20.04.18
AyAU JUMA'A LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa
www.leadershipayau.com Leadership A Yau
JARIDAR HAUSA
LeadershipAyau
20 Ga Afrilun 2018 (3 Ga Sha’aban, 1439)
TA FARKO MAI FITOWA KULLUM A NIJERIYA
Bugu na: 032
N150
PDP Na Shirin Yin Maja Da Sauran Jam’iyyu? Daga Abdulrazaq Yahuza Jere, Abuja
Shugaban babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya ta PDP, Prince Uche Secondus ya bayyana cewa jam’iyyar tana tattaunawa da sauran jam’iyyun adawa, da qungiyoyi masu zaman kansu, da tsofaffin shugabanni na qasa gabannin zaven 2019.
Da yake jawabi a lokacin taron gaggawa na kwamitin gudanarwar jam’iyyar a Abuja jiya Alhamis, shugaban na PDP ya ce maqasudin faxaxa tuntuvar tasu shi ne haxa qarfi da qarfe domin kafa sabuwar gwamnati a 2019 don “ceto Nijeriya”. Sai dai kuma shugaban bai yi cikakken bayani kan jam’iyyar maja take son yi da sauran jam’iyyu ba, illa kafe kai da fata
da ya yi cewa dole ne su kori APC daga karagar mulki saboda ta gaza biya wa ‘Yan Nijeriya buqatunsu. “Wannan mummunan koma-bayan da qasar ta faxa ciki babban qalubale ne a gare mu a matsayin babbar jam’iyyar adawa mu sauya salon cimma burinmu tare da qwace goruba a hannun kuturu. >Ci gaba a shafi na 2
A Janye Amfani Da Naira 100 Da Gwamnatin Jonathan Ta Buga 4
— MURIC
Daga hagu: Muqaddashin Babban Kwamandan Askarawan Amurka mai kula da Afirka, Birgediya Janar Leboceuf, Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Nijeriya, Janar Gabriel Olonisakin; Babban Hafsan Dakarun Sojin Qasa na Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai da kuma Jakadan Amurka a Nijeriya, Stuart Symington yayin rufe babban taron dakarun sojin qasa na Afirka a Abuja, jiya Alhamis.
Fursunoni Masu Xaurin Rai Da Rai Za Bincike: Yin Wanka Kullum Su Yi Digirin Digirgir A Jami’ar NOUN Na Iya Haifar Da Cuta > Shafi na 2
> Shafi na 2
Kotu Ta Halasta Wa EFCC Hana Fayose Amfani Da Asusunsa Na Banki > Shafi na 7