LEADERSHIP A Yau Juma'a E-paper 30 Ga Maris 2018

Page 1

30.03.18

AyAU JUMA'A LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

JARIDAR HAUSA

LeadershipAyau

30 Ga Maris 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

TA FARKO MAI FITOWA KULLUM A NIJERIYA

Bugu na: 029

N150

PDP Tuban Muzuru Ta Yi, In Ji Bola Tinubu Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto

Babban Jigon Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya shawarci ‘yan Nijeriya da kada su karvi tuba da afuwar da Jam’iyyar PDP ta yi masu kan kura-kuran da ta tafka a yayin da take kan karagar mulki. Tinubu ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis Lagas a wajen taron qarawa juna

sani kan bukin murnar cikarsa shekaru 66 a duniya. Wakilinmu ya labarto cewar Shugaban Jam’iyyar PDP na Qasa, Mista Uche Secondus a ranar Litinin xin da ta gabata a Abuja ya nemi gafarar ‘yan Nijeriya kan kura-kuran da jam’iyyar ta tafka a yayin da take saman mulki. A kan wannan Tinubu ya bayyana tuban

babbar jam’iyyar adawar a matsayin wata sabuwar yaudarar da suka vullo da ita da nufin neman sake samun tasiri a siyasance. Babban jigon na APC ya qara da cewar PDP ta durqusar da Nijeriya ta hanyar cin hanci da rashawa da ya yi katutu a mulkin ta yana cewar kada a bari su sake dawowa saman mulki domin tubansu na mazuru ne. >Ci gaba a shafi na 4

Ana Zargin Dakarun Soji Da Luguiguita Mutane A Katsina 5

Shugaban Qasa Muhammadu Buhari, mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbanjo tare da Bola Ahmed Tinubu (a tsakiya), yayin gudanar taron qoli na jagoran APC, Bola Tinubu jiya a otel xin Eko da ke Birnin Ikko.

Dino, Tsuntsun Da Ya Jawo Ruwa Shi Ruwa Kan Doka – Gwamnan>Kogi Shafi na 4 Yadda Aka Yi Jana’izar Sojojin Ahlul Faidati Sun Buxe Mauludin Da Aka Kashe A Kaduna> Shafi na 4 Shehu Ibrahim Na Bana A Kano > Shafi na 2


2 RAHOTO

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

Ahlul Faidati Sun Buxe Mauludin Shehu Ibrahim Na Bana A Kano Daga Abdulrazaq Yahuza Jere, Kano

Samarin ‘Yan Faila daga sassa dabandaban na qasar nan sun yi dandazo a Unguwar Gyaxigyaxi da ke Birnin Kano domin buxe Mauludin Shehu Ibrahim na bana da suka saba yi duk shekara a wurare daban-daban. Taron Mauludin na Gyaxigyaxi wanda aka gabatar a ranar Asabar da ta gabata a qarqashinhin jagorancin Shehu Isma’il Umar Almaddah (Mai Diwani), Sayyada Fatima Baballe Ila ta karvi baquncinsa a Babban Masallacin Juma’a na Gyaxigyaxi da ke kan hanyar Zariya. Mauludin na dare ne amma tun da jijjifin safiya ‘Yan Faila daga lunguna da saqo-saqo na cikin Kano suka fara hallara domin tarbar baqi masu shigowa. Kafin Azuhur, babbar tawagar da Shehu Isma’il ya jagoranta daga Kano ta isa wurin Mauludi tare da dakon isowar ragowar masu halarta. Baqi ba su daina kwarara ba har zuwa lokacin da aka fara gabatar da Mauludin daidai misalin qarfe tara na dare. Kafin fara gabatar da Mauludin, xaya daga cikin samarin Faila, Halifa Sunusi ya rera karatun Diwani mai daxi bayan an gama Wazifa kafin Sallar Isha’i. Dattawa da sauran mahalarta taron Mauludin sun cika Masallacin Juma’ar da ake taron maqil domin saurarar karatuttukan da za a gabatar wanda aqalla an shafe kimanin sa’o’i uku ana yi. Bayan buxe taro da addu’a, Alarammomi biyu daga cikin samarin na Faila, Alaramma Mustapha daga Kaduna, da Alaramma Ibrahim Gusau sun yi karatun Alqur’ani mai girma da muryoyi masu ratsa zukata. Yanayin natsuwar da ya wanzu a wurin ya qara tabbatar da yadda mahalarta Mauludin suka riqa karvar karatun Alqur’anin daga zuciya zuwa zuciya. Ba tare da vata lokaci ba, mai gabatarwa a wurin Mauludin ya nemi Shehin da zai karanta Mauludin, Shehu Isma’il ya fara karatu, sai dai saboda kyautatawarsa, shi kuma ya gabatar da xaya daga cikin jagororin samari ‘Yan Faila na Kano, Malam Rashidu inda ya yi taqaitaccen jawabi. Ya bayyana farin ciki tare da godiya ga Allah a kan Mauludin kana ya nunar da cewa “komai na ‘Yan Faila godiya ce ga Allah”. Kammala jawabinsa ke da wuya, Shehu Isma’il ya fara gabatar da karatun Mauludin tare da rera shahararriyar qasidar da xaya daga cikin manyan Almajiran Shehu Ibrahim Inyass, Shehu Malam Tijjani Zangon Barebari Kano ya rubuta wa Shehin da ake ma ta laqabi da “Mimiya”. Manyan baqi da sauran al’ummar gari da suka halarta sun cika da nishaxi, zukatansu suka yi daxi, soyayya a cikin Allah ta qaru saboda jindaxin qasidar da aka karanta cikin shauqi. Bayan kammala rera qasidar, Shehu Isma’il Mai Diwani ya xauki xan lokaci yana gabatar da samari ‘Yan Faila na yankuna dabandaban da suka halarci taron ga mai girma Hakimin Qiru, Xanmadamin

•Shehu Isma’il Umar Almaddah (Mai Diwani), Hakimin Qiru, Xanmadamin Kano, Alhaji Ibrahim, Sayyadi Malam Rashidu (a dama) a wurin Maulidu Kano, Alhaji Ibrahim domin sada domin yin hakan babban bala’i ne zumuncin Faila. Ko wanne aka kira, da mutum zai iya jawo wa kansa. Ya yi addu’ar Allah ya hana masu ana bayyana irin qoqarin da yake yi a kan hidimar Faila tare da godiya neman hakan cimma buqatunsu na ga Allah a kan haka, sannan da tuna son rai. A nasa jawabin, mai girma baya kan tarihin kafuwar Faila da Kiru, Xanmadamin Masarautar Kano tun daga zamanin Hakimin mai martaba Sarki Abdullahi Bayero Kano, Alhaji Ibrahim ya nuna wanda shi ne silar zuwan Shehu jindaxinsa da karatun da Shehu Ibrahim Inyass Nijeriya a shekarar Isma’il ya gabatar inda ya qara da 1945, bayan sun haxu a Aikin Hajjin cewa “Alhamdulillahi duk abin da Shehi ya faxa mana mun ji kuma shekarar 1935 a Ka’aba. Bayan nan, Shehu Isma’il ya mun yi imani. Allah ya maimaita cigaba da bayanin cewa bayani a mana wannan Mauludi na Shehu kan Mauludin Shehu Ibrahim tun Ibrahim”. Bayan kammala jawabin nasa, daga haihuwarsa zuwa ayyukansa na Musulunci da Imani da Ihsani Samarin na Faila sun rera Littafin abubuwa ne masu girma da faxi, Rihlar da Shehu Ibrahim Inyass amma yadda za a samu bayanin ya rubuta kafin daga bisani a rufe cikin sauqi a duba cikin Diwaninsa taron da addu’a. Mauludin na Gyaxigyaxi shi ne tare da fahimtar abin da ke ciki. “Ko haxuwar nan tamu ta irin sa na farko da Ahlul Faidati isa a san Failar Shehu Ibrahim suka gabatar a Babban Masallacin (RA). Yaranmu da manyanmu, Jumma’ar unguwar, inda ake sa talakawanmu da attajiranmu, ran cigaba da gabatarwa a ko wace malamanmu da mu almajirai shekara daga yanzu cikin yardar dukka ga mu a waje xaya muna Allah. Wasu daga cikin mahalarta rangaji; muna jindaxi muna nishaxi cikin Allah Tabaraka wa ta’ala. Mauludin da suka zanta da Tare da haka; mu yaran muna wakilinmu sun yaba da abubuwan girmama manya, manyan kuma da suka ji tare da addu’ar Allah ya suna tausayinmu, masu shi suna nuna musu na baxi. • Hakimin Qiru, Xanmadamin Kano, Alhaji Ibrahim yana jawabi taimakon marasa shi, marasa shi kuma suna gode wa masu shi xin ba tare da butulci ba. Da dukkanin siffofin ‘Yan Faila na Allah, da Qur’ani da Hadisi da maganganun Bayin Allah an haxu a ciki, to mun gode Allah”. Shehu Isma’il ya nunar da cewa Shehu Ibrahim Inyass ya faxi kansa da kansa a cikin Diwani, don haka Mauludinsa da ake gabatarwa ana yi ne don nuna godiya ga Allah bisa abin da aka samu na Musulunci da Imani da kuma Ihsani. Da yake tsokaci kan batun gagarumin Mauludin Shehu Ibrahim na qasa da aka saba gudanarwa duk shekara, Shehu Isma’il ya yi kira ga masu neman raba kawunan Almajiran Shehu Ibrahim su ji tsoron Allah su bari •Alhlul Faidhati kafin fara zaman Mauludin a Kano


A Yau

3

Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

ra’ayinmu

Matsalar Shaye-Shaye A Tsakanin Matasa A farkon wannan watan ne qungiyar Gwamnonin Arewa ta yi kira na musamman ga gwamnatin tarayya da ta kafa dokar ta vaci a kan matsalar yawaitan shaye-shayen kayan maye a cikin qasarnan. Sun kuma yanke wannan shawarar ne, a bisa ganin yadda matsalar ta shaye-shayen kayan mayen ke ta qara yaxuwa a tsakanin matasa, musamman ma a nan Arewacin qasar da ma qasar bakixayanta. Gwamnonin na Arewa, sun yi wannan kiran ga gwamnatin na tarayya ne, jim kaxan da fitowarsu daga wani taro da suka yi a Kaduna, inda suka nu na matuqar damuwarsu a kan yadda matsalar ta shaye-shayen kayan mayen ke qara tambatsa tana zama tamkar wani abin ado ga matasan duk da irin illa da kuma cutuka gami da naqasan da kayan mayen ke haddasa wa matasan, lamarin sai qara tavarvara yake yi a tsakanin matasan, duk da matakan da gwamnatocin yankin ke xauka na daqile matsalar shaye-shayen. Gwamnonin sun nu na matuqar damuwarsu da ganin yadda tu’ammuli da muggan qwayoyin da matasan ke yi yake saurin lalata rayuwar matasan bakixayanta. Kwankwaxar ababen sa maye kamar su, ‘amphetamine’ da sauran ababen da ke haddasa jirkitar da hankali idan an sha su ba bisa qa’ida ba, na narcotic, irin su, codeine, tramadol da ireiren su, hanya ce kai tsaye mai saurin lalata hanta, sanya hauhawan jini, ciwon daji da sauran cututtukan jiki waxanda ke haddasa gaggautowan mutuwa. Rahotannin da aka samu a wannan shekarar kaxai, masu nu ni da yadda matasa suka riqa sheqawa lahira tun da quruciyarsu a sabili da matsalar ta shaye-shayen kayan mayen abin akwai ban tsoro saboda yawaitan su. Kwanan baya kaxan aka shelanta mutuwar wani matashin da ya sha kayan mayen har su ka yi ma shi karo ya kuma sheqa lahira tun da sauran kwanansa a garin Abraka, da ke {aramar Hukumar Ethiope ta gabas, a Jihar Delta. A dai Jihar ta Delta, wani matashi xan makarantar Sakandare ta, ‘Army Day Secondary School,’ da ke garin, Effurun, ta {aramar Hukumar Uvwie, shi ma hakanan kawai aka gan shi yana tangal-tangal a cikin aji, nan take kuma sai aka ga ya faxi qasa matacce ba rai. Ko da aka kai gawarsa xakin bincike, sai aka taras ya kwashi Tramadol ne har ya yi ma shi karo ya mutu. Mista Akindele Akingbade, Kwamandan Hukumar yaqi da shan muggan qwayoyi ta Jihar Abiya, a kwanakin baya ne ya shelanta mutuwar wani xalibin qaramar Sakandare a {aramar Hukumar Ohafia, ta Jihar ta Abiya, wanda shi ma ya sheqa lahira babu shiri bayan da ya haxiyi qwayar ta tramadol har guda 10, wanda aka ce wai ya sha ne domin ya sami qarin qwazo a gasar wasanni da ake yi a makarantar na su. Ainihin ita wannan qwaya ta, tramadol, an qirqirota ne domin ta kasance maganin da ke rage raxaxin ciwo ko kuma ya rage zafin jikin da ya tsananta. Amma a savanin hakan, sai matasan suka samo wata hanyar yin amfani da shi ta daban wacce ta kauce wa qa’idar amfani da shi xin, ta hanyar shan sa da yawa fiye da qa’ida. Matasan, sun ma yi iqirarin cewa wai shan qwayar ba bisa qa’ida ba, yana qara ma su qarfi, musamman a wajen jima’i. Duk da

cewa, akwai dokoki a qasarnan waxanda suka yi hani da yin tu’ammali da shigen waxannan qwayoyin kamar qwayar ta tramadol, da amphetamine, sai dai abin da aka rasa shi ne, tabbatar da yin aiki da dokokin. Kasantuwan yanda ake yawan shan ababen sa mayen, a yanzun haka, diloli da masu sayar da kayan mayen sun zama hanshaqan ‘yan kasuwa. A wannan satin kaxai, hukumar ta hana yin tu’ammali da kayan mayen, NDLEA, ta bayyana cewa, ta qwace qwayoyin na tramadol har milyan 159 a tashar jiragen ruwa ta Apapa, da ke Legas. Daraktan hukumar ne

ta, NDLEA, mai gudanar da bincike, Mista Femi Oluruntoba, ya bayyana hakan, a wani zama na musamman da Majalisar Dattawa ta gayyace shi domin ya yi bayani kan illoli da kuma rawar da hukumar na shi ke takawa wajen hana shan muggan qwayoyin. Ya ma qara da bayyana cewa, a kwanan nan a Kano kaxai, hukumar na shi ta lalata sama da Tan 50 na qwayar ta tramadol. Ya kuma yi nu ni da cewa, baya ga qwayar ta tramadol, akwai sama da ababen sa maye 31 da ake haxiya ko kwankwaxa domin jirkitar da hankali tun daga shekarar 2016.

EDITA Abdulrazaq Yahuza Jere

MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama DARAKTAN SASHE Mubarak Umar

RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah

BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John

manufarmu

LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!

Matsalolin kan iyakan qasarmu, da kuma zafafan dokokin da suka haramtawa hukumar lura da lafiyar abinci da magunguna, NAFDAC, gudanar da ayyukansu a tashoshin jiragen ruwan qasarnan, sun qara taimakawa wajen yaxuwar haramtattun kayan maye a cikin qasarnan. Wani bincike da kamfanin nan na, NoI Polls Limited, ya gudanar a ranar 1 ga watan Yuli 2013, ya yi nu ni da yadda qaruwan tu’ammuli da kayan mayen a cikin qasarnan ke qara janyo mana mugun talauci da rashin aikin yi. Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, a wani zama na musamman da Majalisar ta Dattawa ta yi kan matsalar shaye-shayen kayan mayen, ya yi nu ni da cewa, shaye-shayen, su ke haddasa yawaitan ayyukan masha’a, kamar su, fashi da makami, garkuwa da mutane, ta’addanci da saura ayyukan laifuka makamantan su, da suke barazana da sha’anin tsaro na cikin qasarnan. Sannan kuma abin takaicin, in ji Shugaban Majalisar ta Dattawa, da yawa daga cikin matasanmu, waxanda ake sa ran su zama shugabannin gobe duk sun rungumi wannan muguwar xabi’ar ta shaye-shayen na kayan maye. Wanda hakan a cewar shi, barazana ne ga lafiyarsu da rayuwar su ma bakixayanta, sannan kuma barazana ce ga iyalansu, don haka tilas ne mu tashi tsaye haiqan wajen yaqar wannan xabi’ar ta shaye-shayen na kayan maye, in ji Saraki. Matsalar ta shaye-shayen kayan maye a tsakanin matasan namu, da suka haxa da, shaqan sholisho da dangogin ta, da kuma ababen da ake sha daban-daban, da suka haxa da tabar wiwi, shaqan masai da makamantan su, waxanda suka zama ruwan dare musamman a nan arewacin Nijeriya. {warraru sun tabbatar da cewa, iyaye suna da mahimmiyar rawar da ya kamata su taka wajen duba halayyar ‘ya’yayen na su dangane da matsalar ta shaye-shaye. Kan haka, suka bayar da shawarar cewa, ya kamata iyaye su riqa duba ‘ya’yayen na su, musamman waxanda suka fara tasowa, ta hanyar duba idanuwansu a kai a kai, numfashinsu da ma yanayin warin jikinsu, gami da lura sosai a kan yanayin xabi’o’in su, na maganganu, hulxansu da kuma yadda halayyarsu ke canzawa. Da zaran an lura da wani baqon abu kan waxanda muka lissafta xin nan, sai a gaggauta xaukan mataki. Dangane da hukuma kuma, qungiyar masu haxa magunguna ta qasa, (PSN), ta kawo shawarar da a sanya dokar rubuta magunguna a qasarnan, wacce za ta baiwa qungiyar ta PSN, damar sanin ko wa da wane ne ke yin abu kaza a kowane waje, da ya shafi bayar da magungunan. Sannan kuma gwamnonin arewa, sun bayar da shawarar dukkanin gwamnatocin Jihohi su kafa wani kwamiti na musamman da zai tabbatar da ana aiki da dokokin hana safara da shan kayan mayen, a qarqashin ko dai mataimakin gwamna ko kuma Sakataren Jiha. Sun kuma bukaci Ma’aikatun kula da harkokin mata da matasa da su qara qaimi wajen shirye-shiryen wayar da kai kan haxarin da ke tattare da shan kayan mayen. A nan arewa kuma, gwamnonin sun shawarta kafa wata doka ta musamman da za ta yaqi safara da shan kayan mayen a yankin na su na arewa.


4 LABARAI

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

PDP Tuban Muzuru Ta Yi, In Ji Bola Tinubu Ci Gaba Daga Shafin Farko

“Ina kira ga al’ummar Nijeriya da kada su aminta da tuban PDP, gurvatattu ne kuma maqaryata waxanda cin hanci da rashawa ya yi wa katutu, a kodayaushe suna canza alqalumma. A tsayin shekaru 16 da suka yi saman mulki suna yin alqawulan bugi, suna ba mu alqaluman bugi suna kuma ce mana ka da mu yi magana a kai.” In ji Tinubu. Ya ce “Kalamansu na qarya ne da yaudara domin idan ka kama varawo zai ce ka da ka kalli abin da ya yi ka je kaima ka saci naka.” In ji shi. Tinubu ya bayyana cewar PDP ta samu cikakkiyar damar bunqasa qasa tare da

kai ta ga tudun mun tsira musamman a bisa ga tashin farashin xanyen mai da haqo albarkatun fetur mai yawa. Ya ce a bisa ga tarihin cin hanci da rashawa da PDP take da shi ba za ta sake yin wani tasiri a mulki ba. A cewarsa alqawulan da APC ta yi wa ‘yan Nijeriya a lokacin yaqin neman xave za ta yi qoqarin cikasu ya kuma bayyana cewar Gwamnatin Muhammadu Buhari ta xauki matakan ciyar da qasa gaba. “Za mu ci-gaba da tafiyar da mulki, tafiyar samun nasara, tafiyar da za ta canja alqiblar Nijeriya tare da kai su a matakin nasara.” Tinubu ya kuma bayyana shirin bunqasa rayuwar

al’umma na Gwamnatin Tarayya a matsayin mai amfani yana cewar shirin zai qarfafawa mutane da dama. Ya ce yana da yaqini a kan Gwamnatin Buhari za ta shayar da al’umma romon mulkin Dimokuradiyya yadda ya kamata. A jawabinsa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana Tinubu a matsayin gogagen xan siyasa kuma mutumin da ya damu da cigaban al’ummar qasa. Shugaba Buhari bayan ya taya shi murnar cika shekaru 66 a duniya ya kuma yi masa fatar alheri a rayuwa da kuma jaddada manufar Gwamnatinsa na inganta jin daxi da walwalar al’ummar qasa bakixaya.

•Bola Tinubu

Yadda Aka Yi Jana’izar Sojojin Da Aka Kashe A Kaduna Daga Abubakar Abba, Kaduna

An yi jana’izar dakarun soja su goma shaxaya da wasu mahara suka hallaka a maqabartar da ake binnr ‘yan mazan jiya da ke Jihar Kaduna. Dakarun sojojin an kashe su ne a Kampanin da ke qauyen doka a cikin qaramar hukumar Birnin Gwari da ke cikin jihar ta Kaduna a kwanan baya. Lamarin ya auku ne lokacin da maharan suka kai farmaki a qauyen a ranar the 20 ga watan Maris na shekarar 2018, inda

sakamakon farmakin, maharan suka hallaka sojojin da aka tura yankin don magance yawan hare-haren da ake kaiwa yankin da garkuwa da mutane da satar Shanu da kuma aikata sauran manyan laifuka a qarqashin shirin na soji mai suna ‘Ayem Akpatuma’ ma’ana ‘gudun mage’. Da yake jawabi a lokacin bizne sojojin, Shugaban rundunar sojin Qasa, Janar Tukur Buratai ya jajantawa iyayen mamatan, inda ya ce sojoji ba za su sassauta ba

wajen cafko maharan don a hukunta su kamar yadda doka ta tanada. Buratai wanda kwamandan bataliya ta xaya dake Kaduna Manjo Janar Mohammed Mohammed ya wakilce shi ya danganta mutuwar sojojin a matsayin babban rashi, sai dai ya yi nuni da cewa, sun sadaukar da kansu ne wajen kare al’ummar Birnin Gwari da na Kaduna da kuma ‘yan qasa baki xaya. Ya sharwarci iyayen mamatan ka da suyi qasa a gwaiwa wajen sanya ‘ya’yansu a aikin soja

saboda mutuwar sojojin. Ya baiwa ‘yan’uwan mamatan tabbacin samun goyon bayan rundunar soji kuma mutuwar su baza ta zama a banza ba. Shi ma a nashi jawabin, Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufai, ya jajantawa ‘yan uwan mamatan. El-rufai wanda Sakataren gwamnatin jihar Lawal Balarebe ya wakilce ya kuma sanar da bayar da gudunmawa Naira 500, 000:00 ga ko wanne xan uwan mamacin. Dakarun sojin da aka kashen

su ne; Olabode Hammed daga Jihar Ogun da Bamidele Adekunle Emmanuel shima daga Ogun da Owochukwu Christian Chigoziri daga jihar Ribas da Adamu Muhammed daga jihar Bauchi da Lamara Ahmed daga jihar Jigawa. Sauran sune; Mubarak Suleiman daga jihar da Bashir Sani daga jihar Katsina da Usman Abubakar Jalo daga jihar Gombe da Nafiu Iliyasu daga jihar Jigawa da Safiyanu Ahmed daga jihar Jigawa sai kuma Alhassan Ibrahim daga jihar Kaduna.

Dino Nema Yake Ya Haxiye Tavarya A Tsaye – Gwamna Bello Daga Idris Aliyu Daudawa

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya qalubalanci Sanata Dino Melaye mai wakiltar mazavar majalisar dattawa ta Kogi ta Yamma cewar, don Allah ya qyale shi, domin ya fuskanci ayyukan da ke gabansa. Ya je ya fuskanci matsalar da ke tsakaninsa da ‘yansanda tunda nema yake ya haxiye tavarya a tsaye. Bello ya furta hakan ne lokacin da yake bayani dangane da zargin da Sanata Dino Melaye yake yi ma sa, cewar yana aiki da ‘yansanda ne saboda ya vata ma sa, da yake qaryata zargin da Dino Melaye yake, jami’in hulxa da jama’a na gwamna, Kingsley Fanwo, ya wanke gwamnan daga duk wani zargi da ake yi ma sa na cewar, shi ne musabbabin halin da Sanata Dino Melaye ya shiga. A cikin sanarwar da ya fitar Fanwo ya ce da ya yi qoqari don ya gana da su’yansanda saboda shi ma ya ba da na sa bayanan a kan abin da duk ya sani dangane da zargin da ake yi ma sa.

‘’Shi gwamna mai bin doka da oda ne kuma xan Nijeriya ne, ba wanda zai so ya sa kansa cikin irin wannan matsala ba, ko a cikin gida ko kuma waje. Ba wata Hukuma da ta bayyana wani laifin gwamnan, saboda shi ya san mutuncin mutane, don haka ba ta yadda za a yi ya kawo masu raini.’’ ‘’ Me kuma ya haxa gwamnan da wannan al’amrin da , saboda ai su ‘yansandan ne suka kama waxanda ake zargi, saboda ai jam’an ‘yansanda ne suka kama su yaran, bayan haka kuma su waxanda ake zargi da aikata laifi, sune kuma suka bayyana wanda yake kawo masu makamai. Babban abin da ya kamata ya ya yi shi ne ya wanke kansa, ya kuma bar zargin gwamna. Ana cikin haka ne kuma sai ga majalisar dattawa ta kafa kwamitin da zai binciki zargi da Sanata Dino Melaye yake, kwamitin kuma shi ne na ’yansanda da shari’a, da kuma umarni na sa kwamitin ya kammala aikinsa cikin kwana biyu , daga nan kuma ya su bayyanawa

• Gwamna Yahaya Bello majalisa abin da ake ciki, tsakanin al’amarin da ya shafi shi Sanata Dino Melaye da kuma Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello. Ana iya tunawa Sanata Dino Melaye tun bara, ya bayyanawa majalisar dattawa ana qoqarin a kashe shi, ya kuma zargi Gwamnan jihar Kogi da kuma Taofik Isa. Ranar 19 ga watan Maris

• Sanata Dino Melaye ne rundunar ‘yansanda ta jihar Kogi ta kama wasu mutane biyu waxanda kuma ta gabatar da, waxanda kuma ta bayyanasu ‘yan barandar siyasa ne, da bindigogi biyu qirar AK47 sa kuma wasu bindigogi biyar da ake kira action machine, suka kuma yi bayanin Sanata Dino Melayen yake xaukar nauyinsu. Ranar 24 ga watan March sai

ga shi Sanata Dino Melaye ya qaryata maganar da su waxanda aka kama suka ce. Ya kuma bayyana cewar ba wadda ya kamata a kama bace, saboda ana son a qallafa ma sa abin da bai yi ba, a ce ya yi dole. Ranar Laraba ta wannan mako da ya wuce ne shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ya yi wani abu na ba zata , inda ya nuna rashin jin daxin sa, a kan yadda Sanata Dino Melaye a gaban majalisar dattawa. Kowa dai ya san shi Dino Melaye yana daga cikin ‘yan gaban shugaban majalisar dattawa, ko kuma a ce su ne ‘yan Mowarsa. Saraki da yake faxin ta albarkacin bakisa inda ya yi bayanin dangane da wani sabon ci gaban da aka samu, inda wasu mutane biyu waxanda aka kama suka ce, shi ne ya ba su bindigogi da kuma kuxi, maganar kuma da ake yanzu sun gudu, daga wurin da ‘yansanda suke tsare da su a Lokoja. Amma maimakon shi Dino ya ci gaba da bayanin abin da ya dame shi sosai, sai kuma ya koma da yin waqa.


A Yau JUMA'A 30.03.2018

5

Babban Labari Ana Zargin Sojoji Da Luguiguita Mutane A Katsina Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Mutanen garin Machika da ke cikin qaramar hukumar sabuwa a Jihar Katsina, sun kai takardar koke ga mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, domin shiga tsakaninsu da wani Kaftin xin soja da ke aiki a wannan yankin. Takardar mai shafi biyu, wacce shugaban qungiyar ‘yan sintiri na garin Machika, Abdullahi Kawun Baraka, ya karanta sannan ya gabatar ga Mai Martaba Sarkin Katsina, tana qunshe ne da wasu zargezarge da ke da alaqa da take haqqin xan adam da suke zargin wani Kaftin xin Soja mai suna, Kaftin Sani, yana yi wa al’ummar garin na Machika. Shugaban qungiyar, ya bayyana cewa, suna zaune kawai ba su san hawa bare sauka ba, suna wajan taya xaya daga cikinsu murnar samun qaruwa, sai kawai sojoji suka kewaye su suka kama su sannan suka ta fi da su garin Faskari, inda aka ci gaba da tsare su kamar yadda ya shaidawa Mai Martaba Sarkin Katsina. Daga nan sai takardar ta ci gaba da cewa, waxanda aka kama xin an ci gaba da tsare su da kuma azabtar da su har tsawon kwanaki takwas ba tare da an gabatar da su a gaban kotu ba, don su san laifin da suka aikata, a rana ta takwas ne aka sake su suka koma cikin iyalansu bayan sun gama galabaita. Abdullahi Kawun Baraka ya ce iyayansu sun shaida masu cewa, sai da suka kaiwa Kaftin Sani kuxi Naira 280,000 sannan ya sako su, ya ce kafin Kaftin Sani, ya sake su, sun tambaye shi laifin su, sai ya gaya masu cewa, mai Anguwar Mika ne ya gaya masa cewa su ‘yan ta’adda ne.

Haka kuma takardar ta bayyana cewa, sakamakon wani kisan qare dangi da aka yi a wannan yankin inda aka kashe mutun 53 a rana xaya, ya sa suka yanke shawarar kafa qungiyar sintiri domin kare kansu da dukiyoyinsu daga farmakin maqiya. A cewar su, kafin kafa wannan qungiyar ta sintiri, sai da ma su ruwa da tsaki suka tantance su da suka haxa da Magaji Machika da DPO da wakilin SSS da shugaban qungiyar Sintiri na qaramar hukumar Sabuwa, to amma a ta bakin su mai Anguwar Mika ya qware wajan haxa baki da ma’aikata domin a cutar da al’umma. Sun kuma yi kira da babar murya ga Mai Martaba Sarki da ya binciki wannan koke na su, idan an kama su da laifi a hukunta su idan kuma ba su da laifi, a bi masu kadin kuxaxan da Kaftin Sani ya karva a hannun iyayansu kafin ya sake su. Sun qara da cewa “Muna roqon Mai Martaba Sarki, da ya sa a yi wa wannan Soja iyaka da qauyanmu ko kuma a tada wannan Soja daga Faskari, domin muna da cikakken bayanin duk talakan da ya kama sai ya amshi kuxi daga hannun iyayansa kafin ya sake shi, kuma babu wani mai alfarma sai mutun biyu daga wata yarinya mai suna gwamma sai mai Anguwar kwanar kura da aka sani da mai Anguwa Mika kawai’’ in ji takardar. Haka kuma sun bayyana cewa, sai da DPO da shugaban riqo na Qaramar Hukumar ya ce, ya sake su, idan kuma suna da laifi ya kai su kotu, amma ya yi watsi da wannan buqata sai da suka yi kwana takwas a hannunsa su na shan baqar azaba. Daga qarshe, sun nu na

kyakkyawar fatan su ga Mai Marbata Sarki da kuma Majalisar sa, da su yi duk mai yiwuwa wajan ganin wannan jami’in Soja bai ci gaba da azabtar da mutanen garin Machika ba, da kuma sauran al’umma. Sai dai jin cewa an amabci sunan mai Anguwar kwanar kura, mai Anguwa Mika, ya sa muka tuntuve shi domin jin ta bakinsa game da wannan koke, sai ya ka da baki ya ce, wannan magana ba gaskiya ba ce, bai san wani soja ba Kaftin Sani, haka shi ma sojan bai san Mai Anguwa Mika ba. Gwamma ita ce wanda masu wannan koke suka ambata a cikin takardar su da cewa ta hannunta ne kaftin Sani yake karvar kuxaxe a hannun iyayan jama’a, hakan ya sa muka tuntuve ta domin jin abin da za ta ce, sai dai kash, mun buga lambar wayar ta amma har zuwa lokacin haxa wannan rahoto ba mu same ta ba. Duk wani qoqari na ji daga bakin jami’an sojojin Nijeriya da ke Katsina domin su ba da na su ba’asin game da wannan koke na mutanen Machika da ke Qaramnar Hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina ya ci tura. Idan za a iya tunawa, Qaramar Hukumar Sabuwa, na xaya daga cikin qananan hukumomi bakwai da ‘yan kiwo haram suka addaba a lokutan baya, inda aka samu asarar rayuka da kuma ta dukiyoyi. Sakamakon wannan matsalar ce ya sa gwamnatin Jihar Katsina ta yi tunanin yin afuwa da sasanci ga varayin shanu, wanda kuma sanadiyyar haka ne, aka tura wata tawagar sojoji da ake yi wa laqabi da ‘operation sharar daji’ yankunan. Kazalika, Kaftin Sani, da ake wannan koke a kansa, shi

•Xaya daga cikin matasan da ake zargin sojojin da luguiguitawa a Machika ne jagoran wannan tawaga ta ‘Operation sharar daji’ wanda ta yi iyaka da Jihar Kaduna domin kammala kakkave sauran varayin shanun da ba su ajiye makamansu ba. Sai dai kuma al’ummar wannan yanki sun riqa shirya qungiyoyin sintiri domin baiwa kansu tsaro na musamman kafin jami’an tsaro su iso gare su idan wata matsala ta afku, kasancewar ana samun kai hare-haren nan da can a wasu lokuta a waxannan yankuna. A vangaran hukumomin tsaro, sun sha bayyana irin nasarorin da suke cewa sun

samu a wannan yanki, inda suka ce yanzu zaman lafiya ya dawo yadda yake, kuma an rage masu kai farmaki da qwace shanun fulani a cikin wannan daji da ya yi iyaka da Jihar Katsina da Zamfara da kuma Kaduna. Haka kuma wani sabon al’amari da ke maida hannun a gogo baya a wannan yankin shi ne, yadda masu garkuwa da jama’a domin neman kuxin fansa ke cin karensu babu babbaka, duk da iqirarin da hukumomin tsaro ke yi na cewar jami’an su na can ba dare ba rana suna aikin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kallo Ya Koma Sama Yayin Da Babachir Ya Halarci Taron Tinubu A Legas

Daga Abubakar Abba

Kallo ya koma sama a yayin da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal ya hallarci taro karo na goma, na tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jagoran Jam’iyyar APC na qasa, Ahmed Bola Tinubu. Jama’a da dama sun shiga tunanin yadda ya iya shiga

taron ba tare da jin nauyin abin da ya aiakata na cin hanci ba. Ahmed Bola Tinubu ya kuma yi amfani da damar taron wajen gudanar da bikin cikarsa shekaru 66 da haihuwa. Sauran gwamnonin da suka halarci taron sun haxa da; na Oyo, Abiola Ajimobi, da na Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da na Sakkwato,

Aminu Tambuwal. Sauran su ne; Alaafin na Oyo da Oba Lamidi Adeyemi Ooni na Ife da Oba Enitan Ogunwusi da Oba na Legas Riliwanu Akiolu da Alake na Egbala da Aremu Gbadebo da tsohon shugaban hukumar yaqi da cin hanci da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin qasa zagon qasa Malam Nuhu Ribadu da

sauran tsofaffin gwamnoni da Sanatoci da Ministoci da kuma ‘yan majalisar wakilai na qasa. In za a iya tunawa, an tsige Lawal ne daga muqamin na sa sakamakon zargin badaqalar kwangilar gyaran sansanin ‘yan gudun hijira da ke yankin Arewa Maso Gabas, wanda a yanzu ake ci gaba da tuhuma a kan zargin badaqalar.

•Babachir Lawal


6

LABARAI

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

Qungiyar Xaliban Kwalejin Ilimi Ta Karrama Jarman Sakkwato Daga El-Mansur Abubakar, Gombe

Qungiyar Xaliban Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari (SSCOE) da ke Sakkwato ta karrama babban jigon xan siyasa kuma Uban Marayun Arewa, Alhaji Dakta Ummarun Kwabo A.A MFR da lambar girma mai daraja ta xaya ta qungiyar. Qungiyar ta SUG ta bayyana Jarman Sakkwato a matsayin wanda ya bayar kuma yake cigaba da bayar da gagarumar gudunmuwa ga ci-gaban al’umma ta fuskoki da vangarori da dama wanda shine dalilin da ya sa ta karrama shi domin nuna masa godiya ga ayyukan alherin da yake yi kamar yadda shugaban qungiyar Shu’aibu Umar Maifura ya bayyana a taron wanda aka gudanar a jiya Alhamis a kwalejin. Jarma shine ya kasance shugaban taro kuma babban mai qaddamar da Mujallar da qungiyar ta wallafa irinta ta farko wadda Jarman na Sakkwato ya qaddamar a kan naira miliyan xaya kuxi qasa. Babban jigo a gidan siyasar Jarman Sakkwato kuma Basarake Alhaji Bello Isa (Shettiman Durbawa) ne ya wakilci Jarma wanda kwanan nan ya samu inkiyar Uban Marayun Arewa a bisa ga xaukar nauyin marayu 200 da ya yi da aljihunsa fisabilillah. A jawabinsa babban attajirin xan siyasar kuma hamshaqin xan kasuwa ya bayyana muhimmancin ilimi ta hanyar bayyana kyakkyawar dangantakar da ke akwai tsakanin ilimi da ci-gaba a bisa ga yadda ilimi ya zama qashin bayan ci-gaban kowacen irin

al’umma. Jarma ya ce a bisa ga qalubalen da sha’anin ilimi yake fuskanta yana kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatocin Jihohi da su fito da wasu hanyoyi na cigaba domin samar da cikakken ilimin jami’a domin a cewarsa Gwamnati kaxai ba za ta iya xaukar sha’anin karatun jami’a ba. “A wasu qasashen Afrika a na kashe aqalla dala 5, 000 a zangon karatu xaya a yayin da a Nijeriya a ke kashe naira dubu 50, 000 amma kuma a na son samun ilimi iri xaya wanda kuma ba zai yiwu ba.” Ya bayyana. Ya ce sakamakon jarabawar shiga jami’a ta JAMB da aka fitar kwanan nan ya nuna xalibai miliyan 1.6 daga cikin miliyan 2 da suka nemi gurabun karatu a jami’o’in Nijeriya; xalibai dubu 500 ne kaxai za a iya baiwa gurabun karatu tare da barin xalibai miliyan 9. Wannan qarara ya nuna buqatar masu ruwa da tsaki da su haxa hannu domin samar da ingantacciyar mafita ga wannan matsalar.” In ji Jarma. Babban jigon xan siyasar ya kuma yabawa Hukumar Gudanarwar Kwalejin kan baiwa xalibai kyakkyawan yanayin karatu a bisa ga yadda suke samun nasara a kwasakwasai daban-daban. Daga nan ya kuma buqaci xaliban Kwalejin da su qauracewa tu’ammali da kayan maye da nesantar qungiyoyin asiri da dukkanin ayyukan assha a ciki da wajen makaranta. Ya ce ya na da kyau a bayar da kulawar musamman ga sha’anin tsaron makaranta tare da kawar

• Alhaji Dakta Ummarun Kwabo A.A MFR

da duk wasu abubuwan da ke iya kawo tarnaqi ga tsaro ta hanyar samar da ingantaccen tsaro yadda ya kamata. Ya ce “Ina qara jinjinawa Gwamnatin Jihar Sakkwato a qarqashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal kan goyon bayan da take baiwa sha’anin ilimi musamman kashe tsabar kuxi har naira biliyan biyu wajen biyawa xalibai kuxin tallafin karatu a ciki da wajen qasa da kuma xaukar nauyin xalibai 200 domin su karanci fannin kiyon lafiya da wasu

fannoni masu alaqa da kiyon lafiya a qasashen waje. Wannan ba qaramin abin yabawa ba ne a irin wannan lokaci da wasu Jihohi ke faxi tashin yadda za su biya albashin ma’aikata.” A ta bakinsa. Tun da fari Shugaban Kwalejin, Dakta Muhammad Wadata Hakimi ya yabawa qungiyar xaliban kan wallafa Mujallar wadda ya ce ita ce irinta ta farko da wata qungiyar xalibai ta tava wallafawa a Kwalejin. Baya ga Jarma qungiyar ta

kuma karrama matar Gwamnan Jihar Sakkwato, Hajiya Maryam Mairo Aminu Tambuwal da kuma Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Dakta Muhammad Javvi Kilgori da shugaban kwalejin Dakta Hakimi. A taron Kwamishinar Ilimi Farfesa A’isha Madawaki Isa ta gabatar da lacca kan Alfanun Karatun ‘Ya’ya Mata yayin da Barista Hafsat Sahabi Dange ta gabatar da qasida mai taken Shigar Matasa A Harkokin Kasuwanci.

‘Yan Sandan Gombe Sun Cafke Varawon Batirin Kamfanin Sadarwa Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Gombe, Mista Shina Tairu Olukolu, ya gabatar da wani |arawo mai suna Adamu Idris mai shekaru 30 da haihuwa da ke zaune a Anguwar Jekadafari fadar Jihar, da ya qware wajen satar baturan kamfanin wayoyin sadarwa. Adamu Idris, an kama shi ne da batura guda goma sha shida masu qarfin 12 volt, kowannen su mallakar kamfanin wayar sadarwa ta

MTN da ke Tumfure a yankin Qaramar Hukumar Akko a Jihar ta Gombe. Kwamishinan ‘yan sandan ya yi amfani da wannan damar, inda ya yi kira ga al’umma da su dinga bai wa jami’an ‘yan sanda bayanan sirri ma su mahimmanci da zai taimaka masu wajen kai wa ga kama vatagarin da suke voye a tsakanin al’umma. A gefe guda, biyo bayan umurnin da Sufeton ‘yan sanda na qasa Ibrahim K Idris, ya bayar a ranar 21 ga watan Fabarairu na wannan shekara,

inda ya umurci kowanne Kwamishina ‘Yan sanda na jiha da ya kafa kwamiti na karvo makamai da ke hannun mutane da suka mallaka ba bisa qa’ida ba, ‘task force,’ ya miqawa hukumar ‘yan sanda sashin bincike na farin kaya CID. Kafin cikar wa’adin da Sufeton ‘Yan sandan na qasa, Ibrahim K Idris, ya bayar yanzu haka jama’a a bisa ra’ayin kansu sun miqa makaman su ga hukumar, inda yanzu suka karvi bindigogi 25. Cikin irin bindigogin

da jama’a xin suka miqawa ‘yan sandan sun haxa da bindigogin Toka guda 15 da wasu masu kyau guda 3, sai single barrel guda 2 da kuma qananan bindigogi qirar fistol na maqera guda 5. Har ila yau, Kwamishina, Shina Tairu Olukolu, ya ce, bisa ga umurnin Sufetan ‘yan sandan na qasa na cewa mutane su dai na sanya jiniya a motocin su suna razana mutane in ban da motocin Banki da motar xaukar marar lafiya, an kafa wani kwamiti na daban shi ma don kama masu

kunnen qashi a kan dokar. A kan haka Kwamishinan ‘yan sandan, ya naxa kwamiti qarqashin mataimakin sufeton ‘yan sanda, ASP Moses Ibrahim, inda aka ba su umurni na su kama kowa ne ne su gurfanar da shi gaban hukuma da aka kama da karya wannan dokar. Daga nan sai ya godewa ‘yan jarida bisa haxin kai da suke ba su wajen yayata ayyukansu a Jihar da kuma yin kira ga jama’ar gari da cewa su kasance masu bin doka da oda.


A Yau Juama’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

TALLA 7


8

LABARAI

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

NUJ Ta Buqaci Baiwa Tsangayar Aikin Jarida Muhimmanci A Bauchi Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Qungiyar ‘yan jarida ta qasa reshen jihar Bauchi ta buqaci sabon shugaban kwalejin kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin taryya da ke Bauchi, Arc. Sanusi Waziri Gumau da ya sanya tsangayar koyar da ilimin aikin jarida a cikin fannonin da zai baiwa fifiko domin bunqasa sashin. Shugaban qungiyar ‘yan jarida ta qasa reshen jihar Bauchi Malam Ibrahim Malam Goje shi ne ya yi wannan kiran a lokacin da NUJ ta kai gaisuwar taya sabon shugaban Kwalejin murnar samun muqamin wanda shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya naxasa a kwanan nan. Ya ce sashin koyar da aikin jarida wani sashi ne da ke da matuqar muhimmanci wajen ci gaban kowace al’umma, don haka ne ya buqaci shugaban da ya sanya wannan fanni a cikin fannonin da zai bayar da gagarumar kulawa a ciki. Ta bakin Malam Goje “Mun ji daxin baka wannan muqamin wanda shugaban Nijeriya ya yi da kuma tabbatar maka da wannan kujerar,” “Federal Polytechnic Bauchi tana xaya daga cikin tsofaffun manyan makarantu ba ma kawai a shiyyar Arewa Maso Gabas ba, a’a tana daga cikin tsoffin manyan makarantu a sassan Nijeriya. Mun sani wannan kwalejin tana da gagarumar ragar da za ka iya takawa wajen havaka sha’anin ilimi a Nijeriya. “Muna da masaniyar mafiya yawa daga cikin mambobinmu ma da muka zo da su wannan ofishin

naka da damarsu a wannan kwalejin suka yi karatunsu na koyon aikin jarida, wasu sun yi Diploma, wasu kuma sun yi babban Diploma wasu ma dai suna kai, da daman mambobinmu wato ‘yan jarida anan aka qenqeshesu,” Ibrahim Goje ya qara da cewa, “Don haka muna da gagarumar rawar da za mu iya takawa wajen ciyar da kwalejin gaba, ba kawai don a samu ci gaba a shiyyar Arewa ba; a Nijeriyar ma gaba xaya, don haka ne muka zo a madadin qungiyar ‘yan jarida domin mu taya ka murnar wannan samun muqamin da ka yi,” In ji shugaban NUJ. Ya qara da cewa baya ga nan kuma NUJ tana da buqatar da za tagabatar domin a samu ci gaba, ya ce duk da qalubalen da yake tunanin akwai, amma kuma hakan ba zai hana shugaban ya himmatu domin kawo ci gaba ba “zan yi amfani da wannan damar wajen neman ka da ka yi amfani da damarka wajen bunqasa wannan sashin na koyar da aikin jarida, domin baiwa sashin muhimmanci,” “Sau tari idan aka tura wasu xaliban aikin jarida domin neman sanin makamar aiki IT akwai matsalolin rashin samun zarafin koyon aikin nan yadda ya dace ta yin aikin a aikace sakamakon qaracin xakunan gaji, don haka muna qiranka da ka samar da studio a wannan kwajen da kuma kayan aiki domin horar da xaliban yadda suka dace aikin jarida a aikace,” A cewar shugaban. Da yake maida jawabi, sabon shugaban Arc. Sanusi Waziri Gumau ya nuna matuqar jin daxinsa a bisa ziyarar da uwar

• A lokacin da Ministan ilimi Adamu Adamu ke miqa wa sabon shugaban Fedpoly Arc. Sanusi Gamau takardar kama aiki gadan-gadan

qungiyar ‘yan jaridan a matakin jihar ta kawo masa, yana mai bayanin cewar qiran da ‘yan NUJ ta yi masa ya zo a kan gava domin yanzu haka ma kwalejin ta himmatu wajen bunqasa wannan sashin “wannan tsangayar ta Kakaki na wannan makarantar, a yanzu haka ma muna kan faxaxa ginin tsangayar da ke wannan kwalejin, da zarar kuma aka kammala za mu samar musu da kayyakin aiyukan da za su bunqasa koyo da koyarwa da kuma wannan sashin domin su samu su havaka fiye da yadda ake a yanzu,” Dangane da shirinsa na bunqasa kwalejin ta FedPoly kuwa Guma ya ce “zan yi qoqarin canzawa ko kuma qara wasu

ma’anoni a cikin tsangayar karatu na wannan makarantar domin a samu tsaro da havakar tattalin arziki a wannan makarantar. Yanzu haka kuma mun fara zuwa makaranti kamar babbar makaranta da take A.B.U da ATBU domin samun dangantaka don tantance wasu abubuwa don samun zarafin bayar da ilimi a matakin Digiri a cikin wannan kwalejin,” In ji Arc. Sanusi Waziri Gumau. Ya ce dangane da matsalolin da ake samu jifi-jifi na qungiyoyin malamai da hukumar gudunarwa, ya sha alwashin cewar zai yi iyaka bakin qoqarinsa wajen ganin a qarqashin kulawarsa an samu sauyi da kuma shawo kan

matsalolin da ake yawan samu, ya ce tuni ya yi qoqarin zama da dukkanin qungiyoyin malamai da na ma’aikata domin tattaro qorafeqorafen kowa don magancewa cikin kwanciyar hankali ba tare da tashi-tashina ba. Arc. Sanusi Waziri Gumau ya kuma bayyana cewar “yawan ilimi shine ci gaban kowace al’umma ba kawai ga tarin dukiyarta ba,” Daga qarshe dai shuwagabanin biyu da na shugiyar ‘yan jarida wato Alhaji Ibrahim Malam Goje da kuma shugaban kwalejin kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin tarayya Arc. Sanusi Waziri Gumau sun sha alwashin yin haxaka domin bunqasa aiyuka a kowani lokaci.

Yadda Tarukan Qasa Na Baya Ke Ci Gaba Da Yamutsa Hazon Siyasar Nijeriya Daga Abubakar Abba

Nijeriya qasarmu ta gado, ta ga taron qasa na siyasa har kala biyu. Dukkan tarurrukan biyu da aka gudsanar yau shekaru ashirin da suka shige, an gudanar da su ne a cikin ruxani. A ranar 21 ga watan Fabrairun shekarar 2005, tsohon Shugaban Qasa, Olusegun Obasanjo, ya qaddamar da taron qasa na siyaya (NPRC). Manyan jami’ai huxu na taron a qarqashin mulkin Obasanjo na wancan lokacin sun haxa da; Mai Shari’a Niki Tobi, da ya fito daga Jihar Delta a matsayin Shugaban taron, sai mataimakinsa, Alhaji Sule Katagum, wanda ya fito daga Jihar Bauci, sai Bishop Matthew Kukah, daga Jihar Kaduna a matsayin Sakatare, sai kuma Farfesa Ishaq Oloyede, daga Jihar Ogun a matsayin

Sakataren haxin gwaiwa. Taron ya shafe daga watan Fabrairu zuwa Yuli na shekarar 2005, kuma wakilai su 398 suka halarci taron wanda aka ware Naira miliyan 932 don gudanar da shi. Bayan kimanin shekaru goma da gudanar da taron qasar da Obasanjo ya haxa, sai kuma gwamnatin tsohon shugaban qasa Goodluck Jonathan, ita ma ta kafa wani taron qasa, wanda ya samu halartar wakilai 49 da aka zavo daga sassa dabandaban na qasarnan. A taron, an yi kasafin kuxi wuri na gugar wuri har kimanin Naira bilyan shida don gudanar da taron. An gudanar da taron tsakanin watan Maris zuwa watan Agustan shekarar, 2014, inda Mai Shari’a Idris Kutigi, ya shugabanci zaman taron, sai mataimakin sa Farfesa Bolaji Akinyemi, inda kuma Dakta

Valerie-Janette Azinge, ta riqe muqamin Sakatare sai Dakta Akilu Indabawa a matsayin mataimakin Sakatare mai tattara bayanan bayan taron, sai Farfesa Mahmood Yakubu, a matsayin mataimakin Sakatare, sai mai kula da harkar mulki da kuxi, sai kuma Mista Akpandem James, a matsayin mataimakin Sakataren yaxa labarai. Taron ya gabatar da shawarwari guda 600 da kuma samar da rahoto guda 10,335 wanda aka miqawa tsohon shugaban qasa Goodluck Jonathan. Taron na shekarar 2014 ya bayar da shawarar qirqiro da sababbin jihohi sha takwas, amma taron na shekarar 2005, bai bayar da shawarar qirqiro da sababbin jihohi ba, inda taron ya bayyana cewar, tafiyar da jihohi talatin da shida da ake da su akwai tsada.

A kan mallakar arzikin qasa, rahoton na shekarar 2014, ya bayar da shawarar yin qari kuxi da kuma kafa gidauniyar bayar da tallafin kuxi don sake ginawa da kuma gyara yankunan da hare-hare da sauran rikice-rikice ya xaixaita har da farfaxo da ma’adanan qasa. Bugu da qari, taron na shekarar 2005, ya bayar da shawarar yin qarin kuxi daga kashi sha uku bisa xari zuwa kashi sha bakwai bisa xari. A kan turawa jihohi kuxi kuwa, rahoton na shekarar 2014, ya bayar da shawarar da a dinga tura kuxi daga asusun tara kuxi na tarayya, inda gwamnatin tarayya za ta dinga samun kasafi 42.5 arba’in da biyar bisa xari jihohi kuma kashi talatin da biyar bisa xari ga jihohi, inda kuma qananan hukumomi za su rinqa samun kashi 22.5 bisa xari. Bugu da qari, taron na

(NPRC) bai fayyace haqiqanin shawarar da ya bayar ba, amma ya bayar da shawara cewar, ka da a qirga su a cikin waxanda za a riqa tura masu kuxi. Har ila yau, rahoton na shekarar 2014 ya bayar da shawarar gyara tsarin shugabancin qasa, wanda ya haxa da yin mulki na shugaban qasa mai cikakken iko da kuma tsarin gwamnati mai Firaminista, inda kuma taron na (NPRC) ya bayar da shawarar a ci gaba da gudanar da mulki na tsarin Shugaban Qasa mai cikakken iko. Sai dai, babu xaya daga cikin waxannan shawarwari da tarurrukan biyu suka bayar da tsohuwar gwamnatin Obasanjo ko ta Goodluck suka qaddamar da su, saboda wasu dalilai na siyaya da kuma saboda yanayi na lokaci.


A Yau JUMA'A

9

30.03.2018

Madubin Rayuwa ALLAH XAYA GARI BAMBAN

Qabilar Rabari: Masu Fifita Rayuwar Dabba A Kan Ta Mutum

Page 11

HANTSI

Yadda Za Ka Tsare Kanka Kafin Hukuma Ta Ba Ka Tsaro Page 18

HANTSI ADON GARI Page 16 Tsarin Da Mace Ya Kamata Ta Yi A Kan Aiki Da Hidimar Iyali -Aisha

Babu Mace Mai Daxin Zaman Aure Kamar ‘Yar Fim – Ladidi Tubeeless Page 10

Burina Suna: Aisha Ghali Sulaima (Nasreem) Sunan mahaifiya: Bishira Aminu Nakura Sunan makarantar : Khalifa Ishaq Rabi’u College International, Goran Dutse Kano Aji: JSS1 Burina: In zama likita don taimakon al’umma. Kalar da na fi so: Fari da Sky blue Abincin da na fiso: Shinkafa da wake da salat Shawara ga yara: Su kasance masu himma da mai da kai wajen karatu, su cire wasa. Allah ya taimake mu

Suna: Faruk Nagogo Sunan mahaifiya: Jamila Umar Tanko Sunan makaranta: JC Best School Aji: SS 1 Buruna: In zama Injiniya Abincin da na fi so: Fried rice Kalar da na fi so: Shuxi Shawara: Yara su dage da karatu su yi biyayya ga na gaba


Madubin Rayuwa

Taurarin Nishaxi

10

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2017 (12 Ga Rajab, 1439)

•Finafinai

•Kaxe-Kaxe

•Waqe-Waqe

Babu Mace Mai Daxin Zaman Aure Kamar ‘Yar Fim – Ladidi Tubeeless A duk lokacin da aka xauko batun aure, wasu da yawa kan yi wa ‘yan fim gani-gani. To amma a wannan karon magana ta qare, domin jarumar da muka tattauna da ita a wannan makon ta ce rashin sani ne ke sa mutane qyamatar auren ‘yan fim. Idan mutum ya fahimci lamarin kuwa, zai fi waxanda ke auren waxanda ba ‘yan fim ba jin daxin zaman aure, ko me ya sa? Sammam Masu karatu ko kun san shahararriyar jaurmar was an kwaikwayon ta tava yunqurin shiga aikin soja kafin ta fara wasa? A karanta firar duka a ji:

Taurarin Nishaxi Muna so mu ji cikakken tarihin rayuwarki Ni dai sunana Ladidi Abdullahi An fi sani na da suna Tubeeless. An haife ni a Kaduna a wata unguwa da ake kira Sabon Gari Nassarawa, wato xirkania ke nan. Na yi Furamare wato a Nassarawa na kuma je makaratar gaba da Furamare.duk a Kaduna wato, ina gama sakandare aka yi min auren fari sai Allah bai yi zamana da mijin ba, sai muka rabu. Daga nan sai na ji ina son yin aikin kaki, na je na sayi ‘form’ xin aikin soja na ruwa na cika na ba da aka kira mu, na je duk abubuwan da ake yi na yi daga, baya ban sake bin ta kan shi kuma ba saboda oda wasu dalillai. Yaushe kika fara fim xin Hausa, da wane fim kika fara, kuma Me ya jawo ra’ayinki kika shiga? Wata rana sai Rabi’u Rikadawa ya zo gida ya same ni ya ce min, ki zo mu je ki yi aikin fim, shi da Obina. Na ce musu ku je zan zo, amma sai na qi zuwa na neme su. Sai muka haxu da Zainab Abubakar muna hira ta ce min, ki zo mu yi aikin fim mana. Na ce mata zan bi ki. Ta ce, min, duk ran da za ta yi aikin za ta kira ni mu je mu yi tare. Na ce mata ba damuwa. kuma kafin nan, muna Hausa ‘drama’ a makaranta dama. Ran da Alfa ‘care’ zai yi wani fim sai ta ce na zo mu je. Na ce mata to, muka je muka gana, sai shi ya tambaya da ma ina fim ne? Saboda ya ga ba na kuskure. Daga nan sai na muka cigaba da zuwa N TA. Oganmu George ya ce,, na iya ‘drama’ ana ta sani. Daga nan kuma ’yan Kano suka zo Kaduna za su yi wani flm sai aka kira ni. Kafin nan mun yi wani flm wanda Rabi’u Koli ya sa Wada Rikadawa ya kira na yi, sai na ciga

• Ladidi Tubeeless a bakin aiki

da aiki sai aka cigaba da kira na ina yi, shi ne. Sai dai na manta shekarar gaskiya. Nasiru Gwagwazo zai yi wani fim Balarabe da Balarabe dila ya kira ina Abuja ya ce na je Kaduna za mu yi wani fim. Shi ma Nasiru Gwagwazo ya kira ni, na ce musu ina zuwa nako zo muka yi. Fim xin da na fara na Turanci ne, shi ne na Alfa ‘care’. Yaya kike kallon rayuwar mace a fim ‘industry’ yanxu? Gaskiya tun daga Alfa ‘care’ na zo NTA .rayuwar mace a harka fim gaskiya tana fuskantar qalubale sosai. Mafi yawan lokaci sai a ce ba za a aure ki ba saboda ’yar fim ce, amma kuma rashin sani ne yake kawo haka. Babu mace mai daxin aure da kuma daxin zama irin ’yar fim. Rayuwar mace a fim ‘industry sai dai na ce qalilan ne saboda za ta yi aure komai girmanka kuma komai tashenta wannan shi ne. A matsayin ki ta tsowar ’yar fim, wace shawara za ki bai wa yara masu tasowa yanzu a harkar? Shawara ta gare su shi ne su yi karatu, saboda na ga gaba abubuwa za su canje wanda zai kai lokaci da sai kana da karatu za ka yi shi kansa fim xin ma. In ba ka da karatu wallahi ka zama ‘sorry’. Ita ce kawai shawarata gare su. Shin Ko Kina da yara da miji kuwa? In da yaran su nawa ne kuma ta yaya kike haxa xawainiyar aikinki da hidimar iyali? Hmmmm! Ba ni da yara, amma insha Allahu zan yi aure kuma zan haihu, amma yanzu kam ba ni da ko xaya.

• Ladidi Tubeeless Ko Kina da sha’awar ‘directing’ ko ‘producing’ fim na kanki nan gaba? Na yi ‘producing’ har sau 5, amma ban ji daxi ba, a gaskiya, saboda haka na bari na haqura na koma ‘acting’ xina kawai.

taimaka Ni ma na gode da kika ba ni lokaci na amsa sa tambayoyin. Na gode Allah ya raya zuriya.

A qarshe shin bayan fim kina wani sana’ar ne ko Aikin ofis? Baya ga fim ba na wani aiki .amma ina yin aure zan nemi aiki, saboda mijin da zan aure ba zai bari na yi fim, ba. Zan kakkave kwalina na nami aikin ofis, tun da ina da kwali kuma don haka ne na yi karatun. Mun gode sosai da haxin kan da kika ba mu, Allah ya

• Ladidi Tubeeless tare da abokan aiki

• Ladidi Tubeeless


11

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

ALLAH XAYA GARI BAMBAN

tare da

Aisha Seyoji aysherseyoji@gmail.com

Qabilar Rabari: Masu Fifita Rayuwar Dabba A Kan Ta Mutum A wannan mako mun sami nasarar kewayawa, mu ka kuma kutsa cikin duniya, filin namu zai sadaku da Al’ummar “Rabari” da ke qasar “Gujarant” ta cikin yankin Indiya. Al’ummar ‘Ribari’ sun kasance makiyaya ma’ana masu kiwon dabbobi daga wani bangare zuwa wani bangare na yankin qasar domin nema wa dabbobinsu abinci, basu da takamaiman wajen zama guda xaya kasancewar su dai ba mazauna waje xaya ba ne,su na kiwon dabbobi kamar shanu, tumakai, awaki, raquma da dai sauran dabbobin gida da aka san su. Abu mafi ban mamaki ga wannan al’umma shi ne da a ce yau an wayi gari wata dabba daga cikin dabbobinsu ya kwana da yunwa, gara ace xaya daga cikinsu bil adama ya kwashe sati guda ba tare da ya sanya koda qwayar hatsi a bakinsa ba. ‘Tirqashi !’ Tabbas wannan xabi’a ta su abar dubawa ce, su kan bawa dabbobinsu kulawa fiye da da bil’adama. Babban tashin hankali ne a gare su ace dabba tana jin yunwa. Al’ada A wasu lokutan akan iya hangar mutanen ‘Rabari’ tafe da shanunsu su na kora su a kan tituna tare da iyalansu waxanda su ke sanye da tufafi irin na su na gargajiya. Mata daga cikinsu su na hura wutar itace ya ruru sosai domin su yi amfani da shi wajen girki,su na debo ruwa domin yin amfani sannan daga bisani kuma su kan tattare dukkan kayayyakinsu su xora a kan raquma, akasarinsu za ka gansu sanye da sutturunsu ma su kyau, wanda yawanci ya kan kasance ‘siket’, mayafai masu kyalli,kayan ado na qawa wadanda su ka kasance masu qara da daukar hankali. Mazaje daga cikinsu sun kasance

masu dan duhu, dogaye ne bugu da qari kyawawa ne matuka. Mafi ban burgewa da sha’awa daga waxannan mutane shi ne ,su dai suna yin tufafi, tukwane, kayan kwalliya, da dai sauran kayayyakin amfaninsu na gida da kansu ba tare da sun ce lallai sai wani ya yi sannan su samu ko su saya ba, ma’ana mutane ne masu kirkira kuma su qera ababen amfani da kuma bukatunsu na yau da kullum. Matansu su na a sahun mata masu ado na bajinta,su kan sanya maka- makan zobba a hancinsu, jibga-jibgan ababen wuya, sannan kuma ga xirka- xirkan kayan ado na qawata hannaye kamar su: zobe, awarwaro, sarqar hannu. Matansu su na sanya tufafi waxanda kalolinsu ke da hasken gaske, akasari su kan yi amfani da kaya masu haske wanda ya sanya har ake iya banbance matan “Rabari” daga cikin sauran mata. Matan aure daga cikinsu su na amfani ne da kayan ado farare misali: farin awarwaro wanda ake sanya shi tun daga tsintsiyar hannu har zuwa kafaxa, ‘yan mata kuwa su ma ba a barsu a baya ba domin kuwa su ma su kan yi nasu kwalliyar iya bakin gwargwado, su na amfani da zoben qafa, sarkar qafa, yankunne, zoben hanci da kuma saqar hannu. Akwai abin xaukar hankali dangane da waxannan mutane,wannan abu ya kasance wani nau’in zane da a kan yi musu a jiki wanda kuma baya fita(tattoo) akan yi musu zanen abubuwa kamar dangin: maciji, kunama da sauransu. Wannan zane ana yi musu shi a wurare kamar fuska, hannaye, qafafu. Auratayya Al’ummar “Rabari” su na aure ne ta sigar haxa aurarraki masu tarin yawa sannan sai ayi hidimar biki a lokaci xaya, ma’ana a tare za’a tara

auren mutane daban-daban sannan sai a gudanar da shi a wani lokaci da su ke kira da”Janmashtani”. Janmashtani: lokaci ne da ake bikin murnar zagayowar shekarar haihuwar Abin bautarsu na ‘hindu’ mai su na “krishna”. A lokacin gudanar da wannan biki akan sakaye amare ta hanyar rufe mu su jiki tun daga fuska har qafafuwansu ,sai kuma a kama wani vangare na jikin tufafin nasu a daure a jikin tufafin mijin da kowacce za ta aura, wanda kuma su ma sanye su ke da maka-makan huluna ta al’ada kamar dai rawani.

Abinci Cimar al’umar dai ta kasance kakkaurar madara ce mai zaqin gaske, ita wannan madara akan sarrafata ne ta hanyar dafawa a kan wuta mai qarancin zafi, sannan kuma sai a bar ta akan wuta ta yi ta dahuwa, zata xauki lokaci mai tsawo ta na dahuwa sannu cikin hankali zata yi kauri kuma sai kalar ta ta koma ruwan hoda. Addini Al’ummar ‘Rabari’ sun kasance masu bautar abin bautar “ hindu” wanda suke yiwa lakabi da “Krisha”.


12

Madubin Rayuwa

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

BABBAN

Li Keqiang: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Kau Da Taqaddamar Cinikayya Tsakaninsu A ran 26 ga watan Maris, a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi ganawa da wakilan kasashen waje wadanda suka halarci taron shekara ta 2018 na dandalin raya kasar Sin, inda suka yi tattaunawa kan batun cinikayyar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka. Yayin ganawar, firaministan kasar Sin Li Keqaing ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, an lura cewa, cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka tana habaka cikin sauri, dalilin da ya sa haka shi ne domin bukatun kasuwannin kasa da kasa, haka kuma domin ka’idojin kasuwancin da ake bi. Ana iya cewa, sassan biyu sun samu babbar moriya daga wajen, idan cinikayyar dake tsakanin sassan biyu ta gamu da matsala, ko shakka babu ba wanda zai samu moriya daga wajen. Yanzu haka Sin da Amurka suna fama da rashin daidaiton cinikayya, kamata ya yi sassan biyu su yi hakuri su yi hangen nesa kuma su yi kokarin sa kaimi kan daidaiton cinikayya ta hanyar kara habaka cinikayyar dake tsakaninsu, to, idan sassan biyu suna son warware rigingimu a fannin, ya fi dacewa su gudanar da shawarwari, in ba haka ba, lamarin zai lahanta moriyar kasashen biyu, har zai lahanta moriyar daukacin kasashen duniya baki daya. Li ya ci gaba da cewa, bude kofa ga kasashen waje babbar manufa ce da kasar Sin ke aiwatarwa, nan gaba kasar Sin za ta kara zurfafa kwaskwarima a fadin kasar. Yana mai cewa, “Bana shekaru 40 ke nan cif da aka fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, nan gaba kasar Sin za ta kara bude kofa ga kasashen waje, saboda hakan ya dace da moriyar kasar Sin, kuma hakan zai taimaka kan aikin tabbatar da cinikayya maras shinge, tare kuma da ciyar da bunkasuwar kasashen duniya gaba yadda ya kamata, muna son koyon fasahohin zamani na kasashen waje yayin da muke habaka hadin gwiwar dake tsakaninmu da sauran kasashen duniya, musamman ma a fannonin samar da kayayyaki da bada ilmi da samar da fasahohin zamani da hidima.” Yanzu ana kokari domin cimma burin kasancewa babbar kasa wajen kera na’urori nan da shekarar 2025, Li ya bayyana cewa, yana maraba da fitattun kamfanonin kasashen waje su zo nan kasar Sin domin gudanar da hadin gwiwa, ta yadda za su samu ci gaba tare da kamfanonin kasar Sin. Li ya ce, “Muna amfani da ma’auni iri daya yayin da

muke gudanar da hadin gwiwa da kamfanonin Sin da waje, haka kuma zamu kara kiyaye ikon mallakar fasaha.” A tsakiyar ranar 22 ga watan Maris agogon wurin, a fadar White House, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan wata takardar bayani ta shugaban kasa game da kasar Sin, inda ya sanar da cewa, bisa sakamakon rahoton bincike mai lamba 301 da kasar ta yi, kasar Amurka za ta karbi harajin kwastam mai yawa, kan yawancin kayayyakin da za ta shigo da su daga kasar Sin, wadanda darajarsu za ta kai dalar Amurka kimanin biliyan 60. Kafin haka, gwamnatin kasar Amurka ta sanar da karbar harajin kwastam na kashi 25% da kashi 10% kan kayayyakin karfen da aka sarrafa, da na karfen goran ruwa masu kirar kasar Sin, • Firaministan Sin Li Keqiang ya ce, wani na hana hanyar cigabansa ne a yayin da yake rufe kofa ga saura wannan ma ya tayar da tashin hankali a kasuwa. Game da wannan ra’ayin kariyar cinikayya na gwamnatin Trump, baya ga kasashe da dama, ciki har da kawayen kasar Amurka da suka bayyana rashin jin dadi da hakan, su ma kafofin watsa labaru, da kungiyoyin cinikayya na kasar ta Amurka ba su amince da hakan ba, ciki kuwa har da kungiyar kula da harkokin tufafi da takalma ta kasar Amurka, da sauran wasu kungiyoyin masana’antu da batun ya shafa na kasar, wadanda suka rubuta wata wasika ga fadar White House, don yin kira ga kasar da kada ta sanya wannan haraji na kwastam kan kayayyakin cinikayyar kasar ta Sin. Sannan, mataimakin shugaban hukumar bunkasa harkokin fitar da kayayyaki zuwa ketare da zuba jari gami da kasuwanci na Jamhuriyar • Jakadan kasar Sin dake Amurka Cui Tiankai ya ce, Sin ba ta son yakin cinikayya amma kuma ba ta tsoronsa Benin, Gaetan Kouponou ya yayin da take daidaita harkokin Daga karshe dai, mai yiwuwa ne bayyana cewa, ya kamata Amurka yawan basussukan da kasar ta ci zai duniya. ta yi la’akari da ra’ayin kasashen Nufin rage gibin kudi ta hanyar kara haddasa matsalar kudi gare ta, dake tasowa gami da ra’ayoyinsu, tayar da gardamar cinikayya, ta yadda hakan zai kara gurgunta kana, abun da Amurka ta yi, sam bai tattalin arzikin kasar da ya soma wannan ba daidai ba ne. dace ba. Muhimmin dalilin da ya farfado ba da dadewa ba. Gaetan Kouponou ya kara da Abin da ya fi muhimmanci sa Trump ya sanya hannu kan cewa, takaddamar ciniki tsakanin takardar bayani game da gudanar da shi ne, ko shakka babu karuwar Sin da Amurka za ta yi illa ga cinikayya da Sin, shi ne a ganinsa basussuka za ta kawo tasiri sauran kasashen duniya, ciki har gibin kudi a tsakanin kasarsa da ga gaskiyar dallar Amurka, a da kasashen Afirka. Masu hikimar Sin ya wuce hasashen da aka yi, matsayinta na kudin kasa da kasa. sun yi magana cewa, idan giwaye wanda hakan ya sa kasarsa samun Saboda haka, Trump na da dalilinsa suka yi fada, ciyayin kasa ne za gibin kudi. Ya zuwa yanzu, jimilar na rage gibin kudi. Amma, a daya su dandana kudarsu. Wannan ya basussukan da tarayyar kasar hannu a gaskiya Trump ya yi nuna cewa, kila kasashen Afirka Amurka ta ci, ya riga ya wuce dalar kuskure wajen neman sai ya binciki za su fuskanci mawuyacin hali Amurka tirilin 21. Kuma nan da kasar Sin a fannin cinikayya. Da sakamakon takaddamar tsakanin sama da shekara guda da Mr. Trump farko, kasashen Sin da Amurka manyan kasashen biyu mafiya karfin ke jagorancin kasar, yawan karuwar suna kasancewa kasar ta farko da tattalin arziki a duniya. basussukan da kasar ta ci ya wuce ta biyu da suka fi samun karfin Ci gaba a Har wa yau, Gaetan Kouponou tirilin 1. Kuma bisa ga manufar rage tattalin arziki a duniya, don haka shafi na ya ce, kasar Sin ta dade tana la’akari harajin da ake gudanarwa, wannan yadda dangantaka take a tsakanin sosai da babbar moriyar kasashen gibin kudi na gwamnatin kasar zai kasashen biyu na shafar ci gaban Afirka gami da abun da suke so su ci gaba da karuwa. Ana iya cewa, tattalin arzikin duniya baki daya. yi, kana, Benin ta yabawa kasar Sin gwamnatin kasar ta Amurka tana Kana yawan al’ummar kasashen saboda hikimar da take nunawa kan wata hanyar kara cin basussuka. biyu sun kai kashi 23% bisa na duk

13


Madubin Rayuwa

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

13

BANGO

Li Keqiang: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Kau Da Taqaddamar

• Hua Chunying ta ce, idan Amurka ta dauki matakin keta moriyar Sin, ko shakka babu Sin za ta dauki matakai da suka wajaba don kiyaye moriyarta

Ci gaba daga shafi na

12

duniya, yayin da jimilar tattalin arzikinsu ta kai kusan kashi 40% bisa na duk duniya. Har ila yau yawan kayayyakin da suke fitarwa ya kai 1/5 bisa na duk duniya, kuma yawan jarin da suka zuba a kasashen ketare, da yawan jarin da suka jawo daga ketare dukkansu sun kai kashi 30% bisa na duk duniya. A waje guda kuma, a matsayinta na muhimmin sashe na tsarin darajar duniya (Global Value ChainsGVC), kasar Sin na kasancewa tamkar ma’auni a fannonin samar da kayayyakin cinikayya masu yawa, da kayayyakin masana’antu, da kuma sana’ar ba da hidima, ciki har da jigilar kayayyaki. Ko shakka babu idan an samu sauyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu, hakan zai kawo babban tasiri maras kyau ga tattalin arzikin duniya. Bisa yanayin da ake ciki na samun tabarbarewar tattalin arzikin duniya, wannan ne sakamako da duk kasashen duniya ba su son gani ba. Ba shakka irin tsayawar Trump kan wannan lamari na iya mai da kasashe daban daban a matsayin kishiyoyi. Baya ga haka, wannan zai kawo tasiri ga masana’antu da jama’ar kasar Amurka. Tuni dai jama’ar kasar ta Amurka suke bayyana cewa, hajojin cinikayyar kasar Sin suna da inganci da kuma araha, ta yadda ba

za su iya rayuwa ba muddin babu kayayyakin kirar kasar Sin a zaman rayuwarsu na yau da kullum. Idan Amurka ta karbi harajin kwastan kan kayayyakin cinikayyar kasar Sin, ko shakka babu hakan zai haddasa karuwar farashin kayayyakin. Bisa binciken da yanar gizo ta harkokin kula da kudi ta bankunan kasar Amurka ta yi a shekarar 2016, an nuna cewa, yawancin iyalan kasar Amurka, na iya magance matsalolinsu da kudin gaggawa da ba su wuce dalar Amurka 2000 ba a kowace shekara, wadanda yawan kudin shiga da suka samu ya yi kasa da dalar Amurka dubu 25 a kowace shekara kuwa na iya magance matsalolin da ba su wuce na dalar Amurka 1000 ba. Don haka ana iya gano cewa, wannan mataki na gwamnatin kasarsu, zai kawo su illa sosai. A nasu bangaren kuwa, idan an tayar da yakin cinikayya a tsakanin kasashen biyu, za a tilastawa masana’antun kasar Amurka su sake neman kamfanonin hadin kai, wanda hakan zai haifar musu da kashe karin kudi. Nufin murkushe tattalin arzikin kasar Sin ta hanyar tayar da gardamar cinikayya zai bi ruwa Burin Trump na daban na tayar da gardamar cinikayya shi ne, murkushe tattalin arzikin kasar Sin, ta yadda kasar Amurka za ta

• Kasashen Sin da Amurka na bunkasa ciniki cikin sauri tsakaninsu

• Trump ya sanya hannu kan takardar tayar da gardamar cinikaya da Sin iya tabbatar da matsayinta na mulkin duniya. Da farko dai, kasar Sin ba ta da nufi ko kadan, na takara da Amurka wajen neman rike rangamar mulkin duniya, a maimakon haka, tana kokarin neman hadin kai irin na samun moriyar juna. Don haka, idan kasar Amurka ta tayar da yakin cinikayya, to kasar Sin ita ma za ta dauki matakai. Kasar Amurka na fitar da jiragen sama na kamfanin Boeing kashi 26%, da wake kashi 56%, da motoci kashi 16%, da kuma hadaddiyar cibiyar sarrafa lantarki domin gudanar da wani aiki na kashi 15% ne zuwa kasar Sin. Don haka, idan kasar Sin ta yarda, dukkansu za su iya kasancewa matakai da za ta dauka don mayar da martani. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, gwamnatin kasar Sin na ci gaba da yin kokarin gudanar da kwaskwarima a fannin samar da kayayyaki, da gaggauta yin watsi da wadancan kayayyakin da ake samarwa dake wuce kima, da kuma kara saurin inganta fasahohi. Baya ga haka, ta yi ta kokarin raya kasuwa a kasashen ketare, da inganta farashin kayayyakin cinikayyar kasar wadanda suke samun kyautatuwa yadda ya kamata. A shekarar 2012, wasu kasashen yamma, ciki har da kasar Amurka

sun yi binciken nuna kiyayya ga sayar da kayayyaki masu yawan gaske cikin farashi mai rahusa, kan kayayyaki masu aiki da makamashin harsken rana na kasar Sin, hakan ya sanya kamfanonin kasar Sin sun ci hasara sosai. Amma, a karshe wadannan kamfanonin kasar Sin sun yi kwaskwarima da kansu, ta hanyar kyautata fasahohi, daga karshe dai sun cimma nasara. Wannan ya nuna cewa, yanzu karfin kamfanonin kasar Sin na tinkarar matsin lamba da hadari ya karu sosai. Tsayawar da Trump ke yi ta nuna wa duniya halinsa irin na dan kasuwa, babban burinsa shi ne neman moriyar siyasa dake gabansa, wannan ma ya sa kasashen duniya ke kara fahimtar halin kasar Amurka na son kai. Ko da yake a yanzu haka kasar Amurka na iya amfani da matsayinta na rike rangamar mulkin duniya, musamman ma amfani da ikon fada a ji a fannin tsarin tattalin arziki da kudi na duniya, da hana ci gaban sauran kasashe, amma, kamar yadda karin maganar kasar Sin ya ce, “Za a samu bacewar kasa daga ban kasa sakamakon son yaki”, tabbas ne, wannan hanyar da kasar Amurka ke bi ba za ta haifar da kyakkyawan sakamako ba. (Bilkisu Xin, ma’aikaciyar sashen Hausa na CRI)

• Amurka ta kan duba kayayyaki bisa dokokin cikin gidanta kan kayayyakin da take shigowa daga kasar Sinn


14

Madubin Rayuwa Ciwon ‘Ya

Taskira Wankan Amare!

Kowa ya san cewa da an ambaci amare, ana nufin matan da ake musu shiri na musamman domin tarewa a gidan miji. Ko wane yanayi yana da irin tanadin da ya kamata a yi ma sa domin idan amarya ta shiga xakin angonta, ta more amarcinta ba tare da fuskantar wata matsala ba. Shi ma kuma ango ya san cewa lallai yayi dacen amaryar da yake burin samu kuma bai yi zaven tumun dare ba. Dangane da yawan wayar da nake samu a kwanakin nan, na gabatowar azumi yawanci amare ne suke neman yadda za su yi da fatarsu don su yi kyau da sheqi a lokacin bikin nasu. To masu neman biyan wannan buqata kusha kuruminku don na yi muku tsaraba. Bisa binciken da na yi ga abun da na fara samowa, Insha Allah wani satin zan qara turo yadda za a cire baqi da ke maqalewa a wurare, kamar su giwar hannu da yatsotsun qafa da hannu da guiwa da kuma matse matsin cinya, Insha Allah. Amma ga wannan yanxu kuna iya farawa. Ana buqatar abubuwa

Tare da Jummai Ibrahim GSM: 08185137255

kamar haka:*DILKA* Ki samu dilka ki zuba mata ruwan zafi, idan ta yi laushi sosai sai ki ajiye ta a gefe. *KURKUM* Ki fasa qwai ki cire yalo xin ki zuba kurkur a ciki da xan lemon ki buga sosai ki ajiye a gefe. *Dorot* Ki tanadi turaren dorot xinki. Ki shafe jikinki da wannan kurkur xin ko’ina, idan ya bushe sai ki xauko wannan dilka xin ki goge kurkur xin da shi ki yi ta murzawa sai komai ya fita ya yi fes, sai ki samu manja ki shafe jikinki da shi, sai ki zuba dorot ki rufe jikinki ruf amma banda kai, idan kika xan jima sai ki fito ki je ki yi wanka, washe gari ba sai kin shafa manja ba da kin shafa kurkur ki yi turaren idan kin fito ki goge da dilka. Haka za ki yi har tsawon kwana huxu, idan ba ki da ‘pimples’ ki yi har fuska. Idan kina da su, in kin gama ki shafa lemon tsami a fuskar. Kar a manta idan an gama wankan a zuba madarar turare a xan ruwa kaxan a watsa a jiki.

A Yau

Juma’a 30 Ga Fabrairu, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

Ciwon ‘Ya Mace…

Ciwon ‘Ya Mace…

Sister Iyami Jalo Turaki 08064666847 sisteriyami@gmail.com

Amfani Da Magungunan Ni’ima: Hattara Dai Mata Mata da yawa a wannan zamani sun fi fifita amfani da magungunan mata na qarin ni’ima fiye da komai a rayuwar aure wanda hakan ba daidai ba ne. Ya na da kyau mu san wasu abubuwa da ke da muhimmanci cikin dukkanin rayuwar aurenmu ba mu riqe vangare guda mu ce shi ne kawai zai yi mana jagora ba. Mu koma can baya a rayuwar iyaye da kakanninmu, mu duba yadda su ka yi rayuwar su shin ya yi iri xaya da yadda muke yin namu a yanzu? Amsar ita ce a’a, saboda mun saka son zuciya da qiwa da gaggawa a cikin zamantakewar mu. Iyayen mu sun yi zama cikin aminci da mazajensu da ganin girman juna da daraja juna, rayuwar aurensu ta yi qarko ta kuma zama abin kwatance. Yanzu me ya sa ba za mu yi koyi da su ba? Mu sa ni a irin wannan wuri mu da kanmu mu ke samarwa kan mu matsala mai girma. Ban ce kar ayi amfani da wadannan magunguna ba amma dai ya na da kyau mu yi amfani da abin da ke da inganci son samu ya zama na ainahi ta yadda mu ka san a wurin wacce mu ka saya tare da tabbacin ingancinsa da kuma ta san abin ko ya san abin sosai. Dalilin faxin haka shi ne a yanzu mafi aksari ma su sayar da waxannan magunguna sun yi yawa ta yadda har sai in an bincika sosai ake samun ma su inganci don masu sayar da na bogi su su ka fi yawa a harkar. Waxanne matsalolin waxannan magunguna na mata ke Haifarwa? Waxannan magunguna na haifar da matsaloli ma su tarin yawa kaxan daga cikin su sun haxa da : 1:Ya na haifar da cuta a cikin mahaifa. 2:Yana jawo matsala a gaban mace na samun cutar da za ta qi

warkewa ko ta qi jin magani. 3:Ya na haifar da cutar daji a gaban mace. 4:Ya na jefa mace ta rasa kuxi a hannunta saboda duk in da ta ji ana sayar wa sai ta kai kuxinta can. 5: Ya na haifar da rashin nutsuwar zuciya. 6. Ya na jawo mutuwar aure. Da sauransu. Ina Mafita? Mafita anan su ne : 1:Ya na da kyau mata mu tsaya a wuri xaya. 2: Mu nemi abubuwan da ke kewaye da mu na ainahi (natural) mu riqe, sun fi amfani ga jiki da lafiyar mu. 3. Kar ya zama komai mu ka gani ba tare da bincike ba mu doru a kai. 4:Mu zama masu samar da wasu hanyoyin samun irin waxannan kaya masu inganci. 5:kar ya zamanto rayuwar auren mu dukka mu dora ta a kan amfani da magungunan mata. 6:Bayan wannan mu zama masu ladabi, taka tsan-tsan, hangen nesa, iya girki, ado da kwalliya hakuri don rayuwar aurenmu ta zama da inganci kamar ta iyaye da kakannin mu. Shawara Mata mu zama masu kula da sanin muhimmanci lafiyar mu, waxannan magunguna akwai wadanda ke da illa ga rayuwar mu, mu sani Allah da Ya halicce mu ya hallice mu da ni’imar mu wanda wani lokaci yawan amfani da waxannan kayan mata kan kashe wasu abubuwa a jikinmu waxanda ke da matukar muhimmanci, mu zama masu yawan alaqa da rake, mangoro, kankana, madara, dabino, romon kaza, da abinci ma su kyau da gina jiki sauran mu barwa Allah don shi Ya san daidai.å


A Yau

Madubin Rayuwa

Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (11 Ga Rajab, 1439)

Raino Da Tarbiyya SADIYA GARBA YAKASAI 08023622757 E-mail: sadiyagarbayks@gmail.com

Sanya Wa Yaro Suna

Fitattun Mata

15

Tare da Khalid Idris Doya (07069724750) Kidrisdoya200@gmail.com

Hajiya Maryam Muhammad Hassan

Jamaa Assalamu alaikum. Kamar yadda mu ka saba haxuwa da ku cikin filina mai albarka, Raino da Tarbiyya, yau ma ga mu cikinsa. Dafatan kuna jin daxin wannan filin. Yau zamu faxa kan tarbiyyar yara bayan haihuwa ma’ana da zarar an haife su ana son a ba su suna na gari wanda ya ke a daraja ba irin sunayen da mu ke bawa yaranmu ba, sunan gayu, shi fa yaro duk sunan da ka bashi da shi zai tashi kuma zai iya koyi da sunayen da ba su da asali, ya na da kyau ka bawa yaronka sunan da mu ka tashi mu ka saba irinsu: Abdullahi Usman Umar Aluyu Tasi’u Surajo Muhammadu Mata kuma irinsu Nanakhadija Aisha Rumasa’u Sadiyyah Fatima Jamila Da sauransu, don Allah iyaye a kula da sakawa yara suna barkatai ba tare da an duba ba don Allah. Bayan suna kuma sai uwa da uba su sa ido ga furuci, ya na da kyau a daina furuci marar daxi ga yara don bakin iyaye babbar masifa ce ga yara, sanan a kyautata musu kalami na tarbiyya da biyayya a nusar da su zagi mugun aiki ne. Ya kamata su tashi da salati da tausayi da imani, a ringa yiwa yara shiga ta gari, don Allah kar ayi musu shiga ta banza domin shi itace tun daga xanyen sa ake tankwasa shi don Allah a kula . Shi yaro fa sai da lura domin mu iyaye mata mu ne ma su zama da su fiye da iyaye maza don haka fiye da rabin tarbiyar yara ta na ga iyaye mata yanayin fitar iyaye maza ba mazauna ba ne. Dole iyaye fa su kula yadda wannan rayuwa ta lalace wallahi sai da kula mu duba yara kanana daga shekara bakwai zuwa goma fa yanzu sun iya shaye-shaye wannan abun Allah wadai ne , tilas uwa ta sa ido sosai irin mu’amalar da yara ke yi. Aiken yara da daddare ko da rana shima ya kamata a daina shi don Allah saboda ana lalata yara sosai daga aiken nan, yara mata don Allah asa musu ido tunda yanzu babu imani yanzu a vata maka xanka ko ‘yarka. Ilimin boko da na islamiyyah ya na da kyau yara su fara karatu ana daxa kwakkwafa mu su , don su tashi dai da hali na gari. Allah ba mu ikon bi. Shigar kaya: a ringa sa wa yara kaya na mutunci tun su na qanana don su yi koyi, sannan har girman yara in su na sa kaya na gari to za su tashi cikinsa yarda ki tafiyar da ‘yayanka fa to haka zai tafi . Maza kuma su zamo masu kulawa da iyalinsu, su na bin me suke yi da zarar sun dawo daga kasuwa ko aiki , ya na da daxi uba ya ja xansa a jiki ya na tambayarsa ya ya kaza yaya kaza? Ya zamo da shaquwa da kulawa yarda da zai sa ki ji ki da shaquwa hakan na matukar taimakawa da kula da iyaye , Allah ya ba mu ikon fita haqqin yaranmu. Zamu faxa sashi na gaba wani satin idan Allah ya kaimu, masu bugo waya ga tambayoyi da yabawa ina godiya sosai Allah sa mu dace Mu tara sati na gaba ta ku ‘Yar Mutan Yakasai

Hajiya Maryam Muhammad Hassan ta kasance cikin waxanda ke yi wa mata nasiha da sanya su a kan hanya a lokacin zuwa Hajji a qarqashin gwamnatin Jihar Adamawa. Ita ce mamallakiyar makarantar Sabilu Rashad wadda ke nufin ‘hanyar shiriya’ da ke Yola na Jihar Adamawa. Ta kasance cikin waxanda ke yi wa mata faxa da sanya su a kan hanya a lokacin zuwa Hajji ta gwamnatin Jihar Adamawa. Ta samu tagomashi wajen faxakar da mata wacce ta je aikin hajji har sau goma kuma dukka domin faxakar da mata da kuma ilmantar da su kan aikin hajji. Wace ce Maryam Muhammad Hassan? Maryam Muhammad Hassan, haifaffiyar garin Yola ce a Jihar Adamawa. Ta yi karatun firamare a Sanda firamare da ke cikin garin Yola. Bayan ta gama karatun firamare sai aka yi mata aure. Bayan da haifi ’ya’ya biyar sannan ta je makarantar Islamiyya. Hakan ma ba ta gama makarantar Islamiya ba sai aka buxe fannin koyon addini na mata da maza a Kwalejin Horar da Malamai ta Mata (WTC) sai ta ta fi can. Baya ga nan kuma ta shiga makarantar koyar da larabci da addini na sakandare, a nan ta yi aji na xaya har zuwa na qarshe. Sai ta ji karatu ya yi mata daxi, wannan dalilin ne ya sa ta kuma faxa fagen karatu gadan-gada inda ta qara karatun Diploma a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta samu shaidar karatun ne a fannin Larabci da Hausa da kuma karatun addini. Bayan ta gama, a daidai wanan lokacin kuma an buxe Jami’ar Ilorin a Yola, tana jin haka, sai ta yi maza-maza domin samun gurbin yin karatu a can. Ana haka ne kuma sai Maryam ta yi wa kanta sha’awar buxe makaranta. Maryam Muhammad Hassan dai ta buxe wannan makarantar ne a sakamakon gazawar qwazon da ta gani a bayyana da wata ‘yarta a lokacin da sanya ta a makarantar Darul‘Arkam kasantuwar ta masaniya kan sha’anin koyarwa sai ta ga akwai gudunmawar da za ta bayar domin kyautatawa ta wannan makarantar tata. Wasa gaske dai bayan buxe wannan makarantar da zimmar sako sauyi wajen samar wa yara ilimi mai nagarta, tun bayan da ta sanar da wannan makarantar a gidan rediyo da jama’a sai ga shi ta fara ta-ta-ta daga Islamiyya yanzu haka wannan makarantar tata ta gudanar da yayen xaliban a matakin sakandari har sau biyu, baya ga Islamiyya, da Nazari. Maryam ta samu ginshiqin

karatu ne tun daga iyayenta domin sun kasance maso sha’awar katau sosai, wannan dalilin na daga cikin musabbabin da suka sanya ta ta yi zarra wajen koyar da ilimi da kuma tarbiyya, wanda hakan ya sanya kowa ke jin sunanta a garin Yola. Maryam dai ta yi fice ne ta fuskacin gangamin faxakar da mahajjata zuwa aikin hajji a qasa mai tsarki, qwarewarta a fannin faxakarwa da kuma wayar da kan mahajjata ya sanya gwamnatin jihar Adamawa ke xaukar nauyinta a kowace shekara domin faxakar da mahajjata kan yadda za su yi ibadarsu yadda addini ya shimfixa. Nasarorin Da Maryam Muhammad Hassan ta samu a rayuwa: Babbar nasarar da ta samu a rayuwarta dai shi ne asassa wannan makarantar, wacce take taimaka wa mata da kuma yara haxe da ba ta dama ta kuma tarbiyatar da ‘ya’yanta. Ta samu nasarar baiwa ‘ya’yanta mata huxu sun haxa Al’qur’ani yanzu qaramar ce take qoqari. A cikin mazan ma su ma sun gama Islamiya. Sannan a kan haka ne gwamnatin Jihar Adamawa take xaukar nauyinta kowace shekara zuwa Hajji domin faxakar da mata

mahajjata waxanda suka fito daga Jihar. Aikin hajjin da ta yi a bara (2017) ya kai aikin Hajji na 10 a rayuwarta. Sannan makarantar da ta buxe ta havaka har zuwa matakin sakandare wacce ake karantar da su ilimin addini da na zamani. Kuma ana rubuta jarabawar fita daga sakandare (WAEC) duk a makarantar. Waxannan kaxan ke nan daga cikin nasarorin da ta samu. Bayan nan kuma ta samu nasara a rayuwarta wajen iya sarrafa zukatan mata domin ta faxakar da su kan abubuwan da suka dace ta hanyar da ta dace ba tare da musgunawa ko kuma nuna wani ya ji haushin ta ba; wannan dalilin ne ma ya xaukaka lifafarta take callawa wadda sunanta ya yi fice a jiharta musamman kan sha’anin koyarwa da kuma aikin Ibadar hajji, shahararta kan fannin ne ma ya sanya gwamnatin jihar ke tafiya da ita wajen hidimar aikin hajji. Burina a rayuwa: Babban burinta a rayuwa shi ne ta zama a kowani lokaci ta ga ban sava wa kowa ba hatta makwabci. Maryam Muhammad Hassan dai ta kasance da mijinta har ma da iyayenta.


16

A Yau

17

Juma’a 30 Ga Fabrairu, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

ADON GARI

Tare da Jummai Ibrahim GSM: 08185137255

‘Tsarin Da Mace Ya Kamata Ta Yi A Kan Aiki Da Hidimar Iyali’ Baquwarmu ta wannan makon qwararriya ce a fagen aikin banki, duk da cewa ba aikin da ta so yi ba kenan tunda fari. To shin ta yaya aka yi ta tsinci kanta a fagen alhali ba ta da muradi tun asali? Wani irin qalubale ta fuskanta ganin cewa wasu sun qyamaci mace musamman Musulma daga yankin Arewa ta shiga fagen aikin na banki? Har ila yau, kasancewar baquwar tamu a matsayin uwa, ta shawarci mata kan yadda za su tsara hidimar iyali da kuma hidimar ayyukansu a waje. Haka nan matan da suke zaune kara-zube ba sana’a, baquwar tamu ta yi musu allurer cewa lallai su tashi tsaye su nemi abin yi, domin rayuwa. Ga cikakkiyar firar: Masu karatu za su so su ji cikaken sunanki da cikaken tarihin rayuwarki? Sunana Aisha Ali, amma da yake na tsaya a sunan mahaifina, ban tava canza suna ba sai dai inda ake buqatatar sunan maigida nakan sa sunansa a qarin nawa Imran. Ni asali ’yar Masanawa ce daga jihar Katsina. Amma a nan Kaduna aka haife ni. Na yi makarantar ‘Capital school’ da Kwalejin Zamani, har Jami’ar ABU Zariya, inda na yi Digiri da Digirgir Ga ki Bahaushiya kuma matar aure, mai ’ya’ya, mene ne ya ba ki sha’awar aiki a banki? Eh toh a gaskiya, don rashin sha’awar lissafi ma ban tava tunanin aiki a banki ba. Na so aikin diplomasiyya, don abin da na karanta a digiri ma nazarin qasa da qasa kuma a Digirgir xina na farko ma na qara yi a kan nazarin al’amurran qasa da qasa da Diblomasiyya. Amma bayan hidimar qasa da na yi a Gwambe. Na sama aiki a ‘Access bank’ da ‘Zenith’ amma duk ban karva ba. Na dawo gida Kaduna kafin na je Abuja don buxe ‘file a civil service commission’ don ina sa ran aiki a ma’aikata lamurran qasashe waje. Dalili kuwa da nake so don ina sha’awan tafiya da koyon yaren duniya. Ina Abuja sai na ji an ce, ana xaukar aiki a FSB ‘International bank’, a shekarar 2004. Ba zan manta ba, na je kurun don dai in gwada. Ina da quriciya kuma ban yi aure ba. Haka dai na rubuta jarabawa duk na kammala har na fara aiki a Abuja. Bayan na yi aure kuma na dawo Kaduna inda har yanzu nake.

In yau ba a je kwas ba gobe akwai taro kala-kala. Toh ina qoqarin daidaita rayuwata da yadda aiki ke zuwa. Ina qoqari kusanta da yara lokacin hutun qarshen mako ko hutun shekara. Ba na ma hutu sai lokacin hutun makaranta, don mu shaqu sosai. Kuma daxin abin maigidana a gari yake, kin ga in uwa ba ta nan mahaifi na nan, don haka babu wani givi da yara ke ganin kamar ba na da lokacinsu. Wani lokaci sai dai akan samu akasi, irin rashin zuwan mahifiya ranar karvar kyautuka ko wani buki na makaranta. Amma dai nakan yi qoqari qarshen mako mu zauna tare in san me suke ciki. Na daxe a aikin banki, wato wanda aka fi sani da Bankin kasuwanci, kafin in koma aikin gwamnati, inda akan samu tsarin hutun haihuwa, da ya fi inda na baro. Toh a haka kam gwamnati na kimanta mata masu haihuwa. Iyaye da ’yanuwa kan taimaka in buqata ta taso. Don haqiqa sau da yawa suna zuwa zumunci wurin kakanninsu inda za su yi wasa da kuma ganin mutane.

Kin fara aikin banki a qarancin shekaru, wane qalubale kika tava fuskanta a aikin? Gaskiya kam, ina gama bautan qasa duk da ana yajin aiki ba mu samu zuwa ba sai shekarar da ta biyo akan ce na yi sa’ar samun aiki da wuri. A lokacin kurun na fara dai da niyyar bari kuma don in samu kuxina don biyan bukqatuna tunda na girma. Za ka ji dai ana magana mutum ba aure, ya bar gida, toh amma alhamdu lillah mahifina bai nuna mana bambanci ba, kuma ya tallafa min a yayin da na sama aiki. Tunda kam ko kuxin jirgin zuwa Lagas in je gwajin lafiya, banda shi, a lokacin sai da ya ba ni. Toh kin ga • Aisha Ali Ta yaya kike iya haxa aikin banki da kula inda ba su amince ba da ba inda zan je. So ganin haka ne ya sa na dage don ni ma in taimaka masu Me za ki ce game da maza da ba sa son matansu da iyali? su yi aikin banki? Ina Fidelity Bank (bayan merger ), na fara tunda qarfinsu ya qare. Matsalar Arewa dama bai wuce maganar aure haihuwa. Kin san aikin banki na da buqatu sosai.

• Aisha Ali (a tsakiya) a wurin ‘yan gudun hijira da ke Rigasa Kaduna

• Aisha Ali tare da yaranta

ba. Balle in mutum ya yi jami’a ba aure har aka fara aiki. Amma tunda iyayena suka amince, duk wata magana ban damun kaina da ita. Ina tafiyar da abu a lokacin da ya zo. Toh Kin san kowa da nasa ra’ayin. Amma na ga ba kamar da ba. Yanzu mata na ga suna aiki sosai. Aikin banki daman tashin dare ne. Amma yanzu duk an gyara abubuwa da yawa kwamfuta ce kin ga ana samun lokaci. Amma ya kamata kuma don mutum na mace kada su nuna bambanci. Dole mutum ya natsu ya yi aiki kada hidimar gida ta bayyana a wurin aiki ko kuma a zo gida da aikin banki. Hakan zai sa a samu matsala. Da yawa za ki ga mata suna aiki suna wasu kasuwanci xin daban, ke kina yi ko da aikin kawai kika dogara? A da dai na gwada saida jewellery (zinare) don mata, amma tunda ban maida hankali ba. Na fi kula aiki sai na bari. Amma muna nan kuma ni da wasu mata yawanci qawayen juna ne sai kamar da wasa muka fara qungiya da kan taimaka wa al’umma. Musamman mata da yara. Sunan qungiyar ‘Muslimah foundation’. Ya zama kamar aiki na biyu. Ina jin daxi a lokacin hutu mukan je asibiti don taimaka wa marasa galihu. Da Ramadan da kuma duk abin da ka taso in an tuntuve mu mu taimaka. Muna tara kuxinmu daga Albashinmu dai kuma jama’a ma na mana tallafi. Ina jin daxin yin aikin qungiya don mukan haxu da mutane musamman mata masu labari a kansu. Ina qaruwa sosai.

To ita wannan qungiyar a wane gari take, Ni ke da godiya. kuma ta ya wasu matan za su iya shiga, idan Suna so su shigo cikinku. Ma’ana kuna da qa’idar cika fom ne ko yaya abun yake? Gaskiya muna ko’ina. Ma’ana ainihin mammabobinmu na asali wato, mu da ke tafiyar da al’amuran qungiyar muna wurairai dabandaban amma ofishinmu na Abuja. Amma Zan iya cewa akwai a Abuja, Kano da Kaduna. Amma duk inda ake buqatar taimako ko ma ina ne a Nijeriya za a tuntuve mu ne mu aiwartar. Za a samu waxanda za su duba aikin. Mukan gyara masallatai, makabarta, biyan kuxin asibititoci da kuxaxen makaranta na yara. Duk wanda ya zo. Akan taimaka. Muna shafin ‘Facebook’. Kuma ga ‘website’ xinmu, mutum zai iya rijista, in yana son biya to akwai 500 a wata ko kuma kurun ka/ ki zama mai taimako na ganin dama wato ba tare da biyan komi ba.

Me za ki ce dangane da matan da suke zama ba sana’a a gidan miji? Toh, ni dai a ganina babu matsala in hakan suke so don zaman lafiya. Amma dai don halin rai ya kamata ko ba za su yi aiki ba su dai nema ilimi, a iya sana’a yadda za ta iya zama da kanta ko ba aure ko mutuwa. Dole ne a riqa magana a kan abubuwan da ba a cika magana akai ba. Rabuwar aure yakan faru tunda dai ana yi da kuma mutuwa. In babu yadda mata za ta yi shi zai kaita cikin matsala. Ni dai kuma a nawa ganin, aiki ko sana’a na sa mutum ya tsaya da qafafunsa Masu karatu za su so su ji qarin bayyani don yin hidimarsa ba tare da jira ba, a yi maka ko wasu naka. Ko ma taimako ne za ka yi yadda kan ‘Muslimah Foundation’. A taqaice qungiya ce da ke taimaka wa al’umma kake so. Yana da muhimmanci amma kuma ba musamman yara da mata don su samu zaman ya zama dole. kansu. Ana iya bincikawa ta shafin www. To mallama Aisha godiya muke da lokacin da kika bamu. muslimahfoundation.com

•Yaran Aisha Ali, Zainab, Huda, Hafsa da Abdulrahman

• Aisha Ali

• Aisha Ali


18

Madubin Rayuwa

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

Hantsi Leqa

Hadari Gabas...

Yadda Za Ka Tsare Kanka Kafin Hukuma Ta Ba Ka Tsaro

Sha’anin tsaro a Nijeriya wani abu ne da za a iya cewa ya zama al’amarin haxa qarfi da qarfe a tsakanin jami’an tsaro da mutanen gari. Hausawa dai kian ce rigakafi ya fi magani. Idan mutum zai duqufa ga neman hanyoyin kare kai kafin ya garzaya wurin jami’an tsaro, zai kauce wa shiga halin jinya ko kuma rasa rai. A kan haka, muka yi nazarin wasu qwararan hanyoyi da mutum zai samar wa kansa tsaro kafin jami’an tsaro su kawo xauki. A karanta a tsanake: • Kada ka bari ‘ya’yanka waxanda ba su iya gane muryar mutum su buxe wa baqo qofa. • A yi qoqarin gane muryar baqi kafin a buxe musu qofofin. • Kulle dukkan qofofin gidanka lokacin da kake cikin gida, musamman da yamma. • Ka kashe duk na’urorin lantarkinka, kafin ka fita, koda lokacin fitarka babu wutar lantarki. • Binciki kayan da kuke dafa abinci, kafin ka fita. • Ka guje wa namijin da ya yi kama da mace mai ciki, wataqila yana

• xauke da wani abin da zai cutar da mutum ne. • Ka kulle motocinka koda kuwa ka shigo da su cikin gida. • Kare makullan abin hawanka

daga yiwuwar sace wa da yin kwafin makullin. • Kare katin layin wayarka (sim card) daga varayi don za su iya amfani da shi wajen yin cinikin kuxin

fansa. • Sayi abubuwan kashe wuta a motarka da kuma gidajenka. • Ka gaya wa malaman ‘ya’yanka kada su ba da su ga kowa, sai da izinka. • Kada ka bari baqon da ba ka sani ba ya kwana a gidanka, ka tura shi zuwa ga ofishin jami’an tsaro. • Kada ka aika da lambar katin cire kuxi (ATM), ko kuma lambar BVN xinka ga kowa. • Kada ka biya kuxin sayan kowace irin mota ta yanar intanet, idan ba ka tabbatar da mai sayar da motar ba. • Kada ka bari yara qanana su je makaranta su kaxai. • Kada ka yi tafiya ba tare da ka sanar da wani ba. • Ba da rahoto ga duk waxanda kake zargi da laifi wajen ‘yan sanda ko dakarun soji ko kuma hukumar tsaron farin kaya da sauransu. Don Allah a watsa wannan ga ‘yan’uwa da abokan arziqa. Harkar tsaro abu ne da ya shafi kowa da kowa.

Lafiya

Maganin Sanyin Mata Ko (Infection) Idan mace tana fama da qaiqayi ko quraje ko fitar farin ruwa mai wari ko bushewa ko xaukewa ko buxewa da kwailewa da rashin sha’awa ko gamsuwa da sauran cututtukan sanyi, sai a gwada xaya daga cikin waxannan hanyoyi. 1. A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya xan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau xaya. Yana maganin buxewa da qaiqayi. 2. A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, Sai mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari. 3. A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono ana sha. Yana magance matsalar ruwan infection. 4. A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a haxa waje xaya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya xan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin qaiqayi da quraje da buxewa da doxewar gaba. 5. A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjaga ta ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushewa da rashin gamsuwa.

6. A dafa Zogale, idan ta dahu sai a murje ta ko a dama, a tace, a yi lemon juice da ita. tana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma tana qara ni’ima. 7. A samu `Xan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki. Sai ta xan tsuguna tururin ya dinga shigarta. Idan ya xan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna. Zai magance mata qaiqayi da quraje kuma yana sa matsewa. 8. A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi, sai ta dake su ta yi Yaji ta dinga cin abinci da shi. Yana saukar da ni’ima da magance duk matasalolin sanyi. 9. A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankaxe. Sai a zuba a kan sabulan da aka daka sannan a kwava da Ma’ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau xaya. Amma da ruwan xumi ake tsarkin da shi. Wannan Sabulu yana maganin quraje da qaiqayi da fitar wari. 10. A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a haxe su waje xaya. Mace ta dinga shan cokali xaya kullum kafin ta karya. Yana wanke dattin mara kuma yana samar da ni’ima.

11. A samu Ciyawar Kashe-Zaqi da Farin Magani sai ta haxa waje xaya ta dinga jiqa rabin qaramin cokali tana sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali xaya kullum kafin ta karya. Wannan yana maganin dattin mara da wanke dauxar mahaifa. Abubuwan Da Suke Kawow a Mata Ciwon Sanyi Ko (Infection). 1) Rashin sanya kamfai (pant). 2) Barin kamfai ya yi dauxa sosai ba a canja ba. Ana so in da hali kullum a canja kamfai sau biyu a wanke. 3) Saka kamfai a jiqe da ruwa. 4) Yawan tsarki da ruwan sanyi. 5) Yawan tsarki da ruwan da zafinsa ya yi yawa. 6) Rashin aski. 7) Wasa da gaba. 8) Yawan cin xanyar Albasa. 9) Yin amfani da Magungunan mata marasa inganci. 10) Daxewa akan Masai ko (toilet). 11) Rashin shan iska. 12) Musanyar tufafi. 13) Saduwa da mai cutar. 12) Cutar Aljanu, wato Jinnul Ashiq. Su ma suna sanya wa mace infection mai wuyar magani. Illolin Da Sanyi Ko (Infection) Ya Ke Yi Wa Mata 1. Yana sa rashin Sha’awa.

2. Yana sa ciwon mara mai tsanani. 3. Yana haifar da qurajen bakin mahaifa ko ya toshe mahaifar baki xaya. 4. Yana sa mace ta dinga jinin al’ada baqi qirin mai wari. 5. Yana sanya farin ruwa mai wari ya dinga fito mata. 6. Yana sanyawa a dinga jin mace tana wari mara daxi kuma a rasa ta ina yake fitowa duk wankanta. 7. Yana sa jin zafi yayin saduwar aure ko kuma ganin jini a maimakon ruwa. 8. Yana rikitawa mace kwanakin al’adarta, su dinga qaruwa ko raguwa ko jinin ya dinga wasa. 9. Yana sanya wa mace tusar gaba, wato iska ta dinga fita ta gabanta. 10. Yana sanya wa mace yawan varin ciki ko kuma rashin shigar cikin kwatakwata. 11. In ya yi qarfi yana hana mace haihuwa. 12. Wani ‘infection’ xin alama ce ta zaman Aljanu a jikin mace, musamman idan tana mafarkin namiji dare ko jarirai. Abin Lura:- Idan mace ta yi magungunan Asibiti da kuma irin waxannan da muka ambata amma ‘infection’ xin bai warke ba, To ta nemi maganin jinnul Ashiq, wato magungunan Aljanu don zai iya yiwuwa matsalarsu ce. Allah ya sa a dace.


Madubin Rayuwa

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

Gidan Kowa

Assalamu aikum. LEADERSHIP A Yau Juma’a, ina farin cikin da samar mana da dama domin mu sada zumunci ga ‘yan’uwa da abokan arziki. Allah ya qara wa wannan Jaridan tamu farin jini da xaukaka a faxin Duniya baki xaya. Da farko, ina miqa gaisuwar Goron Juma’a ga babana Alhaji Bello Abubakar, sai kuma matarsa Hajiya Bilkisu Bello Abubakar, tare da ‘ya’yansu Hafiz Bello Abubakar, da Hauwa Bello Abubakar, da kuma Mustapha Bello Abubakar, da Fatima Bello mamammu wato Hajiya Bilkisu Bello Abubakar kamar su Hajiya Safiya Ahmad Yabo, sai kuma Hajiya Sa’adatu Ali Haruna, da Hajiya Halimatu Abbas Bella, daga qarshe ina miqa saqon Goron Juma’a ga Hajiya Hauwa Abbas Bello. Da fatan duk suna nan cikin qoshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a. Daga Muktar Bello, Sakkwato. 08065718705 Bayan gaisuwa mai tarin albarka, tare da fatan Allah ya xaukaka wannan gidan jarida tamu, nake miqa gaisuwar Goron Juma’a ga abokan arziki kamar su: Salis Kalifa Baba Ahmad, sai kuma babban aminina wato Muhammad wanda aka fi sani da Mamman a cikin garin Kaduna, da kuma Barista Muhammadu Tasi’u Sirajo, da Yunus Abubakar da ke Kaduna, sai Malam Uwaisu Buhari Imam a Abuja, da kuma Muhammad Idris a ‘Lake View Homes Phase 2’ a Kado, daga qarshe ina miqa saqon gaisuwar Goron Juma’a ga mai gidana Raji Musa Yakubu. Da fatan duk suna nan cikin qoshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a. Daga Ubale Xahiru, Kaduna. Salam, gaisuwar Goron Juma’a ga masoyana kamar su mai gidana Farfesa Musa Yakubu, sai kuma ‘ya’yansa Raji Musa Yakubu da Aminu Musa

19

Tare da Yusuf Shuaibu

Goron Juma’a

Yakubu, tare da Fatima Hamisu, da Imam Ahmad, daga qarshe ina miqa saqon Goron Juma’a ga Mustapha Hamisu. Da fatan duk suna nan cikin qoshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a. Daga Usman Hamisu, Kaduna. 08160874213. Dubu gaisuwa tare da fatan alheri ga wannan Jarida tamu mai tarin albarka. Ina so in miqa gaisuwar Goron Juma’a ga abokanaina kamar haka: Muhammad Idris, sai kuma Kalifa baba Ahmad, tare da Umar Dogara Inkiya Lauqalauqa,da Adon Wanki wato baban Amir da Muhibbat, Oga Ubale Mai wanki da guga, tare da Zubairu Dogi, daga qarshe ina mai miqa gaisuwar Goron Juma’a ga Xan ladi Kalmi. Da fatan duk suna cikin qoshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Daga Abdurrazaq Badarawa, Kaduna. 08056455866. Gaisuwar Goron Juma’a cike da farin ciki ga dangina Hassan Yusuf da ke qaramar hukumar Kagarko a jihar Kaduna, da Shehu Umar Kagarko, sai kuma Shehu Yusuf Kagarko, tare da Abdul’Aziz Abdullahi Kagarko, da Zakari Isma’il, daga qarshe ina miqa saqon gaisuwar Goron Juma’a ga Malam Falalu Abdullahi da ke garin Abuja. Da fatan duk suna nan lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a. Daga Isma’il Yusuf, Kagarko. 08168499372. Dubun gaisuwa tare da fatan alheri ga wannan fili namu mai tarin albarka. Ina so in miqa gaisuwar Goron Juma’a ga masoyana kamar su

08034980391

Shugaban Kwamitin Badarawa Road Kaftin, sai kuma Shehu Shagari, tare da Yakubu Kada, da Ali Police, sai Baba Kafinta, da Xansisi, tare da Miko a Legas, sai kuma Iliya Kazode, da Sagir Kazode mai Lemu a Abuja, daga qarshe ina miqa saqon Goron Juma’a ga Muttaqa ango Batsari. Da fatan duk suna nan cikin qoshin lafiya, Allah ya sa haka, amin. Barka da Juma’a. Daga Shugaba Ahmad Na Malam Kazode Kwaru Badarawa, Kaduna. 08066039228. Da farko, gaisuwa tare da fatan alheri ga wannan Jarida tamu mai tarin albarka. Ina so in miqa gaisuwar Goron Juma’a ga abokanaina kamar haka Muhammad Idris, sai kuma Kalifa baba Ahmad, tare da Umar Dogara Inkiya Lauqa-lauqa,da Adon Wanki wato baban Amir da Muhibbat, Oga Ubale Mai wanki da guga, tare da Zubairu Dogi, daga qarshe ina mai miqa gaisuwar Goron Juma’a ga Xan ladi Kalmi. Da fatan duk suna cikin qoshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Daga Abdullahi Mai Kano, Kaduna. 08026441039. Salamu alaikum. Fatan alheri ga wannan fili namu mai tarin albarka, Allah ya xaukaka wannan Jaridan tamu a Duniya baki xaya. Gaisuwar Goron Juma’a ga makusantana kamar su Abubakar Shuaibu, sai kuma Maharazu Shuaibu, tare da Fatima Shuaibu, da kuma Halima Shuaibu, da Yusuf Shuaibu, sai kuma Usman Shuaibu, daga qarshe ina miqa saqon Goron Juma’a ga Kakan mu Hannatu Shuaibu. Da fatan duk suna nan cikin qoshin lafiya, Allah ya sa haka, amin summa amin. Barka da Juma’a. Daga A’isha Usman Shu’aibu Badarawa, Kaduna. 07039863413.


20

Madubin Rayuwa

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

Tare da JAMILU ADAMU jamiluadamu11@yahoo.com +23408100800997 (Tes kawai) jamilu.adamu@leadershipayau.com

Rai Dangin Goro

MAI IDO A TSAKAR KA

Injiniyan Injiniyoyi

Duniya juyin-juyi

Raino ko chartin?

Xakin haya

Ko ba lantarki, akwai ruwa mai sanyi

Shawar gargajiya

Mu Qyaqyata • Daxin Inuwa

• Hadarin Masu Talla Wasu Fulani ne, za su je tallar nono, sai mota ta kwacewa direba, suka faxa rami. Bayan an fito da su, wata ta tava kanta ta ga farin abu (kindirmo) sai ta fashe da kuka tana cewa: “A kai ni asibiti qwaqwalwa ta fito waje.”

Wasu mutane, su biyu wata rana suna zaune a wata inuwa, Daya daga cikinsu sai ya kama tunanin ya samu aiki a kamfani kuma shine manaja: xaya kuma ya yi tunanin cewa abokin zaman nasa ya yi masa laifi, sai ya mare shi, har sai da ya faxi. Mutane suka ba shi haquri, ya ce ba komai. sai da ya tashi zai tafi, da ya juya sai ya qwaxa masa mari, har ya suma aka yayya fa masa ruwa. Da ya farfaxo, ana yi masa sannu, shi kuwa yana cewa: “an kama mai motar daya kaxe ni?”

• Addu’ar Yaro A Gaban Mahaifinsa Wani ne yake da yaro Musa ya dame shi, asiya masa keke, sai ya ce masa ya riqa yin addu’a Allah, ya bashi kuxi ya saya masa. Wata rana an gama Sallah sai yaron ya xaga hannu ya na addu’a ya na cewa, ‘Allah kaba baba na kuxi naira xari da hamsin.” Sai ya gyara masa yace: ”ka ce naira miliyan xari da hamsin.


A Yau

Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

Madubin Rayuwa

Hannunka-Mai-Sanda

21

Mukhtar Anwar 0803 667 9084

Matasan Zamani: Karuwan Siyasa A Nijeriyar Yau

Idan ana batun “Karuwa ko Karuwanci”, babu makawa za a iske wani yanayi ne da ke da alaqa ta qudda-qud da musayar Nairori ko Daloli a kan turbar qarya. Karuwa, kan shahara birbishin sauran takwarorinta yayin da ta kere su samun shigowar qazaman kuxaxe babu qaqqautawa daga abokanan dadironta. Abin nufi, Matasan wannan Zamani da muke ciki musamman na qasarmu Nijeriya, sun fi ganin qimar “yan mutsabbai ko Nairori sama da “yancinsu da mutuncinsu cikin zarafofin siyasar yau. Qwalamar son abin duniyar kuwa, tuni ya jima ga fizgar su zuwa ga aikata duk wani irin munkari a bisa turbarsu ta begen samun nasara ga Jam’iyyunsu na Siyasa, ko da kuwa hakan zai bayu zuwa ga mujazar kyalayar da jinanen al’uma da sunan abokanan hamayyarsu ta siyasa. Zan iya tunawa cikin Shekarar 2004, yayin da nake gudanar da wani bincike game da yadda ya dace a riqa tafiyar da harkokin Fina-finan Hausa na Zamani, yadda za su yi kwabo-dakwabo da kyawawan al’adun Malam Bahaushe da koyarwar Addinin Musulunci, na nemi abokina Sha’aibu Usman Anto (Na-fallomi, a lokacin da yake bisa kujerar Sakataren Jam’iyyar PDP a Dala), wanda a yanzu haka yake Shugaban Jam’iyyar Gwamnati ta APC a dai Dalar, da ya raka ni wajen

Marigayi Alhaji Mudi Sipikin don neman tattaunawa da shi bisa wasu muhimman abubuwa da suka shafi al’adunmu da siyasarmu. Ni da Anton, mun yi katarin samun Sipikin xin a gidansa dake a “Unity Road” daura da Kasuwar Kantin Kwari. Bayan tattaunawar tamu ta fara nikatawa ne, sai yake nuna mana rashin jindaxinsa na irin yadda a yau aka mayar da harkar tafiyar da jam’iyyun siyasa da tamkar sabgar KAMFANI, tare da yin hannunka-mai-sanda na yadda aka rasa cikakkiyar aqida wajen tafiyar da zarafofin siyasa musamman a tsakanin Matasan Zamanin da muke ciki. Malam Mudi Sipikin yake faxa mana cewa, wani lokaci can baya, Malam Aminu Kano ya aike shi zuwa garin Kura, don gabatar da wani zarafi na siyasa. Ya cigaba da cewa, a qafa ne ya je garin Kurar, ya dawo a qasa ba tare da ko tambayar kuxin mota ba. Ga wasu daga cikin muhimman bayanan da marigayi Sipikin din yai mana a lokacin waccan tattaunawa da mukai da shi a gidansa; “...Babu maganar kuxin mota. A wancan lokacin, “yan jam’iyya ne ke yin aikin jam’iyya da kuxaxen aljihunsu, ta hanyar yin karokaro. A lokacin, samsam ba a tunanin wai wani bajimin mai kuxi ne za a zurawa-ido ya dinga samarwa da “yan jam’iyya wasu maqudan kuxaxe wajen

tafiyar da aikin jam’iyya. A lokacin, hatta FASTA ta XAN TAKARA, kasawa ne ake yi “yan jam’iyya su zo su saya...” Shin yanzu haka batun yake cikin jam’iyunmu na siyasa? Shi ya sa a wancan lokaci aka fi mayar da hankali ga yin Siyasar Aqida. Idan xan takara a wancan lokaci ya sami nasarar lashe zave, dolensa ne ya saurari buqatun al’umar mazavarsa, ya je ya zartar a aikace. Ko ya je ya gabatar da muradun nasu a gaban Majalisa, don tattaunawa gami da lalubo bakin zaren a aikace. Babu batun yin wata homa ko ta-da-karan-hanci da Xan takara ya isa ya yi. Eh mana! Nawa ne ya ba da aka zave shi?. Cikin wani littafi na Dr Auwalu Anwar da ake kira da “Gyara Kayanka”, ya tabbata cewa, a zamanin mulkin Ibrahim Badamasi Babangida ne “yan siyasa cikin wannan qasa suka fara sanya ganyen bishiya bisa kawunansu a Tashoshin Zave suna faxin, “suna siyarwa ne”. Ba sai an faxawa mai karatu ba, ya sani cewa irin waxancan harqalloli na rashin mutunci da akan yi kwalli da su a tashoshin zavuka a wannan qasa, za a ga cewa Matasa ne kan gaba wajen aiwatar da su. Wasu Daga Miyagun Janibobin Da Akan Yi Amfani Da Matasan Wannan Zamani A Siyasance Cikin Nijeriyar Yau Vangare mafi muni gami da haxari

da a yau ake amfani da Matasan wannan Zamani a siyasance shi ne; wajen ta da hargitsi gabanin ranakun gabatar da zavuka; afkar da husuma a ranakun zave da kuma haddasa rikicerikice bayan kammala zavukan. Abu mafi sharri a wannan janibi shi ne, amfani da gungun matasan namu wajen aike wa da abokanan Hamayya zuwa Barzahu. Irin wadancan Matasa da ba su xauki ran abokin adawar siyasa a bakin komai ba, na da mabambantan sunaye ko a ce laqabobi da ake kiran su da, a mabanbantan garuruwa na wannan qasa. Misali; i-Ana kiran su da “ “Yan Daba” a Kano ii-Ana kiran su da “ “Yan Kalare” a Gombe iii-Ana kiran su da “Sara-suka” a Bauci iv-Ana kiran su da “Area Boys” a Sakkwato v-Ana kiran su da “Ecomog” a Borno vi-Ana kiran su da “Agaba Boys” a Cross-River vii-Ana kiran su da “Omo-ita Renegades” a Osun (Ille-Ife) viii-Ana kiran su da “Area Boys” a Delta (Warri) ix-Ana kiran su da “Ofio Boys” a Rivers (Port Harcourt) x-Har’ila yau dai a jihar Ikko ana kiran waxancan ‘yan ta’adda da laqabin “Area Boys”


22

Madubin Rayuwa

A Yau

Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (11 Ga Rajab, 1439)

Ciwon ‘Ya

Tare da JAMILA UMAR TANKI (JUT) 08037196708

Rubutunka-Tunaninka

Matsalar Kasuwa Ta Fi Addabar Marubuta A Yanzu – Maryam Ali

Hajiya MARYAM ALI ALI marubuciya ce ta litttafan Turanci da na Hausa, sannan Malama ce a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano. Haka nan ta riqe muqamai a Qungiyar Marubuta ta Qasa (ANA). Ta halarci taron marubuta a qasashe daban-daban. A tattaunawar ta da shafin Rubutunka Tunaninka da a garin Katsina ta, ta yi bayani dalla-dalla a kan yadda sha’anin rubutu yake a zamanin baya da yanzu. Musamman ta tavo batun matsalolin da suka zama qarfen qafa ga marubuta a wannan zamanin. Masu karatu, a karanta tattaunawar daga farko har qarshe a sha bayani daga basirar wannan gogaggiyar marubuciyar: Assalamu alaikum, Hajiya za mu so ki fara da taqaitaccen tarihinki. Wa’alaikumussalam. Sunana Maryam Ali Ali. Ina koyarwa a kwalejin ilimi na Sa’adatu Rimi a yanzu haka ina karatun digirina na uku a Jami’ar Bayero. Na yi digirina na biyu a Usman xan fodiyo, digirina na farko kuma na yi a Jami’ar Jos. Yaushe ki ka fara rubutu? Na soma rubutu tun ina ‘yar qarama ina firamare amma littafin da na fara bugawa na buga shi a shekarar 1996 mai suna fuskokin Naira. Wannan littafi mai suna fuskokin naira a shekara ta 2006 na fassara shi zuwa turanci na wallafa shi sunansa ‘the faces of Naira’ kuma ya samu karvuwa sosai don yanzu babu saura a kasuwa sai an sake bugawa. Sannan kuma littafina na biyu shine ‘sai gani na biyu’ sai kuma littafina na uku wanda shi ne na qarshe sunansa ‘almajiri.’ Shi wanan littafi mai suna almajiri me ya qunsa? Akan almajirai na yi ko da ya ke qagaggen labari ne. A vangaren rubutun turanci fa? Ina rubutu da turanci ina yi da Hausa, akwai ‘chief dudu and the goden sea’ littafi ne da ya tavo harkar siyasar qasar nan. Sannan akwai waqoqi na turanci da na rubuta akan yanar gizo-gizo sunanansa ‘lost and glow’ amma shi ban buga shi a takarda ba dai amma ana shirye-shirye. Ki na cikin qungiyoyin marubuta ne ko zaman kanki kawai kike yi? Ina cikin qungiya, na riqe muqamai da yawa a qungiyar marubuta ta qasa wato ANA farko da aka yi zave a 2005 a kano a ka zave a ex official member sannan da aka sake dawowa na tsaya a takarar financial sactary aka zave ni sannan muqamin da na riqe a qarshe a qungiyar marubuta ta

qasa shine National terajara Dukka waxannan littafai da ki ka wallafa ana iya samunsu yanzu haka a kasuwa ko kuma sun daxe da vacewa? Eh! Yanzu dai almajiri kawai ya ke a kasuwa sai kuma na gaba da na ke shirin fitowa da su. Yaya ki ke ganin rubutu a yanzu da kuma na da, musamman ta vangaren kasuwa? Marubuta suna iyakacin qoqarinsu amma a harkar kasuwa duk marubuci zai ba ki labarin cewa baya jin daxinta gaskiya ba wai makarantan ne babu ba amma yadda ake tsara siyar da litttafai ne bai yi ba. Domin ni abin da ya sa ma na buga littafina na qarshen nan a yanar gizo sabo da matsalar kasuwa. Sai ka kai littafinka kasuwa ya yaxu a cikin duniya ka ji ana ta kiranka a waya ko ana turo saqonni cewa an karanta littafinka a argungun da sauransu wasu ma daga qasar waje za su kira ka su ce sun karanta littafinka amma kuma idan ka zo karvar kuxi sai a ce ba a siyar ba. Idan ka buga littafi ka kai kasuwa sai dai ka nemi wani kuxin idan za ka buga wani amma kada ka saka rai cewa wannan littafin da ka kai kasuwa har za ka siyar ka sami wata riba a kai, kawai duk wanda ya ke wallafa littafi a yanzu sai dan kawai ya na da ra’ayin abin ne amma ba wai dan ana samun wani ciniki ba. Sannan kuma ga hayar litttafai da ake bayarwa mutum ya sayi litttafi guda xaya ya dinga bayar da haya yana karvar kuxi yana sakawa a aljihu kuma ba za ka tava jin hukumar kare haqqin xan adam sun shigo ciki ba domin babu ruwansu da mu idan ka ji kuzarinsu toh harkar ‘yan fim ne ‘yan fim xin ma na kudu wato Nollywood. Misali idan ki ka je kasuwar Bata ga litttafai nan barkatai ki na xauka kin san cewa ba mai kyau ba ne bugu ne na voge amma ba za ka tava jin sun zo sun

• Maryam Ali

bi haqqin marubuci ba kamar yadda aka xauke su aiki su yi ba. Ga shi kin haxa rubutu biyu na Hausa da turanci , kamar gari irin kano littafanki na turanci sun samu karvuwa kuwa ko kuwa sai na Hausar ne kawai su ka karvu? A gaskiya litttafan turanci ba sa tafiya sosai a Kano dan na buxe shago ma mai suna ‘vatual authors publishers’ in ki ka ga an zo sayen litttafan turanci tabbata yaro a ka rubutawa a makaranta za ki ga uba ko uwa ta zo saye amma don littafai na karantawa na nishaxi da na qaruwar ilimi ba a cika saye ba, sai dai a waje kamar in za a yi taron marubuta sai in tafi da littattafan turanci sai ka ga ana

saye shiyasa na ce na turancin ya qare guda xaya tal na ke da shi na ajiye. Kwanakin baya akwai taro na marubuta da masu zane Kabafaest ‘kaduna books and art festival’ an gayyaci marubutan Hausa da na turanci sai na fuskanci rubutun turanci ya danne na Hausa sosai. Musamman ta wajen bugu za ki ga littafan Hausa ba su da ingancin bugu har ma su na kunyar nunawa savanin bugunsu na turanci masu inganci. Rashin haxin kanmu ne domin kin ga harshen Hausa ba qaramin harshe ba ne duk duniya kuma duk in da ka je sai ka sami Bahaushe. Muhimmancinsa ne ma ya sa manyan qasashen duniya su

Ci gaba a shafi na

23


A Yau

Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

Ciwon ‘Ya

Madubin Rayuwa

23

Rubutunka-Tunaninka

‘Matsalar Kasuwa Ta Fi Addabar Marubuta A Yanzu’ Ci gaba daga shafi na

22

ke watsa shi a gidajen radiyon su kuma kuxi su ke biya su xauki ma’aikata ,in da bashi da muhimmanci ba za su bawa kansu wannan wahalar ba idan ki ka yi la’akari ai akwai wasu yaruka na duniya akwai manyan yaruka a qasar nan amma baa xauke su ba sabo da haka duk wani gyara babu wanda zai yi maka sai ka tashi ka yiwa kanka su ma na turancin su su ka yiwa kansu su ka nemawa kansu ‘yanci sun inganta wa kansu rubuce-rubuce a yanar gizo Marubuta Hausa su na da basira sosai da a ce za su dinga juya rubutunsu zuwa turanci mutane da dama za su amfana. Yaya kika ga wannan maganar? Kwarai da gaske mu na da basira akwai ma hanyar idan ba ka da ilimin da za ka yi rubutu da turancin. Kin ga akwai qasashen da ba turanci ne yarensu ba amma sai a samo masu fassara su fassara littafin cikin turanci da ma wasu yarukan kamar faransanci da sauransu. Shi ya sa idan ana taron gangami na litttafai na duniya wato ‘international book fair’ za ki ga waxanda su ke zuwa wajen har da masu fassara idan ka je wajen za ki ga su na tallata kan su su na cewa suna fassara littafi daga yare kaza zuwa kaza . Misali idan ka ga wanda ya ce ina fassara daga Hausa zuwa turanci za ka iya xaukar littafinka na Hausa ka bashi ya fassara ma ka ba a turanci kaxai ba har zuwa faransanci yadda abin da ka rubuta zai yaxu a duniya iyakaci ka biya shi. Yaushe ne ake yin wannan taro na gangami na litttafai na duniya? Ana sanarwa su ce za su yi a qasa kaza duk shekara, amma wannan taron marubutanmu xai-xai ne su ke zuwa su ma xin ba na Hausa ba. Gaskiya marubuta Hausa ba sa cusa kansu, kin ga kamar anan a arewa an ba da dama ANA ta kasu kashi biyu vangaren Hausa da na turanci, an ba marubuta Hausa dama su tallata kansu akwai kyautuka da qungiyar ‘ANA’ ta ke qoqarin samowa a zo a saka cewa ga marubutan Hausa don su sami wannan kyauta amma idan a ka zo wajen taro ba za ki ga ‘yan arewa ba ba sa zuwa kuma in da ana zuwa da yawa xin ai dole mu yi tasiri dole a san da mu. Kamar yanzu a taron nan na ranar marubuta ni banga babba daga

cikin ana ya zo ya wakilci ANA ba, ban sani ba ko baa gayyace su ba ne amma ya kamata ace wannan taron ya yi tasiri a ANA har sun turo wakilai da za su zo su karanta ko da jawabin shugaban ANA na qasa, amma babu wannan. Kin ce marubuta Hausa basa cusa kansu, ba kya ganin ko ba a sanar musu lokutan taron ne shiya sa ba sa zuwa? Marubuta Hausa ba su da cusa kan su. Yanzu akwai wani marubuci da ya ke rubutu a kan yaren Nupe, duk wani taron ANA sai ya tashi ya yi magana a kan wannan yaren nasa cewa ga abinda ya ke yi, tun ba a sani ba har yanzu an zo an san shi. Amma yadda marubuta Hausa su ke da yawa xin nan mu ke da tasiri mu ke da makaranta. Ki duba ki ga shirin nan na radiyo da a ke yi ‘rai dangin goro’ idan ki ka yi goggling za ki ga mutane nawa ne su ke sauraro, za ki ga miliyoyin mutane su ke saurare ya nuna ana da sha’awa, in za a sami yawan masu saurare za a sami yawan masu karantawa ko ma fiye, amma ba za ki shiga yanar gizo ba ki ga marubutan Hausa su na talaata kan su ba sai xai-xai-ku. Ga ki a wajen taron Ranar Marubuta Hausa ta duniya, zai yiwu kin ga wasu kurakurai. Wacce shawara za ki bawa marubuta a kan su haxa kai su kuma inganta taron anan gaba? Taro an yi qoqari matuqa sabo da an yunquro da wasu tunani da za a ci gaba amma da ya ke na farko-farko ne dole sai an sami kura-kurai. Ina ba su shawara duk abin da za a yi a dinga tsari . Yawanci a taron nan babu tasirin rubutu a ciki, kashi saba’ain cikin xari waxanda su ka sami dama a wajen taron nan mawaqa ne, kuma taron nan ba na ranar mawaqa ba ne kuma in mawaqa su na taronsu ba za su ce marubuta su zo su karanta rubutunsu ba amma su su ka babbake komai . A bawa marubuta dama ma su gabatar da kansu ma babu, a zo a karanta littafai kamar yadda aka saba yi a taron marubuta dukka babu, gabatar da sababbin littattafai, gabatar da sabbabin marubuta, gabatar da tsofaffin marubuta duk babu. Daga ‘yan siyasa sai manya sai tsofaffin marubuta da su ka tsufa su ka ajiye rubutu, an rabu ba a san juna ba sannan kuma wasu abubuwa

kamar idan za a yi gangami irin

sami kwali ka jefa ka ajiye ko ba

• Maryam Ali wannan akwai wajen waxanda aka san za su tallafa ba lallai sai ‘yan siyasa ba, akwai ‘yan kasuwa ,akwai malamai ma su kishin abin ya kamata a baza koma a nemi kowa da kowa ko da mutum ba shi da qarfin da zai bada kuxi akwai mai basirar da zai bada gudunmawa da basirarsa a wajen taron . Sannan idan za a yi a nemi shawarwarin jamaa daban-daban ba dole sai ‘yan kwamiti ne za su yi komai ba. Akwai abinda za ki iya qarawa wanda ba mu tambaye ki ba? Abin da zan ce shi ne Allah Ya bawa marubuta sa a idan ka zama marubuci kasancewa baiwa Allah Ya baka wani ko gajeren saqo ya tura a waya ba zai iya rubutawa ba. Ba za ka san cewa baiwa ce Allah Ya baka ba sai wanda ya karanta littafinka ya kira ka da qarfe xayan dare ya ce yanzu na gama karanta rubutunki Allah ya biya ki . Akwai wani marubuci manazarci malamin jami’a ne Allah ya jiqansa sunansa Hambali jinju xan Niger ne amma yawancin rayuwarsa nan ya yi yawancin manyan furofesoshin nan sun san shi malaminsu ne. Shi ya ke cewa idan kai marubuci ne duk sanda tunani ya faxo maka na rubutu, ka rubuta ka xaure ka

ka da halin bugawa ka rubuta ka ajiye, ranar da halin ya zo sai dai ka xauka ka karkaxe ka buga kayanka Hajiya mun gode muna fatan nan gaba idan mun neme ki za ki ba mu dama… Mun gode muku kuma ai abokan tafiya ne, ku ke yaxa al’amuranmu a duniya ba za mu iya gode muku da baki ba sai dai mu ce Allah Ya saka mu ku da alkairi ,dan kuma kusan marubutan ne matsalollinmu kusan xaya ne da mu da ku.

• Maryam Ali


24

Madubin Rayuwa

Magunguna A Musulunci facebook: Magunguna A Musulunci

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439) Dakta Jamil Nasir Bebeji 07017790084 magungunaamusulunci@gmail.com

Ciwon Sanyi Da Maganinsa (3)

Ko Kun San?

Domin Tuntuva: 08033225331

•Warin sararin sama Masana kimiyya sun bayyana cewa sararin samaniya ya yi kama da warin qarfen da aka sa a wuta ya fara qauri.

•Sau biyu kacal shugaban amurka ya tava aika saqon email Wajibi ne ko wane malami ko malama da ke son aiki a Qasar Koriya ta Arewa ya iya rawa da waqa kafin a ba shi takardar shaidar malanta. Da rawa da waqa ake tantance malaman a shekarun 1990.

Idan masu karatu suna biye da mu, har yanzu muna nan cikin bayani kan ciwon sanyi da alamun kamuwa da shi, da irin illolin da yake tsakanin maza da mata, da dalilan da suke jawo shi. Kuma mun tsaya ne a kan illar da yake yi wa mace mai ciki da kuma yadda yake cin naman jariri tun yana cikin mahaifiyarsa. Za mu ci gaba. Kuma qazanta da rashin kyakkyawan abinci yana qara wa ciwon qarfi, ya kan qara tsanani in ya haxu da ciwon (Siflis) sai ka ga har da qurarraji, da ganin farin ruwa da gurvataccen ruwa, inda wani lokacin wani lokacin ya kan fara da ‘yan quaraje, ko qurji xaya a qasan ciki ko saman mara, ko tsakanin cinyoyi a gaba, wani lokaci kuma ko a hannaye ko a qafafuwa, waxanda suke da saurin jini wurin tavawa ko sosawa. Banbancin su da na (Siflis) shi ne, su suna da zafi ko qaiqayi in dai sun fito. Sannan sun fi saurin bayyana a jikin namiji fiye da mace, qurajen ke nan. Shi wannan ciwon sanyin in aka kamu da shi, ana fara ganin alamarsa tun daga kwana uku zuwa sati biyu a mafi yawa, kuma ana iya warkewa gaba xaya in aka samu maganinsa mai kyau. Sannan ya watsu sosai cikin duniya, da yake dama tsohon ciwo ne, musamman qasar Indiya da maqotansu kamar yadda qididdiga ta nuna, ha rake cewa kashi 31 cikin xari na ciwon sanyi yana qasar Indiya. Wannan wani nau’in ciwon sanyi kamar yadda ma’abocin littafin (Qissatul’axibba) ya faxakar wanda yake sananne a fannin likitanci, da masu bincike, wanda shi xan qasar Indiya ne, ya kawo labarin wani mutum da ya kasance a nahiyarsu yake cewa, shi irin wannan ciwon mai rarake cikin jiki ya cinye shi, ya kama mutumin. Shi ko mutum ne da kwata-kwata bay a iya haquri da jima’i, sanda alamar ciwon ta bayyana, sai da likitoci suka ce masa ya qauracewa saduwa amma sai ya qi ji, saboda haka wata rana yana saduwa da matarsa, sai kawai gabansa ya guntule a cikinta. Nan da nan suka garzaya wurin wani likita akan wannan matsala, inda ya tambaye su tun yaushe ciwon yake jikinsu? Sai wannan ya ce, tun shekara 13, ya ce to ba a ba su magani tare? Ya ce ana ba su. Likita ya ce, to me ya sa ciwon ya qi warkewa tun wancan lokacin?

To ku gaya min gaskiyar rayuwarku, domin matsala ce ta faru da ake so a yi maganinta, a cikinku waye yake saduwa da wani a waje? Wannan mata tai rantsuwa da alqur’ani ta ce, wallahi tun da Allah ya halicce ta bata tava sanin wani xa namiji in ba mijinta ba. Shi kuma ya faxi gaskiya cewa ya sadu da mata sun fi dubu 3, kuma a yanzu ma akwai wasu. Shi ne likitan ya ce da shi, “To wannan shi ne dalilin da ya sa ciwon ya qi warkewa saboda kuna shan magani kai da matarka, amma sauran masu ciwon da ka sa masu ko ka xauko a jikinsu su ba sa sha, saboda haka kullum ciwon yana nan a jikinka ba zai tava raguwa ba, sai ma qaruwa ya ke yi. Saboda haka wannan matsalar ta ciwon sanyi ta daxe tana cutar muyane, gashi har ta kai tana guntule gaban maza, wanda na yi qoqari na tuntuvi likitocin bature na manyan asibitoci, ka,ar asibitin Murtala da na Malam Aminu duka a Kano, suka tabbatar min da cewa tabbas akwai mutanen da suka zo gabansu ya guntule, kuma aka yi bincike aka gane cewa ciwon sanyi ne ya haifar da hakan. Mu ka cigaba akan cewa, to a wannan lokaci da wayar da kai sun yi yawa me yake sanyawa har mutane ciwon sanyi zai yi masu wannan illar ba su nemi magani ba? Inda muka gane cewa akwai jahilci, akwai kuma kunya, akwai kuma talauci. Mutum ya kasa gane wurin wa zai je neman magani, in ma asibiti zai nema ya tafi wurin waxanda ba su qware ba, in kuma na gargajiya ne, ya ji wurin waxanda su kawai ‘yan kawai hau ka ci warke ne ba sanin ilmi suka yi ba. Haka kuma in wurin irin mu ne magani da maganganun da suka zo daga Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam, su ma ka ga mutum ya tafi wurin ‘yan jabu, waxanda su ma suna ji ne don wani na yi ba karanta suka yi da kyau yadda ya kamata ba, waxanda kamata ya yi su dinga sai da maganin ba wai su dinga aikin likitanci ba, ko kuma ko kuma ba wa mutum maganin ya kasa amfani da shi yadda ya kamata. Ko kuma a bashi maganin da ya fara amfani da shi ya ga ciwon ya fara sauqi sai ya yar da maganin, saboda haka sai ciwon ya dawo ya fi qarfin maganin, gashi nan dai da saurarnsu.

•Qasar da tafi amfani da lantarkin kogi Qasar Norway ita ce qasar da ta fi ko wace qasar duniya amfani da kogi wurin janyo wutar lantarki. Kashi 98 zuwa 99 na wutarta daga kogi take samar da makamashinta.

•Satar jarirai a Spain An tava sace jarirai kimanin 300,000 a Qasar Andulus (Spain) a tsakanin 1939 zuwa 1989. An zargi qungiyoyin likitoci da jami’an jinya na qasar da tafka aika-aikar. A wancan lokacin sukan faxa wa iyayen jariri ne cewa xansu ya mutu.

•Yankin da ya fi tara tsofaffi a duniya Yankin Tsibirin Okinawa na Qasar Japan shi ne ya fi ko wane yankin a doron qasa yawan tsofaffin da suka haura shekara 100 a duniya. Kuma an ce yankin shi ne mafi inganci muhalli mai lafiya a doron qasa


A Yau

Dausayin Musulunci 25

Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

Sayyid Isma’il Umar (Mai Diwani) 08051529900 (Tes kawai)

Girman Darajar Manzon Allah SAW (4) A uzu billahi minas shaixanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Wa sallallahu alan Nabiyyil karim. Assalamu alaikum warahmtullahi Ta’ala wa barkatuh. Masu karatu barkan mu da sake haxuwa a wannan makon Malam Alqadiy Iyad ya ce waxannan ayoyi na “Wannajmi” guda 18 sun tattare sanarwar Allah kan yadda ya tsarkake komai na Annabi (SAW). Allah ya sanar da mu a cikin waxannan ayoyin cewa ya tsarkake Manzon Allah baki xaya. Sannan ya riqa bin gavagava na Annabi yana magana a kai. Kuma Allah ya tsare Manzon Allah (SAW) daga aibi a wannan tafiya da aka yi. Duk abin da ya faxi a game da tafiyar gaskiya ya faxa. Allah ya tsarkake zuciyarsa (da take riqe abin da ido ya gani), ya tsarkake harshensa da dukkan gavvansa. Wurin tsarkake zuciya Allah ya ce zuciyar Manzon Allah (SAW) ba ta qaryata abin da ya gani ba, ma’ana ya san me ya gani. Da aka tambaye shi (SAW), ya ce “Na ga Ubangijina”, “Na ga Al’arshi” ya lissafa shimfixunta iri kaza, “Na ga Kursiyyu, na ga Rafrafu, na ga Aljanna, na ga wuta”, duk Hadisan Isra’i sun zo da bayanan waxannan. Allah ya tsarkake harshensa (SAW) da faxarsa cewa Manzon Allah ba ya furuci a bisa son rai sai an ma sa wahayi. Allah ya tsarkake idonsa da ya ga ayoyin da su a inda Allah ya ce “Idonsa bai kauce ba, kuma bai tsallake iyaka ba”. Yanzu misali muna ganin rana amma ba mu san ta ba. Idan mun iya rutsa idonmu muka kalle ta wani xan qwallo ne za mu gani da kore-kore a cikinta, aba ce ta wuta amma idonmu yana nuna mana kore ne a ciki. Wuta ce da ta ninninka ta duniya. Malaman sanin falaki (physics) sun ce girman rana ya ninninka duniya sau adadi da yawa amma sai ga shi idonmu yana nuna mana girmanta kamar qwallon qafa. Idan ka je gaban abin da ya ninka duniya yaushe za ka ga farkonsa ko ka ga qarshensa? Don haka har yau ba mu iya ganin rana ba. Amma idon Manzon Allah (SAW) ya riski abin da ake so ya gani. Akwai wani karatu mai zurfi a wajen. Allah Tabaraka wata’ala da hikimarsa ya faxa mana wani karatu. Manzon Allah (SAW) ya ya ce Allah ya yi wa Aljanna

fenti da abubuwan da muke qi (wahala, yawan ibada da sauran su), ka ga ba za mu yi kusa da ita ba kenan in ba don falalar Allah ba. Manzon Allah ya kuma ce Allah ya yi wa wuta fenti da abubuwan da muke so (varna, vata abubuwa), a nan sai mai hankali ne zai fahimci ya kamata ya kutsa wa wannan abubuwan da rai ba ya so don ya shiga Aljanna, ko ya haqura da wannan daxin na wajen wuta don ya kauce wa azabar Allah. Allah Tabaraka wata’ala shi ya kira Annabi (SAW) don ya yi Isra’i da shi ya nuna ma sa ayoyinsa manya. Kuma cikin Qudura ta Allah da Ibtila’i (Allah ya fi jarraba manya dama), maimakon Annabi (SAW) ya shige zuwa fadar Allah; sai ya ci karo da wata bishiya da aka yi wa ado (Manzon Allah ya ce ‘ya’yanta kamar Tulunan Hajaru, ganyenta kamar Kunnen Giwa dukkansu an musu ado da gwalagwalai) amma Annabi (SAW) kallonta ma bai yi ba saboda abin da yake gabansa (na ganin Alah) ya fi duk wannan. Sai Allah ya yabe shi da cewa “idonsa bai karkata ga duk wannan ba”. Haka nan ma a hanya, duniya ta kira shi amma Annabi duk bai kula da su ba. Allah ya kiyaye ya tsarkake ganinsa (SAW). A cikin wasu ayoyin kuma dai da Allah ya yi kirari ga Annabi (SAW) na cikin Suratut Tak’wiri, Allah (SWT) yana cewa “ina rantsuwa da taurari masu noqewa (idan sun kai qarshen buruji sai su koma farko, su ne guda biyar: Zuhal, Mushtariy, Mubriqu, Zahratu, Quxaritu. Su ma Turawa masu falaqi suna da sunayensu: Mars, Jupiter, Neptune da sauran su)”. Su ne waxannan taurarin masu tafiya suna faxuwa. Allah ya kuma ce “Na yi rantsuwa da dare idan duhunsa ya fuskanto”. “Na yi rantsuwa da asuba yayin da ta numfasa”. Idan dare ya take sai ka ji komai ya yi cik amma da Alfijir ya keto sai ka ji kamar an saki iska, hayaniyar abubuwa sun cika ko ina. Iska mai daxi da ake kira ‘Saba’ ta riqa tasowa, tsuntsaye su fara kuka. Don haka fitowar Alfijir kamar numfashin dare ne. Shi ya sa Allah ya ce ya rantse da asuba idan ta nunfasa. Jawabin waxannan rantse-rantse shi ne: wallahi “wannan Qur’anin maganar annabi ne mai girma a wajen Allah (ai mai girma wajen wanda ya aiko shi)”. Ba

Idan dare ya take sai ka ji komai ya yi cik amma da Alfijir ya keto sai ka ji kamar an saki iska, hayaniyar abubuwa sun cika ko ina. Iska mai daxi da ake kira

wai maganar Manzon Allah ake nufi ba, ana nufin wanda aka aiko ya kawo Qur’anin ga al’umma (Manzon Allah SAW), mai girma ne a wajen Allah. A nan ko mutane ba su ga girman Annabi (SAW) ba, to ya isar ma sa girman da yake da shi a wurin Allah. Kuma shi Annabi, “Ma’abocin qarfi ne a bisa isar da abin da aka xora ma sa na Manzanci”. Har a ranar Hajjin bankwana da ayar da ta cika shari’a (Shikashikan Musulunci) ta sauka, Manzon Allah ya ce wa al’umma “idan na koma wurin Ubangiji ya tambaye ku, me za ku ce? Shin na isar?” Suka ce “eh mun shaida ka isar”. Sai ya ce “Ya Allah ka shaida su da kansu sun shaida na isar musu”. Manzon Allah ya faxi haka har sau uku (SAW). A cikin surar, Allah ya cigaba da bayyana Manzon Allah (SAW) a matsayin “Mai tabbatacciyar daraja (matsayi) ne daga Ubangijinsa”. Ma’ana yana da xaukakar daraja a wurin Allah. “Abin bi ne (a sama) sannan amintacce ne (wurin isar da wahyi)”. Manzon Allah ya isar da Manzancinsa, bai qara ba; bai rage ba (SAW). Malam Aliyu Xan Isah (Malamin Tafsiri, Nahwu, Lugga da sauran su) mutumin Bagdad, Almajirin Ibn Duraid, ya ce Ma’aikin da ake nufi a wannan wurin (ayar) Annabi Muhammadu ne (SAW). Dukkan waxannan siffofi a bisa fassarar Malam Aliyu duk na Manzon Allah ne (SAW). Wasu Malamai kuma suka ce ayoyin suna magana ne a kan Mala’ika Jibrilu (AS). Idan aka tafi a wannan fassarar, to qarfin da sauran siffofin sai su koma wurin Jibrilu (AS). Allah Tabaraka wata’ala

ya cigaba da cewa “Haqiqa (Manzon Allah) ya gan shi (Mala’ika Jibrilu) a sasannin mahudar rana mabayyani”. Sai dai lamirin da aka yi amfani da shi a cikin ayar, wataqila an ce fassararsa “ya ga Ubangijinsa” ne. Sayyidina Abdullahi bin Abbas da wasu daga cikin Sahabbai (RA) suka ce Manzon Allah ya ga Ubangijinsa ne. Waxanda suka kafa hujja da maganar Sayyada Aisha (RA) kuma suka ce “ya ga Jibrilu” ne. Sayyada da ta ce Manzon Allah Jibrilu ya gani, amma ba cewa ta yi Manzon Allah ne ya faxa ma ta ba. Ijtihadi ta yi ta fassarar ayar “Ido bai riskar ganin Allah…”, idan Sahabi ya kawo abu, sai aka samu maganar Annabi (SAW) a kai, toh shikenan sai a karvi na Annabin. Akwai Hadisin da Manzon Allah (SAW) ya ce “na ga Ubangijina”, kun ga yanzu wannan ya warkar. Idan bai inganta ba (Hadisin), to maganar Abdullahi bin Abbas a kan Manzon Allah ya ga Ubangijinsa ta inganta. Idan aka samu Sahabbai biyu, wannan ya ce akwai; wannan ya ce babu, to sai a xora na wanda ya ce akwai a kan na wanda ya ce babu. Abdullahi bin Abbas ya tabbatar da cewa Manzon Allah (SAW) ya ga Ubangijinsa. Ya ce ai abubuwa ne guda uku. Annabi Ibrahim (AS) an bashi Badaxantaka, Annabi Musa (AS) an bashi – jin- maganar Allah, shi kuwa Annabi Muhammadu (SAW) sai aka haxa ma sa jin maganar da gani. Hadisai ne da yawa a wurin. Za mu dakata a nan sai Allah ya kai mu mako mai zuwa. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadiy wa ala alihi haqqa qadirihi wa miqdarihil aziym.


26 Mu Koyi Addini

A Yau

Fahimta Fuska tare da

Sheikh Ibrahim Khalil A aiko da tambaya ta waxannan imel: shafinfahimtafuska@yahoo.com ko nasirsgwangwazo@ yahoo.com ko kuma saqon ‘text’ ta wannan lamba domin Malam ya amsa tambaya: 08096972247.

Salam. Malam, don Allah ina so a yi min qarin bayani a kan wankan tsarki. Wankan tsarki shi ne, wankan janaba ko wankan jinin biqi ko wankan haila. A nan ana nufin kawai mutum ya wanke dukkanin jikinsa da ruwa, ya cuxa ko’ina da ina a kafatanin jikinsa shi kenan ya yi wankan tsarki. Idan wankan janaba ne dukkanin jikinsa zai wanke da ruwa kamar yadda yake yin wanka, banbancin kawai shi wannan ba wankan sabulu ba ne. Sannan za ka iya yi da shawa ko kuma ka shiga cikin ruwa ka wanke ko’ina a jikinka. Haka ita ma mace duk wankan iri xaya ne babu wani banbanci. Assalam. Malam, idan ana bin mutum bashi sai wasu suka kashe shi misali kamar ‘yan fashi, za a biya masa wannan bashin ne ko kuwa alhakin bashin zai koma kan waxanda suka kashe shi? A’a, ai idan mutum ya yi kisan kai abinda yake komawa kansa kaxai shi ne zunuban wanda ya kashe. Idan mutum ya yi kisan kai, zunuban wanda ya kashe za su dawo kansa, amma haqqin da wani yake bin sa na bashi, dole sai ya biya ko dai ‘yan’uwansa su biya masa ko kuma a lahira a biya masa da ayyukansa na alheri. Amma zunuban wanda aka kashe shi ne yake koma wa kan wanda ya kashe shi. Saboda haka, wajibi ne idan wanda ake bi bashi bai samu ya biya ba har ta Allah ta kasance ‘yan’uwansa ko iyayensa su biya masa. Babu maganar cewa don kashe shi a ka yi ko wani abu makamancin haka ba za a biya masa bashi ba, wannan nauyin na bashi yana nan a kansa tunda haqqi ne na wani. Maganar kisan da aka yi masa kuma wannan shi ma wani abu ne daban mai zaman kansa, ma’ana dukkanin zunuban da wanda aka kashe xin ya aikata, za su koma kan waxanda suka kashe shi kai tsaye. Assalam. Malam, don Allah ina so na san ko akwai Nassi ko Hadisi da ya halatta yin Mauludin. To, ala aiyu halin ita dai maganar Mauludi abu ne da aka fara yi shekaru dubu da suka gabata. Abin nufi a nan shi ne, an fara yin Mauludi a shekara ta xari huxu da wani

abu bayan hijira, don haka yanzu kimanin shekaru dubu kenan. Don haka abinda nake so a fahimta a nan shi ne, da wanda ya ce a yi Mauludi da kuma wanda ya ce ka da a yi, babu wani wanda ke da nassi ko nadisi, kaxai kowannen su ya ginu ne a kan wata fahimta tasa, amma ba nassi ko nadisi ba. Wani fahimtarsa da qur’ani da hadisi da waxansu qa’idoji da kuma wasu dalilai ne yasa yake ganin bai kamata a yi Mauludi ba, wasu kuma fahimtarsu da qur’ani da hadisai da wasu qa’idoji ne yasa suke ganin ya halatta a yi Mauludin. Saboda haka, kowannan su a kan fahimta ne domin kuwa da akwai nassin da ya bayyana cewa a yi Mauludin da tuntuni rigima ta qare, haka da akwai nassin da ya ce kada a yi Mauludin, nan ma da tuni rigimar ta qare. Misali, tunda Sallah Allah ne ya ce a yi ta, babu wata rigima a kan ta, haka tunda giya Allah ne ya haramta shan ta, nan ma babu wata rigima a kan shan ta, amma duk mas’alolin da babu nassi a kan su cewa a yi ko kada a yi, kowane vangare zai dogara ne da tunaninsa da kuma fahimtarsa. Don haka, wanda yake yin Mauludi bai kamata ya qyamaci ko ya furta kakkausan lafazi a kan wanda ba ya yi ba, shi kuma wanda ba ya yi shi ma bai kamata ya faxi kakkausan magana ko lafazi a kan wanda yake yi ba. Wannan shi ne abin da ya kamata, ma’ana dai kowa ya yi qoqarin tsayawa a matsayinsa. A taqaice dai, wanda yake yin Mauludi ba za a zo a hana shi dole ya daina yin Mauludin ba, wanda kuma baya yin Mauludin ba za a sa shi dole ya yi Mauludin ba. Amma da zarar wani ya fahimci wani ya fi shi hujja, shi kenan sai ya sakar masa babu wani abin tashin hankali. Saboda haka bai kamata wani ya yi wa wani gani-gani ba tunda dukkanin su a kan fahimta suke babu wani mai nassi ko hadisi. Sai dai da yake xabi’a ta xan Adam, duk lokacin da ya xauki wani tunani ko fahimta, yana fifita ta a kan wata ne. Kamar jam’iyyar siyasa ce ko sayan tufafi ko abin hawa, duk lokacin da mutum ya zavi wani abu da ya yi masa, to yana fifita shi ne a kan wanin sa.

Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

Mufti Menk Hanyoyi 22 Na Tarbiyyantar Da Matasa A Musulunce (1) Fassarar Bello Hamza An bijiro da maganganu ga iyaye da Malamai da sauran jama’a da suke da yara matasa a qasashen Turai a kan hanyoyi da za a xauka wajen taimaka musu tabbatuwa a kan addininsu, qa wasu shawarwari. 1: Iyaye su xauki tarbiya da muhimamci, abin nufi uwa da uba su sani cewa, ‘ya’ya amana ne gare su daga Allah kuma Allah Zai tambayesu yadda suka tarbiyantar da ‘ya’yan nasu, in har ‘ya’ya suka kasa yin addini yadda ya kamata saboda sakacin iyaye, lamarin ba zai yi kyau ba ga yaran da iyayen a nan duniya da gobe kiyama. 2: Rage tsawon lokuttan zama a wurin aiki ko kuma canza tsarin kasancewa a wurin aikin saboda samun daman kasancewa tare da iyali. Ya fi alfanu a riqe aiki qwaya xaya na din-din a kuma rage kayan alatu a cikin gida domin samar da lokacin kasancewa tare da iyali, wannan ga iyaye mata da maza ne, maimakon qarin aikin Asabar da Lahadi a yi amfani da lokacin wajen zuwa da yara masallaci da ziyarar sada zumunci. 3: Karatun Alkurani da fahintar ma’anarsa na tsawon aqalla minti 5 a kullum. Minti biyar kacal, ko a cikin mota in ana samu goslow ko lokacin sallar asuba ko kuma kafin ka kwanta da daddare, ka karanta Alku’ani tare da fassasara to lallai za ka samu qarin kusanci ga Allah za ka kuma zama abin koyi ga yaranka, su ma zasu samu kusanci ga Allah. 4: Halarta Tarukan Addini Ka musanya wassanin karta da kalon talabijin da zuwa tarukan addini a ranakun Asabar da Lahadi, idan har babu wani shirin taron addini a wannan

Wannan shi ne abin da ya kamata, ma’ana dai kowa ya yi qoqarin tsayawa a matsayinsa

lokacin,ka haxa hannun da Limamin unguwanku wajen shirya wa ka kuma tabbatar ka kasance na gaba-gaba a halartar tarukan, alfanun wannan shi ne in yara suka ga iyayensu na qoqarin fahintar addini ya na qarfafa su akan suma su rungumi neman sanin addinin. 5:Ka mutunta ‘ya’yanka matasa Mutunta matasa daga cikin‘ya’yanka na nufin kada ka rinqa hulxa da su kamar ‘yan qananan yara ta hanyar daka musu tsawa ko zagin su, abin nufi a rinqa sa su cikin harkokin gudanar da gida ta hanyar neman ra’ayoyin su, hakan yana da muhimmanci. 6: Ka sa hankali a kan abin da suke yi. Ka lura da ka kuma sa ido a kan dukkan wassani ko aiyukan da yaranka ke yi tare da taimaka musu da kuma basu shawara a in da ya kamata, hakan zai qarfafa su ya sa su samu nasara a kan abin da suke yi. 7: Ka lura da matsaloli ka kuma yi maganin su kai tsaye. A yayin da ka qara kusantar matasan ‘ya’yan ka zaka iya fahinta in akwai abin da ke damun su, in har akwai kada a kawar da ido ka yi maganinsa kai tsaye ba a cikin mutane ko gaban sauran yaran ba amma a qeve. 8: Ka samu lokacin Qeve wa da matasan ‘ya’yan ka A na danganta qevewa a matsayin wani abu tsakanin saurayi da budurwa amma ka na iya xaukar wannan salon domin qara neman kusanci tsakanin yaranka musamman in sun samu wani nasara a bin da suke yi ko sun kai wani matsayi a harkokin karatun su, matasan yaran ka su ma na buqakatan kulawa da shiryar wa, hakan kuma zai qara kusanci tsakanin ku, zai kuma basu dama namayar da abin da ke damun su.

A yayin da ka qara kusantar matasan ‘ya’yan ka zaka iya fahinta in akwai abin da ke damun su, in har akwai kada a kawar da ido ka yi maganinsa kai tsaye ba a cikin mutane ko gaban sauran yaran ba amma a qeve


A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku

Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku

Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.

Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com

TALLA 27


28

WASIQU

A Yau

Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439) 08034980391 08069824895 leadershipayaujumaa@gmail.com

Duk abin da aka bayyana ba ra’ayin LEADERSHIP A YAU ba ne, ra’ayin waxanda suka aiko da saqonnin ne.

‘Sako ‘Yan Matan Dapchi: Sai Bango Ya Tsage…’ Tun bayan dawo da ‘yaran makaranta da ‘yan Boko-haram suka yi awun gaba da su makwanni da suka wuce a garin Dapchi da ke jihar Yobe, mutane sun yi ta bayyana fahimtarsu, wasu na qorafi, wasu na zargin hanun gwamnati, wasu na farincikin sako yaran. Tambayoyi ko ta ina. Daga cikin tambayoyin jama’a akwai: “Wane ne ya sace yaran matan? Mene ne aka biya kafin aka sako yaran matan? Ministan yaxa labarai ya ce qarfe 3am (dare) aka sako yaran, amma kuma mazauna garin sun ce da safiya ne. Yaushe ‘yan Boko-haram suka tava sakewa da jama’a da har za su yi musabiha da ‘yan gari? Yaya aka yi har ‘yan Boko-haram suka dawo da yaran matan babu jami’an tsaro da suka kama su? “Idan kuma ‘yan Boko-haram xin ba a biya su komai ba, to mene ne dalilin da ya sa suka sako yaran matan? Idan saboda yaran Musulmi ne, ai sun sha kama Musulmi su qi sake su. Mene ne dalilin sako yaran matan? Me ya sa gwamnatin Nijeriya ba ta fito ta yi bayani filla-filla game da sace yaran matan ba?” Na san akwai tambayoyi da yawa, kuma kowanne na buqatan amsa. Amma zan so farawa da jaddada farin cikina ga Allah da ya dawo da yaran lafiya, da kuma jinjina ga gwamnatin shugaban qasa Buhari da duk wanda ya qoqarta wajen sako su. Babu wani abin farin ciki game da lamarin nan fiye da dawowarsu. Sannan ina so masu tambayoyi su ma su yi wannan farin ciki. Kowani xan’adam yana da fahimta da Allah yai masa. Kuma kowa yana faxin abu ne a bisa yadda yake gani. Ina nufin fahimta fuska ce, kowa da irin tasa. Wannan ya sa komai za ka faxa, kowa da yadda zai fahimce ka. Sannan kuma fahimta tana da alaqa da ilimi. Ma’ana, fahimtar mutum dangane da abu ya danganta ga ilimin rayuwa da yake da shi, ko kuma sabuwa da wannan abu, wanda shi ne za mu iya cewa ilimin wannan abu. A fahimtata, lokacin da aka sace ‘yan matan Dapchi mutane ba su tada jijiyoyin wuya kamar yadda yanzu suka tayar da aka sako su ba. Wannan kuma ko dai yana nufin mutanen da suke tada jijiyoyin wuya yanzu a lokacin da aka sace yaran matan hakan ya burge su, amma sako yaran matan ya musu zafi saboda ba sa so su yaba qoqarin gwamnati a kai, ko kuma suna ganin cewa gwamnati ba ta da qoqarin da za ta ingiza Boko-haram ta dawo da yaran nan. Ko ma wanne ne daga cikin fahimta biyun nan mutum ya xauka hatsari ne ga dukkanmu ‘yan Nijeriya. Idan ka ce kana farin ciki don an sace ‘yara qarqashin gwamnatin APC, kuma kana jin zafin an sako su saboda kai a ganinka sace yaran matan ya sa gwamnatin APC ta yi kama da ta PDP, to kana da matsala a fannin fahimta. Ina nufin tushen fahimta, wato ilimi. Jahilcinka ya rufe fahimtarka. Idan kuma ka ce kana gani gwamnatin Nijeriya ba ta da wata bajinta da za ta iya yi har ‘yan Boko -haram su sako yaran matan nan, to kana da matsala saboda ka yanke qauna ga gwamnati. Masu nazarin fasahar Xan’adam suka ce duk lokacin da mutum ya yanke qauna (hope), to basirarsa na aikata daidai a wannan abun da ya yanke qauna ya tafi. Ka ga kana da matsala ke nan.

• ‘Yan matan Dapchi da aka sako A fahimtata, babu abun farin ciki da ya kai dawowar yaran matan nan cikin aminci ga iyayensu. Ina da qanne ‘yan makarantar Sakandire, ba na tsammanin bayan an sace su, idan aka dawo da su zan tsaya qalubalantar gwamnati da tayi ruwa ta yi tsaki (bisa dukkan alamu) a kan dawo da yaran. Idan da haka ne gwamnatin da ta gabata ta yi, to da ba mu daxe muna jimamin sace yaran matan Chibok ba. A fahimtata, (ina yawan maimaita fahimta saboda muna magana ne a kan fahimtar): Bai kamata mu qalubalanci gwamnati a kan sako yaran matan Dapchi ba. Abun da ya kamata mu qalubanaci gwamnati a kai shi ne sace yaran da aka yi da ranar Allah, ido na ganin ido. Aka tafi da su zuwa waje mai nisa. Jaridar Premium Times ta ruwaito hirar da wakilinta ya yi da xaya daga cikin yaran matan. Yarinyar ta ce “Sun shigo suna harbin bindiga, suka ruxa mu, sai wani ya ce mana mu zo ta qyauren makarantar mu same shi. Sai aka kawo manyan motoci aka saka mu a ciki. Aka yi ta doguwar tafiya da mu, kafin aka tsaya, suka tambaye mu su waye suke azumi, suka bai wa masu azumi Maltina da nama. Sai muka yi sallah kafin muka cigaba da tafiya. “Mun cigaba har muka kai wani wuri da ke da manyan itatuwa, sai muka tsaya, suka saka mu muka dafa abinci, bayan mun ci abinci sai muka cigaba da tafiya…” inji yarinyar. Wannan yana nuna ba Aljanu ne aka yi amfani da su wajen safarar yaran ba, mutane ne, kuma ba wai daji aka dugunzuma da su a kan dawakai ba, a cikin motoci aka fita da su, kuma ana tsayawa cin abinci da sallah, duk a cikin Nijeriya, amma a ce jami’an tsaro su kasa damqe su. Wannan shi ne abun tambaya ba sako yaran matan ba. Daga qarshe, ina jinjina wa gwamnati kan rawar da ta taka wajen sako yaran matan, sannan kuma ina kira ga shugaban

qasa Muhammadu Buhari da ya qara inganta harkar tsaro a jihohin da suke fama da wannan ta’addanci, ta hanyar yalwata makaman yaqi na zamani da kuma a qarfafa hukumar bayanan sirrin (intelligence department). Saqo daga Mahmud Isa, Yola. 08106792663. Dawowar ‘Yan makarantar Daphchi Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. haqiqa mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana qaiqayi a rai tare da isar da saqon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar qasa. Muna muku addu’ar Allah ya qara muku hikima da basirar aiki da kuma bunqasar wannan jarida mai farin jinni baki xaya. Maimakon mu yi Sujudu Shukur ga Allah a kan amsa mana addu’o’inmu da yayi na dawowar ‘yan matan makarantar sakandare na garin Daphci da aka sace a kwanakin da suka gabata, amma sai muka kama surutai marar kan gado da sharhi kala-kala. Mai makon mu taya iyayen yaran murnar dawowar xiyan su, sai wasu suka vigewa da surutai marar kan gado, wasu ma qoqarin suke yi su danganta Gwamnatin Baba Buhari da laifin, wasu kuma sun mai da shi qabilanci, kai sharhi kala-kala a dandalin sadarwa na zamani. Amma abun murna da godiya a wurin Allah shi ne yanzu haka ana bincikar lafiyarsu domin hannunta su ga iyayensu. Fatan mu da muke a koda yaushe shi ne Allah ya qara tsare mu da tsarewarsa, kuma ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari jagora da nasara a wannan mulki nasa amin summa amin. Saqo daga Uwaisu Bahari Imam, Sakkwato. 07064756693 Sulhu Da ‘Yan Boko Haram

Salam LEADERSHIP A YAU Juma’a, ni dai ra’ayina shi ne maganar da shugaban qasa ya yi na cewa zai yi sulhu da ‘yan Boko-haram. Tabbas shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi tunani mai kyau da ya ce zai yi sulhu da ‘yan Boko-haram. Ya kamata al’ummar Nijeriya su fahimci cewa son zaman lafiya ne da cigaban qasa da kuma al’ummar qasar nan ne ya sa shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ke son yin sulhu da ‘yan ta’addan na Boko-haram. Lallai tawaye ya kassara NIjeriya. Shin ko kun san adadin dukiya da ta’addancin Boko-haram ya salwantar a yankin Arewa maso Gabas kawai? Toh a halin yanzu dai Nijeriya ta yi hasarar sama da Naira miliyan dubu 2.6 a Arewa maso gabas kawai. Ya kamata a inganta albarkatu da ma’adanan Nijeriya wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, sai dai tawaye daban-daban ya maida Nijeria wani xan qaramin filin yaqi da ake fafatawa. Yaqi na siyasa, qabilanci da kuma rikicin addini sun sa Nijeriya ta koma baya. Yana xaya daga cikin Alqawarin da shugaban Nijeria Muhammadu Buhari yai ma al’ummar qasar nan lokacin yaqin neman zaven 2015, shi ne samarda zaman lafiya mai xorewa a faxin Nijeriya baki xaya. Tabbas yin sulhun shi ne zai qara dawo wa Nijeriya cikekken zaman lafiya da cigaba mai xorewa. Tabbas duk qasar da ke fama da tashin tashina, za ka same ta cikin qasashe marasa cigaba domin da zaman lafiya ne ake samar da kumai. Amma maganar sulhu ita tafi dacewa tsakanin gwamnatin Tarayyar da qungiyar Boko-haram. Dominwa ko Allah yana son a yi sulhu tsakanin jama’a. Sannan mu al’ummar Nigeria mun yarda a yi sulhu tsakanin gwamnati da ‘yan Boko-haram in har za su yarda da umarnin gwamnati. A qarshe ina roqon Ubangiji Allah ya tabbatar da alherin da ke cikin wannan sulhun amin. Saqo daga Malam Abdullahi Mai Kano. 08026441039


A Yau

Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

TALLA 29


30 TALLA

A Yau Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”

Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.


Wasanni A Yau Juma'a 30.3.2018

Argetina Ku Gode Allah Da Ya Ba Ku Messi, In Ji Costa Xan wasan gaba na qungiyar qwallon qafa ta Atletico Madrid, xan qasar sipaniya, Diego Costa, ya bayyana cewa ‘yan qasar Argentina su godewa Allah da Allah ya yi Messi xan qasar ne saboda babu kamarsa. Tawagar qwallon qafa ta Spaniya ta doke ta Argentina da ci 6-1 a wasan sada zumunta da suka kara a ranar Talata a qasar Sipaniya Spaniya ta ci qwallayen ne ta hannun Diego Costa da Thiago Alcantara da Iago Aspas da kuma Isco

wanda ya ci uku rigis a wasan da ya kwashi ‘yan kallo. Ita kuwa Argentina wadda Messi bai buga mata fafatawar ba, ta ci qwallo ne ta hannun Otamendi xan qungiyar Manchester City tun kafin a tafi hutun rabin lokaci. Spaniya tana rukuni na biyu a gasar cin kofin duniya da ya qunshi Iran da Morocco da kuma qasar Portugal wadda Cristiano Ronaldo yake jagoranta. Argentina kuwa tana rukuni na

huxu da ya haxa da Iceland da Croatia da kuma Nijeriya a gasar ta cin kofin duniya. Costa ya ce ba kowacce qasa ba ce take da xan wasa kamar Messi kuma xan wasa ne wanda bai kamata a dinga sukar sa ba ko da kuwa ba ya qoqari saboda kasancewar sa a cikin fili ma wani abu ne. A qarshe ya ce Messi xan wasa ne mai nasara kuma idan yana cikin qungiya to tabbas ana sa ran abin arziqi.

United Ke Kan Gaba Wajen Neman Seri Wani mai sharhi a kan qwallon qafa na kamfanin ESPN da ke qasar Spaniya, Moreno, ya bayyana cewa qungiyar qwallon qafa ta Manchester United ce a kan gaban Manchester City wajen neman xan wasa Seri daga qungiyar Nice ta qasar Faransa. qungiyoyin biyu dai suna gwabzawa

wajen neman xan wasan tsakiyar mai shekara 26 wanda ya bugawa qungiyarsa wasanni 22 a wannan kakar, kuma ya zura qwallo xaya sannan ya taimaka aka zura qwallaye guda biyar. Ya bayyana cewa, duk xan wasan da ake haxa shi da xan wasan Chelsea,

N’Golo Kante, dole qungiyoyi su yi rububin sa, saboda haka, Seri ana danganta shi da Kante, kuma ya na buga wasa irin na sa saboda haka manyan qungiyoyi za su so su same shi. Ya ci gaba da cewa, Manchester United dole tana buqatar xan wasa irin sa, amma Manchester City idan ba ta same shi ba ba ta da matsala, saboda qarfin qungiyar da kuma yanayin yadda suke buga wasa ba sa buqatar xan wasa irin sa a dole. Ya qara da cewa, hakan yana nufin dole Manchester United sai ta nemi xan wasan saboda wasu daga cikin ‘yan wasan ta na tsakiya da suka haxa da Machael Carrick da Maroune Fellani za su bar qungiyar a qarshen kaka. Seri, xan asalin qasar Ivory Coast, ya koma qungiyar Nice ne tun a shekarar 2015.

31

Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com

‘Abokin Wasan Qarshe Kawai Madrid Ke Jira A Gasar Zakarun Turai’ Tsohon xan wasan qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid, Christian Karambue, xan qasar Faransa, ya bayyana cewa yanzu maganar da ya kamata a yi shi ne da wa Real Madrid za ta buga wasan qarshe a gasar zakarun Turai domin babu qungiyar da za ta iya taka mata burki. Karambue ya ce, idan aka kalli yanayi da girman kowacce qungiyar da take buga gasar zakarun turai a yanzu tabbas babu mai qarfin qungiyar Real Madrid kuma ita ce qungiya xaya tilo da za ta iya doke kowace qungiya. Ya ci gaba da cewa, duk da cewa akwai qungiyoyi irin su Real Madrid da Barcelona da Bayern Munchen da Manchester City a gasar amma kuma idan ana maganar gogewa babu kamar Real Madrid kuma za su iya doke kowace qungiya. A qarshe ya ce, yanzu a daina maganar wasan kusa da na kusa da na qarshe, ko kuma wasan dab da na qarshe kawai a fara tunanin da wace qungiya Real Madrid za ta haxu a birnin Kiev na qasar Ukrain domin buga wasan qarshe. Karambue dai ya koma Real Madrid ne daga qungiyar Sampdoria a shekara ta 1997 inda ya shafe shekaru uku kafin daga baya kuma ya koma qungiyar Middlesbrough da ke qasar ingila.


30.03.18

AyAU LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

JARIDAR HAUSA

LeadershipAyau

Juma’a 30 Ga Maris, 2018 (12 Ga Rajab, 1439)

MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA

Bugu na: 029

N150

WASANNI

United Ke Kan Gaba Wajen Neman Seri > Shafi na 31

Kada A Ci Moriyar Ganga A Alqalami Mance Da Kwaure!

Dr. Ibrahim Shehu Liman

Assalamu alikum, tare da fatan alheri ga xaukacin jama’a. Muna kuma jinjina ga ma’abota bibiyar gudunmuwar da Alqalaminmu ke bayarwa a wannan shafi na jaridar Leadership A Yau Jumu’a. A kowane zamani, tun daga waxanda suka shuxe har wanda muke ciki, mai yiwuwa ma da ma waxanda ake hasashen zuwansu, a kan sami wasu fitattun mutane, da ake laqaba musu sunaye na yabawa da matsayinsu da kuma gudunmuwarsu wajen kyautatawa da kuma ciyar da al’ummominsu gaba. Ire-iren waxannan laqabi sun haxa da ‘gwanaye, ‘yan-baiwa, jarumai, haziqai, fasihai, zaqaqurai, zakaru da jajirtattu.’ To kuma a gefe xaya sai a ci karo da abintakaici, inda duk da irin ficen da waxannan jarumai suka yi, sai a tarar ba’a taskace duk bayanan da suka shafe rayuwarsu da ficen nasu ba, haka kuma, a kan samu wasu da suka yi tsawon rai, amma sai a qyale su ba tare da agaza musu a wannan lokaci da suka gajiya ba. Anya haka za a ci gaba da cin moriyar ganga, a mance da kwauren? Daga sharar fagen da muka yi, zurciyar kowa za ta harao irin waxannan fitattun mutane da dama. Ganin abin ya zama da yawa, bari mu waiwayi inda muke da ‘yar masaniya, wato fagen masu fasaha kan adabin Hausa, inda ake da shahararrun marubuta da shiryawa da kuma aiwatar da wasannin kwaikwayo na Hausa. Mun yi haka ne ba domin a wannan fage ne kaxai ake samu mashahurai ba, sai dai don a samu sandar dogarawa wajen bayar da misalai. Bari mu kawo sunayen wasu fitattun da ke hajar tallata wa duniya a fagen na wasan kwaikwayo, sannan mu tambayi kawunanmu, ko an yi abin da ya kamata gare su don yabawa da kuma

(08023703718) ibrahimshehu781@yahoo.com

samar da madubi ga sauran al’umma. Fitattun sun haxa da Alhaji Shu’aibu Maqarfi, Alhaji Adamu Gumel, Malam Muhammadu Ango Zaria, Alhaji Idi Jibrin Jos, Alhaji Yusufu Ladan, Alhaji Usman Baba Pategi, Alhaji Qasimu Yero, Alhaji Umaru Xanjuma Katsina, Alhaji Sani Gwarzo, Alhaji Bashir Isma’ila Ahmed, Alhaji Umaru Kwantagora, Alhaji Mainasara Idris da sauransu. Waxannan misalai da muka kawo kaxan ne, kuma idan aka waiwayi fagen masana, masu nazari da kuma tarken wannan fagen adabi, su ma suna nan da tarin yawa. Amma zamu taqaita ne kan marubuta da shirywa da aiwatar da wasannin kwaikwayon na Hausa kamar yadda muka ambata a baya. Wajibi ne fa kada a yi sake waxanda Allah ya yi wa baiwa iri-iri su rayu har su bar duniya ba tare da an tattara ayyukansu na basira an tsarasu tare da yin gamsassun bayanai da sharhi yadda za a daxe ana cin moriyarsu. Bari mu xan waiwayi sunayen da muka ambata, mu yi wasu ‘yan tambayoyi a kansu, da fatan hakan zai zama matashiya, kuma hannunka mai-sanda Ko mai karatu zai iya tunawa da marubucin littafin Jatau Na Kyallu da Zamanin Nan Namu, wato Alhaji Shu’aibu Maqarfi? Ko za aiya tunawa da mashiryin wasan Dagurasa, Alhaji Adamu Gumel a gidan Rediyon NBC? Ko za a iya tunawa da Malam Muhammadu Ango Zariya mashiryin wasan Jami’ar Jatau Na-Albarkawa? Ko za a iya tunawa da Alhaji Idi Jibrin Jos, mashiryin wasan Samanja Mazan-Fama na farko a tashar talabijin na RTK, Kaduna? Haka nan ko za a iya tunawa da Alhaji Yusufu Ladan, marubuci kuma mashiryin wasannin Zaman Duniya Iyawa

• Alhaji Yusufu Ladan, Xan-Iyan • Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja/ Baba Samanja) Zazzau

Ne, Basafce Xan Malam Dogara, Gundumi Fasa-Kwanya Zangayi da sauransu? Ko za aiya tunawa da Alhaji Usman Baba Pategi a wasannin Samanja MazanFama da Duniya Budurwar Wawa? Wani gwarzon da shi ma ake bukatar waiwayensa shi ne Alhaji Qasimu Yero a wasannin Mgana Jari Ce, Karambana, Tumbin Giwa da sauransu. Sai Alhaji Umaru Xanjuma Katsina da ke fitowa a matsatyin babban tauraro a wasan Kasagi, haka nan shi ne marubucin littafin Kulva na varna. Shin kuma za a iya tunawa da Alhaji Sani Gwarzo, wato Tumbuleqe a wasan Duniya Gidan Kashe Ahu na NTA Kaduna, Wasu jaruman da in dai ba vatar basira ba, bai kamata a ce marubuta da masu nazari sun kawar da kai daga gare su ba. Waxannan sune Alhaji Bashir Isma’ila Ahmed, wanda shi ne Basafce xan Malam Dogara mai Karen kamun kura a wasan Basafce na Alhaji Yusufu Ladan. Shi ne kuma Gundumi a wasan Gundumi FasaKwanya na Alhaji Yusuf Ladan. Haka nan akwai Alhaji Umaru Kwantagora da ke fitowa a matsayin Sanqira a wasan Duniya Gidan Kashe Ahu. Haka kuma, ko masu kallon NTA

Kaduna, musamman a wajajen shekarar 1980. Ko za a iya tunawa da Oga kuma abokin karawar Samanja Usman Baba Pategi? Shi wanan shugaba na Samanja, Ci-O (C/O) shi ne Alhaji Mainasara Idris. To alqalaminmu ya tsakuro mana waxannan gwarzaye, akwai kuma makamantansu da ba a ambata ta ba. A mako mai zuwa zamu tambayi marubuta da manazarta da cewa wai za a yi sakaci ne, idanuwa da zukata, da qwaqawale da hannuwan da ke riqe alqalumma su rasa katavus?

Babba Da Jaka Gwamnati ta mayar da darasin tarihi a makarantu - Labarai

Ka ga yara za su san mahandaman da suka nemi wa’adin mulki na uku!

Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 08039216372 Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 01-8963459. E-mel:leadershipayaujumaa@gmail.com


Turn static files into dynamic content formats.

Create a flipbook
Issuu converts static files into: digital portfolios, online yearbooks, online catalogs, digital photo albums and more. Sign up and create your flipbook.