LEADERSHIP A Yau 19 Ga Afrilu 2018

Page 1

19.4.18

AyAU Alhamis

LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

LeadershipAyau

No: 127

N150

Jonathan Ne Silar Wahalhalun Da Ake Sha A Nijeriya –Tinubu Daga Umar A Hunkuyi

Shugaban Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya sake xora zarginsa kan gwamnatin farar hula da ta gabata, kan matsalar tattalin arzikin qasarnan da ake fama da shi a halin yanzun. Tinubu, ya bayyana hakan ne cikin jawabin sa, a matsayin sa na babban baqo a taron shekara-shekara na 35 na tunawa da Malam Aminu Kano,

wanda aka yi ranar Talata a Kano. Tinubu, wanda Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya wakilce shi, ya bayyana cewa, gwamnatin tsohon Shugaban qasarnan, Goodluck Jonathan, ita ce babbar mai laifi wajen wawashe albarkatun qasarnan. Masu jawabi a wajen taron su ne, mawallafin kafar yaxa labaran nan ta, Premium Times, Mista Dapo Olorunyomi; da kuma wani babban

jigo a Jam’iyyar APC, Dakta Usman Bugaje, duk sun yi nazarin mulkin Dimokuraxiyya ne a qasarnan, da kuma matsayin aqidar Jam’iyyun siyasa. Tinubu, ya danganta rashin samuwar manyan ayyuka a qasarnan kan bilyoyin kuxaxen da gwamnatocin baya suka sace.

>Ci gaba a shafi na 2

•Tinubu

Zargin Badaqalar Biliyan 18:

EFCC Za Ta Fara Farautar Kwankwaso Da Wamakko 4

•Shugaban Qasa, Muhammadu Buhari a wurin taron dandamalin kasuwanci na qasashe rainon Ingila wanda ya gudana jiya a Xakin Taro na Guild Hall dake Landan

Yadda Aka Kashe ’Yar Shekara 2019: Ya Kamata A Haxa Qarfi Uku Da Fyaxe A Kano Don Korar Buhari –Falae > Shafi na 2

> Shafi na 2


2 LABARAI

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

2019: Ya Kamata A Haxa Qarfi Don Korar Buhari –Falae Daga Umar A Hunkuyi

Shugaban Jam’iyyar SDP na qasa, Cif Olu Falae, ya ce, ‘yan Nijeriya za su haxa qarfi su kori Shugaba Buhari, bisa hanqoran da yake na sake tsayawa takara a 2019. Ya yi magana ne kan tavarvarewar tsaro da ke addaban qasarnan a halin yanzun, bisa yawaitan kashekashen da makiyaya da kuma Boko Haram ke ci gaba da aikatawa ko’ina a cikin qasarnan. Falae, ya bayyana hakan ne sa’ilin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan fitowar sa daga wata tattaunawar sirri da tsohon Shugaban qasa, Cif Olusegun Obasanjo, wace suka yi a babban xakin karatun sa da ke Abeokuta, ranar Talata. Ya bayyana cewa, gwamnatin ta Buhari, ta gaza wajen farfaxo da tattalin arzikin qasa da tsaro. Falae ya ce, ‘yan Nijeriya suna bukatar canji ne daga yawaitan rashin ayyukan yi, damuwa, rashin tabbas da kuma canji daga tararrabin

masifun Boko Haram, ba irin wannan canjin halin ni‘yasun da suke cikin sa ba yanzun a qarqashin wannan gwamnatin. Ya ce, tattaunawan da suka yi da Obasanjo, ta zama tilas ne domin ganin ko akwai hanyar da za su iya taimakawa qasarnan kan ximbin matsalolin da ta ke fuskanta. “Matsalolin Nijeriya sun fi qarfin burin duk wani xan siyasa.Na zo ne na ga Baba Obasanjo, kan matsalolin da ke addaban Nijeriya. A baya can tsakanin shekarar, 1977 da 1979, na yi aiki tare da shi. Yana Shugaban gwamnatin mulkin Soja, ni kuma ina babban Sakatare a tare da shi. Mun aiwatar da mahimman abubuwa da yawa a wancn lokacin na ganin ci gaban Nijeriya.” Kan yiwuwar samar da haxin kai tsakanin Jam’iyyar na shi da qungiyar Obasanjo ta,CNM, Falae ya ce, akwai bukatar ‘yan Nijeriya su haxa kai tare domin samar da ci gaban Nijeriya. “Ni da kai duk mun san wannan gwamnatin ba ta

Auren Neman Biza: An Xaure Ango Shekaru Biyu Kan Auren Qarya Daga Umar A Hunkuyi

A jiya, Mai Shari’a Mojisola Dada, na kotun hukunta laifuka na musamman ta Jihar Legas, ya xaure wani da ke neman bizar zuwa qasar Ingila, mai suna, Kolawole Viyon, shekaru biyu, bisa laifin bayar da bayanan qarya kan matsayin Auren sa. Mai shari’a Mojisola Dada, ya zartas masa da wannan hukuncin ne, bayan da Viyon xin ya amsa laifin tuhumomi ukun da hukumar kama masu laifuka na musannan ta, ICPC, ta gabatar da shi a kan su. Hukumar ta ICPC, ta shaidawa kotun laifin na shi ya savawa sashe na (1) (b) da 25 (1), (a) na dokar hana aikata laifuka ta shekarar 2000. Hukumar ta ce, Viyon, ya haxa kai ne da wata mata mai suna, Olaronke Akerele, domin ya aikata laifin ranar 13 ga watan Disamba 2016. Hukumar ta ce, “Lokacin da jami’an Ofishin jakadancin Ingila suka kama mai laifin a shekarar 2016, sai suka miqa shi tare da abokiyar burmin na shi, wacce ta arce a yanzun, ga hukumar ta ICPC, suna tuhumar su da bayar

da bayanan qarya wajen cike takardun su na neman biza. “Viyon, ya yi wa, jami’in bincike na hukumar ta ICPC, Nkem Ezenwa, bayanin qarya na cewa, Olaronke Akerele, matarsa ce ta uku. Wacce wani Limami na cibiyar, ‘Jama-atul-Islamiyya of Nigeria, ne ya xaura masu auren kamar yadda Shari’ar Musulunci ta tanada. Ya kuma gabatar da takardar shaidar auren na su mai lamba kamar haka, JUN/LB/0000064, wacce ke da kwanan watan, 9 ga watan Janairu 2016. “Ya kuma qara da cewa, an yi shagalin auren na su ne a gida mai lamba, 108, titin Tokunboh, da ke tsibirin Lagas. Da take yanke hukuncin, Mai Shari’ar, ta ba shi zavin zaman gidan yari na shekaru biyu, ko kuma ya biya tarar Naira 300,000, wanda tilas ne ya biya a cikin sa’o’i 24, ko ya wuce gidan yarin. Mai shari’ar ta ce, “Idan ya kasa biyan tarar cikin awanni 24, zavin ya faxi, tilas ne ya yi zaman gidan yarin.” Nan take sai Lauyar wanda ake qarar, Hannah Adeyemi, ta miqe ta ce, ai ya ma zo da tsabar Naira 300,000, a tare da shi cikin Kotun.

tsinana komai ba. Babban aikin da ke gaban kowace gwamnati shi ne, kare rayukan ‘yan qasar ta. Wannan gwamnatin ba ta yi hakan ba. “Ana ta ci gaba da kisa da yanka mutane kullum. Duk gwamnatin da ta kasa magance hakan, tabbas ta gaza. “Shugaba Buhari, aboki na ne. na tava xaga hannunsa a filin wasa na, Adamasingba, a Ibadan, na kuma nemi

mutane da su zave shi, saboda ya ce zai gyara Nijeriya. Don haka ka ga ashe ba qiyayya ce ba. “Gaskiyan lamari shi ne, bai tavuka komai ba. Na yi zaton shi kan shi zai lura da hakan, ya yi tunani mai kyau, ya kyautata wa kan shi, da mu bakixaya, bisa la’akari da yadda komai ya lalace, ya ce ba zai sake tsayawa takara ba. Na yi zaton zai yi hakan, amma bai yi hakan ba. “Abin da nake cewa a nan

shi ne, gaskiya, yawancin ‘yan Nijeriya sun haxa kai, sun yunquro da nufin neman canji kan wannan halin quncin da ake ciki. Za su yi duk abin da za su iya su ga sun kori Buhari, don amfanin kan shi da qasar kanta. Tattaunawar na su, wacce ta kai tsawon awanni biyu da rabi, tare da su akwai masu neman kujirar gwamna biyu daga Jihar Ogun, Yarima Gboyega Nasir Isiaka da Mista Sina Kawonise, da sauran su.

•Falae

Yadda Aka Kashe ’Yar Shekara Uku Da Fyaxe A Kano Daga Bello Hamza

An tsinci gawar yarinya ‘yar shekara 3 mai suna Khadijah Abubakar Abdullahi a wani ofishi dake makarantar Khairat community school dake unguwar Walalambe a qaramar hukumar Nassarawa ta jihar Kano, bayan an yi cigiyar ta tsawon kwanaki 4, kamar yadda jaridar Kano Chronicle ta ruwaito. Binciken farko da yansanda suka gudanar a kan gawar ya nuna jinni a al’auranta abin da ke nuna kamar anyi mata fyaxe kafin mutuwar, har yanzu kuma ba a san waxanda suka aikata wannan xanyan aikin ba. An samu bayani cewar, Khadijah ta vace ne a yayin da ita da ‘yanuwanta 2 suka tafi makaratar na Khairat ne domin gani mahaifiyarsu dake karantarwa a makarantar. Jami’in watsa labaran rundunar ‘yansanda SP Magaji Musa Majia, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce tuni aka kama mutum 9 yawancinsu malamaine makarantar inda ake zarginsu

da hannu a kisan wanna yarinya. Majia ya kuma tabbatar wa jama’a cewa, rundunarsu zasu qara qaimi na ganin an kama duk mai hannu a wannan xanyen aikin a cikin kwanaki 4. Da yake qarin bayani, mahaifin yarinyar mai suna Malam Abubakar Abdullahi wanda aka fi sani da suna IBB, ya ce, a lokacin day a y arba da gawar xiyarsa ya ganta tsirara ne a cikin jinni, jinni kuma na ta kwarara daga al’auranta da duburanta. Ya qara da cewa, “yanayin da muka ga gawar xiyar raw a ya nuna qararar kamar anyi mata fyaxe ne, bamu iya tava gawar ta ba” “har gawar ya fara ruvewa ya na wari, nan take muka sanar da ‘yansanda inda suka xaki gawar domin gudanar da bincike daga baa suka bamu muka yi mata jana’iza kamar yadda addinin usulunci ya tanada. Khadijah ta rasu, lalai ina neman a yi mani adalci, yau abin ya faxo aka Khadijah, Allah ne kaxai ya san a kan wanda lamarin zai faxawa gobe”

“A kwai buqatar gwamnati ta xauki muhimmin mataki domin kare rayuwar mutane musamman yara qanana”. Abdullahi ya kuma bayyana cewar, a lokacin da suka fahinci marigayya Khadijah bata dawo gida tare da sauran ‘;yanuwanta ba, nan take shi da sauran ‘dangi suka shiga neman ruwa a jallo. Ya yi bayanin cewa, a rana ta farko sun zagaye gidajen makwabta da ‘yanuwa domin gano ta amma babu nasara. “Mun ci gaba da neman ta har tsawon kwanaki 3 babu xuriyarta sai gas hi an ga gawar ta a cikin wani ofis a makarantar a rana ta 4” “Mahaifiyarta malama ce a makarantar da aka ga gawar nata, ita da sauran ‘yanuwan ta a nan suke karatu, a ranar da abin ya faru mahaifiyarta bata raka zuwa makaranta ba saboda bata da lafiya” “Bayan an tashi makaranta ne ‘yan uwan Khadijah suka zo da labarin cewar basu ganta ba bayan da aka tashi makaranta da qarfe 5 ; 30, daga nan ne muka shiga wannan tashin hankalin” inji shi.


3

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Ra’ayinmu

Yayin Da Aka Yi Bikin Ranar Mata Ta Duniya… A ranar Alhamis xin da ta gabata 8 ga watan Maris 2018, xaukacin al’ummar duniya suka gudanar da bikin ranar Mata ta duniya. Ranar 8 ga watan Maris, rana ce da aka keve musaamman domin qara sanar da duniya matsayi, qima da kuma darajar da Allah Ya yi wa Mata. Rana ce, da a kan gudanar da taruka domin yayata irin ci gaban da kuma gwagwarmayar da mata suka yi ko kuma ma suke kan yi a dukkanin sassan duniyar nan. Tun a farkon wannan qarnin ne aka keve wannan ranar ta 8 ga kowane watan Maris na kowace shekara domin nu na halin da matan ke ciki a jiya da kuma yau, rana ce da gwamnatoci, Qungiyoyin mata, Kamfanoni da ma sauran xaixaiku sukan yi taruka, shirya wasu bukukuwa na musamman, domin su tattauna halin da matan ke ciki saboda mahimmancinsu, a duk faxin duniyar nan. Ranar mata ta duniya, rana ce da a kan dakatar da komai domin a tsaya a yi dubi da kyau a kan qimar matan, a matsayin su na, Matan aure, Iyaye, manyan ‘yan kasuwa, Shugabanni, ‘yan gwagwarmaya, da makamantan hakan. Taken ranar ta wannan shekarar shi ne, “Lokaci ya yi: da ya kamata a sami canji a rayuwar mata,” a taqaice kenan, da turanci taken ranar matan ta bana shi ne, “Time is Now: Rural and Urban Activists Transforming Women’s Lives”. Bikin na bana, ya yi karo da yunquri kala-kala da matan ke yi a dukkanin sassan duniyar nan,na ganin sun fitar da kansu daga wasu al’adu ko dokokin da suke tawaye ne a cikin darajar da Allah Ya yi masu. Suke kuma gwagwarmayar tabbatar da samun ‘yanci wanda ya yi daidai da na kowane mahaluqi a bisa gaskiya da adalci ba kuma tare da nu na wani bambanci ba. A wasu qasashen kamar qasar Amurka da makamantansu, matan sukan gudanar da jerin gwano ne a bisa tituna da kuma bin gidaje a cikin birane da qauyaku, inda suke tunatar da mutane a kan wasu haqqoqinsu da aka tauye masu, musamman a wuraren da a kan bambanta albashin matan da na maza ko abin da ya shafi matsayin su wajen raba muqamai a siyasa da sauran qungiyoyi. Hakanan kuma sukan yi amfani da wannan ranar domin tunatar da al’umma haxarin da ke tattare da cin mutunci, tsagwama, qoqarin raina matsayi, Fyaxe, da duk da a kan yi wa matan. Mu a nan, muna ganin kamata ya yi Shugabanninmu da sauran masu faxa a ji, su yi amfani da wannan ranar ta wannan shekarar wajen tsayawa tsam da kuma yin dubi bisa hali da kuma yanayin da matan ke ciki musamman

ma matan karkara. Waxanda za mu iya cewa, sune kaso aqalla xaya bisa huxu na al’ummar wannan duniyar tamu. Tare da wannan ximbin yawan na su, da kuma gagarumar gudummawar da suke baiwa al’umma ta dukkanin fannoni, sai kuma sukan zama abin tausayi, domin kuma za ka taras a duk wani sashe na more rayuwar da suka taimaka wajen daxaxa ta, su ne a baya. Akwai bukatar xaukan matakai na gaggawa waxanda za su ciyar da rayuwar matan da muke kira da iyayen

al’umma gaba, tilas ne mu baiwa matan gudummawa ta kowane sashe kuma a birane da karkara da ma dukkanin qauyaku. Tilas ne mu zaqulo matan da suka yi dukkanin abin yabo a cikin al’umma domin mu yaba masu kamar yadda a kan yabawa kowa. Tilas ne mu qarfafi mata ‘yan gwagwarmayar fito da haqqi da qimar mata a duk inda suke. Sannan kuma ya zama wajibi ga gwamnatocinmu da su tabbatar da sun gusar da dukkan wani abu mai qarfafa qyama da kuma nu na bambanci ga

EDITA Sulaiman Bala Idris

MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama

MATAIMAKIN EDITA Bello Hamza

DARAKTAN SASHE Mubarak Umar

RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah

BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John

manufarmu

LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!

mata. Kamar yadda ya zama wajibi ga gwamnatocin namu da su yi dukkanin abin da za su iya yi na ganin sun kyautata rayuwar matan, ta hanyar fito da shirye-shirye da kuma wasu ayyukan da za su kyautata rayuwar matan. Kamata ya yi, wannan rana ta kasance ta shekara ce sukutum, ba ranar 8 ga watan Maris ba kaxai, muna ganin lokaci ya yi da dukkanin mutane a xaixaikun su ne ko gwamnatoci, Kamfanoni, Qungiyoyi da sauran dukkanin al’umma za su yi dukkanin abin da ya dace na ganin sun fitar da haqqin matan gami da kyautata rayuwar su ta hanyar samar masu da dukkan abin da zai iya ciyar da rayuwar ta su gaba. Kowace al’umma ya kamata ta duba ta ga hanyar da ya kamata ta taimakawa rayuwar matan ta yadda za su mori rayuwar su daidai da sauran mutane. Mutane da yawa, zaton su shi ne, fifiko yana ga mawadata da kuma masu mulki ne kaxai, wanda lallai ba hakan ne ba. Wannan zamani ne wanda duniya ta kasance tamkar ta taru ne a cikin xaki guda, musamman kasantuwar hanyoyin sadarwa na zamani da ake da su yanzun, ta yadda duk abin da ya faru a nan duk duniya za ta kasance da masaniya a cikin sa. Wannan ya isa ya nu na mana cewa, ya zama tilas mu guji taka haqqin mata da ma sauran marasa qarfi, domin kuwa dukkanin abin da muka yi tabbas duk duniya tana kallonmu. Wannan aiki ne da ya hau kan kowa. Ya wajaba, mata su fito su ma su faxa domin a ji su a kuma saurare su, su kuma yi amfani da hannuwansu wajen yin nu ni da dukkanin halukan da suke ciki ta hanyar rubuce-rubuce, su kuma yi amfani da dubarbarun da Allah Ya huwace masu wajen taimakawa junansu kamar yadda suke taimakawa al’umma bakixayanta. Su kuma ci moriyar dukkanin kafafen sadarwa wajen yayatawa duniya hali da kuma yanayin da ‘yanuwansu na karkaru da qauyaku ke ciki. Ya kuma kamata al’umma da ta baiwa matan sarari domin su nu na irin bajintar da Allah Ya yi masu, a makarantu, wuraren aiki, wajen wasanni da dai sauran su. Dukkanin gwamnatoci ya kamata su samar da hanyoyin kare haqqin mata da mutuncin su, musamman mu a wannan nahiyar matan da rigingimu da yaquka suka xaixaita su, suka raba su da gidajen su da kuma iyalan su. A qarshe muna kira ga gwamnatin tarayya, da ta hanzarta sanyawa a cikin dukkanin tsare-tsaren ta, gami kuma da aiwatar da abubuwan da muka bayar da misalan su dangane da kare haqqi da mutuncin mata.


4 LABARAI

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Zargin Badaqalar Biliyan 18: EFCC Za Ta Fara Farautar Kwankwaso Da Wamakko Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja

Hukumar yaqi da cin hanci da rashawa EFCC za ta fara gudanar da wani bincike na musamman kan tsohon gwamnan Kano, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da takawaransa tsohon Gwamnan Sakkwato, Aliyu Magatakarda Wamakko. Binciken na EFCC za a gudanar da shi ne kan zargin tsoffin gwamnonin kan badaqalar zunzurutun kuxaxe har Naira biliyan 18.08 . LEADERSHIP A Yau ta bankaxo cewa hukumar za ta tuhumi Kwankwaso Wamakko ne bisa zargin sama da faxin Naira Biliyan 15, wanda dukiya c eta Jihar Sakkwato, shi kuma Kwankwaso za a tuhume shi da zargin tarwatsa naira biliyan 3.08 dukiyar qananan hukumomi 44 na Jihar Kano. Binciken na waxannan manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, kuma sanatoci masu ci, sun biyo bayan wasu qorafeqorafe mabambanta da aka gabatarwa Hukumar ta EFCC. Bincikenmu ya tabbatar mana da cewa EFCC ta amshi qorafi daga wata qungiya mai suna ‘Movement for the

Liberation and Emancipation of Sokoto State’, wanda ta ke zargin Wamakko da wannan almundahanar. Surajo Saidu da Mudassir Umar Alhassan su ne shugabannin wannan qungiya, wanda kuma su ne suka rattaba wa qorafin hannu a ranar 10 ga watan Agustar 2015. Qungiyar ta zargi Sanata Wamakko, wanda ya yi gwamna daga shekarar 2007 zuwa 2015 da laifin yin sama da faxin dukiyar raya jihar, inda yayi ta ayyukan gaban kansa da su. Wata Majiya daga hukumar EFCC ta sanar da LEADERSHIP A Yau cewa, hukumar ta bankaxo yadda aka zuba naira biliyan 1.5 cikin asusun ajiyan bankin Sanata Wamakko. “Mutane uku mabambanta ne suka zuba waxannan kuxaxe, waxanda kuma ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Sakkwato ne, waxanda har zuwa yanzu ba a gano ko su waye ba.” Majiyarmu ta ce kuxaxen an zuba su ne a asusun ajiyan Wamakko daga shekarar 2012 zuwa 2015, sannan kuma hukumar EFCC na shiryeshiryen gayyatar Wamakko

kowanne lokaci daga yanzu domin ya amsa tambayoyi. Haka kuma Hukumar ta EFCC ta amshi wani qorafin daga Barista Mustapha Danjuma a madadin Abubakar Ali Maishani da Alhaji Najume Garba Kabo, waxanda suka shigar akan zargin tarwatsa kuxaxen qananan hukumomi 44 na Jihar Kano wanda Kwankwaso ya yi.

Majiyarmu ta shaida mana cewa, a lokacin bin sahun batun, hukumar EFCC ta samu risixan fitar da kuxi, wanda ke nuni da cewa kowacce qaramar hukumar daga cikin 44 xin da ake da su a Kano sai da ta bayar da gudummawar miliyan 70 ga takarar shugabancin Qasar Kwankwaso. Sannan kuma majiyar ta shaida mana cewa, Hukumar

EFCC za ta bi diddigin asusun da aka zuba waxannan kuxaxe. Sannan kuma nan ba da jimawa ba za a gayyaci Kwankwaso don bincikensa. Mai magana da yawun hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya sanar da LEADERSHIP A Yau ta wayar tarho cewa, hukumarsu na kan binciken waxannan tsoffin gwamnoni biyu.

Har Yanzun Akwai Katin Jefa Quri’a Milyan 7.9 Da Ba A Karva Ba –INEC Daga Umar A Hunkuyi

Hukumar zave mai zaman kanta ta qasa, (INEC), ta ce, a yanzun haka akwai katunan jefa quri’a guda 7,920,129, waxanda masu su ba su zo sun karva ba a Ofisoshinta na cikin qasarnan. Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata takardar bayanai da ta fitar a Abuja,

ranar Talata. Takardar bayanan ta nu na, ya zuwa watan Maris 2018, Jihar Legas ce ta fi yawan katunan zaven da ba a karva ba, inda take da katunan zave, 1,401,390; sai Jihar Oyo, 647,586; da Jihar Edo, 449,001, Jihar Kano ita ma tana da katuna, 195,941, a qasa. Takardar ta nu na Jihar

Bauci ce take da qarancin katunan zaven da ba a karva ba, inda take da katuna, 15,542, a qasa, sai Jihar Bayelsa da Flatau, masu katuna, 28,533 da 25,300, bi-da-bi. Hukumar kuma ta bayyana cewa, ya zuwa yanzun ta raba katunan zaven guda, 351,272, a Jihohi 36 har da babban birnin tarayya,

a tsakanin shekarar 2015 zuwa watan Maris na shekarar 2018. Ta ce, an karvi katunan zaven, 230,175 daga cikin, 351,272 a shekarar 2017 sauran, 121,097 kuma an karve su ne a shekarar, 2018. Jihar da aka fi karvar katunan zaven a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2018, ita ce, Jihar Anambra, inda

aka karvi katuna, 102,264. Jihohin Kogi da Legas na biye da katuna, 41,174 da 20,002, bi-da-bi. Jihohin da aka karvi katunan ma fi qaranci su ne, Jihohin Zamfara, guda arba’in ne kacal aka amsa, sai Taraba, an amshi guda 158 ne kacal, Bauci, an amshi guda, 558, ne in ji Hukumar.

Sanya Ni Cikin Varayin Qasa, Vata Suna Ne –Secondus Daga Umar A Hunkuyi

Shugaban Jam’iyyar PDP na qasa, ya ce, zargin da ake yi na cewa, yana cikin mutanan da suka handame dukiyar qasarnan qoqarin vata suna ne kawai. A cikin bayanin da mai ba shi shawara kan harkokin manema labarai, Ike Abonyi, ya sanya wa hannu, Mista Secondus, ya ce, duk wani qoqarin vata suna da tursasawa daga abokan adawa na gwamnatin tarayya ba za su hana shi ci gaba da qoqarin da yake yi na sake farfaxo da Jam’iyyar na shi ba. “Ofishin hulxa da manema labarai na Shugaban Jam’iyyar PDP, Uche Secondus, ya lura da yunqurin da gwamnatin

tarayya da kuma Jam’iyyar ta ta APC ke yi na neman vata ma sa suna da wasu qagaggun bayanai da nufin taka masa burki a qoqarinsa na sake xinke Jam’iyyar sa.” Ofishin yaxa labaran na shi ya ce, “Mista Secondus, ba zai so tsayawa cacan baki da gwamnatin ba, kan lamarin da yake a gaban kotu, “Amma abin takaici sai ga shi, gwamnatin tana raina umurnin kotu tana kuma taka doka yadda ta ga dama, ta tsaya da neman vata suna a kafafen yaxa labarai, domin ta vata shaksiyar abokanin adawanta.” Wannan gurguwar dubarar ta su ba ta yi nasara ba, domin kuwa ‘yan Nijeriya sun fahimci gurguwar dubarar ta gwamnatin da ke shirin

valvalcewa. “A yunqurin na su na neman ko ta wace hanya su vata masa suna, sun kasa ma daidaita alqalumman na su na qarya, Ministan yaxa labarai, Lai Mohammed, ya kasa bayyana ranar da ya ce an karvi kuxaxen da yake qoqarin yin qagen a kansu, sannan kuma ya kasa bayyana wa ya karvi kuxin, Secondus ne ko kuma mutumin da babu shi ne da yake laqabawa suna, Chukwura, wanda ya ce bai san sunan uban shi ba. “Tun a shekarar 2015 suke qoqarin binciko sunan mahaifin mataimakin qaryan da suke cewa wai na Secondus xin, a wata ganawar sa da manema labarai ranar 29 ga watan Maris 2018, Lai Mohammed,

cewa ya yi, Secondus, ya karvi kuxaxen ne ranar 19 ga watan Fabrairu 2015, su kuma hukumar EFCC, suka ce, an karvi kuxin ne a ranar 9 ga watan Fabrairu 2015, a wani qaulin na hukumar ta EFCC, kuma cewa suka yi ranar 2 ga watan na Fabrairu ne aka karva. Shugaban na PDP, ya bayyana takaicin sa, da haxarin da ke tattare da yadda hukumar ta EFCC, wacce ya kamata a ce tana yaqi ne da masu neman kashe tattalin arzikin qasa, sai ga shi tana zama wata shirwan gwamnatin APC, da ake amfani da ita wajen farautar ‘yan adawa. Ya kuma qalubalanci gwamnatin ta APC da duk wata hukuma da ke da

rahoton wata tavargaza ko satan da ya yi, da ta zo su gamu a kotu da cikakkun shaidun ta, ba a tsaya a kafafen yaxa labarai ba. “Ba bukatar yin magana cikin jaridu kan abin da yake gaban kotu. Idan gwamnati tana da wata magana, kamata ya yi su nufi kotu kawai.” “Ni ban karvi kwabo daga hannun kowa ba. Ban kuma sanya wani ya karvan mani kuxi ba, ban kuma sanya hannu kan kowace takardar karvan kuxi ba. Qoqarin vata suna ne kawai, ba kuma zai yi aiki ba. “Ba wani vata sunan da za su yi wa mutane da zai sanya APC ta sake cin zave, bayan mutane sun gano su sun kuma yi watsi da su, 2019 kawai muke jira.


A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Ku kasance tare da tawagar OCTOPUS a shafin sadarwa na Telegram

TALLA 5


6 LABARAI

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Jonathan Ne Silar Wahalhalun Da Ake Sha A Nijeriya –Tinubu Daga Umar A Hunkuyi Ya ce, a tun shekaru uku da suka shuxe, gwamnatin APC tana ta qoqarin wanke datti ne ta yadda al’umma za su sami sabuwar madafa. Shugaban na APC ya ce, “Akwai yiwuwar gwamnatin ta APC ta aikata kuskure a wasu lokutan, a karantarwa irin ta Malam Aminu Kano, amma dai mun xarar ma Jam’iyyar PDP, wacce ba ta tsare komai ba sai satan dukiyar al’umma. “Gwamnatin APC tana ta qoqarin karkato da Nijeriya ne daga mummunar hanyar da akaxora ta, domin mutanan mu su sami sauqi. “Idan da a ce an yi amfani da milyoyin daloli da bilyoyin Nairorin da aka sace a gwamnatocin baya, da yanzun qasarnan tana taqama da wasu manyan ayyuka na a zo a gani.

•Tinubu

Gwamnatin Tarayya Ta Himmantu Kan Ceto Harsunan Nijeriya Daga Vacewa Daga Umar A Hunkuyi Gwamnatin Tarayya, ta sha alwashin xaukan duk matakan da suka dace na ganin ta ceto harsunan Nijeriyan da ke ta qara dushewa da nufin ganin ba su kai ga vacewa ba, inda take qarfafa koyar da su a makarantun qasarnan. Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ne ya faxi hakan ranar Talata a Abuja, lokacin da yake buxe taron da aka yi wa laqabi da, “Enabling Writers: Bloom Software Training of Trainers workshop” wanda

cibiyar ciyar da Ilimi gaba ta Afrika, (ADEA) ta shirya, tare da haxin hannun Kamfanin, ‘Global Book Alliance (GBA) da United States Agency for International Development (USAID). Ministan ya ce, wannan gwamnatin ta Shugaba Buhari, tana yin duk abin da ya dace domin ta farfaxo gami da inganta al’adar karatu da rubutu a Nijeriya. Don haka, sai ya qalubalanci marubutan qasarnan da su riqa yin rubutun na su da harsunan qasarnan, wanda hakan zai

qara samar da yawan littafan karatu da harsunan cikin gida. Ministan, wanda Daraktan tsare-tsare da bincike na ma’aikatar ta ilimi, Dakta Chioma Nwade, ya wakilce shi, ya ce, hakan zai janyo hankulan matasan qasannan wajen iya karatu da rubutu da harsunan su, wanda hakan zai ceto harsunan Nijeriya da ma na Afrika daga vacewa. Ya bayyana dagewan da gwamnatin tarayya ta yi wajen samar da wadatattu kuma isassun kayan karatun da suka dace a makarantu, ya ce hakan

kuwa ba zai tabbata ba, ba tare da kayan aikin da suka dace ba, na littafai da sauran kayan aiki. Babban mai jawabin na ADEA, xin, Lily Nyariki, daga qasar Kenya, a jawabin na ta, ta bukaci gwamnatin qasarnan da ta havaka al’adar nan ta karatun littafai domin qarfafa al’adar ta rubutu da karatu a cikin qasarnan. Ta yi jimamin sakamakon binciken da aka yi a yanzun haka, wanda ya nu na cewa, yara 15 ne suke fafutukar yin karatu da littafi guda a makarantunmu. Ta qara da cewa, ya kamata

marubutan Afrika su samarwa da nahiyar matsayi ta hanyar yin rubututtukan na su da harsunan nahiyar. Shugaban qungiyar marubuta ta qasa, (ANA), Denja Abdullahi, cewa ya yi, xaya daga cikin babban matsalar marubutan na Afrika shi ne, ayyukan masu satar fasaha, wanda a cewarsa, hakan ya shafi ayyukan qungiyar marubutan na qasarnan matuqa. Ya ce, qungiyar shi a yanzun haka tana yin aiki tare da hukumar hana satar fasaha domin magance matsalar.

Mai Talla Shi Ke Da Riba:

LEADERSHIP A YAU Ta Shirya Tsaf! Kamar yadda kowa ya sani ne, wannan jarida mai albarka, LEADERSHIP A YAU ta kafa tarihi wajen zama jaridar Hausa da ta fara fitowa a kullum. Wannan fara fitowa a kullum yana da alfanu masu yawan gaske, gare mu Kamfanin LEADERSHIP da ku masu karatu, musamman masu sana’o’i manya da qanana. Wannan ne ya sa muke farin cikin shaida wa masu karatunmu cewa mun shirya tsaf domin tallafa wa kasuwancinku, ta hanyar tallata maku shi zuwa inda ba ku zata ba. Domin a halin yanzu mu kanmu da muke buga wannan jarida ba za mu iya bayyana iya inda ta ke shiga ba. Muna da tsare-tasare da dama don talla ku da hajojinku, inda muka fitar da tsarin ‘IYA KUXINKA IYA SHAGALINKA.’ Wato akwai cikakken shafi, akwai rabi, akwai kwata, akwai kuma daidai iyaka abin da mutum ke so a sanya masa. Wanda a wannan shafin muna so masu sana’o’i, musamman manyan dillalai su tallata hajojinsu, su qananan ’yan kasuwa akwai

nasu tsarin. A wani tsarin ma da muke da shi, akwai yanayin da mutum zai tallata hajarsa, sannan ya tallata kansa, inda za a sanya hoton shagonsa, hotonsa da kuma taqaitaccen tarihinsa, kuma wannan duk a kuxi kaxan. Maza ku kasance cikin kashi na farko na masu cin moriyar wannan shiri. Ina ’yan Canji, dillalan yaduka, masu kayan masarufi, mayan da qananan ’yan tireda, dillalan magunguna, masu kamfoni da masana’antu, dillalan hatsi, dillalan mota, masu sayar finafinai da dai sauran masu sana’o’i, ga dama ta samu. A tuntuvemu a lambarmu ta 08148507210, 07036666850, 08039216372, 07037934034, 08032875238 da 08038011382: email leadershipayau@gmail.com. Ko kuma a tuntuvi wakilanmu na jihohi don qarin bayani.


A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku

Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku

Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.

Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com

TALLA 7


8 TALLA

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Domin Qarin Bayani A Tuntuvi: • Mubarak Umar – 0703 6905 380 •Sulaiman Bala Idris –0703 6666 850


A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

TALLA 9

Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”

Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.


10 LABARAI

A Yau

Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

•Mataimakin Shugaban Qasa, Farfesa Yemi Osinbajo a jiya yayin da ya jagoranci zaman majalisar zartaswar tarayya a fadar shugaban qasa dake Abuja

’Yan Jarida Sun Gudanar Da Rangadi Kan Ayyukan Ci Gaban Gwanmnatin Kaduna Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

Qungiyar ‘Yan jaridu ta Jihar kaduna qarqashin jagorancin Kwamared Adamu Yusuf, ta fara wani rangadin zagayen ayyukan ci gaba da Gwamnatin Jihar kaduna, qarqashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed El-rufai, ta gudanar a xaukacin Qananan Hukumomi 23 dake faxin Jihar kaduna. A yayin da yake jawabi jim kaxan da kammala ganin wasu ximbin ayyukan ci gaba da gwamnatin Jihar kaduna qarqashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed El-rufai, ta gudanar a ciki da wajen Jihar kaduna, Babban Sakataren Ma’aikatan Ayyuka ta Jihar kaduna, Malam Murtala Dabo, ya bayyana irin ximbin ayyukan ci gaba da wannan gwamnatin ta xauko yi ma Al’ummar wannan jiha, duk da kasancewar gwamnatin na fuskantar barazanar rashin kuxaxxen ci gaba da gudanar da irin waxannan manyan ayyukan ci gaban Al’umma. Malam Murtala Dabo, ya qara da cewa daga cikin kuxaxxen da gwamnatin ke tsammanin samu domin qarasawa da kuma sabbinta wasu manyan ayyuka da gwamnatin ta xauko, sun haxa da bashin Dalar Amurka Miliyan 350 da Gwamnatin Jihar kaduna ta naima daga Babban Bankin Duniya, wanda rashin samun wannan bashi na naiman ya haifarwa ayyukan ci gaban jihar tafiyar Hanwainiya. Babban Sakataren ya

qara da bayyana cewa, Gwamnatin Jihar Kaduna qarwashin jagorancin Gwamna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’I, na da tabbacin cewa za ta samu wannan bashi daga Bankin Duniya duk da tarnaqi da wasu Sanatoci suka haifar akan batun, kuma a fili yake babban burin Gwamnatin Jihar Kaduna shi ne, xaga martaba da kuma dawo da darajar Jihar Kaduna, yadda zata zama Zakaran gwajin dafi a tsakanin sauran jihohi 36 dake faxin qasar nan. Gwamnatin Jihar Kaduna dai ta xauko ayyuka na sabunta tituna a dukkanin faxin Qananan hukumomin Jihar 23 dake faxin Jihar

kaduna. Daga cikin wuraren da tawagar qungiyar ‘Yan jaridu ta ziyarta sun haxa da Unguwar Tudun Wada, inda Al’ummar Unguwar suka dai shaidawa Tawagar cewa wannan gadar da suka ziyarta an ginata ne tun zamani Sardauna Firimiyan Arewa, amma ta karye ba a samu wanda zai Gina ta ba sai a yanzu da Gwamna El-Rufa’i ya kammala aikin baki xaya. Sun qara da bayyana cewa, “Wannan gadar a can baya har akan raba aure saboda babu hanyar da za a wuce idan miji da mata na vangare daban daban shi kenan, amma yanzu kamar

an yi ruwa an xauke, Malam Nasiru Tuni ya kammala mana ita wanda dalilin hakan Mayanka dabbobi ta zama kullum sai san barka muke yi.” Inji jama’ar yankin. Shi ma a na sa vangaren Sarkin Fawan Kaduna, Alhaji Suleiman Sabo, ya jinjinwa Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i, sakamakon wannan namijin qoqarin da ya aiwatar na wannan makekiyar Gada mai ximbin tarihi da kuma tasiri mai yawa kasancewarta hanya ce ta Mayanka dabbobi. “Haqiqa wannan hanya ta haxa ximbin al’ummar wannan yankin na Tudun

wada da kuma mutanen qaramar hukumar Kaduna ta kudu domin suna amfani da ita sosai”. Inji An dai gina wannan katafaren aikin titi tare da Gada da kuma hanyoyin ruwa mai tsawon mita xari 375 da mita 100 na hanyoyin ruwa, dukkansu an yi aikin ne a kan kuxi Naira Miliyan xari da biyar. Tawagar manema labaran ta Kuma ziyarci wurare irin su Barnawa, Unguwar Rimi, Rafin Guza, Unguwar Sabon kawo, da katafaren titin ‘Yan Majalisu dake Unguwar Dosa, da kuma wurin ajiye manyan motoci na Marabar Jos, da Gwamnatin Jihar kaduna ke gudanarwa.

Za Mu Ci Gaba Da Haxa Kan Vangarorin Tsaro Domin Kyautata Tsaro -Sarkin Bauchi Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Masarautar Bauchi ta bayyana cewar za ta yi aiki kafaxa-kafaxa da fannonin jami’an tsaro domin inganta tsaro da kuma zaman lafiya a faxin jihar ta Bauchi. Mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji (Dakta) Rilwanu Sulaiman Adamu ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da ya amshi baqoncin hukumomin gudanarwa na kwalejin nazarin ilimin tsaro da ke Abuja a fadarsa da ke Bauchi a makon jiya. Dakta Rilwanu Suleiman Adamu ya buqaci masu

samun horo kan hidimar tsaron da su tabbatar da yin duk mai iyuwa wajen inganta hidimar tsaro a faxin qasar nan domin ingatawa gami da samar wa qasar Nijeriya dauwamammiyar zaman lafiya a Nijeriya. Sarkin ya bayyana cewar masarautar Bauchi za ta ci gaba da himmatuwa wajen wayar wa jama’an jihar kai dangane da muhimmancin zaman lafiya a tsakanin jama’a domin samar da jama’a ta gari a kowani bigire. A sakamakon yaqi da ake yi da masu haifar da rikicin ta’addanci a shiyyar Arewa

Maso Gabashin qasar nan, Rilwanu Suleiman Adamu ya jinjina wa ci gaban da ake samu da kuma irin gudunmawar da shugaban qasa Alhaji Muhammadu Buhari ya ke bayarwa domin shawo kan matsalar tsaron a wannan yankin. A na sa vangaren, Darakta a cibiyar nazarin ilimin tsaro da ke Abuja, (Institute for Security Studies Abuja) Dakta Mathew B Seiyefa ya nuna matuqar jin daxinsa da gamsuwarsa a bisa yadda ya samu zaman lafiya na samun tagomashi gaya a jihar ta Bauchi, sai ya jinjina wa Sarkin garin a

bisa qoqarinsa da kuma gudunmawarsa wajen tabbatar da doka da oda a tsakanin al’umma. Dakta Mathew Oseiyefe ya bayyana cewar majalisun sarakuna suna da gagarumar rawar takawa wajen faxakawa da kuma ci gabantar da zaman lafiya, tsaro, kiyaye rayuka, kawo zaman lafiya, tabbatar da bin doka da oda a tsakanin jama’a a kowani lokaci. Ya yaba sosai a bisa yadda ya ga Sarkin na Bauchi na qoqarin bayar da dukkanin gudunmawarsa wajen haxaka kan jama’an jiharsa domin karesu daga faxawa matsaloli.


LABARAI 11

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Kotun Xa’ar Ma’aikata CCT Za Ta Saurari Qararraki A Bauchi Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Kotun xa’ar ma’aikatan Nijeriya wato CCT za ta gudanar da zamanta domin sauraron qararrakin da suke gabanta kan ma’aikata da kuma masu riqe da muqaman siyasa da suka gaza bayyana qaddarorinsu na haqiqa a jihar Bauchi. Zaman da korun za ta yi a jihar Bauchi zai gudana ne a tsakanin ranakun 24 zuwa 27 na watan Afrilun da muke ciki. Hakan yana qunshe ne a cikin wata sanarwa daga kotun xa’ar ma’aikatan, wacce Ahmad Abdullahi ya sanya wa hanu a madadin jami’in da ke kula da harqoqin kotun ta CCT a jihar Bauchi, sanarwar wacce aka raba wa ‘yan jarida a Bauchi. Sanarwar ta kuma ce shugaban kotun CCT, Mai Shari’a Xanladi Umar shine zai jagoranci zaman na kotun domin sauraron shari’un haxe da yin aikinsu yadda kotun take tafiya a kai. Kotun dai za ta saurari qararraki akan masu riqe da muqaman siyasa haxe da ma’aikatan gwamnati waxanda suka gaza bayyana qaddarorinsu wa hukumar kula da xa’ar ma’aikata haxe da waxanda suka buye gaskiyar kaddarorin da suka mallaka na haqiqa a hukumar. Kotun dai za ta gayyaci dukkanin waxanda abun ya shafa domin kare kai daga qararsu da aka yi.

Gwamnatin Tarayya Ta Himmantu Kan Ceto Harsunan Nijeriya Daga Vacewa Daga Umar A Hunkuyi

Gwamnatin Tarayya, ta sha alwashin xaukan duk matakan da suka dace na ganin ta ceto harsunan Nijeriyan da ke ta qara dushewa da nufin ganin ba su kai ga vacewa ba, inda take qarfafa koyar da su a makarantun qasarnan. Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ne ya faxi hakan ranar Talata a Abuja, lokacin da yake buxe taron da aka yi wa laqabi da, “Enabling Writers: Bloom Software Training of Trainers workshop” wanda cibiyar ciyar da Ilimi gaba ta Afrika, (ADEA) ta shirya, tare da haxin hannun Kamfanin, ‘Global Book Alliance (GBA) da United States Agency for International Development (USAID). Ministan ya ce, wannan gwamnatin ta Shugaba Buhari, tana yin duk abin da ya dace domin ta farfaxo gami da inganta al’adar karatu da rubutu a Nijeriya. Don haka, sai ya qalubalanci marubutan qasarnan da su riqa

yin rubutun na su da harsunan qasarnan, wanda hakan zai qara samar da yawan littafan karatu da harsunan cikin gida. Ministan, wanda Daraktan tsare-tsare da bincike na ma’aikatar ta ilimi, Dakta Chioma Nwade, ya wakilce shi, ya ce, hakan zai janyo hankulan matasan qasannan wajen iya karatu da rubutu da harsunan su, wanda hakan zai ceto harsunan Nijeriya da ma na Afrika daga vacewa. Ya bayyana dagewan da gwamnatin tarayya ta yi wajen samar da wadatattu kuma isassun kayan karatun da suka dace a makarantu, ya ce hakan kuwa ba zai tabbata ba, ba tare da kayan aikin da suka dace ba, na littafai da sauran kayan aiki. Babban mai jawabin na ADEA, xin, Lily Nyariki, daga qasar Kenya, a jawabin na ta, ta bukaci gwamnatin qasarnan da ta havaka al’adar nan ta karatun littafai domin qarfafa al’adar ta rubutu da karatu a cikin qasarnan. Ta yi jimamin sakamakon binciken da aka yi a yanzun haka, wanda ya nu na cewa,

•Hon Lawali Hassan Anka

yara 15 ne suke fafutukar yin karatu da littafi guda a makarantunmu. Ta qara da cewa, ya kamata marubutan Afrika su samarwa da nahiyar matsayi ta hanyar yin rubututtukan na su da harsunan nahiyar. Shugaban qungiyar marubuta ta qasa, (ANA), Denja Abdullahi, cewa ya

yi, xaya daga cikin babban matsalar marubutan na Afrika shi ne, ayyukan masu satar fasaha, wanda a cewarsa, hakan ya shafi ayyukan qungiyar marubutan na qasarnan matuqa. Ya ce, qungiyar shi a yanzun haka tana yin aiki tare da hukumar hana satar fasaha domin magance matsalar.

NSCRA Ta Cafke Xan Shekaru 70 Da Zargin Yi Wa Qananan Yara Fyaxe A Neja Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Hukumar kula da haqqin yara (Niger State Child Right Agency) a jihar Neja ta cafke Abdullahi Umar xan kimanin shekaru saba’in da biyar da haihuwa wanda aka fi sani da suna Malam bisa zargin yi wa qananan yara fyaxe a Tungan Maje cikin garin Minna da ke qaramar hukumar Chanchaga. Da ta ke qarin haske ga manema labarai, babbar daraktan hukumar, Barista Mariam Haruna Kolo, tace a safiyar littinin xin makon nan ne aka zo wa hukumarta da qorafin Abdullahi Umar ya tara da yarinya ‘yar shekara tara da haihuwa. Bayan samun nasarar cafke shi ne suka miqa shi hannun jami’an ‘yan sanda masu binciken miyagun ayyuka dan bincike akan lamarin. Washe gari talata kuma sai ga wani qorafi akan shi na qarin wasu yaran gida biyu ‘yan kimanin shekaru bakwai da haihuwa waxanda suma ake zargin

•Gwamnan Jihar Neja

yana lalata da su. Wani jami’in hukumar da ya nemi a sakaya sunansa, ya yiwa wakilin mu qarin haske, inda ya ce wanda ake zargin ya daxe yana vata qananan yara ta hanyar kwantawa a jikinsu yana sanya masu yatsa a cikin al’aura. Ya ce amma ita ‘yar shekara taran da abin ya rutsa da ita ya sha kwanciya da ita ta hanyar

jima’i. Ya cigaba da cewar yaran da abin ya rutsa da su sun ce ya kan ba su naira goma a duk lokacin da yayi baxalar da su. Binciken da wakilin mu ya gudanar ya gano cewar an daxe ana zargin wannan bawan Allah da wannan ta’asar wanda yanzu haka jami’an ‘yan sanda na kan bincikensa na cewar ya bar gidansa ya zama mahaxa na ‘yan mata da matan

aure masu shaye-shaye. Yana dai zaune a wannan unguwa sama da shekaru ashirin da biyu yana sana’ar wani da guga. Da take qarin haske kan lamarin, Barista Mariam Haruna Kolo ta jawo hankalin Iyaye da su kula da tarbiyar yara da ganin sun kashe tallacetallace ga yara mata. Tace rashin kulawar Iyaye yasa yara ke faxawa a wannan taskun, game wannan tsohon kuwa mun miqa shi a hannun CID dan suke da ikon bincike idan sun kammala kuma an same shi da laifi zamu miqa shi kotu. Hukumar mu ba za ta sanya Ido hakan na gaba da faruwa ga qananan yara ba, duk wanda ya shiga komar mu tabbatar mun tsaya tsayin daka wajen ganin an hukunta shi. Don haka a kowani lokaci mai girma gwamna yana ba mu haxin kai ta yadda zamu gudanar da aikin mu ba tare da tangarxa ba, mun tsayu kuma tsaya tsayin daka wajen bin haqqoqan yara qanana.


12 LABARAI

A Yau

Kashe-Kashen Taraba: Sojoji Na Neman Mutum Biyar Ruwa A Jallo Daga Bello Hamza

A ranar Larabar nan ne rundunar sojojin Nijeriya ta aiyana neman mutum 5 ruwa a jallo dangane da hannun da suke dashi a kashe kashen daya auku a qaramar hukumar Takum dama sauran sassan jihar Taraba baki xaya. Waxanda ake neman sun haxa da Tanko Adiku Dantayi da Kurusi Danladi da Chindo da Big Olumba da kuma Chairman Poko. Jami’in wasta labaran rundunar sojojin Brigadia

Janar Texas Chukwu ne ya bayyana haka a wata sanarwa daya saw a hanunn, ya kuma buqaci al’ummar jihar das u miqa duk wani bayanin da zai taimaka wa jami’an wajen cafke mutanen ga hukumar tsaro mafi kusa dasu. Kanfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, rundunar sojojin Nijeriya ta sanar da mutum 2 da suka kissa kashe kashen da aka yi a qananan hukumomin Takum da Ussa ta jihar Taraban. Waxanda aka kama sun haxa da Mista Danjuma da Mista Danasebe Gasama.

Jami’in wasta labaran. Brigadia Janar Chukwu, Danjuma, ya ce, an kama wanda a kan kira da suna American da Gasama ne ranar Jumma’a a yayin da jami’an sojoji na rundunar “Operation Ayem Akpatuma” ke sintiri a yankin Takum, bayan da suka samu bayanan asiri na mavoyaer mutanen. Ya qara da cewa, binciken farko da aka gudanar ya nuna waxannan mutanen a matsayin waxanda suka jagoranci ta’addancin da aka yi a qananan hukumomin biyu.

Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Qungiyar Akantoci Ta Qasa Ta Kai Wa Gwamna Masari Ziyara Daga Sagir Abubakar, Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya nanata buqatar dake akan qwararru na hukumomi su yi amfani da qwarewarsu don cigaban qasar nan. Gwamnan ya faxi haka ne lokacin da ya amshi baquncin shugaban qungiyar akantoci ta qasa (ANAN) Alhaji Shehu Ladan daya ziyarceshi a gidan gwamnati. Ya bayyana cewa shirin ciyar da qasar nan gaba ba zai samu nasaba ba tare da gudummuwar hukumomi na qwararru ba. Gwamnan ya ce matsayin akantoci shi ne wakilan al’umma ne akan kuxaxe inda yace su kasance a sawun gaba don samun nasarar gwamnatin shugaban qasa Muhammadu Buhari na yaqi da cin hanci da cigaban qasar nan. Ya buqacesu da su

zage damtse don hana sace kuxaxen al’ummaa ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati a lokacin da gwamnatinsu na yaqi da cin hanci da rashawa. Tun farko shugaban qungiyar akantoci ta qasa Alh. Shehu Ladan yace sunzo jihar Katsina ne don gudanar da taron qungiya na shekarar 2018. Ya yabawa gwamna Aminu Bello Masari game da biyan kuxin qwarewa ga yan qungiyar na jihar Katsina. Sannan ya jinjinawa gwamna game da xaukar nauyin mambobin qungiyar don zuwa taron qarawa juna sani a ciki da wajen jihar nan da kuma bada fili don gina ofishin qungiyar da sauransu. Shugaban qungiyar ya yaba da irin nasarorin da gwamnan jihar Katsina ya samu a vangaren ilimi, lafiya, aikin gona, samar da tsaro da sauransu.

Za A Gudanar Da Maulidin Annabi Na Hilaqu Zikrullahi A Garin Kurgwi Jihar Filato Daga Muazu Hardawa, Bauchi

•Gwamnan Jihar Taraba

Hukumar Ilimin Bai Xaya Ta Yi Taro A Katsina Daga Sagir Abubakar, Katsina

An gudanar da taro domin tsara yadda kwamitin aiwatarwa na jiha akan tattara bayanai a hukumar ilimin bai xaya ta jiha zai gudanar da aikinsa a nan Katsina. Shugaban hukumar Alhaji Lawal Buhari Daura ya bayyana cewa hukumar ilimin bai xaya ta qasa ita ce ta bayar da umurni ga hukumar ta gudanar da shirin da nufin tattara bayanai. A cewarsa bayanan sun fara gano yawan malamai masu koyarwa da waxanda basu koyarwa a dukkan makarantun dake qarqashin hukumomin kula da ilimin bai xaya dake faxin qasar nan. Ya nemi haxin kan dukkan masu ruwa da tsaki domin samun nasarar shirin. Tun farko, shugaban kwamitin aiwatarwa na jiha, kuma daraktan mulki da saye-saye na hukumar

Alhaji Halliru Duwan ya bayyana cewa domin samun nasara, hukumar ta shirya wata horaswa ta musamman ga mambobin kwamitin da kuma sauran ma’aikata wanda jami’an hukumar ilimin bai xaya ta qasa zasu gudanar a ranar litinin mai zuwa. A jawabinshi mataimakin Daraktan tsare-tsare da qididdiga Hajiya Zainab Kaita ta bayyana cewa shirin ya haxa da samar da muhimman bayanai da kuma da samar da muhimman bayanai da kuma buqatar da ke akwai na ayi bincike akan ilimin bai xaya a Nijeriya. Ta bayyana cewa wasu matsaloli sun hana a gudanar da shirin a watan Afrilu na shekarar data gabata kamar yadda aka shirya a wani labarin kuma shugaban hukumar ilimin bai xaya ta jihar Katsina Alhaji Lawal Buhari Daura tare da wasu Daraktoci da sauran ma’aikatan hukumar sunyi jaje ga iyayen Bello

Salisu xalibi xan aji 6 xan makarantar Morawa Primary dake qaramar hukumar Vatagarawa. An samu labarin cewa jami’an hukumar hana fasa qwabri ta qasa sun harbi yaro a lokacin da suke qoqarin kama wani wanda suke zargi da fasa qwabrin shinkafa. Shugaban hukumar ya bayyana harbin yaron da abun takaici kuma ya roqi Allah ya bashi lafiya. Ya shawarci jami’an hukumar hana fasa qwabri da ako da yaushe dasu riqa bin doka wajen kama masu fasa qwabrin a maimakon harbi cikin jama’a. Haka kuma a wani labari shugaban hukumar yaje garin XanAli inda ya jajanta ma wasu ma’aikatan hukumar waxanda suka samu haxarin mota akan hanyar Kabomo zuwa Funtua. Ma’aikatan hukumar 2 sun samu raunuka, yayin da ma’aikata 2 daga hukumar ilimin bai xaya ta qasa suka sami karaya a hannuwansu.

A ci gaba da gudanar da Maulidin tunawa da manzo (SAW) da Sheikh Ibrahim Inyas wanda ake gudanarwa duk shekara a garin Kurgwi da ke qaramar hukumar Quanpan a Jihar Filato a bana ma qungiyar Hilaqu Zikrullahi ta matasa masu zikiri na qasa a qarqashin jagorancin babban naqo muqaddamin xariqar tijjaniyya a Nijeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, za a gudanar da taron maulidin daga ranar juma’a 20 ga watan Aprilu zuwa wayewar garin asabar. Sheikh Abdurrahman Zakariyya Khalifa Kurgwi sakataren qungiyar Hila’u Zikrullahi na qasa wanda ke shirya taron Maulidin a zawiyyar garin na Kurgwi cikin hirar sa da wakilin mu ya bayyana cewa tun ranar juma’a za a fara gudanar da wannan bikin Maulidi inda za a zagaya garin na Kurgwi a safiyar juma’a don jaddada ambaton Allah maxaukakin sarki tare da yabon manzo mai tsira da aminci. Bayan haka kuma za a ci gaba da karatu har zuwa dare inda baqi za su shigo garin yadda za akwana ana wa’azi da yabon manzo (SAW) da

kuma zikiri kamar yadda ake gudanarwa a duk shekara. Shugaban taro shi ne Alhaji Abdullahi Aliyu Agwai dan majen Lafiya Uban taro kuma shi ne Maimartaba sarkin Kanem kuma uba qungiyar Hilaquziikri na Jihar Filato Alhaji Muhammad Babangida Muazu na biyu. Manyan baqin da za su halarci wurin taron kuma sun haxa da Farfesa Abdulhamid Garba Sharubutu da Dokta Mohammed Bashir Yusuf da Malam Sulaiman Muhammad da Alhaji Idris Ismail Wali Kano da Sharif Rabi’u Usman Baba Kano da Sheikh Alhaji Aliyu Alhassan Kurgwi. Cikin jawabinsa ga manema labarai Sheikh Abdurrahman Kurgwi ya bayyana cewa taron na bana zai mayar da hankali wajen ganin an haxa kan musulmi tare da taimakon addinin musulunci da kuma yi wa a’umma da qasa baki xaya addu’ah domin samun qaruwar ingancin zaman lafiya a Nijeriya baki xaya. Don haka ya yi fatar duk wanda za su halarci taron su zo lafiya su koma gidajen su lafiya.


LABARAI 13

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Za Mu Xauki Matakin Hukunta Waxanda Suka Jefi Gwamna A Sansanin Gudun Hijira –Kwamishinan Yan Sanda Daga Zubairu T. M. Lawal , Lafia

Kwamishinan Yan Sandan Jihar Nasarawa Ahmad Bello ya ce, ya zuwa lokacin zantawa da manema labarai ba su kama kowa ba amma nan bada daxe wa ba za su zaqulo waxanda sukayi wanan aika aikan a hukunta su. Kwamishinan ya ce; waxanda suka aikata wannan xanyen aikin ba a cikin yan gudun hijira suke ba sun dai shiga rigar yan gudun hijirar ne suke aikata xanyen aiki. Ya kara da cewa ; yan gudun

hijira iyakar yadda suke shi ne filin makaranta amma waxanda suka zo suka tsare hanya suna jifa da dutse ba yan gudun hijira bane. Wanan dalili ne ya sanya ‘yan sanda suka xauki matakin korarsu ta hanyar yin amfani da barkonon tsohuwa saboda doka ce ta ce duk wanda ya tare hanyar Gwamnati to ko waye Jami’an tsaro sun hukunta shi. Ya ce, “haqqin Jami’an tsaro ne su kare Gwamna saboda hakin kulawanshi yana qarqashin su. Gwaman ya je wannan wuri ne da nufin duba

yan gudun hijira lokacin da Gwamana ya fara jawabi sai muka ga hayaniya yayi yawa shiyasa mukabada umurnin abar gurin saboda sha’anin tsaro.” Kwamishinan ya kara da cewa, wasu na ganin cewa lokacin da ake kashe-kashen Jami’an tsaro ba su je wurin ba ya ce, “Ai mu ba Allal musuru gare mu ba idan abu ya faru sai an sanar damu muke sani idan aka sanar damu sai mu shirya gamayyara Jami’an tsaro da zamu tura domin kawo sauqin lamarin.”

•A yayin da ‘yan gudun hijirar ke yiwa gwamna ihu

Amma abin da ba a sanar da kai ba a ce ba ka je ba ta ya ya za ka sani idan ba a sanar maka ba. Gwaman Jihar Nasarawa

Alhaji Umar Tanko Al-makura ya janye ziyarar ta shi ta zuwa sansanin yan gudun hijirar dake garin Keana da Obi dama Awe.

Ya Kamata A Kafa Kwamitin Taimakekeniya A Jihar Kano Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An shawarci al’umma a unguwannin jihar Kano su kafa kwamitoci na taimakekeniya a tsakaninsu musamman ma ta tallafawa masu matsaloli a harkar lafiya ,ilimi da ciyarwa wannan shawara ta fitone ta bakin Alhaji Ali Nuhu Wali da yake zantawa da wakilimmu. Ya ce yanada matuqar muhimmanci ace kowace unguwa su yi kwamiti dazai haxa da dattawa waxanda za su riqa tuntuvar masu hannu da shuni da sauran al’umma dansu riqa taimakawa buqatun

al’ummarsu. Ali Nuhu Wali ya ce kullum ka buxe rediyo sai kayi tajin neman taimako wani na Asibiti ko makaranta wani harkar rayuwa,wanda sai mutane sun taru sun kawo canji da kansu kamar yanda Allah ya ce baya canzawa sai mutane sun haxu canza,wannan zai taimaka wajen kulada tsaro ta unguwa da za’a riqa kulada masu aikin tsaro da hakan zai rage sace-sace da sauran miyagun xabi’oi. Ya ce wannan gidauniya idan kowace unguwa ta xauka asa iyayen qasa a ciki tun daga

kan hakimai dagatai da masu unguwanni da jami’an tsaro na yankin da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro wannan zai kawo raguwa aikata laifuka domin harkar laifi abune mai zaman kansa yanada mataimaka da zakaga in an toshe wannan laifin sai wannan ya vullo,dole sai an haxu gaba xaya an taimakawa jami’an tsaro yakamata kowace unguwa tayi hovvasa sai a sami sauqi. Alhaji Ali Nuhu Wali ya ce kullum zakaji ana neman taimako,da anyi Gidauniyar Kano wanda ba’a maganarta

yanzu.Yakamata yanzu a kafa Gidauniya a kowace unguwa da mutane za su haxu su haxa kuxi dan anfanawa kansu ta danqa tafayarda gidauniyar a hannun masu gaskiya da riqon amana da bibiyar yanda ake aiwatarda kuxinda ake samu wannan zai taimakawa cigaban al’umma ta dogaro dakansu a buqatunsu ba tareda sun jira gwamnati ba ko kuma suna zuwa neman taimako ta kafafen labarai. Ali Nuhu Wali yaja hankalin iyaye akan su riqa kulawa da kyautata tarbiyar ya’yansu dan gina al’umma ta gari masu anfani a rayuwarsu.

•Alhaji Ali Nuhu Wali

Ba Mu Buqatar Jam’iyyar Da Ba Ta Da Manufa Akan Inganta Kiwon Lafiya –Likitoci Daga Abubakar Abba

Qungiyar Qwararrun Likitoci ta Qasa (NMA) ta gudanar taron muhawar wanda bata tava yin irin sa don yin muhawara akan dama da kuma barazanar dake shafar fannin kiowon lafiya kafin zuwan zaven shekarar 2019. Qungiyar ta sanar da hakan ne a Abuja a ranar Talatar data gabata. A cewar shugaban qungiyar na qasa Mike Ogirima,taron wanda ya samu halarcin jam’iyyun siyasa da kafafen

yaxa labarai da ‘yan makaranta da qungiyoyin sa kai da kuma qungiyoyi masu zaman kansu, ya bayar da damar tattaunawa akan manufofin jam’iyyu da tsare-tsaren da suke dashi na inganta kiwon lafiya a qasar nan. Ogirima ya ce gaba da cewa, taron shiri ne na inganta kimiyya wanda ake sa ran gudanar dashi a cikin watan Mayu kuma za a yi amfani dashi wajen bai wa masu ruwa dakundi xaukar matsayi a Abuja akan zagewar da za a yi na inganta fannin kiwon

lafiya a qasar nan. Shugaban a taron manema labarai akan shirye-shiryen gudanar da taron na kimiyya wanda shi ne ya yi na qarshe a zaman na shugaban qungiyar ya ce, fannin kiwon lafiya a qasar nan yana cikin tsaka mai wuya kuma fannin na qara fuskantar barazana. A cewar sa,Nijeriya ta kai matsayin ta 181 daga cikin qasashe 187 akan fannin kiwon lafiya, inda kuma yin rigakafi ya sauka da kashi saba’in da shida bisa xari a ‘yan shekaru da suka gabata

zuwa kashi ashirin da uku bisa xari. Ya yi nuni da cewar, Nijeriya tana xaya daga cikin qasashen da har yanzu ta kasa shawo kan ciwon Foliyo kuma qasar tana akan siraxin qara samun mace- macen mutane. Ya yi nuni da cewa, gaba xayan inshorar lafiya bai wuce kashi biyar bisa xari ba da aka yiwa ‘yan Ni tun a shekarar 2005, inda hakan ya nuna cewar, qasar ta sauka daga matsayin ta tun a binciken da aka gudanar a 2003. Ya sanar da cewar, “Nijeriya

bata buqatar zartarwa ko samar da wani tsari akan fannin kiwon lafiya”. Ya ce, abin da Nijeriya take buqata ayau shi ne, dagewa wajen mayar da hankali a dukkan matakan iko na qasar don inganta fannin kiwon lafiya. A cewar sa, “wannan zai faru ne idan an samar da kuxi da sayar da hannun jarin fannin da samar da qirqireqirqire don inganta fanin na kiwon lafiya da kuma sanya takunkumi ga waxanda suke da qunnen qashi.

’Yan Sanda Sun Cafke ‘Yar Qonar Baqin Wake A Maiduguri Daga Khalid Idris Doya

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno, a Talatar nan ne take tabbatar da batun kame wata mace ‘yar qonar baqin wake a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Bakassi da ke Maiduguri a sa’ilin da take kitsa yadda za ta yi ta tayar da wannan bom xin da ta xauko a jikinta. Hakan na qunshe ne a cikin sanarwar da rundunar ‘yan sandan ta fitar, xauke da sanya hanun Kakakin Rundunar

Edet Okon, wacce ya rana a Maiduguri, ya ci gaba da cewa sun samu nasarar kame ‘yar qonar bakin waken ne a sa’ilin da take kai-kawo domin ganin yanayin da ya dace don tayar da bam xin, ya bayyana cewar ‘yan sandan sun samu nasarar a bisa sa’ayin sashinsu na musamman masu dakile tashi bom wato (EOD) wajajen qarfe 6: 50 na safiyar ranar Talatar a sansanin ‘yan gudun hijran. Jami’in ‘yan sandan ya bayyana cewar rundunar tasu,

sun yi qoqarin killace muhallin a wannan lokacin, inda ta samu nasarar warwar bom xin gami da taso qeyar wacce ta xauko bom xin. Ya zuwa yanzu kamar yadda ‘yan sandan suka shaida, wacce ake zargin tana gargame a hanunsu. Okon ta cikin sanarwar nasa ke cewa: “A Talatar nan, wajajen qarfe 6:50 na safiya, wata mace wacce take auke da bom, inda ta shiga sansanin ‘yan gudun hijira ta Bakassi (IDP) da ke cikin garin

Maiduguri. “A lokacin da take xauke da bom xin, haxakar ‘yan sanda na sashin musamman masu dakile tashin bom, (EOD) sun xauki kakkawar mataki inda inda suka samu nasarar warware bom xin daga yunkurin tashinsa,” In ji PPRO. “Wacce muke zargi mai suna Zara Idriss mun samu nasarar kameta, yanzu haka tana hanunmu a tsare,” Okon ya buqaci dukkanin jama’a da su ci gaba da gudanar

da dukkanin harqoqinsu ba tare da wata matsala ba, domin a cewarsa ‘yan sada da haxin guiwar sauran jama’an tsaro suna kan gudanar da dukkanin aiyukan da suka dace domin ci gaba da kare jama’a da dukiyarsu. Ya sha alwashin cewar a kowani lokaci haqqinsu ne kare dukiya da rayukan ‘yan qasa, don haka za su ci gaba da kawar da bata gari domin wanzar da zaman lafiya a cikin qasa.


14 LABARAI

A Yau

Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Mun Yaba Da Kalaman IBB Kan Sanata Maqarfi –Qungiyar Matasan Nijeriya Daga Abubakar Abba

Qungiyar matasa da suka fito daga yankin Kudu maso Kudu na qasar nan sun jinjinawa tsohon Shugaban kwamitin riqo na qasa na jamiyyar PDP kuma tsohon Gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmed Maqarfi saboda nuna ladabin sa da kuma jajircewar sa akan xorewar jamiyyar a qasar nan. A cikin sanarwar da qungiyar ta fitar wadda kuma Shugaban shiyyar Kudu maso Kudu Honarabil InioriboTamunotonye ya sanyawa hannu ya sarawa Sanata Maqarfi sarawa Sanata Maqarfi akan nuna wannan halin na dattako wajen yiwa jamiyyar biyayya. Qungiyar ta fitar da sanarwar ce, akan martanin da aka danganta cewar tsohon Shugaban qasa na mulkin soji Janar Ibrahim Babangida mai ritaya ya yi a lokacin da ya karvi baquncin wakilan Kwamitin zartarwa na jamiyyar PDP da Shugaban PDP na qasa Yarima Uche Secondus ya jagorance su zuwa gidan IBB dake garin Minna. Tsohon Shugaban qasar a lokacin ziyarar, ya yaba da biyayyar da wasu jigogin PDP suka yi a lokacin ziyarar. Sanarwar taci gaba da cewa,” mu waklilan qungiyar matasan da suka fito daga jihohi shida na Kudu maso Kudu muna maraba da yadda tsohon Shugaban qasar ya karvi jigogin jamiyyar PDP hannu bibiyu a lokacin ziyarar. A cewar sanarwar, bayan yin fashin baqi, mun yi amanar cewar, mai girma Sanata Ahmed Maqarfi, tsohon Shugaban Kwamitin riqon qwarya na PDP shine yafi chanchanta ganin cewar shine jigo babba na PDP, wanda biyayyar sa ga PDP a shekaru da dama da suka shige bata misaltuwa. Sanarwar ta qara da cewa, a

•IBB

yanayin siyasar Nijeriya irin ta yau, zai yi wuya a samu xan siyasa da yake ta yin biyayya ga PDP har da lokacin da take fuskantar qalubale kamar Sanata Maqarfi. Ta bayyana cewar, abin mamaki shine, duk da cewar Sanata Maqarfi ya faxi a takarar kujerar Sanata a shekarar 2015 da kuma yadda tsohon Shugaban Kwamitin riqo na PDP Sanata Ali Modu Sheriff, ya yamutsa hazon siyasar cikin gida na PDP, amma Sanata Maqarfi ko gizau bai nuna ba har sai da yaga PDP ta tsaya da qafarta. A cewar sanarwar saboda nuna halin dattako da Sanata Maqarfi ya yi, hakan ya baiwa xan takarar Kujerar Sanata a PDP Sanata Ademola Adeleke

sukunin lashe lashe zaven. Sanarwar ta ce, Sanata Maqarfi ya tserewa tsara idan ana maganar yiwa PDP ladabi da kuma qasar nan, har da matakan gwamnati. A cewar su, a matsayin mu na matasa, munyi amanra cewar, samun irin su Maqarfi yana da wuyar gaske kuma ya kamata ayi koyi da irin wannan halayen nasa don yin aiki tare musamman don ya fito takarar shugabancin qasar don ya tsamota daga cikin mawuyacin halin data samu kanta. A wani labarin kuma, qungiyar matasa da suka fito daga shiyyar Arewa Maso Yamma da suka haxa da jihohin Kaduna da Katsina, Kano daSokoto da Kebbi da

Zamfara, da kuma Jigawa suma sun gudanar da taro a jihar Kano, inda suma suka mayar da martani akan furucin da ake dangana shi da IBB akan matsyin na zavuvvuka 2019. A cewar qungiyar, kamar yadda IBB ya zayyana kyawawan halayyen shugaba na qwarai, hakan ya nuna a zahiri cewar, Sanata Maqarfi shine kaxai yake da irin waxannan kyawawan halayen, idan akayi la’akari da kujerar Gwamnan jihar Kaduna da ya riqe har tsawon shekaru takwas musamman yadda ya yi qoqarin samar da wadataccen tsaro ba kamar a wannan mulkin da ake yi ayau ba. Qungiyar ta bayyana cewar, dukkan hukomomin da

Maqarfi ya kafa a lokacin yana gwamnan har yau ana cin gajiyar su a jihar musamman yada suka inganta fannin rayuwar ‘yan jihar tun daga fannin ilimin zamani da aikin noma da raya karkara da inganta tattalin arzikin jihar. Sakamakon irin waxannan ximbin ayyukan, hakan ya sanya Maqarfi ya shiga gaban sauran.Qungiyar ta qara da cewa, duk da cewar akwai sauran ‘yan takara da suka chanchanta tsayawa, amma idan ana maganar matashi, Maqarfi ne ya dace da wannan damar. Sanarwar ta qara da cewa, “ matsayin mu na ‘yayan qungiyar, muna son mu sanar da duniya cewar, duk da cewar IBB yana jin an barshi a baya, saboda wasu kurakurai da ya yi a baya, munga shugaba gwarzo kuma uba wanda kuma za’a yi koyi dashi wanda kuma yake xauke da halayen Marigayi Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, Dakata Nnamdi Azikiwe da Obafemi Awolowo da Olusegun Obasanjo harda shi IBB kamar Ahmed Mohammed Maqarfi. Bugu da qari, sanawar tace, duk da cewar a yankin Arewa maso Yamma muna da mutane kamar su Sule Lamido tsohon gwaman Jigawa da Shekarau tsohon gwamnan Kano, amma dukkan su, munyi amannar cewar, su marawa Maqarfi baya da bashi dukkan goyon bayan da ya dace don tunkuxe APC daga kan mulki, musamman yadda ta jefa talakawan qasar nan a cikin qngin yunwa da fatara. Waxanda suka haxu yayin sanarwar sun haxa da Zainab Al-Amin. Ko’odineta, Arewa Maso Yamma da Kakinta, Stephen Bala Gora. Sai Ambasada Sunny Nnaemeka StClement, Ko’odineta, Kudu Maso Gabsa, da Nze UgoAkpe Onwuka Oyi of Oyi II), Ko’odineta na jihar Anambra.

’Yan Sara Suka Sun Rautanata Mutane Biyar A Kusa Da Cibiyar ‘Yan Jaridu Ta Bauchi Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Wasu matasa ‘yan sara suka sun kai hari cibiyar sadarwa da kasuwanci ta Reinsurance House da ke kan titin Ahmadu Bello da ke Bauchi inda suka raunana mutane da dama yawancin su mawaqa da kuma waxanda ke halartar cibiyar don gudanar da bincike kan sadarwa irin ta zamani da bukukuwa bayan haka kuma sun lalata dukiya mai yawa a yayin wannan farmaki. Harin an kai shi a wannan larabar da rana inda yawanci suka fi aiwatar da ta’addancin su inda suka fi illata mutane

shi ne ofishin Shamaki Media wata cibiyar sadarwa mai tallace tallace da wayar da kan jama’a, wacce ake ganin bata ga maciji da juna da gwamnatin Jihar Bauchi saboda yawancin tallace tallacen adawa da ake yi don watsawa ta kafafen labarai su ke gudanar da shi. Cikin mutanen da suka raunata mafi tsanani akwai Haruna Aliyu NIngi da Ali Shamaki da Jibrin Abubakar da Naziru Danautan mawaqa da kuma wasu mutane da dama da tsautsayi ya faxa kan su a daidai lokacin da suka halarci cibiyar don

gudanar da ayyukan su na yau da kullum kamar yadda suka saba. Al’amarin ya zamo abin takaici saboda ganin maharani rana tsaka suka je a kan baburan hawa masu xauke da mutane uku uku xauke da makamai inda shigar su ke da wuya suka fara saran mutane, yadda wasu da dama kafin saran ya je kan su suka riqa faxowa daga kan beni mai hawa biyu suna karyewa. Yayin das hi kuma Aliyu Shamaki wanda ke yawan tallar sukan gwamnatin M. A. Abubakar aka raunata shi a hannu da wasu sassa na jikinsa da wuqa, shima

Haruna Aliyu Ningi mai waqar PDP shima ya samu rauni sosai, lamarin da ya sa mutane a halin yanzu suka qara razana da lamarin na mata ‘yan sara suka a garin Bauchi. Matsalar sara suka a Jihar Bauchi an jima ana fama da ita amma jami’an tsaro da sarakuna da iyayen yara suka qoqarta wajen shawo kan matsalar, amma zuwa wannan lokaci lamarin ya fara dawowa inda matasan da ake ganin wasu na samun xaurin gindin wasu ‘yan siyasa ko kuma masu aikata laifuka a voye suka fara dawo da

wannan mummunar xabi’a. Bayan aukuwar lamarin rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta tura jami’anta amma basu samu nasarar kama ko mutum guda ba saboda duk sun hau mashinan da suka zo da su sun gudu. Amma kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar ya bayyana cewa suna ci gaba da gudanar da bincike don gano waxanda suka aikata wannan ta’adda. Kuma ya shawarci jama’a da su riqa ba ‘yan sanda bayanai game da masu aikata laifuka don a samu damar magance irin wannan matsala.


RAHOTO 15

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Gwamnatin Tarayya Ta Karya Doka Wajen Biyan Dala Miliyan 462 Na Jirgi Mai Saukan Angulu –Majalisar Dattawa Daga Bello Hamza

Majalisar Dattawa ta yi sammacin ministicin kuxi dana Tsaro tare gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN)a kan fitar da Dala Miliyan 462 daga asusun gwamnatin tarayya ba tare da bin cikakken qa’ida ba. A na sa ran Minitan Kuxi, Kemi Adeosun dana Tsaro, Mansur Dan-Ali da gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele zasu bayyana a kwamitocin majalisar a mako mai zuwa domin su amsa tambaboyi. Sanata Sam Anyanwu mai wakiltar jam’iyyar PDP daga jihar Imo ne ya gabatar da qudurin dake cewa, an fitar da kuxaxen daga asusun gwamnatin tarayya ne ba tare da izini ko sa hannun majalisar Dattawa ba. Ya ce, “A watan Maris na shekara 2018 gwamnatin tarayya ta fitar da Dala Miliyan 465 daga asusun tarayya in da aka biya wani kanfanin qasar Amurka a masatyin kuxaxen sayen jirage masu saukan augulu” “An yi wannan ne ba tare da iznin majalisar Dattawa ba ko izinin majalisar qasa baki xaya, a iya sani na babu lokacin da gwamnatin tarayya ya zo da buqatar neman amincewar mu na fitar da waxannan kuxaxen” “A kwai buqatar mu gayyato gwamnan CBN da ministan tsaro dana kuxi, su zo su yi mana bayanin yadda suka fitar da waxannan kuxaxen aka bai wa kanfanin na qasar Amurka ba tare da amincewar majalisar Dattawa ba” inji shi. Qoqarin neman qarin bayani daga sanata Anyawu a daren jiya yaci tura, majaliar Dattawa nan take ta amince da gaiyyato munistocin su uku domin su qara wa majalisar haske a kan yadda aka fitar da kuxaxen. A nasa tsokacin, mataimakin shugaban majalisar Dattawa Mista Ike Ekeweremadu wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya ce, ministocin da shigaban bankinb CBN su gurfana a gaban kwamtin majalisar Dattawa mai kula da kasafin kuxi domin gabatar da ba’asin nasu. An kuma ba shugaban kwamitin kasafin kuxin Sanata Danjuma Goje (xan APC mai wakiltar jihar Gombe) mako xaya don binciken lamarin. An tayar da lamarin fitar da kuxaxen a majalisar wakilai ta tarayya inda suka umurci kwamitocin daya kamata su gudanar da bincken yadda aka fitar da kuxaxen daga asusun gwamnatin tarayya domin sayen kayan yaqi. Xan majalisa Toby

Okechukwu ne bijiro da maganar a lokacin daya ke bayar da gudummawarsa a kan buqatar gwamnatin tarayya ta tabbatar da dawowar ‘yan matan Chibok da sauran ‘yan matan Dapchi da ‘yan ta’adda suka sace. Ya ce, batun fitar da kuxaxen domin sayen makamai ba a yi shi bisa qa’ida ba kuma harmun ne. Ya qara da cewa, kuxaxen sun kai Naira Biliyan 165, kuma bai haxa da Dala biliyan 1 da shugaba Muhammadu Buhari ya amince da bai sojoji domin sayen kayan aiki ba. “Daga dukkan alamu vangaren zartaswa na neman karve mana aikinmu na yin dokoki, ba zai yiwu mu zura ido muna kallon haka na faruwa ba” inji shi. Da yake tsokaci akan lamarin, shugaban majalisar Dattawa Yakubu Dogara, y ace. In har wannna lamarin da gaske ne, to ba qaramin karya doka bane. “In har da gaske an fitar da waxannan kuxaxe daga asusun gwamnatin tarayya ba tare amincewar majalisar tarayya ba, wannan yana nuna kai tsaye kamar sata kenan, na tabbatar da qasar Amurka a matsayin ta uwa ga wannan tsarin na dimokraxxiyar da muke aiwatarwa ba zata yarda da karvar kuxaxen sata ba” inji shi. Dogara ya miqa lamarin ga kwamitin na musamman a majalisar wakilan das u binciki gaskiyar labarin kafin majalisar ta san cikkaken matakin da zata xauka. Yarjeniyar Tsakanin Nijeriya da Amurka Na Sayan Jirgin Super Tucano guda 12 Wata majiya a shaida mana

cewar, jirage masu saukan aunguklun zasu iya zama qirar Super Tucano guda 12 da A-2t9 da wasu makamai har na dala Miliyan 593 da Amurka ta amince ta sayar wa da Nijeriya. Jakadan Amurka a Nijeriya ne ya miqa takardar yarjejeniya kwangilar ga hukumar rundunar sojojin sama inda aka shirya kammala tsara sharuxxoxin kwamgila da kuma biyan kuxaxen kafin ranar 20 ga watan Fabrairu na shekara 2018. Jirage Super Tucano na aiki ne da furopela yana qarfin sunsuno bayanai daga can sama yana kuma iya kai farmaki da nesa, kanfanin Embraer na Brazil suka qera, tare da haxin gwiwa tsakanin kanfanin Embraer da wani kanfani mai zaman kansa mai suna “Sierra Nevada Corp of Sparks”, na garin Nevada ta qasar Amurka. Kuxin kowanne jiirgi ya kai Dala Miliyan 10, yana kuma iya fin haka in an nemi a qara ingantasu. Da aka tuntuve shi akan batun kuxaxen jirgin saman qirar A29 Super Tucano, jami’in watsa labaran rundunar sojojin sama, Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya y ace,zai bayyana ainihin kuxaxen jiragen a lokacin dayab kamata. Ya kuma qara da cewa, baya ga kuxaxen sayen jiragen, yarjejeniyar ya haxa dana horar da matuqan jirgin dana masu gyaran jirgin da kuma na sayen albarushin da za a yi amfani dasu a jiragen. Wani xan kwangila a kan kayayyakin tsaro y ace, jiragen da ake Magana na iya zama jiragen da aka shirya sayen su tun fiye da shekaru 2 da suka wuce.

Majiyar ta kuma ci gaba da cewa, kuxaxen irin waxannna jiragen na iya kai wa tsakanin Dala Miliyan 18 zuwa Dala Miliyan 30 ko wannen su. Majiyar ta kuma qara da cewa, jiragen mai saukanaugulu na iya zama qirar qasar Rasha sanfurin MI35 ko MI24 domin ana iya sarrafa irin waxannan jiragen su yi akin xaukan sojoji ko kuma suyi yaqi kai tsaye. Haka nan an kuma gano cewa, an umurci hukiumar sojojin sama su shiga tattaunawa kai tsaye da kanfanin nan qasar Rasha domin sayen makaman. Ana gudanar da irin wannan tattaunawar ne ta hannun wakilai da suke amfana da la’ada na musamman in an kamala cinikin. Hukumar rundunar sojojin sama sun yi bayanin cewa, a ranar 23 ga watan Oktoba rundunar ta fara aiwatar da shirin nan mai suna “RUWAN WUTA II,” a qoqarin da take yin a kawar da ‘yan ta’adda daga lungunan qasar nan. Babban jami’in watsa labaran rundunar NAF Air Commodore Olatokunbo Adesanya, ya bayyana haka a wata sanarwa, in da ya ce, shirin zai yi rowan wuta ne ba dare ba rana a sabbin mavoyar ‘yanta’addan da aka gano. “A ranar farko na shirin, an yi rowan wuta a wurare da dama a Arewa maso Gabas, musamman a garin Maloma. “Bayan sirrin da muka samu ta hanyar amfani da fasahar “Surveillance and Reconnaissance (ISR)” ya nuna mana mavoyan ‘yan ta’adda sin da suke voye, musamman a garij Maloma. Daga nan ne muka yi amfani da jirage 2 qirar Alpha inda muka fattatake su” inji shi.


16

Siyasa A Yau

A Yau Alhamis 19.4.2018

Aikin Gona Da Tsaro Zan Ba Muhimmanci Idan Na Karvi Kujerar Buhari -KT Turaki Daga Mustapha Ibrahim Kano

Ganin yadda Nijeriya Allah ya albarkace ta da qasan Noma da Ma’adanai masu tarin yawa a Arewa da Kudancin Qasar nan to idan na samu Nasara zama shugaban qasa a Jam’iyyar mu ta PDP to aikin Gona da bunqasa harkar Tsaro dayin adalci a tsakanin al’ummar qasar nan shi zan ba muhimmanci domin ta haka ne kawai za a samu bunqasa zaman lafiya da Tattali arziqi mai yalwa da zai maida Nijeriya xaya daga cikin Qasashe masu qarfin tattalin arziqi da kuma tasiri a tsakanin qasashen Duniya manya da ake dasu a wannan Duniyar. Wannan bayanin ya fito ne daga Babban Masanin Shari’a Lauya mai muqamin babban lambar girma ta kwarewa a fannin sharia’a wato SAN Kabiru Tanimu Turaki xan masanin Gwando Zurmin Kebbi tsohon Minista mai kula da aiyuka na musamman wanda ya riqe muqamai daban daban a Tarihin sa wanda yanzu haka ya fito neman zama Shugaban Qasa a Jam’iyyar adawa ta PDP. Ya bayyana cewa, rashin bunqasa harkar tsaro da yin adalci a tsakanin A’ummar Nijeriya ba tare da nuna ban banci a tsakanin A’ummar qasar nan ba abin takaici ne da a ce Jam’iyyar APC da Gwamnatin Muhammadu Buhari na adalci da girmama Doka da Oda da yanzu ta bi umarnin Kotu na sakin tsohon mai ba shugaban qasa shawara ta fuskar tsaro Alhaji Sambo Dasuqi kamar yadda Kotu ta ba da umarni, haka kuma da Gwamnatin Buhari ta Jam’iyyar APC na bin doka da oda da yanzu ta saki Sheik Ibrahim Al’zazzaky da kuma ba ta rushe Gidan sa ba domin babu wata Hujja da Kotu za ta ce a saki mutum kuma Gwamnati taqi bin umarnin Kotu wannan rashin girmama doka da oda ne acewar KT Turaki. Kuma Gwamnatin da take iqirarin bin Doka da Oda ce ta taje ta kama Alqalai a Gidajan su a tala tainin dare kuma haryanzu Hukumar EFCC ta kasa gabatar da Hujjar ta a gaban Kotu na laifin Alqalai da aka kama wannan abin kunya ne kuma abin takaici ace Gwamnati ba ta

mutun ta doka da oda a qasa. Ga matsalolin da qasar nan ta shiga na halin ha’ula’I wanda Al’ummar Qasan na ta samu kanta a masifar Talauci, Fatara da Yunwa da Jam’iyyar APC ta jefa qasar nan sakamakon rashin iya tafi da al’amura yasa ya zamewa Yan Nijeriya dole su tashi su nemi Canji mai ma’ana ba irin na yanzu ba. Ko ni ma wannan ce ta zame min wajibi na amsa kiran Al’ummar da su kayi wata tara suna kira na da na fito Takarar Shugaban Qasa domin ceton qasar nan daga koma bayan da ta samu kanta sakamakon rashin iya mulki na Jam’iyyar APC wanda ta rusa tsari da cigaban da Nijeriya ta samu kimanin shekaru 50 da suka wuce duk wani abu na kirki APC ta rusa shi a cewar KT Turaki. Manyan matsalolin da Nijeriya ta samu kanta a wannan zamani kamar faxan Qabilanci, Rikicin Addini da kuma matsalar kasha kashe da take faruwa yau da kullum a qasar nan ya ce kafin wannan lokaci ya ce Qabilar TUBI da FULANI abokan wasa ne da kuma zumunci a tsakanin su amma yanzu tsakanin su sai kashe kashe saboda gazawar Mulkin APC kamar abinda yake faruwa na kashe kashe a yau da kullum a Kaduna, Katsina, Zamfara ga kuma satar mutane a ko ina hatta akan hanya mutane basu tsira ba wannan wani abune

da yazama dole a taka masa burki ta hanyar dawo da Gwamnatin PDP a Nijeriya. Kalli kuma abubuwan da yake faruwa marasa daxi a Kudu Maso Yamma wanda sun fara iqirarin Yancin kansu haka Arewa Maso Gabas na iqirarin qasar kansu ta Biyafara. Ga kuma qasashen Kudu na iqirarin sungaji da zama tare a Nijeriya haka su kansu Qabilun Arewa sun fara kuka da cewa manyan Qabilun a Qasar nan na nuna musu rashin adalci da dai sauran matsaloli da suke faruwa sakamakon gazawar Gwamnatin APC ya ce kuma wannan abin tsoro ne a riqa samun haka a Nijeriya musamman idan akayi la’akari da abin da ya faru a Qasar RASHA da Qasar Yugus Labiya na xai xai cewar qasar, kar mu manta maganar Muhammadu Buhari ya ce duk wani rikici na rashin zaman lafiya da yake da alaqa da kashe kashe na Addini ko na Qabilanci ko na Vangaranci da ya xau lokaci anayi to akwai hannun Gwamati ko kuma sakacin ta dan haka dole ne Gwamnati ta kawo qarshen matsaloli da suka addabi Kudu da Arewa a qasar nan. lalacewar Al’amuran tsaro ne yasa TY Xanjuma Sarkin Zamfaran Anka da Sarkin Birnin Gwari sukayi Magana na neman xaukin tsaro ko da daga Hukumomin waje ne domin

tavarvarewa da kuma kasawa na tsare lafiya da Dukiyoyin Mutanan su da rashin tsaro ya ta’azzara a yankunan su kowa yasan wannan a cewar Xan Masanin Gwandu. Xan masanin Gwandu ya bayyana cewa Mulkin PDP ta duqufa da kuma samun Nasara wajan shawo kan rikicin daya addabi Jahohin Arewa shida wanda sai da yadawo Jahohi uku kawai yadawo Jahohi biyu kuma abu dai anfara samun Nasara wajan war ware matsalar Yan Tada Qayar Baya na Jahohin Arewa Maso Gabas wanda ya kasance sai wasu qana nan Hukumomi a Jahohi 2 abin ya rage to anma yanzu ga halin da ake ciki dan haka su basu gamsu ansamu tsaro ba bias la’akari da abubuwan da yake faruwa na faxan Manoma da Makiyaya Satar Shanu da makamanta su a yanzu. Tun farko dai ya zargi Gwamnatin APC da kasa Aiyukan cigaban Qasa kamar yadda Gwamnatin PDP ta yi a ko ina inda ya yayi nuni da cewa sun samar da Jami’oi sha uku a faxin qasar nan da kuma samar da Babban Asibitin Koyarwa ko Babbar Cibiyar Kiwon Lafiya a duk Jaha wanda yace su dai a yankin Sokoto, Zamfara, Kebbi Gwamnatin APC ko Rijiyoyin Zamani ba tava samar musu ba a shekaru uku da su ka wuce na Mulkin APC.


A Yau

Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

SIYASA

17

Gwamnatin Buhari Ta Yi Nasarar Kawo Gyara Ga Matsalolin Qasar nan -El-yakub HON. UMAR EL-YAKUB jigo ne a jam’iyyar APC. Kuma tsohon xan majalisar wakilai ta tarayya daya tava wakiltar Birnin Kano. A wannan hira ya bayyanawa IBRAHIM MUHAMMAD irin rawar gani da Gwamnatin Buhari ta yi wa qasar nan, musamman don kyautata ci gabanta. Ga yadda hirar ta kasance: A matsayinka na xaya daga jigo a jam’iyya me mulki ta APC zuwa yanzu tun daga kama mulkin Buhari kusan shekaru uku a matsayinka na xan jam’iyya kana ganin kwalliya ta samu biyan kuxin sabulu bisa zavenda a ka yi mata? A’uzu billahi minas shaixanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. To alhamdu lillahi dukkan godiya ta tabbata ga Allah maxaukakin Sarki. Babu shakka wannan tambaya taka akan gava take kuma amsar shi ne, eh mun gode Allah kwalliya ta biya kuxin sabulu , saboda ko babu komai an sami canjecanje na kwarai, ingantattu wanda suka kawo tsari na gyara na tabbatarda xorewar ci gaban al’umman Nijeriya ta vangare dabandaban. Misali kamar yadda koda yaushe nasan kukanji, kukan gani kuma abu ne wanda ya ke da muhimmanci a jaddada shi harkar tsaro, babu shakka har yanzu akwai barazana iri-iri da sauransu a wurare daban-daban, amma akan gaskiya kai ka sani ni na sani, yawanci waxanda suke zaune a Arewacin qasar nan har a wannan gari namu na Kano da jihohin arewa maso gabas irin barazanar da muka gani. Irin zaman da muka yi na fargaba da tsaro da rashin walwala da kowa hankalinsa ba a kwance yake ba cikin tsawon lokaci. Bana mantawa kamar yadda ake cewa filin dagar yaqi haka muka zama a garuruwammu masu babura sai sun sauka sun tura, shingen bincike a wannan garin namu na Kano in an ce ya kai 70 ba mamaki ba zan manta ba ko’ina ka je ‘yan sanda, idan kana tafiya ko leda ka gani a hanya tsoro kake kana tunanin ko bam aka saka. Masallatai da makarantu tsoron zuwa

ake majami’u ma kiristoci tsoron zuwa suke. Ba wanda ya ke da kwanciyar hankali da natsuwa balle ma ya je yayi al’amuransa na yau da kullum. To wannan ba qaramar nasara ba ce da wannan Gwamnati tamu ta yi. Idan ka tafi zancen harkar noma kowa ya sani daga shigowar Gwamnatin Buhari zuwa yanzu an sami gagarumar nasara yanzu dani dakai wataqila bazamu iya qirga waxanda suka shiga noman shinkafa da sauran al’amura daban-daban na noma ba, kowa ya koma yana cewa ashe noman nan da muka bari ba qaramin alheri bane a cikinsa zai cida al’umma kuma zai kawowa mutane aikin yi da sana’oi kuma muna ganin canji muna ganin gyara. Na xan daxe ban yi tafiya ba daga Abuja zuwa Kano a mota yawanci na kan shiga jirgi, amma da na yi kwanan nan sai na qara gode wa Allah da murna da sha’awar yadda na ga wurare suna ta tasowa na noma ne ko kuma inda ake sarrafa amfanin gona duk ga su nan sai qara bunqasa suke, kuma mutane da yawa sai sha’awar shiga suke har mutanen qasashen waje da wanda suke nema su kawo kuxinsu qasar nan su sa a harkar noma ga manyan masu kuxinmu, irinsu Xangote da sauransu kusan yanzu jihohin arewacin qasar nan kowa qoqari yake ya zuba kuxi masu yawa a bunqasa harkar noma da kiwo, to wannan babbar nasara ce, saboda shi ne zai ci gabantar da jama’a ya kuvutar damu daga qangin talauci kuma ya bada sana’a da aikinyi ga miliyoyin yan Nijeriya wanda Gwamnati bazata iya basu wannan sana’ar ba, kuma ba wani abu dazai kawo sana’a mai yawa face irin waxannan ayyuka na gona da bunqasa masana’antu da sukeda alaqa da harkar noma.

•HON. UMAR IBRAHIM EL-YAKUB

Sannan harkar ginegine in aka duba ana samun canje-canje da ci gaba, yanzu ana buga sabon layin jirgin qasa daga Legas zuwa Ibadan wanda zai zo harkano, kuma kwanannan za a fara daga Kano ya tafi Kaduna dan a haxa da wuri, haka shugaban qasa ya faxa a bayaninsa kwanannan, saboda haka ba qaramar ci gaba bane idan aka sami layukan jiragen qasa suna gangarawa ko’ina a cikin qasar nan ana xiban mutane da kayayyakinsu ba qaramin bunqasa tattalin arziqi bane, haka harkar ilimi kanta an sami xaukikala-kala wanda Gwamnatin tarayya ta shigo ciki da kuma Gwamnatocin jihohi, karka manta idan a ka yi zancen Gwamnatin APC ba za ta tsaya kawai ga akan Gwamnatin tarayya kawai bane harda suma Gwamnatocin jihohinmu na APC dana qananan hukumomi tunda abin haxaka ce ayyuka daga sama zuwa qasa ko daga qasa zuwa sama ya danganta yadda ka duba al’amarin, to shi kansa wannan a Gwamnoninmu ma sai sam barka dan da damansu sun yi abubuwa na a zo a gani musammam ma

harkar noman nan tunda bamuda abin da ya fi noman nan, tunda ba za a ce kowa yana da mai ba ko ma’adinai , to a ma’adinan ma wannan gwamnati ta qara himma wajen azo ayi tsarin haqosu dan ci gaban al’umma saboda haka fanni dabandaban ina tabbatar maka an ci nasara Mutuncimmu na yan Nijeriya a idon Duniya ya canza, ba kamar daba da ba a xaukarsu da kima da mutunci, wanda yanzu Buhari ya qara mana kwarjini da martaba saboda irin girmamawa da ake dashi a kansa a qasashen Duniya na ganin mutumne mai kamala, mutunci ba varawo ba, me kishin al’ummarsa. Idan ka duba wajen varnatar da dukiyar al’umma wanda da ake yi a qazamce kamar babu gobe shi kansa wannan an sami sauqi na cin hanci da rashawa, ba zance an daina ba, dan babu inda za ace an rasa irin wannan amma dai an sami sauqi, muna fata a yi ta samun sauqi dan mutane su gane babu alkhairi a cin hanci da rashawa kuma yana cutarda al’umomi da fatan waxannan abubuwa mutane za su fuskancesu su

Ci gaba a shafi na

18


18 SIYASA

A Yau

Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Gwamnatin Buhari Ta Yi Nasarar Kawo Gyara Ga Matsalolin Qasar nan -El-yakub Ci gaba daga gane an sami nasara. shafi na Ba za a ce duk abin da a

17

ke so a wanzar ya wanzu ba a sherannan uku dan shekaru huxu ma bashida yawa a wajen gyara. Varna ce nan da nan sai ka yi ta amma gyara abune da yake xaukar lokaci saboda haka babu shakka shi yasa muke fata a qara ba shugaban qasarmu dama dashi da ragowar Gwamnatocimmu na jihohi a sake ba APC dama idan Allah ya yarda abin da muka fara na ci gaban al’umma na gyara tattalin arziqin qasa muna gani zai xore a samu nasara. To kuna maganar an sami tsaro amma mutane suna kukan Gwamnatin ta sakasu a tsadar rayuwa fiye da baya da ake samun sauqi fiye da yanzu, bayan zaton cewa zuwan Buhari sunasa ran samun sauqine fiye da baya sai gashi tsadar na ninkawa me za ka ce gameda wannan? To idan aka ce abin yana ninkawa ba a yi adalci ba, wani abin ya qaru amma wasu abubuwan sun ragu babu shakka. Yanzu saboda Allah kuxin shinkafa da ake sayarwa da da yanzu xaya ne? Ai an sami sauqi , haka ne? Tambayarka nake malam Ibrahim ko baka saya ne? Tambaya nake maka ka amsa mana, (dariya)Ya kaqi amsawa, to an sami sauqi a wasu kayayyakin kuma gyara ita takeda wahala, ai dama wannan abin sai an xan sha wahala za, a sami sauqi. Saboda irin varnar da a ka yi ta baya da ginshiqin tattalin arziqinda aka ragargaza na qasa saboda varna da sata da rashin tsari mai inganci mai xorewa shiya jawo irin waxannan abubuwa ke faruwa amma insha Allahu muna ganin za a riqa samun sauqi tunda an xauki hanyar gyara. Wani abin in yazo na gyara dama sai an sami xan qunci amma baai zama mai xorewa ba a yardar Allah. Tunda idan aka gyara tattalin arziqi, mutane suka sami aikinyi aka havaka kasuwanci da noma to za ka ga cewa abubuwa da kansu sai suzo su riqa saukowa , wanda abin zai shafi al’umma gaba xaya. Ban yarda ace matsuwar tafi daba an sami sauqi an sami raguwa yanzu misali kamar kayyayakinda ake shigowa dasu da qasar nan, na yarda

lokacin Janaton tunda an sami kuxi masu yawa aka yita varnatawa daidai da Dala yadda ake sayenta bata kai yanzu ba amma kar a manta fa saida Dala takai sama da N500 amma yanzu ta sauko N300 da wani abu, to ashe an sami xan sassauci ba kamar baya ba, to a hankali muna fata zata sauko saboda yawan abin da muke fitarwa da yawan kuxi da yake shigo mana ba kawai ta mai ba ta harkar noma da ma’adinai da yawan bunqasar masana’antu shi zai sa dalar ta rinqa saukowa saboda muna kawota da dama ta fitarda abubuwa da yawa sai kuma a sami sauqi. Saboda tsadar dala wani sa’in in aka sayo kayan masana’antu za ka ga saboda tsada da yadda ake gudanar da masana’antu za kaga kayan sukan yi tsada , amma sai kaga cewa yanzu saboda ana yi xin da yawa a hankali sai ya riqa saukowa. Abin da ya faru da mun wofintar da qasarmu ne mun yarda kawai mu shiga da komai saboda haka akazo aka riqa kawo mana aka kashe masana’antu shikenan , misali akwai masana’anta da kayadda take ace na miliyan 100 ne, amma dana xaukar ma’aikata 30 ko 40 da suke samun kuxin shigowa, amma saboda kayadda take na miliyan 100 anje an kawo kayan miliyan 200 irin wannan na miliyan 100 anje an kawo kawo daga waje. Mutun xaya sai ya kawo kayan miliyan 200 irin wannan na miliyan 100, zai kawosu ne akan idan kai kana sayarwa a N10 shi sai ya sayar N8 saboda basuda biyan ma’aikata, kuma ya sayo kayan da araha, idan ana haka sai kaga kanfanoninmu da suke ba mutane aiki an kashe su, sai mutun xaya ya kashe sana’ar mutum 100 wanda da anayin sana”oin dasu waxannan mutun 100 sun sami kuxin shiga a hannunsu da za su kulada iyalamsu kuma su shiga kasuwa suyi amfani dasu amma sai kuxin ya koma hannun yan’tsirarun mutane duk kuwa da mutane suna gani sun sami sauqi , amma sauqin ya xauke musu kuma nasu”Purcharsing power”Basu ganeba abin da ya faru kenan a baya varna ce shi ne ake gyaranta sai a hankali tattalin arziqi yana qara gyaruwa yana havaka

•HON. UMAR IBRAHIM EL-YAKUB

sannan mutane su yita samun sauqi kuma tunda sauqin an ginashi kan turba ta gaskiya sai ya ama mai xorewa. Akwai masu cewa ayyana muradin takarar Buhari a karo na biyu ba wani abu azai canza koda ya sake dawowa saboda rashin gamsuwa da mulkinsa a wannan karon kamar yadda masu hamayya ke faxa kanada ja akan hakan? Dama yaya za ayi xan hamayya ya gamsu. Su ba so suke a barsu su yita badaqalarsu yadda suka saba dama sun kashe qasa sun sace duk kuxin mutanen qasa anzo ana badaqala da”Impunity”Babu doka babu tsari babu sanin yakamata, to kuma yaya za suso wanda zai kawo gyara ya tottoshe wannan varna tasu ai dama baza su soba, kuma basu suka haifa mana wannan bala’in ba shekaru da yawa da suke mulki. Kuma karka manta Allah ya taimakemu yaba shugaban qasarmu lafiya tsawon lokuta wanda shi kansa wannan ya xan daqila wani abu da za a samu na irin aikinda zaiwa mutane

a wannan lokacin, saboda haka yanzu Allah ya bashi lafiya kowa ya yarda an fara samun canji da gyararraki akan al’umura. Mu muna fata mun kuma sani Allah zai taimake mu ya bashi karo na biyu cikin qoshin lafiya ya bashi mataimaka nagari da za a ci gaba da yin aiki fiye da baya. To wace shawara ka ke da ita ga al’ummar Nijeriya? A yi haquri a ci gaba da yi wa shugaban qasa muhammadu Buhari addu’a ya qara lafiya kuma Allah yayi masa jagora su ci gaba, dan alkhairin ci gabansu shi ne alkhairin ci gabammu, gyaransu shi ne gyarammu saboda haka ba zance bane na a yi ta vatanci, tsinuwa da addu’a mummuna, a’a zance ne na ayi musu addu’a tagari a sami jagorancinsu ingantacce. Ina kira ga yan Nijeriya idan Allah ya kawomu 2019 a qara marawa shugaban qasa Muhammadu Buhari baya da jam’iyyar APC da yardar Allah za mu qara tabbatar da gyara da ci gaba mai xorewa mai inganci yadda yan’baya yadda za su amfani abin da suka shuka.


19

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Adabi

Tare da Dakta Aliyu Ibrahim Qanqara 07030797630 imel: ibrahim@fudutsima.edu.ng

Sa Usman Nagogo: Sarki Mai Dubun Nasara Sunan Usman Nagogo suna ne fitacce, ba ma wai a qasar Hausa da ma Afirka da kuma sassan qasashen Turai ba, har da ma a cikin sarakunan gargajiya, don ya na wata muhibba da xaukaka ta musamman a cikinsu. To tsaya ka sha labari. Waxanda su ka rayu a Katsina tsakanin 1905 da 1981 sun san ko wanene Usman Nagogo. Xa na 14 a cikin jerin ‘ya’yan Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (18561944), mai turawa mai Katsinawa. Usman Nagogo ya yi karatun allo, sannan ya shiga Elementare wadda daga baya ta koma Middle School ta Katsina, daga 1922. Ko da ya ke Sarki Muhammadu Dikko ya jawo shi kusa da shit un ya na qarami kuma ya nuna masa harkokin mulki, wannan ya sanya bai mayar da cikakken hankali ga karatun bokon ba. Ba’ada bayan haka, mun san cewa ba a yin kamar Sarki Dikko har qasa ta naxe, amma shima kan sa Nagogo mai Turawa ya na da nashi baiwa ta musamman, musamman irin yanda ma ya gudanar da mulkinsa. Salon mulkinsa ya fita daban da na sauran sarakunan Arewa. Tun daga mulkin Have zuwa na Faulani babu wani sarki daga Arewacin qasarnan ko Lardin nan da ya tafi aikin Haji sai Sarki Muhammdu Dikko, shi ya tafi aikin Haji a qasa watau a cikin mota cikin 1921. Wai don sarakunan da su ka gabata kafin zuwan Dikko sun yarda da wani zance na cewa wai duk sarkin da ya tafi aikin Hajji bay a dawowa qasarsa da rai wai can za ya rasu. Wannan ne ya zame masu shinge ga halartar Makka don sauke farali, duk da yak e cewa wasunsu da dama sun so zuwa aikin Hajin. Aka yi ta surutu, ana ganin watakila ma Sarki Dikko ya zautu, ya fita daga hankalinsa. Ya kuwa rubuta wa gwamnan Najeriya mai suna Sir Hugh Clifford. Lokacin da gwamnan ya ziyarci Katsina a karo na farko cikin Fabrairun 1920 sai ya ce masa tunda Sir Lord Lugard, wanda ya gada ga mulki ya amince ya kuma shata iyakar ayyukan sarakunan Arewa cewa su na da ikon gabatar da ayyukansu na addinin musulunci to ba ma ya bashi izinin zuwa Qasa mai tsarki ba, har ma ya taimaka masa da shirya masa tafiya ta Ingila. Ranar Lahadi 29/5/1921 da safe su ka bar Katsina, a cikin tawagarsa har da Sarki Nagogo, su ka bi ta Kano, su ka nufi Legas. Daga nan su ka wuce London a cikin jirgi. A wannan tafiya sun zagaya wurare da dama. Kai!, daga nan tafiya ta tafi. A cikin 1933 Sarki Dikko ya koma London tare da su Usman Nagogo. Cikin 1937 da 1939 ma haka. A tafiyar Ingila na 1939 harda Usman Liman Durvin Katsina. Sarki Nagogo ba ya da girman kai, ya na da sauqin kai. Kofur Ibrahim Masanawa wanda Sarki Nagogo da kansa ya bada sunansa a xauke shi aikin Xandoka, ya bayyana cewa a

lokacin da ya na aikin gadin gidan Sarki a nan Qofar Soro, ya ga Sarki Nagogo na da wata al’ada. Al’adar ita ce kullum da dare ya na fitowa daga gida da kimanin qarfe 10 daga shi sai ‘yar shara ya nufi unguwar Alqali wajen wani malaminsa wanda kafin ya zama Sarki ya na zuwa xaukar karatu wajensa. Kuma a qasa za ya tafi. Sai ma ka rava shi ba ka san Sarki ba ne. A nan za ya yada dare, su yi hira ta wani lokaci. Sannan idan qarfe 12 ta buga sai ya kuma nufi gidan wata ‘yar uwarsa watau yayarsa, a nan cikin birni. Nan za ya zauna su yi ta hira har qarfe 2 na dare. Sannan ya kamo hanya ya dawo gida. Shi xaya kuma ya ke tafiya ba ya yarda ma wani ya raka shi. Duk lokacin da ya fito za ya tafi za ya tarar da Kofur Ibrahim Masanawa a tsaye, sai ya sanya hannu a cikin aljihu ya xauko fam xaya ya ce masa ‘ungo’. Galiban, su biyu ake sanyawa gadin, da Masanawa da wani mutum. Kowanne ya na daga qarshen kusurwa, ma’ana kowannensu na hannun riga da xan uwansa. To duk sa’adda Nagogo za ya fito sai ya tarar wancan na kwance ya na barci, shi ko Masanawa na a tsaye. Amma saboda sauqin kai irin na Sarki bay a cewa a tada shi, amma kuma ba za ya ba shi wannan fam xaya ba. Sannan kuma ya na da wata aqida ta yawan zuwa cikin daji ya yi zamansa ya huta sai dare ya komo gida saboda hayaniyar birni. ‘Yammata na wannan lokacin masu zuwa sarin rogo ko gwaba ko zogala a garekanin jama’a su na yawan wuce shi, su tarar ya share fili a qarqashin ice ya shimfixa babbar riga ya yi kwanciyarsa. Sai su ce masa : ‘sannu’. Shi kuma sai ya amsa masu: ‘sannunku ‘yammata’. Nagogo kenan. Sarki Usman Nagogo ya na da matuqar adalci, irin na mahaifinsa. Don hakane Katsina ta zauna lafiya. Ba a sata, ba a yin moxi, ba a shan barasa, sai dai idan a sha a voye amma ba a sarari ba. Talaka ya samu gata a zamaninsa kamar dai yanda mahaifinsa Dikko ya gatanta talaka. Sarki Nagogo

ya na da matuqar tausayi da nuna ragowa ga mutane. Kuma ya iya mutane. Komin qanqantar ka kuma komin qasqancin ka ba ka zuwa ku gaisa ya wulaqanta ka. An tava bada labarin wani sanannem varawo da aka kai bursuna. Watarana sai aka kai su gonar Sarki su na noma. Da almuru ya yi sai aka sako su cikin mota kitika, wadda ta kais u don ta dawo da su gida. A can ne hanyar Batsari. To sai wannan varawon, ya rates ya tsuguna, aka tafi aka barshi. Sai ya biyo hanya shi xaya ya na ta tafiya. Can sai ga motar Sarki Usman Nagogo shi da direba ya dawo daga yawon halbi/gona shima. Sarki ya sa direba ya tsaya. Ya tambaye shi yaya aka yi aka bar shi? Sai ya ce ya shiga gaban mota. Aka taho da shi aka ajiye shi a bakin gidan yari. Ma’ana ya rage masa hanya ko? Sir Usman Nagogo, Sarkin Sulluvawa Ibrahim Ladan Fari, Sarkin Sulluvawa Sule Jikan Korau (‘ya’yansa) Kamar dai yanda Sarkin Katsina Dikko ya yi alkahura ya yi tarayya da Turawan Mulkin Mallaka, akan abinda ya kira ‘lokaci ne ya yi, mu bi mutanen nan in ba haka ba su na iya hallakamu’ to shima Sarki Usman Nagogo ya yi tarayya da su, ya rungume su. Ya yi amana da su. An zauna girma da arziki, sun kuma mutunta juna. Da bai yi haka ba da ba su shawo ta da daxi da su ba. Bayan ma wannan, kasancewa Sarki Dikko shi ya fara kawo wasan qwallon Polo a Najeriya daga Ingila (Birtaniya) cikin 1922, to sai kuma ya zama shi ne shugaban qungiyar na farko a Najeriya. Shi ma Sarki Usman Nagogo, bayan zamewarsa Sarkin Katsina cikin Mayun 1944 sai ya zama shugabanta. Sarki Nagogo ya yi wasan polo gaya. A tsakanin 1942 zuwa 1948, tare da haxin gwuiwar Razdan na Katsina (Mista R. L. Payne da Mista H. B. Leonard da kuma Mista D. C. Fletcher ) Sarki Usman Nagogo ya himmatu wajen buxe makarantun Elementare (Firamare) a duk faxin lardin Katsina domin assasa karatun boko tare da tilasta wa iyayen yara su kai yaransu makaranta. Ga dai jerin sunayen Turawan Birtaniya da su ka riqe muqamin Razdan a Lardin Katsina lokacin Usman Nagogo

na Magajin garin Katsina ya zuwa lokacin sarautarsa. 1. Mista W. Nash 1934-1935 2. Mista G. G. Feasey 1935-1937 3. Mista R. L. Payne 1937-1943 4. Mista H. B. Leonard 1943-1947 5. Mista D. C. Fletcher 1948-1948 6. Mista R. L. Maiden 1949-1953 7. Mista R. H. Maddox 1953-1955 8. Mista J. H. D. Stapleton 1956-1956 9. Mista T. F. G. Hopkins 1957-1958 Cikin 1957 wani Bature Ba’ingile ya halbo giwa a dajin Rugu ta qasar Safana ya kawo wa Sarki Usman Nagogo, wanda shi kuma ya bada izinin a kai qasusuwanta da sauran fatar jikinta a ajiye gidan Tarihi na Katsina. Har yanzu qasusuwan da kuma kunnuwan giwar sun a nan an ajiye don nuna ma al’umma na baya masu zuwa. Hakama ba da daxewa da wannan al’amarin giwa ba shima Magaji da ake kira Magaji Xan’iska ya kamo wata giwar a dajin Batsari. Amma an ce da ya zo har qofar fada ya kawo ma Sarki ita sai Sarki Nagogo ya kora shi ya ce maza ya koma daji ya mayar da ita. Ana kyautata zaton ita wannan giwar makuwa ta yi ta vace hanya har ‘yan uwanta su ka gudu su ka barta. Saboda mu’amulla da Turawan Birtaniya na yin aiki da su kafaxada-kafaxa ake ma ce masa ‘Nagogo mai Turawa’. Duk Baturen da ya zo daga Ingila, fatarsa ya sadu da Sarki Usman Nagogo. Nagogo ba ya da lalaci, ba ya da son zuciya. Ya kuma qware wajen aikin sarauta da tafiyar da jama’a. Saboda adalcin Sarki Usman Nagogo ba ma ‘yan gida ba birnin Katsina sai da ya cika ya batse da baqi masu zuwa daga wurare ko’ina cikin qasar nan. Ranar Laraba 10/3/1981 Allah Ya yi masa rasuwa sabili da ciwon qafa da ya yi fama da shi. An kuma rufe shi a cikin gidansa. Allah Ya gafarta masa, Allah Ya gafarta mana baki xaya.


20

A Yau

CINIKI

Kasuwanci MASANA’ANTU

INSHORA

HANNUN JARI

Alhamis 19.4.2018

KASUWAR SHINKU

Mene Ne Sirrin Tsawon Ran Masaqar Funtuwa?

Daga Hussaini Baba

A shekarun baya Masaqun Funtuwa Testiles, Gusau Testiles da ta Kaduna Testiles, na da ga cikin manyan masaqun da al’ummar Arewancin Qasar nan ke cin moriyar su kuma gwamnatocin ke alfaharin d su wajan samun kuxin shiga. Sai gashi yanzu haka Masaqar Kaduna Testiles, ta samun shanyewar Rabin Jiki, wani sashe ne kaxai nata ke aiki yanzu haka. Wannan kuma ya sanya cewa ‘Dubannan Ma’aikata ne suka rasa ayyukan su sakamakon ciwon da ya samu Masaqar. Ita kuwa ta Gusau watau Gusau Testiles , ta yi doguwar suman da yasa duban nan ma’aikatanta an sallame su da ga aikin a cikin masaqar wanda yanzu haka mutu kwakwai rai kwakwai. Funtuwa Testiles kuwa yanzu haka tana cigaba da aiki kai kace ko ciwon kai ba ta tava yi ba, balle shanyewar rabin jiki ko kuma Doguwar suma. Wannan ya sa LEADERSHIP A Yau ta yi bincike na musamman akan wane sirri ne ya sa wannan masaqar ta yi tsawon rai, ta tsallake annubar, durqushewar

masana’antun Qasar nan duk da matsalar wutar lantarki? Waiwaye adon tafiya ita dai Masaqar Funtuwa Testiles, yanzu haka ta kwashe tsawon shekaru arba’in tana aiki, babu dare babu rana har zuwa yau da nake wannan rubutu a kan ta. Masaqar Funtuwa Testiles ta fara aiki ne da ma’aikata ashirin kuma yanzu haka tana da ma’aikata na dumdum dum, dubu xaya da xari biyar sai kuma masu kwantaragi xari huxu da hamsin. kuma alokacin kaka ana xaukar mata xari dan tsuce duwatsu da manona ke sa wa a cikin Audugar don algushu. Wannan katafariyar Masaqar da ma’aikatanta ke yi wa mata kirari da lahira; Lahirar Auduga don duk audugar da ta shiga cikin wannan masaqar, zavi biyu ne gare ta ku ta kuma Zare ko Yadi. ’Ya’yanta ne kaxai ke fita watau (Gurya) don da ita guryar ne ake irin don samun wacce za su shuka a shekara mai zuwa. Haka kazalika kuma, Funtuwa Testile na Saqa, yadiddika masu xauke da Auduga zalla wace ke raya fatar jikin xan adam. Kuma ta samar da Yadi mai akoko, Farin yadi

alawayyo da kuma yadin kuwa da kuwa watau wanda ake yin likkafani da shi da kuma wanda ake wa Sarakuna rawuna duk Funtuwa Textiles ne ke samar da su. Wannan ya sa kamfanonin katifu daga ko’ina cikin qasar nan ke zuwa ana sarrafa masu yadiddikan da suke buqata, kalarsa da ingancinsa da kuma yawansa. LEADERSHIP A Yau ta binciko sirrin tsawon ran wannan masaqa ne na ganin ko da yaushe tana ware kuxaxe na musamman don a yi wa kamfanin addu’o’i a masallatai da wurin ibadu. Sai kuma yin Yadiddika masu inganci wanda babu almundahana a cikinsa watau suna aiki tsakani da Allah babu almundahana a cikinsa. Sai kuma babban sirrin shi ne biyan ma’aikata albashin su akan lokaci, tun kafin gumin jikinsu ya bushe ana biyansu albashi kuma sai Allah ya albarkaci ma’aikatan na masaqar da sadaukarwa daga cikin albashinsu suna ba masallatai gudunmuwa da kuma yi wa kamfanin addu’oi don ganin bai durqushe ba. Kuma wannan masaqa kasha tamanin da biyar masu cin gajiyarta ‘yan jihar Katsina

ne musamman ma ‘yan yankin funtuwa. Kuma Masaqar ta samu lambobin yabo daga jama’a da gwamnatina taimaka wa wajen samar wa al’umma aikin yi. Sai dai wani qalubalen da masaqar ke gamuwa da shi shi ne na Algushin da wasu miyagun manoma ke yi na sanya ruwa a cikin Audugar su don ta qara nauyi wajen awo wasu kuma na sanya Duwatsu ko Yashi. LEADERSHIP A Yau ta ji ta bakin tsohon ma’aikicin masaqar wanda yayi ritaya da qashin kansa Malam Yusuf Auwal Funtuwa ya bayyana mata cewa, ‘lallai Masaqar Funtuwa Textiles, aiki a cikinta akwai riba babba don za ka ci halas xinka ita kuma hukumar masaqar za ta baka haqqinka don ba ta wasa da haqqin ma’aikacinta don ka ga gidan da nake cikin nan da kuxin aikin masaqa na same shi. Kuma yanzu haka a cikin Funtuwa ma’aikatan masaqa da dama ne suka samu muhalli a cikinta kuma rashinta masifa ce ga al’ummar yankin Funtuwa. kuma sirrin xorewar wannan masaqa shi ne, ba ta ha’inci wajen aiki don duk ma’aikacin da aka kama da ha’inci lallai korarsa ta ke yi.


KASUWANCI 21

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

NCC Ba Za Ta Amince A Sayar Da 9mobile Ba Tare Da Qwararru Ba

Daga Abubakar Abba

Nigeria Hukumar sadarwa ta qasa (NCC) ta sanar da cewar, baza ta amince da sayar da kamfanin layin sadarwa na 9mobile ba ga dukkan waxanda suke son su saya in ba tare da qwararru ba. Mataimakin shugaban hukumar Umar Xanbatta ne ya sanar da hakan a ranar Litinin data gabata. Xanbatta ya bayar da wannan tabbacin ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a jihar Legas. Ya ce, waxanda suke son sayi kamfanin na 9mobile sun bayyana amma ba tare da shigar hukumar ba xingurungun. Ya qara da cewar, sayarwar tuni ana ci gaba da yinta,

amma ba tare da bin qaidar sayarwa ba. A cewar sa, “tuni babban bankin qasa CBN ya shiga maganar sayarwa, amma dole sai hukumar ta tantance qwararru da zasu duba maganar sayarwar. Ya qara da cewa, “In har ba’a tantance maganar sayarwa yadda ta kamata ba, CBN zata yi dubu akan tambayoyin akan tantance bin hanyar sayarwa don ayi ta a bisa qa’ida. Mahukunta kamfanin na 9mobile an basu nauyin tare da waxannan abubuwan da ake buqata. Xanbatta ya bayyana cewar, hukumar ta baiwa kamfanin infracos lasisi guda huxu. A kwanan baya kamfanin Zinox Technology an bashi

lasisi don sanya kayayyaki a yankin Kudu Maso Gabas, inda kuma kamfanin Brinks Integrated Solutions, shima an bashi lasisi na yankin Arewa maso Gabas. Xanbatta ya sanar da cewar, kamfanin MainOne Cable, shima an bashi lasisi don fara gudanar da aiki a Legas. Har ila yau, Xanbatta ya ce, kamfanin IHS shima an bashi lasisi don fara aiki a yankin Arewa ta Tsakiya harda Abuja. Xanbatta ya sanar da cewar, akwai sauran aiki sosai da ya kamata ayi don tura kayan aiki na 4G LTE don taimakawa ma’adanar bayanai. A cewar sa, ya zuwa yanzu umarnin da aka bayar shine, za a samar da 3G da 4G LTE. Xanbatta ya bayyana

cewar,kafafen sadar sun bayar da naira tiriliyan 1.45 don inganta kayan cikin gida a farkon shekarar 2017. Ya ce, alqaluman sun haura zuwa tiriliyan 1.5 a tsakiyar shekarar 2017 duk da matsalin tattalin arzikin qasa da aka shiga. A cewar Xanbatta, kamfanonin sadarwa sun zuba jarin da ya kai yawa dala biliyan 70 a watan Satumbar 2017, sai dai fannin bai iya bunqasa dala miliyan 50 na zuba jari a 2001 ba. Shirin da ake yi na sayar da kamfanin na 9mobile da kamfanin Teleology Holdings, sun biya dala miliyan 50, don sayen kamfanin sadarwa na SmileCommunications don shiga sayen kamfanin na 9mobile.

ne da kanfanin zai samar tuni harma ansa guda 20 baya ga haka akwai wasu makarantun da suka sami kwanftocin. Alhaji Nasiru ya ce cikin irin ayyukanda gidauniyar tayi akwai xaukar nauyin karatun yara mata 10 da aka tura makarantar koyon harkar lafiya ta Funtuwa da yanzu haka sun kusa ma kammalawa kowacce za;a kashe mata kuxi qasa da N500,000 daga farawa da kammalawa. Ya ce gidauniyar ta Xanbatta ta jawo kanfanin MTN ya bada gudummuwa ga gidan gajiyayyu na Xanbatta da Makoxa da kuma kai agaji gadan marayu dake yankin

Nasarawa tareda aiwatarda aikace-aikace ga makarantu 10 a yankin. Alhaji Xanguda ya qara da cewa gidauniyar ta samawa matasa da dama aiki a hukumomi daban-daban na Gwamnatin tarayya da koqarin samawa wasu aiki a kanfanin sadarwa na MTN. Ya ce gidauniyar ta assasa da gina makarantar islamiyya mai ajujuwa guda huxu aka damxata ga gwamnati yanzu haka ana karatun Islamiyya dana zamani a makarantar wanda yara da dama suna nuna kwazo a haddar Qur’ani da hazaqa a fannin ilimin zamani,yanzu haka ma ana

xora qarin ajujuwan bene guda Biyar a makarantar. Ya qara da cewa cikin shekaru uku da kafa gidauniyar ta “Charity”a Xanbatta tayi aikacaikac na maganin matsaloli da bada aiki ga matasa ta kuma kai xalibai makarantar koyon sana’a “ITF”ta xorayi inda suka sami horo aka yayesu aka basu tallafin jari. Alhaji Nasir Xanguda ya ce ana samawa mutane da suka haxa da Dattawa da zawarawa tallafin sana’a da ake basu N5000 wanda mutane samada 500 sun anfana Farfesa Umar Garba Xanbatta ya kafa Gidauniyarne dan anfanar ci gaban al,ummar Kano.

Gidaunyar “Charity” Xanbatta Ta Samar Da Kwanfuta Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Gidauniyar tallafawa ci gaban Danbatta da akafi sani da”Charity foundation Danbatta”wanda mataimakin shugaban hukumar sadarwa na qasa, Farfesa Umar Garba Xanbatta ya assasa da xaukin kanfanin “Huawei” Sun gina xakin kwamfuta da samarda kwamfutoci a makarantar sakandiren Yan mata ta Gwamnati ta maimuna dake garin Xanbatta.Shugaban Gidauniyar Alhaji Nasiru Xanguda Xanbatta ya bayyana hakan. Ya ce yanzu haka a tsarin za a sanya kwanfitoci guda 60


22

Kiwon Lafiya

A Yau Alhamis 19.4.2018

WHO Ta Rabar Da Babura Kyauta Ga Qananan Hukumomin 23 Dake Kaduna Daga Abubakar Abba, Kaduna

Ofishin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) dake cikin jihar Kaduna ya bayar da babura kyauta ga ko wacce qaramar hukuma ashirin da uku dake cikin jihar don yin amfani dasu wajen sanya ido don daqile aukuwar varkewar cututtuka. Shugaban hukumar na jihar Dakta Dauda Madubu ya bayyana cewar, an rabar da baburan akan lokaci don a taimaka wajen daqile varkewar cututtuka a xaukacin qananan hukumomin har da kuma jihar baki xaya. Ya ci gaba da cewa, baburan za kuma ayi amfani dasu wajen taimakawa don gudanar da bincike zargin vullar cututtuka don xaukar matakin gaggawa. Dakta Dauda ya qara da cewa, sanya idon yana buqatar alumomi da sarakuna da da malaman addini su kawa rahoto a cikin gaggawa. A cewar sa, “idan an samu kabarin vullar cuta ko wacce iri ce, wadda kuma ba’a kawo rohoton ta a cikin gaggawa ba, zata qara zama tirniki ga alumar jihar. Ya shawarci shugabannin

na qananan hukumomin dake jihar dasu tabbatar da suna kula da baburan domin samar da kyakywan sakamako. Dakta Dauda ya kuma yi kira ga ma’aikatar kiwon lafiyar jihar dasu bai wa shirin goyon baya don yaqar cututtuka a jihar baki xaya. Shima a nashi jawabin babban sakataren a ma’aikatar kiwon lafiyar jihar Mallam Shehu Mohammed wanda ya karvi baburan a madadin kwamishinan kiwon lafiya na Dakta Paul Dogo ya yi alqawarin qara qarafafa sanya ido akan cututtukan daka iya vulla a jihar. Ya ce, xaya daga cikin qalubalen da jami’an kiwon lafiya na sanya ido suke fuskanta a jihar shine na rashin kayan aiki da ababen gudanar da zirga-zirga a cikin alumomin da suke lunguna da saquna na qauyuka da nisan sosai. Mohammed ya yabawa hukumar ta WHO akan tainakwar da ta yi,inda kuma ya yi alqawarin cewar, za a yi amfani da baburan a bisa yadda ya dace. Ita jami’in sanya ido akan varkewar cututtuka ta jihar uwargida Aisha Sadiq, ta bayyana cewar, manufar

•Yayin raba baburan

xaukin anyi ne don ayi nazari akan yadda za a sanya ido akan cututtuka da kuma gudanar da aikin gaggawa wanda aka shafe shekaru uku ana yi. Ta kuma zayyana varkewar cukututtukan da aka fi sanin su a cikin jihar kamar qyanda da kwalara da sanqarau. A cewar ta, jihar tana fuskantar yawan shigowar jama’a, inda hakan yake qara samar da barazanar yaxuwar cututtuka a jihar. A cewar ta, an samu varkewar kawalara da

qyanda a shekarar 2016 da shekarar 2017, da kuma vullar sanqarau guda takwas a shekarar 2017. Aisha ta sanar da cewar, “ a shekarar 2017, mun tabbatar da ciwon zazzavin guda huxu a kuma cikin wannan an tabbatar da guda xaya sai dai, har yanzu mana kan yi bincike don mu gani ko akwai saura. A cewar ta, “mana son jami’an mu masu sanya ido akan cututtuka da daraktocin kiwon lafiya na cibiyoyin kiwon lafiya dasu amince da cewar, sakamakon waxannan

canje-canjen akan daqile yaxuwar cututtuka a xaukacin faxin jihar, abune da ake buqatar a qara jajircewa sosai. Ta bayyana cewar, daraktocin dake a cibiyoyin kiwon lafiya na qananan hukumomin jihar, an wayar masu da kai domin sune sukafi kusa da al’ummar. A qarshe Aisha ta bayyana gamsuwar akan samuwar rahotannin da ake sanya ido da kuma qoqarin da ake yi akan daqile yaxuwar cututtuka a xaukacin faxin jihar.

Kashi 95 Na Mutanen Duniya Ke Shaqar Gurvataccen Iska –Bincike Daga Bello Hamza

Kashi 95 iskan na mutanen duniya ke shaqa gurvatace ne, abin daya gaza ma’aunin da hukumar lafiya ta WHO ta tsara a matsayin lafiyayyar iska. Rahoton da aka gabatar ranar Talata ya ce shaqan gurvataccen iskan ya yi sanadin ma cewar miliyoyin mutane a shekarar 2016, wata cibiyar qasar Rasha ne mai suna “Health Effects Institute” ce ta gudanar da bincike. “A bisa bincike da muka gudanar da qididdigar jama’a dake faxin duniya na shekarar 2016,kashi

95 na Mutanen duniya na zaune ne a wurare dake shaqan iskan da ya gaza qaidar da hukumar WHO ta aiyyana na ma’aunin iska na PM2.5 nada matuqar haxari ga rayuwa, kamar yadda sakamakon da aka samu na “State of Global Air” ya nuna. PM2.5 na nufin daidai da micrometres 2.5 na abin da ake kira aerodynamic diameter. Gurva cewar iska a duniya da ya yi daidai da mamaki PM2.5 Ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da Miliyan 4.1sakamakon cututtukan zuciya dana huhu da kuma shanyewar jiki da kuma

wasu cututtukan da suka shafi nunfashi a shekarar 2016, kamar dai yadda rahoton Ya nuna. Haka kuma Gurva cewar iska a cikin gidaje ya yi sanadiyar ma cewar mum Miliyan 2.6. Rahoton ya kuma fito da banbancin dake tsakanin qasashen da suka fi fuskantar Gurva cewar iska fa waxanda lamarin nasu bai tsananta ba lamarin kuma yana qara qaruwa a kullum. Musamman da yake ana samun qaruwar bunqasar tattalin arziki daga qasashe masu tasowa, waxanda suke a baya a qoqarin tsaftace iskan da ake shaqa a duniya.


A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

KIWON LAFIYA 23

Gwamnatin Ta Ja Kunnen ’Yan Nijeriya A Kan Amfani Magungunan Da Ke Xauke Da Codeine

Daga Abubakar Abba

Hukumar dake bayar da kariya akan cin abinci(CPC) ta gargaxi ‘yan Nijeriya akan shan magunguna dake xauke da sanadarin (codeine), ba tare da umarnin likita ba. Garagaxin yana qunshe ne a cikin sanarwar da Darakata Janar na hukumar Babatunde ya fitar, inda ya ce, codeine wasu iyalan suna amfani dashi wajen baiwa ‘yayansu a matsayin magani, amma an haramta hakan. Babatunde ya ci gaba da

cewa, Codeine yawanci ana amfani dashi ne wajen sauke raxaxin zazzavi ko tari, inda yake kasancewa wani sanadari dake warkar da tari. Ya ce, a bisa ayyukan da hukumar tabbatar da ingancin abinci (NAFDAC) take yi ta sanar da cewar maganin tari yana xauke da sanadarin codeine. Ya qara da cewa, wannan haramtacciyar hanya ce kuma ta savawa qa’ida doka wajen sayen sa kuma akwai buqatar a kwashe su daga shagunan sayar

da magunguna, in har ba qwararrun likitoci ne suka bayar da umarnin ayi amfani dashi ba. Ya yi nuni da cewar, mallakar sa ko kuma rabar dashi ko samar dashi in bada umarnin qwararrun likitoci ba,savawa dokaci kuma shan kayan maye ne, inda shan ke jefe rayukan jama’a a cikin haxari domin yana janyo hauka da kuma hana haihuwa. Babantunde ya bayyana cewar, sanadarin Codeine yana janyo illa ga lafiyar

mutum, inda tsananin sa yake kasancewar kamar shan barasa ne ko kayan lemon da aka haranta sha. Ya yi nuni da cewar, wannan dabarin na yin gauraye yana qara zama barazana ga lafiyar mutum har da janyo ciwon hauka. Ya bayyana cewar, akwai buqatar qwararrun lafiya masu tasowa da hukumomin da abin ya shafa dasu hana yin amfani da magungunan dake xauke da sanadarin codeine da ake baiwa yara ganin yadda yin amfanin,

yake hallaka yara qananan. Babatunde ya bayar da shawarar cewar, a dinga yin amfani kawai da magungunan dake xauk codeine da qwararrun likitoci suka bayar da shawara asha. Ya bayyana cewar, savawar cewar savawa dokar hukumar akan sarrafa yin amfani da magungunan dake xauke da sanadarin haramun ne kuma babban laifi ne kuma za a iya hukunta duk wanda keda hannu a cikin har da (NDLEA), kuma hukuncin shine zama a gidan Yari.

WHO Za Ta Kashe Dala Miliyan 178 Kan Kiwon Lafiya A Nijeriya Daga Idris Aliyu Daudawa

Ranar Litinin ne Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce zata kashe kuxaxe har dalar Amurka milyan 178 tsakanin shekarun 2018 da kuma 2019, akan al’amuran da suka shafi harkar lafiya a Nijeriya. Wakili mai kulawa da ofishin Nijeriya na Hukumar lafiya ta duniya Dokta Wondimagegnehu Alemu, shi ne ya bayyana haka lokacin ta aka yi taron haxin guiwa na amincewa da kuxaxen da za a kashe a kasafin kuxi

na shekarun 2018 da kuma 2019, tare da Ministan lafiya Farfesa Isaac Adewole a Abuja. Alemu ya ce, dalar Amurka milyan 127 wadda kashi 66 cikin 100 ne na kasafin kuxin, waxanda za a kashe su ne wajen tsare tsaren mganin shan Inna wato polio. Ya qara da cewar dalar Amurka milyan 30 za a kashe kuxaxen wajen maganin zazzavin malaria, tarin fuka, da kuma cutare qanjamau. Ya jaddada cewar dalar Amurka fiye da milyan 8.1 an ware ta ne za akashe wajen

kula da lafiya ta hanyar rage mutuwar qananan yara, da kuma tsarin tazarar haihuwa. Ya yi qarin bayani na cewar sauran kuxaxen za a kashe su ne ta hanyar ta maganar vullar kota kwana, wato annoba ta cututtuka. Wakilin Hukumar wanda ya bayyana ya sa hannu a kasafin kuxina madadin Darektan, ya bayyana cear shi Darektan ya amince da kasafin kuxin. Bugu da qari za ariqa yin taron tuntuva tsakanin masu ruwa da tsaki, domin a tabbatar da ana yin al’amuran

kasafin kuxin kamar yadada aka amince. A nashi jawabin Adewole ya jinjinawa Hukumar lafiya ta duniya, a qoqarin data ke yi na bunqasa harkokin kiwon lafiya a Nijeriya. Ya bayyana Nijeriya ta samu gudunmawa mai yawa da ga Hukumar,don haka sa hannu a kasafin kuxin wani abu ne da ke nuna cewar Hukumar zata ci gaba da taimkawa Nijeriya. Shi ma Ministan lafiya ya jinjinawa ita Hukumar lafiya ta duniya, sabioda taimakon da take ba Nijeriya,

musamman ma al’amarin da ya shafi kawar da cutar polio. Maganar kasafin kuxi na kawar da qwayar cutar polio babban al’amari ne, don haka za ayi amfani da kuxaxen kamar yadda aka baiyana. Ya ce, ‘’Ina farinciki akan kuxaxen da aka ware ma cututtuka masusaurin yaxuwa, saboda yaan kasafin kuxin can zai fi amfani. ‘’A madadin al’ummar Nijeriya da kuma gwamnati, ina mai nuna farin ciki na akan gudunmawar da aka bamu, da kuma wadda muka yi ta masa daga Hukumar’’.


24 TALLA

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)


25

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Kimiyya

Dala Miliyan 500

ne adadin kuxi Nijeriya ke kashewa duk shekara waurin safarar xanyen man fetur da wasu sinadaran da ake amfani da su a sashen sinadarari da magunguna

Ana Zargin Satar Bayanai Fiye da 250,000 Kullum Daga Google

Shafin Google sun ce a kullum suna iya qoqarinsu don ganin sun ba wa bayanai da mutane suke shigar wa intanet tsaro na musamman, ana zargin a kullum masu Kutse suna samun nasarar satar bayanan masu amfani da intanet, anfi satar sunayen shiga da lambobin buxe su. A wani bincike da aka gudanar a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017, an gano hanyoyin da dama da masu Kutsen suke amfani da su wajen satar bayanan mutane masu muhimmanci, shafin Google sun wallafa sakamakon binciken da haxin gwiwar jami’ar Kalifoniya ta Amurka, inda binciken ya nuna yadda aka samar da hanyar da za a iya gano bayanan da aka sata. Masu binciken sun yi qoqarin gano duk hanyoyin da masu Kutse suke bi wajen satar bayanan mutane, wanda ana ganin yawan hanyoyi da dabarun sunkai 25,000, sun samu waxannan hanyoyi da dabaru ne da ta hanyar tsananta bincike ba tare da an gano manufar yin hakan ba. Google sunce shaidawa masu amfanin da shafinsu, zasu gudanar da binciken na tsawon lokaci domin gano hanyoyi da dabarun da masu Kutse suke bi don satar bayanan mutane, kuma lallai sun samu nasarar gano hanyoyi masu yawan gaske da masu Kutse suke bi don

satar bayanai, sun bada misali da cewa ko mutum bai da qwarewa sosai a dabarun yin Kutse to mai sauki ne ya samu bayanai na yadda zai iya yin Kutse a dandalin masu Kutse dake intanet. Misali a kwanan nan anyi wani Kutse da ake kira da sunan “Equifax Hack” wato Kutsen Equifax, inda masu Kutse suka samu nasarar sace bayanan mutane masu yawan gaske, ana ganin a cikin shekara xaya an saci bayanai da suka biliyan 1.9, an hada sakamakon binciken gaba xaya harda watan Satumba an samu adadin bayanai da aka sace sun kai biliyan 3.3. Amma ana ganin masu aikata laifukka a intanet suna da matuqar dabaru sosai, suna amfani da hanyoyi biyu da suka fi shahara domin satar bayanai, hanya ta farko itace suna yaudarar mutane sai mutum ya dauka wasu amintattu ne don haka sai ya basu bayanai da suka shafi harkokin shi na intanet, sai kuma hanya ta biyu wato suna dibar duk bayanan da mutum yake sawa a shafukkan intanet, misali lambar katin ajiyar banki da sauransu. Binciken na Google ya iya gano adaxin mutum kusan 788,000 da za a iya yaudara a saci bayanan su, mutum miliyan 12.4 kuwa za a iya

dibar sirrikansu ba tare da sun sani ba, don haka wannan Kutsen yana iya afkuwa a ko wanni lokaci, a kullum ana iya yaudarar mutum sama da 234,887 ta intanet, a yayin da ake iya dibar bayanan mutum kusan 14,879. Lambobin buxe ma’ajin bayanai kaxai basu wadatarwa wajen yi wa mutum Kutse, dan haka masu Kutse suke qoqarin samun sauran bayanai masu muhimmanci, wasu masu Kutsen suna iya satar bayanin wajen da mutum yake, lambar waya, lambar katin ajiya da sauran bayanai masu muhimmanci na mutanen da suke qoqarin shiga shafukkan intanet. Duk da shafin Google yana iya ganowa in aka yi qoqarin shiga shafin intanet a wajen da ba a saba shiga ba, misali in kamfanin yaga ana qoqarin shiga shafinka a jihar Kalifoniya ta Amurka bayan an saba kai daga jihar Kadunan Nijeriya ka saba buxe shafinka to Google xin zasu yi qoqarin ankarar da kai, saboda hakane ma Google xin suke iya hasashen duk guraren da yakamata ka bude shafinka. Google xin sun kara wani mataki na tsaro musamman ga masu amfani da akwatin wasiku na Gmail, kuma wannan matakin yayi nasarar kiyaye akant kusan miliyan 67 na Gmail daga masu Kutse.

A watan da ya gabata Google xin sun kara fito da wasu hanyoyi da mutane zasu yi amfani da su don kara tsare akant dinsu na Gmail, cikin mataken harxa wanda kai da kanka zaka saka don lokacin da ka ga dam aka zaka iya canzawa, duk da masana da dama suna ganin yakamata Google xin su sake fito da dabaru sosai na bawa mutane kariya daga masu Kutse, amma ana ganin mutane da yawa basu damu suyi amfani da matakan kariyar ba. Ana sa ran mutane zasu rungumi waxannan matakan na tsare akant dinsu, mutane da dam sunfi son hanya mai sauki wajen tsare akant dinsu, misali kamfanin Amazon suna da matakan kariya ga masu tahamulli da shafinsu, inda duk masu tahamulli da shafinsu sai sun amsa wasu tambayoyi da suka shafe su kafin su iya buxe akant dinsu, ana ta qoqarin fadada hanyoyin maganin masu Kutse ga masu tahamulli da shafukkan intanet. Kuma kamfanin Google ne a sahun gaba a wannan qoqarin, saboda masu amfani da shafukkansu kusan sunfi na ko wanni shafi yawa, sannan mutane suna tara bayanansu masu matuqar muhimmanci a shafin, don haka suke ganin baza su yi qasa a gwiwa ba wajen samar da hanyoyin da masu tahamulli da shafinsu zasu bi don tsare bayanansu daga ‘yan Kutse masu satar bayanai.


26 RAHOTON MUSAMMAN

A Yau

Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Nijeriya Ba Ta Da Cikakkiyar Ma’adana Kan Yadda Ake Amfani Da Mai —NBS Daga Abubakar Abba

Koda yake Nijeriyake akan itace kan gaba a cikin nahiyar Afrika wajen fitar da manfetur, sai da abin takaici, itace ta xaya a nahiyar wajen shigo da man da aka sarrafa cikin qasar. A cewar hukumar NBS duk da cewar, itace ke akan gaba wajen shigo da dangin mai da aka sarrafa harda fetur,babu xaya daga cikin hukumin gwamnatin dake da cikakken ma’adanar bayanai akan yadda ake yin amfani da man a kullum a qasar nan. Janar na qididdigar na qasa, Yemi Kale ya shaida wa kafar yaxa labarai ta Premium Times cewar, dukkan ma’adanan bayanai da kafafen ‘yaxa labarai suke bugawa a yanzu da wanda sauran hukumomin gwamnati suke fitar wa sun tsufa ko kuma ana yi masu kwaskwarima ne kawai. Mista Kale, wanda ya sanar da hakan a ranar Juma’ar da ta gabata a Abuja ta hanyar mataimakin Esiri Ojo, ta hanyar wayar tafi da gidan ka, ya ce waxannan ma’ajiyar bayanan baza a iya dogaro akan su ba wajen samar da tsari ko xaukar matakai a hukumance ba. A cewar sa, “a yanzu mu a (NBS) bamu da cikakkiyar ma’adanar bayanai akan man da ake amfani da shi, amma muna gudanar da bincike da zai samar da cikakken bayanai a fannin. A cewar sa, duk alqaluman da ku ke ji hukumin gwamnatin tarayya harda kafafen yaxa labarai suke bugawa kawai shaci faxi ne. Hukumar ‘yan NBS itace keda alhakkin tara dukkan bayanai da qididdiga akan dukkan ayyukan da suka shafi fannonin tattalin arzikin

qasar nan. Bayanai Masu Cin Karo Da Juna Na Kamfanin Nnpc Dana Hukumar PPPRA: Mai magana da yawun kamfanin (NNPC), Ndu Ughamadu, shima ya tabbatar da wannan maganar, inda ya ce har yanzu qasar nan ba ta da qididdigar ma’adanar bayanai takamai miya akan bayanan man da ake amfani da shi a qasar ba. A cewar sa, kamfanin NNPC baida tabbacin qididdigar man da ake amfani da shi a qasar nan. Ya ci gaba da cewa, kamfanin ya dogara ne kawai akan alqaluman sashen qayyade farashin mai (PPPRA) take samar wa. Mista Ughamadu ya bayyana hakan ne a hirar da kafar Premium Times ta yi da shi ta hanyar wayar tafi da gidan ka. A cewar sa hukumar (PPPRA), itace keda alhakkin qayyade farashin mai a qasar nan, amma har ita kanta kuma alqaluman data ke samarwa suna cin karo da juna. A 2012, lokacin da tallafin mai yake xaya daga cikin tambarin farashin yin amfani da mai alqaluman sun haura daga qasa da lita miliyan

talatin a duk kullum zuwa kimanin lita miliyan sittin. Alqaluman Kamfanin NNPC da hukumar PPPRA ma’adanan bayanan su suna cin karo da juna akan yadda ake yin amfani da mai, inda hakan ya sanya yan ‘yan kasuwa masu sayar da man suke yin amfani da alqaluman wajen yin iqirari ga gwamnati akan tallafin na mai don samar da shi. A ranar bakwai ga watan Fabirarun 2017, qaramin da albarkatu Ibe Kachikwu ya shedawa kwamitin dake majalisar wakilai cewar, man da ake amfani da shi a kullum a qasar nan, ya kai yawan lita miliyan ashirin da takwas. ministan ya ci gaba da cewa, alqaluman sun sauka daga kimanin lita hamsin zuwa hamsin da biyar a ranar da hukumar hukumar (PPPRA) ta fara yin amfani da biyan tallafi akan mai. MA’ADANAR BAYANAI TA NBS DA TA NNPC SUNA CIN KARO DA JUNA: Qididdigar hukumar NBS a yanzu akan yadda ake yin amfani da mai a watan Nuwambar 2016. A cikin rahoton da hukumar ta wallafa ta ce,

kimanin lita biliyan 12.66 na mai ne ake amfani da shi a qasar nan daga cikin watan Janairu da kuma watan Satumba shekarar. Yawan kwanukan daga tsakanin xaya ga watan Janairun da kuma na ranar talatin ga watan Satumbar 2016 ya kai yawan 273 ko kuma watanni takwas da kwana ashirin da tara. NBS ta ci gaba da cewa, alqaluman sun kai kimanin lita miliyan 51.87 a kullum. Amma alqaluman sun haura yadda ake yin amfani da man kamar yadda NNPC ta wallafa a cikin sanarwar akan qididdiga ta shekara a kafar ta ta yanar gizo. Sanarwar data wallafa ta nuna cewar, kimanin lita biliyan 17.41 ko lita miliyan 47.6 ta mai ake samar a kullum, aka rabar a 2016. TAYAR DA JIJIYAR WUYA TSAKANIN NNPC DA SHUGABAN R I K O N O N I N KAMFANIN: A lokacin da ake cikin rikici ta kwanan baya, shugaban kamfanin rikonin kamfanin NNPC Maikanti Baru, ta qara janyo ruxani akan maganar. A cikin watan Maris na wannan shekarar a

Ci gaba a shafi na

27


A Yau

Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

RAHOTON MUSAMMAN 27

Nijeriya Ba Ta Da Cikakkiyar Ma’adana Kan Yadda Ake Amfani Da Mai —NBS Ci gaba daga shafi na

26

lokacin ganawar da aka yi da Kwamtirola Janar na Kwastam Hameed Ali, Baru ya bayyana cewar, a qarqashin maidowa da wasu suke kira tallafi, ya kai yawan tsadar da kamfanin NNPC ya qiyasat da kimanin yadda ake samar da mai naira biliyan N774 na dukkan samar da shi. Amma Mista Ughamadu ya warwarewa kafar Premium Times alqaluman da Baru ya bayar cewar basu ne na haqiqar abinda aka kashe ba. Ya ce, anyi kawai kirdado ne akan farashin mai da kuma xanyen mai akan wani matsayi na kasuwar mai ta duniya da kuma kuxin saukale na mai a qasar nan. A cewar Ughamadu, sakamakon qarin da aka samu na farashin xanyen mai a kasuwar mai ta duniya da kuma irin qarin da aka samu na shigo da mai, an samu qarin farashi mai yawa maban banta tsakanin farashin da aka qayyade na sayar da kuma yadda aka karya farashin a qasashen dake maqwabta ka da Nijeriya. Ya ce, abinda wannan yake bufi shine, farashin da gwamnati ta qayyade na kimanin sayar da mai akan lita naira 145 da kuma buxe farshin da aka yi wanda ya kai naira 171 akan ko wacce lita xaya banbancin farashin ya tsaya akan naira ashirin da shida na kowacce litar mai xaya. Ya yi nuni da cewar, a bisa wannan kirdadon da aka yi kimanin lita miliyan talatin da biyar ta mai ake amfani da ita a kullum, inda kuma yawan karvowa ko tallafin mai ya kai kimanin naira biliyan 774 a duk shekara. A wata ‘yar gajeriyar hira da manema labaran fadar shugaban qasa suka yi da Maikanti Baru ya ce, a qarqashin dawo da naira biliyan 774 a shekara, anyi

tane akan kirdadon da aka yi na yawan man da ake amfani da shi a kullum da kuma farashin xanyen mai a kasuwar mai ta duniya. A bisa fasalin da aka yi na alqaluman zasu kai kimanin naira biliyan 64.5 duk wata ko kuma naira biliyan 2.081 a kullum. Sakamakon banbancin farashi tsakanin buxaxxiyar kasuwa na farashin naira 171 da kuma farashin da aka amincewa ‘yan kasuwa akan naira 145 na kowacce lita xaya. A dogon nazarin da akayi, ya nuna cewar a qalla ana yin amfani da mai lita biliyan talatin a kullum a qasar nan. Kakakin kamfanin NNPC a kwanan baya ya sanar da cewar, man da ake xaukowa daga ma’ajiyar mai ya ragu da qasa lita miliyan talatin a kullum. A cikin watan Agustar 2017 an samar da sama da lita miliyan hamsin na mai. Ya bayyana cewar, alqaluman daga baya sun qaru da kimanin lita miliyan 84.2 a ranar takwas ga watan Dismabar 2017. Ya ce, yadda farashin xanyen ya tashi, haka kuxin saukale na mai yake tashi a qasar nan.

A bisa qiyasin da NNPC ta yi na yin amfani da mai, ya hau da kimanin lita miliyan hamsin da biyar a kullum, inda kuma a qarqashin dawo tsadar, shima ya haura da kimanin naira biliyan 993 a shekara. A kan lita miliyan hamsin a qarqashi maidowa ya haura da naira tiriliyab 1.11 na lita miliyan hamsin da biyar a kullum ko zuwa naira tirliyan 1.22 na lita miliyan sittin a kullum ko naira tiliyan 1.33 akan lita miliyan sittin da biyar a kullum ko naira tiriliyan 1.44 akan lita miliyan saba’in a kullum da kuma naira tiriliyan 1.55 a shekara. BINCIKEN NBS DAKE TAFE: A kwanan baya Mista Kachikwu ya sanar da cewar akan tsafar dawo wa ta haura da kimanin naira tiriliyan 1.4 a shekara, inda hakan ya nuna cewar, ma’aikatar mai da albarkantu mai yuwa ta yi kirdado ne akan yawan man da ake amfani da shi, inda NNPC ta qiyasta ya kai yawan lita miliyan sittin da biyar a kullum. Sai dai, Ibe daga baya ya janyew wannan furucin da ya yi akan alqaluman, inda

ya ce, ma’aikatar tana kan gudanar da aiki da wasu hukumomin gwamnati don samar da cikakken bayanai. Mista Kachikwu mai yuwa ya yi wannan bayanin ne a bisa binciken da NBS ta fitar na cewar tana kan yin haxaka da ma’aikatar mai da albarkantu da kamfanin NNPC da kuma PPPRA gidauniyar albarkantun mai akan yawan man da ake amfani da shi a qasar nan. A cewar Mista Ojo, binciken zai haxa da yadda ake amfani da man a gida da masana’antu akan tattalin arzikin qasa don samar da bayanai na haqiqa akan alqaluman man da ake amafani da shi a qasar nan. Ojo ya ce, a bisa bayana da NBC ta gudanar da bincike akai, zata yi nazari akai don fitar da bayanai na haqiqa akan man da ake amfani da shi a qasar nan, amma ba wai kawai yin shaci faxi ba. Ya bayyana cewar, a yanzu haka ana kan gudanar da tarurruka da dama tsakanin NBS da hukumomin aka yi haxaka da su tuni don samar da wani tsari da ake son kammalawa a cikin ‘yan watanni kafin tsakiyar shekara.


28 RAHOTO

A Yau

Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Tsarin Ci Gaban Nijeriya: FCDA Ta Himmatu Wajen Kammala Abubuwan More Rayuwa A Idu Daga Idris Aliyu Daudawa

Yayin da ake ci gaba dayin dukkan abubuwan da suka dace saboda dawo qimar ta da komaxar ci gaban tattalin arziki na Nijeriya, ya kuma kasance an ya koma dai dai dana sauran sassan Nijeriya. Hukumar babban birnin tarayya ta ba masu zuba hannun jari tabbacin cewar, a shirye take domin ta ga cewar, ta kammala cikin lokaci, abubuwan more rayuwa a sashe na biyu wurin shaqatawa na masana’antu dake Idu. Wannan kuma shi zai sha masu sha’awar zuba hannun jari na gida dana waje. Ministan babban birnin tarayya Malam Muhammed Musa Bello shi ne wanda ya bada wannan tabbacin ranar Talata, a Abuja Sheraton Hotel. Ministan babban birnin tarayya Malam Muhammed Musa Bello shi ya bada wannan tabbacin ranar Talata ta wannan mako, a ranar babban birnin tarayya Abuja, a wurin taron ci gaban tattalin arziki da kuma tsare tsaren yadda za a cimma kai gaci, wanda aka yi a Hotel xin Sheraton. Bugu da qari tawagar babban birnin tarayya a wurin taron ta qunshi, Sakataren

din din din Mr Chrisrtian Chinyeaka Ohaa, Sakataren babban birnin tarayya Engr Umar Gambo Jibrin, Shugaban ma’aikata Bashir Maibornu, da kuma sauran manyan jami’ai, sun tattauna da masu zuba hannun jari, ba domin komai ba, sai saboda idan akwai wasu matsaloli, waxanda zasu iya kawo cikas, ayi maganinsu, saboda kada su hana masu sha’awar zuba hannun jari zuwa. Babba daga cikin masu sa hannun jarin shi ne Zeberced wanda xan qasar Turkiyya ne, wanda a halin yanzu yana yana gina kashi na biyu na filin masana’antu na Idu, wanda fili ne mai hekta 245, ana sa ran zai samar da fulotai 170 na kafa masana’antu, waxanda masu zuba hannunn jari daban daban, da suka haxa da yin kayayyaki, sayar da kayayyaki, kasuwanci , da kuma samar da dubban ayyuka. Shi dai taron ya gano wata hanya wadda ba a kammala ba,. Wadda zata kais u masu zuba hannun jarin zuwa filin masana’antun, abin da suka fahimci yana xaya daga cikin abubuwan da zasu kawo matsala ga masu sa hannun jari. Ministan babban birnin tarayya da kuma Ministar

•Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja

kasafin kuxi, da kuma tsare tsaren manufofin qasa, Zainab Ahmed, sun amince da zasu yi aiki tare, wajen samo kuxaxen da za a kammala ita hanyar. Fahimtar junan da aka samu tsakanin shi Zeberced da kuma su Ministocin biyu, hakan ya bada dama wajen samun makamar zaren, domin shawo kan al’amura, waxanda suka shafi sauran masu son zuba jari, saboda suma sun bayyana al’amuran da suke sha masu gaba. Manyan masu zuba jari a Hukumar lafiya ta duniya, kamfanonin harhaxa

magunguna waxanda aka amince dasu, kamfanin iskar gas, kamfanonin da suke yin takalma, duk sun buqaci da a basau filaye, domin su kafa masana’antun su, duk an haxa su da shi wanda yake lura da gina wurin saboda su suna sha’awar dawo da masana’antunsu. Ministan babban birnin tarayyar ya umurci Kamfanin zuba hannun jari wanda ake kira Abuja Investment Company, dasu gaggauta tabbatar da cewar, masu sha’awar zuba hannun jari, waxanda suka nuna sha’awarsu ta a basu fili a

Abuja Technology Village (ATV) , an basu dukkan gudunmawa da kuma shawarwarin da suka kamata. Ma’aikatar kasafin kuxi da tsare tsaren qasaita ta shirya taron , wanda kuma shi ya bayyana dalilai uku na shirya shi taron, na farko shi ne a dawo qarfin ci gaban tattalin arziki, kamar yadda yake a da, da a qalla kasha 7 cikin xari nan da zuwa shekara ta 2020, su sa hannun jari a Nijeriya, wannan kuma shi taimakawa ‘yan Nijeriya samun daxi zaman rayuwarsu, da kuma havaka shi tattalin arzikin.

2019: Dukkanin Mabiyi Na Ya Fito Ya Yanki Katin Zave Domin Kwarar ‘Yancinsa –Shaikh Dahiru Bauchi Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Babban Malamin xarikar Tijjaniyyar a Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi qarin haske kan qiran da yake yi wa mabiyansa na su fito kansu da kwarkwatansu wajen yankan katin zave na dindindin domin takadarwa don yin amfani da wannan katin a zaven da ke tafe don aza nagartaccen mutumin da suka ga ya dace kuma zai yi musu aiyukan da suka kamata. Shehu Xahiru Bauchi, wanda ya yi wannan qarin hasken a hirarsa da manema labaru a gidansa da ke Bauchi a ranar Talatar nan, yana mai cewa, Nijeriya qasa ce wacce kowa na da ikon yin zaven da ya dace da shi domin kafa wanda zai biya masa dukkanin buqatunsa ta hanyar shugabanci. Ya bayyana cewar ta wannan hanyar ne kaxai

xan Nijeriya zai iya yaqar wanda bai so kuma cikin sauqi domin a cewarsa zavar shugaba na gari tamkar bayar da dama ce wajen wanzar da shugabanci na gari, don haka ne ya umurci mabiyansa da cewa; “Dukkanin mutanenmu su fito su yanki katin zave,” a ta bakinsa. Shehi ya bayyana cewar qasar Nijeriya qasar su ce don haka suna da haqqin fitowa domin neman wanda suke so, haxe da xavar mutumin da suka tabbatar zai yi musu aiyukan da suka zave sa don su. Ta bakinsa yake cewa Nijeriya musulmi da kirista kowa na da zarafin zavin da yake so ta fuskacin shugabanci, “Ai qasar Nijeriya ta musulmi ne da wanda ba musulmi ba; waye zai yadar da haqqinsa? Wani dai ba zai yada haqqinsa ba. tun da abun ya zama yaqin

da ‘yar qaramar takarda ake yi bada makami ba; ai ya yi sauqi, ka je ka jefa kuri’ar ka zavi wanda zai mallakeka wanda kuma kake ganin alamar zai biya maka buqatarka a zamanka na xan qasa,” In ji Xahiru Bauchi. Bauchi ya xaura kuma da cewa kuri’ar mutum makaminsa ce, domin da quri’a mutum ka iya kashe kansa ko ya yanka kansa, don haka ne ya buqaci kowa ya yi amfani da wannan makamin tasa wajen zavar na gari, “Wai wasu ‘yan siyasa suna cewa quri’arka-‘yancinka. Ni kuma ba haka nake cewa ba. ni ba xan siyasa bane, amma abun da na ke cewa, shi ne quri’arka makaminka, wuqarka ka bai wa wanda zai yanka ka ko kuma wanda zai yanka maka. “Masoyinka wanda yake sonka zai yanka maka in ka bashi quri’arka zai yanka maka, maqiyinka ko kuma

masoyinka na suna idan ka ba shi wannan quri’ar to soyaka zai yi kuma ya yanka ka. Soboda haka ka san fuskokin mutune tun daga farko, ka san masoyinka ka san maqiyinka. Dukkaninmu ‘yan Nijeriya mun san masoyanmu da kuma maqiyanmu, mun san su, sai in lokacin kada quri’ar idan ya kammala yi sai mu kada ma wanda muke so,” in ji Shi. Daga bisani ya kuma nemi dukkanin wani xan Nijeriya da ya fito fagen zave domin zavar na gari a kowani lokaci. Da ya juya kan shuwagabanin kuwa, Shehu Xahiru Bauchi ya gargaxi shugabanni kan waxanda suke shugabanta domin a cewarsa kowani shugaba ya dace ne ya tabbatar da cika alqawuran da ya yi wa jama’arsa a lokacin yaqin neman zave “Ainuhin abun da ake nufi da gwamnati musamman gwamnatin

siyasa, jama’a ne idan suna da wasu abubuwan da ba za su iya samu ba sai su nemi gwamnati ta hanyar siyasa, su kuma ‘yan siyasa za su nemi yin aiyukan da za su kare mutane daga sharri da kuma samar musu da alherin da suke buqata. in an zavi gwamnati ba ta kawo alheri ba sai sharri, ba ta ture sharri ba sai alheri ta ture wannan ai ba gwamnati bace, a don haka ne muke jawo hankulan mutane su yi karatun ta nutsu,”. Ya bayyana cewar duk wanda ya fito gaban jama’a aka kada masa kuri’a ya ci ya kamata ya yi dukkanin mai iyuwa domin rage wa jama’ansa matsatsin da suke ciki “Ana wahala don haka muna qira ga gwamnati ta yi duk mai iyuwa domin rage wa jama’a halalhalun da suke ciki domin a samu gudunar da shuganci yadda ya dace,” kamar yadda ya ce.


A Yau

29

Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Qasashen Waje

Tare da Rabiu Ali Indabawa 08069824895

An Kori Ma’aikatan Jinya 4,000 A Zimbabwe Gwamnatin ta Zimbabwe dai na zargin ma’aikatan jinyar da fakewa da aikinsu wajen nuna adawar siyasa gareta duk da matakan inganta bangaren lafiyan da ta ke dauka. Gwamnatin Zimbabwe ta kori dukkanin kananan likitoci da suka shiga yajin aiki domin neman kara masu albashi. Adadin wadanda aka kora daga aikin zai kai mutane dubu 4 kamar dai yadda mataimakin shugaban kasar Constantino Chiwenga, ya sanar. Tuni dai aka kwashe dubban marasa lafiyan da ke kwance a mabanbanta asibitoci tare da raba su zuwa manyan asibitocin kasar kafin daukar mataki na gaba. Dubban jami’an kiwon lafiyar dai na bukatar gwamnatin kasar ta kara musu albashi tare da alawusalawus duk kuwa da cewa

a baya gwamnatin ta fitar akalla dalar Amurka miliyan 17 don habaka bangaren lafiyar kasar. Kalaman mataimakin shugaban kasar Constantino Chiwenga ya zargi jami’an da fakewa da aikinsu wajen nuna adawar siyasa ga gwamnati mai ci. Chiwenga ya ce gwamnati za ta yi hayar tsaffin jami’an kiwon lafiyar don ci gaba da jan ragamar harkokin lafiyar kafin daukar mataki na gaba. Sanarwar da qungiyar jami’an kiwon lafiyar ta fitar a yau ta ce sun samu sanarwar mataimakin shugaban kasar kuma hakan ba zai hana su ci gaba da yajin aikin don neman hakkokinsu ba. Qungiyar dai ta koma yajin aikin ne bayan wanda ta shafe mako guda tana yi a cikin watan nan kan abin da ta kira rashin biya mata wasu hakkokinta.

Barbara Bush, Matar Tsohon Shugaban Amurka Ta Rasu

Kamar yadda aka yi fargabar zai faru saboda laulayin jikinta, Barbara Bush, matar tsohon Shugaban Amurka George WH Bush, ta rasu a shekaran jiya. Matar tsohon Shugaban Amurka Barbara Bush ta mutu da shekaru 92 a duniya. Wata takardar bayani daga iyalinta ta ce marigayiyar ta mutu ne da yammacin jiya Talata, yayin da dangoginta ke gangan da ita. “Kaunatacciyar mahaifiyata ta rasu da shekaru 92,” abin da tsohon Shugaban Amurka George W. Bush ya fada kenan a wata takardar bayani. Ya kara da cewa, “Da Laura, da Barbara, da Jenna da ni duk mu na cikin bakin

ciki, to amma hankalinmu ya kwanta saboda mun san ita ma hankalinta ya kwanta. Barbara Bush ta kasance mashahuriyar matar Shugaban kasar Amurka kuma mace wacce samun irinta sai an tona, wadda ta rika kawo farin ciki da kauna da kuma ilimi ga miliyoyin mutane. A gare mu ta ma zarce hakan. Mahaifiyar ta mu ta sa mun yi tsaye, mu na ta dariya har zuwa karshen rayuwarta. Na yi sa’a da Barbara Bush ta kasance mahaifiya ta. Lallai za mu yi matukar kewarta a cikin dangi, kuma mun gode ma ku duka saboda addu’o’i da fatan alharin da ku ke ma na.” Iyalin Bush ba su yi wani

cikakken bayani game da lafiyarta ba, inbanda cewa da su ka yi a ‘yan shekarun nan ta yi fama da ciwo mai alaka da illa a zuciya. Ta yanke shawarar daina shan magani yayin da halin da ta ke ciki ke dada munana a ‘yan kwanakin nan. Barbara Pierce, (kamar yadda sunanta ya ke kafin aure) ta auri George Herbert Walker Bush ranar 6 ga watan Janairun 1945. Sun haifi ‘ya’ya shida kuma sun kasance ma’aurata mafiya dadewa cikin dukan wadanda su ka taba shugabantar Amurka. George H.W. Bush ne Shugaban Amurka na 41 wanda ya yi mulki daga 1989 zuwa 1993.

Bayan zarginta da kai harin guba: Qasar Syria ta kai Hari Yankin Ghouta Dakarun gwamnatin Syria sun kai hari da jiragen sama kan yankin Ghouta da ke gabashin birnin Damascus, karo na farko daga lokacin da aka fara zargin gwamnati da yin amfani da makami mai guba a garin Douma. Qungiyar da ke sanya ido kan lamurran da ke faruwa a rikicin kasar ta Syria, ta ce an jikkata mutane da dama a harin. A shekaran jiya ne dai Jami’an da ke bincike kan amfani da makami mai gubar kan fararen hula suka isa birnin na Douma ko da yake dai shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Rasha ta goge duk wasu hujjoji da ake da su na kai farmaki da makaman masu guba kan fararen hula, batun da Rashan ke ci gaba da musantawa. Kasashen yammacin duniya dai da suka kunshi Birtaniya Faransa da kuma Amurka sun kai wasu farmaki Syrian kan abin da suka kira kunnen kashi da Bashar al-assad ya yi na kai hari da makami mai guba kan fararen hula. Masharhanta dai na gani abu ne mai wuya Shugaba

Assad ya kai farmakin da makami mai guba la’akari da cewa ya yi nasarar kwace kashi 90 cikin dari na yankunan da ke hannun ‘yan tawaye da sauran ‘yan bindiga, kuma ko a wancan lokaci bai yi amfani da makamancin makamin ba. A jiyan ne dai kasashen Turkiyya da Iran suka kara jaddada matsayarsu na ci gaba da mara baya ga Syrian musamman kan hare-haren da kasashen na yammacin duniya suka kai mata. A bangare guda suma kasashen Birtaniya da Faransa yanzu haka na ci gaba da shan suka daga al’ummarsu ganin yadda suka yi gaban kansu don kai harin Syria.


Wasanni A Yau Alhamis 19.4.2018

30

Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com

Ko Ka San ’Yan Wasan Da Suka Fi Yi Wa Manchester City Qoqari? Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

A ranar Lahadi ne Manchester City ta lashe kofin firimiyar qasar ingila bayan Manchester United tasha kashi a gidanta a hannun West Bromwich Albion daci 1-0. Manchester City ta zama zakara a Ingila ne da tazarar maki 16 tsakaninta da Manchester United da ke matsayi na biyu bayan daya rage wasanni huxu a kammala gasar. Kofin firimiya na uku ke nan da Manchester City ta lashe a shekara bakwai, kuma na biyar a tarihin qungiyar. Manchester City ta lashe kofin ne ana saura wasa biyar a kammala gasar, tarihin da Manchester United ta tava kafawa a kakar 2000-01. Idan kuma City ta samu maki tara daga sauran wasa biyar da ya rage, zai kasance ta samu maki 95, tarihin da Chelsea ta kafa a kakar wasa ta 2004 zuwa 2005. Sai dai ko yaya yan wasan qungiyar suka taimakawa qungiyar? KEVIN DE BRUYNE Ana ganin Kevin De Bruyne na iya lashe kyautar gwarzon xan wasan firimiya na bana, duk da yana hamayya da Mohammed Salah na Liverpool wanda shi kuma yafi zura qwallo a raga. De Bruyne ne ya fi yawan taimakawa a ci qwallo a gasar ta bana bayan daya taimaka aka zura qwallaye a raga sau 16 a gasar firimiya kawai. Amma rawar da xan wasan na Belgium yake takawa a Manchester City ta zarce haka, kamar yadda wasu ke kiran shi "zuciyar Manchester City kuma wanda babu kamarsa a qungiyar kawo yanzu. A lokacin da yake yabonsa, mai koyar da yan wasan qungiyar, Pep Guardiola ya ce De Bruyne ne ya taimaka wa qungiyar ta zama "gagara gasa."

DAVID SILVA Samun De Bruyne da David Silva a tsakiyar fili ya qara wa Manchester City qarfi tsakaninta da abokan hamayyarta na gasar fiurimiya kuma yan wasannin biyu sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar qungiyar David Silva na cikin 'yan wasan da ke nuna kansu a manyan wasannin Manchester City kuma shine ya fara buxe raga a karawar hamayya da Manchester United a Old Trafford. A kakar bana Silva ya taimaka an ci qwallo 11 a firimiya, kuma shi ne na uku a jerin 'yan wasan da suka fi bada qwallo a ci. RAHEEM STERLING Raheem Sterling bai tava nuna qwazo ba kamar kakar bana bat un bayan komawarsa qungiyar daga Liverpool shekaru biyu da suka gabata. Wasu na ganin Guardiola ne ya sauya xan wasan na Ingila mai shekaru 24 yazama qwararre kamar haka yayinda wasu suke ganin daman xan wasan da qwarewarsa. Sterling ne xan wasan Manchester City na biyu da ya fi yawan cin qwallaye a raga bayan Sergio Aguero, kuma qwallayensa na cikin waxanda suka yi tasiri ga nasarar lashe kofin firimiya. Raheem Sterling ya ci qwallo biyu a kwanaki uku ana dab da tashi wasannin da Manchester City ta doke Huddersfield da Southampton 2-1 a watan Nuwamba shekarar data gabata SERGIO AGUERO Sergio Aguero ya yi zamani da 'yan wasa da kuma masu horar da 'yan wasa da dama a zamanin da Manchester City ta fara tashe a yan shekarun baya. Amma duk da haka xan wasan ya ci gaba da zama dodon raga a kulub din duk da cewa girma yafara kamashi kuma akwai matasan yan wasa yanzu a

qungiyar. Xan wasan na Argentina da ya koma Manchester City a shekara ta 2011, kuma yanzu shi ne wanda ya fi yawan cin qwallaye a tarihin qungiyar. A bana ma Sergio Aguero ne kan gaba da yawan cin qwallaye inda ya ci wa Manchester City qwallo 21. Xan wasan ya kafa tarihi a bana duk da ya fuskanci qalubale bayan zuwan Gabriel Jesus da Guardiola ya sayo a watan Janairu. MAI TSARON RAGA EDERSON Mai tsaron raga Ederson mai tsaron ragar da Manchester City ta sayo a kan fam miliyan 35 ana dab da kammala kakar da ta gabata, yana cikin 'yan wasan da suka taka muhimmiyar rawa. Mai tsaron ragar ya saje da irin salon qwallon da Guardiola yake so, inda ya qwace gurbin Claudio Bravo. Guardiola ya fi son ana tava qwallo da gola, kuma Ederson ya iya take qwallo da yanka sannan yana taimakawa 'yan wasan gaba da doguwar qwallo domin kai farmaki ga abokan hamayya, tsarin da Guardiola ya fi so. PEP GUARDIOLA Guardiola ya lashe kofin firimiya ne a kakarsa ta biyu a Manchester City kuma ana ganin cefanen sabbin 'yan wasa da Guardiola ya yi sun taimaka ma sa, musamman Gabriel Jesus da Leroy Sane da John Stones da Benjamin Mendy da Bernardo Silva da kuma mai tsaron raga Ederson. Kuma salon tsarin qwallon tsohon kocin na Barcelona da Bayern Munich shi ne ya yi tasiri a Manchester City. Sai dai tuni mai koyarwar yayi alqawarin cigaba da mamaye gasar ta firimiya bayan daya xauki aniyar siyo sababbin yan wasa


WASANNI 31

A Yau Alhamis 19 Ga Afrilu, 2018 (2 Ga Sha’aban, 1439)

Guardiola Yana Zawarcin Mbappe Da Thiago Alcantara Daga: Abba Ibrahim Wada Gwale

Rahotanni daga qasar ingila sun bayyana cewa mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Manchester City yafara zawarcin xan wasan qungiyar qwallon qafa ta PSG, Kylian Mbappe da kuma Thiago Alcantara na qungiyar qwallon qafa ta Bayern Munchen. Guardiola dai ya koyar da Alcantara a qungiyoyin Barce-

lona da Bayern Munchen a shekarun baya sannan yanzu ma yana qoqarin sake siyo xan wasan domin sake haxuwa a Manchester City sakamakon yan wasan tsakiyar qungiyar, David Silva da Yaya Taure da kuma Fernandinho girma yafara kamasu. Mbappe dai yakoma PSG daga qungiyar Monaco a matsayin aro da yarjejeniyar zai koma qungiyar a matsayin na din-din-din akan kuxi fam miliyan 166 a qarshen wannan kakar da ake bugawa. Guardiola dai yana son siyan yan wasan da yake buqata kafin a tafi gasar cin kofin duniya a watan Yulin wannan shekarar inda tuni ya bayyana waxannan yan wasa a matsayin yan wasan da yake ganin zasu taimaka masa wajen kare kambunsa. Xan wasa Wilfred Zaha ma na qungiyar Crystal Palace yana cikin yan wasan da ake tunanin Guardiola zai nema amma baya cikin waxanda yake nema ruwa a jallo sai dai yanason siyansa domin qara qarfin yan wasansa na gefe. Manchester City dai ta lashe gasar firimiya a ranar Lahadin data gabata bayan Manchester United, wadda take mataki na biyu tasha kashi har gida a hannun Westbrom har gida daci xaya mai ban haushi wanda hakan yasa yanzu maki 16 tsakaninsu yayinda ya rage saura wasanni biyar a kammala gasar ta firimiya.

Ban Damu Da Halin Da Bale Da Benzema Suke Ciki Ba -Zidane Daga Abba Ibrahim Wada Gwale Mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana cewa bai damu da halin da yan wasan qungiyar, Karim Benzema da Gareth Bale suke ciki ba na rashin buga wasanni a qungiyar akai-akai. Duka yan wasannin dai su biyu, Gareth Bale da Benzema basa samun wasanni a wasu lokutan a qungiyar sakamakon rashin qoqarinsu wanda hakan yasa aka fara raxe raxin cewa zasu bar qungiyar zuwa inda zasu dinga buga wasanni. Zidane yace yana farin ciki daga

qoqarin yan wasan sai dai kuma yace yanzu yafi mayar da hankali akan yan wasan qungiyar masu buga wasanni akai-akai kuma suke qoqari sosai. A hirarsa da manema labarai Zidane yace baya tunanin yan wasan suna cikin wani hali mara daxi sai dai kuma yace daman tana faruwa acikin qungiya a samu wasu yan wasan suna qoqari wasu kuma basayi saboda haka ba wani babban abu bane. A qarshe yace tabbas akwai qwararrun yan qwallo a qungiyar kuma kowa yasan haka, kuma Benzema yasan da cewa dole sai yana zura qwallo a raga sannan kuma yana taumaka yan wasan qungiyar

wajen zura qwallo. Bale dai ya zura qwallaye 11 cikin wasanni 21 daya buga a qungiyar a wasannin laliga yayinda Benzema yaci qwallo biyar cikin wasanni 26 daya buga a qungiyar a wannan kakar.

Fitila Mai Hoton Muhammad Salah Ta Bazu A Qasar Masar Daga Abba Ibrahim Wada Gwale Fitaccen xan wasan qungiyar qwallon qafata Liverpool Mohamed Salah ya bayyana a kasar Masar, amma ba a filin wasa ba. Xan wasan ya bayyana ne a matsayin wata fitilar azumin watan Ramadan a faxin qasar. Yayin da al'ummar Masar ke shirye-shiryen watan azumin Ramadan wanda za a fara a tsakiyar watan Mayu, wata fitila da ake raba wa lokacin watan azumin ta xauki sabon salo - wato fuskar shahararren xan wasan qasar. Hotunan fitilu masu xauke da fuskar Salah sun karaxe kafafen sada zumunta da shafukan Intanet a duk fadin kasar. Kafar yada labarai ta Al-watan a shafinta na Intanet ta rawaito cewa masu kantuna suna murna da zuwan azumin Ramadan da kuma nasarar samun gurbin zuwa gasar Kofin Duniya wanda za a fara a watan Yuni. Qasar Sin wato China ce take qera fitilar kamar yadda Al-Watan ta ruwaito, kodayake an tava hana shigo da fitilar a baya. Jaridu dai a qasar sun rawaito cewa kantuna sun fara samun kuxi daga sayar da fitilun. Xan wasan Masar din Mohamed Salah ya burge 'yan qasar ne tun daga watan oktoban shekarar 2017, lokacin da qasar ta samu gurbin zuwa gasar Cin Kofin Duniya ta 2018 - a karon farko tun shekarar 1990. A watan Maris, Salah ya kafa tarihi na kasancewa xan wasan da ya fi zura qwallo a raga a gasar firimiya a kakar wasa ta 2017 zuwa 2018.

Gasar Cin Kofin Duniya Idan Babu Ni Bazaiyi Armashi Ba, Inji Zlatan Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Ajiye Yan Wasan Da Na Yi Ya Yi Amfani, Inji Valverde Daga Abba Ibrahim Wada Gwale Mai koyar da yan waswan qungiyar qwallon qafa ta Barcelona, Enesto Valverde ya bayyana cewa hukuncin daya yanke na ajiye wasu daga cikin manya-manyan yan wasan qungiyar a wasan da qungiyar ta buga 2-2 da qungiyar Celta Vigo yayi dai-dai saboda yan wasan sun huta. Valverde ya yanke wannan hukunci ne saboda qungiyarsa ta Barcelona zata fafata wasan qarshe da qungiyar Sevilla na cin kofin Copa Del Rey na

qasar ta sipaniya a ranar Lahadi mai zuwa. Yace yan wasan da basa samun buga wasa yanzu sun samu kuma waxanda suke buga wasa koda yaushe sun samu hutu duk da cewa ba haka akaso sakamakon wasan ya kasance ba amma kuma tunda basuyi rashin nasara ba babu matsala. Ya qara da cewa yanzu zasu mayar da hankalinsu wajen yadda zasu buga wasan qarshen da Sevilla kuma yana fatan yan wasansa zasu dage domin ganin sun lashe kofin kafin kuma su lashe kofin laliga na bana.

Yaci gaba da cewa kawo yanzu wasanni biyu ya rage musu su samu nasara wato maki 6 domin su zama zakara a laliga kuma wasan da suka buga da Celta Vigo ma matsalar jan kati suka samu wanda aka bawa Sergio Roberto saboda haka da babu jan katin da sai sun samu nasara. A qarshe yace jan katin da suka samu ne yasa suka kasa matsawa Celta Vigo domin samun maki uku amma kuma matasan yan wasan da suka buga wasan sun burgeshi kuma yana fatan nan gaba idan suka sake samun dama zasuyi abinda yafi haka.

Tsohon xan wasan gaba na qungiyar Manchester United wanda a yanzu yake buga wasanninsa a qungiyar LA Galaxy ta qasar Amurka ya bayyana cewa yanason dawowa daga ritayar da yayi domin wakiltar qasarsa a gasar cin kofin duniya. Zlatan Ibrahimovic dai rabonsa da bugawa qasarsa qasa tun shekara ta 2016 bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Turai sai dai yace zai dawo domin har yanzu da ragowarsa a qwallon qafa. Yaci gaba da cewa gasar cin kofin duniya babu Zlatan bazaiyi armashi ba saboda yadda yake cin qwallaye da kuma yadda yake yin abubuwan burgewa idan yana buga wasa. Tun bayan da qasar tasa ta Sweden tasamu tikitin gasar cin kofin duniya aka fara raxe raxin cewa xan wasan zai iya dawowa daga ritayar da yayi domin wakiltar qasarsa a gasar saboda zai taimaka matasan yan wasan qasar. Ibrahimovic dai shine xan wasan dayafi zurawa qasarsa qwallaye a raga a tarihi inda ya zura qwallye 62 cikin wasanni 116 daya bugawa tawagar yan wasan qasar tun yana matashin xan wasa.


LEADERSHIP 19.4.18

AyAU Alhamis

Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA

LeadershipAyau

No: 127

N150

QASASHEN WAJE

Barbara Bush, Matar Tsohon Shugaban Amurka Ta Rasu > Shafi na 29

2019: Daga Ayyana Tsayawar Shugaba Buhari, Sai Kuma Me? Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@gmail.com

A

wannan makon Shugaba Buhari a wajan wani babban taron jiga-jigan jam’iyyar APC, shugaban ya bayyana musu aniyarsa ta sake tsayawa neman zave a shekarar zave ta 2019 dake taje a badi. Wannan batu bai zo da mamaki ba, domin da yawa daman ana tsammanin faruwar hakan. Tun kafin wannan lokaci da Shugaban ya ayyana cewar zai yi takara a zave mai, tuni masu neman gindin zama, da ‘yan bani na iya, da kuma masu tunanin za su iya ci gaba da al’adar nan ta lavewa a bayan Shugaba Buhari su ci zave suke ta batun idan har yaki bayyana cewar zai tsaya takara to za su maka shi a kotu. Kusan za a iya cewar yanzu Shugaba Buhari ya katse hanzarin duk wani mai son yin takarar Shugaban kasa musamman a jam’iyyarsa ta APC, wadda ake ganin akwai mutanen da suka nuna sha’awarsu ta yin takara a wannan zave da yake tafe. Cikin masu nuna irin wannan sha’awa akwai tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki (duk da yace bai ayyana zai yi takara ba) Ana ganin waxannan da ma wasu za su iya neman karawa a zaven fitar da gwani tare da Shugaba Buhari a zaven da za a yi. Zamu yi waiwaye kan zaven baya da kuma irin yadda ‘yan Nijeriya suka ci moriya ko akasinta a wannan mulki na Shugaba Buhari a zangon farko. A shekarar zave ta 2015, da yawan masu neman mukamai a kujerun Sanata da Gwamna da ‘yan majalisun tarayya, sun shiga rigar Buhari ne, inda suka dinga nuna cewar su nasa ne, zavensu kamar zavensa ne, domin shi za su taya aiki. Amma daga bisani, bayan Shugaba Buhari ya shimfida mulki suka yi wancakali da wannan taguwa ta Buhari da suka sanya. EH, gaskiya ne, ba daidai bane ‘yan majalisun kasa da Gwamnoni su zama ‘yan amshin shatar Shugaban kasa ba, su zama ba ra’ayin al’ummarsu bane a gabansu, kawai me Shugaban kasa yake si shi za a yi ko da kuwa ba shi ne ya dace ba. Wasu ‘yan majalisun, sun shiga rigar Buhari suka ci zave, amma daga bisani suka zo babu wanda suke yin adawa ko hamayya da shi sai Shugaba Buhari, duk kuwa da cewar adawa ba wai ana yinta bane domin ci gaban kasa, illa kawai domin wasu bukatun

Muqalar Alhamis

kai. Bayan haka kuma, Shugaban kasa ya sani, duk wanda ya sha inuwar gemu bai kai ya makogoro ba. Mutanen Arewa su ne suka bashi kaso 70 na quri’un da yaci zave da su, amma bisa irin yadda mutane ke yin qorafi, shi ne an bar mutanen Arewa wajen cin moriyar ayyukan raya kasa,inda yankunan Yarabawa suka fi kowa rabauta da ayyukan raya kasa na wannan Gwamnati. Dole ne mutanen Arewa su yi qorafi, domin tun da ake yin Gwamnati tun daga 1999 zuwa yau, babu wata Gwamnati da dan Arewa yake jin cewar tasa e 100 bisa 100 kamar wannan, domin mutane suna ganin Buhari ne zai kula da bukatun wannan yanki fiye da duk wani Shugaba da aka taba yi, amma kuma abin yazo da baza ta. Ya kamata Shugaban kasa ya sani cewar, matukar ba’a juya ko karkata akalar yin ayyuka kamar yadda aka yi a yankin kudu maso yamma zuwa ARewa ba, to mutanen Arewa ba za

su taba yafewa Buhari ba, domin sun fito kwai da kwarkwata suka zave shi domin cire musu she daga wuta, amma kuma yayi wancakali da dukkan bukatun yankin, wasu mutane da suka raba kafa wajen zavensa sune suke samun moriyar ayyukan raya kasa. Lallai muna bukatar ganin manya manyan ayyuka waxan da Arewa za ta yi bugun gaba da su wajen nuna cewar dan ta dan Arewa shi ne ya kawo su, ba wani bare ba. Tundaga harkokin ilimi da lafiya da raya kasa, tituna da masana’antu da sauransu. Sannan kuma, dole Shugaba Buhari ya kiyaye kawowa mutane gurbatattun ‘yan majalisa da Gwamnoni, domin abinda ya farau a baya, wasu suka sanya Sugaba Buhari ya dinga yi musu yakin neman zave da kansa, suna ta yayatawa a gidajen Radiyo na jihohinsu, karshe suka azo suka zama abokan gabar al’ummar da suke Shugabanta, suna yin abinda aba shi ne zabin al’umma ba, sun fi baiwa bukatunsu fifiko.

+23408099272908

Tilas ne, Shgaban kasa yayi takaa tsantsan, wajen marawa irin waxannan baragurbi baya da sunan cewar su ‘yan jam’iyyar Shugaban kasa. Saboda haka kuma, yanzu kan mage ya waye, ya kamata jama’a su bude idonsu, su dena bin innarududu, su tsaya su zabi mutanen kirki waxan da za su tausaya musu su jikansu, a kowacce jam’iyya suke ba lallai sai jam’iyyar da Shugaban kasa yake ciki ba. Ko ina akwai mutanen kirki kuma akwai baragurbi. Dan haka mutane su gane cewar, koma bayan tunani ne mutum ya dauka jam’iyya kaza ita kadai ce ta mutanen kirki, jam’iyya kaza kuma ta barayi ko mutanen banza, wannana ba gaskiya bane, wasa ne kawai da hankalin jama’ah, kuma babu abinda yake sabbaba irin haka sai jahilcin masu zave. Domin babu yadda za a yi, ace idan a jam’iyya kaza ne ba zaka zabi mutum ba, amma idan jam’iyya kaza ne sai ka zave shi, wannan ya zama wasa da hankali kenan, mutanen anza da dama sun fito daga wasu gurare sun shiga jam’iyya tare da Buhari, an zave su, sun koma yadda suke a matsayin barayi mabarnata masu ci da gumin talakawa. Lokaci yayi da za a daina yaudarar masu zave da sunanBuhari, ko jam’iyyar buhari, inda duk kaga mutumin kirki wanda gaskiyarsa da amanarsa suka bayyana, ko a wacce jam’iyya yake shi ne mutumin da ya kamata a zaba ba tare da wani la’akari da cewar jam’iyyarsa ta saba da ta Buhari ba.

Babba Da Jaka EFCC na gab da fara farautar Kwankwaso da Wamakko –Labarai

An zo daidai wurin!

Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 07036666850; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 07036666850. E-mel: leadershipayau@gmail.com, Leadershipayau@yahoo.com


Turn static files into dynamic content formats.

Create a flipbook
Issuu converts static files into: digital portfolios, online yearbooks, online catalogs, digital photo albums and more. Sign up and create your flipbook.