shugaban qasar ne kan harkokin manema labarai, Malam Garba Shehu, ya bayyana wannan godiyan a lokacin da yake karvar tawagar Majalisar qarqashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, da suka isa garin na Daura domin ta’aziyya ranar Asabar. Shugaba Buhari, ya gode wa ‘yan majalisar kan yadda suka nu na jimamin su ga al’umman Jihar ta Katsina, Masarautar Daura da kuma iyalan mamacin.
Duk Varagurbin PDP Sun Koma Wasu Jam’iyyun —Makarfi
Ci gaba daga shafin farko Daga nan ya nemi ‘ya’yan Jam’iyyar ta PDP da su yi qoqarin wayar da kan al’umma da su mallaki katunan su na jefa quri’a. Shi ma da yake magana, Shugaban Jam’iyyar na qasa, Uche Secondus, bayyana farin cikin sa ya yi da ganin ximbin magoya bayan Jam’iyyar da suka halarci taron, ya kuma nu na hakan a matsayin tabbacin qarfin da Jam’iyyar ke da shi a Jihar ta Katsina, da zai ba ta ikon karvan mulkin Jihar a zave mai zuwa. Kamfanin dillalancin labarai na qasa, ya ruwaito cewa, an sami jama’a da yawa da suka fito daga Jam’iyyun, PDM, APGA, APC suka komo Jam’iyyan ta PDP, a wajen taron.
•Sanata Makarfi
Shugaban, ya yi addu’an Allah Ya gafarta wa marigayi Madakin Dauran, Ya kuma baiwa iyalan sa jimirin xaukan wannan babban rashin. A cewar takardar bayanin, Sanatocin da suka kaiwa Shugaban qasan ziyarar ta’aziyyar sun haxa da, Sanata Ovie Omo-Agege, Ali Ndume, Babajide Omoworare, Adamu Abubakar, Yusuf Yusuf, Hassan Adamu, Abu Ibrahim da kuma Umar Kurfi. A ranar Juma’ane, Shugaba Buhari, ya kasance tare da Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq, da sauran al’umman garin wajen addu’an uku ga marigayi Sanata Mustapha Bukar, mai wakiltar mazavar Katsina ta Arewa. Shugaban, ya sauka garin na Daura ne ranar Juma’a,inda kai tsaye ya wuce gidan mamacin, inda
• Shugaban Qasa Muhammadu Buhari tare da jerin wasu sanatocin da suka ziyarci Katsina domin yin ta’aziyyar rasuwar Sanata Mustapha Bukar a shekaran jiya
Sarkin Daura xin, da ‘yan
majalisar sa gami da iyalan
mamacin suka tarbe shi.
Xan Shekara 12 Ya Lashe Gasar Lissafi Ta Qasa Daga Umar A Hunkuyi
Wani xalibi xan kimanin shekaru 12, da ya fito daga makarantar koyon harshen Indiyanci a Legas, Rishe Gnana sekaran, ya zama zakara na shiyyar kudu maso yamma, a gasar lissafi na shekara-shekara ta 15 ranar Asabar. Gasar wacce Kwalejin, ‘Nigerian Tulip International Colleges,’ da haxin gwiwan cibiyar lissafi ta qasa da ke Abuja, ke shiryawa ga xalibai ‘yan ajujuwa biyar da shida na makarantun Firamare na qasa. Kimanin xalibai 39,000, ne suka shiga gasar daga wannan shiyyar, inda daga bisani aka
zavi zakaru 12 daga cikin su, gami da malaman su da makarantun su, suka cinye kyaututtukan. Gabakixayan dai waxanda suka cinye gasar, an ba su guraban qaro ilimi da wuraren zama duk a kyauta. Xalibin da ya zama zakara, ya sami kyautar kuxi Naira 300,000, inda malamin sa ya sami Naira 150,000, makarantar sa kuma ta sami kyautar Na’urar Fotokofi. Wanda ya zo na biyu, ya sami kyautar Naira 200,000, malamin sa kuma ya sami Naira 100,000, makarntar sa kuma ta sami kyautar Kwamfuta. Wanda ya zo na Uku, ya sami kyautar Naira 100,000,
malamin sa ya sami kyautar Naira 75,000, makarantar sa kuma ta sami kyautar na’urar buga takardu. Su ma waxanda suka ci gasar tun daga na huxu har zuwa na 12, duk sun sami kyaututtuka. Shugaban makarantar, Mista Ercan Yilmaz, ya ce, makarantar shekaru 15 kenan tana shirya gasar, domin bunqasa koyar da darasin na lissafi a makarantun Firamare. Ercan Yilmaz, ya ce, ba abin da ya fi mahimmanci ga zuriyarmu ta gaba a qasashen mu, fiye da samar ma su da ingantaccen ilimi. “A yanzun haka dai ana ci gaba da gudanar da wannan gasar ta lissafi ta 15, (ANMC), a xaukacin Jihohin qasarnan,
a shiyyar ta Legas ta qunshi Jihohi 9 ne, da suka haxa da, Legas, Ogun, Oyo, Osun, Ondo, Ekiti, Kwara, Delta da kuma Jihar Edo. “Xalibai 39,600 ne suka shiga gasar na wannan shekarar daga Jihohi 36, zakarun ne muke tare da su a yanzun haka. Ita dai Kwalejin ta, ‘Nigerian Tulip International College,’ ita ce wacce a baya aka sani da, ‘Nigeria Turkish International Colleges,’ cibiyar ilimi ce da ke da rassa 16 a Jihohi biyar na qasarnan. Makarantar, ta himmantu ne wajen qyanqyashe qwararrun xalibai, masu tarbiya da kishin qasa a Nijeriya da ma duniya bakixaya.
Za Mu Faxaxa Kasuwarmu Ta Iskar Gas –Baru Daga Umar A Hunkuyi
Babbna Shugaban hukumar daraktoci na kamfanin Mai na qasa, (NNPC), Dakta Maikanti Baru, ya sake jaddada aniyar kamfanin na bunqasa kasuwar sa ta samar da Iskan Gas (LPG), a Nijeriya. Baru, ya bayyana hakan ne ta bakin Kakakin Kamfanin na mai, Mista Ndu Ughamadu, ranar Jum’a a Abuja. A cewar sa, Kamfanin
Man, a shirye yake da ya haxa gwiwa da Cibiyar Injiniyoyi ta qasa, ‘Nigerian Academy of Engineers,’ domin inganta martaban qere-qere da kimiyya a qasarnan. Ya ce, daga cikin shiryeshiryen da kamfanin ke aiwatarwa domin inganta wannan sashen, Kamfanin Man, ya xauki nauyin shirya gasar xaliban Kimiyya tare da haxin gwiwar, sashen samar da iskan Gas, (NLNG), da sauran su.
Shugaban kamfanin ya qara da cewa, Kamfanin, ya kashe dala milyan biyu, domin samar da kayayyaki da na’urori a cibiyoyin bincike na Jami’o’in qasarnan guda shida. Ya kuma ce, babban burin sa shi ne ganin duk wasu girke-girke da al’umman qasarnan za su yi, sun koma yin su ne da iskan ta Gas. Baru, ya nemi cibiyar da ta wayar da kan ‘yan Nijeriya kan mahimmancin komawa amfani da iskar ta
Gas a wajen girke-girken su. Bayanin ya ci gaba da cewa, Shugaban cibiyar, Uwargida Olu Maduka, ta lura da cewa, matsayin ilimin na injiniyoyi yana ta qara ci baya ne a qasarnan, inda ta yi kira da a yi mai yiwuwa don ganin an magance matsalar. Maduka ta ce, “Kamfani ne kaxai kamar na NNPC, zai iya xaukan nauyin farfaxo da sashen na kimiyya da qere-qere.”
6 LABARAI
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Kwamared Goro Wakilin Fagge Ne Na Gari A Majalisar Tarayya -Zainawa
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An yi kira ga al’ummar qaramar hukumar Fagge da su ci gaba da ba da haxin kai ga xan majalisa mai wakiltarsu a majalisar wakilai ta tarayya, Kwamared Aminu Sulaiman Goro. Xaya daga cikin Dattawan jam’iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Alhassan Zainawa ne ya yi wannan kira a wurin bukin rabon kayayyakin tallafi na dogaro da kai da Kwamared Aminu Goro ya raba wa al’ummar mazavarsa, taron wanda ya gudana a xakin taro na gidan Gwamnatin Jihar Kano. Alhaji Murtala Alasan Zainawa ya ce Fagge Allah ya
inganta ta da xan majalisar tarayya mai nagarta da sanin ya kamata, ba su yi zaven tumun dare na yan amshin shata ba. Kullun yana kawo quduri da yake amfanar al’ummar kano, arewa da ma qasa baki xaya. Zainawa ya ce; “Akwai wasu yan majalisu a wasu wuraren da ba su iya kai ko quduri ballantana su yi aikin ci gaban al’ummarsu, don haka ya kamata yan Fagge su riqa yin addu’a, Allah ya ci gaba da bai wa Aminu Goro kwarin gwiwa ya ci gaba da samo ga matasa da kyautatawa al’ummarsa.” Alhaji Murtala Alasan zainawa ya yi kira ga sauran ‘yan majalisu da ba su iya tavuka komai da su yi koyi da Kwamared Aminu Goro wajen
tallafawa al’ummarsu. Ya ce; “Xan majalisar Fagge mutum ne mai qima, mai babban suna, kuma mai laqabi da Goro, wanda kowa ya san goro abu ne mai albarka na alkhairi. Zainawa ya ce, a zave mai zuwa na shekarar 2019, duk wanda yake da hannu da zai xaga a Fagge na xan takara, idan ba goro ya xaga ba to ba ya son al’ummar Fagge da alkhairi. Ya qarqare da cewa, da ana bayar da aron xan majalisa da sun karvi aron Aminu Goro a mazavun Gezawa da Gabasawa ko su ma sa amfana da kai quduri,samarwa da matasa aiki da tallafi da suka rasa a mazavun.
• Honorabul Aminu Goro
Bana Goyon Bayan A Sakar Wa Matasa Jagoranci -Hon. Ata
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Kakakin majalisar dokokin jihar Kano Alhaji Yusuf Abdullahi Ata ya nuna rashin goyon bayansa ga baiwa matasa damar shugabanci a qasar nan. Kakakin majalisar wanda ya shaidawa manema labarai hakan bayan wata ziyara da gamayyar matasa suka kai majalsar dokokin jihar kano. Ya ce shi baya goyon bayan
xan ficicin yaro a bashi muqami,domin shine bai san kansa ba,wanda bai san shine za a jagabar dashi akan al’umma? Ata ya qara da cewa shi kansa inka tsaya ka kalleshi bai natsu ba,kuma ka xebo miliyoyin mutane kace ka bashi”Ni har yau bana goyon bayan hakan. Mu duk abinda yake ba daidai ba ko ba gaskiya anan muke tsayawa bana wani
shakkar wanda bai fahimci abin ba.Bana goyon bayan “Nottooyoung to run” wallahi har gobe domin muna ganin abubuwanda suke faruwa”Inji Kakakin na Kano. Ya qara da nuni da cewa ai musulmi ma in ya ce shekaru a shugabanvi basa tasiri in yayi wasa sai yayi ridda, ai sai an sami natsuwa sannan za ace ka jagoranci al’umma ba kai kanka kana fama da kanka
ba watakila ma nauyin iyali mutum bashi da shi. Alhaji Yusuf Abdullahi Ata ya ce al’umma da yanayi na shekaru 40 baya ba xayane da yanzu ba, yan’kasuwa na shekaru 40 baya dana yanzu ba iri xaya bane.Malamai na shekaru 40 na baya da malamai na yanzu ba iri xaya bane.haka ma yan siyasa saboda yanayin akwai banbanci, shi wannan yanayin akwai banbanci,
wancan akwai natsuwa, akwai mutunci da dattako akwai tarbiyya ta addini data zamantakewa a qasar hausa. Ata ya ce in aka ce Buhari da Gawon sunyi mulki suna matasa wannan yanayin daya sami kansa da al’ummarsa mai tafiya ce mai taimako kuma tasan yakamata tanada hankali da lura amma wannan al’ummar bata da wannan natsuwar.
Mai Talla Shi Ke Da Riba:
LEADERSHIP A YAU Ta Shirya Tsaf! Kamar yadda kowa ya sani ne, wannan jarida mai albarka, LEADERSHIP A YAU ta kafa tarihi wajen zama jaridar Hausa da ta fara fitowa a kullum. Wannan fara fitowa a kullum yana da alfanu masu yawan gaske, gare mu Kamfanin LEADERSHIP da ku masu karatu, musamman masu sana’o’i manya da qanana. Wannan ne ya sa muke farin cikin shaida wa masu karatunmu cewa mun shirya tsaf domin tallafa wa kasuwancinku, ta hanyar tallata maku shi zuwa inda ba ku zata ba. Domin a halin yanzu mu kanmu da muke buga wannan jarida ba za mu iya bayyana iya inda ta ke shiga ba. Muna da tsare-tasare da dama don talla ku da hajojinku, inda muka fitar da tsarin ‘IYA KUXINKA IYA SHAGALINKA.’ Wato akwai cikakken shafi, akwai rabi, akwai kwata, akwai kuma daidai iyaka abin da mutum ke so a sanya masa. Wanda a wannan shafin muna so masu sana’o’i, musamman manyan dillalai su tallata hajojinsu, su qananan ’yan kasuwa akwai
nasu tsarin. A wani tsarin ma da muke da shi, akwai yanayin da mutum zai tallata hajarsa, sannan ya tallata kansa, inda za a sanya hoton shagonsa, hotonsa da kuma taqaitaccen tarihinsa, kuma wannan duk a kuxi kaxan. Maza ku kasance cikin kashi na farko na masu cin moriyar wannan shiri. Ina ’yan Canji, dillalan yaduka, masu kayan masarufi, mayan da qananan ’yan tireda, dillalan magunguna, masu kamfoni da masana’antu, dillalan hatsi, dillalan mota, masu sayar finafinai da dai sauran masu sana’o’i, ga dama ta samu. A tuntuvemu a lambarmu ta 08148507210, 07036666850, 08039216372, 07037934034, 08032875238 da 08038011382: email leadershipayau@gmail.com. Ko kuma a tuntuvi wakilanmu na jihohi don qarin bayani.
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku
Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku
Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.
Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com
TALLA 7
8
TALLA
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Domin Qarin Bayani A Tuntuvi: • Mubarak Umar – 0703 6905 380 •Sulaiman Bala Idris –0703 6666 850
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
TALLA 9
Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”
Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.
10 LABARAI
A Yau
Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Zaven 2019: INEC Za Ta Yi Wa Mutum Miliyan Biyu Rajista A Ebonyi Daga Abubakar Abba
Hukumar Zave ta qasa (INEC), ta sanar da cewar za ta yi wa a qalla waxanda suka kai munzalin ayi masu rijista miliyan biyu a jihar Ebonyi a kakar zaven 2019. Kwamishinan hukumar na jihar Farfesa Godswill Obioma, ya sanar da hakan a taron liyar da hukumar ta shirwa manema a garin Abakaliki dake jihar. Obioma ya ce, yawan waxanda suka kaxa quri’a a zaven 2015, ya kai yawan 1,074,273,inda ya qara da cewa, hukumar tuni ta tsara don tabbatar da waxanda suka kai munzalin jefa quri’a suma ba’a barsu a baya ba. A cewar sa, hukumar ta yi wa a qalla mutane su 132,170 rijista a 2017 da kuma a farkon tsakiyar 2018. Ya jadda da cewa, hukumar tana son yi wa mutane miliyan biyu rijista. A cewar sa, “ nufin mu a qalla mutane miliyan biyu muke son yi wa rijista a jihar don kakar zaven 2019.” Ya ce, “zamu yi hakan ne tare da yin qari akanwaxanda suka yi rijista a 2015.” Ya ci gaba da cewa, “ a yanzu munyi wa 132,170 mutane a 2017 da kuma farkon 2018.” Ya bayyana cewar, “wannan ya nuna muna da givin mutane su 793,557 da za’a yi masu rijista don kai wa yawan adadin na mutane miliyan biyu.” A cewar sa,“abin da ya rage mana a yanzu shi ne, mu haxa qarfi da qarfe ganin cewar mun qara zagewa don tattaro waxanda suka kai munzalin a yi masu rijistar da basu riga sun yi ba.“ A cewar sa, hukumar ta samu nasarar ganin ba’a yi wa masu qananan shekaru rijista ba ko masu yin rijista fiye da xaya ba kuma za’a gudanar da yin rijistar ce, a cibiyoyin da hukumar ta ware. Obioma ya bayyana jin daxin sa akan goyon bayan da ya samu daga kafafen yaxa labarai dake jihar tun lokacin da ya kama aiki a cikin watanni tara da suka wuce, inda ya yi kira a gare su akan qara tabbatar da goyon bayan. Kwamishinan ya yi nuni da cewa, kafafen yaxa labarai, suna da gagaruwar gudunmawar da zasu bayar wajen qarfafa dokokin zave da kuma tabbatar da gudanar da sahihin zave ta hayar rahotanni su da sauka yaxa wa. A cewar sa,“ kafafen yaxa labarai suna da muhimmiyar
rawar da zasu taka don don qarfafa tsarin zave, inda ya ce yin haxaka dasu don burin gudanar da sahihin zave a jihar Ebonyi 2019 yana da mahimmanci.” Obioma ya bayyana cewar, don a tattaro kan masu zave da ilimantar da su, musamman a ci gaba da yin rijistar masu jefa quri’a, hukuma ta qirqiro ta gudanar da tarurruka ga alumomin jihar. Kwamishin ya bayyana cewar, kafin zuwan sa jihar, ana wayar da kan masu yin zave ne kawai ta hanyar Radiyo sai kuma xan qoqarin
da aka yi na ilimantar dasu a gidajen su. Ya qara da cewa, masu ruwa da tsaki da ‘yan siyasa da mutanen dake karkara maza da mata da matasa da ‘yan makaranta da masu riqe da sarautun gargajiya da qungiyoyin sa kai da musamman nakasassu, duk sun halarci taron. Ya yi nuni da cewa, “mafi yawancin ku da suka fito daga kafafen yaxa labarai dabandaban, sun halarci zaven haxe da bayar da gaga rumar gudunmawa a tarurrukan wanda ya bai wa mutanen da
suka zo daga karkara damar yin tambayoyi a lokacin zaven akan zave. Ya ce,“ tarurrukan sun kuma baiwa mutanen sukunin yin tambaya akan jami’an hukumar da abinda suka lura da qwarewar su da qalubale da kuma gabatar da shawarwari don samar da kyakyawan yanayi akan harkar zave a jihar. Kwamishinan ya ce, hukumar ta samar da na’urar tattara bayanai don qara faxar da masu jefa quri’a jihar akan su je su yi rijista wanda hukumar ta amince da hakan.
Ya bayyana cewar, don aga ayi wa masu jefa quri’a rijista, an hukumar ta samar ta amince da na’urorin yin rijista guda uku a kowacce qaramar hukumar dake jihar. Ya ce, na’ura xaya a ofishin yin zave dake qaramar hukuma, inda sauran kuma ake zagaya wa dasu a sauran yankunan da ake yin rijistar ko kuma a mazavu. A cewar sa, “ana sa ran ko wacce na’ura xaya za ta yi kwana uku zuwa huxu a cibiyoyin na yin rijista ko mazavada ya kamata ayi wa wa masu jefe quri’a rijista.
• Daga dama zuwa hagu: Shugaban Qasa Muhammadu Buhari; Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu jiya a tashar jirgin Umaru Musa Yar’adua dake Katsina, yayin da shugaban Qasa Muhammadu Buhari ke qoqarin barin Jihar domin komawa Abuja
Yakubu Dogara Ya Yi Wa Iyalan Marigayi Sanata Ali Wakili Jaje Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
A ranar Juma’ar ne Kakakin Majalisar Wakilai ta Nijeriya, Honorabul Yakubu Dogara ya kasance a jihar Bauchi a cikin gidan marigayi Sanata Ali Wakili domin jajanta wa iyalansa da kuma ‘yan uwansa a bisa rasuwar Sanata Wakili a kwanakin baya. Dogara ya bayyana cewar rashin da su ka yi na Sanata Ali Wakili rashi ne wanda har shi kansa ta shafesa, don
haka ne ya bayyana cewar babban abin da ke akwai shi ne a yi masa addu’ar Allah ya jiqansa. Yakubu Dogara ya misalta Ali Wakili a matsayin wani mutum wanda ke da haquri da kuma sadaukar da kansa domin yi wa qasa hidima, ya bayyana cewar marigayin ya kasance daga cikin Sanatoci masu kwazo sosai, sai ya neman iyalansa da su yi haqurin jure wannan banban rashin.
Kakakin ya samu marawar baya daga sauran ‘yan majalisun tarayya daga Bauchi, inda aka yi wa marigayin addu’o’i na musamman da neman mara gafara a wajen Allah. Ali Wakili dai ya rasu ne a kwanakin baya a wani asibiti da ke Abuja bayan faxi da yayi a tsakiyar gidansa da ke Abuja, an kuma yi masa biso da kaisa makwancinsa na dindindin a makabartar da ke Abuja tun ranar da ya rasu.
•Honorabul Yakubu Dogara
LABARAI 11
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Mun Yarda Badaru Gwamnan Haxejawa Ne –Hon. Qa’is Daga Mustapha Ibrahim Kano
Mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dokin jihar jigawa, Honarabil Qa’is Abdullahi ya bayyana cewa irin ayyuka da Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru ya kawowa yankin Hadejia da Hadejawa da ma Jigawa baki xaya a matsayin wani abu na tarihi da Haxejawa ba za su tava mantawa ba, kuma ba za su daina ganin Gwamnan a matsayin mai qaunarsu fiye da kowa ba. Ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, kan irin ci gaban da gwamnan ya kawo wa Jihar Jigawa, ya ce, yankin Haxeja ya samu Asibitin qwararru, ya samu makarantar fannin kiwon lafiya, ya samu abubuwa masu yawan gaske. “Don haka mu Haxejawa tsakaninmu da mai girma Gwamnan Jigawa, Muhammadu Badaru sai ganin girma da qauna kuma ba mai rabamu da shi sai dai har ta Allah ta kasance a tsakaninmu, kuma ba wata damuwa don an ce Gwamnan Haxejawa ne. Xan Majalisar ya ci gaba da cewa, “Mun yarda kamar yadda wasu suke gaya mana cewa Gwamnan Jigawa na yanzu cewa gwamnan Haxejawa ne domin ya kawo yanki haxeja da Jigawa ci gaba. “Dangane da kyakkyawar alaqa da `yan majalisar dokin Jihar Jigawa ke da ita da gwamna Badaru ba wani abu bane ya jawo haka sai sanin qa`ida da yadda ya kamata a tafida `yan majalisa dama sauran al`umma shi ne yasa ba`a jin kanmu a koyaushe domin gwamna ne da yasan haqqin Jama`a da kyakkyawar mu`amala a matsayinsa na Gwamnan Jigawa don haka su ba `yan amshin shata ba ne.” Haka kuma Shugaban masu rinjayen ya bayyana qudure-qudure da dokoki da ‘yan majalisar jihar suka yi a matsayin babbar nasara ga xaukacin al`ummar jigawa inda kuma ya ce, su na alfahari da yadda suka samu nasarar tabbatar da dokar bada kuxin akwatu ga al`ummar xaukacin mazavun Jihar Jigawa wanda wannan zai kawo wadata da rage Talauci a tsakanin al`ummar Jihar Jigawa.
Shugaban Izala Na Gombe Ya Yi Kira Ga Shugabanni Da Su Riqa Taimakon Al’umma Daga El-Mansur Abubakar, Gombe
Shugaban qungiyar jama’atul izalatil bidi’a wa’ikamatus sunna ta kasa reshen jihar Gombe Injiniya Salisu Muhammad Gombe, shi ya yi wannan kiran a lokacin bikin rufe taron atisaye da qungiyar reshen qaramar hukumar Gombe ta shiryawa yan agajin ta a masallacin Juma’a na Tumfure dake yankin qaramar hukumar Akko a jihar ta Gombe Injiniya Salisu Muhammad Gombe, ya ce an shirya wannan taron ne dan koyawa Yan agajin yadda za su bada agajin gaggawa ga marasa lafiya a wurare daban- daban. Shugaban ya ce wannan tsalle-tsalle da aka koyawa Yan agajin yana zaburar da su ne su zama masu kuzari a ko da yaushe ba malalata ba sannan kuma su koyi yadda za su bada agajin gaggawa ga marar lafiya. Ya ce qungiyar Izala ba ta daukar dan agaji wanda bai da sana’a saboda ba yadda za ayi ta xauki batagari a duk lokacin da za ta xauki dan agaji sai wanda yake da abun yi domin yunifom na agaji ba abun banza bane. Ya kuma yi kira ga shugabanni da yan siyasa wajen ganin suna taimakawa qungiyar da guraben aiki dan samarwa da yan agajin dama ta shiga aikin gwamnati na xamara ko na ofis.
•Jerin Yan agaji a wajen taron rufr atisaye
Ganin cewa siyasa ta karato sai ya yi kira ga jama’a da cewa su fita su yanki katin zabe dan zabar wanda ya kamata kuma idan za a yi zaben ayi da kyakkyawar niya dan kar ayi zaben a dauka wanda aka zaba shi ne zai kawo canji ba Allah ba. A nasa jawabi shugaban qaramar hukumar Gombe Sani Hassan Sarkin Dogarai, cewa ya yi wannan atisaye na yan agaji da ya gani ya burgeshi kuma yana mai cike da farin ciki na yadda yaga irin damarun aikin da aka koya musu. Da ya taba batun tarbiyar Yara Sani Sarkin Dogarai, ya ce ba Malamai ne keda hakkin koyawa Yara tarbiya kadai ba hakkin Iyaye ne
domin ita tarbiya tun daga gida ake fara koyon ta sannan Malamai su dora. Sannan sai ya yi batun samar da aikin yi ko sana’a da zai sa a dogara da kai wanda ba lallai a dogara da aikin gwamnati ko wani mutum daban ba dan idan mutum yana da abun yi ba ruwan sa da sai ya sa rai a aikin albashi wanda idan ba’a biya akan lokaci ba kaga mutane na korafi. Shi ma Hakimin Tumfure Alhaji Muhammad Zailani Abubakar, cewa ya yi iyaye ne ke da alhakin bai wa yayansu tarbiya su zama mutane na gari amma sai kaga wasu iyayen sun nade hannu sun barwa Malamai inda ya ce hakan ba dai dai
bane. Hakimin Tumfure, ya kuma godewa shugabannin qungiyar lzala da Malamai kan wannan horo da suka shiryawa yan agaji dan sanin makamar aiki. Shi ma shugaban qungiyar Izala na qaramar hukumar Gombe Alhaji Adamu Mai Shinkafa, bayyana cewa ya yi a lokain da izala ta fito sabo sabo mutane da suka karbeta basu wuce yawan yan agajin da suke wannan wajen ba amma a hankali a hankali yanzu ta girma ta kai ko’ina. Daga nan sai ya yi addu’ar Allah ya sakawa jagororin qungiyar bisa wannan aikin alkhairi da suka shirya dan horar da matasan izalan.
Shugaban Qasa Ne Doka Ta Xora Wa Kiyaye Rayukan Al’umma –Xan Majalisa Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Xan majalisar tarayya mai wakiltar Bunguxu da Maru daga jihar Zamfara, Alhaji Abdulmalik Zubairu Bunguxu, Zannan Bunguxu ya bayyana gamsuwarsa bisa matakin dashugaban qasa Muhammadu Buhari ya xauka na tura sojoji jihar Zamfara. Matakin wanda aka xauke sa domin daqile matsalar ‘yan ta’adda da ya addabi wasu sassan jihar. Zannan na Bunguxu wanda ya bayyana hakan a yayin da yake zantawa da jaridar LEADERSHIP A Yau a Kano, ya ce, dama al’amarin tsaro
doka ta qasa ta xora shi ne a wuyan shugaban qasa, shi yake da alhakin kare rayukan al’umma don haka wannan mataki da aka xauka ya dace qwarai da gaske, kuma yana fatan idan Allah ya yarda za a sami nasara da hakan zai kawo qarshen kashe-kashe da ake fama da shi a yankin. Alhaji Abdulmalik Zubairu Bunguxu ya ce a matsayinsu na yan majalisa da suka fito daga yankin zasu bada goyon baya akan abin da ya shafi inganta tsaron yankin don a sami nasara a kai. Daya juya kan harkokin kasuwanci a yankin ya ce abu ne wanda za su haxa qarfi da
qarfe a matsayinsu na ‘yan majalisa da gwamnati da ‘yan kasuwa da masu sanya jari, don sai an haxa kai tunda abu ne wanda ake cewa hannu xaya baya xaukar jinka, sai kowa ya tashi ya bada gudummuwa. Xan majalisar ya ce a zamansa na majalisa ya kai quduri huxu wanda uku sun shafi yankinsu xaya kuma ya shafi qasa. Alhaji Abdulmalik Zubairu Zannan Bunguxu ya ce cikin qudurin akwai wanda ya shafi kashe-kashe da ake a yankinsa da kuma na saran daji da kuma na abin da ya shafi cutar kansa da yakamata gwamnati
•Abdulmalik Zubairu Bunguxu
tayi wani abu dan sauqaqawa masu larurar saboda tsadar jinyar cutar kuma waxannan quduri sun sami karvuwa a majalisa.
12
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2017 (22 Ga Rajab, 1439)
Hatsin Bara Tare da Dokaji Jr.
arabiandokaji@gmail.com 08180897610
Talaka Bawan Masu Gari Lallai wani abu na kusa da faruwa a qasar nan, ko dai talaka ya tashi ya kawo qarshen zaluncin da ake masa, ko kuma zalunci da ake masa ya karu. Sai dai akwai kyautata zaton zaluncin ne zai ci gaba da karuwa saboda dalili biyu. Na farko, juyin juya hali na faruwa ne idan al’amura suka fara daidaituwa amman ba sa tabbata da sauri yadda ake bukata. Komai a qasar nan kara tabarbarewa yake, ba ga tsaron da ake murna ya samu ba, ba ga abinci ko muhallin zama ba. Dalili na biyu kuma shine, a kullun a qasar nan talaka rage hankali yake a filin siyasa da zave. Wannan rashin zurfin tunani na talaka ya kai ra’ayin talaka na zave ya kai matakin nan da Karl Marx ke cewa ‘duk shekara huxu talakawa na haxuwa su zavi jerin mutunen da za su ci gaba da zaluntarsu’. Hangen nesan talaka ya zama abin jimami da Allah wadai. Hankalin mutum ba zai tashi ba har sai ya fahimci cewa wai fa maimakon ya’yen masu kuxi su zama su ne suke kare iyayensu akan zaluncin da su ke, xan talaka ne yake kashe kuxinsa ya shiga yanar gizo, ya caja wayarsa da injin da ya sa fetur mai tsada ko kuma ya biya a wajen mai caji, sannan ya hau ya kare masu zaluntar ta sa! Lallai Malam Sa’adu Zungur yayi gaskiya: ‘wagga al’umma me za ta wo a cikin zarafofin duniya’! Ban sani ba dai, amman a ganina ba’a taba talakan da ake zaluntarsa yake kuma taimakawa a zalunce shi ba irin na qasar nan. Banda dai xan qasar nan xan qasar nan ne, ya mutum zai dau maka alqawaruka, ya banzatar da kai, ba zaka kuma ganin shi ba sai zave ya gabato amman kuma ka ci gaba da tada jiniyar wuya a kanshi? Rana guda saboda zave ya zo daga kaga wannan xan siyasar ya zama lebura sai kaga wannan ya yanko hanya da talakawa yana shan rake, wai shi na su. An mayar da talaka tisqi Masifar da ake ciki a qasar nan ta kai wai ayi amfani da talakan da banda cutarsa ba abinda Turawan Yamma da yan barandansu ke yi a rufe bakin masu kokarin fadar ko tabbatar da an daina zaluntarsa. A biya shi kuxi, ya sace, ya razana ko ya kashe mutanen da sun fi shi amfani. To wai ranar da masu cutar mu suka yi nasara masu fahimtar ana cutarmun suka kare, malam talaka ya zai yi? Lallai akwai bukatar talaka ya fahimci cewa ba fa shi da wata mafita da ta wuce ya kama abokin shan wahalarsa hannun bibbiyu su nemi mafita. Xan qasar Isara’ila ba zai taba haxa kai da xan Falasdinu a cuci abinda ya shafi qasarsa ta Isra’ila ba, wannan sai xan Afirka, xan Afirkan ma xan Nijeriya, xan Nijeriyar ma
sai... Na dai yi shiru! Amman dai baitin da Malam Mu’azu Hadeja ya fasalta Bahaushe da shi, na so talaka gaba daya ya siffanta da su. Sai mu din ga cewa: Talaka mai ban haushi, Na Tanko mai kan bashi Da ba ruwansa da kishi Sai dai a san mai dashi Bashi son xawainiya/ Babba! A gaida sarakiBabu sana’ar kirki mai kwazo wajen bikiSai a yi rokon baki Don neman abin miya Babu wani abu da yake tafiya daidai a qasar nan banda rashin sanin ya kamata a tsakanin mahukunta da talakawa. An kafa gwamnati wadda talaka ya dora buri a kanta kamar zuwan Mahadi. An dau alqawari kamar an so a cuci budurwa, sai dai fa har zuwa yau banda tsaro da aka kamanta abinda ya kamantu a inda zai kamantu, babu wani abin a zo a gani da talaka ke mora. Ilimi na halin da yake ciki na rashin kyau, babu wani canji da aka samu. Makarantunmu babu wani canjin a zo a gani da aka samu. Har yau ‘yan qasar nan ba su fara morar wani tsari da zai sama musu ma aikin yi ba. An kawo tsarin N-Power, wanda idan aka duba da kyau wata dabara ce ta dauke hankalin xan talaka daga neman aiki a ma’aikatun da ya’yen masu kuxi kadai ke samunsu. Su bamu N-Power, su kai ya’yensu FIRS, PENCOM, NCC da irinsu NDIC inda ake biyan albashi, kamar yadda wani kakana yake fada, mai sa murmushin ba shiri. Kana magana a ce Buhari ya ce a koma gona! Kai sai ka ramtse da Allah kasashen da suke amfanar noman, da fatanya da lauje suka kawo ci gaba. Babu kayan noman zamani, me zaka noma? Sun sace kuxin takin, sun ki bada motocin noma sun ki yi kwalta, ina noma
za ta inda ake so? Ba ruwan talaka! Shi dai sai xan amarya! A matakin tsaro dole za’a yabawa gwamnati wajen dakile hare-haren rashin hankalin da a baya suka gallabi qasar nan. Sai dai fa akwai lauje a cikin nadi idan muka duba cewa rashin tsaron na nan, salo da muhalli kawai ya canja. Maimakon bama-bamai, yanzu harbe da yanka mutane ake. Wai a kwantar da Xan Adam a yanka, sai ka ce wata akuya! Kai! Wani aikin sai talaka! Kullun a shafukan jarida sai mutum ya karanta an kashe mutane, mun ma saba ba ma jin wani tashin hankali akai. Da kuxin man fetur aka qara da watakila yanzu mun kashe titinan qasar nan da zanga-zanga. Ga abin zanga zanga nan kuma ba ruwan mu, ko da yake ai gwamnatin xan amarya ce! Xan amarya ba ka laifi! Akwai matsala kwarai a ce soyayya ta rufe idanuwan mu daga ganin wannan tashin hakali da ake ciki, kawai saboda mu bala’in ya bar kofar gidajen mu ya koma na wasu, ko kuma saboda kar mu ai bata namu, tunda wasu basa aibata na su, ko kuma saboda dai kawai muna bayan xan Amarya. Babu soyayyar da ta wuce ka fadawa naka gaskiya, ba don ka tozarta shi ba, sai dai xan ka nusar da shi haxarin da yake jefa kansa da kuma wanda yake jefa ka. Duk kyakkyawar niyyar da shugaba ke da ita fa, matukar bai amfani da ita wajen amfanar talakawansa ba, ba ta da wani amfani, gara kashin safe da ita. Ina amfanin gaskiyar shugaba ya bari ana sace kuxin al’umma kuma baya daukan matakin da ya kamata akai? Ina amfanin kishin shugaba yana zama da varayi, matsawar varayin masu dadadada ransa ne? Ina anfanin rashin tsoron shugaba idan ba zai iya amfani da shi ya yakice mugaye daga cikin tafiyarsa ba? Shugaban
mu ya gaza, akwai bukatar mu tashi tsaye haikan mu nusar da shi hakan, mu kuma dafa masa ya gyara. Sai dai fa ba yadda zai zama ma’anar da mu ka bawa barawo da mu da shi ta banbanta. Ya za’ace in dai xan siyasa yana wuridin “sai Baba” shi mai gaskiya ne wanda kuma yake wuridin “baba ya gaza” shi kuma shine barawo. Duk sanda aka kwafsa sai a zo da uzurin ai PDP ce ta lalata qasar nan, kamar dama basanin hakan ne yasa muka koreta mu ka kawo APC su gyara mana ba kenan! Idan fadar itace ta lalata qasar ba tare da an wani yunkurin gyarawa ba muke so, ai ba sai mun kawo wani ba domin mun jima da fadawa duniya hakan. Akwai tashin hankali kwarai idan ni da nake zama a kan dakali a umguwa in zagi PDP akan cutar qasar nan da ta yi ace wai shugaban kasa ma babu wani da zai in ba hakan ba! Mun yarda PDP ta lalata qasar nan, to me APC take domin ta gyara? Shin duk ranar da muka sha wajen zaven Buhari, duk cin mutuncin da mukai wa sarakunan mu na gargajiya da wasu daga malamanmu, yi mukai dama don idan an hau an gaza a dame mu da uzurin su su ka lalata qasar nan? An fitar da jerin sunayen waxanda suka sace kuxin qasar nan, amman babu suna varayin jirgin ruwan fetur a ciki, babu sunan dillalin ciyawa, babu sunan varayin da suka sace kuxaxen jihohinsu suka marawa xan amarya baya yaci zave! Zave dai na gabatowa. Ya kamata duk wanda ya kuma fitowa ya ce mu zave shi ya sanar da mu abinda ya yi mana. Idan ya dau alqawari mu tabbatar ya cika. Babu dalilin da zamu riqa zabar mutanen nan su riqa wasa da hankalin mu kamar ‘yan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na gwada qwarewarsu ta tiki-taka.
LABARAI 13
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Al’umma Sun Yi Tururuwa Wurin addu’ar Bakwai Na Xan Majalisar Lakwaja Daga Ahmed Muhammed, Lokoja
Dubban al’umma daga ciki da kuma wajen jihar kogi suka halarci addu’ar kwana bakwai ta Marigayi xan Majalisa mai wakiltar mazavar lakwaja da Kogi a majalisar wakilai ta qasa, Arc. Umar Buba Jibril wanda Allah ya yi wa rasuwa a a watan baya. An dai gudana da addu’ar ne a gidansa dake birnin lakwaja, babban birnin jihar Kogi. Cikin waxanda suka halarci addu’ar har da shugaban Majalisar dattawa, sanata Bukola Saraki da Xan Majalisa Mai wakiltar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye da Shugaban Masu rinjaye na Majalisar wakilai ta qasa, Femi Gbajabiamila da mataimakin gwamnan jihar Kogi, Cif Simon Achuba da tsohon gwamnan jihar Kogi, Kyaftin Idris Wada da dai sauran manyan yan siyasa. Yayin da yake jagorantar addu’ar, babban limamin garin lakwaja, Sheikh Jimada Shafi’i wanda Sheikh Aminu Makera ya wakilta ya yi addu’ar Allah ya jiqan Marigayi Honorabul Umar Bubar Jibril. Ya kuma tunatar da alummar musulmi cewa watan wata rana kowa zai koma ga Ubangiji Allah Madaukin Sarki, Inda kuma Yayi Kira ga Musulmi da a kowace lokaci su rika aikata alheri domin samun tsira a duniya da kuma lahira. Ya qara da cewa Marigayin a lokacin rayuwarsa ya aikata abin kirki na inganta rayuwar jama’ar da yake wakilta. A dalilin haka ne ya yi kira ga sauran yan siyasa da su yi koyi da marigayi Umar Buba Jibril. Shi ma a nasa jawabin, shugaban majalisar dattawa ta qasa, sanata Bukola Sarakin yace ya kadu matuka gaya a lokacin da ya samu labarin rasuwar Umar Buba Jibril Wanda a cewarsa ya bada gagarumin gudunmawa wajen ci gaban dimukradiya ba a jihar Kogi kawai ba har ma da qasa baki xaya idan aka yi la’akari da rawar da yake takawa a
•Marigayi Arc. Umar Buba Jibril
majalisar dokoki ta qasa. A don haka ya yi adduar Allah ya jikan marigayin tare da baiwa iyalansa da al’ummar mazavarsa ta lakwaja da Kogi da Kuma Jihar Kogi hakurin jure rashin da suka
yi. Haka shi ma gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Cif Simon Achuba ya bayyana cewa jihar Kogi ta
yi babban rashin xan siyasa na gari kuma mai kishin qasa wanda ya sadaukar da kansa wajen inganta rayuwar al’ummarsa. Ya nanata da cewa marigayi Umar Buba
Jibril Shugaban siyasa ne wanda rashinsa zai samar da babban gibin da zaiyi wuyar cikewa. A don haka yayi adduar Allah ya yafewa marigayin kurakuransa da ya aikata yana raye tare da baiwa Iyalansa jimirin jure babban rashin da sukayi. Xan majalisa mai wakiltar mazavar lakwaja ta xaya, a majalisar dokokin jihar Kogi, wanda har ila yau shine tsohon Shugaban Majalisar dokokin najiha, Hon. Umar Ahmed Imam yace rashin marigayin babban koma baya ne ga siyasa mazavar lakwaja da Kogi dama jihar Kogi gaba xaya ganin irin yadda marigayin yake bada gudunmawarsa ga sha’anin siyasar yankin. Hon. Imam Ya Kuma bayyana marigayi Buba Jibril a matsayin Shugaban Siyasar yankin wanda yake bashi shawara a duk lokacin da matsaloli suka taso a siyasance, kana yayi adduar Allah ya jikansa da rahama da tare da kuma baiwa Iyalasa da sauran jamaa hakuri jure rashinsa. Marigayi Umar Buba Jibril rasu yana da shekaru 58 a duniya kuma ya bar mata 3 da ‘ya’ya takwas.
Sai An Cire Kwaxayi San Nan Dimokraxiyya Za Ta Zauna Daram A Nijriya -Xan Sa’a Daga Balarabe Abdullahi, Zariya
An tabbatar da cewar, sai an cire kwaxayi da kuma son raid a kuma qabilancin harshe da kuma na addin, san nan Dimokraxiyya za ta zama mai amfani ga al’ummar qasar nan. Wani fitaccen xan siyasa day a fara siyasarsa tun a zamanin jamhuriyya ta farko, mai suna Alhaji Aliyu Xan Sa’a da ke Unguwar Qaura a birnin Zariya ya bayyana haka a zantawarsa dawakilinmu da ke Zariya. Alhaji Aliyu Xan Sa’a ya ci gaba da cewar babu abin day a lalata Dimokraxiyyar da ake ciki a yayu sai abubuwan da aka ambata,wanda kuma ya ce a jamhuriyya ta farko da kuma ta biyu babu waxannan abubuwa da aka ambatagaba xaya, sai mai za a yi a ciyar da al’ummar Nijeriya gaba a ko wane vangare. Fitaccen xan siyasar ya
qara da cewar,a jamhuriyya ta farko, babban abin da aka saw a gaba shi ne, duk wanda ya shiga takara ya ya halayensa suke wasu ire-iren gudunmuwa yak e bayarwa a cikin al’ummar day a fito, amma baya ga waxannan abubuwa, a cewarsa, babu wani abu da ake dubawa, har ya zuwa xan siyasa ya kai ga nasara a duk takarar da ya shiga a ko wane mataki na zave. Alhaji Alyu Xan Sa’a, ya qara da cewar, a yau abubuwan da ake sa wa a gaba su ne, me xan takara ya ke da shi na kuxi, da kuma yawan kuxin day a tanada domin raba wa jama’a a lokacin tafiya yaqin neman zave tare da al’umma da suke rufa ma sa baya, duk mutuncinsa a cikin al’umma, in ba shi da kuxin da zai shiga takara, dole ya haqura da takarar da ya fara. Fitaccen xan siyasar
ya bayar da misali da a lokacinsu, na har xan takara ya fara takara ya kai ga samun nasara, ba a tambayarsa ko da kwabo xaya da sunan abin da za a ci a tsawon raka shi yaqin neman zave a tsakanin al’umma. Da kuma yak e tsokaci na yadda a yau shugabannin jam’iyya ba su da daraja a idon ‘yan takara, Alhaji Aliyu Xan Sa’a ya ce, sanya kwaxayi ga ‘yan takara ke yi, shi ne kan gaba na yadda xan takara a yau ya mayar da su gugar yasa, suna da amfani kafin zave, bayan zave kuma an manta da su, wannan ne ke sa a yau shugabannin jam’iyya ba su da mutunci a idon duk wani zavavve, domin mafiya yawansu, sun nuna kwaxayinsu, kafin zave a tsakaninsu da ‘yan takara ko kuma xan takara. Wannan matsala, a cewarsa a yau shugabannin
•Aliyu Xan Sa’a
jam’iyya ba su da mutuncin da za su yi kirar zavavve ya je garesu, sai dai shi ya kira su, su kuma je wajensa a guje. A qarshe Alhaji Aliyu ya ce ,a lokacinsu babu wannan matsala ko kuma kwaxayi a tsakanin shugabannin jam’iyya, suna kirar duk wani zavavve a duk lokacin da suka ga dama, ya je garesu a lokacin da sukae buqata.
14 RAHOTO
A Yau
Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
ANCOPSS Ta Horar Da Malamai 500 Dabarun Ladaftar Da Xalibai A Bauchi Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
A ranar Larabar makon da ya gabata ne qungiyar shugabannin makarantun Sakandare na jihar Bauchi, wato ANCOPSS ta shirya taron horaswa na wuni guda wa malaman da suke aiki a vangaren ladaftarwa da kuma koyar da tarbiyya wa xalibai, bita kan dabarun dakilewa gami da ladaftar da kangararru masu aikata munanan xabi’u a makarantu, haxe da sanya kan hanyar da ta dace kuma daidai da salon zamani. Malamai sama da xari biyar daga faxin jihar Bauchi ne suka samu wannan horarwar kan dabarun shawo kan tavarvarewar tarbiyya a tsakanin xalibai wanda hakan ke toshe wa xalibai hanyar samun ilimin da ta dace, taron ya gudana ne a cikin garin Bauchi wanda wani shehun malamin boko daga jami’ar Jos ya gabatar da maqala kan dabarun shawo kan matsalolin xaliban. Da yake jawabi a wajen taron bitar, babban malamin bokon, wanda kuma shi ne Farfesa Bitrus Longbap ya bayyana cewar aikin ladaftarwa da kuma gyaran tarbiyya wata aiki ce da ya dace a kowani lokaci a bata fifiko fiye da sauran wasu janibobin, yana mai imanin cewar idan xaliban suka samu tarbiyya da kuma ladabi iliminsu zai kasance mai nagarta kuma za a samu al’umma ta gari, ya bayyana cewar aikin da sadaukarwa ne don haka masu kula da sashin su yi don Allah. Ta bakinsa. “ina mai qarfafa cewar muddin in dai waxanda suke aiki a sashin ladaftarwa da gyaran tarbiyya za su yi aikinsu yadda ya dace, to tabbas suna neman goyon bayan shuwagaban makarantun da kuma iyayen xalibai, da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki,” In ji Bitrus Longbap. Ya qara da cewa mai koyar da gyaran tarbiyya dole ne ya zama alami, “Da fari ma shi kansa mai gyaran tarbiyya dole ne ya fara gyara kansa, ya zama rayuwarsa ma kawai isharace ga masu kallonsa, hallayensa ya zama abin koyi ga matasa da sauran waxanda ke hulxa da su. Su kuma ‘yan makarantar nan, kai mai aikin ladaftarwa za ka ke nuna musu cewar in suka gina rayuwarsu yau gobe sune za su ci ribar rayuwarsu, amma fa matuqar aka barsu babu tarbiyya to tabbas sun lalace, mu kanmu za mu san gobenmu ta gama
•Mudi Jahun (a tsakiya); mai tallafa wa gwamnan Bauchi kan ilimi (a hagu) a lokacin da sukeke sauraron jawabi a wajen taron
lalacewa,” Farfesan ya qara da cewa, “Na tabbatar wannan taron bitar za ta kawo sauyi, domin idan malaman nan suka xauki ababen da muka koyar musu suka je suka yi aiki da shi za a samu gyara. dole ne mu tsaya mu yi aiki tsakani da Allah mu kuma kasance masu kishin qasarmu da ci gaban qasar nan, idan muka tabbatar da yin abin da ya dace tabbas muna da lada mai kyau,” A cewar Bitrus Longbap . Da yake ganawa da manema labaru, shugaban qungiyar shuwagabannin makarantun gaba da firamare a jihar Bauchi (ANCOPSS), wanda kuma su ne suka shirya taron, Dakta Musa Mudi Jahun ya bayyana cewar sun duba yanda za su lalubo bakin zaren ne ya sanya suka shirya taron domin a samu gyara a tsakanin al’umma, “Abin da ya sanya muka ga ya dace mu shirya wa jinsin waxannan malaman wannan taron bitar shine idan ka duba yadda tarbiyya ta tavarvare, rashin sanin ya kamata daga wajen xalibai kowa ya xauki wata hanyar ta daban, ba a yin abin da ya dace, taurin kai ya yi yawa, kuma wasu xaliban basu jin magana,” Kwamared Jahun ya qara da cewa, “waxannan dalilan ne suka sanya mu ka ce to mene ne musabbabin irin waxannan abubuwan da ke jawo irin wannan matsalolin, sai mu ka ce to ai a kowace makarantu akwai sashin ‘yan ‘guidance and counselors’, wanda babban
aikinsu shine bayar da shawari da kuma gyara tarbiyya. wannan dalilin ya sanya muka ce bar mu kirawo su mu basu sabon horo domin ta tafiya daidai da tsari na yau, qila da suna horar da su kan tsari irin na da ne, wanda hakan ke sanyawa ba a samun raguwar wancan matsalar, sai muka ce idan tsarin yin laifuka suka canza, tsarin shawo kansa ma dole ya canza don haka ne muka shirya musu wannan horaswa don sanin makamar da ta dace,” Dakta Mudi Jahun ya bayyana cewar baya ga wannan kuma suna qoqarin horar da malamai daga sassa dabandaban, ya kuma bayyana cewar suna yin hakan ne domin rage wa gwamnati xawainiyar da ke kanta, ya bayyana cewar dole ne a kowani lokaci ake baiwa malamai horo don sabinta aiki da kuma gudanar da aiki, ya kuma bayyana cewar yanzu mataki na gaba za su zaqulo Daraktoci da kuma waxanda suke sashin gudanar da mulki domin basu horo kan inganta aikinsu. Da ya jawabinsa Kwamishina a ma’aikatar ilimi na jihar Bauchi Farfesa Haruna Danwanka ya bayyana cewar wannan horon zata kawo sauyi matuqa wacce za kuma a samu natija matuqa “Idan ka duba yanzu zamani ya zo da wasu abubuwa da dama da suke kawo matsalar tarbiyya, kamar wayar nan, wani lokacin ma za ka ga xalibi yana amfani da waya a lokacin da ake xaukan
darasi, don haka irin wannan taron zai kawo sauyi domin samun dabarun yadda za su yi domin shawo kan,”. Babban mai tallafa wa gwamnan jihar Bauchi kan ilimi da faxakarwa, Kwamared Sabo Muhammad ya bayyana cewar taron zai kawo sauyi mai sunan sauyi la’akari da irin horon da aka baiwa malamai da suke aiki a sashin ladaftar da xaliban, ya horesu da su jajirce bisa aikinsu domin haqa ta kai ga cimma ruwa. Wasu malaman da muka zanta da su, sun sha alwashin cewar za su ci gaba da zage damtse domin yin aikinsu tsakani da Allah “idan ka lura, tun da ma muna sadaukar da kanmu domin mu ga mun tabbatar da yi wa xaliban nan hidima, sau tari idan ka ce za ka yi wa xalibi tarbiyya kana fuskantar kalubale kamar na daga xalibin, babansa da sauran wasu ma, amma idan aka jure yaron nan ya samu tarbiyya kowa zai amfani ba mu kaxai makaranta za mu ji daxi ba idan yaro ya samu zama na gari; za mu ci gaba da sabintawa da kuma bin hanyoyin da aka xaura mu domin samar da sakamako mai kyau,” In ji wasu malaman. Dakta Mudi Jahun ya bayyana cewar suna fatan malaman da suka samu horo kan dabarun shawo kan matsalolin tarbiyya daidai da zamanin, za su kuma ilmantar da sauran abokan aikinsu da suke makarantunsu domin a samu kai wa ga nasara.
RAHOTO 15
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Manyan Shugabanni Sun Halarci Bikin Saukar Markazi Minhatil Islamiyya A Kaduna Daga Wakilinmu
Manyan shugabanni dabandaban a matakin qasa da jiha sun halarci bikin yaye xalibai na Makarantar Islamiyya ta Madrasatu Minhatil Islamiyya wa Tahfizil Qur’an da ke Unguwar Rimi Kaduna, karo na huxu. Bikin wanda ya wakana a Layin Rafindaxi a Unguwar Rimi, yankin Qaramar Hukumar Kaduna ta Arewa a ranar Asabar xin nan, an fara shi ne da misalin qarfe goma da rabi na safe zuwa qarfe xaya da rabi na rana. Xaliban da aka yaye su 16 maza da mata sun kammala karatun Alqur’ani mai girma da wasu darussa na ilimin addini da fannin Larabci. Xaliban da aka yayen sun gudanar da karatun Alqur’ani xaya bayan xaya a kan mumbarin da aka kafa a tsakiyar filin taron, inda iyayensu da ‘yan’uwa da abokan arziqi suka riqa nuna jindaxinsu a fili kan ilimin da suka samu. Da yake gabatar da jawabi, shugaban taron kuma babban uba na makarantar, Alqalin Alqalai na Kotun Xaukaka Qara ta Shari’ar Musulunci da ke Kaduna, Dakta Shehu Ibrahim Ahmed, ya yi kira ga xaliban da aka yaye su xora daga inda suka tsaya domin samun karatu da ilimin addini mai zurfi tare da yin aiki da abin da aka koyar da su. Ya kuma buqaci al’ummar Musulmi na nesa da na kusa su ba da gudunmawa sosai wajen kammala aikin ginin makarantar a Kadaure, Unguwar Rimi Kaduna. “Allah (SWT) ya ce wa zai ba shi bashi bashi mai kyau? Allah zai ninninka ma sa ladansa. Kowa ya san Allah ba ya buqatar bashin wani abin halitta, halitta ce take da buqata a wurin Allah. Wannan hidimar da za mu yi kanmu za mu yi wa. Mu za mu samu ladan. Mu yi qoqari kafin nan da xan wani lokaci mu kammala aikin ginin makarantar nan”. Kamar yadda ya bayyana. Alqalin Alqalan ya yi addu’ar Allah ya saka wa malaman makarantar da alheri bisa jajircewarsu wurin koyar da xaliban. Kana ya buqace su su cigaba da qwazo kasancewar abin
• Shugaban Gudanarwar Makarantar, Abdulrazaq Yahuza Jere (zaune a tsakiya), shugaban Malaman Makarantar, Malam Usman Adam (na huxu a zaune daga dama), Malaman Makarantar, Sayyid Abubakar da Sayyid Shamsu (na uku da na biyu zaune daga dama), Sakataren Makarantar, Ustaz Isma’il Odoh Aliyu (na farko a dama) da sauran Malamai mata, Malama Nafisa, Malama Hafsat da Malama Aisha (daga hagu a zaune) tare da Xaliban da aka yaye
da suke yi sadaka ce mai gudana. A nashi vangaren, shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Qasa (NIS), Alhaji Muhammad Babandede, ya ce karantar da yara ilimin addini da tsoron Allah babban abu ne da yake gyara zamantakewar jama’a sannan uwa-uba ya qara kusanta su da Mahalicci Allah (SWT). Alhaji Muhammad Babandede wanda Babban Jami’in hukumar ta NIS, shiyyar Kaduna, Alhaji Habibu Haruna ya wakilta, ya jinjina wa qwazon da xaliban da aka yaye suka nuna. “Shugabanmu, CG NIS ya so ya halarci wannan wuri da kansa amma sai uzurin wani taro ya gitta. Shi ne ya ce mu wakilce shi. Insha Allahu za mu shaida ma sa abubuwan da muka gani. Haqiqa koyar da yara ilimi muhimmin abu ne da yake gyara rayuwar al’umma. Yara sun yi karatu alhamdulillah. Musamman ga mata nan a cikinsu sun nuna qwazo wanda Manzon Allah (SAW) ya ce idan mace ta yi ilimi tamkar an karantar da al’umma ce. Saboda haka wannan ba qaramin lamari ba ne. Insha Allahu har da mu za mu ba da gudunmawa domin cigaban wannan makaranta. Mun tantance abin kuma za mu shaida wa CG. Malaman da suka koyar da xaliban Allah ya saka musu da alkhairi.” Kamar yadda ya bayyana. Shi ma da yake tofa
albarkacin bakinsa, Dakta Abubakar Adah daga Jami’ar Jihar Kogi, ya jinjina wa ingancin karatun da xaliban da aka yaye suka samu, kana ya yi kira ga iyaye su qara baiwa malaman makarantar haxin kai ta hanyar biyan kuxin makaranta a kan kari da kuma bincikar yanayin karatun ‘ya’yansu don sauqaqa wa malamai aikinsu na koyarwa. Ya ce qungiyarsu ta Al’ummar Igala Musulmi reshen Unguwar Rimi Kaduna, za ta ba da gudunmawa sosai wajen ganin an kammala ginin makarantar da ake yi. Tun da farko da yake ba da tarihi da irin nasaroin da makarantar ta cimma zuwa yanzu, Shugaban Gudanarwar Makarantar, Sayyid Abdulrazaq Yahuza Jere wanda har ila yau shi ne Editan LEADERSHIP A Yau Juma’a, ya ce duk da ximbin qalubalen da makarantar take fuskanta, ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da cusa wa yara ilimi mai amfani da kuma kyakkyawar xabi’a. “Marigayi Malam Haruna Allah ya qara ma sa rahama ya kafa makarantar a shekarar 2004. Xalibai biyu ya fara yayewa a karon farko. Wannan biki da muke yi a yau shi ne karo na huxu. A wancan karon da muka yi sauka mun yaye xalibai 11, a yanzu kuma ga shi muna yaye 16. Wannan ya nuna cewa mun samu cigaba. Malaman da suke koyarwa a makarantar nan ba mu da
abin da za mu ce musu sai dai Allah ya saka da alkhairi. “Da saboda kuxi suke koyarwa ba za su yi ba. Domin akwai daga cikin iyayen yaran da ake bin su bashin kuxin makaranta na wurin shekara guda cur! Kun ga kenan da don kuxi suke yi wallahi ba za su tsaya ba. Ina amfani da wannan damar wurin yin kira ga iyaye su riqa biyan kuxin makarantar ‘ya’yansu a kan kari”, in ji shi. Shugaban ya nunar da cewa ba ilimi kaxai ake koyar da xalibai a makarantar ba har da cusa musu tsoron Allah da kyakkyawar xabi’a inda ya buga misali da cewa, “daga cikin xaliban makarantar nan da muka yaye akwai wanda ya samu aikin soja. Alhamdulillah lokacin da aka tura su Gambiya da sallar layya ta riske su a can shi ne ya yi musu limancin sallar idi. Kuma a wannan makarantar ya yi karatu ba wata ba. Kun ga da ilimin da ya samu mara inganci ne ba za su amince ya yi musu limanci ba, ko kuma da sun gan shi da muguwar xabi’a ba za su yarda ya jagorance su ba. Muna faxar wannan ba domin alfahari ba ne sai don gode wa Allah (SWT) domin ya ce idan ya yi mana ni’ima mu bayyana. Alhamdulillah”. Sayyid Abdulrazaq ya kuma nunar da cewa baya ga fannin karatu, har ila yau suna da qudirin kafa sashen koyar da sana’o’i na makarantar kamar yadda wanda ya kafa makarantar
yake da burin yi kafin rasuwarsa. Inda ya yi kira ga al’umma su zuba jarinsu a cikin aikin don Allah. Ya gode wa waxanda suka baiwa makarantar masauki a layin Rafindaxi da ke Unguwar Rimi Kaduna bayan an tashe su daga inda suka fara karatu a kan dalilin zikiri. Har ila yau, ya gode wa dukkan waxanda suka halarci taron da kuma waxanda uzuri ya tare su, “muna godiya ga kowa da kowa musamman Alqalin Alqalai na Kaduna, Dakta Shehu Ibrahim Ahmad, da Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Qasa, Alhaji Muhammad Babandede, da Mai ba da shawara ga Gwamna el-Rufa’i Malam Hafiz da sauran manyan baqi duk Allah ya san ku; ya san kun zo. Allah ya saka wa kowa da mafificin alkhairi”, ya bayyana. Daga bisani Shugaban malaman makarantar, Malam Usman Adam ya bayyana xaliban da suka fi qwazo a cikin waxanda aka yaye kamar haka: “Asiya Ya’u ita ce ta zo ta xaya, sai Sani Isah ya zo na biyu, Sa’idu Lukman kuma ya zo na uku”. Alqalin Alqalai Dakta Shehu Ibrahim Ahmad ya miqa wa dukkan xaliban da aka yaye takardun shaidar karatu da kyaututtuka sannan ya miqa wa manyan baqi kalandar makarantar. Taron ya kammala cikin lumana da kwanciyar hankali.
16
Siyasa A Yau A Yau
Litinin 9.4.2018
Ba Za Mu Amince Da Naxin Kamakarya Ba A PDP –CBSPS Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Biyu bayan wata bayanin da wasu waxanda suka kira kansu masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasa a jihar Bauchi wanda suka bayyana cewar sun amince wa tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, Bala Muhammad Kauran Bauchi da ya tsaya a matsayin gwamnan Bauchi qarqashin jam’iyyar PDP a zaven 2019 wanda suka wallafa a wata jarida. Masu faxin hakan sun ce shi kaxai suka amince masa da ya fito neman gwamna, wasu kuma suna ganin hakan karantsaye ne wa dokokin qasa da kuma na jam’iyyar a bisa haka ne suka yi suka mai qarfi kan lamarin. Wasu waxanda suka kira kansu da cewar su kuma masu ruwa da tsaki ne kuma waxanda suka damuwa da sha’anin jam’iyyar PDP ne a jihar Bauchi wato ‘Concerned Bauchi State PDP Stakeholders’ sun yi suka kan wannan lamarin, inda suka ce ba daidai ba ne wasu su fito su mara wa xan takara xaya tilau baya, alhalin ko zaven fidda gwamni jam’iyya ta yi ba. Sun bayyana matsayarsu ne a taron da suka yi a sakatariyar NUJ Juma’ar nan da ta gabata, Maijama’a Mohammaed Bununu shine ya yi magana a madadin haxakar masu ruwa
da tsaki a jam’iyyar inda ya bayyana cewar suna ganin wannan matakin a matsayin wata shiri na yin kama da kuma karya, don haka ya ce dole ne su yaqi shirin xaura musu wani a maimakon a bari jama’a su zavi wanda suke so. Maijama’a ya ce, “Inda jama’a ne magoya bayansa ko wasu masu ra’ayinsa suka bayyana wannan da ba za mu damu ba; amma a ce wasu qungiya masu ruwa da tsaki kan siyasa a jihar Bauchi dole mu damu. Amma a cikin waxanda suka sanya hanu kan wannan takardar har da shuwagabanin jam’iyyar PDP, wannan ya sanya muka ga hakan ya sava wa ainuhin manufofi da tsarin jam’iyyar PDP, a kowani marhala ba a amince wa shuwagabanin jam’iyya su nuna fifiko ko banbanci tsakinin yan takara ba,” Ya qara da cewa, “Abun da muke suuka a nan shi ne, waxanda jam’iyya ta tsara ta basu dama wato ‘Delegate’ sune ke da alhakin zaven xan takara, ka ga an yi musu katsalandar, ka fito ka ce ka zavi wane, alhali ga waxanda jam’iyya ta amince musu da wannan aikin sune, kai lokacin yin ma bai yi ba, kuma ba a gama fitar da masu son tsayawar nan ba; kawai ka zo ka ari bakinsu ka ce ka tsaida wane muna ganin
wannan ya sava wa doka,” In ji Shi. Ya nuna takaicinsa kan yadda uwar jam’iyyar ta qi zuwa domin barranta daga wannan “jam’iyya kamar yadda na faxa a baya, da muka samu wannan lamarin mun tuntuvi jam’iyya muka ce mata mene ne ke faru, sai jam’iyya ta ce mana za su fid da jawabai daga vangarensu, suka nuna mana kamar ba da yawunsu aka yi ba; amma fa da sanya hanun wasu daga cikinsu,” Bununu ya ce dole ne su tsaya har sai an bi qa’idar da PDP take tafiya a kai “Ai jam’iyyar ta fi qarfin shugaba, mune muka zavesu, don haka za mu zauna a cikin jam’iyyar mu tabbatar da an bi abun dokar jam’iyya ta ce,” Ya bayyana cewar ba wai varakace ke neman kunno kai ba, illa dai son zuciya da wasu ke qoqarin shigowa da ita wanda a cewarsu ba za su lamunci kowani mai neman kawo musu barazana ba. “Dukkanin xan jam’iyyar PDP a kowace mazava manufarsa shine yana tare da sabon tsarin bin doka da tarbatar da adalci, don haka masu bin wannan matakin suna bayan matakinmu,” A cewar shi. Ya bayyana cewar suna kira ne ga shuwagabanin jam’iyyar da su fito su bayyana wa duniya
•Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus
cewar ga haqiqanin zance kan wannan batun domin wanzar da adalci “mu ba muna maganar wai wani xan takara bane, a’a muna maganar a bi
dokar jam’iyya ne, shi ya sa ma mu ba mu ga alfanun su ma shuwagabanin su fito su mara baya wa wani mutum xaya ba.” A cewar Mai jama’a Bununu.
KASOSA Za Ta Iya Fidda Shugaban Qasa –Wali Daga Mustapha Ibrahim, Kano
Shugaban Qungiyar KASOSA ta qasa, Alhaji Mustapha Wali ya bayyana cewa Qungiyar ta tsofaffin xaliban Kimiyya da fasaha ‘Kano Science Old Students Association’ za ta iya fid da shugaban qasa dama sauran muqamai da ake riqe wa a faxin duniya. Alhaji Mustapha Nuhu Wali yayi bayanin hakan ne a lokacin wata hira da manema labarai bayan kammala taron qungiyar da ake yi duk bayan wata uku wanda ya gudana a babban ofishin qungiyar na qasa dake Kano, a wannan lokacin.
Wali ya ce, wannan qungiya tana da duk wani nau`in ilimi da ma`aikata a kowanne fanni, a kowanne mataki, a kuma kowacce ma`aikata da ke qasar nan har ma da waje. Inda ya ce a ciki akwai likitoci, Injiniyoyi maza da mata `yan jarida sauran masu riqe da muqaman siyasa tun daga kan Gwamna, mataimaki kwamikshinoni, yan majilisu a kowanne mataki shugabannin qananan hukumomi dana ma`aikatu da dai sauran su don haka wannan ya nu na KASOSA za ta iya fitar da shugaban qasa a cikin ta kuma yayi Nasara, bisa baiwar ilimi da gogewa da ya ba mambobin KASOSA a Nijeriya.
Haka kuma ya koka akan yadda gwamnatocin qasar nan suke fifita kamfanonin waje wajen ba da aikin gine-gine hanyoyi da Gadoji da sauran gineginen ma`aikatu da sauransu. Don haka ya qalubalanci hukumomin qasar nan akan cewa Injiniyoyin qasar nan zasu iya yin komai mai inganci don haka a daina fifita baqi akan `yan gida, domin xorewar tattalin arziqi da samawa xumbin matasan mu aiki inda yace qungiyar na tallafawa marayu ta kowacce fuska na `ya`yan qungiya inda ko a bana sun samawa marayu 17 takardun shiga makaranta da kumaxaukar nauyin karatun su
a matakan karatu daban-daban. Ita kuwa kallabi tsakanin Rawuna Injiniya Hajiya Ramatu Aminu Ahmad `yar kwamitin amintattu a KASOSA kuma shugabar qungiyar mata injiniyoyi ta farko a Kano, xaya daga cikin Daraktocin a Jami`ar maitama Sule da ke kano ta ce wannan qungiya tasu ta samu nasarar cusama xalibai mata sha`awar karanta wannan fanni na Injiniya ta hanyar binsu makarantu da kuma wayar musu da kai, inda kuma ta bayyana akaicin ta akan yadda shugabannin qasar nan a kowanne mataki basu da wani tsari na tallafawa yaran mu
masu basirar qere-qere a qasar nan, musamman yaran arewa da Allah ya basu basira da kaifin kwakwalwa fiye da takwarorin sun a wani vangare aqasar nan. Injiniya Ramatu Aminu Ahmad ta ce yanzu haka a wannan qungiya tasu ta KASOSA ta ba da kundin shawarwari ga Gwamnati za`a bunqasa ilimin Kimiyya da kuma tallafawa yara masu basirar qere-qere domin cigaban qasa, ta ce kamar yaron ya qera injin bada hasken wutar lantarki mai aiki awa 24 ba tare da qara ba da sauran yara masu basira suna buqatar kulawa ta musamman daga masu kishin al`umma da qasa.
TATTAUNAWA 17
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Jam’iyyar APC Ta Zo Ne Domin Ceto ’Yan Nijeriya -Ibrahim Ago IBRAHIM GAMBO KOBI, wanda aka fi sani da Ibrahim Ago yana xaya daga cikin ‘ya’yan Jam’iyyar APC waxanda suka yi tsayuwar daka wajen kafa ta, tun daga matakin haxaka ‘Maja’ har zuwa yau, kuma ya kasance a kowanne lokaci kan qoqarin ganin ba a samu wata matsalo ko varaka a cikin jam’iyyar ba, yana daga cikin waxanda suka yi qoqarin kawo qarshen ta matsala da ta kunno kai a jam’iyyar APC a jihar Bauchi kwanakin baya. A hirarsa da LEADERSHIP A YAU ya bayana cewar jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta yi nasarar ceto Nijeriya daga shirin rugejewa, ya kuma bayyana dumbin nasarorin da ya ce shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya cimma a wannan shekaru uku da suka yi a bisa qaragar mulkin jihar, ya kuma yi tsokaci kan gwamnatin jihar Bauchi da qoqarin da M.A ke yi a jihar, ya kuma yi hasashen sake lashe zave a 2019 da APC ya ce, za ta yi. KHALID IDRIS DOYA ne ya tattauna da shi kamar haka: Mai karatu zai so sanin da wanda muke tare? Suna na Ibrahim Gambo Kobi, wanda ake kira na da Ibrahim Ago. Me za ka iya cewa a kan jam’iyyar APC a matakin qasa da jihar Bauchi ganin cewar shekaru uku kenan jam’iyyar tana jan ragamar mulki? Zan fara ne da godiya ga Allah, Alhamdullahi! Dukkanin godiya ga Allah. Jam’iyyar APC wata jam’iyyar APC da ta haxu waje guda domin ceto ‘yan Nijeriya, abun da ya sanya na faxi hakan nan kuma shi ne, qasar Nijeriya ta shiga wani irin hali da yanayi a wancan lokutan baya, shekarun da suka shuxe. Wannan ne ya sanya masu kishin qasa da son fidda Nijeriya daga halin Ni-’yasu suka yi haxawa ‘Maja’ domin ceto jama’an qasa da qasar baki xaya, an yi majan nan ne da irin jam’iyyu kamar CPC, ANPP, ACN suka zama sun haxu waje guda inda aka samar da jam’iyyar APC. APC ta cimma nasarori da daman gaske a cikin wannan shekaru ukun. yanzu kamar dukkanin jahohin da suke Nijeriya akwai jahohin da sukan haxa wata 9 wasu ma shekara ba tare da biyan albashi ba; amma ka ga jam’iyyar APC, Shi mai girma shugaban qasar Nijeriya Janaral Muhammadu Buhari bai yarda da irin wannan tsarin ba. dukkanin jahar da aka bata kuxi ana qoqarin sai ta biya albashi; basussukan da ake bi a baya ma APC ta himmatu wajen biya. Kamar yanzu jiharmu ta Bauchi, ma’aikata basu binmu bashin albashi koda na wata xaya ne kuwa, kuma ba a tava kaiwa wata ya zo kwana 30 ba tare
da biyan albashi a jihar Bauchi ba, mai girma gwamnan jihar nan iyaka qoqarinsa wajen ganin ya sauqe wannan nauyin albashin ma’aikatan da suke aiki a jihar tun daga matakin jiha da na qananan hukumomi. Hatta masu amsar fansho babu watan da zai qare masu amsar fansho basu samu kuxinsu ba, ka ga sai godiya wa Allah. Malam baya wannan fannin, in ka duba fannin tattalin arziki ai ba a ma yi magana domin an samu gagarumar ci gaba, fannin tsaro da kuma toshe kafar sata da sauransu, kuma ana ci gaba da samun ci gaba a wasu janibobin. za mu ce Alhamdulla, an samu nasarori sosai daman ba za ka ce daga kama mulki komai ya tafi yadda kake so ba, kamar juyin mulki ne, ba wai daga lokacin da ka yi juyin mulki kuma sai komai ya dawo daidai ba, a’a da kaxan-kaxan ne har a samu gyara ababuwa da dama, wannan dalilin ne fa ya sanya wasu ke cewa shugaban qasar Nijeriya yana tafiya a hankali ‘slow’, wannan tafiyar da yake a nutse a hankalin ita ce ke bashi dama yana gyara abubuwan da ba za wuce shi daga baya kuma ka zo ka sake dawo masa ba. an samu sosai a qarqashin mulkin APC kawo yanzu. Duk da nasarorin da kai kake faxi, wasu ‘yan qasar nan suna qorafi sosai a kan wannan jam’iyyar taku ta APC me za ka ce kan masur qorafin nan? Idan ka ji mutum na kuka akan abubuwan da ake yi yanzu a qasar nan, qila shi a baya yana cikin wasu mutane ne da suka kasance ‘yan kama wuri zauna, a xauki dukiyar qasa kawai ana basu ba tare da na qasa na amfana ba.
• Ibrahim Gambo Kobi
bar na dawo maka da baya, fannin makarantu a qasar nan yanzu yaran da suke zuwa makaranta waxanda suke qin zuwa a da baya yanzu suna zuwa, adadin masu zuwa makaranta ta ninku saboda gwamnati ta waiwayi fannin ta ce ana son yaran nan su yi karatu, don haka ne gwamnati ta tsara yadda za a ke baiwa yaran abinci kyauta wanda hakan zai ke jawo hankulansu zuwa ga makarantu, ana kulawa da su, idan ka dawo ka duba sha’anin lafiya a qasar nan, yana samun ci gaba fiye da yadda zan misalta maka, domin a da baya komai fa ya tashi rugejewa ne a qasar nan. Duk wanda ka ji na cewa gwamnatin APC ta qasa walllahi shine ya gaza, dalilina kuwa na faxin haka shine sun saba raba dukiyar jama’a a xaki, don haka wannan gwamnatin kuma ta ce ba ta yarda da wannan ba, ba ta lamunta ba, kana zaune kawai a xauki kuxin jama’a ana raba muku, shugaban qasa na xaukan kuxi na kaiwa wa wannan dakacin ko wani basarake, ko kuma gwamna ya kwashi kuxin al’umma
wani na zaune kawai a cikin gidansa a xauki abun da za a yi amfani wa jama’a sama da dubbai kawai a ce an bashi shi kaxai, matuqar ka jiyo mutum na qorafi to na cikin irin waxanan mutune ne waxanda ba gyaruwar qasar ne a gabansu ba. Wasu ma fa suna ganin kamar Muhammadu Buharin nan ya gaza ne gaba xaya ba zai iya shugabancin qasar nan ba? Wallahi bai gaza ba; shi shugabanci da ka ganshin nan, kai mu gode wa Allah ma da Allah ya kawo mana Janaral Muhammadu Buhari, domin shi ba mutum bane azzalumi, ba varazo ka marar gaskiya ba ne. inda a ce maka qasar nan ta sake faxawa a hanun azzalumai marasa gaskiya da ba Buhari ba ne, wallahi da mun sanya hanu a kayi mun yi ihu. Ina son ka gane wani abu xaya, akwai mutanen da suke zaune a gida kamar yadda na faxa maka, wai su ‘yan qasar nan ne da su aka kafa qasar nan wanda sun handame rijiyan man qasar nan,
Ci gaba a shafi na
27
18
RAHOTON MUSAMMAN
A Yau Laraba 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Tashin Hankali Dangane Da Yadda Likitocin Nijeriya Ke Barin Qasar Wannan rahoto ne wanda kafar sadarwa ta PREMIUM TIMES ta wallafa, kuma wakilinmu ABUBAKAR ABBA ya fassaro mana domin amfanin masu karatu. Rahoto ne na yadda qwararrun likitocin Nijeriya suke arcewa daga qasar zuwa wasu qasashen qetare, domin an can qasashen wajen an fi kiyaye haqqoqinsu, musamman a vangaren albashi. “Kwanakin baya a Otal xin Hawthorn dake Abuja na haxu da maza da mata matasa likitoci waxanda za su kai su 200. Ko da na tuntuva sai aka ce min ai wasu jami’ai ne daga qasar Saudiyya suke yi musu intabiyu, don tantance waxanda za a xauka aiki qasar ta Saudiyya. “A karon farko na xauka taro ne ake gudanar wa a otel xin, inda na kai wa wani baqo na ziyara. “Na ga wani xan qasar ta Saudiyya ya na yi wa dandazon likitocin bayani, inda na jiyo shi yana faxi da qarfi cewa; ku je ku dawo gobe. “Na yi qoqari na tambayi wata mata da ta qagara tana jira, hannunta riqe da fayil, na tambaye ta meke faruwa? Matar ta ce mini dukkansu qwararrun likitoci ne da suka zo otel xin tun qarfe bakwai na safe don a yi masu intabiyun xaukar aiki kuma sama da 100 sun samu nasara. Sauran an ce su dawo gobe don a ci gaba da yi masu tambayoyi.” Wannan bayanin wani Malami ne a Jami’ar Maiduguri, mai suna Shehu Liberty ya yi a ranar 31 ga watan Janairun 2018, inda ya rubutawa Shugaban qasa Muhammadu Buhari buxaxxiyar wasiqa a turakarsa ta ‘Facebook’, inda ya ke roqon Shugaban da ya dakatar da yawan hana fitar qwararrun likitocin qasar nan zuwa qasashen waje. Shehu Liberty ya ci gaba da cewa, ”ga alamu tuni likitocin sun yanke shawarar barin qasar duk da qoqarin da ya yi na jan ra’ayinsu na su fasa fitar.” Shin mene ne ba ya tafiya daidai akan fannin kiwon lafiyar Nijeriya da har hakan ya janyo qwararrun likitocin suke yin watsi da qasar nan don yin aiki a qasar Saudiyya? Shin mene ne ya sa ba za a xauke su aiki a sauran matakan gwamnati dake xaukacin qasar nan ba? Na tabbatar ana buqatar aikin su a mafi yawancin karkara dake qasar nan. An sha kawo rahotanni
akan yadda ake samun yawan naqasu a kan harkar kiwon lafiya a shekarun da suka gabata ganin yadda likitoci a qasar nan suke fitar Farin xango zuwa qasashen waje a kai - a kai. Binciken da aka gudanar ya nuna cewar, Likitocin Nijeriya suna ta fita zuwa qasashen Amurka da Kanada da Saudiyya da Birtaniya da kuma sauran qasashen duniya. Hukumomin kiwon lafiya dake qasar nan dabandaban ba su iya samar da bayanai a hukumance akan qwararrun Likitocin da suke yin balagoro zuwa qasashen waje. Amma watan Yulin 2017 qididdiga daga Hukumar Kiwon Lafiya (GMC) dake qasar Birtaniya ya nuna cewar, sama da qwararrun Likitoci ‘yan Nijeriya su 4,765 a yanzu suna aiki a qasar ta Birtaniya. Wannan shi ne kashi 1.7 bisa xari na jimillar qwararrun Likitocin dake aiki a qasar Birtaniya. Wannan lamarin ya jima yana kawo wa harkar kiwon lafiyar Nijeriya naqasu. Sakamakon hakan ne qwararru suka yi ittifaqin cewar Nijeriya tana fuskantar taskun qarancin qwararrun likito a mafi yawancin Asibitocin dake qasar. Bugu da qari, qwararrun sun ce yawan qwararrun Likitoci dake duba marasa lafiya a Asibitoci sun yi qaranci. Bayanai a hukumance sun bayyana cewar a yanzu Nijeriya Likita xaya ne yake duba marasa lafiya 3, 500 a qasar,inda hakan ya savawa shawarar da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi na Likita xaya marasa lafiya 600. Dalilan Da Likitocin Dake Barin Nijeriya Suke Bayar Wa: Wani qwararren Likita xan Nijeriya dake aiki a qasar Birtaniya Ayokunle Michael ya ce, yanayin yadda Likitocin suke ficewa daga Nijeriya har yanzu bai qazanta ba, amma nan bada jimawa ba zai qazanta sosai”. Ya ce, ganin yadda qasar Birtaniya take buxewa qasashe rainon (commonwealth) kuma likitoci Nijeriya da dama suna samun bayani akan yadda ake baiwa Likitoci kulawa da samun albashi mai tsoka a can, da yawan su za su fice zuwa can. “Nijeriya ta sani za ta qara rasa qwararrun Likitoci, inda mafi yawancin su za su fice zuwa qasar Saudiyya wannan wani xan somin tavi ne. Mafi yawancin su suna
harin Amurka da Birtaniya da Australia da Kanada da sauran qasashen dake nahiyar turai ne, inda ake samun damar samun aiki.” Mista Michael ya ci gaba da cewa, yanayin aikin Likita a Nijeriya yana qara tavarvarewa. “Na bar qasar nan kimanin shekaru shida kuma kafin in fice, na yi faxi tashin neman aiki bayan na shafe kusan shekaru tara a makaranta ba tare da faxuwa ba. Na bar qasar nan bayan ta yi tsanani kuma kuma damar ta kawo kanta da kanta. Wasu abokan aiki na sun yi amfani da damar wasu kuma sun yanke shawarar tsayawa. “Wasu daga ciki waxan da basu fita ba suma za su fice domin yanayin na qara tavarvarewa”. Wasu abokan aiki da dama da suka shiga aikin a shekarar 2010, har yanzu basu samu wani aiki takamai mai ba. Mista Michael ya kuma koka akan yadda ake tsawwala tsadar rubuta jarrabawar kiwon lafiya a Nijeriya. ” Kuxin da ake biya a matakin zana jarrabawar (National Postgraduate College of Nigeria) ko ta (West African Postgraduate College) yana qara yin tsada. Haka tashin farashin dala baya taimakawa ya qara da cewa, har yafi sauqi a Birtaniya wajen rubuta jarrabar (PLAB) wadda mutum yana da dahir xin rayuwa mai kyau a nan gaba yafi kashe kuxi irin wannan kuxaxen akan zana jarrabawa wadda za ta kasance bata da wani amfani.”
Rashin Adana Bayanai: A lokacin da wakilin kafar Premium Times yake haxa wannan rahoton duk iya qoqarin da aka yi don samun qididdiga a hukumance akan qididdigar yawan Likitocin dake aiki a qasar nan da kuma waxanda suka fice daga hukumar kula da lafiyar haqora ta qasa (MDCN), hukumar dake sanya ido akan sana’ar a Nijeriya, babu wata cin nasara. Har ila yau, yawan ficewar da Likitocin suke yana qara zama darasin tattaunawa akai a qasar nan, inda jami’an kiwon lafiya na qungiyar suke ta samar da alqaluman dake cin karo da juna akan ‘yayan ta musamman waxanda suke ficewa daga Nijeriya domin neman aikin mai tsoka. Hukumar (MDCN) hukuma ce da aka xora mata ragamar yin rijista da sanya ido akan sana’ar aikin Likita a Nijeriya. Hukumar yana daga cikin ayyukan ta an kuma xora alhakkin yiwa sababbin Likitoci rijista da sabunta lasisin su da kuma adana bayanan Likitocin ‘yan Nijeriya da suka fice zuwa qasashen waje. Har ila yau, hukumar yana daga cikin ayyukan ta wajen adana bayanai Likitoci ‘yan qasar waje da suke shigo Nijeriya. A wasiqar da kafar yaxa labarai ta Premium Times mai xauke da kwanan watan huxu ga watan Disambar 2017 ta rubutawa hukumar ‘MDCN na buqatar neman yawan adadin
Ci gaba a shafi na
19
A Yau
Laraba 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
RAHOTON MUSAMMAN 19
Tashin Hankali Dangane Da Yadda Likitocin Nijeriya Ke Barin Qasar Ci gaba daga shafi na
18
Likitoci ‘yan Nijeriya da a yanzu suke yin aiki a Nijeriya da kuma yawan adadin waxanda suka fice. Kana jin mafi yawancin su za su sake lashe waccan jarrabawar? Me ya sa zamu vata lokacin a nan gida Nijeriya, akan yadda ake yiwa abokan aikin mu, inda hakan ya sanya suke ficewa daga qasar?” Da yake jawabi akan qasar da ya zava Mista Babajide ya bayyana cewar, ya fi son ya je Birtaniya ko Amurka ganin cewar suna baiwa Likitoci aikin da yafi kyau”. Binciken da qungiyar (NOIPolls) ta gudanar tare da haxin gwaiwar Qungiyar Kiwon Lafiya ta qasa ta sanya ido(NHW) a cikin watan Agustan 2017, ya nuna cewar. Kimanin takwas daga cikin goma na qwararrun Likitoci a yanzu suna neman aiki a qasashen waje. Wannan bincikin ya karaxe dukkan tsakanin qanana dana tsakiya da manya ako wanne matakai na gwamnati dana masu zaman kansu. Mafi yawancin su sun yi rijista don zana jarrabawa kamar ta (PLAB) ta Birtaniya a bisa kashi 30 data (USMLE) ta Amurka mai kashi 30 data (MCCE) ta qasar Kanada data kashi 15 ta AMC ta qasar Australia da kshi 15 ta DHA ta qasar Dubai da kuma kashi 10 na sauran qasashe. Har ila yau, an qara turawa
hukumar matsahiya akan dokar data bayar da damar samun bayanai ta (FOI) a cikin watan Janairu inda aka buqaci neman bayanai akan rahoto. Sai dai, bayan watanni huxu dokar ta neman bayana ta farko an miqawa hukumar(MDCN), babu wani martani duk da yawan tattakin da wakilin na kafar ta Premium Times ya yi zuwa hukumar. Wani jami’I a hukumar ta (MDCN) ya shedawa Premium Times cewar, hukumar ta yiwa kimanin qwararrun Likitoci su 80,000 da kuma Likitocin haqora dake Nijeriya da kuma qwararru na qasashen waje tun lokacin da aka qirqiro da hukumar a shekarar 1963. Daga cikin wannan adadin na 80,000, akwai waxan da suka mutu wasu kuma sun fice zuwa qasashen waje wasu basa aiki a matsayin Likitoci a yanzu wasu kuma sun dakatar da sabunta lasisin aikin su na Likita wasu kuma da suka tsufa a aikin, an basu takardar shaida ta ci gaba da gudanar da aikin har tsawon rayuwar su ba tare da ci gaba da sabunt lasisinsu a duk shekara ba. Ya ce ya kamata ace hukumar ta MDCN ta na da adadin waxanda suka fice daga qasar domin qwararrun Likitocin Nijeriya da suke son zuwa qasashen qetare kamar hukumar ta amince ne da hakan.
Har ila yau, kafar Premium Times ta yi tattaki zuwa qungiyar qwararrun likitoci ta qasa, (NMA),don neman bayanai akan Likitocin dake qasar nan da kuma waxanda suka fice qoqarin hakan ya ci tura ganin cewar mahukuntan qungiyar sun tura wakilin kafar zuwa ga hukumar (MDCN). Qungiyar ta (NMA), amma a martanin da (NMA) ta bayar a hukumance akan wasiqar data turawa Premium Times ta ce, irin waxannan bayanan ganin cewar ita qungiyar qwararru ce, qungiyar ta ce hukumar (MDCN) bata yin rijista kuma hukumar ita kaxai ce keda irin waxannan bayanai kuma ita ce ya dace ta bayar dasu.” A cewar qungiyar NMA, hukumar MDCN ce ke da alhakin adana bayanai da hukuntawa a saboda haka ita ce ke da bayanai akan hakan. Sai dai Shugaban qungiyar (NMA) Mike Ogirima, a martani maban banta ya bayyana cewar, koda yake (NMA) bata da qididdigar a hukumance akan kimanin 10,000 zuwa 15,000 na qwararrun Likitoci ‘yan Nijeriya dake aiki qasashen waje, inda kashi 90 bisa xari, a Nijeriya aka horar da su.” Mike Ogirima, Likitan qashi wanda ya bayar da qididdigar ta Likitoci daga 9000 zuwa 13,500 da aka horar a Nijeriya, amma a
yanzu suke yin aiki a qasashen waje. Ya bayyana cewar qwararrun Likitoci ‘yan Nijeriya da dama suna ficewa daga Nijeriya saboda rashin kyakwan yanayin aiki a asibitoci.” Muna buqatar gwamnati ta inganta yanayin aiki da samar da kayan aiki da suka dace ga Likitoci da qaea masu albashi.” Mista Ogirima ya ce, tuni qungiyar tana yin nata qoqarin don ta tanadi na ta qididdigar bayanan yayanta da suke aiki a Nijeriya ta hanyar gabatar da hatimi ga qwararrun Likitocin wanda ko wannen su zai kasance ya mallaka.” A jikin hatimin zai kasance yana xauke da sunan Likita da muqamin sa da lambar sa kuma wannan zai bayar da damar samun bayanan Likitocin dake qasar nan da kuma bankaxo Likitocin bogi.” Bugu da qari, Mista Ogirima ya bayyana cewar, za a tabbatar qwararrun Likitocin dake qasar nan, sun yi rijista da hukumar MDCN. Ya bayyana cewar, a “a qungiyar mu muna qoqari wajen taimakawa qoqarin da hukumar (MDCN) keyi ta hanyar gabatar da hatimi wanda zai zama dole akan dukkan bayanai don yin amfani dasu a qasar nan. Da wannan za mu samu damar tattara bayanai Kuma qungiyar ta (NMA) za ta
Ci gaba a shafi na
26
20
A Yau
CINIKI
Kasuwanci MASANA’ANTU
INSHORA
HANNUN JARI
Litinin 9.4.2018
KASUWAR SHINKU
Mata A Jihar Bauchi Sun Samar Da Hanyar Gargajiya Ta Sarrafawa Da Adana Tumatir
Daga Abubakar Abba
Mata a jihar sun samar da hanyar sarrafawa da kuma adana Tumatir a gargajiyance don sayarwa da kuma yin amfani dashi a abinci a gida. Binciken da aka gudanar ya nuna cewar, akwai waxanda suke sayar dashi don samun riba da kuma waxanda suke adana shi don yin amfani dashi a gida don rage kashe kuxi. A cewar wasu daga cikin matan aure da aka yi hira dasu, a Bauchi, hanyar sarrafa shi bata da wani wuya kuma xanxanon sa zai kasance yadda yake har tsawon watanni uku ko fiye da haka. Sun bayyana cewar, waxanda suke da ra’ayi, suna da zavin ko su shirya Tumatirin shi kaxaiko haxe da Tattasai tare kuma da haxa shi da Albasa. Wata matar aure Adama Balteh, ta bayyana cewar, hanyar sarrafawar ta
farko shi ne a sayi xanyen Tumatirin da yawa sannan a niqa shi aka kuma tafasa shi. Ta ce, idan an tafasa shi aka kuma niqa shi, bayan an cire dukkan ‘ya’yan dake cikin sa, sai kuma a wanke shi sannan a tafasa shi. A cewar ta,”mafi yawancin su ana zuba kwalben ruwa na salat wajen don wanke shi baki xaya da kuma tafasa shi har zuwa minti biyar. Ta ce, kwalaben da ba za da ba za su iya jurewa ba, za su iya tsagewa, inda kuma ba za a iya samun adadin da ake buqata ba. A na so a bar Tumatirin ya bushe gaba xaya sanna sai a zuba shi a cikin kwalaben sai a zuba Gishiri xan kaxan da kuma mai xan kaxan sai a rufe shi don kada qwayoyin cuta su shiga. Waxannan kwalaben suna xauke da Tumatirin sai a sake tafasa shi zuwa mintuna goma daga nan sai a cire a ajiye shi a wuri mai kyau don sayar dashi a
nan gaba da kuma samun riba har da rage abinda ake kashewa a gida a lokacin da ake qarancin Tumatirin. A cewar ta, kwando xaya ana sayar dashi akan naira 1,000 a lokacin da aka girbe shi a Bauchi, kuma zaka iya samun kimanin kwalabe goma na xanyen Tumatirin. Ita ma wata matar aure Saadatu Mohammed ta ce, ta jima a cikin sana’ar har sama da shekaru uku kuma bata tava samun wani savani ba. Ta ce, sana’ar za ta iya samar da kuxin shiga, amma abinda keda mahimmanci shi ne, mutum zai iya yin amfani da hanyar ta gargajiya don sarrafa shi da kuma adana shi a lokacin da ake qarancin shi kuma sannan za a iya amfani dashi a gida. Da take bayani akan mahimmancin sa, Rukayya Ibrahim ta ce, adana shin da ake yi a gargajiyance yafi Tumatirin gwangwani, sai dai ta yi gargaxi akan yadda
ake shirya shi da kuma killace shi sai an kiyaye. Ta ce, a duk lokacin aka samu akasin hakan ma’ana akwai matsalar da ta faru wajen sarrafawar,inda hakan zai janyo asara. Ita ma wata matar aure Hajara Jibrin ta ce, ta fara da Tumatir na naira 3,000,inda hakan ya bata damar samun ribar naira 7,000. A cewar ta,“ da naira 3,000 na fara, inda na samu samar da kwalbe ashirin kuma ko wacce kwalba xaya ta kai naira 500 zuwa naira 800 a lokacin da Tumatirin yake qaranci, inda har nake samun ribar a qalla naira 7,000.” An ruwaito cewar, a lokacin da ake qarancin shi, kwando yana kaiwa har naira 25,000 a jihar Bauchi. Waxanda suka rungumi sana’ar, suna kuma adana shi bayan sun girbe shi, inda suke sayar da kwando xaya daga naira 600 zuwa naira 1,000.
A Yau
Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
KASUWANCI 21
Dalilin Da Ya Sa Xangote Ya Fasa Gina Masana’antar Siminti A Kenya
Daga Abubakar Abba
Sanannen hamshaqin xan kasuwan nan dake Aliko Xangote ya soki shugabancin qasar Kenya akan nuna zalama da gazawa wajen sanya abinda ya shafi cigaban qasar a kan gaba. A wata hira da yayi da shahararren xan jaridar nan na qasar ta Kenya, Jeff Koinange, Xangote ya yi shelar janye shirin sa na gina babban kamfanin sarrafa siminti a Kenya bayan kuma ya kammala dukkan tattaunawar data kamata da mahukuntan qasar,inda ya danganta su a matsayin waxanda suka fi ‘yan Nijeriya cin hanci da rashawa. Hirar wadda aka yi ta a kafar gidan Radio mai matsakancin zanho Jeff ya kuma tavo fannin rayuwar ta Xangote a lokacin da ya halarci xaurin auren ‘yar hamshaqin xan kasuwan a Nijeriya a cikin watan da ya gabata. Jeff ya tambayi Xangote cewar, “Alhaji yaushe zaka dawo Kenya?,inda Xangote ya ce, ‘Jeff, akwai wasu wasu mutane a Kenya waxanda suka nuna zalama da kuma nuna ra’ayin qashin kansu sama da ra’ayin qasar akan gaba, kuma ina ganin Kenya tafi Nijeriya cin hanci da rashawa.” Mista Koinange, ya sanar da hakan a kafar ta gidan Radiyon.Xangote wanda wanda aka qiyasa ta zai zuba
jarin naira tiriliyan 1.5 akan aikin, ya kai ziyara a Kenyaa cikin watan Satumbar 2013 a cikin tawaga mai qarfi da ta qumshi hamshaqan ‘yan kasuwa ‘yan Nijeriya hamsin da
suka take masa baya a lokacin mulkin tsohon shugaban qasa Goodluck Jonathan. Hamshaqin xan kasuwar a kwanan baya ya tura kamfanin nasa zuwa a Kenya 2021,
bayan tunda farko ya shirya gina kamfanin sarrafa siminti a qasar a shekara mai zuwa. Xangote wanda aka sani yafi yin amfanin da qaramin farashi, don samun kasuwa a
sababbin kasuwanni sannan kuma ya vata lokaci wajen shiga kasuwannin, ya kan bayar da dama ga masu hadahadar dake a qasa a kasuwar da tuni ake samun gasa mai qarfi.
Gwamnatin Tarayya Ta Farfaxo Da Kamfanonin Sarrafa Takin Zamani 12 Da Suka Durqushe Daga Abubakar Abba
Gwamnatin Tarayya za ta farfaxo da kamfanonin sarrafa takin zamani guda sha biyu, inda hakan zai qara adadin kamfaninin zuwa ashirin da uku da za a sanya su a cikin shirin (PFI)na qara samar da takin a 2018 na fadar shugaban qasa. Ministan yaxa labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a jihar Legas, inda ya qara da cewar, an masana’antar sarrafa takin guda sha xaya dake da qarfin samar da taki sama da miliyan biyu, an gyara su. Ministan ya ci gaba da cewa,an samu nasara akan sarrafa taki sakamakon kafa samar da shirin na(PPI) da Shugaban qasa Muhammadu Buhari ya yi cikin watan Disambar 2016. Lai ya bayyana cewar shirin na(PFI), an kafa shine
don samar da ingantaccen taki mai yawa kuma akan lokaci ga manoman qasar nan. A cewar Ministan,“ shirin na(PFI) ya zama kamar wani baza ta akan sarrafa taki. Ya yi waiyaye da cewar, fanin aikin noma da kuma sarrafa abinci a qasar nan ya samu ci gaba ganin cewar a 2016, manoma samu sukunin wadata qasa da abinci da kuma samun ximbin riba. A cewar sa,“ a 2017 shirin na (PFI) ya samar da buhun taki samfarin NPK mai nauyin kilo giram hamsi miliyan goma wanda kuma aka sayar akan naira 5,500, savanin farashin naira akan ko wanni buhu xaya a 2016, inda hakan ya nuna an samar da rangwame kashi arba’in bisa xari. Ya bayyana cewar, a 2018 shirin na (PFI) yana da qudurin samar da taki tan miliyan ashirin don qara ruvanyya yawan na 2017.
Lai ya yi waiwaye akan cewar kafin qirqiro da shirin na(PFI), dukkan buhun taki xaya da ake shigo dashi, an samar da tallafi na naira 6,000. Ministan ya ce, a 2017, shirin ya adanawa gwamnati naira biliyan 60 akan samar da rangwame. Kuxin da aka tara a 2017 ya kai yawan dala miliyan 150, a saboda haka muna godiya akan rangwamen da gwamnati ta yi akan taki sunfurin NPK da ake shigowa dashi. A cewar sa, sinadarin (limestone) da na taki sunfurin urea, ana samun su a cikin gida,inda kuma ake shigo da sanadarin (phosphate) daga qasar Morocco kanwa kuma ake shigo da ita daga nahiyar turai. Lai ya ce shugaba Buhari da kansa ya shiga haxakar ta dogon zango akan yarjejeniyar sawo sanadarin (phosphate) da Sarkin qasar
na Morocco da kuma tawagar sa. Da yake qara yinbayani akan sauran amfanun tsarin na(PFI), Lai ya ce, sama da buhu miliyan shida na taki aka sayarwa da manoma akan naira 5,500 na ko wanne buhu. Ya bayyana cewar, a yanzu an samu qarin hanyar layin dogo a qasarnan, inda hakan ya samar da sukunin dagon kaya da kuma kayan da aka sarrafa. Minisatan ya ce, hakan ya kuma qara havaka tattalin arzikin qasar sakamakon samar da sama da buhun taki miliyan goma da aka sarrafa a qarqashin shirin na(PFI). A cewar sa, a qarqashin shirin, an samar da ayyuka kai tsaye har 60,000 da kuma qirqirar sauran ayyukan yi. A qarshe ya jadda da qudurin gwamnatin take yi akan akan samar da isassen taki da kuma farfaxo da aikin noma a qasar.
22
Kiwon Lafiya
A Yau
Litinin 09.4.2018
Kiwon Lafiya: WHO Ta Shawarci ’Yan Nijeriya Kan Motsa Jiki Daga Idris Aliyu Daudawa
Yayin da ake bikin ranar lafiya ta duniya Hukumar lafiya ta duniya ta yi kira ga ‘yan Nijeriya, da suyi koyi da al’adar nan ta motsa jiki. Dokta Wondimagegnehu Alemu shi ne wakilin Hukumar lafiya ta duniya mai kulawa da ofihin Nijeriya, shi ya bayyana hakan da yake bayani, lokacin da ake tattakawa domin samun lafiya, wadda Hukumar lafiya ta duniya ta shirya, saboda tayi bikin ranar lafiya ta duniya, wannan shekara ta 2018, wanda aka yi ranar Asabar a Abuja. An dai ware ranar 7 ga ko wane wata na Afrilu a matsayin ranar lafiya ta duniya, taken wannan shekarar shi ne ‘’Lafiyar duniya gaba xaya, ga kowa da kuma kmo ina.’’ Ya ba ‘yan Nijeriya shawarar domin su kasance cikin qoahin lafiya, akwai buqatar su riqa tafiya ta a qalla, minti talatin, sau uku ko wane mako. Da akwai kuma buqatar ta a canza yadda ake tafiyar da
rayuwa, kamar cin abincin da ya kamata, da kuma motsa jiki, zai taimaka wajen maganin wasu cututtukan da suke yi wa mutane barazana. Su dai cututtukan sun haxa da kansa, hawan jini, ciwon sikari, da dai sauransu. Ya ci gaba da cewar ‘’Na baku shawarar da ku mayar da abin kamar wanda zaku yi ne kullun, na a qalla mutum ya yi tafiyar minti talatin, sau uku ko wane mako’’. ‘’Al’amarin lafiya ba wai ya tsaya bane ya kasance sai idan babu wata cuta ne, maganar lafiya ta qunshi, mutum ya kasance yana cikin walwala, ba wani abin daya shafi lafiyar hankalin sa, kuma surar jikin shi ta kasance ita ma cikin lafiya’’. ‘’Da yake mun yi wannan tafiyar yau, mun yi wani babban al’amari, wanda zai sa mu kasance cikin qoshin lafiya, ina mai kira gareku da ku riqa yin hakan’’. ‘’Babban dalilin da yasa aka yi wannan motsa jiki shi ne, ba ka wai ana buqatar ko wane xan qasa
ba ne, ya riqa zama cikin lafiya, amma an yi hakan ne domin a tunatar da gwamnatin tarayya, akan cewar hakkin tane na, tabbatar da akwai isassun wuraren da za a kula da lafiyar al’umma.’’ ‘’Hukumar kula da inshorar lafiya ta qasa gwamnati zata yi amfani da ita, a matsayin wani mataki wanda zata yi amfani da shi, wajen da kula da lafiya masu qyau, wannan kuma duk inda mutum yake ya kamata ace ana kulawar ada shi’’. ‘’Gwamnatin tarayya ana buqatar data taimakawa shi tsarin da kuma saurar Hukumomi na lafiya, wajen gudanar da ayyukansu, wajen amincewa da kasafin kuxi, ta hakan za su samu damar aiwatar da ayyukansu’’. Wakilin Hukumar lafiya ta duniya mai kulawa da afishin Nijeriya, ko wane xan qasa yana da dama, ta ya samu, a kula da lafiyar shi, domin haka shugabanni ya kamata su, kula sosai da kuma maida hankali . akan lafiyar al’umma, wadda
zata kasance abu ta farko. Aremu ya qara jaddada cewar Nijeriya ta samu ci gabawajen qoqarin da take,na samar da tsare tsare, saboda samun cimma daidaito, dangane da tsarin kula da lafiya na duniya, nan da zuwa shekara ta 2030, ta hanyar inganta wuraren kula da lafiya. Aremu ya yi qarin bayani na cewar ‘’An xauki mataki da kuma yin dukkan wasu abubuwan da suka kamata ayi, domin tabbatar da Nijeriya ta shiga cikin sahun qasashen duniya, da za su kai gaci , dangane da cimma ingantacciyar lafiya nan da shekara ta 2030. Babban muradin cimma ingantacciyar lafiya nan da shekara ta 2030 shi ne saboda a kare mutane, daga matsalar da za su iya shiga, wajen biyan kuxin kula da lafiyarsu, da aljihunsu, wannan shi ne zai kare su daga shiga quncin fatara. Ma’aikatar lafiya ta tarayya tare da taimakon abokan sun zayyana hanyar da za a bi domin cimma ingantacciyar lafiya nan da shekara 2030.
KIWON LAFIYA 23
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Batun Daqile Abubuwan Da Ke Saurin Kashe ‘Yan Nijeriya (I) Daga Idris Aliyu Daudawa
Lokacin da aka qaddamar da kantin sayar da magani na St Racheal a Lagos wanda aka yi bada daxewa ba, ya bayyana abubuwa, akan dalilan da suka sa, qasar Nijeriya ta kasance qasa ta qarshe, duk kuwa da yake tana arziki daya qunshi albarkatun qasa , da kuma al’ummarta waxanda suke da fasahada basira da basu misaltuwa. Yayin da Nijeriya take ci gaba da xaukar kanta a matsayin wadda it ace uwa ma bada mama a Afirka, wadda take da fiye da dala bilyan 400 a matsayin kuxaxen da suk shigo mata, amma kuma sai ga yadda rayuwar ‘yan qasar take kasancewa, wato yaan shekarun da mutane ke yi, abin har yaqnzu yana xaure kai, idan ka yi la’akari da yadda ita Nijeriyar ta xauki kanta, da kuma yadda takea idsanin qasashen duniya. Watan Mayu 2016 al’amarin da suka shekarun da mutane ke yi wanda Hukumar lafiya ta duniya, ta fitar ya nuna cewar Nijeriya ita ce qasa wadda take da mizani na qarshe, a Afirka, da kuma duniya gaba xaya, da shekaru 55 ga mata, 54 na maza, wato shekarun da ake sa ran zasu yi a duniya. Wannan ya sa ta kasance qasa ta 177 a duniya akan matsayin, wannan ya nuna ke nan tana gaban, wasu qasashe takwas na duniya. Abin da aka fi so shi ne 54. 4 da aka fi sa ran mutanen qasa zasu kasance a shekarau kafin su mutu. Bugu da qari akwai wata qididdigar da aka gabatar a yammacin Afirka wadda ta nuna cewar Nijeriya, yawan shekarun da ake sa ran mata su yi a shekara ta 2015, sune 56 yayin da kuma maza 53. Wallafe wallafen biyu daga wurare daban daban waxanda Hukumomi suka yi bayan shekara shekara xaya,ya bada shawarar, ba anyi wani abu ba sosai, domin xaukar mataki dangane da,yaan shekarau da al’ummar Nijeriya suke yi. Wani abin mamaki bala’oin da suke faruwa a qasashgen da yaqi ya zama masu abinda suka saba da shi,kamar su Sudanta
Kudu, Rwanda, Haiti, Yemen, Afganistan, da kuma matalautan qasashe, kamar su Mozambique, da kuma jamhuriyya damuraxiyyar qasar Congo, dukkan waxannan qasashe suna da, yawan shekarun da mutanen qasashen su ke yi, wanda ya fi babbar qasa Afirka wadda ke jagoranci wato Nijeriya. Wannan ya nuna ke nan mutanen su qasashen da aka ambata, suna yin shekaru masu yawa fiye da na ‘yan Nijeriya. Alal misali a qasar Yemen mutanensu na kaiwa shekaru 65, yayin da su kuma al’umma qasar jamhuriyyar damukuraxiyar Congo, al’ummarta na kai wa shekaru 59, su kuma ‘yanqasar Mozambique suna shekaru 57 ne a duniya. Sai kuma qasar Japan mutum yana iya kaiwa shekaru 83. 7, su kuma al’umma haxaxxiyar daular Turawa wato United Kingdom suna yin shekaru 81 ne, su kuma qasar Amurka shekaru 79, ya yinda kuma qasar Algeria wadda tana daga cikinnahiyar Afirka shekaru 75 ne. Kwamishinan ‘yansanda na jihar Abia Dokta John Ahukannah lokacin da
yake gabatar da qasidar sa, lokacin da ake bikin buxe kantins ayar da magani na St Racheal’s Pharama a Lagos, shi dai bayanin nashi ya yi ma shi taken ‘’Yadda Za A Inganta Yawan Shekarun ‘Yan Afirka’’ ya bayyana cewar shekaraunda ake sa ran da mutum zai yi sune 7i.4 wannan kuma shi yasa Nijeriya al’amarin na Nijeriya ke xaurewa mutane kai idan ka yi , la’akari da yawan arzikin albarkatun qasar da ake da shi da kuma na mutane, waxanda za aiya amfani dasu domin su samu canza al’amurra. Ya dai bada ma’anar abin da life expantancy take nufi, wato gaba xaya akan yadda ake kallon qasar data fi yawan mutuwar mata da jarirai. Kamar yadda Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana dangane jarirai sabuwar haihuwa a qasashe 29 dukkansu kuma masu yawan samun kuxaxen shiga ne, ana sa ran mutum zai yi shekaru 80 ko kuma fiye da haka, sai kuma jarirai sababbin haihuwa dukkansu na qasashen Sahara, ana sa ran shekarun mutanen basu kai 60. Ahukannah ya jaddada cewar gaba xaya a duniya
nahiyar Afirka ce ke da mafi qarancin yawan shekarun da akesa ran mutun zai yi, yayin da kumaita qasr Saliyio ita ce mai jagorancin, saboda mazajen ta suna shekaru 49.3 mata kuma na da 50.8. Yayin da kuma qasar Switzerland, ita maza na shekaru 81.3, sai kuma qasar Japan ita ce ta fi kowa mai shekaru 86.8. ‘’Akwai dalilai da yawa waxanda suka sa maganar shekaraun da ‘yan Nijeriya ke yi, suke da dangantaka da ciwo mai kashi 26, sai kuma fatara mai kashi 26 ita ma, sauran sunhaxa da haxarin mota, mai kashi 16 rashin samun isasshen abinci kashi 7, sai kuma mutuwa kashi 6 yawan matsaloli da kuma hawan jini kashi 5, rashin qyaqqyawar kulawa da lafiya kashi uku, rayuwar da bata qyau kashi 2, aikata ayyukan savo kashi 2, aikata laifuka kashi 2, rashin nuna kulaw ko kuma dana sani kashi 2, sai kuma saura kashi 2. ‘’Kashi 45 na al’ummar nahiyar Afirka ba su da wata hanya ta samun ruwan sha mai tsafta a Afirka, wannan ba wani abin mamaki bane ana ta fama da cutar amai da gudawa da kuma wasu cututtuka da ake xauka ta hanyar gurvataccen ruwa’’.
24
TALLA
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
25
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Kimiyya
Dala Miliyan 500
ne adadin kuxi Nijeriya ke kashewa duk shekara waurin safarar xanyen man fetur da wasu sinadaran da ake amfani da su a sashen sinadarari da magunguna
Binciken Wayoyin Mata Laifi Ne A Qasar Saudiyya Daga Idris Aliyu Daudawa
Miji ya duba abubuwan dake cikin wayar matar shi yanzu laifi ne a qasar Saudiyya, za kuma ayi ma shi tarar dala 133,009, da kuma shekaraxaya a gidan kurkuku, a wata sabuwar doka wadda aka yi domin,’’ A kare damar da kowa yake da ita a cikin al’umma da kuma kare’yanci’’. Wannan dokar za ta shafi dukkan maza da mata axanda suke zaune a gruruwan da muslmai suke. Wannan doka za ta kare maza ne daga matansu, kamar yadda abin yake a qsashen musulmai, dokar sakin aure a qasar Saudiyya kamar yadda take cikin Alkur’ani mai girma,sau da yawa, tana buqatar mata su, bayar da shaida akan, yadda aka danne hakki. Wayar miji kuma nan ne za a iya samun hujjoji masu qarfi waxanda za
aiya amfani dasu, wajen xaukar wani mataki. Dokar Anti- Cybercrime wato laifin da ya shafi hanyoyin sadarwa na zamani da nuna cewar, ‘’Kallo, qwacewa, ko amfani data ta abokin zama, ta hanyar samar da dama ta network, ko kuma komfuta, ba tare da izni ba, babban laifi bane’’. Wannan laifi akwai hukuncin dalar 133,000 ko kuma xaurin shekara xaya gidan kurkuku ko kuma a haxa duka. Hanyoyin sadarwa na zamani sun kasance wani wuri ne na aikata laifuka, da suka haxa da sharri, almubazzaranci, ga ma wani sharri, wannan ma ya haxa da amfani da account xin wani,kamar yadda ma’aikatar ta jaddada. Irin wannan doka maqwavciyar qasar wato haxaxxiyar daular Larabawa wato United Arab Emirates,ana iya xaure mutum watanni uku da kuma
biyan dala 817. Qasar mai arzikin manfetur da wasu qasashe waxanda suka fi amfani da
hanyoyin sadarwa na zamani a duniya, amma kuma amfani da al’adu, na kawo masu cikas akan amfani da hanyoyin.
A Karon Farko Isra’ila Za Ta Qirqiri Maganaxisun Nanosatelite Daga Abubakar Abba
A kwanakin baya ne Cibiyar qirqira ta qasar Isra’la tare da hukumar lura da sararin samaniya ta qasar suka sanar da cewar qasar ta Isra’ila, za ta qaddamar da tawaga uku na na’urar tauraruwar xan adam a sararin samaniya a wannan shekarar ta 2018. Qaddamarwar wadda itace karo ta farko a qasar ta Isra’ila, kamfanin dake qasar Jamus ne zai gudanar da aikin wanda shine ya qware wajen qaddamarwar da na’urar ta xan adam kuma qaddamarwar, tana xaya daga cikin akin (AdelisSAMSON). Aikin dai, tawagar wasu masu bincike ne suka qirqiro dashi wanda Pini Gurfil Darakta a cibiyar gudanar da bincike akan sararin samaniya ta Asher kuma wakili a sashen a sashen qereqere na (Aerospace). Cibiyar Adelis da hukumar sararin samaniya ta qasar Isra’ila sune suka bayar da goyon bayan gudanar da aikin. Abinda shirin yake son cimma buri akan aikin shine, don a tauraruwar ta xan adam, za ta iya tashi a yayin da ake kula da ita har zuwa tsawon shekara xaya, ayayin da take zagayawa a sararin samniya akan kimanin ma’uni mai kilo mita xari da shida.
A cewar Ministan kimiyya da fasaha na qasar Isra’ila Ofir Akunis, kimiyuar qasar ta Isra’ila ta samar da sabon abu ne da zai nuna ficen da ta yi akan qirqire-qirqiren ta. Ministan ya ce,“ muna tunqahon mu kasance a akan wannan aikin da za a qaddamar dashi wanda zai nuna cewar, an samar da wakilci akan bayar da gudunmawa akan ci gaba ta qirqire-qirqire a qasar ta Isra’ila da kuma samar da hanyar horar da xalibai a wannan fannin.” Akunis ya ce,” na’urar ta tauraruwar xan adam, za a yi amfani da ita wajen karvar saqwanni daga doron qasa da kuma yadda take juyawa, musamman don a dinga gudanar da bincike da kai xauki a lunguna da saquna na alumomi ta hanyar sanya ido. Na’urorin na tauraruwar xan adam guda ukun, an auna su dukkan su sun kai santi mita (10X20X30) kimanin tsawon akwatin takalmi kuma ko wacce xaya,tanada nauyin kimanin takwas. A cewar Darakta Janar na hukumar sararin samniya na qasar Avi Blasberger, na’urorin na tauraruwar xan adam, za a sanya masu kayan aiki kamar na na’ura mai qwaqwalwa da Ariya da na’urar da za ta dinga kula da sarrafa ta, inda kuma za a waya mai sauqi wajen
rabarwa, ya qara da cewa, na’urar ta tauraron xan adam tanada mahimmancin gaske a shekarun da suka gabata kuma qaddamar da ita xin tana qaruwa a duk shekara. Ya ce,“ ci gaban da kuma tsadar qaddamarwar, na irin wannan na’urar ta xan adam tana yin qasa akan wadda aka saba qaddamar. A cewar Blasberger “ a nan gaba, zamu sanya rai samar da dubban na’urar ta tauraruwar xan adam da zasu tashi daga doron qasa zuwa sararin samaniya da kuma tabbatar qarawa kafar sadarwa ta Internet sauri akan tsada kaxan fiye da yadda yake ayau.” Ya ce, mahimmancin kimiyyar ya haxada; tsari na( Rafael’s krypton) na gas, wanda shine na farko akan sahun tsari na duniya na na’urar xan adam. Ya jaddada cewar a yayin komawa akan tsari na na’urar zamani da Elta ya samar, za ta taimaka wajen kula da tsarin masana’antun MABAT na qasar Isra’ila tare da haxin kan masu gudanar da bincike na Technion. Gurfil ya qara da cewa, a bisa tsarin (propulsion) na na’urar tauraruwar xan adam zai samar da haske ta hanyar amfani da hasken rana wanda zai qara gusawa daga ko wanne sashi na na’urar ta xan adam kuma zai zama kamar fuka-fukai da
zai kula da tashin na’urar zuwa sama ba tare da anyi amfani da mai ba a matsayin jurewa iskar dake sararin samniya. Ko wacce na’urar ta xan adam, za a sanya mata kayan aiki na karvar sakwanni, da kuma xayar mai amasar bayanai kuma xaya da tafi wahala wajen zana na’urar ta xan adam. Ya ce, za ta taimaka wajen gudanar da aiki ga vangarorin tauraruwar xan adam kuma kafar sadarwar da tsarin ya haxada; masu karva guda biyu na(GPS) wanda za a yi amfani dasu wajen bugawar na’urar. Ya bayyana cewa,“ hanyar sadarwar za a yi amfani da ita akan tsari uku na tauraruwar xan adam don a samu sukunin sadarwa da xayar dake a kan doron qasa da kuma tashar dake kan doron qasa, wanda yin hakan an kawar da babbar matsalar qalubale ne akan aikin. Ya qara da cewa,za a ayi amfani da tasha da za a dinga amfani da ita wadda za ta dinga tura ma’adanai daga kan doron qasa. Ya ce,” idan muka lallava wajen tabbatar sararin na samaniya burin da aka sanya a gaba za aci nasara akai.” A cewar Gurfil ,“ za ta qara havaka samar da ci gaba na qananan taurarin xan adam da kuma kimiyya musamman a sararin samaniya.
A Yau
Laraba 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
RAHOTON MUSAMMAN 26
Tashin Hankali Dangane Da Yadda Likitocin Nijeriya Ke Barin Qasar Ci gaba daga shafi na
19
samar da (App) wadatacce akan waya qirar android da iOS daga watan Afrilu, wanda ko wanne Likita ya kamata ya shiga tsarin kuma za a samar da nayanai isassu daga ofishin qungiyar ta (NMA). Wani jami’I a qungiyar ta(NMA) Olumuyiwa Odusote, a shekarar data wuce ya ce, 40,000 daga cikin 75,000 na qwararrun Likitocin ‘yan Nijeriya da aka yiwa rijista suna gudanar da ayyukan su a qasashen waje. Mista Odusote ya ci gaba da cewa, sauran suma suna shiye-shiryen ficewa daga qasar.” A cewar Mista Odusote qwararrun Likitoci 100 sun yi ritaya daga daga asibitin qwararru (UCH) dake Ibadan a shekarar 2017, inda kuma a shekaru biyu da suka gabata qwararrun Likitoci 800 suka ajiye aiki daga asibitoci mallakar gwamnatin jihar Legas.” Ya qara da cewa, a shekarar 2012, sama da qwararrun Likitoci 1,000 suka rubuta jarrabawar Kwalejin qwararru ta West Africa domin su samu aiki a asibitin qwararru dake qasar nan. Amma a shekarar 2017 Likitoci su 236 ke kacal suka zana jarrabawar. Likitoci Sun Yi Magana: Shugaban qungiyar (NMA) reshen jihar Kogi Magnus Ogaraku a hirar da aka yi dashi ta wayar tafi da gidanka ya shedawa kafar Premium Times cewar zai yi wuya jami’an kiwon lafiya a Nijeriya musamman qwararrun Likitoci za su qi ficewa daga qasar nan don nema kansu mafita saboda yadda ba a tanadar masu da wani kyakywan yanayi ba a qasar nan.” Mista Ogaraku ya ce, ficewar qwararru daga qasar nan ba wai kawai ya tsaya akan Likitoci bane kawai. Ya ci gaba da cewa, sauran jami’an kiwon lafiya kamar Nas-Nas da waxanda suka karanci fannin sarrafa magunguna da waxanda suka karanci fannin yin gwajegwaje da sauran su suma suna ficewa daga Nijeriya. Mista Ogaraku ya qara da cewa, ficewar jami’an kiwon lafiya daga Nijeriya ya janyowa asibitocin dake jihohi da yawa matsala. Ya bayyana cewar, wasu daga cikin dalilan dake janyo ficewar sun haxa da rashin samar da kyakyawan yanayin gudanar da aiki. Ya ce kayan aikin da ake
buqata ba a wadata su ba, inda hakan bai baiwa Likitocin damar yin aikin yadda ya kamata. Ya ci gaba da cewa, rashin ladabtarwa da nuna qiyayya gasa a fannin, shi ma yana haifar da naqasu, inda wannan yana daga cikin dalilan da yasa wasu Likitocin suke ficewa daga Nijeriya. “Likitoci basa son irin wannan qiyayyar ganin hakan yana sanya aiki ya tsawalla. Ma’aikatan kiwon lafiya da yawa a yanzu suna son yin aikin Likitocin wasu mutane basa son hakan kuma mafi yawancin su sun fice.” Na uku kuma ya qara da cewa, albashin bai wani taka kara ya karya ba, inda Likitoci a jihar Kogi a yanzu ana biyan su kashi 60 ne bisa xari na albashi ga kuma yankar kashi 100 na albashin su da ake yi a matsayin haraji. Shi ma wani likita a hirar da kafar Primium times Wale Ajayi ya ce, mafi yawancin Likitocin suna ficewa ne saboda rashin tanadar masu da kyayawan yanayin aiki kuma an basu rabin albabashi ne ko kuma wasu jihihin ma basa biya su.ya koka akan yadda jihar Osun misali take biyan su rabin albashi har sama da shekara xaya. Ya ci gaba da cewa, “Shugaban sashe na wanda Farfesa ne, a shekarar data wuce ya ficewa daga Nijeriya
bana zargin su sam da suke ficewar.” Har ila yau, shi ma wani wani Likita Abiodun Babajide ya ce, tun shekaru biyu da suka shige yake shirye-shiryen ficewa daga Nijeriya. Misata Babajide ya kuma koka akan cewar ya kammala gwajin sa tun a shekarar 2014 kuma har yau bai samu wani takamai man aiki na wanda wannan wani abin baqin ciki ne. “Idan kaga mafi yawancin abokan aikin mu bawai suna maganar yin aiki a Nijeriya bane suna harin ficewa ne.” Mafi ywancin mu suna son su fice ne faga Nijeriya domin ba a a tanadar mana wani kyayawan yanayi ba. “Babu kyau, inda sai mu shafe samada shekaru takwas a makaranta in an ware sanin makamama a gefe amma har yanzu babu wani aiki mai kyau.” Mista Babajide ya ce, “lamarin na ficewar Lkikitoci faga Nijeriya, ba sabon abu bane, amma sai qara tavarvarewa yake yi kuma lamarin zai qara munana in ba a xauki wani mataki ba.” ”Mafi yawancin abokan aikin mu basa son su rubuta jarrabawar matakin farko ta ta kwalejin qwararru ta West Africa College. Shin meya sanya za su zana kuma mafi yawancin manyan mu da suka zana jarrabawar
basu samu aiki ba kuma jarrabawar tasu sai wargajewa take yi ba tare da sun samu aiki ba. Yadda Za A Shawo Kan Matsalar: Mista Ogirima ya yi nuni da cewar samar da mafita akan matsalar ita ce, gwambati ta yi haxaka da ma’aikatun kiwon lafiya masu zaman kansu dake cikin qasar. Ya ce wannan zai sanya tsarin ya yi aiki yadda ya kamata da kuma bayar da dama sukunin xaukar ma’aikata sosai.“ Ya bayyana cewar akawai buqatar matakan gwamnati su xauki Likitoci aiki ganin cewar mafi yawancin su basu da aikin yi. Ya yi nuni da cewar, a qasar da bamu da isassun Likitoci kuma bamu iya xaukar waxanda za su horar dasu. Ya jaddada cewar, dole ne gwamnati ta qara yawan cibiyoyin kiwon lafiyar da muke dasu, in har ma ta kama a qara giggina Asibitoci. Ya yi nuni da cewar, “akwai ayyuka da dama da aka yi watsi dasu a qasar nan, amma fannin kiwon lafiya bai kamata ya faxa a cikin wannan jerin ba”. Shugaban na NMA a qarshe ya ce, ya kamata gwamnati ta qara giggina Asibitoci da kuma xaukar Likitoci da yawa saboda Likitoci a Nijeriya suna mutuwa saboda wahala.”
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
TATTAUNAWA 27
‘Jam’iyyar APC Ta Zo Ne Domin Ceto ’Yan Nijeriya’ Ci gaba daga shafi na
17
sun yi babakere a kan kamfanonin mutane, kamfanonin mutane sun yi babakere, irin su ne fa Buhari yake yaqi da su kan cin hanci da rashawa domin qasar nan ta zauna daidai, idan ka ce irin waxannan mutanen ne, za ka ji suna qorafi sosai, mabiyansu ma na qorafi. Kai kuxin makamai a qasar nan, aka ce an ware kuxi domin a sayi makamai saboda talakar da ke cikin wata uquba saboda wasu buqatu na wasu ‘yan qungiya tsiraru wanda ina jin ana xaukan nauyinsu ne daga wasu qasashen, wasu jama’an qasar nan suka kwashe kuxin sayen makaman suka sanya a aljihunsu, ka gane cewar wannan gwamnatin fa ba a haka, hatta soja ne ko xan sanda ne hakkinsa ba a riqe masa idan ka kwatanta da gwamnatin baya. Buhari ya cimma nasarori da dama, wallahi idan mutum bai yaba masa ba, bai kuma kamata ya zage sa ba, mu kuma ‘yan jam’iyyar APC muna nan kamar jiya ne muka zavesa, za mu sake fitowa mu yi ununu mu zavesa domin ya cancanta ya kuma cire mana kitse a wuta, domin babu yadda za a yi a kakkarya hanun mutum a ce ana son a gyara masa a rana xaya ba zai iyu ba. Wasu na ganin Buharin ya zo da niyyar gyara amma bai samu muqarrabai na haqiqani ba kamar gwamnonin APC ma akwai masu yi masa zagon qasa, kana da abun cewa? Ka san Annabin Allah ma ya yi fama da munafukan musulmai a lokacin da ke raye a duniya. Don haka idan Buhari shi kaxansa ba zai iya iyuwa ya iya shawo kan gaba xaya muqarrabansa da masu dafa masa ba a wajen gudanar da shugabanci ba, ba zai kuma iyu a ce dukkanin gwamnonin Nijeriya suna bin abun da shi yake tafiya a kai ba, wallahi ba zai iyu ba, muna dai musu addu’a Allah ya dawo da hankalinsu ya zama daidai ne domin a samu nasarar kawo wa Nijeriya ci gaba. Ka fahimci wani abu guda, na yi imani da Allah! na yi imani da Allah!! na yi imani da Allah!!! Har sau uku, ba zan boye maka ba, Buhari qasar nan ne a gabansa, kuma gwamnoni akwai waxanda suke kan ra’ayin Buhari na ganin an fid da Nijeriya daga wannan yanayin, kamar gwamna jiha ta Bauchi, wallahi gwamnan jihar ce a gabansa, da badin
jihar bace a gabansa da ba zai iya kawo wa jihar nan ci gaba kamar haka ba, domin an yi wa jihar Bauchi cin kaca, ya zo ya samu jihar a dagole, albashi ma na wata uku ba a biya ba, an zo an ciyo basussuka, an dai yi abun da ake so, ya zo ya ce bar ya ga ta ina zai fidda jihar daga qunci, nan da nan kuwa ya kamo bakin zaren wannan babu abun da za mu ce sai godiya, don haka mu qara haquri, mu ci gaba da yi wa shuwagabaninmu addu’a, mu qara basu goyon baya, ba wai a ita zaginsu ana cewa Allah ya tsine wa wane da mun sani da ba mu zavesa ba, ai in muka tsine musu za su qara lalacewa ne, idan kuma muka yi musu addu’a za su gyaru ne har al’amura su zo su tafi daidai. Shi fa gwamnan Bauchin nan na samun suka sosai, musamman masu kafa misalai da cewar bai iya cimma wata aikin a zo a gani ba, suna ma kafa misali da cewar tun da ya hau mulki yake aiyukan hanyoyi amma har yanzu ya gagara kammalawa, me za ka ce? • Ibrahim Gambo Kobi Ya kamata masu wannan tunanin su daina, domin da wannan kason jiha take gwamnan Bauchi Muhammad gudanar da harqoqinta. Abdullahi Abubakar na Dukkanin jam’iyya matuqar qoqarin iyaka nasa, idan ka duba aiyukan hanyar ba ta rasa qalubale a da ake magana a kai, ba gabanta, APC kama daga fa wai akwai kuxin da ake matakin qasa da jiha ware wa ne a ce na yin aikin kuna fuskantar wasu nan ba, daga cikin kason matsalolin cikin gida ne da jihar take samu da shine ko na waje? Abun da ke faruwa, ake biyan albashi, bayan kammala biyan albashi xan jam’iyyar APC a jihar Bauchi a sauran abun da ya rage da da baya kaxan mun samu ‘yan xan kuxin haraji da ke zuwa matsaloli wanda jam’iyyar ba wa jihar da sune ake samu a ta tafiya yadda ya kamata ba. biya masu aikin hanya, to ni amma yanzu Alhamdullahi kuwa ina ganin idan jama’an shugabannin APC da na Bauchi basu gode masa ba, qananan hukumomin Bauchi bai kamata su kushe masa 20 da shi karan kansa ba, ya kamata ne ma su yi shugaban jam’iyyar na jiha masa godiya ne ma. Yanzu Alhaji Uba Ahmad Nana ka ga kamar titin da ya tashi an zauna an fahimci juna, daga Central Market zuwa wannan fahimtar junan ba Awala ai a kwanaki idan ka qaramar nasara ne aka cimma bi hanyar babu daxin bi da ba, don ya wuce nasara xaya, abun hawa mota ko mashin, nasarori ne a samu. Domin da aka zo a ka gyara musu da mu a kowani lokaci jihar da yake mutanen unguwar sun jam’iyyar ne a gabanmu, idan fahimci abun da gwamnatin jam’iyya mai mulkin jiha tana ta yi musu zuwa suka yi tafiya a karkace to dole ne matasa da dattawan unguwa shugabancin a jihar ma yake suka yi wa gwamnan godiya a tafiya a karkace, amma idan kan wannan aiyukan da ya yi ita jam’iyya tana xinke za ta musu. Ba za ka fahimci wani iya samar da nasarori gaya abu bane, ka san mutanen wajen ci gaban shugabanci. mu, suna xaukan gwamnati a Da baya, lokacin su marigayi kullum ne take samun kuxi, Tattali Ali, Ajiyan Bauchi gwamnati bata samun kuxin yana mataimakinsa, Barayan kullum, ita gwamnati sai Bauchi na wancan lokacin wata ya qare ne take samun shi ne shugaban qaramar kasonta, dukkanin wani abu hukuma na jam’iyya, yakan
kira gwamna ya zo, yakan kira shuwagabanin su zo, kai babu abun da jam’iyya ba ta iya gyarawa. Don haka an xan samu gaf ne a cikin jam’iyyar ka san shi shugabanci, wani ya fi kwarance ne ta fuskacin kaza ne ya iya, wani kuma jagorancin jama’a ne ya iya a qaramar hukuma ko kwamishina da sauransu, don haka jagorantar jam’iyya na da faxi, sai an samu mutum mai haquri haziqi, amma mu a yanzu APC ba ta fuskantar wasu qalubale. Jam’iyun adawa kuma ba mu kallonsu a matsayin bazara ma. Wani tabbaci ne za ka bayar wa jama’a na cewar za ku maimaita shugabancin a matakin jiha da qasa? Da yardar Allah tun daga kan shugaban qasa Muhammad Buhari, zuwa Gwamnan jiharmu da sauran gwamnoni, Sanatacocinmu da ‘yan majalisun tarayya da na jahohinmu cikin yardar Allah APC za ta sake kashe dukkanin kujerunmu, muna sake neman haqurin jama’an jihar Bauchi su qara mana hakuri gyara ake yi za su ji daxin mulkin nan fiye da yadda suke tsammata, kuma a kowani lokaci shi xan adam bai fi qarfin kuskure ba, in an faxa masa sai ya gyara.
28
Tauraruwa Mai Wutsiya
A Yau
Litinin 09.4.2018 08174743902 wutsiya2019@gmail.com
‘Yadda Na Kashe Kawuna Bayan Ya Nemi Yi Min Fyaxe’ Daga Mustapha Hamid
Wata Matashiya nai suna Rebecca Tina, mai shekarun haihuwa 22, tana can tsare a hannun ‘yan sandan Jihar Enugu, bayan kisan Kawun ta mai suna Friday Mathiew da ta yi. Ta dai aikata aika-aikar ne a Unguwar Independence Layout da ke Jihar Enugu. Tina, wacce ‘yar asalin Ikot Udobang Ukanafon ce da ke Jihar Akwa Ibom, ta shiga hannun Jami’an tsaron ne yayin da ta yi yunqurin arcewa bayan da ta aikata kisan kan. Yayin da take amsa laifin ta a gaban hukumar ‘yan sanda, Matashiyar, ta bayyana cewa, ta kashe Kawun nata ne yayin da take qoqarin kare kan ta daga yunqurin yi mata fyaxe da ya yi. Ta bayyanawa ‘Yan sandan cewa, Kawun nata ya daxe yana nuna buqatun saduwa da ita. Ta yi iqirarin cewa, ta sha zullewa yunqurin da Kawun nata yake yi a lokuta dabandaban, har zuwa ranar 26 Ga Watan Oktoba, da misalin qarfe 8:30 na dare, lokacin da mai faruwa ya faru. Tina ta qara da cewa, ta makawa Kawun nata wani qatoton Dutse ne a kansa, lokacin da ya tare ta, ya hana ta hanyar da za ta iya suvuce
masa. “Ko kaxan ban yi niyyar kashe shi ba, babu niyyar hakan sam a Zuciyata, ya takura mini ne a kan sai ya yi jima’i da ni, na kashe shi ne bisa haxari yayin da yayi yunqurin zai yi mini fyaxe. Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan Jihar Enugu, Mr. Eberu Amaraizu
ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike a kan kisan kan. Ya bayyana cewa, “lokacin da Xan marigayin ya koma Gida ya tarar da gawar mahaifin nasa, sai ta umurce shi da kada ya kuskura yayi ihu, dan kar hankulan jama’a ya kai ga abinda ta aikata”. “Ta yi wa qaramin Yaron alqawarin cewa, ita za ta
ci gaba da kula da shi, daga nan ne ta xauki Yaron, ta garqame Gidan nasu, ta je ta kai shi Gidan wata ‘yar’uwar su, daga can ta yi vatar dabo”. “Tana nuna matuqar nadaman abinda ta aikata, inda take ta neman a yi mata afuwa, ta shaida mana cewa, ita sam ba da niyya ta kashe Kawun nata ba”.
Dubun Wasu Masu Aikata Fyaxe Ta Cika Daga Mustapha Hamid
Shugabar qungiyar kare ‘yancin Yara a Jihar Niger, (Niger State Child’s Right Protection Agency) Mariam Kolo ta ce, hukumar ta su ta kame wasu Mutane 8 da ake tuhuma da laifin yin fyaxe, kuma ta damqa su zuwa sashi na musamman na rundunar ‘yan sanda masu binciken miyagun laifuka da ke Jihar. Rahotannin da muka samu sun shaida mana cewa, mafi yawan waxanda fyaxen ke shafa, yara Mata ne ‘yan qasa da shekaru 20 da galibin su suke yawon gararambar tallace-tallace a
cikin tsakiyar birnin Minna. Waxanda ake tuhumar sun haxa da Ibrahim mai Nama, mai shekaru 30, mazaunin unguwar Tunga Sabon Titi, da Musa Ibrahim dan shekaru 35 mazaunin Bosso, da Nasiru Abubakar mai shekaru 35 mazaunin rukunin Gidajen Abdussalam, da Yahaya Kuso mai shakeru 48 daga Lapai. Ragowar sun haxa da Mohammed Yusuf mai shekaru 25 daga Barikin Sale, da Yusuf Idris mai shekaru 35 daga Tudun Nasira, da Isa Garba mai shekaru 30, da kuma Tukur Buhari dan shekaru 35. Kolo ta shaidawa kafar
labarai ta ‘Northern City News’ cewa, waxanda ake zargin, sun daxe suna lalata Yara Mata qanana. Ta ce, bayan kama su, da aiwatar da bincike a Ofishin hukumar su, waxanda ake zargin sun amsa laifukan su, inda take hukumar tasu ta danqa su a hannun ‘yan sanda dan cigaba da gudanar da bincike. Ta ja hankukan Iyaye da su riqa yawaita sanya idanu a kan ‘ya’yansu, gudun kar su riqa faxawa hannun vata gari. Shugabar hukumar, ta alaqanta Addini da Al’ada, da rashin wayarwa da jama’a kai a matsayin abubuwan
da suke ta’azzara laifukan fyaxe a jihar, inda ta yi nuni da cewa, masu aikata laifin fyaxen sam ba sa nuna wata alama ta daina aikata wannan mummunar aiki da suke aiktawa. Ta ce, “za mu cigaba da wayar da kan al’umma a dukkanin qananan hukumomin Jihar 25 har sai an daina aikata wannan mammunar ta’asa, an samar da kyakkyawan yanayi da sauyi mai nagarta”. Ta yaba wa irin goyon bayan da suke samu daga Gwamnan Jihar Abubakar Bello, inda ta ce hakan ya samar musu da nasarori masu ximbin yawa.
A Yau
29
Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
Qasashen Waje
Tare da Rabiu Ali Indabawa 08069824895
Ko Mene Ne Dalilin Takaddamar Ciniki A Tsakanin Amurka Da Qasar Sin?
Gwamnatin Trump tana son yin amfani da kasar Sin wajen warware matsalar gibin cinikinta, wanda aka bayyana cewa Amurkar tana tafka hasarar daruruwan biliyoyin daloli a duk shekara. Wannan shine dalilin da yasa shugaban kasar Amurka Donald Trump yake son ya jagoranci kasarsa wajen tada takkadamar ciniki a tsakanin kasarsa da babbar abokiyar huldar kasuwancinta kuma kasa ta biyu mafi girma ta fuskar karfin tattalin arziki a duniya. Daga karshe dai wannan shine abinda suke ta fadawa duniya. Amma a yayin da dangantakar take kara yin tsami, al’amurra suna kara bayyana a fili karar cewa, alal hakika abinda Amurka take tunani shine, babbar matsala ce gareta yadda kasar Sin ke kara samun bunkasuwar yin gogayya a harkokin ciniki, kuma wannan babban kalubale ne ga Amurkar a matsayinta na kasar dake da karfin fada aji a duniya. Gabatar da bukatar karin haraji da adadinsa yakai dalar Amurka biliyan 50 wanda aka azawa mafi yawan kayayyakin da kamfanonin kasar Sin ke samarwa wadanda ke da alaka da burin kasar Sin na “Made in China 2025,” wanda aka tsara shi
da nufin daga martabar rukunin kamfanonin kasar Sin. Ba wani bakon abu bane ga kowace kasa ta tsara wani shiri da nufin tabbatar da cigabanta. Kamar dai yadda kasar Sin ta tsara shirinta na “Made in China 2025”, kuma itama Jamus tana da shirin masana’antunta na “Industry 4.0”. Ita kanta Amurka tana da nata tsarin wanda tsohon shugaban kasar Barack Obama ya bullo da shi da nufin farfado da masana’antun kasar Amurka. Amma sai dai gwamnatin Trump ta kuduri aniyar haddasa sabani tsakaninta da kasar Sin. Menene hujja? Saboda, idan har aka aiwatar da shirin yadda ya kamata, Sin za ta iya shan gaban Amurka wajen kwace ikon manyan masana’antu dake tashe a halin yanzu, kamar su na’urori masu fasahar zamani (AI), da kuma mutum-mutumin inji. Tattalin arzikin kasar Sin yana cigaba da bunkasuwa cikin sauri na ban mamaki a cikin shekaru 40. Kuma karuwa da yake samu babu wasu alamu dake nuna zai iya tsayawa cak. Kasar Sin itace kasar da tafi kowace kasa fitar da kayayyakinta zuwa kasashen duniya, kuma babbar abokiyar ciniki ce ta
kasashen duniya kimanin 130, ciki har da Amurka. Ta kasance a sahun gaba wajen gina kayayyakin more rayuwa, yayin da yawaitar jiragenta masu saurin tafiya suka kasance a matsayin daya daga cikin misalai. Haka zalika tana zuba jari mai dunbun yawa a fannin kimiyya da fasaha a matsayin wani bangare na shirinta na “Made in China 2025”. Shin ko kasar Sin zata iya shan gaban Amurka na zama kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya? Mafi yawan masana tattalin arziki suna tunanin hakan. Kuma wannan lokacin na zuwa ne nan da shekaru 10. Amma wannan ba wani abu ne da za’a dinga musayar yawu da Amurka ba. Yawan al’ummar sinawa sun ninka Amurkawa har sau 4, ke nan me zai hana tattalin arzikinta ya zarce na Amurka? A idon shugaba Trump, cigaban tattalin arzikin da kasar Sin ke samu barazana ce ga Amurka. Wannan batu ya kasance a bayyana a manufar tsaron Amurkar, inda gwamnatin Amurkar ta bayyana kasar Sin a matsayin abokiyar gaba kuma babbar abokiyar takara. Gwamnatin Trump ta bayyana aniyarta a fili na hana kasar Sin cigaba, da samun bunkasuwarta
cikin lumana ta hanyar yi mata zagon kasa wajen bunkasuwar tattalin arzikinta. Abin tambaya a nan shine: shin za su iya ne? Hakan ba abune mai yiwuwa ba. Kasar Sin ta riga ta zama kasar da ta fi kowace kasar a duniya yawan kudaden ajiyar waje. Masu matsakaicin karfi da kasar Sin ke dashi sun zarta na Amurka. Kuma a watan Nuwamba a birnin Shanghai, kasar Sin zata karbi bakuncin taron baje kolin kayayyakin shigi na kasa da kasa irinsa na farko mafi girma – alamu ne dake nuna cewa kasar ta riga ta cimma matsaya na cigaba da aiwatar da sauye sauye a cikin gida da bude kofa ga waje, da kuma kyautata mu’amalarta da sauran kasashen duniya. Baya ga irin girman kasar da take dashi, da yawan al’ummarta, da kuma bunkasar tattalin arzikinta, kasar Sin a shirye take ta tinkari matsalar da za a haifar mata. Duk da irin matsayin da gwamnatin Trump ke dauka, na daukar matakan da zasu haifar da tarnaki game da mu’amalar cinikiyayya tsakaninsu, kasar Sin zata cigaba da aiwatar da manufofinta na bunkasuwa, ciki har da shirinta na “Made in China 2025.”
Wasanni 30
A Yau
Abin Kunya Ne City Ta Lashe Firimiya Akanmu -POGBA Xan wasan tsakiyar qungiyar qwallon qafa ta Manchester United, Paul Pogba ya bayyana cewa daman babu yadda za su yi su bar Manchester City ta lashe gasar firimiya a kansu. Poba ya bayyana hakane bayan da ya jefa qwallo biyu a ragar Manchester City a wasan hamayyar da suka fafata a ranar Asabar a filin wasa na Ettihad bayan da aka tashi daga wasa Manchester United tanada ci 3 sai City tana da ci 2. Manchester City ta rasa damarta ta tabbatar mata cin kofin gasar firimiyar bana bayan da abokiyar hamayyarta Manchester United ta farfaxo ta doke ta 3-2 a filin wasa na Etihad.
Jagorar ta firimiya wadda ke gida na buqatar ta doke abokiyar hamayyar tata ne a karawar ta dauki kofin, da ragowara wasa shida a kammala gasar. Amma ta saryar da wannan dama bayan da ta yi sake United ta rama qwallo biyu da ta zura tun a kashin farko na wasan, bayan an shiga kashi na biyu. Kyaftin din Man City Vincent Kompany ne ya fara zura qwallo a raga a minti na 25 da fara wasa kafin kuma GĂźndogan ya qara ta biyu minti biyar tsakani. Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 53 Paul Pogba ya rama
wa Man United xaya sannan bayan minti biyu ya farke ta biyun, kafin kuma Smalling ya ci ta uku a minti na 69. Manchester City za ta kara a gidanta ranar Talata da Liverpool a wasa na biyu na matakin dab da na kusa da qarshe na kofin Zakarun Turai. Kafin ta je Wembley ta fafata da Tottenham a gasar ta Premier ranar Asabar mai zuwa wasan da idan tasamu nasara za ta zama zakarar gasar firimiya. Manchester United wadda a ranar Lahadi mai zuwa za ta karvi bakuncin ta qarshe a tebur West Brom ta cigaba da zama ta biyu da maki 71 akan teburin na firimiya.
Real Madrid Tana Zawarcin Jugen Klopp Rahotanni daga qasar ingila sun bayyana cewa qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid ta fara tunanin tuntuvar mai koyar da qungiyar qwallon qafa ta Liverpool, Jugen Klopp domin ya maye gurbin mai koyar da yan wasan qungiyar na yanzu, Zidane a qarshen kaka. Klopp xan qasar Jamus wanda yakoma Liverpool a shekara ta 2015 ya farfaxo da qungiyar ta Liverpool inda a yanzu haka take mataki na uku akan teburin firimiyar ingila sannan kuma qungiyar tana buga gasar zakarun turai har yanzu. Real Madrid ma dai tana qoqari a gasar ta zakarun turai sai dai batajin daxin gasar laliga ta wannan kakar bayan da a yanzu take mataki na uku a kan teburin na laliga maki 15 tsakaninta da Barcelona wadda take mataki na xaya.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana masu ruwa da tsaki a qungiyar ta Real Madrid sun shirya korar Zidane idan har yakasa xaukar gasar zakarun turai na wannan shekarar bayan da tuni qungiyar ta fita daga gasar Copa Del Rey. Hukumomin qungiyar dai sun tabbatar da cewa Klopp ne mai koyarwar da zai saka karsashi da yunwar lashe kofi a qungiyar ta Real Madrid bayan da yabuga abin azo agani a qungiyar Dortmund da kuma qungiyar Liverpool. Liverpool dai tana mataki na uku akan teburin firimiya sannan kuma ta doke Manchester City daci 3-0 a gasar zakarun turai a wasan farko da suka fafata a zagayen kusa dana kusa dana qarshe a filin wasa na Anfield.
Litinin 09.4.2018
Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com
Barcelona Ta Karya Tarihin Shekara 40 A Laliga Qungiyar qwallon qafa ta Barcelona ta karya tarihin da qungiyar qwallon qafa ta Real Soceidad ta kafa na lashe wasanni 38 a gasar laliga bayan da Messi ya zura qwallaye 3 rigis a ragar qungiyar Legannes a wasan da suka fafata a ranar Asabar. Real Soceidad ta kafa tarihin ne shekara 40 data gabata bayan data buga wasanni 38 ba tare da tayi rashin nasara ba wanda hakan yasa babu wata qungiya data tava haxa wannan tarihi sai a wannan shekarar. A yanzu haka Barcelona ta xauki hanyar lashe laliga na wannan shekarar sannan kuma har yanzu tana buga gasar zakarun turai ga kuma wasan qarshe da za ta fafata da qungiyar Sevilla a gasar cin kofin Copa Del Rey. Mai koyar da ’yan wasan na Barcelona, Enersto Valverde ya bayyana cewa abin farin cikine ace sun karya tarihin da wata qungiya ta kafa shekaru 40 da suka gabata kuma zasu xora daga kai har sai yadda mita ta nuna. Ya ci gaba da cewa yana son kafa tarihin da babu wata qungiya da za ta iya kafashi ko kuma ma ace su kafa tarihin da za’ayi wahalar karyawa. Barcelona za ta kai ziyara qasar italiya a ranar Talata domin fafata wasa da qungiyar AS.Roma a wasan zakarun turai a wasan farko dai da suka fafata Barcelona ce tasamu nasara daci 4-1 sannan kuma a mako mai zuwa za ta karvi baquncin qungiyar Valencia a gasar laliga.
A Yau Litinin 9 Ga Afrilu, 2018 (22 Ga Rajab, 1439)
PSG Za Ta Zazzagawa Liverpool Kuxi Akan Muhammad Salah
WASANNI 31
Daga: Abba Ibrahim Wada Gwale
Rahotanni daga qasar Faransa sun bayyana cewa qungiyar qwallon qafa ta Paris Saint German ta shirya kashe naqudan kuxaxe domin siyan xan wasan Liverpool, Muhammad Salah, xan qasar Masar a kakar wasa mai zuwa. Salah yakoma Liverpool ne daga qungiyar Roma akan kuxi fam miliyan 36 bayan yayi zaman aro a qungiyar daga Chelsea kafin kuma Chelsea xin ta siyar dashi. Qungiyar qwallon qafa ta PSG tana ganin Salah zai taimaka mata wajen ganin ta samu nasara a gasar zakarun turai da qungiyar take fatan lashe wa bayan da tuni ta kusa lashe gasar rukuni-rukuni na qasar Faransa. Hakan yasa qungiyar take ganin cewa za tayi duk yadda za tayi domin ganin Liverpool ta siyar mata da Salah akan kowanne farashi bayan da qungiyar ta kashe kuxi fam miliyan 200 wajen siyan Neymar daga Barcelona a watan Agustan shekarar data gabata. Sai dai ana ganin xan wasa Edinson Cavani ne zai bar qungiyar domin Salah yasamu wajen bugawa bayan da aka danganta Cavani da komawa qasar ingila da buga wasa inda tuni aka bayyana cewa Chelsea za tayi zawarcin xan wasan gaban. Amma ana ganin abune mai wahala Liverpool ta iya siyar da Muhammad Salah bayan data siyar da Coutinho zuwa Barcelona a watan Janairu wanda ake ganin abune mai wahala ta sake yadda ta rabu da babban xan wasanta. Salah dai ya zura qwallaye 38 sannan ya taimaka an zura qwallaye 13 cikin wasanni 43 daya buga a qungiyar Liverpool a wannan kakar sannan kuma zai wakilci qasar sa ta Masar a gasar cin kofin duniya da za’a fafata a qasar Rasha.
Dole Mu Haqura Da Buga Gasar EUROPA — Conte Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Chelsea, Antonio Conte ya bayyana cewa dole sai shugabannin qungiyar sun haqura qungiyar za ta buga gasar Europa a kakar wasa mai zuwa. Conte ya bayyana hakane bayan daqungiyarsa ta tashi daga wasan da suka buga da qungiyar Westham a gasar firimiya inda ya ce daman tun farko yayi hasashen qungiyar bazatiyi qoqari ba a wannan kakar saboda yadda qungiyar bata siyi manya yan wasa ba. Yaci gaba da cewa qungiya kamar Chelsea daman yakamata
ace tana buga gasar zakarun turai amma tunda ba’a samu ba haka zasu haqura su buga gasar Europa idan har aka kammala gasar firimiya basu dawo matsayi na huxu ko uku ba. Ya qara da cewa tun farkon fara kakar wasan wannan shekarar yayi hasashen cewa qungiyar baza ta yi qoqari ba kuma ga maganarsa nan tana bayyana inda ya ce hakan yasamo asali ne sakamakon rashin mayar da hankalin da hukumomi sukayi na siyan xan wasan daya dace da qungiyar. Ya ce yanzu amma ba maganar qorafi zaiyi ba domin yanzu
’Yan Wasa Na Basu Da Laifi A Wasan Mu Da United
ba lokacin bane yakamata ya mayar da hankali akan wasannin qungiyar na gaba nan gaba idan wasa ya qare kuma sai yayi Magana akan abinda yakamata Daga Abba Ibrahim Wada Gwale qungiyar tayi nan gaba. A qarshe ya ce yana fatan nan Mai koyar da qungiyar yan wasan qungiyar qwallon gaba qungiyar za tayi hankali qafa ta Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana wajen siyan yan wasan da suka cewa yan wasan qungiyar basu da laifi duk da sunsha dace da girman qungiyar a kashi a hannun Manchester United a ranar Asabar xin data gabata. kasuwar siye da siyar da yan Manchester City dai taso ta samu nasara akan wasa kuma yasan shugabannin Manchester United domin ta lashe gasar firimiya a qungiyar sun shirya yin hakan. ranar sai dai rashin nasara yasa dole sai a wasan gaba Chelsea dai tayi rashin nasarar zasu lashe gasar idan har sun iya doke Tottenham a wasanni biyar cikin wasanni wasan gaba a Wembley. bakwai data buga a kwana Guardiola ya ce yan wasansa sunyi qoqari sosai kuma kwanan nan sai dai tana matsayi sun buga wasa yadda yakamata kuma sunso ace sun na biyar akan teburin firimiya ta samu nasara amma basu samu ba saboda haka zasu wannan kakar. tara a wasan gaba. Yaci gaba da cewa nan gaba za su yi qoqarin samun nasara a wasan gaba musamman a wasan da zasu buga da qungiyar Liverpool a wasan zakarun turai a ranar Talata mai zuwa. Ya qara da cewa a wasan da suka sha kashi a hannun Manchester United sune da nasara amma cikin minti goma Manchester United suka juya wasan amma zasu cigaba da neman nasara har qarshe. Manchester City dai za ta karvi baquncin Liverpool a wasan zagaye na biyu ma gasar zakarun turai bayan da a wasan farko suka sha kashi a hannun Liverpool xin daci 3-0 a filin wasa na Anfield sannan kuma a mako mai zuwa zasu kai ziyara Landan domin fafata wasa da qungiyar Tottenham wasan da idan sun samu nasara ta tabbata sun lashe firimiya.
AyAU LEADERSHIP 9.4.18
Litinin
Don Allah Da Kishin Qasa
www.leadershipayau.com Leadership A Yau
JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA
LeadershipAyau
No: 0120
Muqalar Litinin
N150
WASANNI
Abin Kunya Ne City Ta Lashe Firimiya Akanmu -Pogba
> shafi na 30
Nazarin Xabi’un Mutane: Wanne Ka Faxo A Ciki?
Sulaiman Bala Idris
0703 666 6850
M
ai karatu a wannan makon zan tavo fagen yanayin xabi’un mutane ne, wanda al’amari ne mai muhimmancin gaske a harkar zamantakewa. Idan ka san yanayin xabi’ar mutanen da ka ke rayuwar yau da gobe da su, wannan zai ba ka damar kaucewa aukuwar rashin fahimta da savanin ba gaira ba dalili. Shafin namu a yau zai yi tsokaci ne dangane da xabi’ar mutum (personality). Akwai nazariyya (theories) da daman gaske dangane da xabi’u (personality), waxanda kuma kowanne ka bibiya za ka taras da irin hujjojin da aka zayyano domin assasa nazarin. Amma dai zan taqaita ne ga yin bayanin guda xaya, wataqila sauran zan yi bayaninsu nan gaba a hankali, idan Allah ya yarda. An xau lokaci mai tsawon gaske ana samun musayar ra’ayi da martani sosai dangane da xabi’a, an samu taqaddamomi da dama daga masana mashahurai tun a qarnonin baya. Akwai waxanda suka xoru akan ra’ayin cewa, ita xabi’a ana gadonta ne daga jini, ana haihuwar mutum ne da dukkanin xabi’unsa. Yayin da wasu masanan ke ganin ai ko kaxan ba haihuwar mutum a ke yi da xabi’unsa ba, koyonsu ya ke yi a hankali sakamakon tarayya da al’ummar da yake rayuwa cikinta. Waxanda ke da ra’ayin haihuwar mutum a ke yi da xabi’unsa su ne a ke kira da ‘Nativist’, su kuma waxanda ke da ra’ayin mutum na koyon xabi’un ne cikin al’umma su ne a ke kira da ‘Enviromentalist’. A qarqashin waxannan mabambanta ra’ayoyi guda biyu, waxanda a ke yi wa muhawararsu take da ‘Nature versus Nurture debate’, akwai nazarori dabandaban waxanda kowanne ke son tabbatar da matsayarsa ta hanyar yin gamsassun bayanai da kafa hujjoji daga madogara ta ilimi. Sai dai har wayau bayan dogon nazari akwai masanan da ke ganin ba zai yiwu mutum ya ce xabi’u na ginuwa ne ta vangare xaya tilo ba, dole sai dai a kalli abin ta fuska biyu; ta fuskacin haihuwar mutum da xabi’unsa da kuma ta fuskacin koyonsu bayan ya zo duniya. Wannan shi ma wani dogon darasi ne mai zaman kanshi wanda zai so a tattauna shi daban. Sakamakon la’akari da irin
mabambantan ra’ayoyi da nazariyyar da ake da su. Na zavi yin bayani ne dangane da Nazariyyar ‘TEMPARAMENT THEORY’. Nazari ne wanda ya tafi a kan cewa gaba xaya mutanen duniya xabi’unsu sun kasu gida huxu ne, ta na iya yiwu wa a samu wani da xabi’u duka huxun, amma dole sai an samu xaya daga ciki wanda ya fi rinjaye. Nazarin na ‘Temparament’ ya bayyana karkasuwar waxannan xabi’u kamar haka: 1. Xabi’un Sanguine 2. Xabi’un Phlegmatic 3. Xabi’un Choleric 4. Xabi’un Melancholic Masu Xabi’un SANGUINE Masu irin wannan xabi’a sun kasance a cikin jininsu qwayoyin jan jini ya fi rinjaye (red blood). Za ka gansu su na yawan son tava mutane, su na son shaqatawa, su na son harkokin more rayuwa, sun fiye surutu, su na saurin qulla abota, su na son su ga sun sa mutane annushuwa da farin ciki. A na gane waxannan masu xabi’a ne da siririyar fuska. Masu Xabi’un PHLEGMATIC Su kuwa waxannan su na da qwayoyin Phlegma da yawa a jininsu. Masu wannan xabi’a sun kasance mutane masu son zaman lafiya,
sauqin kai sannan su na da tsauri da kiyaye dokoki. Su na da zurfin ciki, ba su damu da harkokin more rayuwa ba, su na da yawan bautan Allah. Kamanninsu shi ne, su na da fuska zagayayye (rounded), fatansu na da laushi, su na da leve cikakke, sannan hancinsu qarami ne. Masu Xabi’un CHOLERIC Wannan xabi’a ce ta mutanen da ke da yawaitar qwayar jini yalo (yellow) a jikinsu. Yawancinsu shugabanni ne, jagorori ne, akwai aiki tuquru. Su na yawan karatu kuma su kan ci nasara a rayuwa. Ba su da yawan abokai, su na da kiyaye lokaci saboda komi na rayuwarsu tsare tsaren gaba ne. Ba su yin kwana kwana a mu’amala. Su na saurin yin fushi saboda akwai hadafin da su ke son cimma. Su a wurinsu morewa rayuwa vata lokaci ne kawai. Kamanninsu shi ne, ba su da tsayi, su na da faxin qirji da qosasshen jiki. Da yawansu na a cikin maza, kaxan a ke samu daga mata. Masu Xabi’un MELANCHOLIC Mutane masu yawaitar baqin qwayar jini a jikinsu. Ba su yawan yin magana, su na da gaskiya, ba ruwansu da harkokin morewa rayuwa. Sun fi son aikata komi da kansu ba su son wani yayi musu hidima. A na gane waxannan ta
hanyoyi kamar haka: idanuwansu na da duhu, sannan za ka ga kansu na wani lilo. Ta na iya yiwu wa a samu wani mutum wanda za a ga jifa jifa daga cikin wasu xabi’unsa a dukkan huxun, amma maganar gaskiya ita ce, dole ne ya zama akwai inda xabi’un nasa su ka fi karkata. Da fatan mai karatu ya gano wacce dabi’a ta fi rinjaye a rayuwarshi. Mu haxu mako mai zuwa!
Babba Da Jaka Duk varagurbin PDP sun koma wasu jam’iyyun –Makarfi
Haba Don Allah?
Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 09-2345055; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 01-8963459. E-mel: leadershipayau@yahoo.com