18.4.18
AyAU Laraba
LEADERSHIP
www.leadershipayau.com Leadership A Yau
Don Allah Da Kishin Qasa
18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA
LeadershipAyau
No: 126
N150
An Cafke Likitan Bogi Mai Amfani Da Takardar Firamare A Legas Daga Umar A Hunkuyi
shaidar kamala makarantar Firamare. Jami’an tsaro sun samu nasarar Dubun matashin wanda yake cafke wani likitan bogi, wanda ya basaja a matsayin likitan bogi ta xauki tsawon lokaci yana aiki ba cika ne a Birnin Legas. tare da mallakar wata takardar Wanda ake zargin mai suna, karatun likita ba. Bilhasali ma, Abdurrahman Mohammed, xan babbar takardar shaidar karatu shekaru 39, xan asalin qauyan da ya mallaka ita ce, takardar Ran, ne da ke Qaramar Hukumar
Gamboru, ta Jihar Borno. ‘Yan sanda ne suka kama shi a can Legas xin. Ranar 14 ga watan Afrilu 2018 ne aka kama shi, a cewar majiyar, wanda ake zargin,tun a shekarar 2014 ne yake aiki a matsayin cikakken likita a gida mai lamba 3, da ke titin Idi-Araba, Mushin.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Legas, Edgal Imohimi, da yake tabbatar da kamun da suka yi, ya bayyana cewa, wanda ake zargin ya amsa cewa, shi ba shi da wata takardar shaidar kammala karatu, face ta Firamare.
Dalilin Savani Tsakanin DSS, EFCC Da NIA –Monguno
>Ci gaba a shafi na 2
4
•Wani sashe na rundunar Sojoji ta musamman a xaya daga cikin jerin atisayen da suka gabatar cikin jerin Bita da aka shiryawa sojojin Afirka a barikin Runduna ta 176 dake Gwagwalada a Abuja
’Yan Bindiga Sun Sace ’Yan Gudun Hijira Sun Yi Xan Qasar Jamus A Kano Wa Gwamna Al-Makura Ihu > Shafi na 6 > Shafi na 4
2 LABARAI
A Yau
Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
An Cafke Likitan Bogi Mai Amfani Da Takardar Firamare A Legas Ci Gaba Daga Shafin Farko
Edgal, da yake gabatar da likitan bogin tare da sauran wasu masu laifin ranar Litinin a Shalkwatar rundunar, ya ce, wanda ake zargin, yakan yi wa marasa lafiya allura, ya gudanar masu da bincike, ya xauki Fitsari da jinainansu da nufin gudanar da bincike, kafin a kama shi. Ya qara da cewa, Mohammed yakan sayo kayayyakin maganin da yake wa marasa lafiyan da suka je wajen sa amfani da su ne, daga Kasuwar Idumota. A cewar Kwamishinan, shaidun da aka samu daga likitan qaryan, sun haxa da na’urar auna jini, ta hannu da mai aiki da kwamfuta, allurori, jakunkunan qarin ruwa, kaloli daban-daban da sauran su. Ya kuma shawarci al’umma da su riqa ziyartan cibiyoyin lafiya da aka amince da su ne a duk lokacin da bukatan hakan ta taso, Edgal ya ce, da zaran sun kammala bincike za su gabatar da mai laifin a Kotu, bisa tuhuman shigan burtu.
•Gwamnan Jihar Legas, Ambode
Matsalar Kuxin Giratuti Ta Kusa Zama Tarihi A Bauchi, Inji Ago Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
An bayyana cewar matsalar nan na masu bin gwamnati kuxaxen kammala aiki na giratuti da kuma masu amsar fansho ta kusa zama tahiri a jihar Bauchi domin gwamnatin jihar ta xauko hanyoyin gyara dukkanin matsalolin da suke jawo a samu matsalar rashin biyan fansho da giratuti a jihar. Alhaji Ibrahim Gambo Kobi xaya daga cikin jiga-jigai a jam’iyyar APC a jihar Bauchi shine ya bayyana hakan a hirarsa da wakilinmu a Bauchi. Ya qara da cewa, kawo yanzu gwamnatin jihar ta kammala dukkanin mai iyuwa domin ganin ta dakile dukkanin wata kafa da ka iya kawo a samu tsaiko ko cikas dangane da biyan ‘yan fansho kuxaxensu, sai ya nemi masu bin haqqin su qara haquri domin gwamnati ta samu kaiwa ga nasarar kammala bin hanyoyin da suka dace kan lamarin. Ibrahim Ago ya qara da cewa gwamnatin PDP takan nuna wariya da ‘yan ubanci wajen zavar waxanda za ta biyasu haqinsu amma APC ba ta sa hakan a cikin manufarta ba, “idan ka duba gwamnatin baya wacce ta shuxe, ai ita takan zavi waxanda da take sone sai ta biya musu kuxin fansho da giratuti, amma ita gwamnatin APC kama daga na jihar Bauchi da na tarayya ba ta zavar wani ta biyasa, wani
kuma ta hana sa, duk wanda yake da haqqinsa na giratuti yanzu haka gwamnatin jihar Bauchi ta yi kwamiti da zarar suka kammala aikinsu na tantance kowani mai bin giratuti zai amshi haqqinsa ba tare da nuna wariya ba,” In ji shi. Ya kuma bayyana cewar bayan da gwamnan jihar ya yi kwamitin tantancewa kan haqiqanan waxanda suke bin haqqin giratutu, shi kansa gwamnan bai da ra’ayin handame kuxaxen ‘yan giratuti sai dai yana son ya tantance haqiqanin waxanda suke da wannan hakkin. Ibrahim Ago ya qara da cewa “Dukkanin mai haqqi na fansho da giratuti walau wanda ya mutu ne ko wadda yake raye wannan gwamnatin a shirye take ta biyashi haqqinsa. Shi babban Akauta Janaral na jihar Bauchi, Alhaji Gambo Aliyu Maigamo da mataimakinsa tuni suka himmatu wajen ganin kowani mai amsar fansho da giratuti ya samu haqqinsa cikin sauqi ba tare da kai ruwa rana ba. kuma ina tabbatar wa kowani mutum cewar nan gaba kaxai haqqinsa zai fita domin APC ba ta da niyyar cutar wani,” In ji Ibrahim Ago. Ago ya bayyana cewar kowani tsohon ma’aikaci abu ne mai matuqar kyau da zarar ya kammala aikinsa na gwamnati ya samu haqqinsa a kan lokaci ba tare da tauye masa wani haqqi ba, amma kuma gwamnatin baya ta
nemi vata lamarin ta hanyar shigar da son rai da son zuciya wajen biyan kuxin giratuti ga tsoffin ma’aikata. Ya kara da cewa “Babu wani xan fansho a jihar Bauchi da ke bin bashin kuxin fansho sai giratuti, ita kuma giratutin nan dole ne sai gwamnati ta tantance cewar wane ya mutun?, da gaske ne ya mutun? kuma tun yaushe?, sannan kuma an tsaida albashinsa ko yaya, kasan wacan gwamnatin da suka shuxe ko ka mutu amma za ka samu ana ci gaba da fitar da albashinka kuma a rasa ta ina yake sulalewa. Don haka a aikin tantancewa da aka yi ne aka gano cewar akwai waxanda sun jima da mutuwa, don haka ina da yaqinin mai girma gwamna da haxin guiwar AG da mataimakainsa AAG Janbaki da kuma kwamitin da aka basu alhakin tantancewar nan nan gaba xayan kowani mai amsar giratuti da fansho kowa zai samu haqqinsa,” A cewar Shi Ibrahim Ago. Ya bayyana cewar dole ne masu amsar fansho da giratuti su baiwa gwamnatin jiha haxin kai wajen dakile masu sata da sunansu, domin a cewarshi ana matuqar tafka cuwa-cuwa a wannan sha’anin “ka sani ba za ka xauki kuxin mutum ka bashi baka yi binciken shin da gaske nasa xin ne ba. ka fa sani cewar an samu matsalar da wani mutum xaya ka samu na amsar kuxin mutum xari
•Ibrahim Ago
da sunan albashin mutane ne, alhali babu ma’aikatan. Domin ko a cikin ma’aikatan gwamnati akwai matsalar nan, da za ka ce kowani ma’aikaci ya zo wasu ba za ka gansu ba, domin daman babu su, kawai wani ko wasu ne ke amsar kuxi da sunan akwai wasu ma’aikata,” In ji sa. Ya kuma bayyana cewar masu fansho su qara haquri domin yanzu ba wai gwamnati na hangen masu gata ne domin ta biyasu giratutin su bane, ya bayyana cewar dole ne a biyasu haqinsu, abun
da ya dace kamar yadda ya shaida shine su xan qara haquri zuwa ga lokacin da za a kammala aikin tantance domin fara biyan wannan kuxaxen. Daga qarshe ya buqaci waxanda abun ya shafa a su haxa hanu da gwamnati waje guda domin a samu nasarar kammala dukkanin aiyukan da aka faro domin a samu nasarar biyan masu bin kuxin giratuti haqqinsu, ya kuma yi amanar cewar APC bata zo da niyyar danne wa wani haqqinsa ba.
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Ra’ayinmu
3
Ya Kamata A Rufe Gidajen Man Da Ke Kan Iyakokinmu
A
daidai lokacin da qarancin man Fetur ya addabi qasarnan da kuma fitintunun da hakan ya haifar, mutane kaxan ne suka yi qyashin muqamin Shugabancin kamfanin mai na qasa, NNPC, wanda aka baiwa, Dakta Maikanti Baru, duk kuwa da morewar da ake tunanin akwai ta a cikin wannan muqamin. ‘Yan Nijeriya fatan su ita ce, su sami hanya mai sauqi ta samun man na Fetur, don haka suke tsammanin wannan sabon shugaban da aka naxawa kamfanin man zai yi wata akara-dabara ne kawai, sai a ga komai ya yalwata. Don haka sai matsi ya yi yawa a kansa, kowa na jiran sa da ya fito ya yi bayanin inda matsalar take. Ba wanda yake sha’awar jin wahalar da kamfanin ke sha wajen ganin ya wadatar da man a cikin qasa. Milyoyin lita ne na man ake sayowa daga waje a kullum, amma duk da hakan wahalar man ake yi, mafi yawa ta hanyar zagon qasa, ga waxanda suke son tsiyata tattalin arzikinmu domin biyan bukatun kansu. A kodayaushe, kamfanin na mai qoqari yake na fahimtar da al’umma kan ainihin yadda matsalar take, kamar ta yadda wasu ke karkatar da man da kuma munanan ayyukan masu yin fasaqwarin man. Amma akwai matsala guda babba wacce take yin tarnaqi a kan qoqarin da kamfanin man ke yi na wadata qasa da albarkatun man na Fetur. Wannan matsala kuwa ita ce, ta yawaitan gidajen sayar da man na fetur a kan iyakokin qasarmu, wanda hakan ke qara taimakawa masu fasa qwarin man wajen karkatar da man namu zuwa qasashen maqwabta, da nufin samun riba mai gwavi. Wasu na iya cewa, ai gina gidajen man a kan iyakoki hanya ce ta kasuwanci wanda kuma kila a ce ba ta da wata matsala. Idan har da a ce, ana yin hakan da nufi ne na qwarai ba da manufar karya tattalin arzikinmu ba ta hanyar karkatar da albarkatun man namu zuwa qasashen maqwabta, to da sai mu ce lallai hakan ba laifi ne ba, hanya ce ta neman abinci. To tabbas, mafiya yawa ba hakan ne manufar su ba, suna gina su ne kawai da nufin yin fasaqwarin man zuwa qasashen qetare. Ma’anar fasaqwari shi ne, shigarwa ko shigowa da duk wani kaya zuwa cikin wata qasa a asirce kasantuwar qasar da ake shiga ko
fita da kayan ba ta halasta hakan ba, ko kuma ana yin hakan ne da nufin kaucewa biyan harajin da aka xorawa kayan. A dukkanin al’ummu na qwarai kamar Nijeriya, masu aikata hakan ana masu laqabi ne da munafukai masu laifin karya tattalin arzikin qasa. Waxanda ma suka fi su haxarin sune, waxanda a kan baiwa albarkatun man da nufin su kai su wurare na musamman, amma
sai su kauce su bi ta varauniyar hanya su karkatar da su zuwa iren waxannan gidajen man na kan iyakokinmu, daga nan kuma sai a fice da kayan wajen qasarnan. Suna cin haramtacciyar riba, kamfanin NNPC kuma na karvan zargi. Gaskiyan lamarin shine, kusan dukkanin iren waxannan gidajen man, duk ‘yan Nijeriya ne ke mallakan su. Abin haushin ma shi ne, ba wahalar su a wajen
EDITA Sulaiman Bala Idris
MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama
MATAIMAKIN EDITA Bello Hamza
DARAKTAN SASHE Mubarak Umar
RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah
BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John
manufarmu
LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!
samar da man nan na fetur da aka yi. Suna zaune, NNPC, na yi masu aiki. A kullum kamfanin na cikin shan suka da zargi, yana ta faxi tashin ganin ya fita kunya, amma su varayin na man, suna gefe suna ta dariyar su. Kullum suna kan hanyar zuwa Banki domin ajiyar maqudan kuxaxen da suka tara ta hanyar haram. Wannan shi ya sanya a namu fahimtar muke ganin jami’an tsaro su na da mahimmiyar rawar da za su taka a bisa qoqarin da kamfanin na NNPC ke yi na ganin ya wadata qasarmu da albarkatun man, ya kuma toshe waxancan hanyoyin da varayin man ke bi suna karkatar da man namu. Kamfanin yana yin aikin shi, wajen baiwa ‘yan kasuwa albarkatun man domin su sayarwa al’umma. Sai dai abin takaicin shi ne, da yawan ‘yan kasuwan suna cikin ‘yan ta’addan da ke sayarwa da gidajen man na kan iyakokinmu da man da ake ba su Kamfanin na NNPC, ya san ire-iren su, sai dai a irin wannan lokacin ba yanda shi a kan kansa zai iya yi da su. Cikin halin rashin kunya kuma, iren waxannan ma su aikata hakan ne za ka ji sun fito suna kururuwar sam su ba sa cikin masu aikata hakan. Su za ka ji su na kukan janye tallafi da kuma tsadan canjin dala da makamantan hakan, da nufin qara tsawwalawa kamfanin na NNPC, da kuma al’umman Nijeriya, domin biyan bukatan kansu. Mu a wannan jaridar muna ganin sam bai kamata a ce iren waxannan marasa imanin sun fi qarfin doka ba. Akwai bukatar da mu yi nu ni da cewa, mafiya yawan hanyoyin da ake bi wajen karkatar da albarkatun man namu, duk ta hanyar mota ne. Wanda hakan ke nufin za a iya lura da su, a kuma iya yin maganin su, mun tabbata jami’an tsaro da ke aiki da kamfanin na NNPC za su iya gano su tare da yin maganin su. Sai dai kuma idan akwai wani abin ne na daban, ko kuma akwai wasu bayanan da al’umma ba su sani ba, muna bayar da shawarar ya kamata gwamnati ta fara kulle ire-iren waxannan gidajen sayar da man na bogi da ke kan iyakokinmu. Muna ganin hakan zai taimaka wajen hana yawaitar fasaqwarin man namu da ake yi zuwa qasashen qetare. Wanda hakan zai sauqaqa mana wahalar man namu da kuma muke fama da ita.
4 LABARAI
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Dalilin Savani Tsakanin DSS, EFCC Da NIA –Monguno Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja
Mai ba shugaban qasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Jana4r Monguno (mai ritaya) ya bayyana cewa ba za a daina samun savani a tsakanin vangarorin tsaron qasar har sai ranar da aka fara aiki da dokar shekara ta 1986. Wannan bayani na Monguno yana qumshe ne a cikin rahoton Majalisa wanda ke binciken savanin da aka samu tsakanin EFCC, DSS da NIA a shekarar da ta gabata. Vangarorin tsaron sun samu savani a shekarar da ta gabata ne bayan da Hukumar EFCC ta yi yunqurin cafke Mista Ayodele Oke, wani tsohon Darakta Janar na NIA da kuma Mista Ita Ekpeyong, tsohon Daraktan DSS. A yayin da Mai ba shugaban qasa shawara kan harkokin tsaro ya ke nuna rashin jin daxinsa dangane da rashin jituwa a tsakanin waxannan vangarori, ya ce lamari ne da
ya kai a ke samun irin wannan savani a tsakaninsu a fili kuma kowa ke iya fahimta. “Ana ta samun irin wannan rashin fahimta ne saboda rashin yin aiki da dokar shekara ta 1986, mai lamba Cap 278 LFN, sashe na 14 01-2 wanda ya ba ofishin mai ba shugaban qasa shawara kan harkokin tsaro ikon sanya ido kan dukkan vangarorin tsaro. amma yanzun dukkansu an basu damar cin gashin kansu, suna iya ganin shugaban qasa a duk lokacin da suka so. Saboda haka akwai buqatar a daidaita waxannan hukumomi ta yadda za su riqa amsa umurni daga ofishin mai ba shugaban qasa shawara kan harkokin tsaro.” Monguno ya sanar da sanatocin cewa Shugaban qasa na sane da duk abubuwan da ke faruwa, ya kuma bayyana wa shugaban qasan irin naqasu da yake samu a ayyukansa saboda rashin xa’ar da hukumomin tsaron suke nuna wa ofishinsa.
•Monguno
Ya bayyana cewa, ba shi da wata masaniya dangane da yunqurin shugaban EFCC na son kama wani tsohon shugaban hukumar tsaro, sai bayan da jaridu suka wallafa
labaran biyo bayan turjiyar da vangarorin tsaron suka nuna. Majalisar dattawan wacce ke nazartar rahoton, qarqashin kwamitin da Sanata Francis Alimikhena ke jagoranta ta
fara yunqurin ganin ta zartas da dokar shekarar ta 1986, ta yadda Mai ba shugaban qasa shawara kan harkokin tsaro zai riqa sa ido kan ayyukan vangarorin tsaron.
Okorocha Ya Yi Alqawarin Kafa Makarantar Makafi Daga Bello Hamza
Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya bayyana shirinsa na kafa makaranta na musamman domin makafi da naqasassu a jihar domin taimaka musu samun rayuwa na gari. Gwamnan ya bayyana haka ne gidan gwamnati dake Oweri babban birnin jihar, a lokacin daya ke karvar qaramin Ministan harkokin Neja Delta Farfesa Claudius Daramola yayin day a isa jijar domin qaddamar da wasu a iyukan gwamnatin tarayya. Ya kuma anfani da wannan daman in day a yi kira ga gwamnatin tarraya ta hannu ma’aikatan Neja Delta da ta kamala aikin ginin cibiyar koyar da sana’o’i da aka shirya gina wa al’ummar
garuruwan dake samar da man fetur na jihar. A nashi jawabin, Ministan ya ce, yana jihar ne domin ya qaddamar da ma’aitan sarrafa kwakwan manya a qaramar hukumar Ikeduru na jihar, shirin na da nufin qara buqasa harkokin noma tare da samar da wasu hanyoyin samun kuxin shiga ga gwamnati da kauce wa dogaro ga harkar man fetur. Mista Daramola ya yaba wa gwamnan a bisa gudummawarsa na kawo ci gaba a jihar da qasa baki xaya. A wata sabuwa kuma, a lokacin daya ke jawabi ga bukin kammala aikin bautan qasa na “Batch A Stream 1” wanda aka gudanar a dandalin “Heroes Square” a garin Owerri, gwamnan ya buqaci ‘yan bautan qasar da
kada su dogara ga aiyukan gwamnati, maimakon haka su zama masu samar da aiki da kansu ta hanyar shiga sana’o’i. Gwamnan ya amince da bai wa kowanne xan bauta wa qasar N10, 000 su 1,542 waxan da suka kamamla aikin bautan qasar na su, sannan ya kuma bai wa wadda tayi fice a aikin bautan qasar na wanna shekarar Misis Umetawara Lorita Ebere N200,000, ya kuma amince da a bata aiki a dukk ma’aikatan da zavi tayin aiki in hart a buqaci zama a jihar, saboda wannan nasarar data samu. Ya ce, gwamnatinsa zata ci gaba gudanar da aiyukan dtaimakawa rayuwan jama’ar jihar har zuwa qarshen zamansa a matsayin gwamna.
•Rochas Okorocha
Babu Wanda Ya Fi Qarfin Dokokin Tuqi A Abuja, Inji FRSC Daga Bello Hamza
Humukar kiyaye haxurra “Federal Road Safety Corps” ta sanar da cewar, babu wani mahaluqi daya fi qarfin bin dokokin tuqi a babban birnin tarayyar qasar nan Abuja. Shugaban yanki FCT na hukumar, Mista Gora Wobin, ya sanar da haka da haka a yayin da yake tattaunawa da manema labarai, ya nuna xacin ransa, musamman ganin yadda manyan ma’aikatan gwamnati da ayarin motocin gwamnati ke karya dokokin
hanya ba tare da wani qaqqautawa ba. Wobin ya kuma lura cewar, ba kamar yadda wasu ke tunani ba masu hannu da shuni da aka fi sani da `Big men’ basu qarfin dokokin Nijeriya ba musamman dokokin tuqi na FRSC. “Babu wannan ya fi qarfin doka, in ka zo ofishinmu zaka ga motocin manyan mutane da muka kama suna karya doka, nasu qaramin qarfi irinmu ba zasu iya mallakar irin motocin ba” “Zaka amince dani da cewa,
duk wani dake kiran kansa “Big guy” ba shi da wani kariya in har ya aikata wani laifi a Abuja” “Muna kama su, a wasu lokttan ma muna qwace motocinsu musamman in laifin ya shafi rashin takardar izinin tuqi na (Lasisi) da karya wasu dokoki masu qarfi” “Babu abin daya dame mu da muqamin da kake riqe da shi” Jam’in hukumar FRSC xin ya kuma yi kira ga manyan mutane a cikin al’umma dasu yi amfani da muqaminsu
wajen tabbatar da bin doka da oda a kan hanyoyinmu. Wobin ya kuma qara da cewa, irin waxannan manyan mutanen ne ya kamata su zama masu da’awar bin doka da oda, ya kuma buqaci su shiga tsarin hukumar na “Special Marshal” domin bayar da tallafinsu na tabbatar da bin doka da oda a hanyoyinmu.. “A matsayin muqamin da kake riqe da shi ya kamata ka zama mai da’awar amfani da hanyar da kyau da kuma bin dokokin hanya a ko wanne
lokaci, ba masu karya doka ba” “Karya doka ba zai xaukaka sunanka ba maimakon haka ma zai vata sunan ka ne ya kuma zubar maka da mutunci” “Ya kamata manyan mutane su shiga tsarinmu na “special marshal” in har an samu irinsu a cikinmu suna sintiri mutane da yawa zasu shiga taitayinsu, irin abin da muke son gani kenan” “yan jarida sun lura da cewa, so da yawa ana ganin manyan ma’aikatan gwamnati da manyan jami’an tsaro suna karya dokokin hanya da tuqin ganganci a cikin garin Abuja.
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Ku kasance tare da tawagar OCTOPUS a shafin sadarwa na Telegram
TALLA 5
6 LABARAI
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
’Yan Bindiga Sun Sace Xan Qasar Jamus A Kano Daga Umar A Hunkuyi
A jiya ne aka sace, Injiniya Michael Cremza, ma’aikacin kamfanin gine-gine na ‘Xantata and Sawoe construction company.’ An kashe xan sandan da ke tare da shi lokacin da aka sace shi xin, in ji wani shaidan gani da ido. Shaidan ya bayyanawa wata kafar yaxa labarai ta Kano cewa, wasu ‘yan bindiga ne su uku da suka zo cikin motar VW Golf, suka harbe xan sandan da ke cikin motar domin baiwa Bajamushen kariya, daga bisani sai suka yi
awon gaba da Injiniyan. Wani jami’in tsaron da ke aikin tsaron kayan kamfanin mai suna, Abubakar Muhammad, ya shaidawa manema labarai cewa, lamarin ya faru ne ranar Litinin da safe, su na gab da fara ayyukan su na ranar. “Su na shigowa sai suka fara harbe-harbe ko-ta-ina, sai kuma suka harbi xan sandan kafin su sace Injiniyan. “Wani harsashin ma ya sami wani direban babbar motan da ke wajen,” in ji shi. Kakakin rundunar ‘yan sanda na Kano, Magaji Majiya, ya tabbatar da faruwar
lamarin. Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano, Rabi’u Yusuf, ya aike da wata qaqqarfar tawagar jami’an tsaro da kuma jami’an tsaro na farin kaya domin su killace sashen da abin ya faru, da nufin su kama waxanda suka aikata wannan xanyan aikin, su kuma kuvutar da Bajamushen. “Ana bukatar duk wanda yake da wani bayani mai amfani yana iya kai rahoton hakan ga Ofishin ‘yan sanda ma fi kusa da shi, ko a kira layukanmu na kota-kwana, 08032419754, 08123821575,” in ji Majiya.
•SP Magaji Majiya
’Yan Gudun Hijira 8,000 Sun Koma Gidajen Su A Bama –NEMA Daga Umar A Hunkuyi
Shugaban shiyyar Arewa maso Gabas na hukumar taimakon gaggawa ta, NEMA, Bashir Garga, ya ce, jimillan ‘yan gudun hijira 8000 ne suka koma gidajen su na gado a garin Bama. Bashir, ya faxi hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Maiduguri a qarshen makon nan, inda ya ce, kimanin magidanta 1200 ne suka dawo bayan shekaru uku suna zaman gudun hijirar. Ya ce, tun da farko sama da mutane 36,000, ne suka nu na aniyar su ta komawa gida,
amma sai hukumomin na SEMA da NEMA, suka ce sai dai su dawo rukuni-rukuni, domin su sami daman aikin tantance baragurbi a cikin su. “Ya zuwa yanzun, aqalla mutane 8000 ne suka koma gidajen na su, bisa qidayar mutane shida a kowane gida za mu iya cewa, magidanta 1200 kenan. In fayyace maku sosai, baya ga mutanan Bama da suka dawo, muna da wasu ‘yan gudun hijirar waxanda ba daga Qaramar Hukumar ta Bama suke ba, da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijirar. Ya kuma qaryata jita-jitar cewa, akwai wata kyauta ta
musamman da gwamnatin Jihar ke baiwa waxanda suka koma gidajen na su. “Muna sane da qoqarin da wasu ke yi na lalata wannan shirin na mu, sam wannan maganan ba gaskiya ce ba. Da farko yawan ‘yan gudun hijirar da suka nemi dawowa Bama su 36,000 ne. mun dawo da su ne bisa sharaxin nan na Majalisar xinkin Duniya na cewa, duk xan gudun hijirar da zaa mayar da shi gidansa tilas ne a tanadar masa da matsugunin da ya dace, ruwa da kuma kayan inganta lafiya gami da sauarn kayan bukatar sa na yau da kullum, duk kuma mun yi ma su hakanan xin.
Mai Talla Shi Ke Da Riba:
LEADERSHIP A YAU Ta Shirya Tsaf! Kamar yadda kowa ya sani ne, wannan jarida mai albarka, LEADERSHIP A YAU ta kafa tarihi wajen zama jaridar Hausa da ta fara fitowa a kullum. Wannan fara fitowa a kullum yana da alfanu masu yawan gaske, gare mu Kamfanin LEADERSHIP da ku masu karatu, musamman masu sana’o’i manya da qanana. Wannan ne ya sa muke farin cikin shaida wa masu karatunmu cewa mun shirya tsaf domin tallafa wa kasuwancinku, ta hanyar tallata maku shi zuwa inda ba ku zata ba. Domin a halin yanzu mu kanmu da muke buga wannan jarida ba za mu iya bayyana iya inda ta ke shiga ba. Muna da tsare-tasare da dama don talla ku da hajojinku, inda muka fitar da tsarin ‘IYA KUXINKA IYA SHAGALINKA.’ Wato akwai cikakken shafi, akwai rabi, akwai kwata, akwai kuma daidai iyaka abin da mutum ke so a sanya masa. Wanda a wannan shafin muna so masu sana’o’i, musamman manyan dillalai su tallata hajojinsu, su qananan ’yan kasuwa akwai
nasu tsarin. A wani tsarin ma da muke da shi, akwai yanayin da mutum zai tallata hajarsa, sannan ya tallata kansa, inda za a sanya hoton shagonsa, hotonsa da kuma taqaitaccen tarihinsa, kuma wannan duk a kuxi kaxan. Maza ku kasance cikin kashi na farko na masu cin moriyar wannan shiri. Ina ’yan Canji, dillalan yaduka, masu kayan masarufi, mayan da qananan ’yan tireda, dillalan magunguna, masu kamfoni da masana’antu, dillalan hatsi, dillalan mota, masu sayar finafinai da dai sauran masu sana’o’i, ga dama ta samu. A tuntuvemu a lambarmu ta 08148507210, 07036666850, 08039216372, 07037934034, 08032875238 da 08038011382: email leadershipayau@gmail.com. Ko kuma a tuntuvi wakilanmu na jihohi don qarin bayani.
LABARAI 7
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
’Yan Gudun Hijira Sun Yi Wa Gwamna Al-Makura Ihu Daga Zubairu T.M. Lawal, Lafia
Bayan kisan gillar da wasu da ake zargin ‘yan qabilar Tivi ne suka yi wa wasu Fulani goma a garin Yalwata dake Qaramar hukumar Guma ta Jihar Binuwai a makonnin biyu da suka gabata. Wannan kisan gillar ya tunzura qabilar Fulani yadda ake kai hare-hare kan mai uwa da wabi masamman ga ‘yan qabilar TV mazauna yankin Nasarawa da Binuwai. A baya bayan nan hareharen da ake kai wa ga qauyukan yan qabilar TV ya yi sanadiyar salwantar rayukan sama da mutum 40 a kauyuka daban-daban da kuma qona gidaje da asarar kayan abinci. Daga shekaran jiya zuwa jiya an qona kauyuka da dama kuma an yi asarar rayuka sama da mutum 20 yanzu haka akwai gawawakin wasu a babban Asibitin Dalhatu araf dake garin Lafia. Sanan ga wadanda suka tsira da munana raunuka dubam yan qabilar TV ne suka yi hijira suka bar gidajensu . Garuruwan da abin y afi shafa a yankin Nasarawa sun haxa daqauyukan Qaramar hukumar Keana da Qaramar hukumar Awe da Qaramar hukumar Obi Kuyuka da dama jama’a sun watse babu kowa saboda gudun ceton rai. A jiya ne Gwamna Umar Tanko Almakura ya ziyarci
•Gwamna Al-Makura a yayin ziyarar
sansanin yan gudun hijira da suke cikin jihar tare da kayayakin masarufi da kuma kwantar masu da hankali. Zuwan tawagar Gwamnan sansani na Farko a garin Agwatashi, inda dubban Jama’a maza da mata ke zaune a makarantar firamare. ’Yan gudun hijirar sun hana Gwamna yayi magana indan
waje ya kaure da ihu dalilin da ya sa Gwamna ya karvi abin magana domin janyo hankalinsu, amma ihu sai qaruwa ya ke yi daga bisani Gwamnan ya ce ko ku yi shiru ko na tafi, amma ina kamar an zuga su, Sai suka fara faxin ya tafi ba su buqata. Jama’ar sun yi ta faxin Gwamnati ta bar fulani
suna kashe su, su na qona dukiyarsu yanzu jama’ansu gawarsu na daji . Hakan ya sanya Gwamna ya kaxa tawagarsa ya qara gaba bai samu damar yin magana ba. Duk da ihu da suka yi bai ishe su ba sai da suka haxa da duwatsu, inda nan take Jami’an tsaro suka fara maida
martani ta hanyar watsa barkonon tsohuwa. Da yake zantawa da manema labarai Gwaman Umar Tanko Almakura ya ce; rikicin baya bayan nan ya samo asali ne a sanadiyyar kisan gillar da wasu mahara suka yi wa Fulani a garin Yalwata. Ya ce; yanzu haka an samu asarar rayuka na mutane da ya wa da varnar dukiya mai yawa. “Saboda haka ne muka kawo kayan agaji na gagawa domin taimakawa wadanda suka samu tsira suka rasa komai na su suka zo nan.” Gwamnan ya ce; Gwamnati za ta qara yawan Jami’an tsaro da za su shiga lungu da saqo domin samar da zaman Lafiya a guraren da wanan rikicin ya varke . Da yake amsa tambayar kan rashin yin magana a sansanin yan gudun hijira? Sai Gwamnan ya ce;”nasan suna cikin halin damuwa duk wanda ya shiga irin wanan damuwar dole hankalinshi ya tashi. Ya kara da cewa basu hanani yin maganaba naga cewa idan nace zamu tsaya har a samu nutsuwa a wajen to zamu bata lokaci shiyasa nace mutafi . Amma akwai kayan agaji da muka kawo kuma zamu rabamuasu “. Daga bisani Gwamnan ya ci gaba da zagaya sansanin yan gudun hijirar da suke sauran wurare.
Za A Fuskanci Gaggarumin Yajin Aiki A Sashin Lafiya Na Nijeriya Daga Bello Hamza
Haxaxxiyar qungiyar qwadago na asibitocin Nijeriya “The Joint Health Sector Unions, JOHESU”, sun sanar da tsunduma yajin aikin sai baba ya gani, sun ce yajin aikin zai tsayar da komai a dukkan aibitocin qasar nan baki xaya. “Dukkan asibitoci da cibiyoyin samar da harkokin lafiya a faxin tarayyar Nijeriya zasu tsayar da aiyukansu, in har gwamnati ta bari yajin aikin ya shiga sati biyu ana yi kuwa to dukkan sauran cibiyoyin samar da kiwon lafiya na jihohi dana qananan hukumomi suma zasu shiga yajin aikin” kamar yadda mataimakin shugaban qungiyar ta qasa JOHESU, Ogbonna Chimela, ya shaida wa manema labarai ranar Litinin. “Yan qungiyar ta JOHESU sun haxa da dukkan ma’aikatan asibitocin qasar nan haxe da “Nurses da Pharmacists” amma banda likitoci da likitoci masu kula da haqori (Dentists). Mista Chimela ya kuma ce,
yajin aikin zai fara ne daga qarfe 12 na daren Talata mai zuwa. A watan Satumba ne qungiyar ta JOHESU ta shiga yajin aiki saboda dalilan da suka haxa da rashin qarin albashi da bashin kuxaxen hutu da suke bi da kuma buqatar kyautata yanayin gudanar da aiyukansu. An ruwaito cewa, a jajin aikin da suka yi a watan Satumba, asibitoci sun rinqa gaggauta sallamar marasa lafiya, hakan kuwa ya qara tsananin rashin lafiyar mutane da yawa, yajin aikin na da kwanaki 9 ne gwamnati ta shawo kan jagororin qungiyar in da suka janye yajin aikin, amma yanzu •Ministan Lafiya, Farfesa Isaac watanni 6 ne kenan har yanzu gobe, amma har zuwa yanzu gwamnati bata cika alkawarin gwamnati bata yi wani katavus na warware rikicin ba” data xauka ba ko xaya. “Sun kiramu ranar 5 ga A kan haka ne qungiyar ta ba gwamnati wa’adin kwanakin watan Afrilu, in da suka aiki 21 daga nan kuma suka bayyana mana cewa, suna qara bayar da wa’adin kwana nan suna duba buqatunmu amma ba tare da bayyana 30. “Kafin yanzu mun ba mana yadda zasu biya mana gwamnati wa’adin kwanaki buqatun ba, saboda hake ne 21, a watan jiya kuma muka shugabanin qungiyar mu qara bada wa’adin kwanaki “National Executive Council 30 wanda shi ne zai qare (NEC)” suka haxu a Abuja in
da aka yi nazarin halin da ake ciki aka kuma yanke shawarar ci gaba da yajin aikin ba tare da gudu ko ja da baya ba” inji shi. Ya qara da cewa, a yarjejeniya da suka yi gwamnatin tarayya a watan Satumba na shekarar 2017, gwamati ta yi alkawarin biya wa qungiyar buqatun ta a cikin mako 5. “Wannan mako 5 xin ne ya koma wata 6 ga shi har yanzu
yana ta tafiya babu ranar cika alkawarin” Ya kuma yi bayanin irin halin da marasa lafiya zasu shiga ciki in har aka ci gaba da yajin aikin. “Muna da sanin cewa, masu qaramin qarfi zasu shiga halin qunci in an ci gaba da yajin aikin nan, hakan ya sa muka bai wa gwamnati cikakken wa’adin daya kamata tayi wani abu amma shiru kake ji, amma daga dukkan alamu abin da gwamnati ke mutuntawa shi ne yajin aiki” “Dokan qwadago ya samar da cewa, in har gwamnati ta qi sauraron buqatunmu muna iya janye aiyukanmu ta hanyar yajin aiki, kuma duk mun bi wani hanyar daya kamata kafin cimma wannan shawarar yajin aikin” Da aka tuntuvi Ministan lafiya Mista Isaac Adewole, ya ce gwamnati na qoqarin ganin an kauce wa yajin aikin da qungiyoyin qwadago ke shirin faxawa. “Muna tuntuvar qungiyar qwadago domin ganin an kauce wa shiga yajin aikin tare da biya musu dukkan buqatunsu” inji shi.
8 TALLA
A Yau
Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku
Ba a chaj a cire k in kuxin n o d i j a h c Ba a saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku
Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.
Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
TALLA 9
Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”
Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.
10 LABARAI
A Yau
Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
•Wani sashe na rundunar Sojoji ta musamman a xaya daga cikin jerin atisayen da suka gabatar cikin jerin Bita da aka shiryawa sojojin Afirka a barikin Runduna ta 176 dake Gwagwalada a Abuja
Yadda Ministan Jonathan Da Wasu Mutum Biyu Suka Fitar Da Naira Miliyan 450 Daga Umar A Hunkuyi
Wani shaidan mai gabatar da qara, Annette Gyen, ya shaida wa Babban Kotun Tarayya ta Jos, a ranar Litinin yanda tsohon Ministan albarkatun ruwa, Sarah Ochekpe, da kuma wasu mutum biyu suka fitar da tsabar kuxi Naira miliyan 450, daga Bankin Fidelity. Uwargida Ochekpe, da mutanan biyu, Raymond Dabo, tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Flatau, da Leo Jatau, Shugaban kwamitin yaqin neman zaven shugaba Jonathan a Jihar ta Flatau, hukumar EFCC, ce ta gurfanar da su gaban Kotun inda take tuhumar su da karvan Naira milyan 450 daga hannun tsohuwar Ministan Mai, Diezani Alison-Madueke, a 2015. Hukumar hukunta masu yi wa tattalin arzikin qasan zagon qasa, tana zargin mutanan uku ne da karvan Naira milyan 450 daga hannun wata mai suna, Annette Olije-Gyen, jami’ar ayyuka na Bankin Fidelity, wanda hakan ya zarta adadin da doka ta amince da a iya xauka. Hukumar ta EFCC, kuma ta yi zargin laifin da suka aikata ya savawa sashe na,
18 (a) (d), 1 (a), 16 (1) (d), an kuma tanadi hukuncin wanda ya aikata hakan a sashe na 16, (2), wanda ya haramta cuwa-cuwan kuxaxe. Gyen, a shaidar da ta bayar, ta shaidawa Kotun Shugaban ta ne, Martins Ezuogbe, ya umurci mai biyan kuxi aBankin da ya biya mutane ukun kuxaxen. “A ranar 26 ga watan Maris 2015 ne, muka kirayi mutanan uku da suka zo Ofishin namu, muka ba su kuxin. “Bayan sun qirga
kuxin ne, sai muka ba su motarmu ta xaukan kuxi domin ta yi masu rakiya,” Ta ce, sai ga shi a ranar 8 ga watan Janairu 2017, sun sami takarda daga EFCC, tana tambayar bayani kan kuxaxen. “Mun kuma ba su amsa a rubuce ranar 11 ga watan na Janairu.” Mai gabatar da qaran, Ahmed Munchaka, ya bukaci da a gabatar da wasiqun biyu a matsayin shaida, amma sai lauyoyin da ke kare waxanda ake qara suka ce sam ba su yarda ba.
Ofishin lauyoyi na, Messrs Gyang Zi da S.O. Oyewale, wanda su ne lauyoyin Messrs Ochekpe, Jatau da Dabo, sun yi jayayyan cewa, ba za a iya gabatar da wasiqun biyu ba, saboda ba asalin waxanda aka rubuta xin ne ba. “Kamata ya yi Bankin ya gabatar da asalin wasiqun, domin bai yiwuwa Kotu ta yi amfani da waxanda aka kwafa, domin kila an jirkita su daga na asalin. Na asalin ne kaxai za mu iya yarda da su,” in ji Lauyoyin.
Mista Munchika, ya dai dage kan a karvi wasiqun tun da duk sassan biyu da suka rubuta su sun amince da su xin. Ya qara da cewa, ya kamata a amshi wasiqun saboda su na da mahimmanci a kan bayar da shaidan.” Bayan sauraron sassan biyu, Alqalin Kotun, Musa Kurya, sai ya xaga sauraron qarar zuwa ranar 17 da 18 ga watan Mayu domin ya yi hukunci kan ko Kotun za ta karvi wasiqun, a kuma ci gaba da sauraron shari’ar.
Kashi 51 Na ’Yan Nijeriya na Kwana Da Yunwa, Inji Binciken Masana Daga Khalid Idris Doya, Abuja
idan ba su da lafiya. A yayin da kashi 47 kawai Gidauniyar CLEEN tare da haxin guiwar PSI suke iya amfani da abin wato ‘Practical Sampling girki dake mai amfani da International’ a makon jiya man Kalanzir ko iskar gas ne su ka fitar da rahoto wajen yin girki. Kuma kashi cewar ‘yan Nijeriya kashi 51 41 ne kawai suke samun cikin xari na ‘yan Nijeriya wadataccen ruwa. Rahoton ya tabbatar ne a cikin shekarar 2017 da cewa; kashi 77 na ‘yan suke kwanciyar bacci da Nijeriya ba sa samun abin yunwa a tattare da su. Sun ce kashi xaya cikin da zai wadace su. Wakilin PSI, Moses kashi uku na ‘yan Nijeriya Olusola ya yi qarin haske ba su iya gudanar da rayuwarsu yadda ya kamata. da cewa; rahoton na su ya Rahoton ya ci gaba da yi la’akari da ra’ayoyin ‘yan cewa; kashi 51 suna kwana Nijeriya waxanda suke fama ba tare da samun isasshen da waxannan matsaloli. abinci ba. inda kuma kashi Ya ce; da yawansu koma 48 ne kawai cikin ‘yan dukkansu suna matuqar Nijeriya suke samun kula fama da matsaloli daban-
daban. Ya ce; sun tuntuvi hukumar qididdiga ta qasa wato NPC kafin binciken na su. Ya ce; sun samu waxannan bayanan ne ta hanyar amfani da hanyoyin
zamani. Ya tabbatar da cewa; sun karvi bayanai 1600 dangane da wannan binciken na su duk da matsalolin kuxi da suka samu wajen wannan binciken.
LABARAI 11
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
NAFET Za Ta Inganta Harkar Malamai Mata Masu Koyar Wa A Makarantu Daga Mstapha Ibrahim Kano
Qungiyar Malamai Mata masu koyarwa a Makarantu ta Qasa wato NAFET qarqashin shugaban Qungiyar ta Qasa Dr. Asuru Chikanele tasha alwashin haxa kai da inganta Rayuwar Mata Malamai a qasan nan kamar yadda Malamai Mata suke buqata a Qasan nan. Dr. Asuru Chikanele ta bayyana hakan ne a lokaci wata ziyara da shugabar ta kawo Kano wanda Makarantar Nazarin Shari’a da Larabci da ke qarqashin Farfesa Garba Shehu ta karvi bakuncin wannan qungiya ta NAFET wanda kuma ya samu wakilcin jigo a wannan qungiya Dr. Atika Bala Mai Yafe Malama kuma shugabar sashin Nazarin Harsuna a Makarantar Ligal da ke Kano ta jagoranci kavar bakuncin wannan Qungiya ta qasa a Kano Dr. Chika tace ankafa wannan Qungiya ne domin daqile matsalolin da Mata Malamai suke fuskanta a Makarantu domin a wayar da kansu kuma a Ilmartar da su na irin rawar da zasu taka domin a samu cigaban Ilimin Mata a Qasan nan kuma Qungiyar ta dukkanin Malamai Mata ne da suke Koyarwa a Makarantu kuma a wanna mataki na koyarwa tun daga kan Malamai Mata na Firamare har zuwa Malamai da ke Jami’oi da manyan Makarantu na Qasan nan. Ita kuwa Dr. Atika Bala Mai Yafe ita ce qirjin Biki kuma mai masauki a wannan ziyara da Qungiyar ta kawo ta bayyana cewa suna samun goyan baya daga Gwamnatin Jahar Kano qarqashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma Ma’aikatar Ilimi qarqashin mataimakin Gwamna kuma Kwamishinan Ilimi na Kano Farfesa Hafizu Abubakar inda kuma ta yabawa shugaban Makarantar Ligal Farfesa Garba Shehu akan irin qarfafa gwiwar qugiyoyin Mata dana sauran Al’umma masu qoqarin cigaban Al’umma koyaushe. Ita ma Hajiya Aisha Muhammad Sani Babbar Jami’ar tsare tsare ta NAFET ta bayyana mahimmancin wannan qungiya a cigaban ilimin Mata.
Kotu Ta Yanke Wa Xan Shekaru 40 Hukunci Shekara Xaya A Kurkuku A Kebbi Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi
Kotun majastare ta uku da ke zaman ta a Birninkebbi a jiya ta yanke wa wani mutun mai suna Sani Abdullahi xan shekaru 40 da haihuwa a duniya wanda xan garin Toranka a qarqashin qaramar hukumar mulkin Kware a jihar sakkwato. Mai laifin dai an gabatar da shine a jiya daga rundunar ‘yan sandan jihar ta kebbi suka gurfanar da laifin haxin kai wanda ya savawa sashe na 97 na dokokin Shari’a da kuma laifin sata wanda ya savawa sashe na 288 na dokokin Shari’a a gaban mai Shari’a Halima Ibrahim da ke kotun majastare ta uku a Birnin-kebbi a cikin Shari’a mai lamba BK/111c/ 2018 . Mai gabatar da qarar a gaban kotu a madadin rundunar ‘yan sanda, insifeto Isah Muhammad ya gayawa kotu cewa mai laifin Sani Abdullahi yana gaban kotu ne kan aikata laifin haxin kai da kuma laifin sata wanda laifin biyu sun savawa sashe na 97 da kuma na 288 na
dokokin Shari’a na qasa. Saboda haka ya ke neman kotu data yanke masa hukunci bisa ga laifin biyu da ake qalubalantar sa dashi a gaban wanda kotu. Har ilayau insifeto Isah Muhammad ya ce “ wannan mai laifin jami’an ‘yan sanda sun kamashi ne a ranar lahadi takwas ga watan afirilu na shekara ta 2018 a garin fakon Sarki da ke cikin qaramar hukumar mulki ta Augie a jihar ta kebbi inda ya sace kayan na’ura mai aiki da hasken rana watau “ kayan solar power “ na malakar kamfanin MTN da garin na fakon Sarki a qarqashin qaramar hukumar mulki ta Augie a jihar Kebbi. Hakazalika kotu ta bada dama ga mai laifin da aka gabatar a gabanta domin kariyar kansa bisa ga abin da ake tuhumarsa da aikatawa. Mai laifin Sani Abdullahi ya ce” bani da wata kariya da zana gabatar a gaban wannan kotu”. “ Na amince da abin da ake tuhumata dashi a gaban wannan kotun”. Bugu da kari kotu tace tunda harya amince da
•Wanda aka yankewa hukuncin
abin da aikata laifin da ake tuhumarsa dashi zata zartar masa da hukunci bisa ga shedar da ke a gabanta. A hukuncin da kotu tayi tace ta kamashi da laifi guda biyu, Laifi na farko shine laifin haxin Kai domin aikata laifin sata wanda ya savawa sashe na 97 na dokokin Shari’a na qasa saboda haka kotu ta yanke masa hukuncin
wata uku a gidan kurkuku batare wata tara ba. Hakazalika laifi na biyu ta kamashi da laifin aikata sata wanda ta yanke masa hukuncin xaurin wata uku ba tare da biyan wata tara ba. Haka kuma ta yi umurnin da cewa ya biya diyar kayan da ya sace na Naira dubu dari da sittin 160,000.00 ko wata shida da kuma mako biyu a gidan kurkuku.
’Yan Bindiga Daxi Sun Bindige Wani Jigon Jam’iyyarAPC A Edo Daga A.A.Masagala, Benin
Wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su waye ba sun harbi wani Babban jigo na jamiyyar A.P..C.mai mulki a jihar Edo mai suna Mista Samson Sedi a qaramar hukumar Etsako ta gabas. Wannan lamarin ya farune aqarshen makon jiya.kuma Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Johnson Kokuma ya tabbatar da faruwar hakan inda ya ce mamacin ya cika ne bayan an garzaya dashi zuwa asibiti. Daga nan kuma sai Musta Kokuma ya jaddada batun xaukan matakan tsaro inda ya ce tuni jami’ansa suka
duqufa wajen ganin sun zaqulo waxannan da suka yi wa wannan Xan siyasan kisar gilla . Don haka ya nemi haxin kan alumman yakin tare da bayanan sirri domin gano miyago mutane a cikin alumma. Wani Labari kuma mai kama da hakan a jihar Imo wani jama’in Xan sanda a jihar ya xirkawa yaron mota dalma ya kasheshi har lahira saboda haka tuni hukumar ‘yan sanda ajihar ta bada labarin ce wa ta sallami mai laifin daga bakin aiki mai suna Abu Itam bisa wannan zargin na kisan kai da ya aikata na yaron motan mai shekara ashirin (20) a
Duniya mai suna Ifeanyi Akafor . Kuma kamar yadda rahoton yayi bayani wannan lamarin ya faru ne a ranar 9 ga watan febrairu na wannan shekara ta 2018 da muke ciki da misalin qarfe 5:00 na safiya daura da cibiyar hukumar ‘yan sanda na Okwelle a qaramar hukumar Onuimo cikin jihar. Wanda faruwar lamarin ya sanya tafasar tukwanyar matasa a yankin har ya kai suka xauki doka ahannunsu kamar yadda jaridar punch ta ruwaito domin matasan sun nun ace wa rashin adalcine ya sanya yaron motan ya
qalu balanci jami’in Xansandan sai kwatsam ya buxe wa yaron motan wuta ya harbeshi har sau uku ya kasheshi daga nan kuma sai ya ranta ata kare. Su kuma matasan yankin ganin abinda wannan jami’in Xan sanda ya aikata suka gaza su yi haquri sai suka cinnawa ofishin yan sandan dake Okwelle wuta ko da yake an ce wutar ba ta yi ta’adin a zo a gani ba. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Chris Ezikel ya tabbatar da faruwan lamarin don haka ya ce tuni har an xauki matakin gurfanar da mai laifin a gaban kotu.
12 LABARAI
A Yau
Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Ba Rabuwar Kai Bane Ya Sa Aka Gudanar Da Maulidin Nyass A Wurare Biyu –Sherrif Bolari Daga El-Mansur Abubakar Gombe
Shugaban kungiyar Masu Yabon Manzon Allah SAW mai suna Ushaqul Nabiyi Aazam ta kasa Sherrif Auwal Sadiq Bolari, shi ne ya bayyana hakan a Gombe a lokacin da yake zantawa da Leadership A Yau Litinin kan yadda aka gudanar da Mauludin Nyass karo na 33 a garuruwan Kaduna da Abuja inda ya ce kar mutane su dauka rabuwar kai ne ya sa hakan ci gaba aka samu. Auwal Sadiq Bolari, ya godewa Allah kan yadda wannan Maulidi ya gudana aka kuma gama lami lafiya a Kaduna da Abuja ba tare da an samu kowacce irin matsala ba da wasu suke ganin kamar matsala ce ta janyo hakan ko rarrabuwar kai to su ajiye Allah ne ya shirya hakan domin da an gudanar da Maulidin a waje daya a Kaduna ko a Abuja yawan mutanen zai
iya kawo rasa rai saboda cunkoso. Ya ce idan a Kaduna kake sai ka dauka a iya kaduna kadai ake yi ba’a yi a Abuja haka idan a Abuja kake sai ka dauka a iya Abuja kadai ake yi saboda yawan jama’a hakan yana nunawa duniya bunkasa ce irin ta addinin Musulunci da kuma faila ta Sheik Ibrahim Nyass R.A. Shugaban kungiyar ta Ushaqul Nabiyi ya kara da cewa duka taron biyu na Kaduna da Abuja Jikokin sheik Ibrahim da ake wannan Maulidi dan Kakansu sun halarci wuraren biyu tare da manya-manyan Shehinan darikar Tijjaniya. Ya kuma yi kira ga al’ummar duniya da cewa duk wanda yake ganin wannan taron Maulidai biyu kamar rarrabuwar kai ne ko wata matsala ce to yaji kunya domin su kansu a hade ake basu rabu ba kuma ba za su rabu ba
saboda kullum a waje daya suke haduwa suke yin sallah suyi wazifa ba tare da nuna wata wariya ba. Kasancewar sa shugaban kungiyar Ushaqul Nabiyi Aazam wacce kungiya ce ta masu yabon manzon Allah ya ce su a waken su basa habaici ko cin mutuncin wani su suna wake ne na yabon fiyayyen halita kuma duk wani mai fakewa da sunan mawakin manzon Allah yana batanci ga wasu to shi da Annabi a ranar lahira ba ruwan su. A cewar sa duk wani mawakin Manzon Allah SAW ba ruwan sa da yin habaici ko shagube ga wani kamar yadda shugaban su kuma shugaban kungiyar Shu’arawu ta kasa sheik Sherif Rabi’u Usman Baba ya koyar da su dan haka duk wanda zai yabi Manzon Allah SAW ya zama ya tsarkake zuciyar sa dan yasan me zai gayawa Manzon Allah. Sheriff Auwal Sadiq
•Sherrif Auwal Sadiq Bolari
Bolari, ya ce cikin irin aikace-aikacen wannan kungiya ta su ta Ushaqul Nabiyi Aazam, bayan yabon Manzon Allah da suke yi suna fadakarwa kan muhimmancin zaman lafiya kamar yadda suke yi a cikin waken su daban daban wajen jawo hankalin al’umma da a zauna lafiya da juna.
Daga nan sai ya ja hankalin irin Matasan nan da suke sanya tsofaffin kaya a lokutan Maulidi dan fakewa da sunan yan Maulidi suna sabawa al’ummar Musulmi da tozarci ga Annabin rahama alaihissalam dan haka su tuba ko kuma su shirya gamuwar su ga Allah a ranar lahira.
Shehi Ya Yi Kira Ga Matasa Su Dage Wa Neman Ilimi Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An yi kira ga matasa akan su dage wajen qoqarin neman ilimi sannan kuma su kaucewa xabi’un ta’ammali da miyagun kwayoyi dake jawo cutarwa ga rayuwarsu. Shugaban qaramar hukumar Fagge Alhaji Ibrahim Muhammad Shehi yayi wannan kiran da yake jawabi a wajen bukin yaye xalibai da suka sami hora akan kawo xaukin farko da
•Alhaji Ibrahim Muhammad Shehi
Sak Ba Za Ta Yi Wu Ba A 2019 –Global Daga Balarabe Abbdullahi, Zariya
An shawarci xaukacin ‘yan siyasa a sassan Nijeriya, das u yi taka tsantsan na nau’in mutanen da za su zava a zaven shekara ta 2019, su kuma batun Sak da suka yi a zaven da suka gabata. Tsohon xan majalisar wakilai day a wakilci al’ummar qaramar hukumar Zariya har sau uku a wannan majalisa da aka ambata,
Alhaji Abdulqadir Shehu Usman ‘GLOBAL’ ya bayar da shawarar a zantawarsa da LEADERSHIP A Yau a Zariya. Alhaji Shehu Usman Global ya ci gaba da cewar, babbar matsalar da ke faruwa a siyasar da ake ciki shi ne, na yadda al’umma idonsu ke rufewa, domin son abin duniya, su zavi wanda ked a kuxi ba mai mutunci ba. A tsokacin da Alhaji Shehu
Usman ya yi kan furucin da shugaban qasa ya yi na cewar zai yi takarar shugaban qasa a shekara ta 2019, sai fitaccen xan siyasar ya ce,tsarin mulkin Nijeriya ya ba shugaban qasa dammar yin takara a zave har sau biyu, in har ya na kan mulki. Sai dai Global ya ce zave da za a na qanananan hukumomi a jihar Kaduna da kuma na qasa ba ki xaya , ya ce wajibi ne al’umma su haxa
aka gudanar a xakin taro na masallacin Juma’a na qofar mata. Shehi wanda yana daga cikin waxanda aka karrama da lambar yabo a yayin taron ya qara da jan hankalin matasa akan su kaucewa shiga bangar siyasa da duk wata xabi’a mara kyau da za ta kawo cutuwa ga al’umma da tauye musu ci gaban rayuwa. Alhaji Ibrahim Muhammad Shehi Kwaciri ya jaddada buqatar
iyaye su kulada tarbiyar ya’yansu musamman ma ya’ya mata domin su zama masu anfani a cikin al’umma. Shehi ya yabawa Makarantar da ta gudanar da horo ga matasa da kuma fatan za su yi amfani da abin da suka samu horo a kai don hidimtawa al’umma ya kuma bayyana farin cikinsa bisa karramawarda akayi masa da cewa hakan zai daxa zaburar da qwazonsa wajen ci gaban al’umma.
kansu dumin samun nasarar ake buqta, na zaven mutane nagari da za su warware wa al’umma matsalolin da suke ciki. Ya kuma nunar da cewar, babu batun yin sak a zave mai zuwa, kamar yadda Alhaji Abdulqadir ya ce,ko da Shugaban qasa Muhammadu Buhari ya furta wa ‘yan Nijeriya cewar su yi sak babu wanda zai yi, domin an yi sak xin babu makoma nagari da
al’ummar Nijeriya suka samu sai matsaloli ma su yawan gaske suka tsinci kansu. Sauran matsalolin da suka zama wa ‘yan Nijeriya gagara badau shi ne na yadda wasu da ba su cancanci zama shugabanni ko kuma wakilan jama’a ba, sai illar bin inuwar Buhari kafin zaven shekara ta 2015, suka shiga wannan inuwarsa suka kai ga nasara, suka kuma zama matsala ga al’ummar Nijeriya.
LABARAI 13
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Mun Tara Sama Da Miliyan 100 A Adamawa –Kwastan Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola
Hukumar hana fasa kwaurin kayayyaki ta qasa Nigeria Customs Service (NCS), reshen jihohin Adamawa da Taraba, ta sanar da tara kuxaxen shiga kimanin naira miliyan xari da huxu da dubu xari huxu da arba’in da shida da xari bakwai (N104,446,746.40) cikin shekara guda. Shugaban hukumar mai barin gado, Mista Adetoye Francis, ya bayyana haka a Yola, lokacin da yake miqa ragamar shugabancin hukumar ga Mista Kamaluddeen Olumoh, yace hukumar ta rage yawan fasa kwaren kayayyaki a yankin jihohin biyu. Farancis ya ci gaba da cewa kashe sittin da tara bisa xari na kayayyakin an biya musu kuxaxen shege na kimanin naira miliyan 124,513,527.70, haxi da buhunan shinkafa hamsin
‘yar waje da kwanjon kayan sawa, da hauren Giwaye, man fetur, magunguna, motoci da dai sauransu. Yace mafiyawan kuxaxen shigar da hukumar ta tara sun samu ne ta hanyar kanayan amfanin Gona, kamar borkono, zuma, auduga, waken soya, irin shuki da sauran kayayyakin. Shugaban hukumar Kwastan mai barin gado a jihar Adetoye Farancis, ya yaba da haxinkan da yace gwamnatocin jihohin Adamawa da Taraba suka bashi, sai ya buqaci da su ci gaba da baiwa hukumar irin wannan goyon bayan. Da yake maida kalami sabon shugaban riqon hukumar Kwastan a jihohin Adamawa da Taraba Mista Kamaluddeen Olumoh, roqi jami’an hukumar da su haxa hanu su yi aiki tare domin cimma nasara a qasar baki xaya.
2019: Festus Keyamo Ya Zama Jami’in Wasta Labaran Yaqin Neman Zaven Buhari Daga Bello Hamza
Shugaba Muhammadu Buhari ya naxa shahararren lauyan nan Festus Keyamo a matsayin shugaban sashin watsa labarai da tsare tsare na ofishin yaqin neman zavensa a zaven gama gari na shekara 2019. Sanarwar naxa Festus Keyamo ya fito ne ta wani wasiqa da aka rubuta ranar 16 ga watan Afril tare da sa hannu Rotimi
Amaechi, Ministan Sifiri kuma shugaban qungiyar yaqin neman zaven shugaba Buhari ta “Buhari Campaign Organisation”. Shugaba Buhari ya sanar a makon jiya cewar, lallai zai sake tsayawa kakarar kujerar shugabanci qasar nan kafin ya nufi qasar Landan. Labarin wannnan naxin ya zo ne kwana xaya bayan da shugaba Buhari ya sanar da Piraministan Ingila Theresa May cewar, shi harkar
mulkin ‘yan Nijeriya ke a gaban sa ba maganan yaqin neman zaven shekarar 2019 ba. Mista Keyamo babban lauyan Nijeriya ne “Senior Advocate of Nigeria” yana kuma cikin masu fafutukan kare haqqin bil adama da yi tsaye wajen goyon bayan gwamnatin Buhari tun daga shekara 2015, ana kuma sa ran zai fitar da sanarwa karvar wannan sabon aiki nasa nan bada daxewa ba.
•Festus Keyamo
An Zavi Sabon Shugaban Qungiyar Abokan Asibiti A Kano Daga Mustapha Ibrahim, Kano
Qungiyar Abokan Asibiti Da Ke Kula da dangantaka da ma’aikatan asibiti da kuma masu da kuma masu ziyartar asibiti domin neman lafiya a asibitoci sama da 800 da ake da su a kano a Tsakanin asibitoci matakai uku da ake da su kamar kananan asibitoci na shan magani a
qananan Hukumomi da kuma Asibitoci manya Kaman Asibin Murtal, Nassarawa, da Makamantansu sai kuma Asibitin Koyarwa Kamar na Mallam Aminu Kano wanda wannan Qungiya take a matsayin Mai alaqa da Asibitoci da masu ziyarar Asibitin dan neman lafiyarsu. Yanzu haqa wannan qungiya ta zavi Bardan Madakin Kano
Alhaji Baban Ladi Satatima a matsayin sabon Shugaban qungiyan Abokan Asibiti wanda zai jagorance ta domin dai Amfani Kano da qasa Bakixaya inda daya yayi alqawarin samar da abubuwa da zasu amfani marasa lafiya qamar Motocin xaukar mara lafiya ta hanyar tamakon Gwamnatoci da mawadatan kano.
Ya ce wani abun lura shine yadda zakaga Motar xaukan Gawa a ko ina amma babu motar kai mara lafiya asibiti wannan ya na bukatar tunani gyarawa domin motar kai mara lafiya tafi motatar xaukar Gawa muhimmanci a Rayuwa. Haqa kuma yayi kira ga Alhaji Aliko Xangote akan Alkawarin Gina Cibiyar Tiyata
a Asibitin Murtala da cewa aikin na tafiyar wahainiya wato ya tsaya cik duc dacewa an rushe wajen Tiyatar na xa kuma sabo ya qi samuwa, sai kuma Tuni ga Shgaban BUA na qasa da yayi alkawarin bada Naira Miliyan 40 domin sayan wasu injina da qayan aiki dan amfanin asibitocin na kano da yayi tun shekarun baya.
Bullar Zazzaven Lasa A Adamawa: Jama’a Su Kula Da Mahallin Da Suke –Dakta Fatima Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola
Kwamishiniyar ma’aikatar lafiya ta jihar Adamawa Dakta Fatima Atiku Abubakar, ya shawarci jama’ar jihar, da su kula da muhallin da suke, domin gujewa kamuwa da cututtuka ma su yaxowa. Dakta Fatima ta yi wannan qiran ne lokacin wani taron manema labarai a Yola, tace ma’aikatar ta qara faxaxa aikinta da samar da ingantattun kayan aiki domin sauqaqe bincike da gano cututtuka masu yaxowa a jihar.
Xaukan waxannan matakan sun biyo bayan gano wani mutum guda xauke da kwayar cutar zazzaven vera (Lasa Ferver) a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Yola FMC, mutumin da hukumomi suka tabbatar da cewa ya mutu. Tace “kula da tsaftace muhalli da tsaftace kayan abinci kada Veraye su tava yana da muhimmanci domin a kaucewa samun vera a gida, kasancewar vera a gida na da haxari ga lafiyar jama’a” inji Fatima.
Dakta Fatima Abubakar, tace mutumin da’aka gano na xauke da zazzaven ya rasu, kuma babu wani da kwayar cutar ta shafa kawo yanzu, tace tuni ma’aikatar ta xauki mataki daqile yaxowar cutar a jihar baki xaya. Tace gwamnatin jihar bata xauki batun bullar cutar da wasa ba, don haka ta xauki matakin raba kayayyakin bincike, ta baiwa jama’ar jihar tabbacin cewa babu wani abu da zai faru, domin sun xauki matakan da ya dace. Tace haka kuma ana ci gaba
da bincike da killace mutanen sama da xarin da sukayi hulxa da mutumin kafin gano cutar, tace za’a ci gaba da bibiyansu na tsawon kwanaki 21, da dama shine adadin kwanakin bayyanar cutar a jikin mai xauke da ita. Dakta Fatima, ta jaddada bukatar ganin jama’a sunyi qoqarin sanar da hukumomin lafiya duk wani yanayin zazzaven da basu gane ba, tace hanzarta sanarwar zai taimaka wajan gano ko wace irin cutace da shawokan matsalar cikin gaggawa.
Kwamishinar ta gargaxe jama’a da cewa cutar zazzaven Lasa zazzave ne mai matuqar haxari ga rayuwar mutane, tace Vera abune da jama’a ke tare dashi, wanda kuma yake shiga abinci da ruwa, ta ce “a kula da tsafta da zuba shara ku’ina a riqa wanke hanu a kowani lokaci” inji Fatima. Daga qarshe kwaminiyar ta jajantawa iyalan mutumin da ya rasa ransa sakamakon kamuwa da cutar, tace gwamnatin jihar na duk mai yiwuwa domin hana bullar cutar a gaba.
14
A Yau
Daga Na Gaba...
Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
08036954354
Tare da Abdurrahman Aliyu
Tsakanin Marigayi Sanata Mustapha Bukar Da Masu Neman Gadon Kujerarsa Daga Hafiz Adamu Koza. hafizkoza@gmail.com 07060438556 09094608450 A yau wannan fili ya samu baquncin marubuci Hafiz Koza Adamu, ina day a yi tambihi kan rayuwar Marigayi Sanata mai wakildar Shiyyar Daura Injiniya Mustapha Bukar. Marubucin ya yi bitar ayyuka da kuma irin yadda rayuwar sanata ta ke kafin Allah ya xauki ransa, sannan ya yi nuni da cewa a shiyyar Daura yanzu ba canji su ke nema ba. Wanda zai ci gaba daga inda aka tsaya. Wannan wata gaskiya ce cewa, Sanatan Shiyyar Daura, Injiniya Mustapha Bukar Madawaki, Allah ya amshi rayuwarsa a daidai lokacin da ake buatarsa. Alaqata (Ni Mai Rubutu) Da Sanata Madawaki: Wannan ma wata gaskiyar ce da zan bayyana dangane da alaqata da Sanata Mustapha Bukar. Cikin jinina rashin Sanata ya shiga. Da na fita daga gida aka yi mini ta’aziyyar wannan rashi, sai kawai in ji qwalla ta cika mini idanu. Tsakanina da Sanata Madawaki hange ne kawai, ba mu’amala ta kusa da kusa ba. Ranar da na fara ganinsa a rayuwata sun zo kamfen xin zabukan 2015 ne garinmu; Koza. A lokacin suna tare da tawagar gwamna, Rt. Hon. Aminu Bello Masari. Yan kalmomi kaxan da ya yi a wajen taron, sai na ji a raina tabbas dattijo ne irin mazan farko. A take na ji karin waqar yabonsa ya darsu a zuciyata, inda na ce: Madawaki muke so ja damara kai ne a gaba, Sanatan Daura Zone kai muka za6a sai Baba. Tun daga wannan lokaci suna tafiya ni kuma na gina baitocin waqar, har ta kai ga kammala, inda na je Katsina domin rera ta. Malam Ahmad A Daura wani mutum ne da na sani a dalilin harkokinmu na rubutu da marubuta. Yana da kamala da iya mu’amala. Na san shi tun kafin shigowar Sanata fagen siyasa, haka kuma ban san cewa tsakanin Malam Ahmad da Injiniya Madawaki na da alaqa ta sosai ba sai da aka fara sha’anonin siyasa ka-in-da-na-in, a nan na ga yana shiga sabgar, da na yi tambaya aka fadi mini alaqarsu. Bayan an cim ma nasarar zabe sai Allah ya sa ya zama PA na Sanata Madawaki. Malam Ahmad duk wanda ya haxa mu’amala da shi tabbas sai ya amfana da kyawawan halayensa; wannan kam ba ja! Idan na koma kan batun waqar can kuwa, da yake ba sana’ata ba ce rera waqa, sai ba ta yi yadda nake so ba. Duk da haka bayan na dawo daga Katsina sai na je na kai wa Malam Ahmad ya saurara. Kar
a manta na ce muna da sanayya a tsakaninmu tun kafin siyasa, don haka sai nake faxi mishi cewa kauna ce kawai silar da ta sa na yi wannan; ba na bidar komai kuma ba dan komai ba; sanadin kauna saboda Allah da kuma tunanin Sanata Madawaki dattijo ne. Tun daga wancan lokacin a duk wata dama idan na samu, nakan bayyana wa jama’a cewa ina zaton Madawaki shi ne mutum mafi cancanta a duk ‘yan takarkarin da ke neman kujerar Sanatan Shiyyar Daura da ke Katsina ta Arewa a zabukan 2015. A haka dai Allah ya cika fata, ya kai mizani. A lokacin da Sanata ke cika shekaru biyu a Majalissa, ba za a tava mantawa da gyaran idanu na dubunnan mutane da ya xauki nauyi ba, bayan gudummowar kayayyakin asibitoci kama daga gadaje da katifu da ledojin jini da ‘Wheel Chairs’, har ma da gina asibiti sukutum a garin Dogon Hawa da gina magewayi da barandu a waxansu asibitocin. Ta vangaren samar da ayyuka kuwa, Sanata ya yi tsayuwar daka wajen samar wa matasa ayyukan soja (na ruwa da na sama da na kasa) da ‘Civil Defence’ da dan sanda da sauran ayyuka a ma’aikatu irin su hukumar EFCC da KEDCO da NBIS da NBDA da DPR da NBS da ayyukan banki da makamantansu. Samar da sana’o’in dogaro da kai na daga cikin ayyukan da Sanata ya ba muhimmaci, a dan qaramin qiyasi an samu mutane kusan dubu biyar da ake da tabbacin sun amfana daga wannan tsari. Kafin Allah ya amshi rayuwarsa, akwai rukuni na biyu wanda ya kunshi dubunnan mutane tsakanin maza da mata waxanda ake koya wa sana’o’in. Babbar hidima a wannan fanni ita ce makarantar koyar da sana’o’i da ya fara ginawa a garin Ganga, kusa da gidan talabijin na NTA Daura. Sanata Madawaki ya taka muhimmiyar rawa a fannin ilmi. Ginawa da gyaran makarantu da samar da kujeru da tebura, ba da tallafin kudin rajista ga daliban gaba da sekondare, biya wa yara marayu kudin WAEC da NECO, sayen fom na JAMB ga daliban shiyyar Daura, sai kuma uwa-uba daukar nauyin koyar da matasa 750 ilmin komfuta domin bunqasa sana’o’in dab’i da abinda ya shafi amfani da komfuta, tare da ba dalibai 75 da suka fi nuna hazaka kyautar komfuta domin yabawa da qarfafa gwiwa. A vangaren samar da ruwan sha da inganta noman rani kuwa ba a cewa komai sai dai a bi Sanata Madawaki da addu’ar Allah kai mishi wannan aiki har ga makwanci. Muhimmai daga ciki sun hada da: _Gina ‘Earth Dam’ a Garni Ward.
_Gina ‘Borehole’ guda goma sha bakwai a sassa daban-daban na shiyyar Daura. _Gina riyojin ban ruwa guda goma-goma a kowace karamar hukuma da ke Daura zone, tare da ba da injinan ban ruwa ga wadanda suka ci gajiyar riyojin. _Gina famfunan tuka-tuka da ba a tantance ba kawo yanzu da sauran ayyuka da suka jibanci samar da tsaftataccen ruwan sha a yankunan birni da na karkara. Taimako da raya al’umma da ayyukan hanyoyi da wutar lantarki da ayyukan ci gaban addini duk an shaida hannun Sanata ya kai inda ya kai a wadannan fannoni. A cikin shekaru biyu Sanata Madawaki ya zama wakili wajen isar da muradun al’ummar da yake wakilta a majalissar qasa ta sanatoci, a inda ya gabatar da qudurori da dokoki sama da guda goma sha xaya wadanda suka shafi rayuwar al’ummarsa da ma Nijeriya baki daya. Mafi muhimmanci daga cikin wadannan shi ne kudirin da ya gabatar a baya-bayar nan da ke yunkurin samar da Makarantar Kimiyya Da Fusaha ta Tarayya (Federal Polytechnic) a shiyyar Daura domin ciyar da karatun jama’ar yankinsa gaba. Ni na san a wannan dan guntun rubutun ban isa in daddale ayyukan da Sanata Madawaki ya wanzar a shekaru biyu da ya yi yana wakiltar shiyyar Daura ba, amma muradi shi ne mu gani, mu ambata; a gani, a karanta. Daga nan kuma sai a san inda aka ba kai! WATA GASKIYAR A KAN GASKIYA! Wannan gaskiya da ke kan waccan da na ambata kuma ita
ce ta neman makwafin Maigirma Sanata Injiniya Mustapha Bukar bayan babu shi a yanzu. Na rantse da Allah Maxaukaki! Sanata Madawaki ya tona asirin wannan kujera da ake yi wa al’ummar Daura da ma Nijeriya baki xaya dodorido da ita. A baya muna aika wakilai sai su je su zauna; su sha kuxi su hau mota, su sha sanyin gida da na ofis, wakilci kuma ko oho! To a yanzu da Allah ya sa muka gano WATA GASKIYA, ya rage namu wajen doras da wannan gaskiya ta ci gaba da wanzuwa. Na sha alwashi a raina cewa ba zan yi wa Sanata Madawaki adawa ba duk da babu shi a raye, haka kuma ba zan bi duk wanda na lura yana yi mishi adawa ba; ko ta wace fuska! WATA GASKIYA da nake son a fahimta daga karshe ita ce, duk Wanda ya zo ya ce shi ne magajin Sanata Madawaki, sai kuma a cikin kalamansa muka ji yana ikirarin zai kawo “CANJI” a shiyyar Daura, to mu fahimce shi lallai ba mai qaunarmu ba ne, kuma ba zai rike mu hannu biyu ba. Amma Wanda duk ya zo ya ce mana, “Za Mu Ci Gaba Daga Inda Aka Tsaya...” To shi ne wanda muke sa rai da cewar ya shirya wajen rikonmu da amana kamar yadda Sanata Engr. Mustapha Bukar Madawaki ya rike mu da girma da karamci. Mu kula da wannan, ba CANJI muke nema ba, CI GABA ne muradinmu a yanzu! Allah ya jaddada wa karimin Sanatanmu rahma. Allah tallafi bayarsa don alfarmar Annabi Muhammadu SAWW, Amin!
A Yau
RAHOTO 15
Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Bunqasar Shehu Inyass Ce Ta Sabbaba Yin Maulidinsa A Abuja Da Kaduna –Shehu Dahiru Bauchi Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
An bayyana cewar girman xaukaka da kuma bunqasar da Shehu Ibrahim Inyass ya yi a wannan duniyar ce ta sanya a wannan shekarar aka samu damar yin maulidinsa a manyan garuruwa biyu na Nijeriya, wato birnin tarayya Abuja da kuma jihar Kaduna. Shehu Dahiru Usman Bauchi, shi ne ya bayyana hakan a hirarsa da manema labaru a sa’ilin da ke warware zare da abawa kan cewar babu wata varakar da ta kunno kai a cikin Tijjaniyya dangane da wannan maulidin, taron ‘yan jaridar wanda ya gudana a gidansa da ke Bauchi a jiya, yana mai amannar cewa miliyoyin jama’a ne suka hallara a Abuja da Kaduna don yin wannan maulidin. Ya bayyana cewar Shehu Ibrahim Inyass mutum ne wanda aka haifa a qasar Senigal ne, an kuma haifesa sama da shekaru 117 da suka gabata, a don haka ne ya ce a sakamakon dumbin alkairai da ya zo da shi ne ya sanya a kowace shekara a ke tururuwar yin bukukuwan tunawa da ranar haihuwarsa domin nuna godiya wa Allah maxaukakin Sarki, “Rayuwarsa ta bamu alkairai da daman gaske don haka ne muke taruwa domin gode wa Allah a bisa samunsa,” In ji Shi. Tun da fari, ya bayyana cewar sun qira taron manema labaru ne domin su nuna godiyarsu ga Allah a bisa samun nasarar yin wannan babban taron na maulidi, haxe kuma da nuna godiyarsu ga waxanda suka dafa tun daga fara taron har ga zuwa kammalasa, ya bayyana cewar sun ji daxin yadda aka yi taron lami lafiya ba tare da wata mummunar matsala ba. Ya ke cewa, “Dukkanin wani abun da ya faru a yayin wannan babban taron ya kamata a yafe wa juna, mu dai ba mu yi niyyar vata ma wani ba, ba mu kuma vawa da kowa ba; waxansu daga cikin manya da suke yin wani abu wannan ba wani abun zargi bane, ko nima haka nake, ko kuma haka kuke. Don haka babu wata matsala, dukkaninmu mun yi ne domin Shehu,” Shehu Xahiru ya ci gaba da cewar da sun so yin taron ne waje guda, amma hakan ya zo ya fi qarfinsu domin girma xaukakar lamarin, “Babu wani abun zargi a cikin lamarin, da mun tsara cewar za mu yi taron ne a waje guda xaya tak. Sai qasaitar bunqasar Shehu Ibrahim ita kuma ta ce to bana taron har guda biyu za a
yi dole ne a yi wani a Kaduna da kuma na Abuja, karamarce ta sanya haka. Da waxanda suka je Abuja da waxanda suka je Kaduna dukkaninmu mutanen Shehu ne, kuma soyayyar Shehu ce ta haxa mu,” In ji Malam. Malamin ya qara da cewa yin taro a waje biyun babu wata doka ko kuma qa’ida daga cikin kurunnai na shiga xarika ko na xarika da wani ya karya don haka babu wata matsala illa nuna soyayya da kuma bunqasuwar Shehu Inyass. Da yake qaryata batun cewar akwai varaka a tsakaninsu ya ce “ai mu bamu rabuwa, qasaitar karamar Shehu ce ta ce bana ba a waje xaya za a yi maulidinsa ba; sai dai a yi a gari biyu, kuma ba a jayayya da karamar yadda taso haka za a yi dole, karamar ce ta ce lallai ne a yi a Kaduna da Abuja kuma rana xaya. Mu ‘yan xariqa ba mu rabuwa, abun da ya haxa mu da kowa a cikin xarika zikiri da lazumin juma’a kuma dukka babu wanda aka karya,” Kamar yadda ya bayyana. A ta bakinsa ke cewa, idan mutum ba sai girma da xaukakar Shehu ba, to idan ya ga miliyoyin jama’an da suka je Abuja zai gane hakan, “mutum bai san girma da karama ba, ka duba taron nan da aka yi a Abuja nan, idan mutum ya gani zai tabbatar da karamar waliyin Allah, Shehu Ibrahim Inyas walihi ne, duk wanda ya gode wa Allah a sakamakon samuwarsa shi ma ya zama wani abu a wajen Allah. Irin miliyoyin da suka je wannan maulidin ko gwamnati ta yi kaxan ta tara jama’a haka nan, amma ka duna karamar Shehu ta yi ta xaukan mutane tana kaisu Abuja don wannan maulidin,” Bai tsaya haka ba, ya kuma kara da nuna alheninsa ga waxanda suka raunata kasantuwar dandazon jama’a da suka yi turuwar zuwa taron kama daga zuwa ko dawowa, ko kuma waxanda suka samu raunuka a wajen taron, “Duk wanda ya ji rauni a yayin sa’ayin wannan maulidin muna miqa sakon gaisuwarmu garesa da kuma yi masa addu’ar Allah bashi lafiya, duk wanda ya rasa ransa (in akwai) muna addu’ar Allah ya jiqansa, sannan kuma jama’anmu gaba xaya Allah ya bada haquri, ya kuma bamu ladan sa’ayi,” A cewar Shi. Da yake bayyana dalilinsu na shigo da yin addu’a wa qasar nan a cikin shakalin taron maulidin na bana wanda
•Shehu Dahiru Bauchi
kuma basu saba yin hakan ba, Xahiru Bauchi ya bayyana dalilinsu “tabbas qasar tamu tana buqatar addu’a a wannan lokacin sosai, da ai babu Boko Haram, babu garkuwa da mutane, babu rikici a tsakanin manoma da makiyaya, babu satar shano, haka babu wani abun wai Buharin daji dukka babu da. A don haka ne muka xauki yin addu’a a matsayin hanya xaya domin kawo qarshen matsalolin da suka addabi qasar nan domin ceto qasar Nijeriya,” Kamar yadda ya shaida. Haka zalika Shehu Xahiru Bauchi ya gode wa tawagar bakin da suka samu halartar wannan maulidin na bana kama daga jikokin Shehu Inyas waxanda suka tattako tun daga qasashen waje da kuma manyan baqi da suka hallara a Abuja da Kaduna domin nuna soyayya ga Shehu Ibrahim “muna godiya wa dukkanin waxanda suka samu halartar wannan taron, jama’armu na Kaulaha, ‘ya’yan Shehu da Jikokinsa, maza da mata, da waxanda suka zo daga Moroko, jikokinsa na qasar Aljeriya, haka kuma da manyan malamai
muqaddamai na Misra da na qasashen Sudan, Amurka da qasashe irin su Nijer da Kamaru da sauran wuraren da suka zo muka yi musharaka da su cikin wannan taron, muna godiya Allah ya saka musu da dukkanin alkairai,”. In ji Shi. Dahiru Bauchi ya kuma yi amfani da taron masu farautar labaran wajen nuna godiyarsa ga shugaban Nijeriya Alhaji Muhammadu Buhari a bisa halartar wannan taron da ya yin a Abuja wanda ya aiko wakilisa Ministan ilimi, Adamu Adamu, haka kuma, ya nuna matuqar godiyarsa ga gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru ElRufa’i a bisa gudunmawar da ya bayar wajen tabbatuwar wannan taron a jiharsa, ya kuma gode wa Sanata Rabiu Musa Kwankwazo a bisa halartar taron da ya yi, sauran waxanda suka samu godiya ta musamman kamar yadda Shehin ya ce sun taimaka wajen samun taron na bana har da Sanata Shehu Sani da sauran waxanda ya ce ba za su misaltu ba, sai dai ya nuna godiyarsa ga dukkanin waxanda suka dafa wajen kammaluwar taron na bana.
16
Siyasa A Yau A Yau
Laraba 18.4.2018
Jadawalin Wakilan Kwamitin Shirya Babban Taron APC Ya Kawo Varaka A Majalisar Dattijai Daga Umar A Hunkuyi
Sabon jadawalin sunayen ‘yan kwamitin shirya babban taron Jma’iyyar APC na qasa ya kawo varaka a Majalisar Dattawa, inda qarfin ikon Shugaban Majalisar ya qara tabbatuwa. Hakan ya biyo bayan kasancewar xaya daga cikin Sanatocin da ya yi qaurin suna wajen ja da Shugaban Majalisar, ya zama shine Sakataren kwamitin shirya taron na APC. LEADERSHIP A YAU, ta kawo labarin cewa Sanata Ben Uwajomogu, (APC Imo ta Arewa), wanda ya zama wakili kuma Sakataren kwamitin shirya taron, yana xaya daga cikin Sanatoci 10 da suka qauracewa zaman Majalisar domin nu na rashin amincewar su da dokar da Majalisar ta amince da ita kan yadda za a gudanar da tsarin zavukan 2019, a ranar 14 ga watan Fabrairu 2018. Daga cikin Sanatocin Majalisar 11 da Jam’iyyar ta APC ta naxa a matsayin wakilai cikin kwamitin shirya taron, xaya ne kawai cikin su aka sani yana kusa da Shugaban Majalisar, Bukola Saraki, sauran duk ‘yan sai Buhari ne. Hatta Sanatan da Majalisar ta dakatar da shi kwanan nan, Sanata Ovie Omo-Agege, yana cikin wakilan kwamitin. Sanatocin da ke cikin kwamitin su ne, Ahmed Yerima, Adamu Aliero, Danjuma Goje, Abdullahi Adamu, George Akume, dakataccen Sanata, Ovie Omo-Agege, Andrew Uchendu, Abdullahi Danbaba, Baba Kuka da John Enoh. Wani Sanata wanda bai so mu ambaci sunansa ba ya shaida mana cewa, “Wannan jadawalin sunayen an yi shi ne domin a jefa razani a zukatan Sanatocin APC, a nu na masu cewa, da yawan su zai yi wuya su sake samun tikitin dawowa Majalisar a 2019. “Hakan zai sa a xauki tsauraran matakai kan Sanatocin da ke nu na ra’ayin riqau xin su kan Buhari, nan gaba Sanata Abdullahi Adamu, ne kuma za ka ji matakin da za a xauka a kan sa, kana iya cewa mayar da martani ne ko ma dai me ka ke iya cewa.
LEADERSHIP A YAU,ta kawo rahoton, Sanatoci, Adamu Abdullahi, Abdullahi Yahaya, Ibrahim Kurfi, Abu Ibrahim, Abdullahi Gumel, Binta Marshi Garba, Ali Wakil, Andrew Uchendu, su ne suka bayyana a wurare daban-daban cewa, dokar zaven nan da Majalisar ta yi wa gyaran fuska ranar 14 ga watan Fabrairu 2018, ba za su aminta da ita ba, tunda a cewar su, Shugaba Buhari ne ake son yi wa zagon qasa da ita. Sanata Abdullahi Adamu, wanda aka sha zargin sa a Majalisar bisa zargin shirya maqarqashiyar tsige Shugaban Majalisar, Bukola Saraki, akwai yiwuwar dakatar da shi daga halartar zaman Majalisar na tsawon sauran kwanukan da suka ragewa Majalisar da zama. Kwanakin baya ne dai aka tsige Tsohon gwamnan na Jihar Nasarawa, daga matsayin Shugaban qungiyar Sanatocin Arewa. An zarge shi ne da jagorantar wasu Sanatocin shirya maqarqashiyar cusa qiyayya tsakanin Sanatocin domin a tsige Bukola Saraki xin. Majalisar ta umurci kwamitin ta na xa’a, da ya binciki zargin shirya tawaye a Majalisar wanda ake zargin wasu Sanatoci qarqashin
jagorancin Sanata Adamu xin ke shiryawa. Makwanni biyu aka baiwa kwamitin ya miqa sakamakon binciken na shi domin sanin matakin da ya kamata Majalisar ta xauka. Matakin da Majalisar ta xauka na bincikar ‘yan Majalisar ya biyo bayan jan hankalin da Sanata Obinna Ogba, ne ya yi kan dokar Majalisar ta 43. Inda ya ce, shaidun da ke tabbatar da ana shirya wannan tawayen su na hannunsa. “A yau na miqe ne da safiyar nan, domin na tona asirin wasu mutane qarqashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu. A watan Janairu, Sanata Isah Hamman Misau, ya yi wata magana a nan, inda ya ke cewa, akwai wata maqarqashiyar da ake yi na tsige Sanata Bukola Saraki, da ma sauran shugabannin Majalisar bakixaya. “To a yanzun haka, ina da qwararan hujjoji a hannu na, da ke nu na wasu mutane na shirya maqarqashiyar rikita Majalisar nan, ta hanyar shirya zanga-zanga. “Ina bukatar a binciki wannan maganan. Ina kuma da hujjojin da zan tabbatar da abin da nake faxa. Akwai kalaman da aka yi ta waya tsakanin Sanata Abdullahi
Adamu, da wasu mutane. “Lokacin da maganan nan ta fara fitowa a watan Janairu duk sai muka yi watsi da ita. Ya zama tilas mu dube ta da kyau. Yin watsi da ita ba shine ba. Idan Shugaba ya amince mani, ina son na gabatar da shaidu na cikakku,” in ji Ogba. Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Ike Ekweramadu, wanda ya jagoranci zaman Majalisar a ranar, ya amince wa da xan Majalisar ya gabatar da shaidun na shi ga kwamitin Majalisar na xa’a domin ya bincike su, ya kuma kawo sakamakon binciken Majalisar cikin makwanni biyu. A cewar shi, duk wata maqarqashiya ta rikita Majalisar, yin gaba ne da mulkin Dimokuraxiyya, wanda hakan ba zai yi wa kowa daxi ba. Idan har an sami Sanata Abdullahi Adamu da laifin da ake zargin sa da shi, za a iya dakatar da shi na wani lokaci mai tsawo, kamar yanda aka dakatar da Sanata Ali Ndume, a shekarar da ta gabata kan yaxa wasu rahotannin sukan Shugaban Majalisar Bukola Saraki da Sanata Dino Melaye, da aka wallafa su a wani shafin yanar gizo.
SIYASA 17
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Za A Yi Bankwana Da APC A Nasarawa, Inji PDP Daga Zubairu T.M.Lawal lafia
A gangamin taron Jam’iyyar PDP da ya gudana shekaran jiya a garin Lafia, babban Birnin Jihar Nasarawa, ‘ya’yan Jam’iyyar na PDP sun bayyana jam’iyyar APC mai mulki a jihar da Qasa da cewa jam’iyya ce da azzalumai suka mamaye ta. Taron wanda ‘yan qabilar Eggon na kudancin Jihar Nasarawa suka shirya a harabar Jam’iyyar PDP dake garin Lafia ya samu halartan dubban ‘yan qabilar waxanda suka nuna goyon bayansu ga jam’iyyar PDP, suka kuma qara da cewa za su bai wa jam’iyyar quri’u masu yawa a zaven 2019 mai zuwa. Jama’a da dama ne suka gabatar da jawabi wajen taron, sannan sun yi kira ga qwararen Likitan nan kuma jarumin xan siyasa, tsohon xan majalisar wakilai a mazavar Lafia da Obi a shekaru 2011 zuwa 2015 da ya sake fitowa takarar kujerar Majalisar wakilai, za su qara zavenshi saboda kowa ya ga ayyukan alheri da ya ke yi a lokacin da yake riqe da kujerar Majalisa da kuma yanzu da ba ya kai. Da yake bayani Dakta Haruna Joshep Kigbu
wanda ake yi wa laqabi da Daktan Talakawa ya ce; “APC jam’iyya ce ta azzalumai saboda a 2015 na lashe zaven xan majalisar Wakilai na tarayya a mazavar Lafia da Obi amma aka yi min maguxi, na yi haquri na je kotu, idan ta tabbatar da cewa ni ne na lashe zave daga nan suka xaga shari’ar suka xaukaka qara zuwa babbar kotu a Makurdi can ma an tabbatar da haka saboda ga hujjojin da muke da sh,i amma aka zalunce mu aka yi murxiya. Hon. Kigbu ya ce; “Mun yi hakuri saboda sarakuna sun bani hakuri ni kuma mai jin maganar manyane nayi hakuri yau ga abinda APC takeyi a wannan jihar da qasa. “Al’umman da suka zave APC yanzu sun cikin tsaka maiwuya saboda talauci yaunwa kasha kasha kota’ina a qasan nan. Hon. Haruna Kigbu ya ce yanzu al’umma suna gaji da bakar mulki irin na Buhari wanda babu tausayi mutani na cikin wahala . “Mafita xaya ne ga al’umma, shi ne su fito qwansu da qwarqwata ranar zave saboda su kori APC a wannan jihar ta Nasarawa da qasarmu Nijeriya.” inji
•Daktan Talakawa
shi Hon. Kigbu ya buqaci al’ummar yankin Arewacin Jihar Nasarawa da su haxa kansu su fitar da xan takarar Gwamna saboda Jam’iyyar PDP tana da adalci ta ga cewa tunda aka fara mulkin farar hula wannan yankin ba su tava yin Gwamna ba shi ya sa ta ce, yanzu babu wanda zai tsaya takara daga wani yanki ta baiwa Nasarawa ta kudu wanan kujerar. ”Amma
idan suka kasa haxa kai su fitar da xan takara, toh ni Daktan talakawa zan fito takarar Gwamna.” Shi ma da yake jawabi, tsohon Sanata a mazavar Nasarawa ta Arewa, Hon. Soloman Ewuga ya yi kira ga maza da mata dasu tashi suyanka katin zave ya ce dauk wanda bashi da katin zave to yaje ya yanka saboda shine makamin da zaka yaki azzalumi.
Ya ce; APC ta kashe qasa yanzu batun gyara ake yi, wannan Gwamnatin ta azzalumai ce masu zaluntar yan qasa . Ya qara da cewa al’umman nasarawa sun gaji da mulkin APC haka ma al’umman Nijeriya saboda zubar da jinin ya isa haka. Ya ce; sai karya ake yi wa jama’a, kullum babu aikin alheri da wannan gwamnatin ke yi a qasa.
tarayyar ya samarwa wasu guraben wasani a kulubkulub xin qwallon qafa da dama a qasar nan da ma qasashen Qetare. Ya kuma ce Bello Suleiman,
shi ne wanda baya nuna bambanci wajen taimakon jama’a domin a yankin Akko inda nan ne karamar hukumar da ta fi sauran kananan hukumomi yawa a jihar jama’a sun ci gajiyar tallafin Noman rani dana damina musamman a garin Tukulma. Auwal Abubakar, ya ci gaba dacewa idan Honorabul Muhammad Bello Suleiman ya zama gwamna a jihar Gombe kusan kowa sai ya san cewa an samu gwamna kasancewar sa matashi kuma mai kishin al’umma. Har ila yau ya ce kamar kamfanin siminti na Ashaka da suke dibar gawayin coal a garin mai ganga a karamar hukumar Akko suke samarwa da kamfanin hasken wuta shi ne ya kawo su wanda yanzu karamar hukumar take
samun kudin shiga. A bangaren yaki da cin hanci da rashawa kuwa ya ce shi ne ya fara zagulo ma’aikatan bogi a lokacin da yake shugaban karamar hukumar Akko kuma idan ya zama gwamna zai hada kai da shugabanin da suka dace dan kawowa jihar Gombe ci gaba irin na ribar siyasa sannan kuma Matasa sai kowa ya zama mai aikin yi dan yanzu ma da ba gwamna ya yi wadanda ya samawa aikin yi a jihar sunfi mutum dubu biyar. Daga nan sai Auwal Abubakar, ya kara jan hankalin jam’iyyar PDP dacewa kar tayi kuskure wajen hana Bello Suleiman Wakilin Wajen Akko, yin takara domin hana shi tsayawa ba karamin kuskure za’ayi ba.
2019 Bello Suleiman Ne Ya Fi Dacewa Da Zama Gwamnan Gombe -Auwal Abubakar Daga El-Mansur Abubakar, Gombe
A lokacin da zaben shekarar 2019 yake ta kara karatowa a jihar Gombe an bayyana Honorabul Muhammad Bello Suleiman shugaban hukumar wasanin na jihar Gombe ne ya fi dacewa da ya zama gwamna a jihar domin shi ne dan siyasa daga tushe. Auwal Abubakar, shi ya bayyana hakan a loakcin da yake zantawa da LEADERSHIP A Yau Litinin fagen siyasa inda ya ce Honorabul Muhammad Bello Suleiman, shi ne mutum daya tilo da ya fara siyasa tun daga tushe inda aka zabe shi ya zama Kansila ya zama shugaban karamar hukumar Akko har sau uku sannan ya zama dan majalisar jihar ya zama dan majalisar tarayya
mai wakiltar mazabar Akko kana ya zama Kwamishina yanzu kuma yake shugaban hukumar wasanni na jihar Gombe. Auwal Abubakar, ya yi kira ga uwar jam’iyyar PDP a jihar Gombe dacewa ta duba kyawun dan takarar gwamnan wato Bello Suleiman Wakilin wajen Akko, wajen ba shi fifiko akan sauran yan takarar domin shi ne dan takarar da ya fi cancanta da ya zama gwamna a zaben 2019 idan Allah ya kai mu. A cewar sa Bello Suleiman a lokacin da yake dan majalisar tarayya ya samarwa da matasa masu yawa aikin yi na dan sanda da Soja da NDLEA da Civil Depence da sauransu. Hakazalika kasancewar sa shugaban kwamitin wasanin na Majalisar ta
•Honorabul Muhammad Bello
18 TALLA
A Yau
Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Domin Qarin Bayani A Tuntuvi: • Mubarak Umar – 0703 6905 380 •Sulaiman Bala Idris –0703 6666 850
RAHOTO 19
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Manoman Shinkafar Gida Sun Yunquro Don Cike Givin Sarrafa Ta Manoman shikafar a qasar nan sun yinquro ta hanyar xaukar matakai yadda zau cike givin sarrafa shikafa a qasar nan, inda suka zuba tan miliyan 2.3. ABUBAKAR ABBA ya kawo rahoton. A shekarar 2016 hukumar samar da abinci (UNF) da qungiyar aikin noma sun bayyana cewar, Nijeriyaa ta fitar da tan miliyan 2.3 na shikafa,wadda ta kai kimanin rabin da ake buqata a qasar nan wancan lokacin. Wasu bayanai da suka fito daga ma’aikatar noma da raya karkara sun sanya jimmlar buqatar shika da Nijeriyaa ke buqata akan kimanin tan miliyan 5.5 a shekara wadda ta kai kimanin tan miliyan 3.3 da ake samarwa a gida,inda kuma aka samu ragowar kimanin tan miliyan 2.2 da ake fitar zuwa qasar waje, inda wannan ya tabbatar da rahoton da UNFAO ta fitar. Amma masu ruwa da tsaki a fannin shikafa sunyi amannar cewar, ragin da aka samu na fitar da shinkafa a cikin sama da watannin da suka gabata,inda hakan ya tabbatar da maganar masu kula da harkar shinkafar dake qasar nan, sun kuma bayyana cewar, anyi nazari akan fitar da shinkafar don ayi dubi akan nasarar da Nijeriyaa ta samu akan sarrafa shinkafar gida da kuma yin dubi akan wuraren da suke buqatar a qara bayar da qaimi. A cewar Manajin Darakata kuma babban jami’i na shirin aikin noma dake qasar nan Aliyu Abdulhameed; “mun yi dubi akan nasarorin da aka samu da kuma qalubalen da suka rage. Abdulhameed a qasadar sa da ya gabatar mai taken: mahimmancin yin haxaka da kamfanoni masu zaman kansu don a cimma burin farfaxo da noman shinkar gida a Nijeriyaa a taron da aka gudanar a kwanan baya akan aikin noman shinkafa na shekarar 2018 da aka gudanar a Abuja mai taken: noma shinkafa don dogaro da kai dole na shugaban na ( NIRSAL) ya bayyana cewar akawai abubuwan da suke kawo naqasu wajen sarrafa shinkafa da adana ta da kuma rashin sauran wasu kaya dake janyo Nijeriyaa koma baya wajen samar da shinkafar da za’a yi dogaro akan ta. A cewar sa, duk dai yadda muka kalli abin, babu wata tantama akwai ximbin aiki a gaba da ya kama ta a yi. Sai dai ya nuna gamsuwa akan yunqurin na sarrafa shinka don cike givin a yau da ya kai tan miliyan 2.3. Ya ci gaba da cewa, buqatar da ake da ita ta shinkafa a Nijeria yana qara qaruwa a cikin sauri da kuma a sauran qasashen dake nahiyar Afrika saboda yadda yawan alumma ke qara ruvanya a cikin sauri inda kuma abin da mutane suke samu na shiga ya qaru gaxe da yadda mutane suke qaura da karkara zuwa cikin
birane saboda canjin rayuwar yau da kullum. Sai dai, ya bayyana fatan cewar masu ruwa da tsaki a cikin fanni zasu samar da mafita a bayyane daga cikin taron da aka kammala bada jimawa ba ko kuma ta wasu hanyoyin da zasu taimaka wajen yin daidai da yawan qaruwar alummar qasar nan wajen sarrafa shinkafar. Kamfanin na(NIRSAL), babban bankin qasa(CBN) ne ya kafa shi don samar da kuxi da kuma zuba jari akan fannin aikin noma. Abdulhameed ya ce, gudunmawar da wannan qungiyar farfaxo da za ta bayar akan noman shinkafar gida shi ne don samar da yadda za’a samar da kuxi da kuma zuba jarin da ake buqata don gudanar da aiki a nan gaba. A cewar sa, waxannan matakan zasu tabbatar da cewar, yin amfani da mai zuba jari da bin diddigi akan gudanar da aikin da kuma biyan kuxin in samu asara. Ya qara da cewa, a taqaice suna qara qulla dangantar kasuwanci tsakanin masana’antu masu zaman kansu wajen zuba jari. Ya ci gaba da cewa, NIRSAL ta samar da sabbin dabaru kimanin guda biyar don inganta numan shinkafa a Nijeriya. Abdulhameed ya qara da cewa, NIRSAL ta kuma shiga shirin noma na Anchor Borrowers na da bankin CBN ya qirqiro dashi don amfanin qanan manoma dake qasar nan ya qara da cewa, ABP da NIRSAL sun samar da dabaru don xorewar shirin. A qarqashin ABP da NIRSAL an tallawa qananan manoma su 27,000 da bashin da aka qiyasta ya kai naira biliyan 3.4, musamman a jihar Kebbi. A cewar sa, a gare mu don inganta noman shinkafa a qasar nan muna buqatar kayan aiki da fasaha da kuxi. Shima da yake qara yin dogon bayani akan matakan da aka xauka ministan noma da raya karkara don samar da abincin da za’a yi dogaro akai, Cif Audu
Ogbeh, an duba masana’antun sarrafa shinka guda 14 a satuttukan da suka gabata. Ya ce, waxannan masana’antun zasu ssamar da zuba jari da ya kai naira biliyan 250 don taimakwa masana’antun akan yadda zasu samar tan miliyan 2.3 na shinkafar da ake nomawa a gida. A wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta fitar a kwanan baya tace qasar Thailand ta fara shirin kafa masana’antar sarrafa shinkafa a Nijeriyaa saboda yadda aka samu raguwar shigo da shinkafa cikin qasar nan da kusan kashi tsasa’in. Sai dai Ogbeh bai bayyana sunayen ko suka kafa masana’antun na sarrafa shikafar guda sha huxu ba. Ministan ya ce qoqarin zai samar miliyoyin kuxin shiga wajen aikin na sarrafa shinkafar a Nijeriya. Ya ce, a yanzu haka akwai masana’antun sarrafa shinkafa guda ashirin da xaya da suke samar da jimlar tan miliyan 1.22 duk shekara da suke a xaukacin faxin qasar nan kamar a jihohin Kano da Enugu, Ebonyi da Kebbi da Anambra da Edo da Nasarawa da Benue da Kwara da Jigawa, Neja da kuma Kogi. Ya bayyana cewar qalubalen da ake fuskanta da suke kashewa manoma qwarin gwaiwa wajen noman shinkafar,an shawo kan matsalar. Qungiyar masu sarrafa shinkafa ta qasa(RIPAN) ta zuba jarin naira biliyan 300 da take tsimayin samun ribar naira biliyan 250. Mambobin ta a yanzu suna da ma’aikata ‘yan Nijeriyaa su 5,000 harda mata data xauka aiki. A lokacin data fara, ta samar da aiyyukan yi sama da miliyan biyar a qasar nan daga cikin masana’antun sarrafa shinkafa guda sha xaya da ake dasu a qasar nan. Ya ce Nijeriyaa itace ke akan gaba wajen noman shinkafa a nahiyar Afrika kuma ta biyu wajen fitar da shinkafa a nahiyar. A cewar sa sama da tan
miliyan 5.1 na shinkafa akece duk shekara a Nijeriyaa da ake sarrafawa, inda ake barin yar kaxan, sama da tan miliyan uku hakan kuma yake barin givi buqatar sama da tan miliyan 2.1 wadda kawai za ta isa a fitar da ita waje. Ogbeh ya yi nuni da cewar, a shekaru uku da suka shige, sarrafa shinkafa ya qaru da tan miliyan 6.9 a shekarar 2016, wanda hakan yake nuna cewar, ya kai tan miliyan 4.14 da masana’antun sarrafa shinkafa suke yi da kuma tan miliyan 8.019 na shinkafar ko tan miliyan 4.81 da masana’antu suka sarrafa a 2017. A cewar sa, Nijeriyaa tana qara gusawa wajen wadata qasa da abinci don a cimma burin hakan da aka sanya a gaba kafin zuwan shekarar 2020. Ya ce, a 2009, Nijeriyaa za ta iya bugun qirje wajen cewar, tanada masana’antar sarrafa shinkafa xaya ce a 2017, bayan cewar tana da guda sha bakwai dake sarrafa shinkafa tan 600,000. Ogbeh ya ce gwamnati za ta ci gaba da samar da kyakyawan yani ga manoman shinkafar gida ta hanyar samar masu da kayan feshi da takin zamani da kayan aiki na noman rani da samar masu da hanyoyi da filin noma da kuma qara daqile yin fasa qwaurin shigo da shinkafa cikin qasa. Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu, wanda kuma shi ne shugaban shirin samar da shinkafa na fadar shugaban qasa, ya bayyana cewar, ya zama wajibi a san da cewar tsadar sarrafa shinkafa a wasu qasashe ya sanya ana yin gasa wajen neman shinkafa mai sauqi da ake sarrfawa a Nijeriya. Ya ce, akwai buqatar a tabbatar da xorewa, inda kuma ya ce, farashin shinkafar da ake sarrafawa a gida zai sauka zuwa naira dubu 10,000 na girman buhu mai nauyi hamsin idan aka kwatanta da farashin shinkafar da ake shigowa da ita da ya kai naira 16, 000.
A Yau Laraba 18.4.2018
20
CINIKI
Kasuwanci MASANA’ANTU
INSHORA
HANNUN JARI
KASUWAR SHINKU
Bankin Zenith Ya Samu Ribar Naira Biliyan 174
Daga Aba Daga Idris Aliyu Daudawa
Bankin Zenith ya samiu riba kafin haraji ta Naira bilyan 174 a shekarar 2017, wannan kuma shi ne ya kasance kashi 24 cikin 100, wannan kuma ya nuna ke nan an samu qarin Naira bilyan 140, da aka samu shekarar 2016, duk kuwa da yake an samu qaruwar masu ajiye kuxi da kashi 8 cikin 100, daga Naira Tiriliyan 2.55 a shekarar 2016, zuwa Tiriliyon 2.74 a shekarar 2017. Kuxaxen masu hannun jarin Bankin ya qaru da kashi 15 cikin 100 daga Naira Bilyan 616 a shekarar 2016, zuwa Naira bilyan 708, a wannan shekarar da ake ciki, ya yin da kuma an samu qaruwar kuxaxen da suke shigowa da kashi 48 cikin 100 daga Naira bilyan 455, a shekarar 2016 zuwa Naiara bilyan 674 a shekarar
2017. Da yake jawabi a taron shekara- shekara na 27 jiya a Abuja, shugaban Bankin Mr Jim Ovia ya ce, duk da yake an fuskanci wasu matsaloli, sabnoda lain da ake ciki, akwai ci gaba wanda kowa zai murna da shi. Ovia ya nuna jin daxin sa akan yadda shi Bankin ya samu ci gaba, wannan kuwa ya kasace haka ne saboda, ayyuka Bankin. ‘’Ya qara bayyana cewar ko shakka babu shekarar 2017 Bankin ya fuskanci matsaloli, saboda daga cikin gida ne da kuma waje. Amma kuma duk da hakan maganar gaskiya shi Bankin Zenith, ya yi amfanine da duk wata dama daya samu shi yasa aka samu ribar mai yawa’’. ‘’Wannan shi yasa aka samu ci gaba wanda ya gamsar da kowa, wannan kuwa kowa yana iya tunawa, da irin taka tsan tsan da muke yi da kuxaxen jama’a’’.
Shi ma a nashi jawabin babban jami’i na Bankin Me Peter Amangbo ya bayyana cewar shugabannin Hukumomin Bankunan sun bada tasu gudunmawar, wadda ita ma ce ta sa, aka samu ci gaban, ya kuma qara jaddada cewar. Shi Bankin zai ci gaba da yin ayyukan shi kamar yadda aka saba, zai ma, a iya zarce nasarar da aka samu shekarar da ta gabata. Ya xan bada wasu has ashen da ake yi a wannan shekarar kuxi ta 2018 , Amangbo ya bayyaana c ewar shekarar da ta wuce an haxu da wasu matsaloli, saboda yadda aka yi ta gogayya tsakanin Bankuna, hakan kuma shi yasa muka iya tsayawa da qafafunmu, wannan ma akwai alamun da suke nuna cewar za a xan ja daga, amma muna ba masu hulxa da mu tabbacin cewar ba zamu sa su ji kunya ba. Idan aka yi la’akari da
yadda shi Bankin ya aikatu a shekarar da ta gabata, masu hannun jari sun amince akam shawarar da shugabannin Bankin suka bada, cewar a biya Naira 2.45 a ko wane hannun jari, a shekarar da ta gabata, amincewar su shugabannin Banki, wannan shin yasa a ko wanne hannun jari na Bamkin za a biya Naiara 2. 70k, wannan kuma ya biyo bayan wasu qarin 25 kobo, ko wanne hannun jari, a shekarar 2017. Yawancin masu hannun jarin da suka yi magana lokacin da aka yi taron, sun nuna jin daxinsu akan yadda shi Bankin, saboda cika alqawarin da suka yi, akan qarin ribar da suka samu, sun ce duk da yake shi Bankin ya fuskanci matsaloli, na yadda Bankuna suka tsinci kansu, amma duk da hakan Bankin ya ci riba, ga kuma kaddarorin daya mallaka, a shekarar da ta gabata.
kai kamar yadda Gwamnatin tarayya ta tsara baiwa matasa sama da 75,000 a qasa baki xaya horo. Malam Iliyasu Ahmad ya ce shirin kashi na biyu ne wanda za a kwashe makonni biyu ana basu horon wanda zai baiwa mata 2,029,000 damar samun horon,sannan maza guda 869 ne zasu anfana da horon. Ya qara da cewa shirin ya maida hankaline wajen tallafawa mata saboda
rauninda suke dashi a cikin al’umma,ta basu horonda zasu dogara da kansu. Shugaban hukumar NDE na kano Iliyasu Ahmad ya ce Gwamnatin tarayya ta tallafawa mutane musamman matasa maza da mata 70,400,000.Wanda jahar Kano ta sami cin gajiyar horarda mutane 6000 tare da basu tallafi dan dogaro da kai. Shi ma a nasa vangaren shugaban sashen kulada
sana’oi dogaro da kai na hukumar NDE a kano Malam Balarabe Xanjuma ya ce sun gama dukkan tsaretsare dan bada horon wanda za a yishi bisa kula da bibiya dan tabbatarda suna aiki da abin da suka koya. Balarabe ya ce za a bada horonne ga mata akan kayan shafe-shafe da sabulu su kuma maza za a koya musu gyaran kwanfuta wayar hannu da haxa tauraron xan’adam.
NDE Za Ta Horas Da Matasa 2,898 A Kano Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Hukumar samar da aikin yi ta qasa”NDE”Za ta horas da matasa guda 2,898 a jahar Kano a fannonin sana’o’i’n dogaro da kai. Da yake jawabi a wajen qaddamar da horon shugaban hukumar na jahar kano Malam Iliyasu Ahmad ya bayyana manufar bada horon dan tallafawa matasa ne koyon sana’o’i’n dogaro da
KASUWANCI 21
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Sama Da Hada-Hadar Kasuwanci 10,500 Ake Yi Kullum A ‘Computer Village’
Daga Umar A Hunkuyi
Kimanin hada-hadar kasuwanci 10,500, ne ke gudana a duk yini a kasuwar Kwamfuta ta Legas. Ahmed Ojikutu, Shugaban masu sayar da kwamfutoci da kuma kayan gyaran su, CAPDAN, na qasa ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma’a. Mista Ojikutu, ya ce, kimanin ‘yan kasuwa 25,000 ne suke gabatar da kasuwanci a cikin shaguna 3,500. “Matasa da kuma manyan ‘yan kasuwa ne ke gudanar da harkokin kasuwanci.” “Kasuwar ta, ‘Computer Village,’ tana samar da harajin Naira bilyan 1.5 a kullum. “Aiki ne mai wahala
jagorantar ‘yan kasuwa maza da mata masu yawa qarqashin inuwa guda, musamman kasantuwan mafiya yawan su masana ne kuma masu kuxi,” in ji Ojikutu. “Ayyukan kasuwancin da ake gabatarwa da kuma yanda kuxi ke canza hannu a Kasuwar namu, za a iya cewa su na da yawa, za a iya cewa cibiya ce kasuwar ta kayan fasahar zamani, kama daga gyaran su, canza masu fasali da makamantan su,” in ji Shugaban na CAPDAN. Ya ce, a yanzun kasuwar tana haxa kai sosai da sassan hukumomin gwamnati fiye da a baya. Ya ce, qungiyar na su kuma tana aiki tare da hukumar sadarwa, NCC, da kuma hukumar ci gaban fasaha da
kimiyya, NITDA. “Gwamnatin Jihar Legas ta taimaka mana sosai, amma dai har yanzun muna neman qarin taimako daga gare ta, domin kimiyya da fasaha shi ne abin da zai iya ciyar da Nijeriya gaba a halin yanzun. Ya ce, shirin da gwamnatin ta Jihar Legas ta ke yi na sake wa kasuwar na su matsuguni zai tabbata ba da jimawa ba, inda ya ce, sabon matsugunin zai kasance tsararre ne sosai. Ojikutu ya ce, sabon wurin zai kasance yana da hanyar shiga yanar gizo ta WiFi, kai tsaye, da kuma babban janareta da zai baiwa kasuwar hasken lantarki bakixayanta. Ya qara da cewa, qungiyar na su tana fafutukar ganin muna samar da wayoyin hannu na kanmu ne a
Nijeriya, suna kuma haxa kai da hukumar ta NCC, domin samar da yanayin da za a riqa horar da matasa yanda za su zama qwararru. “Rashin ilimi ne ke hana mu iya qera wayoyin hannu a Nijeriya. Ya kamata mu matsa daga masu amfani da wayoyin hannu, mu zama masu qera wayoyin. “Kamar yadda muka dage wajen ganin mun horar da matasan mu yadda za su qera wayoyin hannun, muna fatan kuma za mu iya haifar da qwararrun masu haxa wayoyin. Ya ce, kasuwar sabbin wayoyin tana ta qara bunqasa ne a cikin qasar da kashi 95, na ‘yan Nijeriya masu bukatar wayoyin duk sabbi suke nema.
suna harkar saye da sayar gwalagwalai ne, (Gold Bars). Masu zuba jarn sun kuma yi qorafin cewa, bayan sun zuba jarin fiye da Naira Biliyan xaya a kan harkar kanfanin taqi biyansu ko kwabo na ribar jarin da suka zuba, haka kuma taqi mayar musu da jarin da suka zuba. Bayan hukumar EFCC ta karvi wannan qorafin ne, sai gaiyaci masu qorafin in da suka bayar da bayanin qorafin nasu a rubuce. Bayan binciken da suka gudanar na sirri ne suka
damqe wani xan qasar Rasha mai suna Maxim Lobaty, da wasu ‘ya Nijeriya 2, Austin Emenike da Dickson Nonso Onuchukwu a garin Legas. Daga nan ne aka wuto dasu zuwa ofoshin Haukumar na yankin Kano domin ci gaba da aiwatar da bincike a kan su. Bincike ya nuna cewa, tsarin “Swiss Golden” dake da hedikwata a qasar Hong Kong, wanai tsarin ne da aka shirye domin damfarar jama’a kuxaxensu. Bayan binciken su da aka yi hukumar EFCC
dake Kano Mista Maxim da abokan harkarsa sun amince da zasu mayar da jarin da mutane suka zuba, a kan haka ne aka fara samun nasarar karvo naira N216,402,565.05. Bincken da jukumar ta yi ya nuna cewa, kanfanin na “Swiss Golden Company Limited” ya damfari dubban ‘yan Nijeriya kuxi har naira Biliyan 3, ana nan ana qoqarin kwato dukka kuxaxen da mutane suka damfari ‘yannNijeriya tare da muqa su hannu kotun daya dace domin hukunta su.
EFCC Ta Kama Waxanda Suka Damfari ’Yan Nijeriya Naira Biliyan 3 Ta Hanyar Bankin Bogi Daga Bello Hamza
Hukumar EFCC, ta qwato Naira N216,402,565.05 daga kanfanin “Swiss Golden Investment” wani kanfanin zuba jari ta intanet dake da’awar sayar da gwalagwalai, kwato kuxaxen ya biyo bayan takardun koke ne da hukumar ta samu daga dubban ‘yan Nijeriya da suka faxa hanun wannan tsari na damfara. Masu koken sun yi qorafin zuba jari ne a “Swiss Golden Investment” wanda aka sanar cewa
22
Kiwon Lafiya
A Yau
Laraba 18.4.2018
Afirka Ta Kudu Ta Na Kashe Kaso Mafi Tsoka Kan Kiwon Lafiya Fiye Da Nijeriya
Daga Idris Aliyu Daudawa
Wani rahoton da aka sake shi cikin makon da ya wuce a adireshin africacheck.org, ya nuna cewar gwamnatin Afirka ta Kudu, kasafin kuxinta na vangaren lafiya ya fi na Nijeriya sau goma sha shida, yayin da kuma abin da ake ciki yanzu (a gwamnatance da kuma masu zaman kansu) ya fi sau biyar a qasar fiye da a Nijeriya, tun a shekarar 2015 aka fara bincike kan waxannan alqalumma. Abin ya nuna cewar kuxin da ake kashewa daga cikin aljihu ya fi sau tara a Afirka ta Kudu, fiye da Nijeriya, wannan ya nuna ke nan kashi 7.7 a Afirka da Kudu, kuxaxen da a ke kashe wa wajen neman lafiya, daga aljihun gwamnati, yayin da kuma kashi 70.3 ma al’ummar Ninjeriya suna biya ne daga aljihun gwamnati. Wannan ya nuna ke nan, shi qiyasin yana nuna (‘yan Nijeriya 126 da aka qiyasta). Hukuma mai tabbatar da alqalumma Hukumar lafiya ta duniya ta nuna qiyasinta na shekarar
2015 da cewar gwamnatin tarayyar Nijeriya ita da qungiyoyi masu zaman kansu, sun kashe dala 97, yayin da ita kuma Afirka da Kudu dala 471 wannan ya nuna kenan kusan sau biyar ta fi Nijeriya. Wannan bambancin shi ne ya nuna yaddaabin yayi qasa daga shekarun 2010 da kuma 2011 lokacin da bin yake, fiye da sau bakwai, kafin shi wancan lokacin, bambanci mafi qasa shi ne na wanda ak fi sau bakwai, shine 2008, wanda kuma ya fi yawa shi ne 2000 wanda ya fi sau 15. ‘’Idan kuma ka bi ta hanyar tsadar rayuwa shi ne Nijeriya ta akan harkokin da suka shafi lafiya ta kashe, dala 215 a shekarar 2015, yayin da ita kuma Afirka ta Kudu ta kashe dala 1,086 wannan ya fi saubiyar akan na Nijeriya.’’ PPP shi wani mizani ne da ake amfani da shi wajen samun bambance bambance, a tsadar rayuwa, shi kuma Bankin duniya, ya yi wani aiki na amfani da purchasing
power parities na qasashe 177, wato bambanci na kuxaxen da ake amfani dasu tsakanin qasa da qasa. Wani Farfesa na harkar aikin lafiya a cibiyar lafiya ta Health Metrics and Evaluation na jami’ar Washington, Joseph Dieleman ya bada shawarar, kasafi harkar data shafi lafiya, ta mutum xaya, idan aka maida ita kuxin da aka fi amfani da shi, ya ce hakan ya zama dole saboda Afirka ta Kudu da Nijeriya suna amfani da kuxaxe daban daban, don haka akwai buqatar a mayar dasu kuxaxen da aka fi amfani da su. Don haka dalar Amurka ko kuma PPP su suka fi dacewa dangane da hakan. Abin da yasa Nijeriya tayi qasa shine yadda gwamnatin bata damuwa da sa kuxaxe da yawa a harkar lafiya, da aka yi amfani da kuxaxen mutane 2015 qasr Afirka ta Kudu ta kashe kuxaxe masu yawa dasuka linka
na Nijeriya sau 16, na mutum xaya, wannan sabodaan yi amfani ne da da dalar Amurka da kuma PPP. ‘’Saboda yawan haraje haraje da kuma fifikon da gwamnati take badawa akan lafiya( ba a qara kuxaxen da ake kashewa ba, akan al’amarin daya shafi cutar qanjamau). Afirka ta Kudu bata sa kuxaxe da yawa akan al’amarin kiwon lafiya ba, waxanda al’umma zasu yi amfani dasu, idan aka haxa da kuxaxen da ake kashewa a Nijeriya’’. Farfesa Frank Feely wanda shi ne ya shugabanci sashe na lafiyar duniya, a jami’ar Boston. ‘’Idan aka yi la’akari da yadda ake fatara a Nijeriya wannan yana nufin ke nan ‘yan Nijeriya da yawa basu da wata hanya ta samun kulawa dda lafiyarsu kamar yadda ya kamata,’’ Lekan Ewaenla wanda masanin tattalin arziki ne, bugu daqari kuma yana daga Hukumar inshora ta qasa.
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
KIWON LAFIYA 23
Shan Kofin Shayi A Kullum Na Da Mahimmanci Ga Zuciyar Xan Adam –Bincike
Daga Bello Hamza
Wani sabon bincike da masana suka sanar da kammala wa ranar Talata, ya nuna cewa, shan kamar kofin shayi 3 a kullum na iya kare mutane daga kamuwa cutar zuciya (Arrhythmia). Shayin coffee na xaya daga cikin ababen shan daya yi suna a duniya yana kuma cikin ababun shan dake sanyaya zukatan mutane. Amma kusan kashi 80 na asibitoci a qasar Amurka na
qarfafa masu fama da cutar “palpitations dasu guji ko su daina shan shayin coffe gaba xaya. Amma wannan sabon bincike da masana daga sashin kula da zuciya na jam’ar University of Melbourne da kuma cibiyar kula da ciwon suga na Diabetes Institute haxe da wasu abokan aikinsu daga qasar Amurka suka yi, sun alaqanta ragowar rashin daidaito nunfashi da yawan sinadarin caffeine da mutun ke sha.
Masu binciken sun yi nazarin mutum 228,465 domin gane yawan raguwar bugun zuciyarsu musamman na kashi 6 na masu shan coffee a kai a kai, sannan bincike da aka qara ya nuna cewa masu jinya mutum 115,993 sun nuna raguwar tsananin rikicin kamuwa da cutar bugun zuciyar da kashi 13 a cikin xari. “A kwai canfi a tsakanin mutane daya daxe yana cikin a’lumma na cewa, yawan shan caffeine yana qara matsalolin
dake tattare da cututtuka zuciya” inji jagoran bincike mai suna Peter Kistler daga hukumar Baker “Heart and Diabetes Institute”. “Amma sake nazarin da muka yi na littafan kiwon kafiya ya nuna mana cewa, lamarin ba haka yake ba” “Ababen shan da aka sanya musu “Caffeine” na da matuqar mahimmanci wajen kare zuciya daga bugu ba kan gado, ta hanyar samar da sidarin antioxidant da antagonism da kuma adenosine,’’ inji Kistler.
“Binciken ya qara tabbatar da cewar, masu jinyar da suke kwankwaxar coffee da tea dai dai gwargwado na samu raguwar kasadar kamuwa da cututtukar da suka shafi zuciya suka kuma iya samun daman qaruwar rayuwa a nan gaba” Sai dai masanan sun ce, saboda yawan caffeine a cikin abun sha, suna bayar da shawarar kauce wa shan ababe masu qara kuzari musamman mutanen da sue da cututtukar zuciya.
Babban Dalilin Da Zai Sa A Halasta Amfani Da Wiwi Daga Idris Aliyu Daudawa
Masana a qasar Amurka sun samu babban dalilin da zai sa su bari a riqa shan tabar wiwi,sun ci gaba da bayanin cewar tana taimakawa Amurkawa, waxanda suke qoqarin, suka saba da shan opioid, da hakan kuma suke ganin rage wa masu cutar opioid. Kmar yadda wani nazari ya nuna a wata mujalla da ake kira JAMA Intrnational Medicine, ya nuna an samu raguwar
shan maganin opioids da milyan 2.11 ko wace shekara, wannan kuma ya nuna, ana samun a qalla daga milyan 23.08 kullun na maganin da ake sha, duk shekara, lokacin da aka amince tabar wiwi a matsayin magani. ‘’Wannan ya nuna ke nan bada dama ta amfani da wiwi saboda samun lafiya, zai sa a riqa samun qaramin bayani, akan amfani da opiod, zai rage cutarwar akan matsalolin da ake fuskanta na opiod’’ An bayyana cewar al’amarin
yana qarfi sosai a jihohin da suka yadda da dokar. Binciken ya nuna yan maganin da ake bisa bayanai na qwararru tsakanin shekarun 2010 da kuma 2015, a qarqashin Medicare Part D, shi zavin da aka bada na bayanai akan maganin da kuma, fa’idar abin zai shafi Amurkawa milyan 42. Yadda ake bayanai akan shan opiod a Amurka ya qaru a cikin shekaru goma sha biyar da suka wuce, kamar yadda masu bayanai akan
magana suka bayyana, cewar shi opoid na maganin ciwon, da ya tsanatada kuma wanda bai kai hakan ba. ‘’Mace mace akan amafani da opiod abinya qarui daga 14,910 a shekarar 2005 zuwa 33,091 a shekarar 2015.’’ ‘’Tsakanin shekar 2000 zuwa 2015 mace macen asanadiyar opiod abin ya qaru da kashi 320’’. Nazarin a sandiyar binciken ya nuna a kai wata gardamar da ka yi, wadda ta goyi bayan al’amarin maganin daya shafi,
cannabis, a matsayin wani tsari na qasa, za ayi amfani da abin domin, hakan ya zama dalilin hana bayanai akan shan opiod. Kusan jihohi 30 ne suka amince da amfani da marijuana a matsayin magani, don haka jihohi tuni sukaamince ma amfani da tabar wiwi. Amma kuma akwai wasu jihohi da suke ganin amfani da wiwi kamar amfani ne da wasu muggan qwayoyi, kamar su heroin.
24 TALLA
A Yau
Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
25
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Kimiyya
Dala Miliyan 500
ne adadin kuxi Nijeriya ke kashewa duk shekara waurin safarar xanyen man fetur da wasu sinadaran da ake amfani da su a sashen sinadarari da magunguna
Gwamnati Za Ta Samar Da Cibiyoyin Kimiyya A Shiyyoyi Shidan Nijeriya Daga Idris Aliyu Daudawa
Gwamnatin tarayya ta bayyan cewar ta kammala shirye shiryen ta, na kafa cibiyoyin kimiyya, a sassa shida na Nijeriya, wannan kuwa saboda a qarawa matasa masu sha’awar al’amuran da suke alaqa da kimiyya. Ministan kimiyya da fasaha Dokta Ogbonnaya Onu shi ne ya bayyana hakan, lokacin da yake qaddamar da,rumfar Chemistry, a cibiyar kimiyya ta Assumpta, cikin makon daya wuce, a Owerri hedikwatar jihar Imo. Sanarwar data fito daga
ma’aikatar ranar Laraba Dokta Onu ya ce ita cibiyar zata kasance kamar hedikwata ce, ta koyar da kimiyya a Afirka, da tauraron xan adam a wasu sassa na duniya. Kamar yadda ya qara jaddawa ita cibiyar zata kasance wataabu mai taka muhimmiyar rawa, da yadda wasu matsaloli, kamar fatara, cuta, jahilci, rashin ci gaba a Nijeriya, da kuma wasu sassa na Afirka, za a iya yaqar su , a kuma samu nasara. Ministan ya ce shi wannan tsarin ya nuna kulawar da gwamnatin take da shi, da kuma haxin kan Vatican domin a taimaka wajen ci gaban kimiyya da fasaha, a wata
aniya ta samar da ilimi wadda ta hanyarta ce, za a samu dabarun da zasu yaimakawa tattalin arziki. ‘’Wannan tsarin ya qara nuna maida hankalin gwamnatin tarayya, zuwa nahiyar Afirka ta kasance wani wuri da zata qarfafa aniyar ta hulxar jakadanci, musamman ma, a qoqarin da take nan a ci gaban nahiyar Afirka’’. Shi ma a nashi jawabin shugaba kuma babban jami’i na al’umma Ofekata Mr Alex Iwuorie sun godewa gwamnatin tarayya, da kuma Vatican, ta haxa kai domin kafa ita cibiyar a garin al’ummarshi.
Amma kuma ya yi kira da gwamnatin tarayya ta qara kafa masu abubuwa na ci gaba, a garin al’umma da kuma jihar baki xaya. Ita cibiyar kimiyya ta Assumpta an kafa ne domin ta samar da xakuna gwaje gwaje, da zasu bada taimako ga koyar da kimiyya da fasaha a makarantu da kuma jami’oi. Ita cibiyar ana sa ran zata kasance kamar wata cibiya ce ta cimma makarantu, a karkaru wato qauyuka, ta hanyar waya, baje kayayyaki, da kuma kayayyakin xakin gwaje gwaje, saboda qwarewa, da dai sauransu.
Kutsen Da Aka Yi Wa Facebook Ya Cutar Da Turawa Sama Da Miliyan 2.7 Daga Idris Aliyu Daudawa
Mutane fiye da (2.7 million) milyan biyu ne a yammacin Turai rikicin ganin asirin masu amfani da shafin Facebook ya shafa. An bayyana haka ranar Juma’a ne wanda ita nahiyar Turan tayi, inda take cewar zata buqaci wasu amsoshi daga jagorar abubuwan da ake amfani dasu ta, hanyar sadarwa ta zamani. ‘’Facebook ya tabbatar da cewar ana amfani da dama (data) ta amfani da hanyar sadarwa ta zamani, ta mutanen da suka fi milyan biyu, ta hanyar da bata kamata ba,an rarraba da Cambridge Analytica, wani mai magana da yawun kamfanin Christian Wigand shi ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Reuters’’. Facebook ya yarda da an aikata laifin, amma kuma ‘’Ta hanyar da bata kamata ba’’ na (data ) dama ta amfani da wata kafar sadarwa ta zamani, a yammacin Turai, an dai bada sanarwar ranar Juma’a, cewar zata buqaci amsoshin wasu tambayoyin da zasu yi. Tarayyar Turai ta rubutawa Facebook makon daya wuce, domin ta tambayi ko Turawa yammacin Turai nawa ne, abin ya shafa, na laifukan da ake aikatawa ta satar (datar) masu amfanin da hanyoyin sadarwa na zamani, wajen rarraba ita datar, da wani kamfanin qwararru mai suna Cambridge analytica, mai bada shawara akan harkokin siysa. Kwamishinan harkokin shari’a na nahiyar Turai Vera Jourova
shi zai magana da babban jami’in gudanarwa na Facebook, Sheryl Sanberg, farkon mako mai zuwa, domin a tattauna matakan da za a xauka, domin samun maslaha akan laifin da aka aikata. Ya yi qarin bayani kamar haka’’ Za muyi nazarin wasiqar da muka samu daga (Facebook), dukkan abub uwan da take magana akan su, amma kuma maganar gaskiya
ita ce, wannan zai biyo bayan wasu tarurrukan, da za ayi da Facebook.’’ Shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg ranar Alhamis ya bayyana cewar akwai mutane milyan 87 aduniya waxanda, ita wannan cuwa- cuwa ko kuma badaqala ta rarraba datar mutane gawasu, wannan kuma ya sa kamfanin shiga wani rikici, wannan kuma shi yasa aka fara tababar
yadda za a iya kare data mutane nan gaba. Ita dai nahiyar Turan tana qoqari ne ne qaddamar da yadda za ariqa kare datar masu amfani da kafofin sadarwa na zamani, za kuma a vullo da wasu dokoki, a qarqashinsu shi kuma shi kamfanin , za a iya cin tarar shi ta kashi huxu cikin xari, na kuxaxen da suka samu a shekara, saboda yadda aka karya qa’idojin.
26 RAHOTO
A Yau
Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Shaida Ya Bayyana Wa Kotu Yadda Nwude Ya Damfari Bankin Qasar Birazil
Daga Abubakar Abba Mai gabatar da sheda Arifayo Falodun, ya sanar da Kotu ta musamman dake da zaman ta a jihar Legas akan yadda wani qwararren mai damfara Emmanuel Nwude, wanda kotun ta yankewa hukunci saboda damfari wani bankin qasar Birazil dala miliyan 242 da kuma yin takardun bogin na wani gida mai shi ya bashi umarnin ya sayar. Falodun wanda lauya ne dake aiki a ofishin Sofunde, Osakwe da Belgore Jiya litinin ne ya shedawa kotun hakan. Mai Shari’a Alqaqali Olubunmi Oyewole ne ya yankewa Nwude hukunci a 2005 saboda yin sojan gona ta hanyar yin amfani da sunan Paul Ogwuma gwamnan babban qasa (CBN), an kuma gurfanar dashi ne a gaban kutun tare wasu lauyoyi biyu EmmanueI I. Iechukwu da Rowand Kalu a bisa sabbin zargi na yin damfara da yin takardun bogi. Nwude dai, Alqalin ya yanke masa hukuncin shekaru ashirin da biyar zaman gidan Yari saboda damfarar wani bankin Brazil da ake kira Banco dala miliyan 242 daga shekarar 1995 zuwa 1998. Hukumar yaqi da cin hanci da rashawa da daqile yiwa tattalin arzikin qasa zagon qasa(EFCC) ce ta gurfanar dashi da wasu lauyoyi biyu a gaban mai Shari’a Mojisola Dada a bisa zargi guda sha biyar da suka haxa da damfara da yin haxin kai,inda hakan ya savawa sashi na 516 na dokar aikata
laifi sha bakwai ta jihar Legas ta shekarar 2003. Da yake bayar da sheda a gaban kotun Falodun ya shedawa kotun yadda yadda waxanda ake tuhumar suka tabka badaqalar. A cewar Falodun a ranar goma ga watan Okutobar 2017, abokan aiki na da muka fito daga ofishi guda hukumar EFCC ta gayya ce su akan maganar wani fili mai lamba 38b, dake kan titin Mobolaji Johnson, Oregun dake cikin jihar Legas. Ya ce, sakamakon wannan gayyatar ta EFCC, mun rubuta wasiqa a ranar tara ga watan Okutobar 2017 zuwa ga EFCC, inda muka yi mata bayani akan rawar da muka taka akan filin. Ya ce, a cikin wasiqar mun gabatar da kayan da suka dace harda hukuncin da Kotun ta yanke akan maganar filin. Yaci gaba da cewa, waxanda muke karewa mafi ywan su suna da jari a bankin na Banco Noroeste dake qasar Brazil kuma mun gabatar da qorafi ga EFCC akan maganar damfarar da wasu suka tabka harda wanda ake tuhuma. Damfarar sauran kuxi dala miliyan 190 kuma bayan gabatar da qorafin, wanda ake tuhuma na farko daga cikin sauran an gurfanar dasu a gaban Babbar Kotun dake jihar Legas haxe da lambar gabatar da qara kamar haka; ID/92C/2004. Ya qara da cewar, bayan gabatar da tuhumar da kuma hukuncin da mai Shari’a Alqali Justice Joseph Oyewole ya yanke a ranar
sha takwas ga watan Nuwambar shekarar 2005, wanda ake tuhuma na farko da kamfani mai suna Emorus Autos Nigeria Limited, an yanke masu hukunci. Ya bayyana cewar daga cikin hukuncin da kotun ta yanke ta bayar da umarnin cewar, kayan na wanda ake tuhuma na farko ne da aka sayarwa waxanda aka damfara da muke karewa. Falodun a cikin shedar sa, ya yi dogon bayani akan hukuncin da aka yankewa Nwude. Ya ce a cikin hukuncin guda uku, musamman na jari da sauran rantsuwar da wanda ake tuhuma na farko da kamfanin Emorus Autos Nigeria Ltd, an sayarwa da waxanda aka damfara. Hukuncin ya kuma yi nuni akan kayan da aka yanke shawarar sayarwa. Sauran bayanan da kuma sauran kaya guda ashirin da shida da canza bayanan, suna xauke da kwanan wata na ranar sha takwas na shekarar 2005 wanda dasu ne aka yankewa wanda ake tuhuma na farko hukunci. Ya qara da cewa a bisa hukuncin, wanda yake karewa da Nwude ya damfara ya sayar masu da filin su dake lamba 38b a akan titin Mobolaji Johnson, Oregun, cikin jihar Legas, wanda a qa’ida mallakar kamfanin Emorus Autos Nigeria Ltd ne da aka sayarwa kamfanin Rossab International Ltd. Kafin yin ya ce, kasuwancin, anyi rijista da kamfanin Rossab
International Ltd, ya qara da cewar, waxanda muke karewa sun yi rijistar shiga yarjejeniyar hukuncin a gaban hukumar yiwa filaye rijista. Ya yi nuni da cewar, sakamakon matsayin hukukuncin da Mai Shari’a Alqali Oyewole ya yanke da kuma yin rijistar yarjejeniyar ce, wanda muke karewa ya sayarwa da kamfanin Rossab International Ltd filin. A cewar sa, “ya mai Shari’a hukuncin da mai Shari’a Alqali Oyewole ya yanke, wanda ake tuhuma na farko ya xaukaka qarar a ganban kotun xaukaka qara. Ya ce, Kotun ta xaukaka qarar ta gano cewar, waxanda suka gabatar da qarar, Nwude ne ya kitsa damfarar. A cewar sa, har zuwa yanzu bamu da wata masaniya akan xaukaka qarar. Sai dai kuma, an dakatar da sauraron qarar saboda buqatar da lauyan EFCC Nnaemeka Omewa ya yi. Omeha ya shawarci Kotun data xage sauraron qarar saboda rashin wasu bayanai da ya kamata a gabatar a gaban Kotun a matsayin sheda. Lauyan ya kuma sanar da Alqalin Kotun cewar, fili dake xauke da bayanan basa kutun, inda ya buaci da’a sanya sabuwar rana don gabatarwa da kotun takardun. Alqali Dada ya xage sauraron qarar zuwa ranar sha takwas ga watan Afirilu don ci gaba da sauraron qarar.
27
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Tare da
Hangen Nesa
Kwamared Sunusi Mailafiya 0803 606 4695
Bashin Da Ya Zamar Wa Shugaba Buhari Dole Ya Biya
Ni har yau bana tantamar komawar Shugaba Buhari kan mulki musamman rashin qarfin gwuiwar tsayayyen xan takara daga jam’iyyar adawa ta PDP za ta tsayar, walau Atiku ko Sule Lamido koma Kwankwaso da ake tunanin zai iya komawa can inde za su bashi takarar Shugabancin kasar nan, babu makawa a hasashe na cinye zaven Buhari ya fi da wajen kaso 67 akan sauran abokan hamayya, duk da cewa qalubalen dake cikin gwamnatin Buhari ya fi nasarorinsa yawa. Shugaba Buhari ya haye kan mulki bayan ya sha kaye akalla so 3 daga jam’iyyar PDP, wani babban abin ban mamaki shi ne yanda yake da dinbin tarin masoya, babu tantama tsananin soyayya da talakawa suke nuna masa ita ta sanya ya cinye zaven 2015, dakuma wahala, gaza wa da kuma tsananin bala’in cin hanci, rashin tsaro daga Shugaba mai Malafa ya sanya dole aka zo da guguwar sauyi har aka dankwala Mai Malafa daga kan Mulki. Talakawa sun jajirce, sun kasa, sun tsare kuma sun raka duk don mutum daya, miliyoyin al’ummar kasar nan daga kowane yanki sun zavi daruruwan mutane duk saboda Buhari, dayawan Gwamnoni, ‘Yan majalisu da Sanatoci sun haye kan karagar mulki saboda farin jinin Buhari ne, bana manta 2003
lokacin da Buhari ya ce a yi APP Sak a Kano, har aka kada Kwankwaso daga kan mulki, abin nufi a nan shi ne Shugaba Buhari ya dade xamfare da soyayyar sa a zuciyoyin talakawa, hakan kuma shi ma ya bashi gudummawa wajen nuna kishinsa da sukar sa ga gwamnatocin baya duk saboda talakawan, bamu manta yanda ya riqa share hawaye duk saboda tausayin talakawa da kuma bugar kirji ya soki lamirin farashin man fetur a gwamnatin baya ba. Amma abin tambayar a nan shi ne, shin Shugaba Buhari yabiya wannan Soyayyar ga talakawan da suka na ce sai shi, shin ya share musu hawayen su alokacin da suke ganin duk duniya babu wanda zai iya gyara kasar nan kamar Buhari? Kafin nafara sharhina ina so masu karanta wannan sharhin su fuskanci wani abu, da yawan mutane na cewa nafiya kwan gaba – kwan baya a rubutuna, abin duban a nan shi ne, ni mai sharhi ne da nazari, yau idan gwamnati ta yi daidai da qarfin gwuiwa zan rubuta hakan, haka kuma idan ta gaza da qarfin gwuiwa zan soki lamirin gwamnati, burina na ga kullum talakawa na murmushi saboda amfanuwa da gwamnati. Maganar gaskiya a fexe ta kar a voye, har kawo yau Shugaba Buhari bai biya tulin bashin da ya kamata ya biya
wa talakawan kasa ba, har kawo yau Shugaba Buhari bai musanya soyayyar da talakawa ke masa da manyan ayyukan da za su amfana ba, miliyoyin al’umma daga jam’iyoyi mabanbanta sun bashi quri’ar sa amma su kuma har yanzu suna zaman sauraren biyan bashin da zai yi. Mu faxi wa junamu gaskiya yanda talakawan arewacin kasar nan ke fuskantar barazanar YUNWA, kowa yasan yanda kayan masarufi suka yi tsada, kowa yasan yanda kwandala ke wahalar samuwa a wannan lokaci, duk da arhar kayan masarufi a gwamnatin baya, amma hakan bai hana a ce kaso 53 da digo 6 na arewacin kasar nan na fuskantar matsalar ciyar da iyalansu so uku a rana, wannan matsala ce wacce ba sabuwa ba ce, amma har kawo yau Shugaba Buhari yakasa kawar da wannan damuwar ga talakawa, sai ma tsadar kayan abincin, dik da noman da ake iqirarin anayi, har kawo yau shekara 3 bamuga wani abu akasa ba, har yau talakawa basuga wani canji ta bangaren kayan masarufi ba. Idan muka koma vangaren karatu, ban tava ganin hukumar data kuma lalacewa kamar wannan ba, babu wani sabon shiri ko gyara da za ka ce harkar ilimi ta samu akasar nan ba, haka kuma bawani shiri da za mu ce anayi. Ilimin firamare, sakandare da gaba
da sakandare yana cikin wani qalubale, kuma shi kadai ne hanyar da ‘yayan talakawa za su ce suna more dimokradiyya kai tsaye, banda kwarafshin, cuta, qirqirar sakamako babu wani abu dake faruwa cikin hukumar, har ta kawo a yanzu talaka yayi kadan ya iya daukar nauyin karatun ‘yayansa shi kadai batare da temako ba, ko muqi ko muso wannan ita ce asalin gaskiya. Idan muka xauki vangaren tsaro, har kawo yau Boko Haram ta kasa zama tarihi, eh, tabbas an yi qoqari wajen dakushe kaifin su, barazanar su tayi sauqi ba kamar baya ba, amma sauran faxace-faxacen makiyaya a wasu garuruwan shi ma wata babbar illa ce ga gwamnatin Buhari, wacce a gwamnati irin tasa be kamata a samu irin hakaba. Madadin asamu raguwar asarar rayuka, har kawo yau rayukan al’umma na ci gaba da salwanta batare da sun aikata laifin komai ba, wnnan wane irin bala’i ne. Dole mu kalli hakan matsayin gazawa daga fadar shugaban kasa, domin irin soyayyar da aka nuna mata, ya kamata a ce tulin matsalolin data tarar, a yanzu ta yi wani babban aiki don kawar da shi, amma har kawo yanzu babu wani vangare da za ka nuna ka ce an kawar masa da matsalolinsa fiye da yadda tazo ta karva a gwamnatin baya. Zan ci gaba
28
Tauraruwa Mai Wutsiya
A Yau
Laraba 18.4.2018 08174743902 wutsiya2019@gmail.com
Yadda Aka Harbe Wata Mata Dake Zaman Makoki A Enugu Daga Abubakar Abba
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Enugu ta fara gudanar da bincike akan zargin harba bindiga a maqabar ta, inda hakan ya janyo mutuwar wata mata mai zaman makoki wani kuma ya samu rauni. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ebere Amaraizu ya tabbatar da hakan a sanarwar da rundunar ta fitar a Enugu ranar Asabar xin da ta gabata. Amaraizu ya ce, lamarin ya auku ne a yankin Amanato Mburumbu dake qaramar hukumar Nkanu East, inda ya ce, an samo bindigar da maqeran gida suka qera a maqabartar. Amaraizu ya sanar da cewar, haxarin ya rutsa da mace da
wadda take zaman makokin. An ruwaito cewar, lamarin ya auku ne a lokacin da wani
mutum da ake kira Daniel Chukwu dake zaune a yankin ya shigo maqabar tar a lokocin
yana xauke da bindigar bayan bai ankare cewar bindigar take shirin tashi.
Jami’an Tsaro Sun Gabatar Da Masu Safarar Mutane Ga ‘Yan Jarida Daga Mustapha Hamid
A ranar juma’ar da ta gabata ne Kwamishinan ‘yansandan jihar Abia Mr. Anthony Ogbizi ya gabatar wa manema labarai wasu Mutum 6 da ake tuhuma da laifin safarar Mutane, wa’yanda ake tuhumar dai sun shiga hannun jami’an tsaron ne a garin Aba da ke Jihar. Kafar labarai ta ‘Southern City news’ ta tattara bayanan da ke cewa, wa’yanda ake tuhumar suna gudanar da mammunan aikin nasu ne tare da haxin guiwar takwarorin su da ke Jihohin Kudu maso Gabas, da kuma Kudu maso Kudu, wa’yanda su suke sayar da Yaran da aka yi safarar tasu ga mabuqata.
Rahotanni sun bayyana cewa, masu aikata laifukan, suna safarar qananan Yara ne da ba su haura watanni 3 zuwa shekaru 3 da haihuwa ba, inda suke sayar da su a kan Kuxin da yake kamawa daga #150,000 zuwa #300,000 daidai gwargwadon qarfin mai saye. Majiyar hukumar ‘yansanda ta bayyana cewa, ‘yan banga ne suka kama wa’yanda ake tuhumar, inda suka miqa su ga jami’an ‘yansanda bayan samun wasu bayanan sirri. Cikin wa’yanda aka ceto bayan an yi kamen har da wani qaramin Yaro mai kimanin shekarun haihuwa 4 wanda aka sato shi tare da xan’uwan sa daga Coci a garin Mbano da ke Jihar ta Imo.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar ya bayyana cewa, cikin wa’yanda aka kaman, har da wasu ma’aurata, wa’yanda a baya su ka riqa sayar da ‘ya’yansu na cikin su, kafin daga baya su ma su ka rikixe suka zama dillalai. Ya cigaba da bayyana cewa, a yunqurin su na faxaxa hada-hadar ta su, ma’auratan sun tsunduma mutane da dama a cikin baqar harkar ta su a wasu vangarorin jihohin Kudu masu gabas, inda su ka fi samun karvuwa ta musamman a Jihar Imo. Obizi ya bayyana cewa, “wuraren qarfe 9 na dare, a ranar Litinin, jami’ai na da suke bakin aiki a yankin Abayi da ke Aba, suka samu rahoton cewa, wasu
Mutane da ake zargin masu safarar Mutane ne sun dira a maqwabtan yankin, lokacin da jami’an mu suka durfafe su, su ka yi musu tanbayoyi, sai suka amsa musu da cewa suna neman Otal xin da za su kama ne”. “Jami’an nawa sai ba su gamsu da amsar da su ka basu ba, daga nan sai suka taso qeyar su zuwa Ofishin mu, inda su ka yi musu tanbayoyin qwaqwaf, a nan take su ka amsa cewa, su masu safarar Yara ne” Xaya daga cikin wa’yanda ake tuhumar, mai suna Kingsley Omoha, mazaunin Mbano da ke jihar ta Imo ya amsa cewa, ya sato wani qaramin Yaro daga Obowo, ya kai shi Aba.
‘Mahaifina Yayi Ta Yin Jima’i Da Ni Tsawon Shekaru’ Daga Mustapha Hamid
‘Yar shugaban wata qungiyar asiri, mai aqidar auratayya birjik, mai suna Warren Jeffs ta ce, Mahaifin nata yayi ta saduwa da ita tsawon shekaru, tun tana ‘yar qaramar Yarinya, har zuwa lokacin da take girma a cikin qungiyar ta asiri. Ta bayyana hakan ne a wata zantawa da ita da aka yi a ranar juma’a a cikin shirin ‘Megyn Kelly Today’. Rachel Jeffs, wacce a yanzu take da shekarun haihuwa 33, ta shaidawa Gidan Talabijin na NBC cewa, Mahaifin nata ya fara yin lalata da ita ne tun
tana da shekaru 8 a Duniya, inda bayan nan ya yi ta saduwa da ita sau ba adadi, duk da yunqurin da mahaifiyarta ta yi na dakatar da hakan, haqar ta bai kai ga nasara ba sai da ta kai shekarun haihuwa 16. Wasu Mambobin Cocin ‘Fundamentalist of Jesus Christ of Later day Saints’ wanda ya qunshi har da Xan sa Roy Jeffs, su ma sun zarge shi da yin lalata da su tun lokacin suna yara. Rachel Jeffs ta rubuta wani Littafi, wanda ta bayyana irin abubuwan da ta sani, inda ta sanya wa Littafin suna ‘Samun ‘Yanci: Yadda aka yi na tsira daga Auratayya, Qungiyar
asiri ta FLDS da kuma Mahaifi na Warren Jeffs’. Yanzu haka dai Warren Jeffs yana zaman kaso a Kurkuku sakamakon hukuncin da aka zartar masa a kan lalata da yayi ta yi da qananan Yara Mata, wa’yanda yake xaukan su a matsayin Matan sa, ba shi da wani Lauyan da yake kare shi, sannan ya qi tankawa buqatar Tashar NBC na ji daga bakin sa. Lokacin da Rachel Jeffs take ‘yar shekaru 18 an sanar da ita cewa za ta kasance Mata ta 3 ga wani mutum a cikin qungiyar tasu, lamarin da yayi matuqar bata tsoro, da kuma girgiza ta.
Ta bar qungiyar nasu ne bayan da Mahaifin ta ya kore ta daga wurin ‘ya’yanta na tsawon watanni, bayan ya tuhume ta da aikata laifin da ita kuma take musanta aikatawa. “Na ji a raina kamar yana yi mini horo ne a kan laifukan da ya aikata a kai na, na ji kamar yana so in rasa duk wani qwarin guiwa ne, sannan in xauki kaina a matsayin wacce ta fi shi wofinta, ba zan tava mayar da kaina in zama hakan ba, na san cewa yayi ta aikata abubuwan da ba daidai ba, dan haka ba zan tava bari ya mayar da ni in zama marar qwarin guiwa ba”.
A Yau
29
Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Qasashen Waje
Tare da Rabiu Ali Indabawa 08069824895
Amurka Da Birtaniya Ba Su Da Hujja Akan Zargin Kutsen Da Su Ke Yi Mana -Rasha A shekara ta 2015 aka fara samun bazuwar kutsen a fadin duniya a cewar Amurka da Burtaniya kuma ta yiwu a cigaba da fadada shi don kaddamar da munanan kutse. Rasha ta yi watsi da zarge-zargen da Amurka da Burtaniya su ka yi na cewa masu kutse ta yanar gizo dake samun goyon bayan Rashar na fadada kutsensu akan kamfanoni, ayyukan gwamnati da kuma cibiyoyin Amurka da Burtaniya. Mai magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce
“ba mu san dalilin da ya kawo wadannan zarge-zargen ba.” ya fada wa ‘yan jarida a lokacin wani taron manema labarai da aka saba yi cewa, Burtaniya da Amurka basu bada wasu hujjoji ba, ya kuma yi watsi da zarge-zargen a matsayin marasa tushe. Wannan gargadin ya zo ne daga ma’aikatar tsaron cikin gidan Amurka, da kuma hukumar bincike ta FBI da cibiyar tsaron yanar gizo ta Burtaniya, sun kuma hada da bada shawara akan abin da kamfanoni zasu iya yi don kare kansu.
Firayin Ministan Japan Ya Kai Ziyara Amurka Trump da Abe ba bakin juna bane. Firayin ministan Japan shi ne shugaban wata kasa da shugaban Amurka ya taba ganawa da shi ido-daido ya kuma yi magana da shi a lokuta da dama. Shugaban Amurka Donald Trump ya karbi bakuncin Firayin ministan qasar Japan Shinzo Abe da safiyar yau Talata don ganawar kwanaki biyu, fadar White House ta ce tana sa ran tattaunawar zata yi tasiri sosai. Da take magana da manema labarai daga cikin jirgin shugaban Amurka
Air Force One zuwa jihar Florida, sakatariyar yada labaran fadar White House Sarah Huckabee Sanders ta ce tattaunawar da za a yi tsakanin shugabannin biyu za ta ta’allaka ne akan shirye-shiryen ganawa da Koriya Ta Arewa, da kuma batun cinikayya. Trump da Abe na da babban kalubale da ya shafe su, batun Koriya Ta Arewa, wadda ke shirin makamai masu linzame da na nukiliya da suka saba wa takunkumin Majalisa Dinkin Duniya.
Cutar Sanqarau Ta Vulla A Jihohi Uku Na Jamhuriyar Nijar
Ministan kiwon lafiya a jamhuriyar Nijar ya tabbatar da barkewar cutar sankarau a jihohi uku na qasar tare da bayyana alamun kamuwa da cutar da kuma sanar da jama’a cewa maganin sankarau kyauta ne kuma yana koina a asibitoci da dakunan shan magani . A hira da yayi da wakilin Sashen Hausa a birnin Yamai, ministan kiwon lafiyar
qasar Dr.Iliyasu Idi Mai Nasara, ya tabbatar da barkewar cutar a jihohi uku duk da cewa bai bada adadin wadanda suka kamu da cutar ba. A cewarsa duk shekara a yankin Afirka akan samu cututka da dama musamman cutar sankarau lokacin zafi. Saboda haka abun da su keyi a hukumance shi ne a fito a yiwa mutane bayani saboda ba sabon
abu ba ne. Inji shi da akan samu ciwon ne tun watan Janairu amma wannan shekarar sai da aka shiga watan Afirilu cutar ta kunno kai. Kawo yanzu dai akwai wurare uku zuwa hudu cikin qasar da mutane suka kamu da cutar. Garuruwan da aka samu bullar cutar sun hada da gari guda a jihar Damagaran da yankin Dan Isa a jihar Maradi, a jihar Tohoua kuma a yankin Bunza. Ministan ya ce suna fadawa mutane matakin da suka dauka tare da bayyana alamun kamuwa da cutar. Idan mutum babba ne, alamun kamuwa da cutar sun hada da ciwon kai da zafin jiki da amai ko kuma kagewar wuya.Idan kuma yaro ne qarami maxiga ta kage kuma ya ki shan nono ya dinga kuka. Ministan ya ce yanzu ba zai iya bada adadin wadanda suka kamu da cutar ba amma ana nan ana tattara alkalumma. An dai tura magani ana kuma jiran sakamako. Kawo yanzu babu asarar rai amma ana ci gaba da daukan matakai kamar fadakar da mutane tare da jinya kyauta.
Wasanni A Yau
Laraba 18.4.2018
30
Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com
EUFA Ta Yi Allah Wadai Da Zagin Da A Ke Yi Wa Macheal Oliver Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Ina Son Muhammad Salah A Real Madrid, Inji Zidane Rahotanni daga qasar Spaniya na nuna cewa Real Madrid za ta yi qoqarin sayen xan wasan gaba na Liverpool Mohammed Salah a qoqarin da suke yi na taka wa barcelona birki a shekara mai kamawa. Jaridu a qasar sun rawaito cewa Madrid na shirin yin tankaxe da rairaya a ‘yan wasanta bayan mummunar rawar da suka taka a bana musamman a gasar laliga ta qasar. Wasu kafafen yaxa labarai na cewa kocin Madrid Zidane ya shaida
wa shugaban kulob din cewa yana sha’awar a sayo masa xan xwallon na Liverpool. Xan wasan xan qasar Masar ya koma Liverpool ne daga Roma a kan kudi fan miliyan 37 a watan Yulin daya gabata bayan Roma ta siyeshi daga Chelsea. Sai dai ana ganin darajarsa ta qaru saboda rawar da ya taka tun komawarsa Liverpool sannan wasu na ganin ya qara kusan dala miliyan 100 a kan farashinsa na asali. Xan wasan ya zura qwallaye 40 a
kakar bana, inda ya jagoranci Liverpool ta kai wasan dab da na qarshe a gasar Zakarun Turai a karon farko cikin shekara 11. Kuma jaridar Diario Gol ta ce Zidane ya shaida wa Perez cewa yana son dan qwallon ya jagoranci ‘yan wasan gaban qungiyar a kakar wasa mai zuwa. Sai dai ana ganin duk da wannan matsayin Liverpool ba za ta sauya ba game da xan wasan bayan da a kwanakin baya tace xan wasanta bana siyarwa bane.
Wataqila Morocco Ta Karvi Baquncin Gasar Cin Kofin Duniya Tawagar hukumar qwallon qafa ta duniya FIFA ta isa qasar Morocco yau litinin don gudanar da gwaje-gwaje da nufin gano ko qasar ta na da zarafin da za ta iya karvar baqoncin gasar cin kofin duniya na shekara ta 2026 kamar yadda ta buqata ko bazata iya ba. Tawagar ta mutane 5 za ta shafe kwana 3 ta na aikin, inda a jiya talata za ta ziyarci filayen wasannin qasar da wuraren atisaye baya ga kafofin yaxa labarai don tabbatar da cewa qasar za
ta iya karvar baqoncin dimbin jama’ar a shekara ta 2026. Matuqar dai FIFAr ba ta samu matsaloli kan yiwuwar karvar baqoncin na Morocco ba, babu shakka qasar za ta zamo guda xaya tilo daga nahiyar Afrika da ta tava karvar bakoncin gasar bayan qasar Africa ta kudu. Sauran qasashen da suka nuna buqatar karvar baqoncin gasar a 2026 sun haxar da qasar Amurka da Canada
da kuma Mexico, ko da yake dai batun Amurka tuni ya fara gamuwa da cikas la’akari da yadda wasu ke ganin akwai qarancin tsaro musamman kan abin da ya shafi harbin babu gaira babu dalili. A kwanakin baya ma dai qasar Morocco ta karvi baquncin gasar cin kofin nahiyar Africa ta yan wasan da suke buga wasannin su acikin gida kumaitace ta lashe gasar bayan ta doke Najeriya daci 4-0 a wasan qarshe.
Hukumar qwallon qafa ta nahiyar turai ta yi allah wadai da kalaman zagi da vatanci da wasu magoya baya sukeyi akan alqalin wasa Macahel Oliver, wanda ya jagoranci wasan qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid da Juventus a ranar Larabar data gabata. Kwanaki kaxan bayan hukuncin na Oliver, magoya baya a shafin sada zumunta suka riqa tura saqon zagi da cin mutunci ga alqalin wasan da kuma matarsa wadda itama tana alqalancin wasannin qwallon qafa na mata. Bayan tashi daga wasanne Buffon yayi hira da manema labarai inda ya bayyana alqalin wasan a matsayin wanda bai san komai ba kuma zuciyarsa babu komai aciki har gwanda kwandon shara. Machael Oliver dai yabawa Buffon jan kati bayan yabada bugun fanaretin hukuncin da magoya bayan qwallon qafa musamman na Juventus suke ganin kamar ba’ayi musu adalci ba. Sai dai hukumar qwallon qafar nahiyar turai ta jaddada goyon bayanta ga Oliver inda tace bata danasanin hukuncin da alqalin wasan yayi kuma zata yi bincike akan waxanda suke tura masa saqon zagi da cin mutunci. Sai dai tuni mai tsaron raga Buffon ya bayyana cewa baya danasanin kalamansa akan alqalin wasan kuma ba zai janye maganarsa ba. Shugaban alqalan wasa dai na qasar italiya, Marcelo Nicchi yace maganganun Buffon basu kamata ba kuma nan gaba zaiyi danasanin yinsu.
WASANNI 31
A Yau Laraba 18 Ga Afrilu, 2018 (1 Ga Sha’aban, 1439)
Wasu Yan Wasan Za Su Yi Zaman Benci A Wasan Mu Da Tottenham -Mourinho
Bayern Munchen Ta Shiga Zawarcin Martial Daga: Abba Ibrahim Wada Gwale
Rahotanni daga qasar Jamus sun bayyana cewa qungiyar qwallon qafa ta Bayern Munchen ta shiga zawarcin xan wasan gaba na qungiyar qwallon qafa ta Manchester United, Antonio Martial domin xan wasan yakoma qungiyar a qarshen kaka. Martial wanda yake shekara ta uku a Manchester United ya buga wasanni 27 a gasar firimiyar wannan shekarar kuma ya zura qwallaye 9 sai dai bayajin daxin zama a benchi a wasu lokutan da mai koyar da yan wasan qungiyar yake ajiyeshi. Qungiyar qwallon qafa ta Bayern Munchen itama ta shiga zawarcin qungiyoyin Inter Millan da Juventus da kuma Tottenham wajen ganin sun xauki xan wasan xan qasar Faransa wanda yakoma United daga qungiyar Monaco. Xan wasan zai shiga shekarar sa ta qarshe a qungiyar bisa yarjejeniyar kwantaragin daya saka a qungiyar sai dai qungiyar bata da niyyar siyar da xan wasan duk da cewa yanason barin qungiyar idan dai har ba zai riqa buga wasanni ba. A kwanakin baya dai wakilin xan wasan ya bayyana cewa xan wasan zai iya barin qungiyar idan har Mourinho ba zai tabbatar masa da cewa zai riqa amfani dashi ba akaiakai inda yace yaron xan wasa ne kuma yana buqatar buga wasanni.
Wataqila Arturo Vidal Ba Zai Buga Wasan Real Madrid Da Bayern Munchen Ba Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Rahotanni daga qasar Jamus sun bayyana cewa wataqila xan wasan tsakiyar qungiyar qwallon qafa ta Bayern Munchen Arturo Vidal, ba zai buga wasan da za’a fafata ba na gasar cin kofin zakarun turai tsakanin qungiyar qwallon qafa ta Bayern Munchen da Real Madrid bayan yaji rauni a qafarsa.
Munich dai zata fafata wasa da qungiyar Bayern Liverkusen a gasar cin kofin qalubale na qasar ta Jamus zagayen kusa dana qarshe kuma tuni aka bayyana cewa xan wasan ba zai samu damar buga wasan ba. Har ila yau abune mai wahala xan wasan yabuga wasan da za’a fafata tsakanin qungiyar qwallon qafa ta Bayern Munchen xin da qungiyar Hannover 96 a gasar Bundes Liga inda a satinne kuma
zasu karvi baquncin Real Madrid Mai koyar da yan wasan Daga Abba Ibrahim Wada Gwale qungiyar ta Bayern Munchen, Mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon Jupp Heynckes ya bayyana cewa qafa ta Manchester United, Jose Mourinho xan wasan zaiyi jinya yar kaxan ya bayyana cewa wasu daga cikin yan wasan sakamakon raunin daya samu sai qungiyar da suka buga wasan da qungiyar dai bai bayyana adadin kwanakin tasha kashi a hannun Westbrom a satin daya da zai xauka yana jiyyar ba. gabata bazasu samu damar buga wasan Vidal dai yabuga wasanni 22 Tottenham ba. a wannan kakar a gasar Bundes Mourinho ya bayyana hakane a hirarsa da Liga inda ya zura qwallo 6 sannan manema labarai inda yace zai saka yan wasa kuma ya buga wasanni 6 a gasar a wasan da zasu buga da Bournemouth a zakarun turai kawo yanzu. yau Laraba kuma duk wanda yayi qoqari zai yi amfani dashi a wasan Tottenahm. Yaci gaba da cewa amma hakan baya nufin wai yana sauye-sauye a qungiyar sai dai kawai domin bawa wasu yan wasan dama suma su shiga cikin qungiyar domin bayyana basirarsu sannan kuma su tabbatar masa da cewa zasu iya wakiltar qungiyar. Ya qara da cewa hanya xaya yasani wadda ake zavar yan wasan da zasu buga wasa a qungiya kuma itace kula da yadda kowanne xan wasa yake qoqari domin idan xan wasa yana qoqari dole ayi amfani dashi a kowanne wasa. A qarshe yace ba zai duba tsadar xan wasa ba domin yayi amfani dashi ko kuma yawan albashinsa ko kuma kyawun fuskarsa, kawai qoqarinka shine zaisa yayi amfani dakai kuma idan baka qoqari zai ajiye ka domin ka huta. Manchester United dai zata fafata da qungiyar Tottenham a ranar Lahadi mai zuwa a wasan cin kofin qalubale na qasar ingila zagayen kusa dana qarshe kuma wannan ce damar Mourinho kawai ta lashe kofi a wannan gasar bayan da tuni Manchester City ta lashe gasar firimiya. Sai dai a yau Laraba qungiyar zata fafata da qungiyar Bournemouth a cigaba da buga wasannin firimiya duk da cewa Manchester City ta lashe gasar.
LEADERSHIP 18.4.18
AyAU Laraba
Don Allah Da Kishin Qasa
JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA
www.leadershipayau.com Leadership A Yau
LeadershipAyau
No: 126
N150
WASANNI
’Yan Wasan Man United Uku Za Su Sake Sabon Kwantaragi > Shafi na 30
Muqalar Karramawar Gidauniyar ZIK Ga Gwamna Laraba Masari, An Xora Abu A Muhallinsa El-Zaharadeen Umar, Katsina
08062212010
S
annu a hankali mutuncin da martabar jihar Katsina sun fara dawowa a Idon duniya, ta fuska da dama sakamakon jajircewa da kuma dagewar gwamna Aminu Bello Masari na ganin haka ta tabbata cikin nasara. Jihar Katsina ta sha fama a hannun marasa kisa, ta yi doguwar suma, wanda take in banda mutane irin su Gwamna Masari ba, to sai dai ayi hakuri da dawowar mutuncinta da ya zuve sakamakon yadda komi ya lallace ta zama koma baya babu wani abu guda xaya da yake tafiya dai dai. Aiki bakon raggo,! Kowa ya ga ji, bai saba ba,! qyaqqyawar niya da manufofi da gwamna Masari ya zo da su, sun taimaka matuqa gaya wajan ganin jihar Katsina ta fara murmurewa daga bakin ciwo da ya addabeta daga hannu ‘yan bani na iya, da man tun kafin zuwansa yana da tsare-tsare na dawowa da martabar jihar Katsina, (Restoration Agenda) A fili yake cewa tun kafin Gwamna Aminu Bello Masari ya samu nasasar cinye zave ya kafa wasu kwamitoci waxanda za su duba su yi binciken qwa-qwaf da zai taimaka masa ya samu haske ta inda zai fara kaninkacin wannan jaha da ta faxa hannu masu kuruciyar vera a zamanin baya. Rantsar da shi ke da wuya, bayan da ya tabbatar yanzu yana da majalisar zartarwa wanda ita ma take a shirye domin taimakawa a kawo gyara a jihar Katsina, sakamakon binciken da kwamitocin nan suka yi, aka xauka aka fara aiki da shi wanda yanzu ake ganin alfanin abun. Wannan yana matsayin shinfixa gane da hanyoyin da wata cibiyar bincike da ke jihar Legas ta gudanar da nata bin diddigin domin gano wanene Aminu Bello Masari kuma wace irin gudunmawa ya bada a matsayinsa na gwamnan jihar Katsina a shekarar 2017 da har ta zave shi a matsayin gwarzanta na shekarar 2017 ta karrama shi a jihar Legas. Abinda na ke son in faxa anan shi ne, duk wanda zai karrama gwamna Masari ko kuma jihar Katsina anan gaba, ga hanya mafi sauki da zai bi ita ce hanyar da waccan cibiyar bincike mai suna ‘’Public Policy Reseach And Analysis Center’’ ta bi domin kaucewa san rai da cuwa-cuwa. Babu shakka wannan kyauta da aka yi wa gwamna Masari ba shi kaxai aka yi wa ita ba, jihar Katsina ce ta samu nasara domin idan da ace mutanen Katsina ba su shi ba shi damar zama gwamna ba, sai dai a bashi wannan kyautar a matsayinsa na Aminu Bello Masari ba gwamnan jihar Katsina ba. Da man dai wannan cibiya ta saba gudanar da lakca duk shekara domin bayyana wasu daga cikin halayyar Marigayi Dakta Nmandi Azikiwe da kuma tunawa da wasu abubuwan da ya bari na alheri. Daga baya kuma cibiyar suka yi tunanin bullo da bada kyauta ta
•Gwamna MAsari Yana karvar Kyautar Gwarzon Shehkrar na ZIK daga hannun chief Emeka Anyaoku musamman ga wasu kevavun mutane da suka taka mahimmiyar rawa wajan cigaban al’ummarsu. ita dai wannan karramawa da aka yi wa gwamna Aminu Bello Masari tare da wasu manyan mutane da suka bada gudunmawa ta fannoni daban-daban ta biyo bayan wani bincike na musamman na wata cibiyar bincike da tsare-tsare da kuma yin fashin baki ta gudanar inda daga qarshe ta bayyana gwamna Masari a matsayin gwamnan da ya kawo canji a fannoni da dama da suka haxa da kawo cigaba a rayuwar jama’a da kuma samar da abubuwan more rayuwa ga mutanen jihar Katsina. Cibiyar ta qara da cewa Masari ya dage kai da fata wajan ganin martabar jihar Katsian ta dawo a idon duniya, ta ce wannan qoqari na shi ya zuwa yanzu ya fara haifar da xa mai ido, kuma jama’a tuna suka fara yin alqalanci akan wannan cigaba da ya kawo. A wannan cibiya Ferfesa Jibrin Aminu shi ne baban mai bada shawara sai kuma shugabanta wanda yake sananne ne, wato Cif George Obiozora waxanda dukkaninsu masana ne game da yadda ake zavan mutun wanda ya bada gudunmawa kafin a ba shi wata kyauta ko girmamawa, wannan yana daga cikin abubuwan da gwamna Masari ake yawan yin masa tambihi akan sa. A jawabansu shuwagaban wannan cibiya Ferfesa Jibril Aminu da Ferfesa George Obiozor sun bayyana cewa Masari mutun ne da yake da ilimin siyasa tsawon lokaci wanda hakan ne ke yi masa jagora akan nasarar da yake samu wajan yin ayyukan cigaba ga al’ummarsa Haka kuma sun qara da cewa Masari ya yi qoqari wajan kawo sauyi na yadda ake tafiyar da gwamnatin jihar Katsina a baya, acewarsu hanyoyin da ya xauka na tunkarar matsalolin jiha tare da kawo cigaba da abubuwan more rayuwa ya buxewa katsina wani sabon sashi a idon
duniya kuma a siyasance. Ferfesa Jibril Aminu ya ce tsayawar da Masari ya yi kai da fata wajan aiwatar da manufofinsa na dawo da martabar jihar Katsina idon duniya abu ne da yakama a duba, kuma wannan kyauta ko karramawa an xora abu a muhallinsa. Wasu daga cikin waxanda aka qarrama wajan wannan gaggarumin biki sun haxa da gwamna Aminu Belo Masari na jihar Katsina wanda shi ne uban gayyar da gwamna jihar Ribas, Barr. Nyeson Wike da Cif Audu Ogbeh Ministan Ayyukan Gona na tarayyar Najeriya da kuma Mista Ernest Ebi shugaban Banki Fidility. Sauran sun haxa da tsohon shugaban jam’iyyar CAN, Cif Adebisi Akende da Babban Darakta a ma’aikatar NNPC Dakta Mai Kanti Baru da Dakta Adedeji Adeleki shugaban kamfanin Pacific Holding Limited da uwargidan gwamnan jihar Anambra, Cif Ebelechukwu Obiano da Uwargidan gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar Daga cikin waxanda suka halarci wannan kasaitaccen biki akwai gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu da gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar, da gwamnan jihar Sakwato, Aminu Waziri Tambuwal, haka kuma an samu wakilcin masu martaba sarakunan Katsina da kuma Daura waxanda ‘ya ‘yan su suka wakilta a wajan wannan taro. Kasaitaccen bikin wanda aka shirya shi a cibiyar Civic Center da ke rukunin unguwanin victoria Inland da ke jihar Legos ya samu halartar dubbin masoya da magoya bayan gwamna Aminu Bello Masari daga jihar Katsina da suka haxa da ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da kuma masu riqe da muqamai a gwamnatance. Daga cikin waxanda suka halarci wannan taro na tarihi sun haxa da mataimakin gwamnan jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu da Sakataran gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammed
Inuwa da ‘yan majalisar Dattawa da ‘yan Majalisar wakilai da kuma ‘yan majalisar dokoki ta jihar Katsina da masu baiwa gwamna shawara a matakai daban-daban Akwai mutane irin su babban alqalin alqalai mai Shari’a Musa Abubakar Xanladi da shugaban kamfanin Max Air, Alhaji Xahiru Bara’u Mangal da shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Shitu S. Shitu da sauran manyan masu faxa aji tare da shuganan Jam’iyyar APC na qasa mista Jonh Oyegun. Shima mai gayya mai aiki, da yake magana a madadin waxanda aka karrama gwamna Aminu Bello Masari ya nuna jin daxi da godiya da wannan cibiya da kuma waxanda suka shirya wannan taro domin karrama su. Masari ya bada tabbacin cewa waxanda suka shirya wannan biki ba su yi san ran su ba, ya ce ya yi farin ciki da wannan girmamawar da ta zama babu san kai acikin, amma da gani an sa tunani da hange nesa kafin a zave su a karrama su. Ya qara da cewa waxanda aka zava aka karrama za su yi amfani da wannan damar su yi abinda ya kamata wajan cigaba da yi wa jama’ar su aiki wanda anan gaba zai zama wani abin koyi ga wasu da za su iya samun wannan karramawa mai girma. Daga qarshen ya yi wa kowa fatan alheri Gudunmawar da wasu masu kishin jihar Katsina suka bada domin ganin wannan taron ya yi nasara abu ne da ba za a tava mantawa da shi ba, domin kuwa Katsinawa mazauna jihar Legas sun yi qoqari so sai wajan ganin gwamna Masari da mutanen jihar sun samu nasarar wannan taro. Suma ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da suke zaune a Katsina ba a bar su a baya ba, domin kuwa sun tsaya ba zaune ba tsaye, Musamman sakataran gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammad Inuwa da ya sa ido domin ganin ba a samu wata matsala ba.
Babba Da Jaka An cafke likitan bogi mai amfani da takardar Firamare a Legas –Labarai
Wannan ya cika shege!
Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 0703 666 6850; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 01-8963459. E-mel: leadershipayau@gmail.com, Leadershipayau@yahoo.com