Leadership A Yau 17 Ga Afrilu 2018

Page 1

17.4.18

AyAU Talata

LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

LeadershipAyau

No: 125

N150

Yawan Masu Rubuta Jarabawar NECO A 2018 Ya Qaru Daga Bello Hamza

An samu qaruwar masu zana jarabawar shiga makaratun haxin ka na gwamnatin tarayya da hukumar shirya jarabawa ta NECO ke gudanawa a wannan shekarar fiye da yadda abin yake a shekarar 2017, a wannan

shekarar xalibai ne 79,887 suka zana a shekarar 2017 kuwa xalibai 78,378 suka shiga jarabawar, an kuma ba xalibai masu naqasa kulawa na musamman a wannan shekarar. Qaramin Ministan ilimi, Anthony Anwukah, ne ya bayyana haka a Abuja ranar Asabar a lokacin

da yake zagayawa cibiyoyin zana jarabawar a yankin babban birnin tarayya Abuja (FCT). Ya ce, xalibai masu hanqoron shiga qananan makarantun sakandare (JSS) na 104 Unity Colleges guda 104 da muke das u wanna da hukumar NEC Ota shirya a faxin tarayya qasar nan,

an gudanar da shi ba tare da wani matsala ba. Mista Anwukah ya lura da cewa, an gudanar da jarabawar cikin yanayi mai aminci, ya kuma yaba wa hukumar NECO a bisa wannan gaggarumun aiki da suka yi.

Tsaro Ne A Gabana Ba Zaven 2019 Ba –Buhari

>Ci gaba a shafi na 5

4

•Mataimakin Shugaban Qasa, Farfesa Yemi Osinbajo (a tsakiya); Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu (Na shida a dama) tare da sauran masu ruwa da tsaki da kuma xaliban da suka wakilci Nijeriya kuma suka lashe gasar ‘Global Robotic Olympics’ jiya a fadar Shugaban Qasa dake Abuja

Kwastan Ta Qwace Sama ‘Yan Sanda Sun Cika Hannu Da Motoci 100 A Sakkwato Da Masu Garkuwa A Katsina > Shafi na 2

> Shafi na 4


2 LABARAI

A Yau

Jami’an Tsaro Sun Qwace Sama Da Motoci 100 Masu Tsada A Sakkwato Daga Umar A Hunkuyi

Jami’an tsaro na Hukumar Kwastam, da ke lura da Jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara, da haxin gwiwan wasu sassa na Jami’an tsaron, sun qwace aqalla Motocin qasaita 160 da aka voye su a wani gida da ke can lungu cikin garin Sakkwato. Motocin yawancin su Jifa-Jifai ne sabuwar qirar, Toyota SUV Avensis, an ce wani sanannen xan siyasa ne a Jihar ya jibge su domin tunkarar zaven 2019. Duk da shike har zuwa lokacin haxa wannan rahoton, ba wani jami’i daga hukumomin tsaron da ya bayar da dalilin qwace motocin, sai dai, wata majiya daga hukumar ta Kwastam ta ce, sun saba gudanar da makamancin wannan samamen tare da haxin gwiwan wasu sassan na Jami’an tsaro. “Kan yawan motocin da muka qwato, a yanzun ba ni da tabbacin adadin su. Sai dai duk motoci ne masu tsada, sun kuma zarta 150,” in ji

majiyar. Harin cikin daren, an ce an kai shi ne wani gida da ke wajajen anguwar Ruggan Waru, sashen Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Aliyu Shinkafi, da ke Sakkwaton. Duk qoqarin da muka yi na sanin wa ke da motocin ya ci tura. An dai tabbatar wani hamshaqin xan siyasa ne na Jihar ya ajiye motocin sama da 150 don zaven 2019. Majiyar tamu da ba ta so a ambaci sunan ta ba, ta ce, da jimawa jami’an tsaron na da labarin ajiye motocin, ta ce, sun dai hanqure ne har kawo yanzun don a kammala jibge motocin sannan su kawo harin. “Ba wanda ya yi zaton faruwan makamancin hakan a wannan gidan, saboda a kodayaushe gidan mai doguwar Katanga a kulle yake. “Jami’an tsaro na farin kaya ne suka fara labarta mana lokacin da suke shigo da motocin kaxan-kaxan. Aikin da muka yi ba yana nufin mun yi hukunci ne ba, mun dai yi aikin mu ne kaxai kamar yadda doka ta xora mana.”

Matan Chibok: Fadar Shugaban Qasa Ta Mayar Wa Salkida Martani Daga Bello Hamza

Ofishin shugaban qasar Nijeriya ta ce, bayanin nan da xan jarida Ahmed Salkida, ya yi a kafar sadarwa ta Twiter na cewa wasu daga cikn ‘yan matan Chibok da aka sace sun mutu, bayani ne da gwamnatin shugaba Buhari bata da shi a hukumance. A na da yaqinin cewar, Mista Salkida nada kusanci na musamman ga qungiyar Boko Haram, qungiyar da tayi garkuwa da ‘yan mata 217 daga makarantar GSS Chibok a shekarar 2014. Yayin da aka riga aka tsirar da dayawa daga cikin ‘yan matan ta hanyar yarjejeniya da ‘yan Boko Haram xin wasu kuma tuni suka gudu daga inda ake tsare dasu yayin da fiye da ‘yan mata 113 suke hannun su har yanzu. A wani saqonnin Twiter da Mista Salkida, ya watsa ranar Asabar da tayi dai dai da shekara 4 da sace ‘yan matan yace, ‘yan ,mata 15 ne kawai ked a rai a cikin waxanda suka rage. Ya ce, majiyarsa daga cikin qungiyar ta Boko Haram ta bayyana masa cewar sauran sun mutu ne a hare jaren da sojojin Nijeriya suka yi kai wa ne a lokuttan baya. Da jami’an gwamnatin tarayya ke maid a martini sun

ce bayanan da Mista Salkida ya yi babu a cikin bayanan da gwamnati ked a shi a hakin yanzu. Gwamnati ta qara da cewa, basu samu irin wannan bayanan daga waxanda suka ksace ‘yan matan ko kuma qungiyoyin qasa da qasa da suke hulxa dasu. Jami’in watsa labaran shugaban qasa, Garba Shehu, a wata sako daya aika wa PREMIUM TIMES, y ace, bas u tava sanya Mista Salkida a qoqarin karvo ‘yan matan Chibok 100 da aka yi a baya ba, kuma har a aka mayar dasu ga iyalansu. Mista Shehu basu sanya xan jaridar cikin qoqarin sakin ‘yan matan ba a wannan karon. “In ma akwai wani bayani daya ke dasu gae da ‘yan matan Chibok to har yanzu bai tuntuvi gwamnatin Nijeriya da wannan bayanin ba” “Saboda haka duk wani neman qarin bayani da kuke nema kuna iya gabatar dasu ga Mista Salkida,” inji Mista Shehu Ya qara da bayanin cewar, bayanan dake hannun gwamnati da qungiyoyin qasashen waje na qarfafa su wajen ci gaba da neman ceto sauran ‘yan matan Chibok, ba zasu yi qasa a gwiwa ba domin ganin haka.

Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Azzalumai Ne Suke Tsiyata Nijeriya –Buhari Daga Umar A Hunkuyi

Shugaban qasa, Muhammadu Buhari, ya zargi waxanda ya bayyana da azzalumai da laifin tsiyata ‘yan Nijeriya. Shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi A Laondon, sa’ailin da yake maraba da wata qungiyar magoya bayansa qarqashin jagorancin, Mista Charles Sylvester. Sai dai, ya ce, bisa la’akari da yadda gwamnatinsa ta sami qasarnan, ba komai a asusunta kuma tattalin arzikinta a ruguje, “ai mun xan tavuka.” Buhari ya ce, varnar da aka yi wa tattalin arziki a lokacin da azzaluman ke mulki yana da yawa, gwamnati na iya qoqarinta na qwato wasu daga kuxaxen da aka sata, duk da ba a iya gano duka. “In a ce sun yi aiki da kashi 50 na kuxaxan Mai da muka samu lokacin da yake dala 143 kan ganga guda, muna kuma fitar da ganga milyan

2.1, a kullum, da ‘yan Nijeriya sun ji daxi. “Za ka iya yin shuka a kan hanyoyinmu, domin duk an yi watsi da su. Satar ta yi yawa, har ma sun kasa voye ta sosai. Buhari, ya yi nuni da yadda Allah Ya azurta Nijeriya da yawan al’umma da kuma albarkatun qasa, sai ya yi juyayin gazawar da wasu da suka yi shugabanci a baya suka kasa cin moriyar su, wanda ta sabbaba kasawan da gwamnatin sa ta yi na cin gajiyar albarkatun qasar domin ta kyautata rayuwar al’umma. Sai dai ya yaba wa ‘yan Nijeriyan da ke waje masu qoqarin kare qasar su, ya bayyana hakan da sadaukarwa. Da yake na shi jawabin, jagoran qungiyar, Mista Charles Sylvester. Cewa ya yi, qungiyar na su tana farin ciki da irin ci gaban da gwamnatin Buhari xin ta kawo ya zuwa yanzun. Ya yi nu ni da cewa,

Buhari, ya gama da yawancin matsalolin da ya taras, musamman a sassan Noma, sauqaqe hanyoyin yin ayyuka, yaqi da cin hanci da rashawa, samawa matasa ayyuka ta hanyar shirin N-Power, da kuma samar da asusun baixaya, (TSA), da sauaran su. Ya kuma yabawa gwamnatin kan yaqin da take yi da ta’addanci a Arewa maso Gabas, da kuma shelantawan sake tsayawa takara da ya yi a 2019. “Mun kuma yaba gaggawan da gwamnatin ka ta yi na amso ‘yan matan Dapchi. Hakan ya nu na lallai kai Janar ne. “Allah da Ya warkar da kai da ba ka lafiya, Shi ne zai ba ka nasara a 2019. Kai Janar ne da ba ka shakkan faxa da Janarori ko waxanda ba Janar xin ba.” “Mun shelanta qauna da goyon bayanmu gareka. Yanzun kana ta gyaran varnar da aka yi ne, zuwanka na biyu ne za ka gina sabbin ayyuka,” Inji shi.

Zan Bayar Da Goyon Baya Ga Majalisar Masu Ruwa Da Tsakin Arewa –IBB Daga Umar A Hunkuyi

Tsohon Shugaban qasa, Janar Ibrahim Babangida, ya yabawa qungiyar Shugabannin Arewa, (NLSA), kan qoqarin su na ganin ci gaban qasarnan, ya kuma alqawarta goyon bayan shi ga qungiyar na su. Babangida, ya yi wannan alqawarin ne Jiya, sa’ilin da wakilan qungiyar suka ziyarce shi a Minna. Babangida, ya bayyana qungiyar a matsayin, “Qungiyar da ya kamata a

•IBB

qarfafe ta,saboda dagewar ta na samar da haxin kan ‘yan qasannan, da kuma kawo gyara a cikin qasar. “Za mu qarfafi abin da ku ke yi, mu kuma mara maku har ku ci nasara.” Shugaban qaungiyar, Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana qungiyar a matsayin wacce ba ta siyasa ce ba. Ya ce, duk xan Arewa yana iya shiga qungiyar, ba tare da la’akari da kasancewar qabila ko Addinin ko Jam’iyyar shi ba.

Ya qara da cewa, “Kasancewar mu ba Jam’iyyar siyasa ba, manufar mu ita ce, samar da fahimtar juna da haxin kai. Yakasai ya ce, an kafa qungiyar ce ranar 10 ga watan Fabrairu 2018. Daga nan sai qungiyar ta naxa IBB a matsayi na Uban qungiyar na ta. Kaxan daga cikin wakilan qungiyar sun haxa da tsohon Shugaban Majalisar wakilai, Alhaji Ghali Na’abba, da tsohon gwamnan Jihar Neja, Dakta Babangida Aliyu.


3

A Yau Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Ra’ayinmu

Sunayen Verayen Gwamnati: Share

A

Fagen Siyasar 2019

kwanakin baya ne babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta bugi qirji ta qalubalanci jam’iyyar mai mulkin qasar, APC, da cewa, idan ta isa ta fitar da jerin sunayen verayen da su ka sace kuxaxen gwamnati, musamman a zamanin da ita PDP xin ke riqe da madafun ikon qasar. Ita kuwa APC ba ta yi qasa a gwiwa ba, sai ta biye wa PDP xin, ta fitar da jerin sunayen wasu ’yan siyasa da a ke tuhuma da laifukan sace-sacen kuxaxen gwamnati a lokacin da a ka damqa mu su amanar ’yan qasa. Tabbas jerin sunayen, waxanda ministan yaxa labarai Mista Lai Mohammed ya fitar a lokuta mabambanta, sunaye ne na ’yan siyasar da ke fuskantar qalubalen tuhuma a gaban kotuna dabandaban ko hukumomin yaqi da cin hanci da rashawa na qasar, ICPC da EFCC ko kuma hukumar kula da xa’ar ma’aikata ta Nijeriya. A wannan kam bau qarya, babu sharri, to amma fa yawancinsu har kawo yanzu gwamnatin ta APC ba ta iya yin nasarar kama su da laifi a gaban kotu ba, ballantana a hukunta su. Bugu da qari, babban abin lura shi ne babu ’yan APC ko qwaya xaya, waxanda a baya su ke gwamnatin PDP, amma su ka yi tsallen baxake su ka dawo APC xin ba, bayan da su ka raba hanya da tsohuwar gwamnatin ta APC. Abin nufi a nan shi ne, maimakon gwamnatin APC ta fitar fa jerin sunayen duk waxanda a ke zargi da sace dukiyar al’ummar qasa a lokacin na PDP ba tare da warewa ko la’akari da waxanda su ka fice daga PDP xin su ka dawo APC ba, a’a, sai gwamnatin ta fitar da zallar waxanda har yanzu su ke cikin PDP kaxai; sauran kuwa da alama sun sha kenan, domin ba sa cikin waxanda za a yiwa terere. Daga dukkan alamu, haqiqa wannan salon ba komai ba ne face tabbatuwar sharar fage ga siyasar 2019, lokacin da za a gudanar da manyan zavukan qasar. Ita kanta PDP ta yi tsaurin kai da yawa da ita fitowa ta murje idanunta a gaban ’yan Nijeriya har ta qalubalanci APC a kan ta idan ta isa ta fitar jerin sunayen

waxanda ta ke zargi da kasancewa manyan veraye a lokacin baya. Kada manta, dukkan varnar da ta faru a gwamnatin baya, ta faru ne fa a qarqashin gwamnatin PDP, wacce ita ce mulki qasar tun daga lokacin da Nijeriya ta dawo mulkin farar hula, bayan da soja

ya miqa mulki ya koma bakin aikin da kundin tsarin mulki ya tanadar ma sa na tsaron qasa. Shekaru 16 PDP ta yi ta na riqe da madafun iko tun daga 1999 har zuwa 2015, inda ta yi faxuwar baqar tasa a babban zaven shekarar, wanda wannan shi ne

EDITA Sulaiman Bala Idris

MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama

MATAIMAKIN EDITA Bello Hamza

DARAKTAN SASHE Mubarak Umar

RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah

BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John

manufarmu

LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!

faxuwar zave irinsa na farko a tarihin siyasar qasar, domin a lokacin ne shugaban qasa mai ci ya faxi a zavi yayin da ya ke yunqurin yin tazarce a karo na biyu. To, amma a zahirin gaskiya za a iya cewa, talakan Nijeriya ba fitar da jerin sunaye ya ke buqata ba; abinda ya fi buqata shi ne a hukunta waxanda su ka aikata laifukan a cikin shekaru ukun nan da APC ta amshe ragamar mulkin qasar, sannan kuma a dakatar da irin wannan ha’incin ya tsaya cak! Sai dai kuma wani abin takaici shi ne, ko a cikin gwamnatin ta APC an samu irin wannan matsalar, inda a ke zargin wasu manyan jami’an gwamnatin da aikata irin wannan mummunar xabi’a, amma kuma APC xin sai ta yi murqisisi ta qi saka sunayensu a jerin sunayen verayen na na lalitar gwamnatin. To, qarara hakan na nufin cewa, an shiga fagen wasan siyasar 2019 kenan, inda za a cigaba da musayar yawun da ya wuce haka a nan gaba. Ba zai zama abin mamaki ba, idan PDP ita ma ta fitar da nata jerin sunayen, wanda babu tantama za ta kwaye bayan ’yan APC ne, domin ta xauki fansa kan kwance ma ta zani a kasuwa da APC ke shirin aikatawa a yanzu da sunan fitar da jerin sunayen waxanda a ke zargi da aikata hali ko samartakar vera a gwamnatin Nijeriya. Wannan zai iya buxe qofar da ita kuma APC za ta iya mayar da martani ta hanyar sauya wani salon na siyasa, la’alla ma za ta iya yin barazanar kamawa da garqame wasu ’yan siyasar ta PDP, don rufe bakunansu, kamar yadda ita ma PDP xin ta yi aikata hakan a baya, inda ya riqa yin amfani da musamman EFCC wajen yunqurin hana wasu ’yan adawa takara, la’alla ko da sunans ne dai ya vaci ko kuma ta hana su sakat har zuwa lokacin gudanar da manyan zavukan, wanda a sannan kuma lokaci ya qure mu su na dawowa su gyara qimarsu a idanun masu kaxa quri’a. To, ko ma dai mene ne zai faru, a fili ta ke cewa, an gama share fagen siyasar 2019. Shi xan tsako mai rabon ganin baxi, ko a na muzuru ko a na shaho, sai ya gani!!!


4 LABARAI

A Yau

Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab 1439)

Tsaro Ne Ke Gabana Ba Zaven 2019 Ba –Buhari Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja

A wata ganawar aiki da Shugaban Qasa Muhammadu Buhari yayi da Firayiministar Birtaniya, Theresa May jiya a Birnin Landan, Shugaban ya bayyana abubuwan da ke gabansa fiye da zaven shekarar 2019 mai zuwa. Abubuwa biyu ne shugaban ya zayyana a matsayin waxanda

su ne a gabansa; harkar inganta tsaro da kuma batun tattalin arzikin qasa. Shugaba Buhari ya ce; “Mun yi yaqin zave ne da zimmar tabbatar da muhimman abubuwa uku, tabbatar da tsaro a qasar, havvakawa da farfaxo da tattalin arziki da kuma yaqi da cin hanci da rashawa. “Za a gudanar da wani babban zaven qasa a shekara

mai zuwa, tuni ‘yan siyasa sun wasa wuqaqensu kan wannan zaven, ni kuma babban abin da ke gabana shi ne tabbatar da tsaro da farfaxo da tattalin arzikin qasa.” Inji Shugaban Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya shaidawa Firayiministar cewa, Nijeriya da Birtaniya sun jima da kyakkyawar alaqa a tsakanin qasashen biyu.

Sannan kuma Shugaban ya yaba wa kamfanonin Qasar Birtaniya irinsu Unilever, Cadbury, da dai sauransu waxanda suke matuqar taimakawa Nijeriya hatta a lokutan yaqin basasa. Daga qarshe Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya yi wa Firayiminista Theresa May qarin haske dangane da irin nasarorin da aka samu

a fannin noma, lamarin da ya tseratar da Nijeriya daga annobar yunwa. A yayin da take tofa albarkacin bakinta, Firayiministar Birtaniya, Theresa May ta jaddada cewa, za su ci gaba da yin aiki kafaxa da kafaxa da Nijeriya, musamman wurin horaswa da bayar da kayan aiki ga sojojin Nijeriya.

Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Alqawarin Sake Sakin Sunayen Varayi Daga Umar A Hunkuyi

A ranar Lahadi ne gwamnatin tarayya ta yi alqawarin sake sakin wasu sunayen na mutanan da take zargi da tsiyata qasarnan. An dai yi ta sukan sunaye kashi biyun da ta saki a baya da cewa duk ‘yan adawarta ne na Jam’iyyar PDP. Ba wanda aka xaure cikin su, wasun su ma an yi masu shari’a, wasun su ma ko tuhumar su da aikata laifi ba a yi ba. A jawabin da ya saki a Legas ranar Lahadi, Ministan al’adu da yaxa labarai, Lai Mohammed, cewa ya yi, tun lokacin da aka saki jerin sunayen biyu na varayin da ake zargi, an yi ta qoqarin suka da shafawa gwamnatin tarayya kashin kaji, kan ta daina sakin sunayen. “Marubutan qarya da kafafen yaxa labarai da yawa sun ta sukan gwamnatin tarayya kan sakin sunayen. Da yawa suna zargin sanya siyasa cikin yaqin da ake na cin hanci da rashawa, ta hanyar sakin sunayen, sam ba mu yarda da sukan na su ba.” “Ba mu da ikon xaure kowa. Wannan aikin kotuna ne. amma muna da ikon shaidawa ‘yan Nijeriya waxanda suka wawashe masu dukiyar su, ta hanyar

•Ministan yaxa labarai, Lai Mohammed

gabatar da qwararan shaidu, mu abin da muke yi kenan,” in ji shi. Sai dai savanin abin da Lai Mohammed xin ne ya faxa, gwamnati tana da qarfin kamawa da hukunta kowa da ake zaton ya saci dukiyar al’umma, kuma ta na yin hakan. Amma cewan da ya yi hakan aikin Kotuna ne, gaskiya ne. “Duk masu maganan an sanya siyasa cikin lamarin, suna so su hana gwamnati sake sakin sunayen ne, in mutum dubu za su yi rubutun sukar mu, hakan ba zai hana

mu sake sakin sunaye a karo na uku ba,” in ji Lai. Ministan, ya qalubalanci duk wanda yake jin qage aka yi ma shi da ya nufi Kotu, maimakon ya tsaya yana zage-zage. Jim kaxan, kafin wannan bayanin da Lai Mohammed, ya aikewa kafar sadarwa ta, PREMIUM TIMES, fadar gwamnati ta saki wani bayanin, inda Shugaba Buhari ya sake zargin gwamnatin PDP, da tsiyata Nijeriya. Inda Buhari ke cewa, lalata tattalin arzikin da aka yi

lokacin waccan gwamnatin ya yi yawa, amma gwamnatin sa na qoqarin qwato wasu daga cikin abin da aka sata, amma ya ce, bai yiwuwa a iya qwato duka. “In a ce sun yi aiki da kashi 50 na kuxaxan Mai da muka samu lokacin da yake dala 143 kan ganga guda, muna kuma fitar da ganga milyan 2.1, a kullum, da ‘yan Nijeriya sun ji daxi. “Za ka iya yin shuka a kan hanyoyinmu, domin duk an yi watsi da su. Satar ta yi yawa, har ma sun kasa voye ta sosai.

Buhari, ya yi wannan maganan ne daga London, lokacin da yake maraba da wasu magoya bayansa da suka kai ma shi ziyara qarqashin jagorancin, Mista Charles Sylvester. Da yake na shi jawabin, jagoran qungiyar, Mista Charles Sylvester. Cewa ya yi, qungiyar na su tana farin ciki da irin ci gaban da gwamnatin Buhari xin ta kawo ya zuwa yanzun. Ya yi nu ni da cewa, Buhari, ya gama da yawancin matsalolin da ya taras, musamman a sassan Noma, sauqaqe hanyoyin yin ayyuka, yaqi da cin hanci da rashawa, samawa matasa ayyuka ta hanyar shirin N-Power, da kuma samar da asusun baixaya, (TSA), da sauaran su. Ya kuma yabawa gwamnatin kan yaqin da take yi da ta’addanci a Arewa maso Gabas, da kuma shelantawan sake tsayawa takara da ya yi a 2019. “Mun kuma yaba gaggawan da gwamnatin ka ta yi na amso ‘yan matan Dapchi. Hakan ya nu na lallai kai Janar ne. “Allah da Ya warkar da kai da ba ka lafiya, Shi ne zai ba ka nasara a 2019. Kai Janar ne da ba ka shakkan faxa da Janarori ko waxanda ba Janar xin ba.”

‘Yan Sanda Sun Cika Hannu Da Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Rundunar ‘yan sanda jihar Katsina ta ce ta yi nasarar damke wasu mutane huxu da suka yi shigar burtu waxanda suka qwarai da yin garkuwa da mutane domin neman kuxin fansa. Jami’in hulxa da jama’a na rundunar DSP Gambo Isah ya bayyana haka ga maneman labarai a Katsina , ya ce an samu nasarar a lokacin da jami’an su suka ga alamun wasu mutane biyu suna yawan shige da fice tare da wani da ya sanya hijabi ya rufe fuskarsa

kamar mace. Ya ce wannan lamari ya faru ne a unguwar G.R.A da ke kusa da ofishin hukumar zave ta qasa reshen jihar Katsina. DSP Gambo Isah ya ce sakamakon xaukar matakin da jami’ansa suka yi ne ta hanya tura masu sa ido, ya sa suka yi nasarar tsafke mutane huxu da suka haxa da Mubarak Babangida xan shekaru 21 da ke unguwar Dutsen safe da Abubakar Lawal Suleiman xan shekaru 19 da ke unguwar Qerau sai kuma Aliyu Lawal xan shekaru 22 da ke unguwar Adoro tare

da Nura Abdulhamid da aka fi sani Bazgi xan shekaru 22 duk acikin Katsina. Ya qara da cewa waxanda aka kama xin sun tabbatar da laifin da ake zarginsu da aikatawa inda suka bayyana cewa sun zo domin su sace xan wani mutun kai suna Alhaji Rabi’u Gide mai shekaru huxu Allah bai ba su sa’a ba. Acewar jami’in hulxa da jama’a na rundunar bincike game da wannan lamari dai ya yi nisa saboda haka da zaran sun kammala za su miqa su zuwa gaban kuliya manta sabo domin fusknatar hukuncin

abinda suka aikata. A wani labarin kuma jami’in hulxa da jama’a na rundunar DSP Gambo Isah ya ce sun kama wani mutun da ake zargin ya qwarai wajan yin garkuwa da mutane domin neman kuxin fansa. ‘Yan sanda sun yi nasarar damke Gambo Lawal mai shekaru 26 xan asalin qaramar hukumar Xanmusa a ya yin da yake qoqarin haxa baki da wasu abokansa wanda yanzu ake neman ruwa a jallo domin sace wani mutun mai suna Alhaji Mustapha Kabirn Dogon Gida a qaramar

hukumar Xanmusa da ke jihar Katsina A lokacin wannan samamaye an samu layin wayar salula da yawa a hannun wanda ake zargi wanda kuma yake amfani da su wajan aikata laifuffuka kamar yadda bincike ya nuna. ‘’wanda ake zargin bai tsaya baiwa baincike wahala ba, inda ya tabbatar da wannan laifin da ake zarginsa da aikatawa, har ma ya qara da cewa yana cikin mutanan da suka addabi wannan yanki da sace sacen jama’a da kuma fashi da makami’’ in ji shi


LABARAI 5

A Yau Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Yawan Masu Rubuta Jarabawar NECO A 2018 Ya Qaru Ci Gaba Daga Shafin Farko

Ya qara da cewa, a wannan shekarar a ana gudanar da jarabawar ne a dukkan faxin qasar ba kamar shekarar 2017 da ba a gudanar da jarabawar a jihar Borno da Adamawa ba saboda harkokin ‘yan tayar da qayar baya. “Na zo ne domin ganin yadda ake gudanar da jarabawar, ina son ganin ko wurin da akr gudanar da jarabawar ya cancanci a yi jarabawa a ciki ko a a, na samu tabbacin lallai ana gudanar da jarabawar a yanayin day a kamata na kuma ji daxin abin dana gani a halin yanzu” Ya kuma qara bayyana cewa, yawan waxanda suka samu nasara a jarabawar ne zai nuna yawan xaliban da za a xauka zuwa makarantun gwamnatin tarayya dake

faxin qasar nan” A nasa jawabin, magatakarda hukumar NECO, Charles Uwakwe, a ana gudanar da jarabawar ne a faxin tarayyar qasar nan a lokaci xaya tare da cikkaken tsaro. Ya ce, xalibai daga jihar Legas su suka yawa, in da suka kai 25, 800 yayin da jihar Zamfara ce take da xalibai mafi qaranci da xailibai 28. “A nazarin da nayi aikin yana tafiya cikin tsari, Minista ya ce mu ba kowa kafar gwada sa’arsa saboda kada a hana kowa samun daman shiga makarantun” “Babu wani matsala daga jihar Barno sune ma suka fi yawan xalibai a Arewa maso Gabas da xalibai 79,887, jihar Legas ked a xalibai mafi yawa na 25,800 yayin da jihar Zamfara ked a mafi qarancta” Ministan ya kuma ce a

wannan shekarar mun yi tanadi na musamman ga xalibai masu naqasa saboda suma su samu daman shiga makarantun Unity na gwa,mnatin tarayya. Ya ce, ma’aikatan ilimi zata xauki xalibai ne ta cin jarabawar da suka yi. Wakilinmu daya zagaya don lura da yadda aka yi jarabawar ya lura da cewa, a fara gudanar da jarabawar a kan lokacitare da halartar jami’an tsaro. An gudanar da jarawar ne cikin kwanciyar hankali a Government Secondary School, Wuse Zone 3 da Government Secondary School, Garki da Tudun Wada Secondary School in Zone 4 duk a cikin garin Abuja. An kuma lura da cewa, xaliban sun fito jarabawar ne a cikin kayan sun a makaranta tare da rakiyar iyayensu.

•Malam Adamu Adamu

Tambuwal Ya Bai Wa Zawarawa Gudummawar Buhunan Hatsi 1000 A Sakkwato Daga Umar A Hunkuyi

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya rabawa Matayen da Mazajen su suka rasu da mabuqatan Jihar buhunan hatsi 1000, ta Ofishin Kwamishinan Zakka da agaji na Jihar. Da yake jawabi wajen rabon hatsin, Shugaban hukumar, Malam Lawal Maidoki, ya ce, wannan gudummawar daga aljihun Tambuwal ta fito domin tallafawa Matayen da

mabuqata. A cewar Maidoki, Matayen ne suka nemi taimakon domin su ciyar da marayun su. Da yake bayyana hanyar da aka bi wajen raba hatsin, ya ce, kowace mace za ta samu buhun hatsi guda gami da Naira 1000, wanda za su biya dakon kayan zuwa gidajen su. Maidoki ya ce, Gwamnan ya bayar da agajin buhun hatsi 1000 ne da suka haxa

da, buhun shinkafa 250, sauran kuma na, Gero, da Dawa ne,domin a rabawa matan da mabuqatan Jihar. “Ya yi hakan ne domin ya sauqaqewa masu qaramin qarfi masifar talauci da Yunwa a Jihar. “Wannan agajin na taimakawa matayen da kuma mabuqata a Jihar, lamari ne da zai ci gaba da gudana, bisa qoqarin Gwamnan na bunqasa rayuwar mutanan sa.

Boko Haram Ta Yi Garkuwa Da Yara Fiye 1,000 Tun Bayan Sace ’Yan Matan Chibok

•Wasu daga matan Chibok da aka ceto a kwanakin baya Daga Bello Hamza

Aqalla yara fiye da 1,000 qungiya Boko Haram tayi garkuwa dasu tun bayan sace ‘yan matan makarantar Chibok da suka yi shekara 4 da suka wuce, Inji qungiyar majalisar xinkin duniya ta UNICEF. Shekara 4 ke nan tun bayan harin da yan ta’aada suka kai makarantar Chibok inda suka sace yanmata 276, qungiyar UNICEF ta ci gaba da kiran Lallai a saki yan matan tare da kawo qarshen hare haren da ake kai wa makarantu a faxin yankin. Fiye da matan Chibok 100 ne har yanzu ke a hannun yan ta’aada ba tare da an samu kwato su na, har yanzu majalisar xinkin duniya da ci gaba da sa kiran a sako su da gaggawar. “Zagayowar shekara 4 da sace yan matan Chibok yana qara tuna mana cewar har yanzu yara sashin Arewa mask Gabas na ci gaba da fuakantar hare hare mai girman gaske” Inji Wakilin qungiyar UNICEF a Nijeriya Mohamed Malick Fall. “Ana ci gaba da kai musu haren taaddacin a gidajensu da makarantu da wurare gudanar da karuwar su” Harin da aka kai garin

Dapchi kwanan nan inda yanmata 5 suka rasa rayukansu nuni ne da cewa wurare kaxan ne ya rage wa yara a yankin Arewa maso Gabas, makarantu ma basu tsara daga taaddacin ba. “Waxannan hare harem akan makarantu dake rutsawa da yara babu dalilin yin haka “ Inji Fall. “Yara da na haqqin a basu ilimi da kariya na musamman, dole aji Ya zama wuri dake da aminci daga dukkan nauyin cuta” Tun da aka fara wanna rikicin a shekarar 9 da suka wuce a kashe Aqalla Malama makarantar 2,295 sun kuma lallata makarantu fiye da 1,400. Har yanzu ba a buxe makarantun ba saboda tsananin lallacewar da suka yi da kuma matsalar tsarin Sanya addabi yankin a halin yanzu. Gwamnatin Nijeriya ta qudiri aniyar tabbatar da tsaro a makarantu da kuma kare su daga hare hare, qungiya UNICEF na tare da gwamnati a kan wannan qudurin inda gwamnati ke bayar da tsaro Na musamman ga manya da qananan makarantun yankin daga duk nauyin hare hare a yayin rikice rikice.

Rajistan Masu Zave: An Ya Rajistan Mutane 110,000 Cikin Wattani 10 A Sakkwato Daga Umar A Hunkuyi

An yi rajistan aqalla mutane 110,000 da suka cancanci kaxa quri’a, a aikin rajistan masu jefa quri’a da ake yi a Jihar Sakkwato, Jami’in ilmantarwa da wayar da kai na hukumar zaven mai zaman kanta, Musa Muhammad, ne ya tabbatar da hakan. Ya qara da cewa, ya zuwa yanzun ba zai iya cewa ko mutane nawa ne aka yi wa rajistan ba, domin har yanzun aikin na ci gaba da gudana ne.

Musa, ya yaba da yawan masu zuwa yin rajistan, a cewarsa,sun cancanci a yaba masu, inda ya ce su na zagayawa ne Anguwa-Anguwa domin su tabbatar komai na tafiya yadda ya kamata. “A qarshe, hukumar INEC, za ta tantance bakixayan rajistan da aka yi, ta kuma tabbatar da ta soke duk waxanda suka yi rajista sau biyu. Sai bayan an gama tantancewan ne,za mu iya cewa ga yawan mutanan da aka yi wa rajistan a Jihar.


6 LABARAI

A Yau

Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Annobar Cutar Zazzaven Lassa Ba Ta Bulla A Asibitinmu Ba –FMC Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Hukumar gudanarwar babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Yola FMC, ta musanta rahotannin da wasu kafafen sadarwa ke yaxawa cewa an samu bullar annobar cutar zazzaven Lassa a asibitin. Da yake magana da manema labarai a Yola, shugaban sashin ayyuka na babban asibitin Dakta Joel Yohanna, yace asibitin ashirye yake da ya tinqarin bullar kowace irin barazana da ta annoba a jihar. Yace babu wani rahoton bullar annobar a jihar Adamawa, yace mutumin da ya mutu sakamakon kamuwa da cutar daga jihar Taraba ya fito, inda aka kwantar dashi a wani qaramin asibiti a Yola bisa tsammanin zazzaven cizon sauro ke damunshi. Yace mutumin ya kwanta tsawon kwanaki huxu kafin

amaishe dashi babban asibitin na FMC, kafin daga bisani ya mutumin ya rasu, yace dama an kive mutumin a wani wurin musamman da’aka tanadar domin kwantar da masu xauki da cutar annobar Ebola, kafin agano mutumin na xauki da cutar zazzaven Vera ne. Ya ci gaba da cewa babu wani daga cikin likitoci ko qananan ma’aikatan jinya da suka kamu da cutar wacce dama tun da farko an xauki matakin kariya daga mutumin wanda ya mutu bayan kwanaki huxu a asibitin. Dakta Joel, yace batun harkoki ya tsaya a asibitin qarce kawai, domin komai na tafiya daidai inba a kafafen sadarwa ba, hatta ma’aikatan asibitin basusan wani abu ya faru makamancin haka ba, komai na tafi daidai. “kaga dai gashi komai na

tafiya daidai a asibitinnan, kuma babu batun bullar Lasa Fever a kowani yanki na asibitin, shi marar lafiyar daga asibitin Peace Hospital aka kawoshi nan FMC, kuma mun kiveshi kafin ya mutu. “kuma mun tuntuve iyalan mamacin da ‘yar ‘uwar gyatumarshi, wacce itama muka xauketa zuwa nan asibitin mun kiveta muna bincike akanta haka kuma duk ma’aikatan asibitin da suka dubata suna xauke da kayan kariya domin kaucewa matsalar” inji Joel. Ita kuwa gwamnatin jihar Adamawa ta bakin kwamishiniyar lafiya ta jihar Dakta Fatima Atiku Abubakar, tace mutumin da ya mutum shine bullar cutar na farko a yankin arewa maso gabashin Nijeriya. Tace tuni gwamnatin jihar ta samar da cibiyoyi

•Dakta joel Yohanna

da tawagar kwararru daga ma’aikatar lafiyar da sauran masu kwararru a fannin ganowa da sanin annoba da suke wakiltar qungiyar lafiya ta duniya WHO domin bincike kan xaixaikun mutanen da mamacin ya’yi mu’amala dasu. Mutumin da ya gamu

da ajalinsa sakamakon kamuwa da cutar xan asalin jihar Adamawa, an bayyana sunanshi da Gabriel Ambe, ma’aikaci a rundunar tsaro ta Civil Defense (NSCDC) da ke aiki a yankin Gembu cikin qaramar hukumar Sardauna a jihar Taraba.

Shugaban Qaramar Hukumar Taraba Ya Koka Kan Yawan Shigowar ’Yan Gudun Hijira Daga Umar A Hunkuyi

Shugaban Qaramar Hukumar Donga ta Jihar Taraba, Mista Nashuku Ipeyen, ya koka kan yawan ‘yan gudun hijira da suka kai 4,000, a Qaramar Hukumar ta shi, sakamakon ci gaban kai hare-haren da makiyaya ke yi a yankin. Ipeyen, ya bayyana hakan ne sa’ilin da yake zagayawa da manema labarai sansanonin

na ‘yan gudun hijira da ke makarantun Firamare biyar na garin na Donga. Shugaban ya ce, sati guda kenan da soma kai hareharen a qauyakun Muzi, Utile, lokacin da makiyayan ke dawowa daga Takum, sai kawai suka buxewa mazauna qauyakun wuta. Ya yi nu ni da yadda hareharen suka watsu zuwa wasu qauyakun da suka haxa da Tormom, Shaakaa, Ovoh, Igo

da Burukunu. Ipeyen ya ce, kwararowar ‘yan gudun hijirar Shalkwatar Qaramar Hukumar, ya haifar da matsaloli masu yawa, duk da gaggawan xaukan matakan da gwamnatin Jihar ta yi wajen kawo agajin kayayyaki ta hannun hukumar SEMA. “Maganan nan da nake da ku, makiyayan na ci gaba da kisa da qona wasu qauyakun ne.

“Daga lokacin fara kawo harin kawo yanzun, sun kashe mana mutane 20, dubbai kuma sun rasa gidajen su na gado,” in ji shi. Ipeyen, sai ya kirayi mutanen yankin da su yi amfani da sanduna da duwatsu su kare qasar su daga maharan. Kansilan yankin, Mista Samaila Ulaha, ya shaidawa manema labarai cewa, Makiyayan sun qaddamar

da harin ne kan mutanan yankin bisa zargin da suke ma mazauna yankin na wai tona asiran su kan hare-haren da suke kaiwa Qananan Hukumomin Takum da Ussa. Uwargida Terhembe Nyijimi, 42, mahaifiyar ‘ya’ya 10, da ke gudun hijira a babbar makarantar Firamare ta Donga, ta shaidawa manema labarai, manyan matsalolin su, su ne, ruwa, abinci, tufafi da magunguna.

Mai Talla Shi Ke Da Riba:

LEADERSHIP A YAU Ta Shirya Tsaf! Kamar yadda kowa ya sani ne, wannan jarida mai albarka, LEADERSHIP A YAU ta kafa tarihi wajen zama jaridar Hausa da ta fara fitowa a kullum. Wannan fara fitowa a kullum yana da alfanu masu yawan gaske, gare mu Kamfanin LEADERSHIP da ku masu karatu, musamman masu sana’o’i manya da qanana. Wannan ne ya sa muke farin cikin shaida wa masu karatunmu cewa mun shirya tsaf domin tallafa wa kasuwancinku, ta hanyar tallata maku shi zuwa inda ba ku zata ba. Domin a halin yanzu mu kanmu da muke buga wannan jarida ba za mu iya bayyana iya inda ta ke shiga ba. Muna da tsare-tasare da dama don talla ku da hajojinku, inda muka fitar da tsarin ‘IYA KUXINKA IYA SHAGALINKA.’ Wato akwai cikakken shafi, akwai rabi, akwai kwata, akwai kuma daidai iyaka abin da mutum ke so a sanya masa. Wanda a wannan shafin muna so masu sana’o’i, musamman manyan dillalai su tallata hajojinsu, su qananan ’yan kasuwa akwai

nasu tsarin. A wani tsarin ma da muke da shi, akwai yanayin da mutum zai tallata hajarsa, sannan ya tallata kansa, inda za a sanya hoton shagonsa, hotonsa da kuma taqaitaccen tarihinsa, kuma wannan duk a kuxi kaxan. Maza ku kasance cikin kashi na farko na masu cin moriyar wannan shiri. Ina ’yan Canji, dillalan yaduka, masu kayan masarufi, mayan da qananan ’yan tireda, dillalan magunguna, masu kamfoni da masana’antu, dillalan hatsi, dillalan mota, masu sayar finafinai da dai sauran masu sana’o’i, ga dama ta samu. A tuntuvemu a lambarmu ta 08148507210, 07036666850, 08039216372, 07037934034, 08032875238 da 08038011382: email leadershipayau@gmail.com. Ko kuma a tuntuvi wakilanmu na jihohi don qarin bayani.


A Yau Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku

Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku

Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.

Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com

TALLA 7


8 TALLA

A Yau

Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Domin Qarin Bayani A Tuntuvi: • Mubarak Umar – 0703 6905 380 •Sulaiman Bala Idris –0703 6666 850


A Yau Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

TALLA 9

Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”

Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.


10 LABARAI

A Yau

Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

• Shugaban Qasa Muhammadu Buhari tare da Firayiministar Birtaniya Theresa May jiya a Birnin Landan

Uwargidan Gwamnan Katsina Ta Hori Qungiyoyi Masu Zaman Kansu Kan Ayyukansu Daga Sagir Abubakar, Katsina

gudanarwa, kamar yadda yace, cibiyar na aiwatar da horas da sana’o’i irin su xinki da kuma haxa guiwa da ofishin hana sha

Uwar gidan gwamnan Jihar Katsina Hajiya Binta Aminu Bello Masari, ta hori qungiyoyi masu zaman kansu da gidauniyoyi, da su qara faxaxa ayyukansu don qara samar da tarbiyya a tsakanin al’umma. Hajiya Binta Masari ta yi wannan horon ne a lokacin da ta karvi baquncin jami’an Daga Khalid Idris Doya gidauniyar horas da sana’o’in hannu ta marigayi M.D Yusuf Qungiyar Musulmai ta NASFAT a wata ziyarar ban girma a wato Nasrullahi Fathi ta bayyana Katsina. Uwargidan gwamnan cewa za ta samar da zauren ta ce, baya ga horas da sana’o’in tattauna matsalolin da suka hannu a cikin al’umma don addabi mata da kuma karantar su zamo masu dogaro da da su yadda za su yi maganin kai, gidauniyar na da rawa waxannan matsalolin. Sakataren qungiyar mai kula muhimmiya wajen ingangta da harqoqin Mata ta qasa Alhaja tarbiyyar matasa. (Hajiya) Samiat Mumuni ce ta Hajiya Binta Masari, ta ce bayyana haka a zantawarta da tavarvarewar tarbiyya a qasar ‘yan Jarida a Kaduna a makon da nan, da ya haxa da she-shayen ta gabata. miyagun qwayoyi, da sauran Hajiya Mumuni ta ci gaba da ayyuka n assha a tsakanin matasa, ya zamo wani abin dubawa da idon basira. Ta kuma gargaxi iyaye da su riqa kula da xaukar nauyin Daga Sagir Abubakar, Katsina ‘ya’yansu, da zai hana su yawon barace-barace akan Sakataren Gwamnatin jihar tituna. Hajiya Binta Masari, Katsina Alhaji Mustapha gta sha alwashin haxa kai Muhammad Inuwa yayi kira da gidauniyar MD Yusuf ga iyayen qasa da masu faxa don cigaba da kyautata wa aji a cikin al’umma a qaramar al’umma, har ma ta qara da hukumar Xanmusa da su cewa, a kodayaushe qofarta a wayarwa da jama’a kai domin buxe take wajen taimakawa karvar katin jefa quri’a. cibiyoyin horas da sana’o’i. Haka kuma, sakataren Ta yi kira ga gidauniyar, da ta gwamnatin yayi kira ga yi iya yinta don ganin ta xora al’ummomin yankin da su bada al’umma a hanya mai vulewa. tasu gudummuwa wajen samar Tun farko, jami’in dake kula da da zaman lafiya a yankin ta cibiyar Mal. Danjuma Muh’d hanyar fallasa miyagun mutane yace sunkai ziyarar ne don da ayyukan su. shidawa uwargidan gwamna Alhaji Mustapha Inuwa yayi irin ayyukan da cibiyar ke

da fataucin miyagun qwayoyi wajen kai rahoton masu aikata laifuka. Sai ya roqi taimakon

uwargidan gwamnan na su haxa hanu da cibiyar don tallafawa masu qaramin qarfi. Jami’in da ke kula da gidauniyar ya kuma

yaba wa gwamnatin Aminu Bello Masari, da take vullo da tsare-tsaren horas da mata da matasa sana’o’i.

bayyana cewa; suna tsammanin halartar mata sama da dubu guda, 1,000 daga sassa dabandaban na qasar nan da sauran qasashen duniya a taron da za su shirya akan haka karo na 6 a jihar Kaduna. Ta bayyana cewa; taron za su shirya shi ne domin mata don samun tattauna matsalolin da suka shafe su da hanyoyin magance su. Ta ce; “sashen mata na qungiyar NASFAT tana gudanar da tarurruka daban-daban waxanda za su kawo sauyi a rayuwar mata.”

Sannan ta tabbatar da cewa daga cikin ayyukansu suna gudanar da ayyukan da suka shafi lafiya wanda ya haxa da duba lafiyar ido da kuma koyawa mata ayyukan da za su dogara da kansu, sannan suna qoqarin taimakawa zaurawa, marayu da kuma naqasassu masu buqatar taimako. Da take magana dangane da maqasudi da kuma taken taron na su, ta jaddada cewa taken taron na su shi ne; ‘Farkar da Musulmai qalubalen da suke fuskanta a wannan zamanin.’

Hajiya Sami’at ta ce; idan aka yi la’akari da abubuwan da Musulmai ke fuskanta a wannan lokacin, lallai taken taron ya dace a halin da ake ciki. Sannan ta tabbatar da cewa; matsalolin da al’umma suke fuskanta a halin yanzu wanda ya haxa da talauci, garkuwa da mutane, musgunawa, zalunci da danniya, matsalolin zamantakewar aure, duk za su bi su tattauna a lokacin taron nan domin samar da mafita.

Qungiyar Musulmai Ta NASFAT Za Ta Gudanar da Taro Kan Matsalolin Da Mata Ke Fuskanta

Haqqi Ne Na Iyayen Qasa Da Su Wayar Da Kan Al’umma –Dakta Mustapha Inuwa kiran ne a lokacin da ya karvi tawaga daga qaramar hukumar Xanmusa sabon magajin Malam na 3 Alhaji Darda’u Mu’azu Xanmusa ya jagoranta suka kai ziyarar godiya ga sakataren gwamnatin. Sakataren gwamnatin da ya nuna damuwa akan ta’ammuli da miyagun qwayoyi, yayi kira ga shugabannin addinai da iyayen qasa da iyayen yara da su qara matsa qaimi wajen yaqi da shan miyagun qwayoyi. Ya baiwa hakimin tabbacin cikakken haxin kansa da goyon bayan gwamnati domin nasara. Alhaji Mustapha umuri

ya bayyana sabon hakimin a matsayin wanda jama’a ke so kana yayi kira ga sabon hakimin da ya riqe gaskantawar da jama’a suka yi masa. A tsokacin sa, sabon magajin Malam hakimin Xanmusa Alhaji Darda’u Mu’azu Xanmusa ya godewa maimartaba sarkin Katsina da sakataren gwamnatin kan qauna da soyayya da suka nuna mashi. Alhaji Darda’u Mu’azu ya bayyana tsohuwar dangantaka dake tsakanin sa da sakataren wadda ya ce bata siyasa ba ce. Tun farko wakilin mai martaba sarkin Katsina da ya riqe kujerar hakimin Xanmusa kafin ayi

naxin sabon hakimin, Hasken Fadar Katsina Alhaji Shehu Sule Dankina ya godewa al’ummar gundumar Xanmusa akan yadda suka bashi haxin kai a zaman da yayi na wakilcin mai martaba sarkin Katsina. Tawagar tun farko ta kai ziyara a fadar maimartaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman akan naxa magajin Malam da al’ummar gundumar Xanmusa ke so da qauna. Daga cikin tawagar akwai magaddai, masu unguwanni, yansiyasa, limamai, yankasuwa da sauran al’ummomi daga qaramar hukumar Xanmusa.


LABARAI 11

A Yau Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Gwamnati Na Asarar Naira Biliyan 300 Kan Cutar Maleriya Daga Khalid Idris Doya, Abuja

Hukumar da ke kula da fafutukar ganin an kawar da cutar Maleriya a Nijeriya, ta bayyana cewa; gwamnatin Nijeriya tana asarar Naira Biliyan 300 a duk shekara wajen yaqi da cutar haxe da yin aiki tukuru kan cutar ta maleriya. Shugaban wannan hukumar na qasa, Audu

Muhammad ne ya bayyana haka a wurin wani taron ‘yan Jarida na farko da aka shirya akan yadda za a yi amfani da sabbin dabaru wajen kawar da cutar ta Maleriya. A lokacin da yake bayani akan rashin alfanun amfani da sinadarin Monethary wajen kawar da cutar ta Maleriya, Audu Muhammad ya bayyana cewa; Hukumar lafiya ta duniya (WHO)

ta shawarci a riqa amfani da haxakar sinadaran Artemisinin. Ya qara da cewa cutar Maleriya cuta ce wacce ake maganinta kuma za a iya kawo qarshen illar da take haifarwa. amma duk da haka cutar nan ita ce babbar matsalar mutanen Afrika da Nijeriya baki xaya kamar yadda yake bayyanawa. Ya qara da cewa irin waxannan

Yunwa Ta Hallaka Yara 150 Cikin Shekara Xaya A Gombe Daga Khalid Idris Doya

Rashin samun isasshen abinci ya kashe Yara aqalla 150 a Jihar Gombe a cikin shekarar da ta gabata wato 2017. Wannan al’amari ya faru ne a ya yin da ake aikin kula da lafiyar Yaran a cibiyar kula da masu cutar yunwa dake qananan hukumomi huxu na jihar. Wani babban Jami’i mai kula da wannan sashen na Jihar ne mai suna Suleiman Mamman ya bayyanawa majiyarmu hakan a makon jiya. Mamman ya bayyana cewa a cikin shekarar 2017, Yara dubu sha huxu da xari da arba’in da uku (14,143) ne suke fama da wannan cuta a cikin Jihar a tsakanin cibiyoyin kula da masu cutar yunwa a qananan hukumomin Gombe da Nafaxa da Dukku da kuma Kaltungo. Ya ce cikin wannan adadin, Yara 13, 069 ne an ci nasarar kula da lafiyarsu inda a qarshe aka sallame su. Sai dai ya ce; Yara 710 kuwa ba a iya cimma nasarar kula da su ba sakamakon daina zuwa da su da iyayensu suka yi wanda su

kaxai suka san dalilin haka. Ya ce; Yara 150 kuwa, ajalinsu ya cika ne a ya yin da ake nema musu lafiya. Sannan Yara 214 ba a iya cimma nasarar kula da lafiyarsu ba sakamakon wasu dalilai masu qarfi da suka sha qarfinsu. Ya ci gaba da cewa; Yaran da ba su warke ba, an ba su kulawa ta aqalla wata takwas amma duk da haka babu wata ci gaba da aka samu. Masanin ya xaura da cewamafi yawansu suna da cutar qanjamau, a wannan dalili ya sa an tura su wasu asibitocin daban-daban a cikin jihar domin kula da su. Hakazalika, Kwamishinan lafiya na Jihar Gomben, Kennedy Ishaya ya bayyana cewa; “jihar Gombe tana xaya daga cikin jihohi takwas a qasar nan da aka ba su bashi a Bankin duniya domin su kawo qarshen matsalar cutar yunwa.” Ya qara da cewa; “gwamnatin jiha ta kammala dukkan shirye-shirye domin ganin mun sabunta dukkanin cibiyoyi da asibitocin da suke kula da wannan al’amarin a jihar, inda muka fara da

asibitin jiha na musamman wanda yake buqatar xa ga darajarsa.” Kwamishinan ya bayyana cewa; sakamakon yadda ake qara samun hauhawar masu wannan cutar a qasarnan musamman ganin yadda ake samun tashe-tashen hankula a arewa maso gabas da arewa ta tsakiya, wannan ya nuna cewa akwai haxarin gaske wajen samun qarancin abinci a shekara mai zuwa in dai ba a gabatar da wannan matsalar ba domin ganin an kawo qarshenta. A zancensa ya ce; tuni aka samar da wani Ofishi wanda za a samar masa da mai gudanar da shi wanda ba da jimawa za a bayyana ayyana shi. Ishaya ya ce; qalubalen a Nijeriya ba wai saboda rashin abinci bane, illa rashin sanin me ya kamata a riqa samarwa na abinci a qasar. Ya tabbatar da cewa; hukumarsa zata duba wannan lamarin domin ganin sun haxa hannu da qarfe da wasu hukumomi da qungiyoyi domin ganin sun kawo qarshen yunwa a Jihar.

matsalolin babbar barazana ne ga zamantakewa da kuma ci gaban tattalin arziqi, inda kuma yake haifar da mutuwa da kashi 11, sannan ya ce kashi 30 na mutuwar Yara yana haifarwa. Sannan ya jaddada muhimmancin kawo qarshen wannan cuta ta Maleriya. hanyar da za a bi wajen cimma wannan manufar shi ne a haxa hannu domin fuskantar matsalar tare kuma da samun kyakkyawan alaqa na zamantakewa a tsakanin domin cimma gaci. Audu ya xaura da cewa, kashi 60 na masu zuwa asibiti zaka same su suna da cutar Maleriya. Ya ce; cutar tana

haifar da rashin zuwan Yara makaranta saboda rashin wadataccen magunguna saboda kashi 13 zuwa 15 ne kawai ake iya magancewa. Ya tabbatar da cewa; hukumarsa a shekarar 2017, ta raba ragar maganin cizon sauro guda miliyan 24 da dubu 519 da ]ari 371. Ya ce yadda ake asarar kuxi saboda cutar Maleriya, ya doshi Naira Biliyan 300 duk sheraka domin ganin an magance wannan cutar. Ya ce kusan maganin wanann cutar Maleriya mai suna ACT Miliyan 130 aka raba a shekarar 2016, a inda a Oktoban shekarar 2017 aka raba guda Miliyan 25.4.

•Ministan Lafiya, Farfesa Isaac

Gwamnatin Buhari Ta Ciri Tuta, Inji Gwamna Masari Daga Sagir Abubakar, Katsina

Gwamna Aminu Bello Masari ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta ciri tuta wajen qirqiro da abunda yan qasar nan ke buqata musamman ma shire-shire masu tasiri kai tsaye ga rayuwar al’ummar Najeriya. Daya juya ga waxanda aka naxa a muqamin qungiyar ya buqace su susa batun katin zave daga cikin shireshirensu na faxakarwa. Ya ce aikin nasu zai qara zama mai muhimmanci da qalubale saboda shugaban qasa daga nan jahar Katsina yake. Tunda farko uban qungiyar na jahar Katsina Sanata Abba Ali ya bayyana fatan cewar yayan qungiyar zasu yi amfani da qwarewarsu a siyasance wajen tabbatar da nasarar gwamnatin APC. Shi ma a nasa jawabin shugaban kwamitin amintattu na qungiyar

Yahaya Maricus Gundir ya ce qugiyar zata taka rawa wajen cimma nasarar gwamnatin Buhari. A yayin da yake buqatar yan Najeriya suci gaba da goyon bayan shugaba Buhari da gwamnatin APC Yahaya Gundir ya ce shekaru uku basu isa a kwatanta da shekaru 16 na gwamnatin PDP ba. A lokacin an bawa gwamna Amkinu Bello Masari shawarar zama babban uban qungiya a yayin da kuma Sanata Abba Ali ya zama uban qungiyar na din din din. Sauran waxanda suka samu nasu takardun muqaman a cikin qungiyar harda mataimakin gwamna Mannir Yakubu, shugaban majalissar dokoki ALh. Abubakar Yahaya Kusada, sakataren gwamnatin jiha Alh. Mustapha Muhammad Inuwa, Kanal Abdul’aziz Musa Yar’adua da Minista Hadi Sirika da sauransu.


12 LABARAI

A Yau

Talata 17 Ga Afrilu, 2017 (30 Ga Rajab, 1439)

Vangarorin PDP A Yobe Sun Yi Baran-Baran Da Juna Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Wata sabuwar taqaddama ta varke a tsakanin qusoshin jam’iyyar PDP a jihar Yobe, yanayin da yaya jawo yiwa juna kallon hadarin kaji, inda kowanne vangare ya shan alwashin raba gari da juna. Dakta Yerima Lawan Ngama (Matawallen Bade), kuma tsohon qaramin ministan kuxi kana kuma jigo a jam’iyyar a jihar Yobe ya bayyana wa manema labaraibayan kammala wani taron qusoshin ta, a Damaturu kan cewa PDP ta na ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida. Lawan Ngama ya ce “wannan jam’iyya ta PDP ta daxe a cikin rikici wanda ya fara tun bayan Kafuwar ta a shekarar 1998 da karvuwar ta a jihar Yobe, duk da nasarar da ta samu a zaven 1998sa’ilin da jam’iyyar PDP ta lashe qananan hukumomi 10 daga cikin 17 da ake dasu a jihar Yobe. “ “Sai dai a cikin rashin sa’a, tun daga wancan lokacin jam’iyyar ta faxa gararari da takon-saqa tare da rikici a tsakanin jiga-jigan ta, har zuwa yau. Rikicin da yake gudana ta dalilin bin son zuciyar wasu tsirarun shugabanin ta a matakin jiha da tarayya.” “A tarihin wannan rikici, wanda ya haifar da yiwa jam’iyyar zagon qasa tare da faxuwa qasa warwas, kuma wannan sananne abu ne ga kowa. Bugu da qari kuma, idan ka bi tarihin wannan savatta-juyen, zaka samu cewa matsalar ta tattaru ne vangare guda, waxanda kowanne lokaci sai dai abi abinda suke so, kuma ba zasu tava yarda wani ya shiga gaba su bi ba, sai dai a bi su, to wannan shi ne rikicin, har yau.” Ya ce, a lokacin yake jan ragamar jam’iyyar, yayi

iya qoqarin sa wajen xinke barakar da ya tarar- wadda ta qunshi vangaren tsohon ministan hukumar yansanda, Adamu Waziri da vangaren marigayi Sanata Usman Albaishir haxi da yanbaruwan mu. “Wanda muka yi qoqari wajen gudanar da zaven sabbin shugabanin jam’iyyar waxanda suka kasance karvavvu ga kowanne vangare, a 2012. Baya ga wannan, kan ka ce me, sai uwar jam’iyya ta qasa a qarqashin Adamu Mu’azu ta tsunduma cikin rikicin shugabanci. Sannan da hargitsa tamu PDP a jihar, wanda ta rusa zavavvun shugabanin- haka kawai ba tare da wani dalili ba, wanda daga bisani kuma ta naxa wani kwamitin riqon qwarya na jeka-na-yika, lamarin da ya jwo muka faxi zave”. “Tun bayan wannan ne, jam’iyyar PDP ta faxa cikin rikita-rikita wanda daga bisani Sanata Ali Modu Sherrif ya kawo wa PDP xauki tare da maido ta cikin hayyacin ta. Wanda a zamanin Modu Sherrif ne zangon shugabanin jam’iyyar ya qare tare da sake zaven wasu sabbi a cikin nasara, ciki kuwa har da a nan jihar Yobe; inda kusan kammala zaven ne wasu suka janye saboda yadda sakamakon bai zo musu yadda suke so ba”. Inji shi. “Saboda haka, tun daga wannan lokacin kawunan yan jam’iyyar ya rarrabu. Wanda shima bayan zuwan Sanata Ahmed Makarfi ya qara iza wutar rarraba kawunan yan PDP waxanda kaso 90 cikin 100 a jihar Yobe suna tare da Sanata Ali Modu Sherrif.” “Wannan ya zo ne saboda yadda a wasu jihohin an rusa shugabanin tare da basu umurnin sake zavar sabbi, amma mu da yake yayan bora ne, bamu samu wannan tagomashin ba. Wanda

•Dakta Yerima

hakan ya sahale wa Adamu Waziri hanyar xora sabbin shugabanin qashin kan sa”. Yerima Ngama ya ce, a yekuwar da suka yi- mai suna ‘Karasuwa Declaration’ ya ce a ciki sun bibiyi komai filla-filla dangane da jam’iyyar, kama daga 2011 zuwa yau, wanda kuma a ciki suka cimma matsayar cewar, wanda shi ne hanya xaya tallin-tal da PDP zata bi wajen samun karvuwa ga jama’ar Yobe tare da qwace mulki daga hannun jam’iyyar APC mai jan ragamar jihar Yobe.

“Hukuncin da kotu ta aiwatar shi ne kan cewa, zavavvun shugabanin jam’iyyar a qarqashin Lawan Gana Karasuwa an yi shi bisa tsari kuma akan dokoki, an rantsar dasu tare da damqa musu takardar shaidar zaven. Duk da wannan kuma, sai kwamitin NEC na qasa a qarqashin Makarfi suka yi amfani da qarfin ikon su wajen sake gudanar da wani zave ba tare da sun rusa shugabanin da aka zava a baya ba”. Bugu da qari kuma, ya ce taron nasu ya cimma batsayar

raba tafiyar su da vangaren Adamu Maina Waziri a siyasance, “ba mu ba Adamu Waziri a cikin kowanne irin lamari wanda ya shafi jam’iyyar PDP- ba zamu tava haxa tafiya tare da su ba.” Inda a qarshe ya bayyana cewa vangaren su ya ayyana cewa suna sauraron alqiblar da Sanata Ali Modu Shariff zai fuskanta a siyasance, a matsayin inda zasu fuskanta. Wanda yar manuniya ke tabbatar da cewa suna iya ficewa su bar tsohuwar jam’iyyar tasu ta PDP.

Shugaban Qaramar Hukumar Nassarawa Na Bai Wa Harkar Kiwon Lafiya Muhimmanci Daga Hussaini Suleiman

Kamar yadda shugaban qaramar hukumar Nassarawa dake jihar Kano, Hon. Lamin Sani Kawaji, ke bayar da muhimmaci wajen gudanar da aikace aikace domin kyautata jin dadin al’ummar yankin da sauransu. Shugaban qarama hukumar har ila yau yana bayar da kulawar da ta dace sosai a kan kula da lafiyar al’ummar yankin qaramar hukumar ta Nassarawa. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin babbar jami’ar kula da lafiya ta

qaramar hukumar Hajiya Saratu Ibrahim, a lokacin da take zantawa da manema labarai a yayin gudanar da alurar rigakafin cutar shan inna watau poliyo da aka kammala kwanakin baya a jihar Kano. Malama Saratu Ibrahim, ta ce, da zaran an shaidawa shugaban qaramar hukumar cewa akwai matsala a kan abin da ya shafi lafiya a yankin Hon. Lamin Sani Kawaji na xaukar mataki a kai. Malama Saratu ta ba da misalin yadda ta shaida mashi rashin biyan alawus na ma’aikatan wucin gadi, inda

nan take ya ba da umurnin a biya su . Ba ya ga wannan yana ba da kulawa sosai ga xaukacin asibitocin yankin wannan na xaya daga cikin abin da ya sa babu mai xauke da cutar Poliyo kwata kwata tun lokacin da gwamnan jihar Kano ya ba da kulawa domin kawar da cutar a qananan hukumomin jihar 44. Daga qarshe ta yi kira ga ma’aikatan qaramar hukumar da su ci gaba da bai wa shugaban qaramar hukumar haxin kai. Shi ma da yake na shi jawabin ga manema labarai

mataimakin shugaban qaramar hukumar Hon Muhammed Shehu, ya ce, haqiqa qaramar hukumar tana da tsare-tsare da kuma manufofi masu kyau domin ci gaban al’ummar qaramar hukuma Nassarawa. Mataimakin shugaban qaramar hukumar ya qara da cewa, kamar yadda Lamin Sani Kawaji yake ba da kayayyakin tallafi ga masu qananan sana’oi ya yi imanin shirin zai ci gaba da yardar Allah, babban abin da suke buqata daga al’ummar qaramar hukumar ita ce addu’a inji Muhammed Shehu.

Ya yi amfani da wannan dama da ya ba wa Gwamnan jihar Kano, game da bijiro da muhimman aikace aikace domin cigaban al’ummar jihar Kano, musamman na baya bayan nan da ya tura wasu malaman jihar kimanin 10 qaro karatu a qasar Cypros, da kuma aikin gadan sama da aka fara aiwatarwa a Dangi dake kan fita zuwa Zariya. Ya yi kira ga xaukacin al’ummar jihar da cewa ranar zabe su tabbatar sun kaxa quri’unsu ga gwamnan jihar Kano a zaben da ake shirin gudanarwa na 2019


LABARAI 13

A Yau Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

An Koya Wa Marayu 50 Gyaran Babur A Zariya Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

A ranar Lahadin da ta gabata, qungiyar ma su gyaran babur na qaramar hukumar Zariya,’’ZAZZAU MOTORCYLE MECHANIC ASSOCIATION’’ wanda ake kira [ZAMMA], ta jagoranci yaye wasu matasa su hamsin da wannan qungiya ta zaqulo su, ta kuma koya ma su sana’ar gyaran babur, domin su sami sana’ar da za su dogara da ita, mai-makon watan-gaririya a tituna. A saqonsa wajen taron, mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, ya nuna matuqar jin daxinsa na yadda shugabannin wannan qungiya suka yi hangen-nesa, inda suka tattara marayu guda hamsin suka koya ma su sana’ar gyaran Babura. Mai martaba Sarkin Zazzau, da Ji-Sambon Zazzau Alhaji Sani Sambo ya wakilta, ya kuma tabbatarwa shugabannin wannan qungiya, zai ci gaba da ba su duk gudunmuwar da suke buqata, domin su sami sauqin aiwatar da ayyukan da suka saw a gaba, na samar da sana’o’in dogaro da kai ga matasa, musamman ma dai marayu da wannan qungiya ta tallafa wa rayuwarsu a wannan rana. Farofesa Muhammad Shafi’u Abdullahi, Wakilin Makarantan Zazzau, wanda kuma ya kasance shugaban wannan taro, ya nanata furucin da mai martaba

sarkin Zazzau ya yi, na yaba wa shugabannin wannan qungiya,na yadda suke bakin qoqarinsu, na ganin sun tallafa wa rayuwar matasa da suke qaramar hukumar Zariya. Da kuma wakilin makarantan Zazzau ya juya ga matasan da aka koyar da su wannan sana’a, sai ya buqace su da su tabbatr sun rungumi wannan sana’a da hannu biyu, domin rayuwarsu ta inganta fiye da yadda ta ke a yau. Shi ko Sarkin Ayyukan Zazzau, Malam Abbas Muhammad Fagaci, bayan shi

ma ya yaba wa shugabannin qungiya na yadda suke tallafa wa rayuwar matasa a qaramar hukumar Zariya, sai Sarkin Ayyukan Zazzau, ya nuna matuqar damuwarsa na yadda xaukacin ‘yan siyasa da suke madafun iko da aka ba su goron gayyar wannan taro, babu wanda ya je wajen wannan taro. Kamar yadda Sarkin Ayyukan Zazzau ya ce, wannan hali da ‘yan siyasa ke yi, babban kuskure ne, musamman in sun tuna, al’ummar da suka yi amfani da lokacinsu ne suka zave

su, suka kai ga biyan buqata, amma sai suka qasa mayar da zanen goyon da aka yi ma su. Kazalika Garkuwan kudun Zazzau, Dokta Muhammad Sani Uwaisu, kira ya yi ga gwamnatin jihar Kaduna da kuma sauran gwamnatoci da su qara tashi tsaye, na ganin sun ruvanya tallafin da suke ba qungiyoyin da al’umma suka kafa domin tallafa wa junansu da kuma matasan da ya kamata a ce gwamnatoci ne aiwatar da tsare-tsare domin inganta rayuwaru a vangaren ilimi da kuma sana’ar dogaro da kai.

Da kuma ya juya ga iyayen yara, sai Garkuwan kudun Zazzau ya nuna matuqar damuwarsa na yadda iyaye maza ba su damu su kai yaransu wuraren koyon sana’o’I ba, sai dai iyayensu mata, ya ce, lokaci ya yi da iyaye maza za su canza daga tunanin sauke nauyin da Allah ya xora ma sun a kula da tarbiyya da kuma ilimin yaransu. Tun farko a jawabinsa, shugaban qungiyar, Alhaji Jibrin Qasim (OZEEZ) wanda mataimakinsa Malam Ibrahim Jibrin ya wakilce shi, y ace sun kafa wannan qungiya a shekara ta 2016, wanda zuwa yanzu, sun koya wa yara fiye da 160 wannan sana’a ta gyaran babur, xaukacin yaran a cewar shugaban, sun fito ne daga sasan qaramar hukumar Zariya. Sauran waxanda suka yi jawabi a wajen taron sun haxa da Garkuwan Ayyukan Zazzau, Injiniya Balarabe Musa da Dokta Muhammad Sani Hassan da dai al’umma da yawan gaske da suka fi mayar da hankalinsu, wajen nuna jin daxinsu na yadda wannan qungiya ta tashi tsaye na ganin sun inganta rayuwar matasa da suke qaramar hukumar Zariya, sai suka yi alqawarin ci gaba dab a wannan qungiya duk goyon bayan da suka kamata, domin su cimma burinsu na tallafa wa matasa da kuma marayu da suke qaramar hukumar Zariya.

Sanata Hunkuyi Ya Kai Tallafin Tiransifoma Qauyen Sabon Birnin Bomo Daga Idris Umar Zariya

A cikin makon daya gabata ne qungiyar ci gaban anguwar Sabon Garin Bomo dake a qaramar hukumar Sabin Garia jihar Kaduna suka samu tallafin Tiransifoma daga Sanata Sulaiman Hunkuyi, sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar datijjai. Alhaji Isa Sa’eed Madaki shi ne shugaban qungiyar ci gaban wannan unguwa ya kuma bayyana wa wakilinmu irin daxin da suka ji har ya qara da cewa, qungiyar tasu ta jima tana neman gudummawa wajan manyan ‘yan siyasan da suke dasu amma basu yi nasara ba amma gashi sun mun shaida da qoqarin Sanata Suleiman Hunkuyi domin shi ya yi mana alkawari kuma gashi ya cika don haka muna fatan Allah yasa sauran ‘yan siyasan zasu yi koyi da halinsa. wajen taimakon jama’ar su , kuma shuganan ya nuna farin cikin sa a madadin sauran

jama’ar unguwar Sabon Garin Bomo ya ce, da fatan za a samu wasu da zasu xauke sauran aikin daya rage daya hada da sayan turakun wutar da fatan Allah ya bashi Sanata sa’an abin daya sanya a gabansa na taimakon mutanen sa. Isma’il A. Bashir shi ne shugaban matasan unguwar na Sabon Garin Bomo a nasa bayanin cewa ya yi wajibin sune su godewa mai girma Sanata Suleiman Hunkuyi don ya cancanci yabo domin ya yi mana Alkawari kuma ya cika don haka suma zasu saka masa da yardan Allah in lokaci ya yi, shugaban matasan ya qara ne da qara kira ga sauran wakilansu da suma suyi musu irin wancan gudummawar da su taimaka masu da sauran kayan da suka rage ba a sayoba kamar turakun da za a xauko wutar zuwa cikin anguwar ya yi godiya ga Sanata tare da fatan Allah ya saka masa da alkairi mai yawa. Malam Yusuf Adam shi

ne mai Anguwar na Sabon Garin Bomo shi ma ya yi godiya ne ga sanata Suleman Hunkuyi da kama qungiyar ci gaban unguwar bisa yadda suka nuna qauna da tsare mutunci da tunanin kawo ci gaban wannanuanguwa ya ce, da ’yan siyasa zasu riqa cika alkawari kamar yadda Sanata Suleiman, ya cika to da an sami canjin rayuwa a aasarmu baki xaya. Shin ko menene ya janyo wannan hangen nesa da Sanata Suleiman ya yi na mika tallafin taransifoma ga wacan anguwar? Tambayar da wakilinmu ya yi wa babban sakataren a ofishin Sanatan dake MTD Zariya wato Malam Suleman inda ya ce “A gaskiya Sanata Suleiman Hunkuyi burinsa shi ne duk inda ya yi alkawari fatansa ya cika kuma in Allah ya so dukk inda suka san Sanata ya yi musu alkawari to suci gaba da addu’a da yardar Allah zai cika shi kuma shi ma Sanata ya nuna

•Suleiman Hunkuyi

godiya bisa godiya da addu’ar da jama’ar shiyya ta daya ke masa a duk rana. Ya zuwa hada wannan labari tuni mazuna wannan unguwa suka shirya walima ta musamman bisa sa rai da

sukayi na sun kusa fita daga wahalar zama a cikin duhu da komowa cikin haske kamar yadda sauran jama’ar wasu unguwanni ke zama a cikin haske da shan ruwan sanyi da nika da surfe cikin sauki.


14 RAHOTO

A Yau

Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

’Yan Sanda Na Ci Gaba Da Fatattakar ‘Yan Sarasuka A Kaduna Daga Bello Hamza

Tashe tashen hankula ya tsananta tsakanin qungiyoyin ‘yan sarasuka daban-daban a cikin garin Kaduna da kewaye a qarshen watan daya gabata zuwa farkon wannan watan. A cikin wata xaya alumma fiye da goma sun fuskanci rikici da hare-haren ‘yan ta’ada, hare haren daya haxa da sare saren mutanen da basu ji ba basu gani ba da sace-sace da qone-qone abin da ya kan kai ga kisa. Wakilinmu ya bada labarin cewa, kwanakin baya wani magidanci a unguwan Kawo ta cikin garin Kaduna ya fito da daddare domin saya wa iyalansa Burodi sai ‘yan Sara suka suka auka masa abin daya kai ga kusan fille masa hannu a qoqarin da ya yi na kare saran da ake kai masa. A unguwan Shehu Idris Crescent, kusa da layin Gwamna, wasu yan sara sunan sun bi wata mata tun daga unguwan Badiko a qoqarin qwace mata waya, hayaniyar da matar ta yi tayi ya yi matuqar tayar wa da mutanen unguwan hankali in da kowa ya yi ta gudu yana shiga gidajensa duk da tana ihun naiman taimako ne. Rikicin daya auku kwanaki tsakanin qungiyoyi yan ta’aadan masu gaba da juna a ungwan Sarki, tayi sanadiyar rasuwar wani bawan Allah dake wuce wa. Unguwannin da suka fi fuskantar wannan bala’i a yan sara sukan sun haxa da Tudun Wada da Rigasa da Nasarawa da Unguwar Mu’azu da Zango, sauran sun haxa da Jos road da unguwan Tudun Nufawa da Sabon Gari da Unguwar Sanusi da Ungwan Sarki da sauransu. Wakilinmu ya gano cewa, qorafe qorafen da jama’ma ke yi ne ya zaburar da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro suka farmaki mavuyar ‘yanta’adan inda suka cafke da yawa daga cikinsu. Alamu sun nuna cewa wannan farmaki da jami’an he kai wa yan ta’aadan ya sanya da yawa daga cikinsu sun gudu domin kaucewa kamu. Wakilinmu ya gano cewa yawancinsu sun gudu daga unguwanin su zuwa wasu jihohi makwabta, hakan kuwa ya yi matuqar

•Wasu daga cikin makaman da rundunar ‘yan sanda ta qwato a Kaduna

rage kaifin ta’addancin da ke faruwa a unguwanni da dama. Wani mazaunin unguwan Badarawa, mai suna Malam Baba Shehu, ya ce, rikicin ta’addancin ya yi sauqi sosai a yan makonnin nan, “Ban samu wani labarin ta’adanci ba fiye da mako da xaya daya wuce, ban san abin daya faru ba amma lallai abin ya yi sauqi sosai “ Inji shi. Wasu nada ra’ayin cewa, an samu sauqin harkokin yan ta’aadan ne saboda kammala zaven fid da gwani na jam’iyyar APC da aka yi kwananan a faxin jihar. Jammiyyun siyasa sun zafafa harkokin siyasa saboda zaven qananan hukumomi dake tafe a watan gobe, saboda haka a ka samu qaruwar harkokin ‘yan sara suka musamman ganin dasu ‘yan siyasa suke amfani wajen harkokin siyasansu domin a xauka kamar suna da magoya baya da yawa. Wani mazaunin unguwan Kawo ya ce, “A lokacin zaven fid da gwani na Jammiyu ne muka fara ganin bakin fuskan da muka daxe bama ganinsu na tsawon lokaci, zaka gansu a cikin mota qarar Golf sun qarar sauti suna yawo a cikin unguwani, amma tun da aka kammala zaven fid da gwani da sai suka shiga kai wa jama’a hari tunda babu wani aiki da zasu ci gaba da yi.’’ Jami’in watsa labaran

rundunar ‘yansanda jihar Kaduna ASP Mukhtar Hussain Aliyu,ya bayyana wa wakilinmu cewar, rundunar ta xauki matakan kakkave yan ta’aadan daga unguwanin Kaduna, ya qara da cewa, a makon daya gabata kwai rudunar ta samu Nasarar cafke yansara-suka 16, kafin nan kuwa an kama yan ta’aadan 23, a halin yanzu a n kama mutum 39 kenan da laifin harka irin na sarasuka. Ya ce wayancin waxanda aka kama matasa ne daga unguwan Shanu da unguwan Sarki za agurfanar dasu gaban kotu da zaran an kammala bincike a kan su. Daga nan ya shawarci iyaye dasu rinqa yi wa yaransu nasiha domin kuwa rundunar ‘yansanda jihar baza ta yarda da rashin bin doka da oda da kuma duk wani harka da zai yi sanadiyar rasa rai da dukiyoyin jama’a. Wakilinmu ya fahimci cewar, rundunar ‘yansanda jihar na shirin gudanar da bincike gida gida domin xaukar bayanan yan ta’aada da ke muahunawa jama’a a faxin jihar. Kwamishinan ‘yansanda jihar, Austin Iwar, ne ya yi wannan bayanin a yayin tattaunawar da ‘yansanda suka yi da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a unguwanni Rigasa da Hayin Malam Bello da Hayin Dan-Mani a qaramar hukumar Igabi, xaya daga cikin matsalolin da masu

ruwa da tsakin suka nuna a matsayin babbar matsalar da ake fuskanta shi ne rashin sanin yan hayar dake shiga da fita a unguwanin. “Ana ba yan ta’aada haya, saboda haka zamu fito da tsarin da zai bamu daman shiga gidaje domin xaukar bayanan mutanen dake zaune a cikin gidajen, wannan bincike zai bamu daman zaqulo mutanen da bamu yadda da halayyarsu ba Domin mu fid dasu daga unguwan mu miqa su ga hukuma domin hukuma wa” Inji shi. Ya kuma qara da cewa, wannan aikin Na buqatar cikakken haxin kai daga dukkan jama’a domin su tabbatar da mutanen dake zaune a gidajensu mutane ne masu halaye na gari. Ya kuma yi alkawarin saiyukansa, ya samar da ofishin yansanda guda 5a unguwannin 3 domin qara samar da kariya. Alhaji Tanimu Aliyu, sakataren hakimin Rigasa ya yaba wa kwamishinan ‘yan sandan a bisa haxin kan daya k enema a wajen jama’a a gudanar da aiyukansa, ya kuma buqaci a qaro jami’ain tsaro a yankin domin maganin ‘yan ta’addan. Sakamakon dawo da doka da oda da aka samu a Kaduna, mutane da yawa na kiraye kirayen cewa, ya kamata ‘yansanda su ci gaba da irin wannna aikin domin tabbatar da ‘yan ta’adda basu dawo da harkokinsu ba.


A Yau

RAHOTO 15

Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

An Fara Yunqurin Dawo Da Martabar Yawon Buxe Ido A jos Daga Abubakar Abba

A makon da ya gabata ne qungiyar masu zagayawa da ‘yan yawon Buxe Ido ta qasa (NATOP) ta gudanar da gudanar da taron ta na shekara haxe da zavar sababbin shuwagabannin a garin Jos dake jihar Filato. An zavi Jos ne don gudanar da taron ganin cewar taron da qungiyar ta gudanar a shekarar da ta gabata an yi shi ne a Jihar Legas kafin wanda za a gudanar Kalaba. Dukkan garurun babu wata tantama sune suke a kan gaba wajen idan ana maganar harkar yawon buxe ido a Nijeriya. A gefe xaya garin Jos, ana iya danganta shi xaya daga cikin garururun da ake girmama yawon buxe ido a qasar nan. A shekarun baya da suka shige, jos tabi sahun gari na xaya a Nijeriya dake da albarkantu na dausayi saboda yanayin ta da kuma ababen ban mamaki kamar yadda duwatsu a garin suke da inda ruwa yake kwararowa daga duwatsuna. Wannan ya kuma qara da gano irin xin alfarma da Allah ya yi wa garin, inda hakan ya sanya tuwan masu mulkin mallaka a shekarar 1960s suma suka zauna a garin har hakan ya sanya baqi daga wasu qasashen duniya da kuma wasu ‘yan Nijeriya suka dinga kwararowa cikin garin. Qabilun ‘yan asalin Jos kamar Berom da Tiv da Jukunawa suna qara samar da armashi wajen kwarara zuwa garin da kuma sauran qabilu ‘yan Nijeriya da suke kwarara zuwa garin na Jos harda waxanda suka fito daga nahiyar turai, inda hakan ya sanya garin ya cika da yarurruka daban-daban sakamakon hakan garin na Jos ya zamo xaya daga cikin garuruwan dake a qasar nan da suka ya yi fice. Sai dai abin takaici, garin a shekarun baya da suka shige, ya koma fagen fama na yin rigingimun qabilanci dana siyasa da kuma na addini. A na yi wa garin da laqabin, “ Garin zaman lafiya da yawon buxe ido”. A hankali a hankaliy garin na Jos wanda a baya yake karvar baquncin ‘yan yawon buxe ido da yawa, amma yanzu garin ya koma mai wahalar shiga duk da cewar zaman lafiya ya dawo a garin. Amma yunqurin da ake yi na canza tunanin akan Jos akwai jan aiki,inda hakan wannan ya zama na xaya daga cikin dalilan da ya sanya gwamnatin

jihar Filato ta yi haxaka da qungiyar(NATOP) don karvar baquncin taron qungiyar na shekara a Jos. Kafin taron qungiyar na shekara, wata tawaga da kwamishiniyar yawon buxe ido da al’adu da nuna kara uwargida Tamwakat Wali, masu zagaya da ‘yan yawon boxe ido sun zagaya da ita tare da ‘yan jaridu zuwa Assop inda ruwa yake kwararowa xaya daga cikin wuraren yawon buxe ido da jihar take alfahari dashi. Mahalarta taron sun ganewa idanun yadda Jos ta zamo mai mahimmaci akan fannin kasuwanci da kuma cibiyar yawon buxe ido. Zagayen da ake yi da tawagar zuwa tsaunukan dake Jos sunga yadda yanayi ke canzawa a cikin ‘yan mintuna sun kuma ga babbar hanyar layin dogo na Nijeriya da dutsen Riyom da kuma yadda Allah ya shinfixa duwatsu da rafuka. Ma’aunin yanayi na Filato ya kai kimanin kafa 4,200 sama da teku, ma’ana anan tekun shi ne yake samar da ruwa ga rafuka da dama har da rafin Nija dana Benue da sauran su haka a yankin Kudanci nan ma akwai duwatsu da yawa da ruwa ke kwararowa daga kansu. Yana yin kuma shi ne ke samar da canjin yanayi a duk wata daga ma’aunin yanayi 21 zuwa 25, wanda yake sauka zuwa ma’aunin yanayi 11 da dare daka tsakiyar watan Nuwamba zuwa watan Janairu. Zaman Lafiya A Wancan Lokacin Da Yawon Buxe Ido: Ganin yadda gwamnatin jihar ta karvi baquncin taron qungiyar hakan ya nuwa cewar

da gaske take wajen mayar da hankali akan yawon buxe ido. Taron qungiyar dashi a otel xin Hilltop haxe da yin bita mai taken, ‘qalubalen rashin tsaro da xaukaka fanin yawon buxe ido a Nijeriya ya kuma tavo yadda za a magance matsalar rashin tsaro da samar da zaman lafiya ga masu yawon bixe ido. A jawabin a wurin taron Gwamnan jihar Simon Bako Lalong ya bayyana cewar, ma’aikatar yawon buxe ido ta jihar da sauran hukumin dake qarqashin ta a cikin shekaru biyu da suka gabata ta yi namijin qoqari don tabbatar da cewar, an qirqiro da ayyuka don sanya jihar a cikin sahun jihohin da ake zuwa yawon buxe ido a qasar nan. Gwamna Simon Bako Lalong wanda mataimakin sa Farfesa Sonni Gwanle Tyoden, ya wakilce shi a wurin taron ya ci gaba da cewa, taron na nuna al’adun gargajiya na jihar da ya haxa da zagaya gari da rayeraye da kuma kaxe-kaxe, ya samu karvuwa a qasar nan, kuma zan iya tabbatar maku da cewar, nan bada jimawa ba taron na nuna al’adun gargajiya zai fi armashi akan wanda abokiyar hamayyar mu garin Kalaba ke gudanar wa. Gwamnan ya qara da cewa, hawan tsauni da sauran wasanni suna qara samun karvuwa saboda zaman lafiya da gwamnatin jihar ta samar da kuma kyakyawan yanayi ga masu yawon buxe ido. Lalong ya yi nuni da cewa, rashin tsaro abune da ya karaxe duniya,inda hakan yake shafar yawon buxe ido da fannin tafiye-tafiye.   Yace, shin baza mu iya magance qalubalen rashin

tsaron da muke fuskanta ba da kuma yin bankwana da masu tasowa akan fannin yawon buxe ido ba. Ya bayyana cewar Filato bata nuna gajiyawa wajen dabbatar da zaman lafiya da samar da tsaro da shuganci na gari. Ya qara da cewa, babu wata gwamnati mai hankali da zata yi sake wajen inganta tattalin arzikin ta da yawon buxe ido harda fannin sufuri wanda waxannan sune abinda gwamnatin mu ta mayar da hankali a kai. Lalong ya qara jadda da mahimmancin da yawon buxe ido yake dashi ga tattalin arzikin da ya shafi duniya,inda ya yi alqwarin baiwa wannan fanonin goyon bayan da ya dace. A cewar sa, “ a cikin watan Nuwambar 2017, na samu damar jagorantar tawaga daga jihar Filato zuwa Kasuwar duniya ta matafiya a da ta gudana a Birtaniya kuma halartar ta bani dama wajen ganin of abinda ake gudanarwa a kasuwar, musamman don sada matafiya qwararru da masu saye da sayarwa”. Ya qara da cewa, “Ina ganin zamu iya gyara namu na gida ta hanyar yin amfani da wannan qungiyar don havaka yawon buxe ido. Ita kuwa a nata jawabin, kwamishiya uwargida Wali ta bayyana cewar, don inganta yawon buxe ido yana xaya daga cikin dalilan da yasa gwamnatin jihar ta bazama wajen giggina hanyoyi ta qara da cewa an kuma samar da kayan aiki don baiwa masana’antu masu zaman kansu dama da kuma yin haxaka dasu akan fannin yawon buxe ido.


16

Siyasa A Yau A Yau

Talata 17.4.2018

Majalisar Tarayya: Al’ummar Kaduna Ta Kudu Ta Nuna Goyon Baya Ga MS Ustaz Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

An bayyana Muhammad Sani Abdulmajid (MS Ustaz), a matsayin wanda ya fi cancanta da kujerar Xan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazavar Kaduna ta kudu, a Majalisar dokoki ta Tarayya. Wannan kira ya fito ne daga bakin Shugaban Qungiyar ci gaban Al’ummar Gundumar yankin Qaramar hukumar kaduna ta kudu, wanda a turance ake kira da concerned citizen of kaduna south local government, Hajiya Hafsat Abdullahi, a yayin da ta jagoranci gangamin taron Matan da Matasan Al’ummar Qaramar hukumar kaduna ta kudu, domin zantawa da manema labarai a kaduna. Hajiya Hafsat Abdullahi, ta qara da bayyana cewa, a bayyane yake cewa kowa yasan Al’ummar Qaramar hukumar kaduna ta kudu, na tare da MS Ustaz Xari bisa Xari, musamman a lokacin da ya fito takarar kujerar Shugabancin Qaramar hukumar kaduna ta kudu, amma daga bisani wasu vatagarin ‘yan siyasa sukayi ma exco qarya da sunan gwamna, suka yaudari exco da sunan wai gwamna yace

ga wanda zasu zaba, alhali su kuma xaukacin exco na goyon bayan MS Ustaz ne. Ta qara da bayyana cewa, sun yi ma exco qaryar cewa wai gwamna ya yi alqawarin cewa duk exco da ya zavi xan takararsu za’a bashi maqudan kuxi da filaye. Wanda kuma ya bijirewa umurnin su, zasu kore shi daga matakin exco. Da wannan qaryar ne da su kayi, ta sanya suka yaudari wasu daga cikin exco domin canja ra’ayinsu daga zaven mutum mai mutunci da sanin darajar jama’a, wato MS Ustaz, domin shi ne zavin Al’umma akan kujerar Shugabancin Qaramar hukumar kaduna ta kudu, amma hakan bai hanasu yin qarya da sunan gwamna ba, wajen qaqaba mana xan takarar da bamaso, wai duk da sunan cewa gwamna ne ya turo shi, kuma mun san cewa qarya akeyi ma gwamna. Hajiya Hafsat Abdullahi, saboda haka muna kira ga Mai Girma Gwamnan Jihar kaduna Malam Nasiru Ahmed El-rufai, da cewa, a yanzu mu Al’ummar kaduna ta kudu, ba mu da wani xan takarar kujerar majalisar wakilai sai Muhammad Sani Abdulmajid, (MS Ustaz). Kuma munyi

•MS Ustaz

alqawarin cewa duk xan takarar da aka ajiye mana ba shi ba, tabbas zamu bijire masa, domin mu cancanta muke nema, ba tinqaho ba. “Sannan muna kira ga kakkausar murya ga Gwamnan mai adalci, akan ya yi gaggawan hukunta duk wani xan siyasa da aka same shi, yana amfani da sunan gwamna domin cinma wani burinsa a siyasa, domin ta

haka ne kawai gwamnan zai dawo da martabar jam’iyyar APC a Jihar kaduna.” Shugabar qungiyar ci gaban Al’ummar Qaramar hukumar kaduna ta kudu, ta qara da bayyana cewa, “Ni a matsayina na wacce na fito daga gundumar unguwar sunusi, bai kamata ace kuma za’a qara xaukar kujerar xan majalisar wakilai a kawo mana ba, domin a yanzu

mune ke riqe da kujerar takarar Shugabancin Qaramar hukumar kaduna ta kudu, ya kamata ayi ma Al’ummar Gundumar tudun wada adalci, suma a barsu su fito da xan takaran kujerar xan majalisar wakilai, domin sune su kafi ko wane gunduma yawa, saboda sune ke da kashi 55% na yawan Jami’ar kaduna ta kudu.” Inji Hajiya Hafsat Abdullahi.

Shugaba Buhari Na Da Damar Yin Takara -Barista Yamu Daga Balarabe Abdullahi ,Zariya

Tun daga lokacin da shugaban qasa Muhammadu Buhari ya furta cewar zai sake yin takara a shekara ta 2019, ‘yan siyasa da ma su tsokaci kan al’amurran yau da kullun da kuma masana shari’a sai ci gaba da tsokaci suke yi kan wannan batu da shugaban qasan ya furta. Barista Shu’aibu Aliyu Yamusa, fitaccen lauya ne da ke Zariya kuma xan siyasa mai takarar shgabancin qaramar hukumar Zariya a qarqashin jam’iyyar PRP a zaven qananan hukumomi da zai gudana nan ba da jimawa

ba a jihar Kaduna, ya ce, tsarin mulkin Nijeriya ya ba shugaban qasa Muhammadu Buhari wannan dama da ya yi takarar a jam’iyyar da ya ke, sai dai kuma ya rage ga ‘yan jam’iyyar su tsayar da shi ko kuma a sami akasin hakan. Barista Shu’aibu Aliyu Yamusa ya ci gaba da cewar, babu tantama, in an dubi ci gaban da aka samu a wasu vangarori a qasar nan, ya dace shugaba Muhammadu Buhari ya yi takara karo na biyu, wannan, a cewar Barista S.A Yamusa zai ba shi dammar kammala wasu muhimman abubuwa da ya fara, kamar matsalar tsaro da warware

matsalolin tattalin arzikn qasar nan da dai sauran matsaloli ma su yawan gaske. A game da cewar ko babu xan takara a jam’iyyarsu ta PRP ne ya sa ya ce Shugaban qasa Muhammadu Buhari ya cancanta, sai ya ce, ko da ma shugaban jam’iyyarsu ta qasa Malam Balarabe Musa ya nuna gamsuwarsa da furta sake takarar da Buhari ya furta zai yi, kafin shi ma ya yi tsokaci a kan batun. Sai dai kuma Barista S.A.Yamusa ya ce, saboda matsalolin da suka faru daga zaven shekara ta 2015 zuwa wannan shekara, ya ce, ko da Shugaban qasa Muhammadu

Buhari ya furta cewar ‘yan Nijeriya da suke son sa su yi SAK a zaven shekara ta 2019,al’ummar Nijeriya ko da waxanda suke cikin jam’iyyar da Shugaba Buhari suke ne ba za su bi wannan umurni ba, domin Ungulu da kan zabon day a faru a wancan lokaci. A kuma tsokacin da masanin shar’ar ya yi ga waxanda suka shiga inuwar Shugaba Buhari a zaven shekara ta 2015 kuwa, har suka kai ga shiga majalisun jihohi da kuma na tarayya, Barista S.A.Yamusa ya tabbatar da cewar,a shekara ta 2019, kowa halinsa ne

zai kai shi ga inda ya ke son zuwa, ba batun shiga inuwar Buhari ba, in ji shi. A qarshen ganawarsa da wakilinmu, Barista S.A.Yamusa ya shawarci ‘yan Nijeriya, musamman ‘yan qaramar hukumar Zariya da kuma jihar Kaduna da su cire siyasar kuxi a zukatansu, su sami mutane nagari, da za su fuskanci matsalolin al’umma, ba waxanda za su fuskanci matsalolinsu ba da zarar sun kai ga nasara a zavuvvukan da za a yi a nan gaba, in an yi haka ne kawai, kamar yadda ya ce al’umma za su fita daga uquban rayuwar da suke ciki a yau.


SIYASA 17

A Yau Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

ADP: Mutum 10,000 Suka Canja Sheqa Da Xan Takarar Kujerar Gwamna Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

An bayyana cewar jam’iyyar ADP ba ta bin mutane dan yin takara, tafi mayar da hankali wajen janyo jama’a zuwa jam’iyyar. Shugaban jam’iyyar reshen jihar Neja, Malam Tanimu Sarki Kwamba ne ya bayyana hakan a lokacin da yake karvan baquncin sama da mutane dubu goma da suka shigo jam’iyyar ranar lahadin nan da ta gabata a sakatariyar jam’iyyar da ke minna. Ya ci gaba da cewar ADP jam’iyya ce da ba ta buqatar kamun qafa balle gwaze, illa canacanta da dacewa, a kowani lokaci muna maraba da masu halaye na gari da ke da kyakkyawan niyyar da zai kawo ci gaba a qasa. Kwamba yace jam’iyyarsa a shirya ta ke wajen haxa qarfi da qarfe dan ceto jihar nan daga halin quncin da ta ke ciki. Yace muna buqatar ‘yan takara na gari, domin zare suma a kitse ba abu mai wahala ba, idan ka zama xan jam’iyya na gari jama’a ke da Ikon amince wa da kai dan yin takara. Biyayya ga dokokin jam’iyya, tare da mutunta ‘yan jam’iyya ne hanya mafi sauqi wajen samun tikitin yin takarar siyasa, duk wanda ke cikin wannan tafiyar ya cire tsoro ya tabbatar da gaske yake buqatar canjin

a 2019 in Alla ya kai mu. Da yake bayani ga magoya bayan jam’iyyar da suka karve shi, Barista Bello Bawa Bwari wanda ya bayyana cewar yazo da mutane dubu bakwai magoya bayansa da kuma wasu qarin dubu uku waxanda suka qunshi abokansa da abokan karatunsa sun quduri zuwa ADP ne saboda nagartattun tsare tsarenta na farfaxo da tattalin arzikin qasar nan da mutunta al’umma. Barista Bwari yace ba zai sake tallata kowani xan takara ba, kowa ta shi ta fishshe shi. Yace a baya kafin haxewar APC mai mulki mun taka rawar gani a ACN kuma ina daga cikin ‘yan sahun gaba na tallata Janar Muhammadu Buhari a 2015 da ya gabata, duba da kasa cika alqawurran da aka yiwa jama’a yasa na yi tunanin neman jam’iyyar da ke da talaka a zuciyarta. Ban taho ADP dan yi takara da qarfi ba, na daxe ina gwagwarmayar siyasa, ina daga cikin ginshiqan da suka tallata Janar Muhammadu Buhari, saboda yadda muka ga abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata kuma muna da burin kawo ci gaba a jihar nan sannan manufofin jam’iyyar nan ya da ce da manufofin mu yasa muka kwaso yanamu yanamu zuwa ADP wanda

•Tanimu Sarki Kwamba, Shugaban ADP a Neja.

in jama’ar da ke jam’iyyar sun amince sun ba mu dama lallai za mu kawo canji mai ma’ana a jihar nan. Kusan yau shekaru ashirin da xaya ke nan muna nazarin yadda jihar ta ke sai muka fahimci ba wani sauyi kusan kullun ana nan waje xaya, abin kunya ne idan kana wajen jihar ka ji yadda ake kiran sunanta kuma ka zo ka iske ta a irin wannan yanayin, duk abinda muke nema na tattalin arziki akwai shi a jihar nan amma rashin jagoranci mai ma’ana yasa muka kasa wuce inda

muke a yau. Ba zan sake tallata kowa ba, kuma ba zan xauki nauyin takarar kowa ba, cancantar ka ta baiwa jama’a damar amincewa da kai sai mu yi aiki tare. Jam’iyyu uku suka nemi mu, akwai jam’iyyar da ta biyo dan mu yi mata takarar gwamna, sannan akwai wadda ta kira mu dan yin takarar sanata, sannan wannan jam’iyyar ba tai mana daxin baki ba amma dai ta nemi mu shigo dan zama ‘yayanta kan haka muka da cewar mu shigo nan ga dukkan Salamu ADP ce za ta

sharewa jama’ar jihar nan hawanta. Taron dai ya samu halartar manyan ‘yan siyasa da suka qunshi, Hon. James Baitachi tsohon Wakili a majalisar wakilai ta qasa. Da tsohon kansila kuma tsohon shugaban qaramar hukumar Bosso, Hon. Yakubu Jukuci, sai tsohon xan majalisar dokokin, Hon Yusuf Kure Paiko tare da wasu jiha jigan jam’iyyun siyasa da suka canja sheqa zuwa yanzu dai ADP na da ‘yan takarar gwamna gida uku a kakar 2019 mai zuwa.

Matsalolin Nijeriya Sun Samu Asali Ne Daga Gurvacewar Tsarin Mulkin Nijeriya -Shugaban Jam’iyyar NPM Daga Khalid Idris Doya

Shugaban Jam’iyyar NPM wato Mustapha Bala Getso ya bayyana cewa; matsalolin Nijeriya ya samo asali ne tun daga rashin kan gadon tsarin mulkin da Nijeriya take gudanarwa gami da tafiya a kai. Mustapha Getso ya bayyana hakan ne a

hirarsa da manema labaru a jihar Kaduna. Ya ce; ko maganar cin hanci da rashawa da ake yi, da take dokoki, to tsarin mulkin Nijeriya ne ya ba da wannan damar. Ya kuma qara da cewa, idan har ana so a samu sauyi a wannan qasar ta fuskancin tattalin arziki da zamantakewa da

kuma ci gaban siyasa, to fa sai an sauya ko yiwa tsarin mulkin Nijeriya garambawul. Ya tabbatar da cewa; “shin ka san inda matsalolin ya fara? To tsarin dokokin mulkin qasarmu ne. Gurvataccen tsarin mulkin da muke gudanarwa ne ya ba da damar dukkannin

waxannan xabi’un.” In ji shi. Ya qara da cewa ta kaima yanzu kotuna ba su iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata balle har su yanke hukunci akan qararraki kan cin hanci da rashawa. Sannan ya ci gaba da cewa; hatta shari’o’in da suka shafi almundana

da kuxi da arzikin qasa da kuma hukunta masu ci da addini, kotuna ba su iya yanke hukunci a kai. Tsarin mulkin ne ya baiwa waxanda ake ganin sun lalata qasa dama su kare kansu. Ya ce abin farko da ake buqatar yi masa kwaskwarima shi ne tsarin mulkin qasar.


18

Muryar Talaka... Tare da Bishir Dauda 08165270879

Makon da ya wuce, shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya fadi abin da nai tsammanin zai fadi. Wato na sake tsayawa takara. Manta da maganar da gwamnan Kano Ganduje yai na cewa za su kai Buhari kotu idan ya ki neman takara. Wannan Magana ce kawai wadda bata da wani hurumi a kundin tsarin mulki ko a Dimokaradiyya. Wandanda suka san mulki, suka san dadinsa, idan har sukai shakku game da ko shugaba Buhari zai sake tsayawa takara, to lalle kila a yanzu basu bisa mulkin. Amma giyar mulki kamar yadda masana ke fadi dadi gare ta. Ba kowane mutum zai dandanata sau daya ba, ya tsaya, kamar yadda tsohon juyin juya halin kasar Burkina-Faso, Thomas Sankara ya fada cewa, giyar mulki tamkar wiski ce, daka lasa sau daya, to za ka ra, lasa, ka kara lasa, ka kara lasa har sai ta bugar da kai, baka sani ba. Wannan maganar fa, ta fito daga bakin daya daga cikin fitattun gwarzayen shugabannin Afirika wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin ‘yanto kasarsu. Tarihi ya nuna ba kowane game-garin mutum bane zai iya sadaukarwar da tsohon gwarzon yaki da wariyar mulkin launin fata na kasar Afirika Ta kudu wato marigayi Nelson Mandela yai ba. Shi ne, yai wa’adi daya ya hakura. Idan ka cire Nelson Mandela, mafi yawancin shugabannin Afirika sai dai ko su mace bisa karagar mulki, ko kuma mutanensu su kore su da karfin tsiya. Kadan daga cikin misalai sune Muhammadu Tanja na Nijar, ya yi shekara goma cif ana ta yabonsa, amma ya biye ma giyar mulki na neman tazarce daga karshe sojoji ne suka cire shi da karfin tsiya. Lokacin da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fara wa’adinshi na biyu, ya yi yunkurin ya canza kundin tsarin mulki domin yai tazarce amma bai samu nasara ba. Abin da nike so in nuna nan yin wa’adi na daya a hakura bai cika samuwa a kasashenmu na Afirika ba.Bayan na biyun ma, wasu kokari suke su kara! Baya ga cewa kundin tsarin Mulkin Nijeriya ya ba Buhari damar neman wa’adi na 2

A Yau

Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Takarar Buhari

kamar yadda tun lokaci da ya bayyana kowa ke jaddadawa, akwai wasu dalilai da zai iya fakewa dasu don sake neman wani wa’adin. Ga batun kamala wasu aikaceaikace da gwamnatinsa ta fara. Wannan dabi’a ce ta kowane shugaban kasar Afirika shi ne a ba shi Karin lokaci ya ida ayyukan da ya fara. Haka Obasanjo ya gaya mamu amma har ya gama, wutar lantarkin bata samu ba, balantana wani abu daban. Shima Jonathan da ya dandana, abin da ‘yanbarandanshi suka gaya ma ‘Yan Nijeriya cewa yai akwai ayyukan da suke so ya kamala. Haka kowane gwamna abin da zai yi kamfen da shi kenan cewa lokaci ya yi kadan a kara mai, domin ya samu ya kamala. Wani abin lura tun lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya fice daga APC, masu hasashen ke ganin Buhari zai yi takara. Hatta wasikun su Obasanjo da Babangida duk suna nuna Buhari zai yi takara. To menene abin hehe yanzu? Saboda haka wadanda shelar Buhari ta zo ma bazata, to suna da saurin mantuwa. Kai ba wai batun Buhari zai sake takara ba, a’a, in zan yi hasashe to Buharin shi ne dai zai lashe zaben fidda gwanin jam’iyyarshi. Haka ake a Dimokaradiyyar Afrika. Yana da wuya ai takarar fidda gwani a kada shugaban kasa mai ci, musamman shugaban kasa kamar Buhari wanda wasu kema kallon ma’asumi. Mai Mala Buni sakataren jam’iyyar APC na kasa, yama fito ya fada ma duniya cewa

shugaban kasa ne keda ikon karbar tayi ko ya ki karba dangane da abin day a shafi takarar jam’iyya. Kuma bugu-da-kari koda an samu wani dan-tabare ya tsaya takara da Buhari, to Buharin zai ci, don haka an san komi. Duk wanda a APC yake son yai asarar kudinsa, wanda yake da wasu kudi amma suna mai kaikai,kuma ya rasa yadda zai yi da su, to ya ja da Buhari takarar fidda gwani a APC. Wallahi in ya sake ma har bashi sai ya ciwo, amma fa Buhari zai tika shi da kasa. Dadina da Dimokaradiyyar Nijeriya saukin hasashe gare ta! ZABEN SHUGABANNIN JAM’IYYAR APC Kwanakin baya shugaba Buhari ya kara ba wasu mamaki, inda lokacin taron jam’iyyarsa ta APC ya ba shugabannin jam’iyar shawara cewa kada sui tazarce, su bi abin da kundin tsarin mulkin jam’iyar ya ce na gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar. Ga dukkan alamu an yi fatali da shawarwarin da Buharin ya ba su . E, za sui zabe amma na jeka-nayi-ka amma, kamar yadda aka ruwaito senata Abu Ibrahim na fadi a wata kafar yada labarai cewa za su hadu ne kawai a amince da shugabanci. Babu zancen a rusa kwamitin zartarwa a sake zabe, su dai wadannan shugabannin da suka kasa hada kan jam’iyyar sune za sui tazarce kuma muna nan da ku za ku gani. Buhari ya ba jam’iyyar kyakkyawar dama na su gyara matsalarsu ta cikin gida amma ga dukkan

alamu za sui asarar wannan damar. Abin da zai faru, shi ne matukar wadannan shugabannin ne za su ci gaba da jagorancin jam’iyyar to yana da matuakar wuya a samu cikakken hadin kan jagoran jam’iyyar na kasa Ahmed Bola Tinubu wanda ko kadan ba su ga maciji da ciyaman din jam’iyyar na kasa.Sannan kusan da wuya a magance sabanin dake tsakanin wasu manyamanyan jam’iyyar kamar irin su tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso, Senata Shehu Sani, gwamnan jihar Bauchi da su Isa Hamma da sauran su. A jiha kamar Katsina akwai ‘yan APC AKIDA, wadanda suke ganin an tura mota da su ta tafi ta bide su da kura, kuma maimakon a zo a zauna da su sai aka koma ana zawarto tsaffin ‘yan PDP wadanda aka ce sune barayi, sun sace kudi dandas ana wanke su ana maido su APC. Ire-iren wadannan mutane da irin su Injiniya Buba Galadima da dimbin ‘yan jam’iyya wadanda aka halatta jininsu a matsayin makiyan jam’iyya sunanan birjik ko’ina lungu da sako a Nijeriya wanda ake ganin da John Oyegun shugaban APC ya ba kwamitin sasanci na Ahmed Bola Tinubu hadin kai maimakon yi masa zagon kasa, to da ko ba a magance matsalar duka ba, to da an rage ta.A haka za a tai 2019 suna yima junansu yankar baya.Shakka babu hakan zai rage karasashin jam’iyyar, kuma zai rage mata armashi a gwagwarmayar neman iko a shekarar 2019 in Allah ya kai mu.


19 RAHOTO

A Yau

Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Sanata Nazif Ya Sama Wa Mutane 250 Aiki Tare Da Duba Lafiyar 6,000 Kyauta -Galadima Itas Daga Muazu Hardawa, Bauchi

A ci gaba da qoqarin sa na ganin ya tallafawa mutanen shiyyar Katagum da ayyukan yi tare da ingantacciyar lafiya, Sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa a majalisar dattijan Nijeriya Injiniya Sulaiman Nazif Gamawa ya samawa mutane 250 ayyukan yi wanda ya shafi shiga ma’aikatun gwamnatin tarayya da kuma shiga shirye shiryen samar da ayyuka na gwamnatin tarayya a qarqashin shirin koyon sana’a. Har way au kuma ya kawo likitoci sun duba lafiyar sama da mutane dubu shida inda aka musu gwadi tare da basu magunguna da aikin fixa kyauta. Alhaji Galadima Abba Itas mai tallafawa Sanata Nazif Gamawa a harkokin siyasa shi ne ya bayyana haka cikin hirar sa da wakilin mu a Bauchi ta wayar tarho. Inda ya bayyana cewa kowane mako Sanatan yana zuwa wasu daga cikin qananan hukumomi bakwai na shiyyar Katagum domin tallafawa jama’a saboda ganin irin mawuyacin halain da mutane suka shiga na rashin ayyukan yi a wannan lokaci, don haka ya ke raba kayan koyon sana’a ga matasa da kuma mata don su samu hanyoyin dogara da kan su. Don haka ya ce a halin yanzu dubban mutane sun amfana da wannan shiri na bayar da jari da kayan koyon sana’a da kuma duba lafiya a qananan hukumomin Katagum da Gamawa da Shira da Giyade da Jama’are da Itas Gadau da Zaki. Galadima Abbba ya qara da cewa amma shirin samar da aiki na gwamnatin tarayya, ya zuwa wannan lokacin Sanata Nazify a samawa sama da mutane 100 aiki a hukumomin gwamnatin tarayya, yayin kuma da ya samawa mutane 150 ayyukan koyon sana’a wanda gwamnatin tarayya ta fito da shi don ganin an tallafawa matasa waxanda

suka yi karatu da wanda ba su yi karatu ba. Don haka a wannan waje ya samawa mutane 150 aiki yadda aka samu jimlar mutane 250 a qarqashin wannan shiri na aikin dindindin da kuma aikin koyon sana’a wanda shima gwamnatin tarayya ta fito da shi kamar aikin gwamnati. Kuma wannan sana’a ta qunshi sarrafa na’ura mai qwaqwalwa da gyara hasken lantarki mai aiki da rana da kuma gyaran rijiyoyin burtsatse da tonon su da sauran ayyukan zamani da ake iya dogara da su a matsayin sana’a mai kawo arziqi da wuri. Bayan haka Sanata Sulaiman nazif ya xauki nauyin xalibai da basu kuxin karatu a makarantu da dama na qasar nan tare kuma da bayar da tallafin karatu wanda ya qunshi xalibai a dukkan gundumomi 116 da ke shiyyar Sanatan Bauchi ta arewa. Yayin da kuma akwai wasu xalibai da ke karatu a qasashen qetare amma suka samu matsalar kuxin tallafi daga hukumomin da ke tallafa musu inda suma ya agaza musu da kuxin fam na ingila da kuma dala don ganin wannan karatu nasu bai lalace ba.

Galadima Abba Itas ya qara da cewa Sanata Sulaiman Nazif a kullum na nuna damuwa game da rashin aiki da matasa ke fama da shi, amma kasancewar mutanen yankin Bauchi ta arewa sun dogara da nomar rani, saboda haka ya sayi injinan bayi don rabawa matasa da suka taimaka wajen shiga harqar aikin gona da kuma waxanda suka tallafawa tafiyar siyasar wannan gwamnati, inda a kowace qaramar hukuma ya bayar da tallafin kuxi wanda ya kama daga milyan biyu zuwa milyan uku don agazawa mutanen da ke cikin wahala ko suke da buqatar tallafi. Saboda haka ya bayyana cewa sun yi haka ne don ganin kowa ya samu abin da zai tallafi kansa a matsayin jarin da zai sa cikin harqar sat a kasuwa saboda mutane su daina xaukar yawon siyasa a matsayin sana’a. Bayan haka kuma sanatan ya bayar da aikin gyaran masallatan da suka lalace da kuma gina wasu sabbi don ganin mutane sun daina sallah a cikin masallatan da suke zubar da ruwa ko basu da gyara musamman ganin yadda ake fiskantar damina a daidai wannan

lokaci. Inda ya qara da cewa bayan wuraren ibada Sanatan ya samar da asibitoci bakwai a kowace qaramar hukuma da ya ke wakilta domin amfanin jama’ar yankin. Bayan haka kuma ya bayar da gina wasu qananan asibitocin sha katafi da gyara asibitocin gwamnati da suka lalace. Game da lafiyar jama’a kuma Sanata Sulaiman Nazif ya samar da likitocin musamman inda suka zo cibiyar kiwon lafiya da ke garin Azare suka duba sama da mutane 6000 aka kuma basu magungunan da suke buqata kyauta yayin da kuma aka yi wa sama da mutane 200 aikin tiyata kyauta don samun lafiya saboda wasu sun jima suna fama da matsalolin cututtuka amma basu da halin a yi musu aiki. Don haka ya kawo likitocin suka duba mutane kyauta kuma suka yi musu dukkan aune aunen da suka dace kyauta. Yayin da a gefe xaya masu fama da larurar ido suma an duba mutane da dama kuma an basu gilasai wasu an basu magani wasu kuma an musu aiki kyauta don su samu gudanar da hidimomin su na rayuwa kamar yadda kowa ke gani.


20

A Yau

CINIKI

Kasuwanci MASANA’ANTU

INSHORA

HANNUN JARI

Talata 3.4.2018

KASUWAR SHINKU

Matakai 10 na Samun Cikakkiyar Nasara A Harkar Kasuwanci Daga Bello Hamza

Samun nasara a harkar kasuwanci na buqatar aiki tuquru da naci saboda babu wani hanya mafi sauqi na samun nasara a harkar kasuwanci ba tare da aiki tuquru ba. Yawancin waxanda suka samu nasara a harkar kasuwanci da suka fuskanta na da labarai iri xaya na hanyar da suka bi har suka kai ga samun nasarar. Da yawa daga cikin litattafan da ake rubuta wa na hanyoyin samun nasara a harkokin kasuwanci zaka samu suna magana a kan mahimman matakai iri xaya ne na hanyar daya kamata mutum ya bi domin samun nasara. Matuqar son harkar kasuwancin da ka ke da dakewa a kan abin da ka ke fuskanta na daga cikin abubuwan da suka banbanta waxanda suka yi fice a harkar sana’a ko kasuwancin da suka fuskanta har suka samu kaiwa ga nasara, samun waxannan matakan na buqatar baiwa na musamman, ga wasu matakan da zai taimaka wajen samun nasarar ga mai buqatar yin fice a harkar kasuwancin daya zava. Son Abin Da Kake Yi. Tsananin buqata da son sana’a ko kasuwancin da kake yi na daga cikin mahimman abin da ke havvaka harkar kasuwancin. Rashin son abin da aka ke yi yana danqwafar da qoqarin da zaka yi wajen samun nasarar a bin da ka ke fuskanta, hakuri da dakewa na xaya daga cikin abubuwan da ke haifar da nasara a kan abin da aka fuskanta, nasara a kan mutum ko aikin ko kuma samun nasara a kan kanfanin gaba xaya. Abraham Lincoln bai yi nasarar a kan abin daya fuskanta ba har sai daga qastshen rayuwarsa amma hakan bai sa ya cire tsammani ba ko ya cire rai ba. Ka da Ka zuba dukka jarin ka lokaci xaya. Zuba jari gaba xaya na da matuqar hatsari kuma ba kasafai a ke samun nasara ba. a kwai labaran waxanda suka zuba dukkan abin da suka mallaka a matsayin jari lokaci xaya kuma suka samu gaggarumin nasara amma ire-irensu basu da yawa, yin taka tsantsan na da mahimmanci musamman ga mai fara harkar kasuwanci, domin zaka iya jure qaramar asara in har ka zuba kuxaxe kaxan, hakan kuma na zama kamar fagen xaukan darasi a kan yadda zaka fuskanci harkar kasuwancin gaba xaya. Xaukan darasi Daga Na Gaba.

Yawanci waxanda suka samu nasara a kasuwanci da suka samu kansu sun tava zama qarqashin wani kafin su soma cin gashin kansu. Zama a qarqashin wani shaharren xan kasuwa na ‘yan shekaru kafin ka fuskanci naka harkar yana da matuqar nahimmanci. Zaka samu yanayin da zaka xauki darasi a kan kurakuran da aka gudanar ka kuma nemo hanyoyin kauce wa irin waxannan kurakuran nan gaba, ka samu wani da zai koya maka yadda zaka gudanar da kasuwancin kafin ka fukanci cin gashi kanka na matuqar mahimmanci. Ka Koyi Yadda zaka gabatar Da kanka. Iya magana da gabatar da nau’in kasuwancin da kake gudanar wa na da matuqar mahimmaci zai kuma xaukaka harkar da kake yi na kasuwanci. Bunqasar kowanne irin kasuwanci ya ta’allaka ne daga wurin wanda ya qirqiro da na’uin kasuwancin. A kwai buqatar ka samu lokacin koyar yadda zaka tallata abin da ka qudirta a ba tare da tsoro ko shakka ba amma ka sani cewa abokin hurxan ka na kasuwanci shin ne ya fi mahimmanci a kowanne lokaci. Gaggauta Xauka Mataki. Qwararrarun ‘yan kasuwa masu kanfanoni na kan ci gaba ne a ko wanne lokaci basu da lokacin vatawa na bin didigin duk abin daya faru domin hakan ba zai kai su ko ina ba, babu lokacin qananan bincike, aiki ne kawai dukkan ranakun mako a cikin awanni 24 na kowanne rana, babu hutu ko hutun rashin lafiya, kawai ka xauki bayanai sama sama na kowanne mataki da ka kai sai ka ci gaba ka kuma yi imani da kanka. Ka Tsara Abin Da ka Ke Son Yi. Ka zama mai karanta labarai da littafan mutane da suka samu nasara a harkokin kasuwanci da suka fuskanta, ka tsotsi ximbin ilimin da suka bayar na hanyoyin

da suka bi har suka samu nasara, irin rubuce rubucen Steve Jobs da na Shark Tank. Tsarin nasara a harkar kasuwanci ba yana nufin sai an rubuta littafi bane, ko da ‘yan shafi kaxan ne matuqar zai qunshij dukan abin da ka ke buqata na matakan samun nasarar ka a harkar kasuwancin. Ka Samar wa Kanka Suna. Kamar yadda wani masani mai suna Brandi Bennett ya yi bayani a shafinsa na intanet HostGator. com ya ce, ya na mahimmanci a samu shafi a kafar intanet domin tallata hajar ka, ko kai da kanka ka rinqa zagaya wa domin tallata abin da ka ke iya yi domin masu buqata a qoqarin wannan zagayen ka yi imani da abin da zaka iya yi tare da yin abin ba tare da wani shakka ba. Ba a Makara Wajen Fara Harkar Kasuwanci. ‘Yan kasuwa da yawa da suka samu gaggarumin nasara sun fara harkar kasuwancin ne daga qarshen rayuwar su kamar irinsu J. K. Rowling (Harry Potter author) da Julia Child (chef) da kuma Sam Walton (Wal-Mart) duk sun fara harkar da suka samu gaggarumin nasarar ne daga can cikin rayuwarsu, rashi farawa da wuri bai hana su samun nasarar ba. Daxewa a rayuwa na iya zama wani sinadarin da zai taimaka wajen samun nasarar da ake buqata. Daxewa a rayuwa na samar da wani hange na musamman da yaro ba zai iya samu ban a hangen nesa da zai taimaka wajen bunqasar harkar kasuwanci. Samar Da Rukunin Abokan Tafiya. A kwai buqatar samar da al’adan mutanen da zasu taimaka maka samun cikakkiyar nasara, abokan tafiyar kuma suna iya kasance wa a kowanne vangaren kasuwancin ka ba wai sai daga cikin vangarenka ba hakan zai taimaka maka buqasa tallan abin da kake fuskanta, samun abokan

hurxa daga kowanne vangaren zai matuqar taimaka maka tallan harkar ka a kusan kyauta tare da tsimin kuxaxen shiga. Ka Kula da Halayar ka. Halin shugaban kanfani ko jagoran kasuwanci na da mahimmanci wajen nasara ko rashin nasarar harkar kasuwancin, lallaci da ragwanci da allubazaranci abubuwa ne da suke saurin cata sunan ka da harkar kasuwancin da kake gudanarwa. Sirrin nasara na tare da yin kurakurai tare da xaukan nauyin kurakuran da aka yi da nufin ci gaba. Yarda da fuskantar qalubale kai tsaye ke mayar da mai harkar kasuwanci ya zama shugaba kai tsaye ba tare da samun cikkakiyar nasara. Fara harkar kasuwanci na da tsananin cin rai saboda haka sai an yi matuqar daurewa. Yayin da dukan waxannan matakan na da mahimmanci wajne samun nasara amma kula da kanka na da matuqar mahimmanci. Motsa jiki da cin abin ci mai kyau tare da samun isasshen barci na da mahimmanci wajen samun nasarar waxannan matakan da muka zayyana. Yawancin shugabannin manyan harkar kasuwanci da suka samu nasarar na da tsarin daya yi kama da juna waxanda suka haxa da tashi daga barci da wuri dad a cin abinci xan kaxan tare da hurxa da abokai da lokuttan nishaxi a kowanne mako.. Za a iya samun tsaiko wajen samun daidaito na waxannan matakan amma idan mutum ya quduri aniyar samun nasara a kana bin daya sa a gaba zai iya samun nasara akan abin daya fuskanta. Girma da irin nasarar da za a iya samu wajen bunqasar kasuwanci ya danganta ne daga irin qoqari zimmar da mutum ya xauka a ciin zuciyarsa, haan ne zai qarfafa da gaggauta samun nasarar da ake buqata.


KASUWANCI 21

A Yau Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Yadda Gidauniyar Aikin Noma Ta Leventis Ta Samar Da Ayyukan Yi Ga Matasa

Daga Abubakar Abba

Gidauniyar kamfanbin Leventis dake Nijeriya yana inganta rayuwar matasa ‘yan Nijeriya ta hanyar basu horo na shekara xaya akan fannin aikin noma kyata a makarantun ta guda shida dake faxin qasar nan. Makarantun shida sune waxanda ke jihohin Kano da Gombe da Kaduna Osun da Ondo da kuma Abuja. Ya zuwa yanzu kimanin matasa ‘yan Nijeriya 25, 000 harda manoma suka amfana da horas war a fannoni da ban-da-ban na a kan harkar noma tun lokacin da aka qirqiro da shirin a 1988. Babban Darakta na gidauniyar Dakta Hope U. Ovie, a hirar ta da jaridar Daily Trust a ranar Lahadin 2017 ya ce, gidauniyar kaxai a makarantar ta horar da aikin noma ta horar da waxanda suka halarci horarwar su tamanin da uku na gajeren zango. Ya ci gaba da cewa, an kuma samu nasarar horar da jimlar matasa su 570 a fannin aikin noma dake xaukacin faxin qasar nan a cikin shekarar data gabata. A cewar sa, “ ako da yaushe ina jin daxi idan naga waxanda aka yaye suna yin magana a bainar jama’a, zasu gaya maka yadda suka zo bada wani abu ba.” Ya yi nuni da cewar, wannan kawai ya nuna yadda ayyukan mu suke da kyau a qasar nan.”

Ya qara da cewa, makarantu na farko suna garin Ilesha ne dake cikin jihar Osun data jihar Ondo da kuma wadda ke a qauyen Dogon-dawa a cikin jihar Kaduna. Ya ce dukkan su an buxe su ne a shekarar 1988 don horar da matasa da manoma akan aikin noma mai xorewa a bisa baya da kashi hamsinhamsin na kuxi tsakanin gwamnatocin jihohi da gidauniyar. Ya qara da cewa, a yanzu suna samar da kuxi don gudanar da aiki a bisa saba’in zuwa talatin, ya qara da cewa, da farko zuba kuxin don yin horarwar gidauniyar ce kawai take samar da kuxin, amma sakamakon samar da sabon tsarin, dukkan jihar da ta yi haxaka da gidauniyar, suna bayar da wani kashi na kuxi na yadda ake zuba kuxi a makarantun. Ya bayyana cewar makarantun horaswar dake jihohin Ondo da Kano da Kaduna, sune sukafi yawan waxanda ake horaswa,inda suke da guda xari da hamsin a duk shekara, amma a yanzu an xauki waxanda za a horas su xari da ashirin a makarantar dake garin Ilesha saboda qarancin bayar da kuxi daga gwamnatin jihar. A alal misali gwamnatin jihar Kano tana son taga makarantar ta xauki waxanda za a horas da yawa ta hanyar shirya manhajar ta yadda za a xauki maza da mata don a horas dasu kuma ana tunanin faxaxa shirin.

Ya ce, a makarantar Dogondawa akwai waxanda ake horaswa su xari zuwa xari da ashirin da kuma mafi qanqanta dake garin Abaji a Abuja dake da waxanda ake horaswa su xari. Akan yadda kamfanin zai fara gudanar da aikin sa a jiha kuwa, ya ce da farko jihar zata fara nuna sha’awar ta sai mu kuma mu tura mata manyan ababen da muke buqata don kafa makarantar a jihar tasu, wanda ya haxa da samar da wuri da zai xauki yawan xalibai da za a horas a qalla waxanda za a horas su kai xari da hamsin da ofishin ma’aikata da gonar da za a horas da xaliban. Ya ce, za kuma a samar kayan more rayuwa kamar ruwan sha da hanya da kayan aikin noma kamar taraktoci da wajen kiwo da noman kifi. Ya yi nuni da cewar, in har aka samar da dukkan waxannan kayan aikin sai muzo a qulla yarjejeniya ta fahimta. Da yake yin qarin bayani, sakataren makarantar horaswar ta Leventis dake Abaji Mista James Owoicho ya ce, manhajar tana qunshe na aiwatar da aiki a zahiri na kashi tamanin bisa xari da kuma kashi ashirin bisa xari. Ya ce, waxanda za a horas xin maza da mata zasu shiga har tsawon shekara xaya kafin a yaye su. Ya ci gaba da cewa, a makarantar za a basu abinci da xakunan da Kaki da kayan aikin noma kyauta har da

kuma basu xan kasafin kuxi 1,000 duk wata wanda daga baya aka qara kuxin zuwa naira 3, 000 a 2017. Owoicho ya sanar da cewar, lokacin da aka buxe makarantar ta fara da xalibai saba’in kuma daga cikn su an yaye talatin zuwa sittin. Ya nuna jin daxin sa akan qaruwar yawan waxanda aka yaye. Shi ma shugaban sashen hatsi da noman gandun daji Mista Bigun Ponman Ishaku,ya tabbatar da cewar sashen yana kadada talatin inda waxanda ake horaswa akan noman Rogo da Kankana da Masara Waken. Ya qara da cewa ana kuma horar dasu akan noman Mangoro da Gwanda an kuma horas dasu a noman zuma. Haka shi ma shugaban sashen kiwon dabbobi Mista Igwemadu Anthony, ya ce ana koyawa waxanda ake horas wa dabaru da ban na noma. Anthony ya qara da cewa, xaliban an horas dasu akan yadda zasu kare amfani noma daga kamuwa da cututtuka. Gidauniyar an kafa ta ne don faxaxa ayyukan ta Nijeriya wadda kuma ta jima tana aiki tun a 1979. Babbar manufar ta shine, mayar da hankali wajen xorewar qoqarin da gwamnatin tarayya ke yi wajen sarrafa abinci da horar da matasa akan dabarun aikin noma don amfanin ‘yan baya.


22

A Yau

Talata 17.4.2018

Kiwon Lafiya Amfanin Qwayoyin Halitta Ga Jikin Xan Adam Daga Idris Aliyu Daudawa

Jikin mutum ya qunshi wasu muhimman abubuwa da ake kira network kowa yasan yadda idan babu network, wadda wata dama ce da mutum ke bi hanya saboda samun biyan buqatar shi , ta yin waya, idan kuma babu shi network xin babu damar sadarwa. Don haka suma network na jikin mutum vessel capillaries wasu sinadarai ne, waxanda suke tuntuvar juna akai akai su da qwaqwalwa don tabbatar da komai na tafiya kamar yadda ya kamata. Manya abubuwa masu taka muhimmiyar rawa sune hormones waxanda ake samar dasu daga glands waxanda zasu samu wurare da dama acikin jikin mutum, suka da waya matuqa ainun ko wanne kuma akwai aikin da yake yi na musamman dangane da ayyukan shi. Hormones su wasu sinadarai ne na musamman, waxanda su kuma masu kai saqone cikin jiki, da ka halicce su a cikin endocrine gladas, su waxannan masinjojin suke yawancin ayyukan jikin mutum, daga masu sauqi kamar wasu abubuwan da jiki yake buqata, kamar su yunwa, sai kuma kamar reproduction, wato yadda ake qaruwa, ko kuma irin yana yi farinciki, ko kuma baqinciki, daga cikin abubuwan da suke yi waxanda suka shafi ayyukansu, suka sa maras lafiya ya lura da lafiyarshi ko kuma kula da ita. Su dai ana masu kallom kamar wasu qananan sinadarai ne masu kai saqo waxanda kuma suke cikin jiki, ba kuma za a iya ganin su da ido ba, amma kuma suna iya shiga ko ina suke so, sun kuma kasance daban daban yadda ayyukansu suka bambanta. Wasu daga cikin waxannan hormones xin, suna yin aikin kamar kitawa da bismillah, su hana yin wani abu, ko kuma su sa ayi wani abu, ko kuma su hana yin wani abu. Waxansu kuma zasu ci gaba da yin wasu ayyuka zuwa wani lokaci mai tsawo domin su yi aikinsu,, wasu daga cikin ayyukan sun haxa da shine yadda jikin mutum yake ci gaba da girma. Daga cikin ayyukan sun haxa da samar shiga wani hali ko yanayin da za a iya yin aiki, ko kuma wajen taimakawa ga saduwa saboda qaruwar

al’umma. Hormones a cikin jikin mutum suna lura ne da yadda yake yin samun ci gaba na girma duk daga haihuwa har ya kai ga kasancewa , nauyin jikin mutum, yadda yanayin zuciyar shi, kodai farinciki, ko kuma baqinciki, halin mutum, al’amarin daya shafi cin abinci da kuma narkewar shi, hali, al’amarin daya shafi qaruwa, gaba xaya lafiyar jiki, sai kuma dukkan al’amura. Su endocrines glands su wasu mashahuran sinadarai waxanda kuma sune suke samar da hormones, su kuma suna ko wanne saqo da lungu na jikin mutum, ko wanne gland yana bada muhimmiyar gudunmawa, ta wajen yin shi hormone, wanda ake buqata domin yin wani aiki, wanda kuma jikii yake buqata a lokacin, wanda kuma taimakawa jiin zai yi , domin ya kasance cikin halin ya kamata ace yana ciki, ko kuma jiki ya kasance cikin halin da ya dace da shi. Jiki dai yana da buqatar ci gaba da kasancewa cikin yanayi mai qyau, saboda yayi aiki kamar yadda ya dace, idan saboda wani dalili jiki ya wani yanayin da bai dace da shi ba, ana iya haxuwa da wata musamman ma idan aqi xaukar

matakan da suka kamata, ba tare da vata lokaci ba. Idan mutum ya shiga wani yanayi mai sanyihar zuwa wani lokaci mai tsawo, yana cikin jijn shi abin zai yi qasa, akwai buqatar yanayin mutum ya kasance zanzan, wato yadda ya kamata ya kasance, saboda ta hakan ne, sauran sassan jikin zai yi aiki kamara yadda ya dace ayi. Domin buqatar jiki ya kasance yadda ya kamata ace yana cikin yanayi, ana aikawa da , wasu sinadaraizuwa wasu wurare, domin bada umarni da za ayi ma wasu qananan sinadarai, kamar su cells da kuma tissues, da su samar da wani yanayi mai kawowa jiki xumi, domi a samu maganin da zai hana yin maqyarqyata da kuma qarar haqoara, saboda nuna yadda jin shi sanyin. Shiga cikin irin wannan yanayin yana nunawa mutum cewar da akwai buqatar a nemi wani abin da zai sa axan ji xumi xumi a jikin shi, saboda hakan zai sa jikin shi, ya koma yadda yake, wannan kuma zai bada dama ga sauran wasu sinadaran jiki, su ci gaba da ayyukansu, kamar yadda aka sansu a da can. Amma kuma idan yana jikin ya qara yin qasa sosai, aka kuma rasa samun yadda za a shiga

shi halin na xumi xumi, domin mayar da yanayin kamar yadda aka san shi a da can, sannu a hankali da akwai al’amuran da zasu riqa xauke wuta su kuma daina aiki. Lokacin da suke halin dda ya dace hormone suna taimakawa jiki domin ya inganta, amma kuma wata qaramar matsala ta hormones, suna iya samar da babbar natsala a rayuwa, wadda zata ita shafar hormone, dom haka idan mnutum yana jin wani abu dangane da hormones xin shi, to sai ya hanzarta, yi wa qwararre akan harkar hormones magana domin a samu shawara. Hormones ana yin su cikin gland ne, wanda shi kuma yana daga cikin endocrine system, su kuma hormoes xin da suke samar da glands sum haxa da : * Hypothalamus shi aikin shi yana kulawa ne da irin yanayi na jikin mutum, akwai kuma jin yunwa, nuna alamar farin ciki, ko kuma baqinciki, sai kuma samar da wasu sinadaran hormones da wasu galands, da su kuma suke kulawa da jin qishirwa, jin barci, da kuma sha’wa da saduwa da nace. • Parathyroid: Wannan yana lura ne da yanayin sinadarin calcium a jikin mutum. • Thymus: Wannan yana taka

Ci gaba a shafi na

23


KIWON LAFIYA 23

A Yau Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Amfanin Qwayoyin Halitta Ga Jikin Xan Adam Ci gaba daga shafi na

22

muhimmiyar rawa ta vangaren aikin na immune system wanda sinadarin da galand ke samar da shi saboda kare jiki, daga kamuwa dawata cuta. Ga kuma maganar yadda ake tarairayar thymus gland, ga kuma samar da qwayoyin halitta. • Pancreas: Shi yana samar da sinadarin insulin, wanda kuma shi ne mai lura da yadda amfanin sikari a jikin mutum yake, bai wuce misali ba. • Thyroid: Yana samar da wani sinadari wanda ke dangantaka da qona calorie, sai kuma yadda zuciya take bugawa.The thyroid produces hormones masu alaqa da qona calorie and heart rate. • Adrenal: Yana samar da sinadarin da yake taka rawa lokacin saduwa tsakanin mace da namiji, da kuma cortisol, sai kuma hormone na shiga wani halin damuwa da zai sa ana sha’awar a samu hutu. • Pituitary: Wannan shi ne tamkar shugaba, saboda yana shugabancin, sauran glands, shi kuma ke samar da hormone mai kawo matsa a girman mutum. • Pineal:Wanda har ma ana kiran shi thalamus , shi wannan glands xin yana samar da seretonic, wanda aka samo daga melatonic, wanda ke shafar yin barci. • Ovaries: Wannan sai wajen mata kawai suna kuma samar da estrogen testestrone, da kuma progesterone, waxanda, su sinadaran saduwa ne na mata, masu qara masu sha’awa. • Testes: Wajen maza ne kawai shi yama samar da testes, wanda shi yana samar da ruwan maniyi. Waxannan

glands xin suna yin ayyuka tare domin tafiyar da glands xin da suke jikin mutum. Manyan sinadaran glands. Me hormones suke yi ? shi jiki yana da hormones da yawa, amma kuma akwai wasu da suke da suke taka muhimmiyar rawa, ta lafiyar jiki, idan aka gane su waxannan ayyukan da suke yi, na taimako da kuma da kuma kare lafiyar jiki. Maimakon jini ya kwarara zuwa wurin glands da kuma tafiya dasu, dom haka sai aka kira su endocrine glands. Yawancin su hormones xin an sa masu suna daga shi gland wanda ya samar dasu. • Waxannan jini ke xaukarsu zuwa wuraren da ake buqatar aikinsu. • Suna lura da kusan ayyukan jikin mutum. • Suna samar da canje canje ta hanyar zayawa ta qwayar halitta ko kuma samar da protein saboda su qwayoyin halittar. • Su waxannan hormones idan sun samu matsala, ko kuma sun yi yawa, suna iya samar dawata matsala. • Suna iya samar da babbar matsala ta rayuwa. Hormones cikin saduwa Ga mata estrogen (or estradiol) sune hormones masu taka rawa lokacin saduwa, su ke samar da lokacin balaga, ta sa ita uterus da jiki domin shirin tarbar ciki, da kuma lokacin da ake jinin haila, lokacin da aka daina haihuwa, shi mizanin estrogen yana canzawa, yana samar da wasu shiga sabon yanayin da zai damu mace. Ko wacce mace na iya shiga wani yanayi a rayuwarta, lokacin da kuma take son

haihuwa, domin yadda mata ke ji , idan sun kasance sun haihu, amma duk da hakan akwai wasu canje canje da mata suke yi, musamman jikinsu lokacin da suke da juna biyu. Waxannan canje canjen ana samun sune saboda hormones na mace, wanda ko wane yana taka muhimmiyar rawa. Akwai canje canje na hormones da ake samu lokacin da mace ke da ciki, ko wanne kuma yana da na shi aikin, akwai hormone xin da bayan an haihu, yana raguwa wajen yin aikin shi, har sai an rage ma shi qarfi, ko kuma an lalata shi. Progestrone shima yana kama da estrogen amma shi kuma ba wai an xauke shi wani hormone na saduwa da mace ba, kamar estrogen shi ma yana taimakawa ne, da maganar data shafi lokacin jinin haila da kuma lokacin da ake da juna biyu. Cristols ana kiran shi hormone na ‘’ stress hormone’’ saboda taimakawa jiki da take yi, wajen xaukar wani mataki lokacin da aka shiga stress, wato wani yanayi na damuwa wadda kan kawo gajiya. Wannan shi ne aikin daga cikin ayyukan shi muhimmin hormone. Melatonic shi mizanin shi yana canzawa duk tsayuwar rana, yana qaruwa ne bayan duhu, domin samar da da sinadarin da zai sa aji ana buqatar da yi barci. Testestrone shi ne babban hormone na harkar data shafi saduwa tsakanin mace da namiji, shi ke sa balaga, sa qarfi da kuma girman qashi, gashi akan fuska. Hormone na mata da maza

waxanda sune estrogen da kuma tsetestrone, su wasu masinjojine da ke aikawa da kuma isar da saqon wanda ya qunshi wani sinadari na, wanda shi mai ruwa ruwa ne. Waxanda a wani wuri na jikin mutum da kuma sanar da sauran wasu sassan abin da ya kamata su yi. Dukkamn maza da mata suna samar da estrogen da kuma testestrone, duk da yake dai yawan ya bambanta. Samar da shi kuma yana raguwa lokacin da shekaru suna qara yawa. Yawanci a dabbobi qwaqwalwa ita ce mai kula da yadda ha rake kai ga saduwar wajen nuna wasu halaye, ta hanyar hormones. Mutum da sauran wasu dabbobi basu daga cikin irin wannan nau’in saboda su, sun dogara ne akan wata qwarewa da kuma sauran wasu al’adu, fiye da dogara akan shi hormones. Rashin Samun Daidaituwa Yanzu halin da ake ciki rashin samun daidaituwa akan al’amarin da ya shafi hormone, yanzu abin ya zama ruwan dare ne game duniya, amma kuma bni zai fi damuwar mata, dangane da shi wannan al’amarin. Saboda sun fi koma shiga canje canje a rayuwarsu, akwai haka lokacin da ake balaga, akwain kuma lokacin jinin haila, lokacin xaukar ciki, lokacin haihuwa, lokacin shayarwa, lokacin da ka kammala haihuwa. Sai dai kuma wani abu daban rashin daidaituwar na iya samar da matsala. Matsalar zata iya samar da lalatar al’amarin lafiyar ita matar da kuma yadda zata kasnce idan mutane suka kalle ta. Hormones na iyasa a riga kallon ki a yarinya.


24 TALLA

A Yau

Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)


25

A Yau Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Kimiyya

Dala Miliyan 500

ne adadin kuxi Nijeriya ke kashewa duk shekara waurin safarar xanyen man fetur da wasu sinadaran da ake amfani da su a sashen sinadarari da magunguna

Binciken Wayoyin Mata Laifi Ne A Qasar Saudiyya Daga Idris Aliyu Daudawa

Miji ya duba abubuwan dake cikin wayar matar shi yanzu laifi ne a qasar Saudiyya, za kuma ayi ma shi tarar dala 133,009, da kuma shekaraxaya a gidan kurkuku, a wata sabuwar doka wadda aka yi domin,’’ A kare damar da kowa yake da ita a cikin al’umma da kuma kare’yanci’’. Wannan dokar za ta shafi dukkan maza da mata axanda suke zaune a gruruwan da muslmai suke. Wannan doka za ta kare maza ne daga matansu, kamar yadda abin yake a qsashen musulmai, dokar sakin aure a qasar Saudiyya kamar yadda take cikin Alkur’ani mai girma,sau da yawa, tana buqatar mata su, bayar da shaida akan, yadda aka danne hakki. Wayar miji kuma nan ne za a iya samun hujjoji masu qarfi waxanda za

aiya amfani dasu, wajen xaukar wani mataki. Dokar Anti- Cybercrime wato laifin da ya shafi hanyoyin sadarwa na zamani da nuna cewar, ‘’Kallo, qwacewa, ko amfani data ta abokin zama, ta hanyar samar da dama ta network, ko kuma komfuta, ba tare da izni ba, babban laifi bane’’. Wannan laifi akwai hukuncin dalar 133,000 ko kuma xaurin shekara xaya gidan kurkuku ko kuma a haxa duka. Hanyoyin sadarwa na zamani sun kasance wani wuri ne na aikata laifuka, da suka haxa da sharri, almubazzaranci, ga ma wani sharri, wannan ma ya haxa da amfani da account xin wani,kamar yadda ma’aikatar ta jaddada. Irin wannan doka maqwavciyar qasar wato haxaxxiyar daular Larabawa wato United Arab Emirates,ana iya xaure mutum watanni uku da kuma

biyan dala 817. Qasar mai arzikin manfetur da wasu qasashe waxanda suka fi amfani da

hanyoyin sadarwa na zamani a duniya, amma kuma amfani da al’adu, na kawo masu cikas akan amfani da hanyoyin.

A Karon Farko Isra’ila Za Ta Qirqiri Maganaxisun Nanosatelite Daga Abubakar Abba

A kwanakin baya ne Cibiyar qirqira ta qasar Isra’la tare da hukumar lura da sararin samaniya ta qasar suka sanar da cewar qasar ta Isra’ila, za ta qaddamar da tawaga uku na na’urar tauraruwar xan adam a sararin samaniya a wannan shekarar ta 2018. Qaddamarwar wadda itace karo ta farko a qasar ta Isra’ila, kamfanin dake qasar Jamus ne zai gudanar da aikin wanda shine ya qware wajen qaddamarwar da na’urar ta xan adam kuma qaddamarwar, tana xaya daga cikin akin (AdelisSAMSON). Aikin dai, tawagar wasu masu bincike ne suka qirqiro dashi wanda Pini Gurfil Darakta a cibiyar gudanar da bincike akan sararin samaniya ta Asher kuma wakili a sashen a sashen qereqere na (Aerospace). Cibiyar Adelis da hukumar sararin samaniya ta qasar Isra’ila sune suka bayar da goyon bayan gudanar da aikin. Abinda shirin yake son cimma buri akan aikin shine, don a tauraruwar ta xan adam, za ta iya tashi a yayin da ake kula da ita har zuwa tsawon shekara xaya, ayayin da take zagayawa a sararin samniya akan kimanin ma’uni mai kilo mita xari da shida.

A cewar Ministan kimiyya da fasaha na qasar Isra’ila Ofir Akunis, kimiyuar qasar ta Isra’ila ta samar da sabon abu ne da zai nuna ficen da ta yi akan qirqire-qirqiren ta. Ministan ya ce,“ muna tunqahon mu kasance a akan wannan aikin da za a qaddamar dashi wanda zai nuna cewar, an samar da wakilci akan bayar da gudunmawa akan ci gaba ta qirqire-qirqire a qasar ta Isra’ila da kuma samar da hanyar horar da xalibai a wannan fannin.” Akunis ya ce,” na’urar ta tauraruwar xan adam, za a yi amfani da ita wajen karvar saqwanni daga doron qasa da kuma yadda take juyawa, musamman don a dinga gudanar da bincike da kai xauki a lunguna da saquna na alumomi ta hanyar sanya ido. Na’urorin na tauraruwar xan adam guda ukun, an auna su dukkan su sun kai santi mita (10X20X30) kimanin tsawon akwatin takalmi kuma ko wacce xaya,tanada nauyin kimanin takwas. A cewar Darakta Janar na hukumar sararin samniya na qasar Avi Blasberger, na’urorin na tauraruwar xan adam, za a sanya masu kayan aiki kamar na na’ura mai qwaqwalwa da Ariya da na’urar da za ta dinga kula da sarrafa ta, inda kuma za a waya mai sauqi wajen

rabarwa, ya qara da cewa, na’urar ta tauraron xan adam tanada mahimmancin gaske a shekarun da suka gabata kuma qaddamar da ita xin tana qaruwa a duk shekara. Ya ce,“ ci gaban da kuma tsadar qaddamarwar, na irin wannan na’urar ta xan adam tana yin qasa akan wadda aka saba qaddamar. A cewar Blasberger “ a nan gaba, zamu sanya rai samar da dubban na’urar ta tauraruwar xan adam da zasu tashi daga doron qasa zuwa sararin samaniya da kuma tabbatar qarawa kafar sadarwa ta Internet sauri akan tsada kaxan fiye da yadda yake ayau.” Ya ce, mahimmancin kimiyyar ya haxada; tsari na( Rafael’s krypton) na gas, wanda shine na farko akan sahun tsari na duniya na na’urar xan adam. Ya jaddada cewar a yayin komawa akan tsari na na’urar zamani da Elta ya samar, za ta taimaka wajen kula da tsarin masana’antun MABAT na qasar Isra’ila tare da haxin kan masu gudanar da bincike na Technion. Gurfil ya qara da cewa, a bisa tsarin (propulsion) na na’urar tauraruwar xan adam zai samar da haske ta hanyar amfani da hasken rana wanda zai qara gusawa daga ko wanne sashi na na’urar ta xan adam kuma zai zama kamar fuka-fukai da

zai kula da tashin na’urar zuwa sama ba tare da anyi amfani da mai ba a matsayin jurewa iskar dake sararin samniya. Ko wacce na’urar ta xan adam, za a sanya mata kayan aiki na karvar sakwanni, da kuma xayar mai amasar bayanai kuma xaya da tafi wahala wajen zana na’urar ta xan adam. Ya ce, za ta taimaka wajen gudanar da aiki ga vangarorin tauraruwar xan adam kuma kafar sadarwar da tsarin ya haxada; masu karva guda biyu na(GPS) wanda za a yi amfani dasu wajen bugawar na’urar. Ya bayyana cewa,“ hanyar sadarwar za a yi amfani da ita akan tsari uku na tauraruwar xan adam don a samu sukunin sadarwa da xayar dake a kan doron qasa da kuma tashar dake kan doron qasa, wanda yin hakan an kawar da babbar matsalar qalubale ne akan aikin. Ya qara da cewa,za a ayi amfani da tasha da za a dinga amfani da ita wadda za ta dinga tura ma’adanai daga kan doron qasa. Ya ce,” idan muka lallava wajen tabbatar sararin na samaniya burin da aka sanya a gaba za aci nasara akai.” A cewar Gurfil ,“ za ta qara havaka samar da ci gaba na qananan taurarin xan adam da kuma kimiyya musamman a sararin samaniya.


26 RAHOTO

A Yau

Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Kafin Lemu: Garin da Arziki Ke Neman Mutane Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

A yanzu haka da Gwamnatocin wasu Jihohin ke Qoqarin ganin sun mayar da hankali wajen zaqulo albarkatun qasa da Allah ya shimfixe a wasu jihohin arewacin Najeriya, musamman ganin yadda ake yiwa al’ummar wannan yanki gorin man fetur da Gwamnatin tarayya ta dogara dashi wajen raba kuxaxen gudanarwa ga Gwamnatocin Jihohin Najeriya. A wasu garuruwan a iya cewa rashin sani yasa kaza kwana kan dami, domin kuwa akwai wuraren da Allah ya jibge ma’adanan da idan akayi amfani dasu wajen haqo su, ko shakka babu an daina maganar man fetur baki xaya. Garin Kafin Lemu gari ne dake qasar Ningi a Jihar Bauchi wanda ya yi iyaka da Garin Magami dake cikin yankin qaramar Hukumar Sumaila a Jihar Kano ta vangaren arewa, sannan kuma ta vagaren yamma garin ya yi iyaka da qaramr Hukumar Tudun Wada, a gabas kuma ya yi iyaka da qaramr Hukumar Birnin Kudun Jihar Jigawa. Garin Kafin lemu wanda masarautar garin ake kiranta da sunan Parda, Allah ya albarkaci garin da Jajirtaccen Hakimi mai suna Alhaji Usman Idris Parda wanda ya samu amsa tambayoyin wakilinmu cikin ‘yan Mintuna biyar. Alhaji Usman Idris Parda haifaffen garin Gatangar Warji dake qaramar Hukumar Warji a Jihar Bauchi cikin Shekara ta 1967, ya shiga makarantar Allo kasancewar bamu shiga ilimin zamani da wuri ba, inji Hakimin na Parda. Bayan na samu abinda na samu na shiga makarantar firamare, nayi sakandire harkuma na samu shaidar diploma , daga nan na fara aiki da wani Banki a matsayin akawu, wanda nayi aiki tsawon shekara biyu daga 1978-1989. Sai na wuce zuwa Jami’ar Maiduguri inda na samu digiri na na

• Abdullahi Muhammad Sheka da ‘yan Kuchka tare da Hakimin Parda a Tsakiya

farko, na gudanar aikin yiwa qasa hidima a wani banki a Jihar Kaduna, wanda sai da na kai muqamin Akanta har kuma na zama Manajan darakta. Ya ciga da cewa Mahaifina wanda alokacin shi ne dagacin Parda Allah ya karvi rayuwarsa, hakan tasa al’ummarmu suka matsa cewar sai na dawo na gaji mahaifin nawa, aka naxa ni amatsayin dagacin Parda a shekara ta 1998. Bayan nan ne kuma alokaicn mai Gwamna Malam Isah Yugudu ya shirya samar da qarin masarautu, Allah ya qaddara akayi wannan masarauta dana ke riqe da muqamin dagaci, aka xaga likkafar ta ta koma Qasar Hakimi wanda aka naxa ni amatsayin Hakimin Parda. Muqamin da na ke riqe dashi har zuwa wannan ziyara da wannan Jarida mai albarka da ta kawo garin Kafin Lemu dake masarautar Parda. Duk da wannan bunqasar da kuma wadataccen ilimi da kuma matsayin Hakimta da wannan mutun yake dashi, hakan ba ta sa shi rungumar mulkin amatsayin abin tinqahon da kila zai sa takalmin qarfe domin murqushe mai qaramin qarfi ba, bilhasali ma ko da Jaridar LEADERSHIP A Yau ta isar fadar Hakimin muka

buqaci ayi mana iso, da ya fito mun xauka wani ne daga cikin fadawansa saboda walwala. Yakana, qasqan da kai da kuma buxaxxiyar fuska ga al’ummar da yake wakilta. Kasancewarsa gogaggen mai lilimn zamani da kuma ilimin addini, ya tabbatarwa da kansa cewa bai kamata basarake ya xade qafarsa kawai sai mulki ba, kamata ya yi ya buxe qofarsa domin gayyatowa al’ummarsa duk wani tsari da zai kawowa garin nasa ci gaba. Garin Kafin Lemu garin ne kamar yadda idonmu ya gane mana wanda Allah ya horewa kogi mai gudana wanda ya taso tun daga tabkin Tiga dake Jihar Kano, ya ratsa T/Wada, ya shiga Bura, ya shigo Kafin Lemu har sai da ya dangana da Kafin Gana. Hakan ta baiwa al’ummar wannan yanki damar gudanar da harkoki Noman rani da damina, sannan kuma wanann Gari ana noma Auduga iya ganinka, Shinkafa, Waken Soya, Gyaxa da sauran manyan amfanin gona da duniya ke alfahari dasu. Kamar yadda cikin bayanin Hakimin ya shaidawa Jaridar LEADERSHIP A Yau cewa wannan gari na Kafin Lemu gari ne da arziki ke neman jama’a, domin akwai manyan Duwatsu tun daga Katangar Warji suka ratsa ta Gwaram, Bura zuwa

Garin Kafin Lemu. Akwai ma’adanai kamar zinare, duwatsun qawa da sauransu masu yawan gaske shimfixe wannan yanki, kenan Karin maganar Bahaushe da ke cewa rashin sa ni ya sa kaza kwana kan dame. Sakamakon wannan manyan labarkatun qasa da Allah ya albarkaci wannan gari dasu yasa Hakimin Alhaji Usman Idris Parda mayar da hankali domin ganin ya gayyato masu harkokin noma irin na zamani da kuma masu sha’awar zuba jari ta fuskar haqar ma’adanai domin shigowa wannan yanki domin gudanar da harkokinsu, hakan zai taimaka kwarai da gaske wajen buqasar tattalin arzikin qasa, samar da sana’un dogaro da kai alokaci guda kuma Gwamnatin qaramar Hukuma, Jiha da qasa baki xaya suka qara samun isassun kuxaxen shiga. Yanzu haka Garin Kafin Lemu wanda ya shahara wajen Noman audugu, Rake, Shinkafa, Waken Suya, Gyaxa an tsara samar da guraren noma ga masu sha’awa sannan kuma manoman qauyen wayayyune, aduk lokacin da aka gabatar masu da wani sabon tsarin noma a shirye suke da karvarsa kuma suna wadatattun filayen noma wanda suke bada aro, haya ko kuma su noma da kansu.


RAHOTO 27

A Yau Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Miliyoyi Sun Halarci Maulidin Shehu Inyas A Abuja Daga Khalid Idris Doya, Abuja

A ranar Asabar xin da ta gabata ne, 15 ga watan Rajab, miliyoyin jama’a a faxin qasar nan da wasu qasashe suka yi wa birnin tarayyar Nijeriya qawanya domin gudanar da gagarumun maulidin tunawa da ranar haihuwar Shehu Ibrahim Inyass (R), wanda suka saba yi duk shekara. Wannan maulidin shi ne karo na 42 da ake gudanar da wannan maulidin a Nijeriya. Wakilinmu ya labarto mana cewar tun kafin ranar ta Asabar, Abujan ya samu cikowar jama’a musamman ‘yan xariqa daga sassa daban-daban na Nijeriya inda suka yi gagarumar addu’a ta musamman wa qasar nan domin wanzar da zaman lafiya da kuma samun shuwagabanai na gari. Babban taron maulidin na kwanaki biyu, wanda ‘yan Xarikar suka yi cincirido a babban Massalacin qasa a ranar Alhamis da yammaci inda suka fara yin addu’o’I na musamman har zuwa Juma’a, a yayin da kuma a ranar Asabar xin ne suka nausa babban filin wasa da ke Abuja Eagle Square domin gudunar da babban maulidin na Shehu Inyass wanda ya kunshi baqi daga qasashe sama da 16 a faxin duniya. Maulidin Shehu Inyass xin wanda ya haxa fuskokin manyan Shehunan, Malamai, shuwagabanai, ‘yan siyasa da kuma dandazon mabiya Xarika daga sassan duniya, cikin manyan bakin da suka halarta har da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, wanda ake tunanin zai tsaya takarar shugaban qasa, tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso. Da yake jawabi a wajen gagarumar taron, babban Malamin xarikar Tijjaniyya a Nijeriya, Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya buqaci dukkanin mabiyansa da sauran ‘yan Nijeriya da su tabbatar da mallakar katin zave na dindindin wato (Permanent Voter Cards) domin fuskantar zaven 2019 da ke tafe. Shehu Xahiru Bauchi ya bayyana cewar ta hanyar mallakar PVC ne kaxai mutum ne da iko gami da zarafin zaven dukkanin wanda yake so a kowani lokaci da zarar aka fara hidimar zave, Malamin ya misalta cewar katin zaven siyasa a matsayin wata makami mai qarfi ga

kowani xan qasa. Xahiru Bauchi ya bayyana cewar katin zave a matsayin wata makami mai qarfin gaske da kowani xan qasa zai yi amfani da ita wajen zavar nagartaccen shugaban da ya dace ya mulkesa a bangaren shugabanci daban-daban. Daga nan kuma ya qirayi dukkanin mabiyansa da su tabbatar da mallakar katin zave na dindindin domin zavar mutumin da suka tabbatar da nagartarsa, wanda zai yi musu aiki na gari a kowani lokaci, Ya ce, ta hanyar zave ne kowani xan qasa zai kwaci ‘yancinsa gami da fitar da damuwarsa ta fuskacin zave. Shaikh Bauchi ya bayyana cewar manufar shirya maulidin dai domin nuna godiya wa Allah da samuwar waliyin Allah a yankin Afirka Sheikh Ibrahim Niyass daga qasar Senegal. Ya bayyana cewar Shehu Ibrahim Inyass ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gabantar da addinin musulumci, haxe da koyar da musulunci a faxin Afirka da duniya baki xaya. Ya kuma bayyana cewar suna amfani da irin taron wajen yin addu’o’I na musamman wa qasar nan domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban qasa a kowani bigire, ya kuma qara da cewa addu’a ita ce hanya

xaya tilau na samun mafita a kan kowace qalubalen ko matsalolin da suke fuskantar qasar nan. Da yake jawabi a wajen maulidin, shugaban Nijeriya Alhaji Muhammadu Buhari ya jinjina wa qoqarin shuwagabanin qungiyar xarikar Tijjaniyya wajen kokarin wanzar da zaman lafiya a faxin qasar nan ta fuskacin yi wa qasar addu’a kan matsalolin da suke addabar Nijeriyar a kowani lokaci. Buhari wanda ya samu wakilcin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya tabbatar da cewar Shehu Inyas ya bayar da gagaruman gudunmawa wajen xaukakar addinin Islama musamman a yankin Afirka, Asia da kuma yankin Europe. Ya kuma aniyar gwamnatin tarayya na ci gaba da bayar da gudunmawa wajen qarfafar zaman lafiya da ci gaban jama’a a kowani lokaci a wannan qasar ta Nijeriya. Babban Limamin Markaz Faidal Islamic Foundation, da ke Suleja, Shiek Abubakar Musa Kwamba, ya bayyana cewar ‘yan Tijanniya suna matuqar girmama ranar haihuwar Sheik Ibrahim Nyass domin nuna murnarsu a kan samuwar tasa. LEADERSHIP A YAU ta labarto cewar kaxan daga

cikin jiga-jigan da suka halarci taron sun haxa da Khalifan shehu Tijjaniyya wanda kuma xa ne ga Sheikh Ibrahim Nyass, Sheikh Ahmad Tijjanni Nyass daga qasar Senegal, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin Mallam Adamu Adamu, ‘yan majalisu, gwamnoni, wakilin Sarkin Musulmai, tsohon xan majalisar Ghali Umar Na’aba, da sauransu. Wasu daga cikin qasashen da suka hallarci taron sun haxa da Morocco, Senegal Tanzania, Egypt, Libya, Britain, Jamus , Aljeriya, Masar, Sudan, Chadi, Ghana, Kamarun da wasu daga qasashen European. Wakilinmu ya labarto cewar birnin tarayyar Nijeriya ta cika ta vatse, inda ‘yan xarikar suka cike kowani lunguna da sakonan titin Abuja a cikin waxannan kwanaki biyun. Tun da fari ma, Xahiru Bauchi ya bayyana cewar ita maulidi ana yin tane domin nuna godiya wa Allah da samuwar bayin Allah na gargaru da kuma salihan bayi, ya bayyana cewar suna taron tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah, don haka ne kuma suke taron tunawa da ranar da aka haifi magadansa, ya ce soyayya da godiya wa Allah ce manufarsu a kowace lokaci na yin irin wannan taron.


28

Tauraruwa Mai Wutsiya

A Yau

Talata 17.4.2018 08174743902 wutsiya2019@gmail.com

Budurwa Ta Kashe Mahaifinta Saboda Ya Hana Ta Auri Masoyinta Daga Abubakar Abba

Wata ‘yar shekara sha shida mai suna Emani Kure ta aikata aika-aika sakamakon hallaka mahaifinta har lahira. Emani Kure wadda take da zama da iyayen a qauyen Karavan dake yankin Bwari a garin Abuja ta kashe mahaifin nata xan shekara 40 mai suna Kusha Kure,inda ‘yan sanda suka tabbatar da cewar, lamarin ya auku ne a ranar Lahadin data gabata da misalin qarfe uku na dare. Yarinyar ta hallaka mahaifin nata ne saboda yaqi amincewa buqatar ta na auren wani saurayin ta mai suna Nasiru Musa. Emani da masoyin nata Nasiru Musa, sun shafe kimanin shekaru biyu suna soyayayya sun bayyana ra’ayin su na son yin aure. Kwamishinan rundunar ‘yan sanda na Abuja Sadiq Bello ya bayyana cewar, an kawo rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na gudumar Bwari. Ya ci gaba da cewa, jami’an sa masu na sashen binciken kisan kai, sun cafko Emanu tare da mahaifiyar ta mai suna Asabe Kure, wadda ake zargin ta taka muhimmiyar rawa

wajen kashe mijin nata. Ya qara da cewa daga baya an mayar da binciken ga sashen binciken kisan kai dake rundunar. A hirar da manema labarai suka yi da wadda ake zargi Emani, ta yi bayani mai girgizarwa akan yadda ta sheqa da mahaifin nata barzahu. Emani ta ce, “na kashe mahaifi na saboda yaqi amincewa in auri masoyi na Nasiru Musa.” Acewar ta, “ mun sahfe shekaru biyu muna soyayya, kuma mahaifi na ya sha jibga ta a lokuta da yawa akan in janye ra’ayi na son auren Nasiru”. Emani ta qara da cewa, na kashe shine da misalain qarfe uku na dare kuma mahaifiya ta ce ta bani wannan shawarar a lokacin da muke kwance a harabar gidan mu, cewar in shiga xaki, inda mahaifi na ke yin barci in kashe shi. Ta umarce in yi amfani da adda don in hallaka shi, inda naje inda yake ajiya addar sa na xauko naje xakin sa na kashe shi. Ta ce, “na sassare shi a wuyan sa,bayan da mahaifiya ta riqe mini qafar sa.” A cewar ta, “bayan na kashe

•Wacce ake zargi

shi, na gudu daga gidan mu zuwa gidan qawa ta mai suna Regina. Ta ce, Nasiru bai da masaniyyar ina son in kashe mahaifin nawa, kuma shi ma ya kixime a lokacin da ya samu labarain abinda na aikata.” A na ta vangaren, mahaifiyar ‘yar shekara talatin da biyar ta qarya zargin da ‘yarta ta xora mata. Asabe ta ce,”nida majina marigayi bama goyon bayan Emani akan son da take na auren Nasiru Musa, amma tayi biris da jan kunnen da muka yi mata” .

A cewar ta, a lokacin mijina yana barci a xaki kuma ‘yar qaramar yata da nake goyo ta tashi ta fara kuka na tashi don in bata Nono tasha, sai kawai naji mijina yana ihu a cikin xakin sa, inda nayi gaggawa na kirawo siriki na mahaifin mijina. Shi da sauran jama’a suka shigo gidan mu suka iske mijina a cikin jini, kuma yata bata wurin, domin ta gudu. Acewar ta, na fara zargin ta da Nasiru Musa a zaman waxanda suka aikata ta’asar. Ta ce, munje ofishin “yan sanda na gudunduma dake Bwari don kai rahoton akuwar lamarin, inda na sheda masu cewar, ina zargin ‘yata da saurin ta akan aikata ta’asar, inda daga baya ‘yan sanda suka cafko Nasiru da ‘yata kuma ta amsa laifin ta, amma ta ce wai nice na umarce ta kashe mijin nawa. Nasiru xan shekara ashirin da biyu, ana zaegin sa da hqxa baki don kashe Kure. Nasiru ya ce bai san cewar Emani ta kitsa son kashe mahaifin ta ba. Har yanzu waxanda ake zargin Emani da mahaifiyar ta da kuma Nasiru suna tsare ana gudanar da bincike akan lamarain.

An Sace Sakataren NURTW Tare Da Neman Kuxin Fansa A Ondo Daga Abubakar Abba

An sace Sakataren qungiyar direbobi ta NURTW reshen jihar Ondo Mista Kayode Agbeyangi. Lamarin ya auku ne dukudukun ranar Asabar data gabata a lokacin yana kan hanyar sa ta zuwa gun iyalan sa dake jihar Legas. Motar Agbeyangi an ganta a yashe a gefen babban titin Akure-Ilesa an kuma ruwaito cewar, waxanda suka yi garkuwar dashi sun tuntuvi iyalan sa da a basu kuxin fansa naira miliyan biyar. Sai dai, har ya zuwa haxa wannan rahoton iyalan sa basu iya haxa wannan kuxaxen ba.. Shugaban qungiyar ta NURTW dake jihar, ya tabbata da aukuwar lamarain. Ya ce, an sace shi ne yana kan hanyar sa ta zuwa Legas Kakakin ‘yan sandan ya ce, lamarin ya auku ne a wajen jihar domin ba a kawo wa rundunar rahoto ba.


A Yau

29

Talata 19 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Qasashen Waje

Tare da Rabiu Ali Indabawa 08069824895

Akwai Yiwuwar Jamhuriyar Nijar Ta Samar Da Tashar Makamashin Nukiliya Tawagar kwararru daga Hukumar IAEA na ziyarar Jamhuriyar Nijar domin binciken shirin makamashin nukiliya a qasar da nufin warware matsalar wutar lantarki da ake fama da ita a yankin Afirka ta yamma. Shugabar qungiyar da ke kula harkokin makamashin nukiliya a Jamhuriyar Nijar wato HANEA, Zeinabou Mindaoudou Souley ta bayyana cewa sun hada wani rohoto da ya yi nazarin yiwuwar amfani da makamashin nukiliya wajen samar da wutar lantarki sannan aka aikawa hukumar ta IAEA domin ta tabbatar da sakamakon binciken. Wannan shine matakin farko na tantance yiwuwar kaddamar da ayyukan samar da makamashin nukiliya a qasar Nijar da ta kasance daya daga cikin kasashen duniya da suka fi kowa arzikin karfen Uranium. Saboda haka wannan shirin zai .shafi yankin Afirka ta yamma gaba

daya. “Wutar da wannan shirin zai samar ya fi karfin Nijar ita kadai. Wutar domin kasashen yammacin Afirka ne,” inji shugabar ta HANEA Shugabar ta bayyana cewa, ana sa ran nan da shekaru 15, bukatar wutar zata karu a yankin yammacin afirka wanda dole sai da wannan makamashin. Shugaban da ke wakiltar mataimakin shugaban hukumar IAEA, Anthony Stout ya bayyana cewa Jamhuriyar Nijar na da niyyar cimma wannan burin na wadatar wutar ganin yadda ta mayar da hankali wajen mutunta ka’idojin ayyukan kafa tashar makamashin nukiliya kuma hukumar ta yi alwashin tallafa mata. Ana sa ran nan da shekarar 2030, wannan tashar za ta fara sarrafa makamashin domin samar da wutar lantarki. Hakan zai bunkasa ayyukan kamfanoni da masana’antu.

Trump Bashi Da Cikakkiyar Tarbiyyar Zave: Taliban Ta Yi Kakkausar Gargaxi Ga Al’umma Da Zai Iya Shugabancin Amurka qungiyar mayakan Taliban neman qungiyar Taliban da ta ce sam, sam ba sauran wata maganar sulhu tsakaninta da gwamnatin qasar Afghanistan, sannan kuma ta nemi mutanen qasar, waxanda suka gaji da yakin da qasar ta jima tana fuskanta, da cewa su gujewa zaven ‘yan majalisar wakilai na qasar mai zuwa, wanda Taliban tace “sojan mamaye da Amurka ke shugabanta” ne suka shirya shi. Sanarwar da ‘yan Taliban din suka bada ta biyo ne bayan tayin da shugaban qasar Afghanistan Asharaf Ghani yayi ne a ranar Assabar da ta wuce, inda ya sake

Tsohon shugaban Hukumar Binciken Manyan Laifukka ta Amurka ta FBI, James Comey yace shugaba Donald Trump baya da “cikakkiyar tarbiyya da kamun kan da zai iya shugabancin Amurka, kuma akwai shedar dake nuna cewa shugaban ya taba yunkurin hana doka tayi aikinta.” Haka kuma Comey ya zargi shugaba Trump da cewa “shi ba mai iya fadar gaskiya bane.”

Duk waxanan kalaman na Comey suna zuwa ne a cikin hirar da tashar telbijin ta A-B-C tayi da shi ne a jiya, yayinda ake dab da fitowa da wani sabon littafin da ya rubuta da zai nuna rawar da ya taka wajen binciken rawar da Rasha ta taka a zaven shugaban kasan Amurka na shekarar 2016 da wanda ya gudanar game da sakkonin email na ‘yar takara jam’iyyar Democrats watau Hilary

Clinton da kuma zantawarsa da shugaba Trump a bara kafin shi Trump din ya kore shi daga mukaminsa na shugabancin FBI. Trump dai ya musanta aqasarin duk waxanan zarge-zargen na Comey, ciki harda wanda yayi na cewa ya kori Comey ne don ya ki tsaida binciken da yake yi akan tsohon mashawarci kan harkokin tsaro, Michael Flynn.

cewa ta fito ta shiga zaven na ran 20 ga watan Oktobar wannan shekara, a matsayin jam’iyyar siyasa. Wannan tayin na shugaba Ghani, wanda tun cikin watan Fabrairu yayi shi, ya sami yabawa sosai daga ciki da wajen qasar ta Afghanistan. Sai dai ‘yan Taliban na ci gaba da yin watsi da tayin a bisa hujjar cewa har yanzu “Afghanistan na karkashin mamayen dubban sojojin kasashen waje waxanda duk wasu kudurorin siyasa da na soja su ne suke yanke shawara a kansu.”


Wasanni A Yau

Talata 17.4.2018

30

Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com

Na Fara Tunanin Kaka Mai Zuwa Saboda Mun Gama Da Wannan -Kompany

Real Madrid Ta Koma Mataki Na Uku A Laliga Qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid ta koma ta uku a teburin La Liga da maki 67 bayan da ta doke Malaga wadda take mataki na qarshe har gida da ci 2-1 a ranar Lahadin data gabata. A wasan na ranar Lahadi Real Madrid ta ajiye da dama daga cikin manyan ‘yan wasanta na yau da kullum da suka haxa da Cristiano Ronaldo da Gareth Bale, bayan tsallake rijiya da baya da ta yi a gasar

Zakarun Turai a hannun Juventus da ci 4-3 jumulla. Xan wasa Isco ne ya fara cin qwallo a minti na 29 inda ya zura qwallo a ragar tsohuwar qungiyar tasa, da wani kyakkyawan bugun-tazara. Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma a minti na 69 Isco xin ya ba wa Casemiro qwallon daya zura ta biyu. Ana dab da tashi bayan minti 90 na qa’ida Diego Rolan ya ci wa Malaga

qwallo xaya bayan kuskuren da Jesus Vallejo ya tafka. Masu masaukin baqin waxanda wasan La Liga huxu kawai suka ci a bana, maki 14 ne tsakaninsu da tsira daga gasar yayin da ya rage wasa shida a kammala. Real Madrid kuwa wadda ta wuce saman Valencia a tebur da wannan nasara, maki huxu ne tsakaninta da ta biyu Atletico Madrid, wadda ita kuma ta doke Levante 3-0 a ranar Lahadin.

Sakamakon Wasan Dambe Na Wannan Makon Kimanin wasanni 11 aka dambata a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a dake babban birnin tarayya Abuja a safiyar Lahadin data gabata. Damben da aka yi kisa shi ne wanda Shagon Shagon Alin Tarara daga Arewa ya bugeShagon Bahagon Sisco daga Kudu yayinda Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa ya doke Garkuwan Ebola daga Kudu shi kuwa Bahagon

Shagon Alabo daga Kudu ya yi nasara a kan Tetenus din Na Bachirawa daga Arewa. Shagon Shagon Mada daga Kudu da Shagon Shagon Lawwalin Gusai daga Arewa. Shagon Bahagon Balan Gada daga Arewa da Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu Shagon Dogon Jafaru daga Kudu da Shagon Garba Dan Malumfashi daga Arewa.

Shagon Dan Digiri daga Kudu da Nuran Mahaukaci Teacher daga Arewa. Bahagon Alin Tarara daga Arewa da Dan Yalo Autan Sikido daga Kudu. Shagon Dan Shariff daga Kudu da Shagon Dogon Kyallu Guramada. Dan Yalo Autan Sikido daga Kudu da Shagon Shagon Alin Tarara daga Arewa. Dunan ‘Yar biyar Guramada da Dan Yalo Autan Sikido daga Kudu.

Qungiyar qwallon qafa ta Manchester City ta lashe kofin gasar firimiya ta qasar Ingila, duk da cewa qungiyar bata buga wasa a ranar Lahadin data gabata ba. Babbar abokiyar hamayyarsu Machester United, ta sha kashi a gida a hannun qungiyar Westbrom wadda take qoqarin faxuwa daga gasar ta firimiya ta bana. Hakan na nufin ba za su tava iya kamo Manchester City a yawan maki ba koda kuwa ace zasu rasa duk wasanninsu da suka rage su kuma yaran na Mourinho su lashe dukkan wasanninsu. Wannan ne karon farko da kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya lashe kofin gasar ta firimiya tun bayan komawarsa daga qungiyar Bayern Munchen Kulob din na Manchester City ya na da sauran wasanni biyar a gaba kuma wannan ne karo na uku da qungiyar ta lashe gasar firimiya a tarihi. Mai koyar day an wasan qungiyar ya tabbatar da cewa bazasu saki jiki ba a ragowar wasanninsu na gaba da zasu buga kuma zasu fara shirye shiryen kakar wasa mai zuwa domin kare kambunsu. A qarshe yace yasan ragowar manyan qungiyoyin gasar suma zasuyi kyakyawan shiri domin kakar wasa mai zuwa ta hanyar siyan manyan yan wasa. Shima kaftin xin qungiyar, Vicent Kampani ya bayyana cewa tuni yafara tunanin gasar kaka mai zuwa tunda sun gama data wannan shekarar.


WASANNI 31

A Yau Talata 17 Ga Afrilu, 2018 (30 Ga Rajab, 1439)

Tunda Muka Doke Chelsea Na San Za Mmu Lashe Gasar Firimiya

Gasar Zakarun Turai Ce A Gabana, Inji M. Salah Daga: Abba Ibrahim Wada Gwale

Xan wasan gaba na qungiyar qwallon qafa ta Liverpool, Muhammad Salah ya bayyana cewa baya tunanin lashe kyautar xan wasan dayafi kowanne xan wasa zura qwallo a raga a gasar firimiya sai dai yace babban burinsa shine qungiyarsa ta lashe gasar zakarun turai. A ranar Asabar ne Liverpool ta doke qungiyar Bournemouth da ci uku babu ko xaya kuma Salah ya zura qwallo xaya wadda tasa yanzu yanada qwallaye 30 kenan a gasar firimiya ta qasar ingila kuma ya karya tarihin tsohon xan wasan Chelsea, Didier Drogba. Har ila yau Salah yana cikin yan wasan da hukumar qwallon qafa ta qasar ingila ta ware don zaven gwarzon shekara na gasar firimiya tare da Kevin De Bruyn na Manchester City da Harry Kane na Tottenham da kuma Lorey Sane da David Silva da kuma David De Gea. Sai dai Salah yace burinsa shine lashe gasar zakarun turai saboda itace a gabansu sannan kuma yafison lashe gasar ta zakarun turai akan wata kyauta da zai lashe shi kaxai. Xan wasan yace idan aka tambayeshi cewa yazavi tsakanin lashe gasar zakarun turai da kyautar gwarzon xan qwallo tabbas zai zavi gasar zakarun turai domin kuwa kowanne xan wasa yanason ganin lashe gasar. Ya ci gaba da cewa lashe kyautar wanda yafi kowanne xan wasa zura qwallo a raga itama tana gabansa amma kuma bata cikin abunda yasa a zuciyarsa saboda kamar yadda yan wasan Liverpool suke taimaka masa wajen zura qwallo suma yan wasa irinsu Harry Kane da Sergio Aguiro yan wasan qungiyarsu suna taimaka musu. A qarshe yace yana fatan doke tsohuwar qungiyarsa ta Roma domin zuwa wasan qarshe na gasar wanda abin da wahala amma idan suka dage zasu iya lashewa.

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

PSG Ta Lashe Gasar Qasar Faransa Bayan Tayi RagaRaga Da Monaco Da Ci 7-1 Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Qungiyar Paris St-Germain ta qasar Faransa ta xauki kofin gasar qasar Faransa, na Ligue 1 bayan da ta lallasa masu riqe da kofin Monaco 7-1 a filin ta na Parc des Princes dake babban birnin qasar. Yadda ‘yan wasan qungiyar mallakar Qatar suka nuna iyawa da bajinta ya sa suka yi wannan nasara ta yankan shakku wadda ta sa suka ba wa Monaco ta biyu a tebur tazarar maki 17, kafin kammala gasar da wasa biyar. Giovani lo Celso da Angel di Maria kowanne ya ci bibbiyu, yayin da Edinson Cavani da Julian Draxler

kowa ya saka xaixai a raga. Xan wasa Radamel Falcao na Monaco shi ya ci kansu ta bakwai xin, yayin da Rony Lopes ya ci musu ladangabe, guda xaya a wasan da za a ce vangare xaya ne ya yi rawar-gani. Kofin shi ne na biyar na gasar ta Faransa, da PSG ta ci a cikin kaka shida datake buagawa tun bayan da Qatar suka karvi ragamar jagorancin qungiyar. Monaco ta xauki kofinta na farko ne a cikin shekara 17 a kakar 201617, bisa jagoranci ko qoqarin Falcao da kuma zuwan matashin xan wasan Faransa Kylian Mbappe. Falcao ya ci gaba da zama a Monaco, amma Mbappe wanda ya koma PSG a kan fam miliyan 166,

farko a yarjejeniyar aro, da kuma wasu manyan ‘yan wasan kamar xan baya Benjamin Mendy sun bar qungiyar a bazarar da ta wuce. Wannan tafiya ta tarin gwanayen ‘yan wasan ta raunana Monaco wadda ita ce mafi qarfi cikin abokan hamayyar PSG. Wannan ne ya sa kusan a ce ba makawa qungiyar ta PSG za ta sake zama zakara a Faransa saboda duk da haka itama ta siyi sababbin yan qwallo. PSG ta doke Monaco 3-0 a wasan qarshe na cin kofin qalubale na lig na Faransa ( French League Cup), a qarshen watan da ya gabata, sai kuma ga shi a wannan karon lallasawar ta ma fi waccan.

Mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewa tun lokacin da suka doke qungiyar Chelsea a gasar firimiya a watan Satumbar shekarar data gabata har gida yasan cewa sunada qarfin lashe gasar firimiya. Manchester City ta zama zakara ne a gasar firimiya bayan da qungiyar Manchester United tayi rashin nasara a gida a wasan da suka fafa ta a ranar Lahadin data gabata wanda hakan yasa Manchester City ta tabbata cewa ta lashe gasar firimiya. Guardiola yace tun lokacin da suka doke Chelsea har gida ranar 30 ga watan Satunba yasamu qwarin gwuiwar lashe kofin firimiya saboda Chelsea ce take kare kambu kuma sunada qarfin doke manyan qungiyoyi. Sai dai Guardiola yace zasu sake dagewa da sabon shiri domin fuskantar kakar wasa ta gaba saboda kakar wannan shekarar ta qare kuma ta tabbata sun zama zakara a gasar. Ya ci gaba da cewa yasan ragowar qungiyoyi zasu cigaba da sabon shiri don fuskantar kakar wasa mai zuwa saboda haka shima qungiyarsa bazatayi qasa a gwuiwa ba wajen siyan sababbin yan wasa don kare kambunsu. A qarshe yace dole ya jinjinawa yan wasan qungiyar bisa qoqarinsu na ganin sun lashe gasar da kuma juriyar da suka nuna tun daga farko har qarshen gasar kuma yasan sun shirya kare kambunsu a shekara mai zuwa.

Har Yanzu Akwai Matsala A Manchester United, Inji Vidic

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Tsoon xan wasan baya na Manchester United, Nemanja Vidic yace har yanzu qungiyar akwai matsala saboda idan suna wasa da qaramar qungiya basa gudu yadda yakamata kuma suna riqe qwallo tana yawa a hannunsu. Vidic ya bayyana hakane bayan da qungiyar ta Manchester United ta tashi daga wasan da tasha kashi a hannun Westbrom da ci 1-0 har gida wanda kuma rashin nasarar ne yasa Manchester City tazama zakara a gasar. Vidic yace yakamata idan qungiyar tana buga wasa ta dinga sauri musamman idan da qaramar qungiyar take buga wa kuma yan wasan basa dagewa kamar yadda sukeyi a shekarun baya. Ya ci gaba da cewa abin kunya ne ace United tayi rashin nasara a hannun Westbrom wadda wasanni uku kawai taci a wannan kakar. Ya qara da cewa tabbas akwai gyara acikin qungiyar wanda kuma mai koyar da yan wasan qungiyar yakamata yayi wani abu akai a shekara mai kamawa idan har yanason ganin qungiyar tasamu abinda take nema. A ranar Lahadi ne dai qungiyar zata kara da qungiyar qwallo qafa ta Tottenham a wasan cin kofin qalubale na FA wasan kusa dana qarshe a filin wasa na Wembley dake birnin Landan.


LEADERSHIP 17.4.18

AyAU Talata

Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA

LeadershipAyau

No: 125

N150

QASASHEN WAJE

Akwai Yiwuwar Jamhuriyar Nijar Ta Samar Da Tashar Makamashin Nukiliya > shafi na 29

Falsafa: Tsafi, Duba Da Rufa-ido (I) Aliyu Dahiru Aliyu

Tsafi: Karatun tsafi da yadda yake yana vangaren “Metaphysics” a Falsafa. Ya wuce ilimin Kimiyya (Science) domin shi yana karatun bayan xabi’a ne (Beyond the nature) ita kuma kimiyya na karantar xabi’a ne (nature). Kimiyya za ta gayamaka daga 1 sai 2 amma “Metaphysics” shine zai gayamaka meyasa daga 1 sai 2. Kimiyya za ta gayamaka daga A sai B amma “Metaphysics” na binciken meyasa daga A sai B. Don haka kimiyya ba za ta iya karantar tsafi ba don haka ta sanyashi a cikin “Pseudoscience” domin hakikar gane tsafi sai a “Philosophy”. Tsafi dadadden abune a tarihin xan adam da ya samu ci gaba a shekaru dubbai da suka wuce. Mutanen Syria, Egypt, Babylons, Nabataens da Chaldaens sune suka samu cigaba a vangaren wannan sana’a. Bayan zuwan musulinci an samu wasu daga malamai da suka karanci sihiri da tsafi don su san hakikarsa a babin ka san sharri ba don ka aikata sharri ba. Jabir bn Hayyan, wanda babbane a cikin masana kimiyya (Alchemy), ya karanci tsafi har sai da aka riqa kiransa da “Chief sorcerer of Islam”. Sannan a Spain an samu irinsu Maslama bn Ahmad Almajiristi da har littafi ya rubuta akan tsafi mai suna “Ghayah” wanda yake tattare da abubuwan mamaki kwarai da gaske! Aikata tsafi haramunne a addinin musulinci saboda cutarwar da yake wa mutane kuma yana bukatar, a mafi yawan lokaci, mutum ya dogara ga wanin Allah a zahiri. Matsafa suna fara iya tasarrufi da ruhinsu kafin su aikata duk abin da suke. Wanda zaiyi tsafi yana bukatar yazama mai iya juya ruhinsa (soul) ta yadda jikinsa ba zaiyi tasiri ba a lokacin da yake aikata tsafin. Tamkar mutumin da yake hawa dogayen gidane (skyscrapers), idan yana so yayi gudu ya tsallaka daga wannan gidan zuwa wancan mai tsawon gaske to dole sai ya cire tsoron da yake ransa kafin ya tsallaka. Rashin haka zai iya sanyawa yayi karkarwa ya fado. Kamar wanda yake tafiya a tsaye akan igiyar da aka xaure tsakanin dogayen gini biyu. Idan mutum yaji tsoro a lokacin da yake tafiya akan igiyar to shikenan sai yayi karkarwa ya fado, amma idan baiji tsoro ba to zai iya tasarrufi da jikinsa ya cigaba da tafiya bai fado ba. Irin wannan hanyar ita take sanyawa matsafa suna iya tasarrufi da jikinsu ta hanyar sarrafa ruhinsu gurin faruwar wasu abubuwan na ban mamaki. Idan mutum ya kware wajen iya tasarrufi da ruhinsa to anan zai iya tasarrufi da abubuwa dayawa a cikin xabi’a. Masu aikata “sorcery” ba su fiye amfani da wani abu wajen yin tsafinsu ba. Ga wanda ya kalli film din Marlin wanda yake iya tasarrufi da idonsa wajen tsafi to wannan shine “sorcery”. Masu “witchcraft” sune bokaye da suke amfani da wasu abubuwan na itatuwa ko dabbobi da suke ganin alakarsu wajen aikata wani lamari da ruhinsu a lokacin da suke tsafin. Irin wadannan sune masu cewa akawo itace kaza ko farar tsuntsuwa wajen aikata wani lamari. Na taba karanta yanayin wani tsafi mai ban tsoro da ya ce a jika gawar mutum da man ridi har tsawon kwana 40 a riqa yagar naman da ya ragargaje ana ci a

dahiraliyualiyu@gmail.com

lokacin da ake tasarrufi da ruhi, to ta nan mai tsafin duk abin da ya fada ya ce zai faru to a kaso 100 za a samu 80 ya faru! Irin wadannan matsafan malaman musulinci sukace a kashe duk mai yi. Banbancin mai tsafi da mai mu’ujiza ko karama shine, shi mai mu’ujiza ko mai karama an san shi da kyawawan xabi’u (ethics) kuma har lokacin da yake aikata mu’ujizar ko karamar bai dena aikata kyawawan xabi’u ba. Shi kuma mai tsafi an sanshi da munanan aiyuka da kuma aikata wasu abubuwan da ake ganin nutsattsen mutum ba zai aikata ba domin har kisa sunayi akan hanyar tsafinsu. Abin da yasa wasu daga masana tsafi suke yarda da Annabawa shine gane cewar hanyar tsafi daban da ta Annabta. Wannan shine yasa matsafa suka yarda da Annabi Musa saboda sun gane cewa hanyarsa daban da tasu. Abin da yasa ingantattun mu’ujizozin Annabi Muhammad (saw) ba su zamo tsafi ba saboda larabawa sun riga sun sanshi da kyawawan xabi’u har suka riqa kiransa da sunan Amintacce. Duba: Duba ta hanyar taurari shi ake kira da “Astrology” (da banbanci da “Astronomy” da take nufin kimiyyar taurari), shi kuma duba ta hanyar zanen kasa (ramli) shi ake kira da “Geomancy”. Wadannan ilimai, kamar na bayansu, suma suna da asali daga mutanen Hindu da asalin ilimin za a sameshi a cikin manyan litattafnsu kamar Veda, inda aka samo “Vedic astrology”, da kuma abubuwan da aka rawaito a litattafansu a yaren Sanskirt. Tun a zamanin Greek ana hade ilimin “Astronomy” da “Astrology” guri guda. Ptolemy a cikin littafinsa da yayi a ilimin falaqi (Astronomy) ya hada da bayanin “Astrology” da kuma yadda yake tafiya a fahimtarsa. Yana fadar cewa, wasu abubuwan suna faruwane daidai da yanayin tafiyar taurari da kuma tafiyar rana da watanni. Don haka idan aka san yadda taurari suke to za a iya gano yadda gaba za ta kasance. Ta haka zamu gane cewa ilimin taurari ya gangaro musulinci daga iliman Greeks ne. Ibn Khaldun a cikin Muqaddima, yana

cewa akwai bukatar asan cewa babu wani bincike na hakika da yake tabbatar da tafiyar taurari da kuma faruwar wasu lamura. Watakila wannan shine zai bamu nasarar da za ta iya nunamana ma’anar cewar Manzon Allah (saw) rana da wata basa kisfewa saboda mutuwar wani (ko rayuwarsa). Wato dai tafiyar falaqi bata nuna wani abu “supernatural” kamar na tsafi ko bokanci ko kuma faruwar wani abu anan gaba. Sir Issac Newton, kamar yadda aka rawaito a cikin littafin “Cambridge Companion to Newton”, ya bada labarin cewa ya tattauna da wani masanin ilimin taurari (Astrology) sai yake gayamasa hakikar ilimin ba gaskiya bane amma hanyar cin abincinsu ce! Masana halayyar xan adam (psychologists) sun tabbatar da cewa abin da yasa mutane suke aminta da gaskiyar ilimin taurari shine yadda suke ganin abu ya faru bayan an fadamusu zai faru. A hakikar lamari ba faruwa yake daidai da yadda aka gayamusu ba. Xan adam yana da saurin manta abubuwane, don haka idan mai ilimin taurari ya ce abu zai faru to mutum mantawa yake har sai wani lokaci can idan abu makamancin hakan ya faru to sai yayi zaton wanda aka taba gayamasa zai faru shine ya faru din. Misali, idan nace mahaifinka zai mutu bayan nayi duba, to mantawa zakai da na taba gayamaka har sai bayan ya mutu din, watakila da karin shekaru masu yawa, kawai sai ka tuno maganar sai kace ai dama na taba dubamaka hakan zai faru! Wannan shine abin da sukace game da yadda abubuwa suke faruwa a ilimin “Astrology”. Ilimin “Geomancy” shi ake kira da “ramli” ko kuma duba akan yashi (har da biro da takarda duk anayi). Ilimine da ya fita daga rubutaccen ilimin taurari (Astrology), don haka yake da sunaye da kuma salon bincike kusan iri daya da na ilimin taurarin kuma anfi kyautata zaton larabawa sune suka fara yinsa har ya watsu zuwa kasashen Africa da Europe. Shi ilimin ramli digo-digo a ke yi kusan kala 14 don a fitar da wasu abubuwa daga jikin digon. Wanda na koya ina shekara 13 yana aiki ne da zanen da ya fito bayan ka gama zanen da baka kirga ba kuma ka soke

Muqalar Talata +2349039128220 (Tes Kawai) biyu-biyu daga cikinsa. Idan 1 ta fito to za a aunata da daidai bukatarka, haka ma idan biyu ta fito. Akwai ababan mamaki a cikin ilimin da suke faruwa amma dai shima ana dorasune kamar yadda ake dora sauran iliman Astrology. Akwai ababan mamaki da suke faruwa a cikin irin wadannan iliman wadanda har yanzu kimiyya ta kasa gano ya hakikarsu take. Wasu abubuwan kamar “Telepathy”, “Entanglement”, “PSI” da sauransu har yanzu suna bawa masu kimiyya mamaki dukda suna dorasu a babin “Pseudosciences”. Yadda aka iya gano “Quantum entanglement” to ana zaton za a iya fahimtar wasu abubuwan irin wadannan da tafiyar lokaci. Zamanin amfani da “Classical Physics” na Newton da ya doru akan lissafin Euclid ya wuce. Yanzu muna kan “Quantum Mechanics” wanda karyata abu tafarar daya don dogaro da kimiyya (classical physics) na nuna raunin mutum a sanin kimiyyar. Ana bukatar bincike na sosai akan abu kafin a karyatashi. Yanzu muna kan “super string theory” wanda ya ce duniya tana da “10-dimensions” maimakon 3-dimensions ko 4-dimensions da Einstein ya kawo! Hankali zai rude bai gano hakikar abubuwa masu “10-dimensions” ba amma hakan baya nufin cewa “super string” karyane don kawai baka fahimci yadda yake ba. Abu Hamidil Gazhali, a cikin “Almunqidh” yana magana akan “secrets of numbers”, yana faxin cewa akwai abubuwan mamaki a cikin wasu lambobin. Ya bada hoton wasu lambobi da ya ce an kasa gane sirrinsu. Lambobine kawai a jere amma idan aka haskawa mai ciki a lokacin da take nakuda sai aga bata shan wahala sosai! Ibn Khaldun ya faxi wasu lafuza da yaren “Armenians” inda ya ce indai ya karantasu to sai ya yi mafarkin abin da yake so! Abubuwan da ban mamaki ta yadda ake bukatar ayi zurfaffen bincike akai. Irin wannan to dasu aka dora iliman “Numerology” da karanta zanen hannun mutum ko kirgen da a ke yi da carbi. Za mu ci gaba

Babba Da Jaka 2019:

Tsaro da tattalin arziki ne a gabana ba zave ba –Buhari

Baba Kenan...

Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 0703 6666 850; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 01-8963459. E-mel: leadershipayau@yahoo.com


Turn static files into dynamic content formats.

Create a flipbook
Issuu converts static files into: digital portfolios, online yearbooks, online catalogs, digital photo albums and more. Sign up and create your flipbook.