3.4.18
AyAU Talata
LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa
JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA
www.leadershipayau.com Leadership A Yau
3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
LeadershipAyau
No: 117
N150
Sunayen Mutanen Da Ake Zargi Da Satar Kuxin Gwamnati Daga Umar A Hunkuyi
Gwamnatin tarayya ta qara sakin wasu sabbin sunayen na mutanan da ake zargi da tsiyata lalitar qasarnan, a zamanin mulkin tsohon Shugaba Godluck Jonathan. Ministan yaxa labarai, Lai Mohammed, ne ya bayyana
sunayen, ya kuma zargi Jam’iyyar adawa ta PDP, a bisa martanin da ta yi wa sunayen farko da gwamnatin ta saki. Sabbin sunayen da Ministan ya shelantawa duniya guda 23 ne. Gwamnatin ta tarayya ta ce, sunayen mahandaman da ta saki tun da farko, an tabbatar da su ne,
gami da bayyana yawan kuxaxen da suka handama, lokaci da kuma wajen da suka yi satan. Da yake bayyana sabbin sunayen mahandaman, a wani bayanin da ya fitar a Legas ranar Lahadi, Lai Mohammed, ya ce, masu qorafin sunayen farkon da aka saki sun yi kaxan, ba su fahimci dubarar da
ake yi ba ne wajen sakin sunayen a matsayin xanxano. “Ai ko a lokacin da na saki sunayen na farko, na ce wannan somin tavi ne, amma ai gwamnatin tarayya tana da dogon jadawalin sunayen mahandaman a hannunta.
>Ci gaba a shafi na 5
Zamfara:
Har Yanzu Ana Tsinto Gawarwaki A Daji 4
Boko Haram Ta Kashe Mutum 28 A Borno Daga Muhammad Maitela, Maiduguri
Aqalla mutum 28 ne suka rasa rayukan su, inda wasu qarin wasu mutum 55 suka samu raunuka daban-daban, a wani sabon farmakin da mayaqan qungiyar Boko Haram suka kai a qauyen Bale, wanda ya ke kusa da Maiduguri, babban jihar Borno. An kai harin ne da kimanin qarfe 8:00 na daren ranar lahadi. Bayanai sun bayyana cewa an xauki awanni ana jin qarar harbe-harben bindiga masu sarrafa kan su da qarajin tashin abubuwa masu fashewa-babu qaqqauta wa, bayan babban birnin jihar. Wata qwaqqwarar majiyar tsaro ta tsegunta wa kamfanin dillacin labarai na Nijeriya (NAN) kan cewa wasu ayarin mayaqan Boko Haram ne suka dumfari qauyukan BaleShuwa da Bale-Kura, waxanda da ke kusa da Maiduguri, a yunqurin su na kutsa kai cikin birnin, Dan misalin qarfe 8:00 na daren. • Al’ummar garin Anka yayin da suke haqa qaburburan da za su bizne gawarwakin da aka tsinto daga dazuka.
>Ci gaba a shafi na 2
Dole Mu Qarfafi Matasa Su ‘Noma Ne Ya Ceto Nijeriya Daga Karayar Tattalin Arziki’ Karvi Shugabanci –IBB > Shafi na 6
> Shafi na 14
2 LABARAI
A Yau
Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Boko Haram: An kashe Mutum 28 A Borno Ci Gaba Daga Shafin Farko
Majiyar ta ci gaba da bayyana cewa, mayaqan sun ajiye motocin su, daf da wurin da ake binciken abababen hawa, na jami’an tsaro, wanda hakan ya basu damar shiga qauyukan. “ankarar jami’an tsaro ke da wuya shi ne suka mayar da martani tare da varin -wuta a tsakanin su da mayaqan waxanda suka rinqa kai kora ta hanyar tayar da ababe masu fashewa da harbin xauki ba daxi”. Inji majiyar. “halin da ya sabbaba gomman jama’a da dama, waxanda suka qunshi mata da qananan yara suka samu munanan raunuka, ta dalilin tashin bama-baman tare da harbin kan-mai-uwa da
wabi”. “kuma da yake akwai tsananin duhun dare, halin da ya sa ba a samu zarafin xauke gawawakin waxanda suka rasu da wuri ba, saboda daga cikin maharan akwai waxanda suke xauke da jigidar bama-bamai a jikin su.” Ya nanata. Har wala yau kuma, shi ma kwamandan tsaro ta ‘Lafiya Dole’, Manjojanar Rogers Nicholas, ya musanta bayanin cewa akwai waxanda suka rasu a cikin wannan harin- walau soja ko jama’ar gari. A cikin bayanin martanin saqon kar-ta-kwana wanda ya aika wa kamfanin dillancin labarai na NAN, ya bayyana cewa yan qungiyar
Boko Haram ne aka hallaka a cikin harin. “Ba gaskiy bane. Akwai harin da aka kawo kuma mayaqan sun gamu da zazzafar turjiya, wanda kuma zaratan sojan Nijeriya suka hallaka Boko Haram a lokacin”. “har wa lau kuma, mayaqan Boko Haram xin sun zo da jigidar bamabamai wanda kuma suka tarwatsa kawunan su da ita, a sa’ilin da suke gujewa martani da sojojin mu suka maida musu- a wasu qauyukan da suke maqwabtaka da Maiduguri, kuma wannan ya jawo mutane 14 sun samu raunuka ta dalilin tashin bam”. Inji shi. • Wasu waxanda suka tsira daga harin da Boko Haram ta kai shekaran jiya a Borno
Gwamnatin Jihar Sakkwato Ta Xauki Matasa 1500 Aiki Don Bunqasa Harkar Noma Daga Bello Hamza
Gwamnatin jihar Sakkwato ta bayyana cewa, a halin yanzu ta xauki matasa 1500 aiki domin su qara bunqasa domin kawo ci gaba a fannin samar da abinci da shuka abubuwan da za a siyar a kasuwannin duniya. Darakta a ma’aitan matasa da wasanni, Malam Muhammad Sarki ya yi wannan bayanin a Sakkwato a taron qara wa juna sani dake gudana wanda qungiyoyin “civil society legislative advocacy centre (CISLAC) dana “Farms And Infrastructure Foundation (FIF)” suka xauki nauyin gudanar wa. Muhammad y ace, baya ga samar da abinci, shirin
• Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal.
zai samar da aiyukan yi ga matasa. Tun da farko, wakilin FIF Miata John Ogbodo y ace, taron na da matuqar mahimmanci ne saboda
qaruwar da ake samu na jama’a ba tare da samun qaruwa ba a vangaren abinci da kuma samun su kan farashi mai sauqi tare da kuma da rashin
kyakyawan tsare-tsare daga gwamnati. Ya qara da cewa, dokan tabbatar dahaqqin xan qasa nay a samu abinci ya shiga mataki na biyu a majalisar qasa, a kan haka ne ya buqaci dukkan maus ruwa da tsaki das u bayar da goyon bayan su domin samun nasarar zartasa da wannan dokar. Daga nan ya buqaci a qara ba mata da matasa daman shiga harkokin aikin gona domin samun qaruwar abinci said ai y ace, mata da yara ne a halin yanzu suka fi shuga wahala sakamakon rikicr rikicen manoma da makiyaya saboda haka ya kuqaci gwamnati da ta kawo xauki domin a samun nasarar cimma burin samarvda abinci ga ximbin
mutanen mu. Mista Ogbodo ya yi kira ga majalisun dokoki na jihohi das u gaggauta zartasa da dokan samar da abinci da ke gaban majalisar dokoki ta qasa domin samun cikakken nasarar yaqi da yunwa a faxin Nijeriya. A nasa jawabin, shugaban majalisar dokoki na jihar sakkwato Hon Magaji Maidaji wanda wakili daga majalkisar ya wakilita Hon Sani Yakubu ya yi bayanin cewa, a kwai kyakyawar dangantaka tsakanin majalisar da vangaren zartaswa a saboda haka zasu bayar da goyon bayan su ga dukkan wani shiri da gwamnatin ta qiqirqiro da zai tattafa wa rayuwar mutanen jihar.
Harajin Jihohi Ba Ya Iya Biyan Bashin Naira Tiriliyan 7.33 Na Tsawon Shekaru Bakwai Daga Bello Hamza
Idan jihohi za su yi shawarar biyan dukkan bashin da ake bin su ta hanyar tattara kuxaxen shigan su, zai xauke su shekara 7 kafin su iya cimma burin haka. Bayanai daga hukumar qididdaga ta qasa “National Bureau of Statistics (NBS)” ya nuna cewa, a qarshen shekarar 2017 a na bin jihohi bashin naira Tiriliya 7.33 yayin da kuxaxen shigan su ke a Naira Biliyan 931.23. Bayanan ya kuma qara nuna cewa, kuxaxen shigan
da jihohi 36 na qasar nan suka tara a shekarar2017 kashi 12.69 ne na abin da ake bin su gaba xaya ya zuwa qarshen shekara 2017. In aka tafi a haka, zai xauki jihihin shekaru 8 kafin su gama biyan bashin da ake binsu ta amfani da Naira Biliyan 916 a kowanne shekara na abin da ke shigo musu na kuxaxen haraji na cikin gida. Ganin cewa, jihohi kaxan ne zasu iya dogara da kuxaxen shigansu kwai cewa ba tare da abin da ke shigowa daga gwamnatin tarayya
ba. gwamnatin tarayya zata iya rage kuxaxen bashin ne kawai na tsawon shekara 3 in har jihohi suna buqatar su kasha dukkan kuxaxen shigan sunna cikin gida da kasonsu dake fitowa daga gwamnatin tarayya wajen biyan basusussukan da ake bi su. A shekarar 2017, jihohi 36 na tarayyarqasar nan sun samu Naira Tiriliyan 1.74 daga asusun gwamnatin tarayya, gaba xaya ya kama Naira Tiriliyan 2.67 in aka haxa da kuxaxen shigan sun a cikin gida a qarshen
shekarar da muke Magana a kai. Gaba xaya basussukan dake a kan jihohin sun kai naira Triliyan 7.33 an samu qarin Naira Tiriliyan 4.66 na abin da ke shigo musu a cikin shekarar. Masana sun qara yin bayanin cewa, in har babu wani matsala jihohi na buqatar shekara 3 wajen biyan basussukan su ta hanyar yin amfani da gaba xayan kuxaxen dake shigo musu ta cikin gida da kuma kason su daga asusun gwamnatin tarayya.
Basussukan sun haxa dana cikin gida da kuma waxanda aka karva daga qasashen waje, kuxaxen shigan kuma ya haxa da waxanda ake tattara wa a cikin gida tare da wanda gwamnatin tarayyar ke rarraba wa jiohi domin aiyukan ci gaban al’umma. Qididdigar bashin Naira Tirikiyan 7.33 da ake bin jihihin ya nuna cewa, bashin qasashen waje ya kai Naira Tiriliyan 1.47 (N4.08 trillion) yayin da bashin cikin gida ya kai Naira Tiriliyan 3.25 a qarshen shekarar 2017.
A Yau Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Ra’ayinmu
3
Muna Maraba Da Tsaftace Sashen Shari’a Vangaren Shari’a na xaya daga cikin muhimman gavovi na matakin shugabancin al’umma a duk inda suke kuma a ko wane irin tsari suke bi. Saboda muhimmancin vangaren shari’a, shi ne aka damqa wa wuqa da nama na hukunta duk wani mahaluqi da aka samu ya aikata laifi, ko da kuwa shugaba ne da kansa. Ke nan, muhimmancin vangaren ba zai misaltu ba. Tun lokacin da Shugaba Buhari ya hau karagar mulki, ya sha nanata cewa babbar matsalarsa a yaqin da yake so ya yi da cinhanci da rashawa ba ta wuce vangaren shari’a ba. Dalili, saboda shi kansa ya sha wuya a hannun vangaren shari’ar Nijeriya bisa yadda ya yi ta zuwa kotu sau shurin masaqi kan maguxin zavukan da ya shiga a baya kuma babu biyan buqata. Shugaban qasan ya sha alwashin daidaita vangaren shari’ar Nijeriya, inda a matakin farko jami’an ‘yansandan ciki suka fafari gidajen wasu alqalai da aka zarga da cinhanci da rashawa. Koda yake, Majalisar Kula da Harkokin Sashen Shari’a ta Qasa ta nuna rashin dacewar hakan tare da bayyana cewa ita ce take da alhakin bin kadin duk wani abu da ya shafi sashen na shari’a. Shugaba Buhari sai ya mayar da lamarin binciken abubuwan kunyar da ake zargin alqalan da tafkawa kuma ta yi bincike ta miqa masa, inda a qarshen makon da ya gabata ya zartar da hukunci bisa shawarar majalisar. Don haka, ritayar dole da aka yi wa Maishari’a Adeniyi Ademola da kuma korar Maishari’a O.O Tokode daga aikin alqalanci, wani qwaqqwaran mataki ne da Shugaba Buhari ya xauka na cimma kyakkyawan qudirinsa na tsaftace sashen shari’ar qasar nan. Ba shi ne shugaba na farko a qasar nan da ya yi yunqurin gyara vangaren na shari’a ba musamman kan abin da ya shafi yin shari’a ta gaskiya da adalci ga waxanda ake kamawa da hannu dumu-dumu wajen aikata miyagun laifuka. Amma kuma shi ne ya karya lagon varnar da galibin ‘yan qasa ke zargin ana tafkawa a sashen inda ya sa waxanda suka kawo iya-wuya kan lamarin suka yi ajiyar zuci. Jaridarmu ta sha ba da rahotanni kan yadda ake haddasa tafiyar hawainiya wajen yanke hukuncin masu laifi a sakamakon nagoron da ake baiwa ma’aikatan shari’a da lauyoyi don su kawo tsaiko a kan shari’a, musamman kan abin da ya shafi yaqi da cin hancin da ake yi a qasar. Kafin wannan lokacin, Nijeriya ta yi fama da borin kunya kan yadda qiriqiri gafiyoyin da suka amsa laifukansu na sata suke tsira daga shari’ar da ake musu kuma su cigaba da wadaqa da
abin da suka sata. A lokuta dabandaban, an riqa wasa da hankali a shari’o’i har a kai ga kwashe tsawon shekaru masu yawa ba tare da an yanke hukunci ba, domin qyale masu aikata miyagun laifuka su cigaba da rawar gaban-hantsi, inda hakan ya sa wasu suka riqa kwaxayin bin sawu domin sun ga abin da riba. Yanayin da Shugaba Buhari yake kokawa da shi da ke kawo masa tarnaqi a yaqin da yake yi da cin hanci da rashawa, ba qaramin koma-baya yake haddasawa
ba a qoqarin rage ko kawar da qumbiya-qumbiya da maguxin zave. Abin da shugaban ya tasa a gaba shi ne gyara vangaren shari’a wanda ya lashi takobin dawo da shi kan turba mafi dacewa. Tabbas mun gamsu da damuwar da shugaban qasan yake nunawa musamman kan ra’ayinsa na cewa sashen shari’a ya kamata ya shiga gaba wajen yaqi da cin hanci da rashawa ta hanyar yanke hukunci na gaskiya da adalci. Domin samun
EDITA Sulaiman Bala Idris
MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama
MATAIMAKIN EDITA Bello Hamza
DARAKTAN SASHE Mubarak Umar
RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah
BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John
manufarmu
LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!
nasarar wannan, ya zama wajibi jagororin vangaren su nuna cewa da gaske suke yi. Har ila yau, mun amince da furucin da ya yi na cewa yana da matuqar muhimmanci, vangaren shari’a a matsayinsa na babban ginshiqin gyara al’umma ya riqa tabbatar da cewa ana yanke hukunci a kan manyan laifuka cikin hanzari saboda qwallafa rai kan haka da jama’a ke yi. Kuma ga shi mutane da dama suna ganin a maimakon vangaren ya zama wurin kare haqqin talaka; sai ya zama wurin murqushe shi. Waxannan matsalolin ana fama da su ne duk da kasancewar ana aiki da Dokar Hukunta Masu Aikata Miyagun Laifuka ta 2015. Domin tunkarar irin kallon da ake ma sa, sashen shari’ar ya fara xaukar matakan tsaftace kansa. Inda ya yi wa wasu ma’aikatansa ritayar dole, wasu kuma ya kore su daga aiki. Aikin cire baragurbin sashen na cigaba da gudana kuma muna yaba wa shugabannin sashen saboda qwarin gwiwar da suka nuna na xaukan qwararan matakin na gyara. A kan wannan ne ma muke jinjina wa Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Qasa (NJC), saboda kyakkyawar shawarar da ta bayar ta hukunta Maishari’a Ademola da Maishari’a Tokode. Xaukar matakin ya tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Kasancewar akwai Alqalan da suke wasa da aikinsu tare da xaukar kotu a matsayin mai shiga tsakani kawai, maimakon yanke hukunci bisa gaskiya da adalci. Sau tari, akan bar shari’a a hannun masu gabatar da qara da lauyoyi su riqa fafatawa a tsakaninsu shi kuma Alqali ya zama xan kallo kurum. Hakan ya sa idan masu gabatar da qara da masu kare wanda ake qara suka haxa baki a junansu, sai a raina wa kotu hankali. Masu gabatar da qara su gaza fito da shaidar aikata laifi varo-varo, lauyoyin da ke kare wanda ake qara kuma su yi ta mayar da hannun agogo baya. Muna fata, daga wannan gyarar da ake yi, dukkan masu hannu a sha’anin shari’a na qasar nan za su haxa qarfi da qarfe domin tabbatar da sashen na shari’a ya dawo kan turbar asali da aka san shi a kai na baiwa mai laifi lafinsa, mai gaskiya kuma a ba shi gaskiyarsa. Sannan ya kamata Qungiyar Lauyoyi ta Qasa (NBA) ta daidaita sahun ‘ya’yanta da suke karkacewa, waxanda suka qware tare da gogewa wajen mayar da fari ya zama baqi, baqi kuma ya zama fari saboda kuxi. Tabbas, idan aka samu sashen shari’a ya yi ado da gaskiya da riqon amana, sauran sassan gwamnati ma ba za a bar su a baya ba, kasancewar sashen a matsayin uwa-ma-ba-damama.
4 LABARAI
A Yau
Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Zamfara: Har Yanzu Ana Tsinto Gawarwaki A Daji Daga Sulaiman Bala Idris
Har zuwa yanzu ba a kamala tantance adadin mutanen da suka rasa rayukansu a harin da wasu mavarnata suka kai a garin Bawan Daji ba. An kai mummunan farmaki a Garin na Bawan Daji wanda ke qarqashin Qaramar hukumar Anka a makon da ya gabata, inda aka samu salwanta rayuka masu adadin gaske, wanda har
zuwa haxa wannan rahoto tsinto gawarwakin ake yi daga daji. Awanni kaxan bayan farmakin, Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Zamfara ta fitar da sanarwar cewa mutum uku ne suka rasa ransu, wanda washegari suka fid da sanarwar cewa adadin ya haura zuwa 15. A haka adadin waxanda suka rasu xin ya ci gaba da hauhawa har zuwa ranar Juma’a yayin da Sarkin Anka, Alhaji Attahiru
Ahmed ya sanar da cewa an samu gawarwakin mutum sama da 30, a yayin da Gwamna Yari tare da rakiyar Sanata Yarima suka kai ziyarar gani da ido a garin. Sai dai ko a tab akin Sarkin, wannan adadin da ya bayar ba shi bane na qarshe, domin ana kan aikin ci gaba da tattaro gawarwaki daga dazuka. Wata majiya wacce ta nemi a sakaya sunanta ta sanar da LEADERSHIP A Yau cewa a ranar
asabar an tsinto gawarwaki sama da 20 daga cikin daji, wanda kuma a ranar Lahadi aka tsinto qarin wasu gawarwaki bakwai. Xaya daga cikin waxanda suka shaidi lamarin, wanda ya ce sunansa Salisu, ya bayyana cewa rijiya ya tsallake da baya, ya kuma ce, har yanzu akwai gawarwaki a daji, waxanda ba a kai ga xebo su ba. Bincikenmu ya tabbatar mana da cewa, ana kaffa-kaffa da shiga
dajin ne saboda tsoron yin gamo da mavarnatan varayin shanun, domin a waxannan dazuka suke rayuwa. Wata majiyar, wacce ta buqaci itama a sakaya sunanta, ta sanar da LEADERSHIP A Yau cewa, ya zuwa yanzu an samu gawarwakin mutane sun fi 70, saboda an kwashe kwanaki uku cur ne ana kisan gilla a garin, kuma a kowacce rana sai an kashe mutane.
Ya Zama Tilas Mu Qarfafi Matasa Su Karvi Shugabanci –IBB Daga Umar A Hunkuyi
Tsohon Shugaban Qasarnan a zamanin mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewa, tsaffi sun jima a kan kujerar mulkin Qasarnan, don haka, ya wajaba su janye su bar matasa su karvi jagorancin tafiyar da akalar mulkin qasarnan ba tare da vata lokaci ba. Tsohon Shugaban Qasan, ya yi wannan tsokacin ne ranar Lahadi, a sa’ilin da wata sabuwar qungiyar siyasa mai suna, ‘The New Nigeria,’ suka kai ma shi ziyara qarqashin shugabansu, Moses Siloko Siasia, a gidan sa da ke kan tsauni a Minna. IBB ya ce, shi da masu fahimta irin na shi, tun a shekarar 1989 ne suka shawarta yiwuwar hannanta ragamar shugabancin qasarnan ga matasan, waxanda suke da
sha’awa da kuma qumajin ciyar wa gami da bunqasa qasarnan, amma sai tsaffin ba su nu na sha’awar hakan ba, a wancan lokacin. Ya ce tarihi ya nu na, an fi samun ci gaba da kuma bunqasan kowace qasa ce a hannun matasan ta, waxanda a cewar sa, su ke da qumaji da kuma sabon jini a jika gami da sabbin tunani masu fa’ida. Inda har ya kawo masu misalin Tsohon Shugaban qasannan a zamanin mulkin Soja, Janar Yakubu Gowon, IBB ya ce, Gowon, yana da shekaru 31 ne ya shugabanci qasarnan, ya kuma yi aiki mai kyau na tabbatar da kasantuwar qasarnan dunqule, sannan ya aiwatar da manyan ayyukan da har yanzun ana iya ganin da yawa daga cikin su, ya qara da cewa, mafiya yawa daga cikinmu duk muna matasa ne
muka sami shugabanci. “Ya zama tilas tsaffi su baiwa matasa waje. Tunaninmu na da ne, yanzun zamani ya canza, don haka ya kamata mu goya wa matasa baya ne, su yi amfani da sabbin tunanin su wajen ciyar da qasarnan gaba,” in ji IBB.
IBB
Ibrahim Babangida ya ce, ya yi murna da jin gabatar da qudurin nan na baiwa matasa shugabanci mai taken, ‘Not Too Young To Rule,’ da aka gabatar a Majalisar wakilai, yana kuma bin dukkanin tattaunawar da ake yi kan qudurin a Majalisar sau da qafa a wancan lokacin. Ya ce, da yawan mu, suna fatan ganin tabbatan hakan, za kuma su taimaka ma ganin tabbatuwan hakan. Jagoran tawagar, wanda tsohon xan takarar neman kujerar gwamna ne a Jihar Bayelsa, qarqashin tutar Jam’iyyar PDM, cewa ya yi, qungiyar na su ta iso garin na Minna ne domin ta tattauna ta kuma nemi tubarraki daga tsohon shugaban qasan domin ganin an samar da sabuwar qasar Nijeriya, mai sabuwar mahanga a shekarar 2019. Mista Siasia, ya yi nu ni da
cewa, matasan sun yi azamar karvan shugabancin ne kasantuwar gazawan da tsaffin hannun suka yi. “Tattaunawar namu ta yi fa’ida sosai, mun kuma ji daxin cewa Tsohon shugaban qasar nan yana tare da mu. A yanzun haka kuma muna kan hanyar mu ne ta Otta, domin saduwa da tsohon shugaban qasa Olusegun Obasanjo, bayan nan za mu kai kwatankwacin wannan ziyarar ga tsohon shugaba Jonathan da kuma tsohon shugaba Janar Abdussalam Abubakar, domin neman goyon bayan su,” in ji shi. Ya kuma ce, qungiyar ta su za ta tsayar da matasa a Jam’iyyu daban-daban, domin neman shugabancin qasarnan a zaven 2019, inda ya nemi matasan daga kowane sashi na qasarnan da su goyi bayan wannan tafiya ta su ta samar da sabuwar qasa Nijeriya.
Hon. Kalanjeni Ya Xauki Nauyin Duba Lafiyar Idanun Mutane 2, 000 A Sakkwato Daga, Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
Xan Majalisar da ke wakiltar Qananan Hukumomin Gudu da Tangaza a Majalisar Wakilai, Honarabul Isah Salihu Bashir Kalanjeni ya xauki nauyin aikin duba lafiyar mutane dubu biyu kyauta a mazavarsa da ke Sakkwato. Qwararrun Likitocin idanu ne suka gudanar da aikin na kwanaki biyu wanda aka gudanar a Manyan Asibitocin Gudu da Tangaza a ranakun Lahadi da Litinin. An gudanar da aikin ne a qarqashin Kalanjeni Foundation, Gidauniyar da Mai Shata Dokokin na Jam’iyyar APC ya kafa domin bunqasa rayuwar al’ummarsa ta fuskoki da vangarori da dama na rayuwar al’umma. Jagoran tawagar Likitocin Dakta Musa Ibrahim ya bayyanawa manema labarai cewar aikin ya gudana cikin nasara ba tare da wata tangarxa ba. Ya ce bakixaya marasa lafiya dubu biyu ne suka amfana da aikin wanda aka duba lafiyar mutanen yankin
a mabambantan matsalolin cututtukan idanu da suka haxa da kwantson ido, yanar ido, jijiyoyin idanu, jan ido, matsalar gira da kuma waxanda aka yi wa aiki a idanu da waxanda aka baiwa magani da kuma waxanda aka baiwa madubin ido. A tattaunawarsa da manema labarai, Xan Majalisar da ya xauki nauyin aikin, Honarabul Isa Kalanjeni ya bayyana cewar ya xauki nauyin duba lafiyar idanun al’ummar mazavarsa ne a bisa ga muhimmanci da tasirin da ke ga idanu ga rayuwar al’umma don haka ya yi amfani da damarsa wajen magance matsalolin da suke fuskanta. Ya ce “Wannan matsalar ta idanu ba wasu kuxi take ci sosai ba amma duk da haka wasu da dama saboda rashin hali ba za su iya zuwa asibiti domin a yi masu aiki ko a ba su magani ba.” In ji shi. Hon. Isah Kalanjeni wanda shine Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai Mai Kula da Sufurin Jiragen Sama ya bayyana cewar a matsayinsa na wakilin al’umma
zai ci-gaba da iyakar qoqarinsa wajen ganin ya bunqasa tare da kyautata rayuwar al’ummar mazavarsa. A nasa vangaren Shugaban Qaramar Hukumar Tangaza, Hon. Nura Shehu Tangaza ya bayyana shirin a matsayin muhimmi wanda aka samu nasarar gudanar da shi ta hanyar magance cututtukan idanun mutane da dama. “Alhamdilillahi aikin ya samu nasara fiye da yadda aka yi tsammani domin mutane da dama a yanzu sun samu sauqi a cututtukan da ke addabar idanun su. Hon. Kalanjeni a matsayinsa na Xan Majalisar wannan yankin ya ragewa Qaramar Hukuma nauyi a wannan shirin da ya xauki nauyi wanda muka ga alfanunsa tun kafin a kammala.” Ya bayyana. Hon. Tangaza ya kuma bayyana cewar a matakin Qaramar Hukuma za su tattauna kan wasu matsalolin da al’ummar yankin ke fama domin samar da mafita a yunqurin share hawayen al’ummar Qaramar Hukumar. Xaya daga cikin waxanda aka yi wa aikin Ibrahim Isah Raka
ya bayyanawa LEADERSHIP A Yau cewar ya kwashe shekaru uku ba ya gani a idanun sa amma yanzu cikin iyawar Allah ya fara ganin sauqi. Garba Tungar Balle yana xaya daga cikin waxanda suka ci moriyar aikin ya kuma bayyanawa wakilin mu cewar a can baya idanunsa suna gani garaye-garaye amma yanzu lafiya ta fara samuwa kamar kuma yadda Mairi Alhaji da Maryam Adamu Kurdula suka bayyana cewar suna ganin hazo a idanun su a inda aka
Hon. Kalenjeni
fito a tsayin shekara xaya amma yanzu da aka yi masu aiki a idanu sun fara ganin alamun sauqi da nasara a aikin. “Muna godiya qwarai ga Hon. Kalanjeni kan wannan hovvasar qwazon da ya yi ta tallafa mana ga matsalolin idanu da muke fuskanta. Muna fatar sauran ‘yan siyasa za su yi koyi da halin karamci, dattako da jinqai irin na Xan Majalisar mu.” Kamar yadda suka bayyana a tattaunawa daban-daban.
LABARAI 5
A Yau Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Sunayen Mutanen Da Ake Zargi Da Satar Kuxin Gwamnati Ci Gaba Daga Shafin Farko
Lai Mohammed, ya zargi PDP kan martanin da ta mayarwa gwamnatin tarayya kan jerin sunayen na farko, yana mai cewa, PDP, ta san matsalan na ta na sace dukiyar al’umma. “Abin da muka tsammata daga PDP a martanin da ta yi, shi ne ta faxi sunayen varayin da suka sace dukiyar al’umma a cikin Jam’iyyar namu a yanzun haka? Ko PDP xin tana zaton satar fitan hankalin da aka yi a zamaninta wasa ne. Ko sun yi zaton zolayar April Fool ne muka yi masu? In ji Lai. Ministan ya ce, ai martanin na PDP, ya nu na roqon gafarar da suka yi ba komai ne ba face wata sabuwar yaudarar, so suke a sake zaven su a 2019 domin su sake cin wata kasuwar wawason dukiyar talakawan. “Ai ana yin tuba ta gaske ce tare da nadama, amma tuban PDP sam babu nadama a cikinta, tuban muzuru ne kawai alhalin ga wata kazan a bakinsa. Lai Mohammed ya ce, ba wanda ya isa ya tursasawa gwamnatin tarayya ta yi shiru ta hanyar shafa mata baqin fenti, ba kuma zamu fasa ba, har sai mutanan da suka sace dukiyar talakawa sun gurfana a gaban shari’a. JERIN SUNAYE NA BIYU NA MUTANEN DA AKE TUHUMA DA SACE DUKIYAR AL’UMMA 1. Tsohon mai baiwa Shugaban qasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki: A bisa bincike da kuma abin
da hukumar EFCC kaxai ta gano a kansa (baya ga dala bilyan 2.1 na sayan makamai), jimillan Naira bilyan 126, sama da dala bilyan 1.5 da Fam na Ingila milyan 5.5 ne aka wawashe a Ofishin na shi. Mafi yawan kuxaxen an rabawa wasu mutane ne da kuma wasu kamfanoni ba tare da sun gudanar da wani aiki ba. 2. Tsohuwar Ministan albarkatun man fetur, Diezeni Alison-Madueke; A abu guda kawai da hukumar EFCC ke tuhumarta a kai, kimanin Naira bilyan 23 ne ake zargin ta wawashe. Sannan kuma tana da hannu a cikin aiwatar da mahimman ayyukan kwangila a sashen na kamfanin mai na qasa, NNPC, inda kamfanukan Jide Omokore da na Kola Aluko, suka mallaki rijiyar mai, ba tare da sun biya gwamnatin tarayya harajin ko sisin kwabo ba. Kuxaxen da ya kamata su biya sun kai dala bilyan 3. A yanzun haka gwamnatin tarayya tana kan tuhumar Omokare da Aluko, za kuma ta yi amfani da duk hanyar da ta dace a nan gida da waje wajen tabbatar da an tsayar da hukunci a kansu. 3. Laftana Janar Kenneth Minimah, mai ritaya; EFCC ta karvo tsabar kuxaxe Naira bilyan 13.9 da kuma Naira bilyan 4.8, da kuma kadarori daga hannun shi. 4. Laftana Janar Azubuike Ihejirika: Ya zuwa yanzun EFCC ta qwato tsabar kuxi Naira bilyan 4.5 da kuma wasu Naira milyan 29 daga gare shi. 5. Tsohon Kwamandan
•Lai Mohammed.
tsaro na qasa, Alex Badeh, Naira bilyan 8, sannan kuma EFCC xin ta karvo wasu tsabar kuxaxen Naira bilyan 4 daga gare shi, gami da wasu kadarori. 6. Tsohon Shugaban hukumar Kwasatam, Inde Dikko: An karvo tsabar kuxi Naira bilyan 40, da kuma Naira bilyan 1.1, da kuma wasu mahimman kadarori daga gare shi. 7. Aiya Mashal Adesola Amosun: An qwato tsabar kuxi Naira bilyan 21.4, da Naira bilyan 2.8, da kuma wasu kadarori manya gami da manyan motoci guda 3 daga gare shi. 8. Tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Sanata Bala Abdulkadir: An qwato Naira bilyan 5, sannan kuma Kotu ta bayar
da umurnin kame wasu kadarori na shi. 9. Sanata Stella Oduah, Naira bilyan 9.8, ita ma Kotu ta bayar da izinin kame wasu manyan kadarori na ta. 10. Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu: Naira bilyan 1.6, wanda ya amsa daga tsohon mai baiwa Shugaban qasa shawara kan harkar tsaro. 11. Tsohon Gwamnan Jihar Flatau, Jonah Jang: Naira bilyan 12.5. 12. Tsohon Ministan kuxi, Bashir Yuguda: Naira bilyan 1.5, sannan kuma an qwato wasu tsabar dala dubu 829,800. 13. Sanata Peter Nwaboshi: Naira bilyan 1.5. 14. Tsohon mai taimaka wa Sambo Dasuki, Aliyu
Usman: Naira milyan 512 15. Wani tsohon mai taimaka wa Sambo Dasukin, Ahmed Idris: Naira bilyan 1.5. 16. Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Rasheed Ladoja: Naira milyan 500. 17. Tom Ikimi: Naira milyan 300. 18. Femi Fani Kayode: Naira milyan 866. 19. Tsohon PPS xin Goodluck Jonathan, Hassan Tukur: dala milyan 1.7. 20. Nenadi Usman: Naira bilyan 1.5. 21. Benedicta Iroha: Naira bilyan 1.7. 22. Wani na kusa da Sambo Dasuki, Aliyu Usman Jawaz: Naira milyan 882. 23. Tsohon Gwamnan Jihar Flatau, Jonah Jang: Naira bilyan 12.5.
Iyaye Ku Qara Kula Da Ilimin Yara Da Allah Ya Ba Ku -A.S.Bello Daga Balarabe Abdullahi, Zariya
An bayyana halin da waxansu iyaye ke ciki na rashin kula da yaransu na ganin su sami ilimin addini da na zamani da cewar, babbar matsala ce ga yaran da kuma iyayen yaran. Babban malami a tsangayar nazarin harshen Hausa na kwalejin ilimi na gwamnatin tarayya da ke Zariya mai suna Malam A.S, Bello ya bayar da shawarar a jawabin day a yi a lokacin yayen xalibai na makarantar
MADARASATU HIZBUL RAHIM LIL-TAHAFIZUL QUR’AN WAL-ULUM da ke garin Nagoyi a qaramar hukumar Zariya a jihar Kaduna. Malam A.S.Bello ya ci gaba da cewar, a yau wasu iyaye na nuna halin ko in kula da yadda yaransu ke watan-gaririya a tituna ba tare da sun sami dammar zuwa makaranta ba, na addini ko kuma na zamani. A cewarsa, wannan mataki da wasu iyaye ke xauka mataki da babu ko shakka, babbar matsala ce ga yaran da kuma iyayen
kansu, na matsayin da yaransu za su tsinci kansu a gobe, na rashin ilimin addini da ilimin zamani da kuma rashin ilimin sana’a da yaran za su dogara da shi, a lokacin da suka zama mutane a gobe. Da kuma Malam A.S.Bello ya juya ga wannan makaranta da ke Nagoyi, ya nuna matuqar damuwarsa na halin matsalolin da makarantar ke ciki na rashin azuzuwa da kuma sauran matsaloli ma su yawan gaske, da ya dace ace wannan makaranta na da shi, sai
aka sami akasin haka. A kan waxannan matsaloli da suka yi wa wannan makaranta qawanya, sai Malam A.S,Bello ya ce, tuni a qarqashin wannan kwamiti na yunqurin ciyar da wannan makaranta gaba, sun fara motsawa, da nufin warware matsalolin da suka warware matsalolin da suke addabar wannan makaranta. Malam A.S.Bello. ya kuma yaba wa shugaban wannan makaranta Malam Muhammad Bello Umar Faga, na yadda
duk da matsalolin da suke addabar wannan makaranta, makarantar ta sami nasarori ma su yawan gaske, na samar da yara da suka kammala karatun Alqur’ani da kuma hadda a cikin wannan makaranta. Malam A.S, Bello ya kammala da cewar, wani kwamiti da aka kafa domin tallafa wa wannan makaranta, zai fara za ga wasu al’umma da suke wannan gari na Nagoyi, da nufin samo bakin – zaren warware matsalolin da suke addabar wannan makaranta.
6 LABARAI
A Yau
Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Minista Fayemi Zai Yi Takarar Kujerar Gwamnan Ekiti Daga Bello Hamza
Tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma a halin yanzu Ministan ma’adanai da qarafa Dakta Kayode Fayemi ya sanar da cewa zai yi takarar kujerar gwamnan jihar Ekiti a zaven da za a gudanar ranar 14 ga watan Yuli na shekarar 2019 a qarqashin tutar jam’iyyar APC. Ya bayyana wannan burin masa ne a taron manema labarai daya kira a garin na IsanEkiti da ke qaramar hukumar Oye ta jihar, taron ya samu halartar shugabani da jagororin jam’iyyar daga qananan hukumomi 16 da mazavu 177 dake faxin jihar. Ya ce, aiyukan daya gudanar a baya ne suka zaburar da shi na neman wannan muqani, musamman aiyukan daya gudanar na taimakon ma’aikata da tsofaffi da suka bar aiki a lokacin da yake gwamnan jihar. Ya qara da cewa, ya yanke shawarar neman kujerar a karo na biyu ne saboda ya quvutar da jihar daga hannun vata gari da basu iya aiki ba, haka kuma yana fatan mayar da jihar zuwa matsayin da ya kamata a ce takai. Bincike ya nuna cewa, tsohon gwamnan shu ne mutum na 35 daga jam’iyyar APC da suka nuna aniyarsu na neman xarewa karagar mulkin jihar, a kwai kuma wasu da dama daga wasu jam’iyyun da suka nuna
aniyar ta hanyar liliqa hotunan yaqin neman zaven su amma basu riga sun bayyana aniyar na neman kujerar bga jama’a. Fayemi ya kuma ce, zai miqa takardarsa na neman takarar ga ofishin jam’iyar APC ta jihar da zaran hukumar zave ta INEC ta xage takunkumin yaqin neman zave a ranar 15 ga watan Afrilu. A kan takardar sakamakon binciken da ta kama shi da cin hanci da rashawa har ma ta haramta masa shiuga harkokin siyasa na shekarar 10, Fayemi y ace, wannan takardar bat a dame shi ba, ya ce, wannan sakamakon binciken ba zai tsayar da burinsa na neman zama gwamna ba saboda takardar aiki ne na tsawon lokaci da gwamnatin Ayo fayose ta yi masa bita da qulli kuma baza su samu nasara ba, kuma sakamakon binciken ba zai samu nasarar ba. “Ko mai wani zai ce, I na da tabbacin cewa, na yi matuqar cancantar takarar wannna kujerar in hard a ban cancanta bad a b azan tava zuwa gaban ki in ce zan yi takarar ba” “ya wancin vatancin da fayose da gwamnatinsa suka yi zargin na aikata an qirqire su ne domin a vata mani suna tare da tunanin kawo mani matsala a harkokin siyasa na amma tabbasgasikiya zata yi halinta, musamman abin ya shafi jirkita kuxaxen da ake bin jihar bashi an yi su ne domin a vata mani
• Minista Fayemi
suna” “Fayose ya fito da “White Paper” da ta haramta mani shiga harkokin siyasa amma ni yau gashi na bashi “red card” yayin da aka gama harkokin siyasa jama’a zasu san wanene ke a kan gaskiya a cikin mu biyu” inji shi. Ministan ya sha alwashin kora Fayose tar da mataimakinsa in har an zave shi a zaven fidda gwani a ranar 5 ga watan Mayu da jam’iyyar zata gudanar da zaven fid da gwani garin Ado Akiti. Ya kuma shawarci ‘yan takara das u yi hattara da magoya
bayansu kada su ne vata zumuncin dake a tsakaninsu, ya kuma qara da cewa, dukk wanda Allah ya bai wa nasarar zama xan takara to dukkan sauran ‘yan takarar su rungumeshi domin a sama kai wag a ci, musamman ganin uwar jam’;iyyar ta yi alkawarin yi zave cikin adalci ba tare da magixi ba. Ya kuma yi alkawarin amfani da zama gwamna a karo na biyu wajen gyara kurakuran day a gabaar a baya tare da yin aiyukan ci gaban al’umma, kafin ya bar gidan gwamnati cikin shekara 4 a matayin gwamna. Daga nan
Fayemi ya nemi gafarar dukkan waxanda ya musgunawa a lokacin da yake gwamna, ya kuma ce shi ya yafe wa dukk waxanda suka musguna masa domin a samu ci gaba. Ya kuma gargaxi Fayose a kan kada ya kuskura ya vata masa hutunan yaqin neman zaven sa kamar yadda gwamnatinsa ke yi wa jamm’iyyun adawa. Ya zuwa yanzu bai yi bayanin lokacin da zai yi murabus daga kujerarsa na, minister ba domin fuskantar harkokin siyasa gadan-gadan.
Mai Talla Shi Ke Da Riba:
LEADERSHIP A YAU Ta Shirya Tsaf! Kamar yadda kowa ya sani ne, wannan jarida mai albarka, LEADERSHIP A YAU ta kafa tarihi wajen zama jaridar Hausa da ta fara fitowa a kullum. Wannan fara fitowa a kullum yana da alfanu masu yawan gaske, gare mu Kamfanin LEADERSHIP da ku masu karatu, musamman masu sana’o’i manya da qanana. Wannan ne ya sa muke farin cikin shaida wa masu karatunmu cewa mun shirya tsaf domin tallafa wa kasuwancinku, ta hanyar tallata maku shi zuwa inda ba ku zata ba. Domin a halin yanzu mu kanmu da muke buga wannan jarida ba za mu iya bayyana iya inda ta ke shiga ba. Muna da tsare-tasare da dama don talla ku da hajojinku, inda muka fitar da tsarin ‘IYA KUXINKA IYA SHAGALINKA.’ Wato akwai cikakken shafi, akwai rabi, akwai kwata, akwai kuma daidai iyaka abin da mutum ke so a sanya masa. Wanda a wannan shafin muna so masu sana’o’i, musamman manyan dillalai su tallata hajojinsu, su qananan ’yan kasuwa akwai
nasu tsarin. A wani tsarin ma da muke da shi, akwai yanayin da mutum zai tallata hajarsa, sannan ya tallata kansa, inda za a sanya hoton shagonsa, hotonsa da kuma taqaitaccen tarihinsa, kuma wannan duk a kuxi kaxan. Maza ku kasance cikin kashi na farko na masu cin moriyar wannan shiri. Ina ’yan Canji, dillalan yaduka, masu kayan masarufi, mayan da qananan ’yan tireda, dillalan magunguna, masu kamfoni da masana’antu, dillalan hatsi, dillalan mota, masu sayar finafinai da dai sauran masu sana’o’i, ga dama ta samu. A tuntuvemu a lambarmu ta 0703 666 6850, 08039216372, 07037934034, 08032875238 da 08038011382: email leadershipayau@gmail.com. Ko kuma a tuntuvi wakilanmu na jihohi don qarin bayani.
A Yau Litinin 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku
Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku
Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.
Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com
TALLA 7
8 TALLA
A Yau Litinin 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
A Yau Litinin 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
TALLA 9
Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”
Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.
10 LABARAI
A Yau
Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
• Wasu yara a jiya yayin da suke murna da zagayowar bukin ranar EASTER a garin Legas
NBA Ta Buqaci Jami’an Tsaro Da Su Daqile Aikace-Aikacen ’Yan Ba-Beli A Bauchi Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Qungiyar lauyoyi ta qasa Nigerian Bar Association (NBA) reshen jihar Bauchi ta buqaci jami’an tsaron da suke aiki a jihar Bauchi da su himmatu domin kawo qarshen aikace-aikacen qungiyar nan mai yanke hukuncin kisa wa jama’an da ake zarginsu da laifuka ba tare da jiran doka ta yi aiki a kansu ba. Shugaban qungiyar lauyoyi ta jihar Bauchi Barrister Mahmud Muhammad Maidoki shine ya yi wannan qiran a wajen bikin rantsar da zavavvun shuwagabanin qungiyar matasa lauyoyi na jihar wato’ Young Lawyers Forum’ qungiyar matasan wacce ke qarqashin uwar qungiyar ta NBA, taron da ya gudana a makon jiya. Maidoki ya bayyana cewar da buqatar jami’an tsaro su tabbatar da kawo qarshen qungiyar nan ta ‘yan ba beli domin kare rayukan jama’an jihar daga kisa ba bisa qa’ida ba “ina qira ga jami’an ‘yan sanda da su tabbatar da kawo qarshen aikace-aikacen qungiyar nan mai yanke hukuncin kisa wanda aka fi saninsu da suna ‘Yan BaBeli’ waxanda suke zartar da hukuncin kisa ga jama’an da suke zargin sun aikata wani laifi wanda hakan ya sava wa doka,” Maidoki ya bayyana cewar masu kawo korafi sun yawaita akan hidimar
Yan Babeli waxanda suke xaukan muggan makamai a garuruwan Ningi, Warji da kuma qaramar hukumar Ganjuwa. Lauyan ya shawarci jam’an tsaro da suka himmtu wajen kare lafiya da dukiyar mazauna jihar domin ci gaba da kare rayukan ‘yan qasa. Maidoki ya bayyana cewar shugabancinsa zai baiwa lauyoyi matasan damarsu na
bayar da gudunmawa domin ci gaban fannin shari’a a jihar. Tun da fari, shugaban qungiyar matasan lauyoyi mai barin gado a jihar Barrister Idris Safiyanu Gambo ya yi bayanin cewar qungiyar matasan lauyoyin wacce aka kaddamar da ita a 2016 ya qara da cewa manufar hakan shine domin qenqeshe sabbin shigowa cikin sha’anin lauya bisa kwarewa da bin dokokin
aikin don sauqawe musu gabanin samun horo sosai. Sabbin zavavvun wacce babban mai shari’a na jihar Bauchi Justice Rabi Talatu Umar wacce Justice Abubakar A Suleiman ya wakilceta, ita ce ta rantsar da su. Wanda aka rantsar a matsayin shugaban su ne Abbas Muazu, Yusuf Abdullahi Aliyu, mataimakin shugaba, Habila Isa Barau a
matsayin sakataren qungiyar matasan lauyoyi na jihar. Sauran zavavvun su ne: Auwal Abdul Aziz muqaddashin sakatare, Kabiru Ibrahim, sakataren kuxi, Amazadu Vivian Iwu, Ma’aji, S. F Famare, jami’an hulxa da jama’a, a yayin da kuma Yusuf Uba Kabiru a matsayin Provost.
makaranta, a cewarsa,suna ci gaba da karatunsu a makarantun sakandare da kuma makarantun gaba da sakandare da suke ciki da wajen jihar Kaduna. Malam Bello Umar ya ci gaba da cewar, sun fara da koyar da yara shida, da kuma malami xaya day a buxe makarantar bayan an ba shi izinin buxe makarantar, zuwa yanzu, kamar yadda ya ce, suna da xalibai fiye da dubi da xari biyar, da suke takure a wannan makaranta da ke Unguwar da aka ambata. Da kuma Malam Bello ya juya ga iyayen yara da yaransu ke wannan makaranta da kuma ma su dukiya ta halas, sai ya yi kira a garesu, da su dubi halin da makarantar ke ciki, na rashin azuzuwa da za a yi amfani da su, wajen koyar da xaliban da suke
wannan makaranta. Malam Muhammad Bello Umar, ya kuma jawo hankalin iyayen yaran da suka kammala sauke karatun Alqur’ani mai girma, da su ci gaba dab a yaransu duk tallafin da suka dace ga yaransu, domin su sami sauqin ci gaba da karatu, a duk matakan ilimi da suke ciki da kuma wajen jihar Kaduna. Har ila yau shugaban wannan makaranta, ya nuna matuqar jin daxinsa da yadda wasu ma su arziki na halas, na yadda suke tallafa wa wannan makaranta,waxanda ke tallafa wa wannan makaranta, sun haxa da Xan masanin Nagoyi, Alaji A.S’Bello Xan Masanin Nagoyi da alhaji Idris Abdullahi, wanda ya saba ba xaliban Alqur’ani mai girma, a duk lokacin
makarantar ke bikin yaye xalibanta.da Alhaji Mustafa mai rake da kuma alhaji Mu’azu da shi ma ke tallafa wa wannan makaranta da kuma sauran xalibai da suke wannan makaranta. Sauran waxanda suka yi wa’azi a wajen yayen xaliban sun haxa da Shekh Abubakar na gidan Marigayi Malam Na’iya a`birnin Zariya da Malam Abdullahi Gyallesu da Malam Lawal Gyallesu, dukkansu sun jawo hankalin xaliban da su kasance ma su qoqrin ganin sun ci gaba ilimin addinin musulunci da kuma na zamani, da za su tallafa ma su su sami natsuwa, kowa da iya ganni. Wasu daga cikin xaliban da suka kammala karatun Alqur’ani mai girma sun fito ne daga jihohin Katsina da Kano da kuma jihar Kaduna.
Madarasatu Hisbur Rahim Ta Yaye Xalibai Karo Na Uku A Nagoyi Daga Balarabe Abdullahi Zariya
A ranar Lahadin da ta gabata, fitacciyar makarantar nan wadda ta ke da sassa da dama a arewacin Nijeriya da kuma wasu qasashe a yankin Afirika mai suna MADARASATU HISBUL RAHIM, LITAHFIZUL QUR’AN WAL ULUM,wadda ke Nagoyi a qaramar hukumar Zariya a jihar Kaduna ta gudanar da yayen xaliban makarantar karo na uku. Tun farko shugaban makarantar Malam Muhammad Bello Umar, ya bayyana tarihin makarantar da cewar, shekara uku da kafa ta a wannan Gari na Nagoyi, ta ya ye xalibai ma su yawan gaskeda suka sauke Alqur’ani mai tsarki da kuma haddar Alqur’ani mai tsarki, wanda wasu da suka kamala wannan
LABARAI 11
A Yau Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
2019: An Nemi ’Yan Jam’iyyar APC Da Su Tabbatar Sun Yi Rijista A Kebbi Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi
Jam’iyyar APC ta qasa reshin Jihar Kebbi ta yi kira ga membobinta na Jihar Kebbi da su tabbatar sun mallaki katin Rijista na jam’iyyar ta APC. An yi wannan kiran ne a
An Buqaci Gwamnatin Bauchi Ta Qara Himma Don Kammala Aikin Titin Zaranda Zuwa Miri Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
An roqi gwamnatin jihar Bauchi da ta qara himma wajen aikin tagawayen titin da take shimfixa a daga titin Zaranda, Wuntin Dada zuwa qauyen Miri domin qara yawaitar asaran rayuwa a sakamakon tafiyar hawainiya da aikin ke yi. Shugaban qungiyar direbobi da ke hanyar Jos, Alhaji Maikudi Adamu shine ya yi wannan roqon sa’liin da ke tattaunawa da manema labaru a Bauchi. Shugaban direbobin wanda ya samu wakilcin sakataren qungiyar Muhammad Waziri ya ce a sakamakon tafiyar hawainiyar aikin ya jawo musababbin yawaitar hadurar da yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a kan wannan aikin. Shugaban qungiyar sai ya yi amfani da wannan damar wajen neman rancen kuxi daga wajen gwamnatin jihar Bauchi domin kyautata sana’arsu da kuma gina sakatariyar qungiyar gami da tashar motar da za suke jigilan fasinjoji zuwa sassan qasar nan. Wakilinmu ya labarto cewar wannan titin da ake magana a kan babban titi da kuma akwai kwalejin gwamnatin jiha a kan titin wanda kowace rana akwai yawan zirga-zirga amma kuma aikin titi har yau bai kawo qarshe ba, wanda hakan ne ya sanya jama’a ke neman a qara azama domin a samu a kammala aikin cikin gaggauwa da kuma yin nagartaccen aikin.
lokacin da aka gudunar da taron musu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na qananan hukumomi 21 da ake da su a jihar ta kebbi. An gudanar da taron ne a xakin taron na masaukin shugaban qasa da ke a Birninkebbi a jiya. Inda aka tattauna abubuwa uku, waxanda suka haxa da yin kira ga duk xan jam’iyyar APC a jihar da ya tabbatar da ya yi Rijistar zama xan jam’iyya. Don akwai waxanda suka canza sheqa daga wasu jam’iyyu zuwa APC da kuma waxanda ke cikin jam’iyyar amma ba su da Rijista ta zama xan jam’iyya. Saboda haka su tabbatar da sun yi Rijistar. Haka kuma an tattauna game da sababbin masu bada shawara ga Gwamnan jihar da aka yi, wanda har yanzu basu kawo lambar asusun bankinsu da kuma lambar BVN domin a fara
biyansu albashi. Sannan kuma an tattauna game da mutanen da suka canza sheqa dacewa su na da damar neman muqami a jam’iyyar, ko neman takara domin wakiltar mutanen mazavunsu. Wannan bayanan sun fito ne daga bakin kwamishinan kasafin kuxi da kuma tsarin arzikin jihar kebbi, Alhaji Zailani Muhammad Yauri. Taron tattaunawar dai an shirya shi ne a qarqashin jagorancin babban Mai ba Gwamnan Jihar Kebbi shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Yusuf Haruna Rasheed. Mahalarta taron sun haxa da mambobbin majalisar dokoki ta jihar kebbi, Shuwagabannin jam’iyyar APC na qananan hukumomi 21 da ake da su a cikin jihar ta kebbi, kwamishinoni, manyan shuwagabanin jam’iyyar ta APC
•Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu.
matakin jihar da kuma sauran su. Daga qarshe an yi kira ga jama’ar Jihar Kebbi da su ci
gaba da bai wa jam’iyyar APC goyon baya domin qara cin gajiyar dimokraxiyya a jihar kebbi da kuma qasa baki xaya.
Mainan Zazzau Ne Ya Dace A Jihar Kaduna -Hajiya Hafsat Daga Balarabe Abdullahi, Zariya
An bayyana xaukacin waxanda suka fito takarar gwamnan jihar Kaduna a zaven shekara ta 2019 da cewar, babu wanda ya dace al’ummar jihar Kaduna su zava a qarqashin jam’iyyar PDP sai Mai-Nan Zazzau, Dokta Muhammad Sani Bello. Bayanin haka ya fito ne daga wata fitacciyar ‘yar siyasa da ke qaramar hukumar Sabon gari, mai suna Hajiya Hafsat Ibrahim, a lokacin da ta zaventa da wakilinmu da ke Zariya kan wasu da suka fito takarar neman gwamna a jihar Kaduna. Hajiya Hafsat ta ci gaba da cewar, in an dubi Dokta Sani
Bello, xan siyasa ne da ke da ked a kishin jama’a, kuma wanda tun kafin ya shiga harkar siyasa yak e tallafa wa al’umma, musamman matasa day a shafi ilimin da kuma samar ma su da sana’o’in dogaro da kaia a sassan jihar Kaduna, ba a qaramar hukumar Sabon gari kawai ba. Da kuma ‘yar siyasar ta juya ga matsayin Mai-Nan Zazzau a siyasa, Hajiya Hafsat Ibrahim ta nunar da cewar, tun daga lokacin da Mai-Nan Zazzau Dokta Sani Bello ya kasance a jam’iyyar PDP, ya rungumi jam’iyyar da hannu biyu, ta vangarori da dama, har da waxanda ke cikin jam’iyyar, ba tare da nuna
wani banbancin vangaranci ba kokuma addini. Waxannan halaye da Dokta Sani Bello ke da su, a cewar Hajiya Hafsat su suka sa al’ummar jihar Kaduna suka neme shi da ya fito takarar gwamnan jihar Kaduna a zaven shekara ta 2019, in mai duka ya kai mu. Hajiya Hafsat ta ci gaba da cewar, babu wani cikin waxanda suke son a tsayar da su takarar gwamna a jihar Kaduna da ya rungumi jam’iyyar PDP da hannu biyu a xaukacin qananan hukumomin jihar Kaduna 23, kamar Mai-Nan Zazzau, in ko za a duba cancanta da kuma yadda ya yi amfani da damar da ya ke da shi, ya rungumi
jam’iyyar da kuma magoya bayan jam’iyyar, musamman bayan zaven shekara ta 2015 da jam’iyyar PDP da kuma magoya bayanta suka tsinci kansu a wani hali na rasa madafun iko. A qarshen ganawar ta da wakilinmu Hajiya Hafsat Ibrahim, ta shawarci wakilan jam’iyyar PDP da aka fi sani da aka fi sani da [DELIGATE] da wajibi ne su sanya makomar jam’iyyar a zukatansu, ba abin da za su samu daga ‘yan takara ba, in kun yi haka, a cewar ta, za a sami mutum nagari da zai warware matsalolin da aka jefa al’ummar jihar Kaduna daga zaven shekara ta 2015 zuwa yau.
2019 : A Shirye Nake Da Duk Wanda Ke Taqama Zai Yi Amfani Da Kuxi -Na Kudu Daga Hussain Suleiman
Daga Munkaila Abdullah, Dutse Sanata mai wakiltar yankin Jigawa ta tsakiya Alhaji Sabo Muhammad Nakudu ya yi bayyana cewa, a shirye yake tsaf don tun karar duk wani xan takara daga jam’iyyar adawa ta PDP dake taqamar zai yi amfani da kuxi domin saye ra’ayin al’umma. Sanata na kudu ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya qaddamar da rabon kayayyaki ga al’ummar yankin sanatoriyarsa a ranar lahadin da ta gabata ya yin
gangamin taro wadda aka gabatar a sansanin taro na Malam Aminu Kano dake Dutse. Ya ce, babu ko shakka mun sami labarin cewa wasu ‘ya’yan jam’iyyar adawa na zagayawa suna rarrabawa mutane kuxaxe da niyyar su zave su duk da irin varnar da suka share shekaru 16 suna tafkawa akan karagar mulkin wannan qasa”. “To muna so su sani cewa, talakawa ba shashashai bane kuma sun san irin gudummawar da jam’iyyar APC ke bayarwa wajen farfaxo da tattalin arziqin wannan qasa gamida xorata
kan bigire nagari domin xorewar ci gaba”. Haka kuma ‘ina so in sanarwa da waxan can mutane da suka wawashe dukiyoyin al’umma cewa, ni kaxai na ishesu, idan kuma suna shakka to mu zuba” inji sanata Nakudu. Sannan ya kuma bayyana cewa, wannan rabon kayayyaki da suka haxa da motoci 16 da babura kimanin samada 120 gamida kayan sawa shadda da kuma tsabar kuxaxe kaxanne daga cikin manufofinsa da kuma jam’iyyar APC na saukakawa al’umma ta hanyar sama musu ayyukan yi domin
dogaro dakansu. Shi kuwa da yake nasa jawabin’ gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Abubakar Badaru ya tuhumi tsohon gwamna Alhaji Sule Lamido da cewa, abin kunya ne gare shi ya ce zai jagoranci al’ummar wannan qasa duk da irin ta’asar da ake zarginsa da yi a lokacin da yake gwamnan jihar ta Jigawa. Haka kuma ya yabawa sanata Nakudu bisa wannan hovvasa gami da kira ga al’umma da su ci gaba da marawa yunqurin gwamnatin APC baya domin ciyar da wannan qasa gaba.
12 LABARAI
A Yau
Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Dalilan Da Ya Sa APGA Ba Za Ta Shiga Zave A Nasarawa Ba -Labaran Maku Daga Zubairu T.M.Lawal, Lafia
Xan takarar Gwamnan jihar Nasarawa a qarqashin inuwar jam’iyyar APGA, mai alamar Zakara Honorabul Labaran Maku ya bayyana dalilin da ya sa Jam’iyyarsu ba za ta shiga zaven Qananan hukumomi da zai gudana cikin watan biyar a Jihar Nasarawa ba. Labaran maku ya bayyana haka ne ga manema Labarai bayan qaddamar da ginin ERCC dake yankin raya qasa na Ekke dake qaramar hukumar Doma. Ya bayyana cewa, tun farko ba abi qa’ida ba, saboda shugaban hukumar zave ta Jihar Nasarawa na yanzu xan jam’iyyar APC ne, kuma a dokar kujerar Shugaban zaven ba a bai wa mutumin da yake siyasa. Ya ce, amma wannan kowa ya san shi xan jam’iyyar APC ne, kuma yana da katin jam’iyyar, har ma ya tava zama Shugaban Qaramar hukumar Doma a qarQashin Jam’iyyar APC. Duk da cewa Jam’iyyun hamayya sun koka, amma gwamnati tana da manufa kan zaven ta qi ta saurari Jam’iyyun hamayya. Maku ya ce, idan da a ce tsakani da Allah za a yi zaven qananan hukumomi ya tabbata APC ko kansila
xaya ba za su ci ba. Saboda a zaven da ya gabata na shekarar 2015 APC ba ta ci zave ba, amma hukumar zave aka haxa kai da ita aka yi murxiya. Labaran Maku ya ce; yanzu al’umma sun qara gano manufar APC a qasar nan, babu wanda yake fatan ya kasance cikin wannan jam’iyya mara tausayi. Maku ya ce; zaven qananan hukumomin da za a yi hatta ‘ya’yan jam’iyyar ta APC su na kokawa saboda mutum yana buqatar yayi takara saboda yana da jama’a, amma sai gwamna ya sa qafa ya take su, ya zavo wanda yake so ya ce, shi ne kaxai zai yi takara. Ya qara da cewa mutane suna koka wa saboda wannan musgunawa da jam’iyyar ta ke yi masu. To su ma ‘ya’yan jam’iyyar ta APC kenan ake yi masu haka, ina kuma ga ‘ya’yan wata jam’iyyar? Honorabul Labaran Maku ya yi kira ga al’umma da su yanki katin zave saboda babban zave mai zuwa, su fito qwansu da qwarqwatarsu, su zavi wanda suke so. Ya ce, siyasa kamar kasuwanci ne idan ka kasa kayanka shi mai saya sai wanda ya ga dama zai saya. Saboda haka kada jama’a su xauki harkan siyasa ya
•Labaran Maku..
zama ko a mutu ko a yi rai. Ya ce; ribar siyasa a duniya ne ake yin ta kada ka yarda ka mutu saboda wani xan siyasa, kuma kada mutane su yarda ‘yan siyasa su riqa yi masu qarya da maganar addini. Labaran maku ya ce; addini mutum yanayi ne tsakaninshi da Allah amma siyasa ana yi ne domin neman duniya. Saboda haka ‘yan siyasa su daina Qarya da addini. Idan mutum bashi da jama’a ya je ya nemi jama’a kada ya tsaya yana cewa, ai
ni Musulmi ne ko kuma ni kirista ne ku zave ni. Maku ya ce; duk mutumin da zai yi adalci a zave shi ko Musulmi ne ko Kirista ne ko mara addini ne. Tunda farko labaran maku ya gayawa al’umman da suka taru cikin wannan cocin cewa; burinshi yaga al’umma suna zaman lafiya tare da abokan zamansu ya ce; babu addinin da yazo da tashin hankali kuma babu addinin da ya koyar da tashin hankali. Addinin Musulunci ko Kiristanci
suna koyar da yadda mutum zai samu sakamako duniya da lahirane. Saboda haka duk wanda ya kashe wani ya sani Allah ba zai kyale shi ba. Ya qara da cewa mutane su riqa bin koyarwan addini kada mutane su zauna kara zube su ce mune addin kaza ko kaza amma basubin koyarwan addin. Labaran maku ya ce babu bambancin yare ko qabila wajen Allah kuma Allah bai kyamaci wasu qabila ba da ya qyamace su da bai halicce su ba.
Za A Gina Gidan Yarin Arewa Maso Gabas A Bauchi Wanda Zai Ci Fursunoni 300,000 Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Za a gina gidan yari da zai lakume kimanin naira miliyan sha uku 13m na yankin Arewa Maso Gabas a jihar Bauchil. Gidan waqafin da aka tsara cewar idan aka kammala samar da shi zai ke cin Fursunoni dubu xari uku cikin kwanciyar hankali ba tare da cinkoso ko kuma matsuwa ba. Mai bayar da shawara na musamman wa Ministan harqoqin cikin gida, Alhaji Aliyu Gebi shi ne ya bayyana hakan wa masu farautar labaru a Bauchi. Ya ce, hakan na zuwa ne biyo bayan amincewa da shugaban qasa, Alhaji Muhammad Buhari da ya yi na sake gina qarin gidajen
yarin a dukkanin yankuna guda shida da duke faxin qasar ta Nijeriya. Alhaji Aliyu Gebi, wanda kuma tsohon mamba ne a majalisar wakilai ta tarayya ya ce gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya amince da biyan kuxin filin da za a gina gidan yarin, ta bakinsa “Ina miqa godiyata ga gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar da shi da Xan Malikin Boto sun taimaka sosai wajen samun wannan nasarar na samar da gidan yarin Arewa Maso Gabas a Bauchi,” A cewar Gebi. Dangane da gidan kason kuwa, ya ce gwamnatin tarayya ta yanke za ta gina gidan waqafin Arewa Maso Yamma a jihar Kano, inda kuma na Arewa Maso
Gabas aka amince da ginasa a Bauchi, ya ce xaukan matakin hakan na zuwa ne a sakamakon cinkosa da kuma lalacewar da waxanda ake da su a yanzu suka yi “Da yake akwai cikowar gidajen yarin da muke da su yanzu suka yi, sannan kuma sun tsufa, Arewa Maso Yamma an kai Kano, na Arewa Maso Gabas kuma aka ce a kawo Bauchi”. a cewar Gebin. Ya ce hakan na cikin namijin qoqarin gwamnatin tarayya ne na tabbatar da samar wa Fursunoni yanayi mai kyau domin samar musu da jin daxi da walwala, don yin zaman jarun cikin wanciyar hankali. Haka nan kuma, ya yi qira ga masu ruwa da tsaki a jihar Bauchi da su mara wa shirin baya domin a samu nasarar da aka sanya a gaba, ya ce ya
yi amfani da damarsa wajen roqon ministan harqoqin cikin gida Abdurraman Bello Dambazau domin ya amince da gina gidan yarin shiyyar Arewa Maso Gabas xin a jihar Bauchi don ‘yan jihar su amfana. Aliyu Gebi ya yi amfani da wannan damar wajen qalubantar masu ruwa da tsaki a jihar da suka haxa da gwamnan jihar Muhammad Abubakar da zavavvun mambobin majalisar wakilai da kuma na majalisar dattawa da suka fito daga jihar da su haxa kansu wuri guda domin kawo wa jihar aiyukan ci gaba mai ma’ana a maimakon su tsaya suna qalubantar juna wanda a cewarsa hakan ba zai kawo wa jihar wani ci gaba ba “Faxa na mene? Akwai wata jihar da ake irin wannan,
bayan ka je Kaduna ai su nasu Kaduna nasu barikanci ne, amma akwai wata jihar da ake irin wannan? faxar gangan ne kawai don kar jama’a su fahimci a tsaya a yi wa jama’a abun da ya kamata wannan kawai shi ne. Ka ga idan ba a yi kaza ba sai a ce gwamna ne bai yi ba; idan shi ma bai yi ba sai ya ce ‘yan majalisu suna bashi wahala, an gagara haxa kai, amma abun ba haka yake ba, haxin kan nan ya zama dole, idan ba a yi ba hatta shi kansa gwamnan ba zai ji daxin mulkin ba duk kuwa qoqarin da yake son ya yi,” A cewar Shi. Gebi sai ya yi qira ga al’umman jihar ta Bauchi da su goyi bayan shirye-shiryen gwamnati da suke da nasaba da inganta musu rayuwarsu a kowani lokaci.
LABARAI 13
A Yau Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Tsare Gaskiya Ke Kawo Ci Gaban Harkokin Kasuwanci -Danmaliki Daga Hussain Suleiman
Gaskiya da amana a lokacin gudanar da harkokin kasuwanci shi ke kawo ci gaba da kuma xaukaka da yardar Allah. Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban qungiyar masu sayar da Buhu na jihar Kano, Alhaji Mansur Ibrahim Danmaliki a lokacin da yake zantawa da manema labarai kwanakin baya. Shugaban qungiyar ya ce, ya kai kimanin shekaru 40 yana gudanar da wannan sana’a ta kasuwancin sayar da buhu, amma sakamakon kwatanta gaskiya da tsoron Allah ya sa har yanzu yake tafiyar da kasuwancin batare da wani fargaba ko tsoro ba. Alhaji Mansur Ibrahim, ya qara da cewa akwai sirri sosai a wannan sana’a matuqar ka tsaya a kan gaskiya da kuma iya hurxa da jama’a. Qungiyar a jihar Kano tana qara samun ci gaba idan ka kwatanta da shekarun baya suna kuma da yawa a jihar Kano ba sa yarda aka gudanar da duk wani abu da zai xata sunan qungiyar. Sai dai shugaban qungiyar a gefe guda ya nuna damuwarsa game da yadda wasu kamfanonin da suke hulxa da su ke cin karansu ba bu babbaka musamman yadda suke yawan qarin farashin kaya a duk lokacin da suka ga dama, wannan abin da kamfanonin ke yi na kawo masu cikas ga kasuwancinsu, sai ya shawarce su da su riqa zama da su lokaci domin ba su shawarwarin da suka kamata domin a gudu tare a tsira tare. Shugaban ya roki Gwamnatin tarayya da ta jihar Kano qarqashin Abdullahi Umar Ganduje, daya tuna da yayan wannan qungiya domin tallafa masu kamar yadda yake tallafawa sauran qungiyoyin yankasuwa a jihar Kano, ganin yadda sana’ar ta su ke bayar da gudunmawa wajen havaka tattalin arzikin jihar da qasa baki xaya.
Sannan gwamnan ya sassautawa ‘yankasuwar jihar wajen karvar haraji. Daga nan ya yi amfani da wannan dama da kira ga yan qungiyar da su qara haxakan da aka sansu da shi da kuma biyayya ga shugabancin qungiya domin ba’a samun nasara da ci gaba sai da samun haxin kai. Daga qarshe
Malam Mansur Ibrahim ya yi addu’ar Allah ya baiwa jihar Kano, da qasa baki xaya zaman lafiya da qaruwar arziki. Da fatan matasa za su qara qaimi wajen neman ilimin addini da na zamani da kuma koyon sana’oin dogaro da kai, waxanda zai rage musu zaman kashe wando.
•Alhaji Mansur Ibrahim Danmaliki.
An Shirya Wa Shugabannin Qananan hukumomin Jihar Kano Bita A Kan Tsaro Daga Hussain Suleiman
Kwanakin baya ne aka shirya wa xakacin shugabannin qananan hukumomin jihar Kano 44 bita a kan tsaro. An gudanar da taron ne a xakin taro na “Efficent” dake Kano, taron ya samu halartar shugabannin qananan hukumomi da mataimakansu da DPM da sakatarori da sauran masu fada aji dake qananan hukumomin na jihar Kano Da yake gabatar da jawabinsa ga manema labarai game da maqasudin shirya taron kwamishinan qananan hukumomi na jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya ce, an shirya taron ne domin faxakar da shugabannin muhimmancin samar da tsaro a yankunansu. Murta Sule Garo ya ce, samar da tsaro na xaya daga
cikin manufofin gwamnati Buhari da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, a kullum burinsu shi ne tabbatar da zaman lafiya da tsare rayuka da dukiyoyin al’umma. Kwamishinan qananan hukumomin ya na fatan shugabannin za su koma yankunansu domin shirya taro irin wannan sannan su tabbatar sun haxa da limaman masallalatan juma’a da hakimai da dakatai da masu unguwanni tare da sassa da suke samar da tsaro. Daga qarshe ya yi addu’ar Allah ya bai wa jihar Kano da qasa baki xaya zaman lafiya . Da shi ma yake gabatar da jawabin shi ga manema labarai shugaban qaramar hukumar Ungogo dake jihar ta Kano, Alhaji Aliyu Abubakar Muhammad cewa ya yi haqiqa sun amfana da
wannan taron bitar sosai sannan kuma zai qara masu qaimi wajen samar da tsaro aqananan hukumominsu. Shugaban qaramar hukumar ta Ungogo, ya qara da cewa zuwa yanzu harkokin tsaro sun canza a yankin na Ungogo domin da zaran sun ji wani abu da zai kawo barazana ta fannin tsaro sukan xauki matakin gaggawa. Har ila yau Aliyu Abubakar ya ce qaramar hukumar Ungogo suna da haziqan mutane da suka san harkokin tsaro, saboda haka za su zauna da hakimi limamai dakatai da masu unguwanni domin faxakar da su a kan taron bitar da aka shirya musu domin suma suyi koyi, ya ce haqqi ne a gare su wajen samar da tsaro domin kula da rayuka da dukiyoyin qaramar hukumar. Ya yi amafani da wnnan
dama da gode wa gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, wajen gudanar da aikace aikace masu muhimmacim domin ci gaban al’ummar jihar, wannan ya sa matuqar gwamnan ya sake tsayawa neman shugabancin jihar karo na biyu babu shakka qaramar hukumar Ungogo na daga cikin qananan hukumomin jihar 44 da za fara kawo kuri’un su da yardar Allah. Ali Namadi Bebeji shugaban qaramar hukumar Bebeji shi ma ya gode wa kwamishinan qananan hukumomin na jihar Kano game da tunanin da ya yi wajen shirya wannan taro mai muhimmanci a kan tsaro. Ali Namadi Bebeji ya ce, shi ma zai shirya taro irin wannan ga duk wani mai ruwa da tsaki dake qaramar hukumar.
Asibitin Abdullahi Wase Dake Kano Na Qara Samun Ci Gaba Daga Hussain Suleiman
A sibitin Abdullahi Wase da aka fi sani da a sibitin Nassarawa a jihar Kano, na qara samun xaukaka da ci gaba idan ka kwatanta da shekarun baya, ta yadda yanzu a sibitin za a iya sa shi a cikin sahun a sibitin da zai iya alfahari da shi a qasar nan baki xaya. Wannan bayani ya fito ne daga bakin babban manajan daraktan a sibitin Dakta Usman Tijjani Aliyu, a lokacin da yake zanatawa da manma labarai kwanakin baya a ofishinsa. Dakta Usman Tijjini Aliu, ya ce, tun lokacin da West African College Surgeon dake qasar Laberiya suka amince a fara koyawa
likitoci ilimin cututtukan mata da kuma ilimin kula da lafiyar qananan yara ya sa asibitin ya qara samun karvuwa sosai daga masana harkokin kula da lafiya. Domin ganin shirin koyawa likitoci kula da bincike a kan mata da qananan yara, ya sa yanzu haka an ware likitoci ‘yan asalin jihar Kano guda takwas da aka fara da su watanni biyu da suka wuce. Kafin a fara wannan karatu a jihar Kano sai ka je kamar a sibitin Malam Aminu Kano Ko jami’ar Jos ko kuma manyan a sibitoci dake qasar nan. Bayan wannan ci gaba a aka samu har ila yau gwamnan jihar ya sayi wani na ‘ura wanda yake gano cututtuka da ake kira “City Scan” wanda ya ce, yana da
matuqar wahala gaske ka samu irin wannan na’urori a asibitocin gwamnatin jihohin qasar nan . Usman ya ce, shekaru biyu da ya yi yana jagorantar asibitin ya samar da wayoyin hannu guda 50 inda aka raba su ga wasu muhimman wurare domin samun saukin sadarwa da abokan aiki kuma idan buqatar gaggawa ta ta so, kuma wannan wayar hannu baya aiki sai a cikin a sibitin kaxai. Matashin likitan ya ce, lokacin daya kama aiki ya iske kwanzaltan 6 ne kawai amma cikin shekaru biyu, ya samar da kwanzaltan 25 waxanda suka qware sosai a kan cututtukan zuciya da Fata da Koda da kuma cutar yara da sauransu.
Sannan kuma an samu ragowar cinkoso wajen ganin likita ta yadda yanzu tun daga safe har dare mara lafiya kan iya zuwa asibitin domin duba lafiyar su, an samar da asibitin ne shekaru 50 da suka gabata, abin farin ciki marasa lafiya na zuwa har daga wajen jihar Kano domin duba lafiyarsu, ya ba da misalin yadda masu fama da sutar qoda daga jihohin Borno da Yobe ke zuwa domin wankin qoda . Daga nan ya godewa gwamnan jihar Kano game da namijin qoqarin da yake yi wajen kula da harkokin lafiya a jihar musamman yadda asibitin na Abdullahi Wase ke kan gaba wajen samun ci gaba a cikin asibitocin jihar.
14 LABARAI
A Yau
Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
’Yan Bulawus A Kasuwar Qofar Wambai Sun Nemi Gwamnati Ta Tsawatarwa Kwastan Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Qungiyar masu saida bulawus ta Kasuwar qofar wambai “Blouse Sellers Association” da ake kira a taqaice da BOSAK ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta tsawatar wa jami’an hukumar hana fasa qwauri kan su daina kama musu kaya da suke zuwa suna sayo wa daga sassan qasar nan. Shugaban qungiyar Alhaji Xayyabu Salisu Sa’ad yayi wannan kiran ne a qarshen mako yayin wata zantawa da jaridar LEADERSHIP A Yau. Ya ce kama musu kayan da ake yana jawo musu koma baya a cikin harkar kasuwancinsu. Ya ce; “abu ne na cikin gida ba daga waje ba, idan da daga waje ne sai a ce sai ka biya kuxin fito, to amma muna cikin gida za muje mu sawo a Aba, Anacha ko Legas amma sai an biya wa kayan kuxi na musamman”. Ya ce suna sayen kayan Bulawus ne a cikin gida,idan wanda suka yi oda daga waje ya qare sai su je su sayo a Aba ko Anacha kafin ace sun sami viza da sauran qa’idoji da ake bi, dan kar a bar wurin haka.kafin aje a sayo. Alhaji Dayyabu Salisu Sa’ad yayi nuni da cewa kayan Bulawus basa daga cikin haramtattun kaya da aka hana shigowa dasu qasarnan, amma sai a karve musu asa wasu kuxi masu xinbin yawa sai sun biya a basu. Idan sun sayo daga kudancin qasar nan. Ya ce da a manyan motocin safa-safa suke sako kayan idan sun sayo, amma sai kwastam su kama, sai an bada kuxi sannan su saki kayan, sabo dayi sai masu xauko kayan a safa su riqa yin qarya, wani lokacin suce an kama kayan sai an biya kuxi bayan ba haka bane, sai an xan cuce ka wani abu, hakan ta sa suka yi tsari, motocin Arewa da suke kai tumatur in sun kai sai suka riqa amfani dasu suna xoro musu kayan Bulawus daga Anacha ko Aba amma daga Legas basu fiye xorowa ba saboda tana da bambanci. Wanna ya sa suka sami sauqi a vangaren inyamurai. Ya qara da cewa amma a hakan duk mota xaya sai mun ware mata Naira 45,000. “Wannan abin ya yi yawa, a cikin gida muke saya, ka sayo daga jaha zuwa jaha amma sai ka biya wasu kuxi” Alhaji Xayyabu Salisu Sa’ad ya ce idan akace watan Sha’aban ya kama zuwa
azumi, watan Sallah dana kirsimeti yan kasuwar ta Bulawus kan taso xinbin motoci yawanci J5 sama da 20 a kullum da ake ware musu Naira 45, 000 kuxin hanya idan aka lissafa Naira 45, 000 kuxin motoci 10 kawai, za a sami suna bada Naira 450, 000 kullum da kwastam ke karva a hannunsu tareda wani dalilin doka akan hakan ba. Ya ce ko yan Bulawu na Kaduna sun tava yi musu qorafin cewa abin yayi yawa da yake su suna qoqarin su biyo motocinsu da suka xorawa kaya da kansu ba kamar na kano ba, da basu fiye biyo wa ba, sun ce ma yanzu jami’an hana fasa kwauri sun qaru a hanyar abin yayi yawa. Shugaban masu saida Buawus xin Alhaji Xayyabu Salisu Sa’ad yayi kira ga Gwamnatin Tarayya akan a sauqaqa musu wannan abu tunda harkace ta cikin gida a duba kayansu idan akwai doka
akansu a bayyanasu idan babu a taimaka a tsawatarwa hukumar Kwastam a janye musu matsalolinda ke addabarsu tunda mulki ake na Damakwaraxiya yanda kowa kejin zai mori romonta suma a basu su sha, amma abin takaici a mulki na Damakwaraxiyya ana matsa musu kamar na soja, abin ba daxi dukiyarsuce, amma anata yi musu barazana a kanta. Xayyabu ya kafa wani misali da cewa an tava kama masa kaya saida ya biya Naira 500, 000 aka fitar masa, Akwai wanda kayanda aka kama a kaduna saida aka bada Naira 950, 000 sannan aka bada kayan. Duk lokacin da aka kama musu kaya suna bibiya akan a sakar musu, amma basu tava samun zamada manyan hukumomin Kwastam dan kai musu qorafinsu akan hakan ba, sai dai sunanan suna qoqarin bin duk hanyar da
•ALHAJI DAYYABU SALISU SA’AD.
ta dace dan ganin Gwamnati tasa an kawar musu da wannan cusgunawa da ake musu a harkokin sana’arsu
a matsayinsu na yan qasa da suke da ikon su je kowane sashe na qasar nan domin saye da sayarwa.
Noma Ne Ya Ceto Nijeriya Daga Karayar Tattalin Arziki -Jakadun Qasashen Waje Daga Abubakar Abba
Jakadun da suka fito daga nahiyar Afrika da muna na nahiyar turai sun jinjinawa Nijeriya akan qoqarin da ta yi wajen yin amfani da harkar aikin noma wajen tsamo qasar daga cikin karayar tattalin arzikin qasa data faxa a baya. Sun yi wannan yabon ne a taron baje kolin kayan amfani noma karo na huxu dake gudana a jihar Legas. A cewar wakilin tawagar jakadun nahiyar turai Ibi Ikpoki, harkar aikin noma ya taka muhimmiyar rawa wajen tsamo Nijeriya daga cikin karayar arziki data tsinci kanta a ciki. Ya ce, harkar ta aikin noma, ta kuma bayar da gudunmawa wajen samar da ayyukan yi musamman a tsakanin mata da matasa da kuma taimakawa wajen yaqar talauci. A cewar sa, “ ina mai matuqar bayyana jin daxi na ayau akan cewar harkar noma a Nijeriya ta wuce ace kawai harka ce ta kasuwanci, amma har da inganta samar da abinci a mataki na farko.” Ya yi nuni da cewar, shi ya sanya baje kolin na bana ya
sha bamban da da sauran na baya musamman don ciyar da harkar noma a gaba a tsakanin sauran masana’antu. Mista Ikpoki ya kuma taya gwamnatin Nijeriya murna akan inganta yadda ake gudanar da kasuwanci a qasar nan. Ya kuma buga misali da adadin harkar kasuwanci ta nahiyar turai, inda ya ce, jimlar kasuwanci ta nahiyar turai a Nijeriya ta qaru daga kashi 27 bisa xari zuwa biliyan 19.9 na kuxin nahiyar turai a shekarar 2016 zuwa kuxin nahiyar turai biliyan 25.3 a shekarar 2017. Ya qara da cewa, “wannan kasuwancin ya qara samar da hanyar havaka hadahadar kasuwancin Nijriya a qasashen waje musamman yadda qasar ta fita daga cikin karayar tattalin arziki a shekarar 2017.” Ya ce, “ina son yin amfani da wannan damar don ta ya Nijeriya murna a akan nasarar da ta samu wajen fita daga cikin karayar tattalin arziki a shekarar 2017, har da inganta yadda ake gudanar da kasuwanci a qasar.” A cewar sa,” a bisa ma’auni munga yadda Nijeriya ta yi
sama ta kai ta 24 daga cikin 169 zuwa 145, inda kuma ta zamo zakara daga cikin qasashe goma da zuka ci gaba a cikin qasashe. Har ila yau, Mista Ikpoki ya kuma yi tsokaci akan qarin zuba jarin da nahiyar turai ta yi a Nijeriya, duk da tsaikon gudanar da mulki akan kasuwanci nahiyar Afrika. Shi kuwa Jakadan qasar Netherlands a Nijeriya Mista Robert Petri ya ce, kayan kimiiya da fasaha da kamfaninin qasar Jamani suka baje a kasuwar ta baje kolin, zasu inganta harkar noma a Nijeriya. Ya qara da cewa, kayan na kimiyya da fasaha da qasar Netherlands ta baje za su kuma samar da mafita ga harkar noma da qayyade yawan qaruwar al’umma da canjin yanayi wanda Nijeriya itama tana fuskantar wannan barazanar. Shi kuwa a nashi jawabin jakadan qasar Faransa Laurent Polonceaux ya ce, qasar sa ta yi haxaka da Nijeriya akan harkar noma, inda hakan ya sanya kamfanoni hamsin na qasar suka shigo baje kolin. Shi kuwa jakadan qasar
Austria a Nijeriya Nella Hengstler yabawa waxanda suka shirya taron na baje kolin ya yi, inda ya yi nuni da cewar, nahiar Afrika sabuwa ce wajen yin baje kolin amfanin gona. Ya ce, “duk da matsalar samar da Biza da kuma sauran abubuwa da suka shafi tafiye-tafiye, ina ganin wannan ya bayar da ma’ana zuwa nan don yin baje kolin kayan mu.” Babban Kwamishinan riqo na Afrika ta Kudu a Nijeriya Bobby Moroe a nashi jawabin ya ce, baje kolin ya samar da gagarumar dama ga nahiyar Afrika da Nijeriya, wannan ba qaramar dama bace ga Afrika da Nijeriya. In za a iya tunawa shugaban qasa ya tava furta cewar, Nijeriya baza ta dogara kacho kam akan mai ba har abada. Baje kolin na kayan amafnin gona shine karo na huxu da aka gudanar a Nijeriya, inda qasashe kamar China da Turkiyya da suran ‘yan kasuwa na Nijeriya da suma suka baje kolin nasu kayan. An ruwaito cewar, kimanin sama da masu baje koli 80 ne suka baje hajar su.
A Yau
RAHOTO 15
Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
PWYSIB Ta Horar Da Mata 210 Kan Sana’o’in Dogaro Da Kai A Liman Katagum Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Wata qungiya mai zaman kanta mai fafutukar inganta rayuwar mata da matasa a shiyyar Arewa Maso Gabas wato ‘Progressive Women and Youth Support Initiative’ reshen jihar Bauchi ta baiwa matasa xari biyu da goma a garin Liman Katagum da ke Bauchi jari da zimmar aza musu tubalin ci gaba da sana’a domin dogaro da kawukansu, kafin nan qungiyar ta baiwa matan horon ne kan sana’o’in hanu daban-daban. Sana’o’in da qungiyar ta inganta rayuwar mata da matasan ta baiwa mata a garin na Liman Katagum sun haxa da xinki, saqa, kayan kamshin daxi, haxa sabulai, turare, da sauran sana’o’in hanu domin dogaro da kai. Matan da suka ci gajiyar tallafin sun haxa da waxanda mazajensu suka rasu ko suka sakesu, marayu da marasa galihu da kuma ‘yan matan da suke zaune a gidajensu babu abun yi ga kuma qarancin akwai da ke addabarsu, qungiyar ta bakin Ko’odinatan qungiyar taimaka ta fuskacin inganta rayuwar mata da matasan, Hajiya Aishatu Jafar Bashir ta bayyana cewar sun zaqulo waxannan matan ne domin a cewarta irin taimakon da ya dace kenan a basu a irin wannan lokacin domin taimaka a wa rayuwarsu. Da yake jawabi a wajen a fadar Sarkin Liman Katagum, Sakataren Janaral qungiyar ‘PWYIB’ Barista Hussaini Suleiman Saraki ya fara ne da bayyana cewar sun kafa wannan qungiyar ne a watan Junairun 2017 da nufin taimaka wa mata, matasa, da kuma marasa galihu a Nijeriya musamman shiyyar Arewa Maso Gabas ta fuskacin tallafa. Barister Saraki ya kuma qara da cewa “Muna yin aiyuka da dama a sassa daban-daban musamman a jihar nan ta Bauchi, don ko a kwanakin baya ma mun je wasu qananan hukumomi mun kai tallafi, a yau ne muka zo gabanka domin mu shaida maka cewar mun baiwa mata 210 horo kan sana’o’in dogaro da kansu, don haka a yau ne muka zo domin mu yayesu mu kuma basu jarin da za su ci gaba da
riritawa domin a samu rage musu raxaxin talaucin da ke addabar al’umarmu a yau,” In ji Barista. Baristan ya shaida wa Sarkin Liman Katagum xin cewa, ba kawai sha’anin sana’a ne qungiyarsu take taimaka wa a kai ba, ya shaida cewar hatta fannonin ilimi da lafiya duk suna duba yadda za su yi domin bayar da tallafi a kowani lokaci domin inganta rayuwar jama’a da kuma nuna wa marasa galihu cewar suna da gatansu. Da yake maida jawabi a lokacin da NGOs suka iso fadarsa domin yaye matan da suka samu horo kan sana’o’in, Mai martaba Sarkin Liman Katagum Alhaji Yakubu Abubakar Ghani ya gode wa Allah matuqa a bisa samun wannan tallafin da al’umman masarautarsa suka yi, yana mai nuna godiyarsa matuqa da tallafin da qungiyar ta yi wa talakawarsa. Ya ke cewa “Idan ka koya wa mutum sana’a don ya dogara da kansa har ga Allah ka taimaka wa rayuwarsa, domin Allah kaxai ya san wa zai taimaka a kai, amam don ka xauki kuxi ka baiwa mutum abun da zai yi amfani da shi yanzu to baka taimakesa ba, don haka muna godiya kwarai da kuka kawo wannan tallafin a masarautar nan” In ji Sarkin. A nata jawabin, Ko’odinatan qungiyar taimaka ta fuskacin inganta rayuwar mata da matasan, Hajiya Aishatu Jafar Bashir, ta bayyana cewar sun kasance a garin
Liman Katagum ne domin raba wa matan da suka samu zarafin zavarsu domin cin gajiyar wannan tallafi, ta bayyana cewar nan gaba ma za su sake duba wani bigiren domin tallafa. Jami’ar ta yi bayanin cewar qungiyar ta bayar da horo na tsawon makonni kan sana’a daban-daban da za su taimaka wa matan kan tsayuwa da qafafunsu, sai ta bayyana cewar bayan kammalawa bayar da horon ne kuma mai Sarautar Uban Dawakin Bauchi, Alhaji Abdu Aliyu Ilelah wanda kuma yake da zimmar tsayawa takarar kujerar xan majalisar tarayya da ke wakiltar mazavar Bauchi ta tsakiya a majalisar wakilai ta qasa a 2019 ya xauki nauyin sayen dukkanin kayakkin da za a raba wa matan 210 da suka samu horon don ya zama ba barsu haka da zallar horon kaxai ba. Mai xaukan tallafin da kayan da aka raban, Abdu Aliyu Ilelah (Uban Dawakin Bauchi) ya ce wa ‘yan jarida “Na zo nan ne a matsayin baqo na musamman domin na raba kayyakin tallafin dogaro da kai wa waxanda suka yi karatu suka koyi sana’o’I na hanu. Mata 210 ne suka samu cin gajiyar wannan tallafin a wannan lokacin a cikin wannan garin na Liman Katagum,” Ya bayyana cewar a qarshe suna fatan matan da suka samu cin gajiyar tallafin su yi amfani da ababen da suka koya da kayyakin da suka samu domin ci gaba da
riritawa, ya horesu da kada su yi garajen saidawa ko kuma yin sako-sako da kayyakin da aka basu “Muna son wannan horon da suka samu ta zama hanyar da za su dogara da kawukansu ba sai sun je suna maula ko suna roqon a yi musu wasu abubuwan buqatun rayuwa ba; su yi amfani da wannan horon don bunqasa rayuwarsu da kuma yin amfani da wannan damar wajen koyar da wasu,” In ji Mai rike da sarutar Uban Dawakin Bauchi. Xaya daga ciki waxanda suka ci gajiyar shirin Halima Sunusi ta bayyana cewar “A gaskiya ban san irin kalmomin da za mu yi amfani das u wajen nuna godiyarmu ba; waxannan sun zo rana tsaka suka ce za su koya mana sana’a muka zo suka koyar da mu, ba mu tsammaci komai daga garesu ba sai ga shi yau sun kawo mana kayyakin da muka koya kyauta domin mu ci gaba da riritawa, muna godiya Allah ya saka,” In ji ta Tun da fari mai dai, isar tawagar qungiyar masu tallafin zuwa Liman Katagum said a suka fara isa zuwa fadar Galadiman Bauchi Surveillance Sa’idu Ibrahim Jahun wanda kuma shi ne ke rike da sarautar Hakimin Liman Katagum wanda ya samu wakilcin Abdullahi Shamakin Galadima ya nuna gamsuwarsa kwarai da fatan alkairi a bisa aikace-aikacen qungiyar sai ya gode musu bisa himmarsu na taimakon marasa qarfi a tsakanin al’umma.
16
Siyasa A Yau A Yau
Talata 3.4.2018
2019: Tsaffin Janarori Ba Su Isa Su Hana Buhari Lashe Zave Ba –Fadar Shugaban Qasa Daga Umar A Hunkuyi
Fadar Shugaban qasa ta nu na tabbacin da take da shi na cewa, babu xaya daga cikin tsararrakin Shugaban qasa a aikin soja kuma tsaffin shugabannin qasarnan da suke baiwa Shugaba Buhari shawarar kar ya sake tsayawa takarar neman shugabancin qasarnan da ya isa ya hana shi sake tsayawa takarar a 2019. Babban mai taimakawa Shugaban qasan a kan harkokin manema labarai, Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Abuja. Ya ma qara da cewa, da tsaffin Janarorin za su nemi tsayawa takarar da Shugaba Buhari, falan xaya zai kayar da su a zaven. Tsohon Shugaban qasarnan, Olusegun Obasanjo, da kuma Tsohon Shugaban qasa, Ibrahim Badamasi Babangida, ne suka baiwa Shugaba Buhari, shawarar kar ya sake neman tsayawa takarar a zaven 2019, a farkon wannan shekarar. Kakakin Shugaban qasan ya ce, shi zai baiwa Shugaba Buhari, shawarar ya sake tsayawa takarar domin tabbas ya cancanci zama Shugaban qasa a karo na biyu, in ji shi. Ya ce, “Ni shawara ta a gare su, (Tsaffin Shugabannin) ita ce, idan suna sha’awa ne, to su ma su fito su tsaya takarar mana tare da shi. Dukkan su nan take zai kayar da su.” Shehu ya ce, ya zuwa yanzun Shugaba Buhari, bai fito ya shelanta tsayawa takarar na shi ne ba kasantuwan ya mayar da hankalin sa ne wajen tunkarar matsalolin da qasar nan ke ciki. “Gyaran qasa ne a gaban Shugaban qasa a halin yanzun. Shi Shugaba ne
•Shugaban Qasa Muhammadu Buhari a lokacin da yake yaqin neman zaven shekarar 2015.
wanda ba wai zaman Ofishin ne ya dame shi ba. Duk da cewa, kowa yana kiran sa da ya ayyana takarar na shi, a karo na biyu, amma dai shi bai ce uffan ba, domin ya mayar da hankalin sa ne wajen gyaran matsalolin qasa,” in ji Shehu. Ga masu bukatar Shugaba Buhari, ya fito ya ayyana takarar na shi, alhalin mutane suna cikin yunwa, sai Garba Shehu ya ce, “Duk da surutan da Jam’iyyar PDP ke yi, a lokacin da su ke kan mulki, sun iya ciyar da mutanan qasarnan sau uku a rana ne? akwai qasar da ba mayunwata ne a duniyar nan? Ba cewa nake hakan daidai ne ba, amma dai siyasa ce kawai su ke yi. “Wannan gwamnati ce da ta raba qasarnan da abin kunyan nan na shigowa da abinci daga waje, dukkanin Jihohin qasarnan suna kan aikin noman shinkafa, a yanzun ba Nijeriya ce kaxai muke ciyarwa ba, dukkanin qasashen yammacin Afrika ne muke ciyarwa. A yanzun kuma gwamnati na aiki tuquru wajen ganin an sami sauqin farashin kayan abinci, farashin kayan
abincin yana ta sauka a hankali. Duk mai kukan yunwa ya kama hanyar gona ya yi noma mana. “Sannan kuma wannan gwamnatin ce kaxai ta vullo da tsarin sauqaqewa talakawa raxaxi, muna biyan talakawa mafi qaranci Naira 5000. Ga kuma ayyuka nan da yawa da muka samar, ga basuka kala-kala waxanda ke da kuxin ruwa kaxan a wasu lokutan ma sam babu kuxin ruwan a cikin su. Ga Bankin masana’antu, Bankin Manoma, Bankin bunqasa qasa da dai sauran su. Don haka akwai hanyoyi da yawa na taimakawa musamman ga mutane da suke a shirye da su yi aiki, musamman a fannin aikin gona.” Kakakin na Shugaban qasa, ya yi nu ni da cewa, Buhari zai ci gaba da yin aiki da Ministocin sa bakixayan su, tun da har ya zuwa yanzun babu xayansu da ya sallama daga aiki. Kamar yanda wasu ke neman a yi hakan. Da yake mayar da martani ga masu ganin gazawarsa kan kasa yin garanbawul a majalisar
Ministocin na shi, sai Shehu ya ce, “Shugaban qasa shi ne ya xauke su aikin, don haka ya san matsayin kowa daga cikin su. Idan har bai kori kowa ba daga cikin su, hakan ya nu na yana jin daxin aiki ne tare da su. “Kila masu neman a canza sun, suna da kwaxayin su su maye makwafin su ne. in kuwa haka ne, ashe ka ga son rai ne kawai. A matsayin shi na Shugaban qasa, kuma Babban Kwamandan askarawan qasarnan, shi yake da da ikon xauka da sallama. Daga nan sai Shehu, ya kare batun yin afuwa ga ‘yan ta’addan Boko Haram, inda ya ce, sam babu laifi da yin sulhu da maqiyi. Ya ce, “Duk mai yaxa wannan jita-jitan, na cewa wai an yafewa ‘yan Boko Haram da sauran su, ina tambayan su, wane ne ba ya son ya yi sulhu da maqiyin sa? Ko ma dai mene ne, kamar yanda masu magana ne ke cewa, ‘kowane yaqi a zauren tattaunawa ne ake qare shi.’ A fagen daga kana iya murqushe maqiyinka, amma kuma dai a qarshe tilas sai an koma zauren
Ci gaba a shafi na
17
SIYASA 17
A Yau Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
2019: Tsaffin Janarori Ba Su Isa Su Hana Buhari Lashe Zave Ba –Fadar Shugaban Qasa Ci gaba daga shafi na
16
•Wadansu magoya bayan Shugaban Qasa Muhammadu Buhari lokacin wani gangami da suka yi a Bauchi na murnar cikarsa shekara uku da lashe zaben shugaban kasa ranar Asabar xin da ta gabata.
tattaunawa domin a warware matsalolin. “Don haka, matsawar dai ‘yan Boko Haram, za su ajiye makaman su, su daina faxa su kuma daina yaxa wannan baqar karantarwar na su, tabbas ba abin da zai hana qasa ta rungume su, su dawo kamar kowa su ci gaba da ayyukan gina qasa. Da hakan, ka ga mun rage kashe kuxaxenmu kenan a kan yaqi, mun kuma ceto rayukan da ake ta salwantarwa, ta hanyar jefa Bamabamai, kashe Jami’an tsaro za kuma mu daina kashe kuxi wajen sayo makamai, inda za mu yi amfani da waxannan kuxaxen wajen aiwatar da wasu mahimman ayyukan raya qasa. ko ma dai mene ne, hakan nasara ce.” Ya qara da cewa, zargin wai cewa, Shugaba Buhari, yana goyon bayan Makiyaya, wannan surutun yanar gizo ne kawai. “Wannan gwamnati ce da ta yi abubuwa masu kyau, ga Shugaban da ya xauki rantsuwa kan zai kare tsarin mulkin qasa, ya kuma kare rayukan ‘yan qasa da dukiyoyin su bakixaya, ba daidai ne ba a ce zai kare duk wani mai laifi. Batun ma shi ne, Shugaban qasa yana riqe da madafa guda ce ta mulki,
su Gwamnonin me suke yi? Ko su ma Gwamnonin duk Makiyayan ne suke karewa daga hukuntawa?” Shehu bai yarda da masu cewa, Shugaba Buhari, ya gaza ba wajen magance matsalar tsaro. Ya ce, “Matsalar rikicin Manoma da Makiyaya tana nan tun daga lokacin da muka sami ‘yancin kai. Idan ka karanta tarihi, za ka taras daman manoma da makiyaya suna yin faxa kan mallakan filaye a qasarnan, tun zamanin da Turawan mulkin mallaka suke nan. Don haka rikicin na su ba wani sabon abu ne ba.” “Amma fa ba cewa nake yi hakan abu ne mai kyau ba, amma ina ganin ana qara kambama lamarin ne kawai a yanzun, kafofin yaxa labarai ne ke qara ruruta lamarin, saboda kuma ‘yan adawa ba su da wata sukan da za su iya yi wa Shugaba Buhari, face su fake da irin waxannan lamurran kawai. Ba za ka ji su na magana a kan yaqin da ake da cin hanci da rashawa da sauran laifukan da ke karya tattalin arziki ba, domin wannan waje ne da ambatan sa ma yakan firgita su. Ba za ka ji suna maganan samar da manyan ayyukan raya qasa ba a gwamnatin ta
Buhari, ko batun hanyoyin da ake bi domin bunqasa tattalin arzikinmu, wanda wannan gwamnatin ta samu nasarori masu yawa a vangaren su, a yau, muna da manoman shinkafa milyan 12 a qasarnan, mun kuma samar da sabbin ayyukan yi har milyan 6. “A fannin noma kaxai, shigowa da abinci ya yi qasa da kashi 95, yanzun mu ke ciyar da kanmu. A wannan shekarar gwamnati tana shirin hana shigowa da shinkafar kwata-kwata. Yanzun muna rage dogaron da muke yi da albarkatun man fetur, muna komawa gona, da kuma qere-qere. Ban ce rikicin da ake yi tsakanin manoma da makiyaya daidai ne ba, amma dai muna qoqari qwarai da gaske. Ayyukan da Jami’an tsaro ke yi a yankunan na Arewa ta tsakiya, sun kai ga nasarar qwato makamai masu yawa da duk aka mallake su ba bisa qa’ida ba, wanda ‘yan banga da kuma makiyayan suka mallaka. Da yake amsa tambayar ko maki nawa zai baiwa gwamnatin ta Shugaba Buhari, musamman a kan aiwatar da manyan ayyuka, Shehu ya ce, “Ai bayanan na nan a sarari, kowa na
iya zuwa ya duba, ba wata gwamnati da ta tava zuba jarin da gwamnatin mu ta zuba, kuma take kan zubawan, a kan aiwatar da manyan ayyukan. tun daga ranar da Buhari ya karvi mulki, ya sanya cewa, a duk kasafin kuxi a keve abin da bai gaza kashi 30 ba domin aiwatar da manyan ayyukan. Ai ba tare da manyan ayyuka ba, ba wata ci gaba da za mu iya ginawa. “A lokacin da wannan gwamnatin ta zo, kuxaxen tafiyar da gwamnati su ke laqume tsakanin kashi 95 zuwa 96, an bar manyan ayyukan da kashi 5 ko 6 ne kacal. Don haka baiwa wannan sashe kashi 30 ya haifar da ci gaba mai tarin yawa, a yanzun haka. Akwai manyan ayyuka masu yawa da ake gudanarwa a yanzun haka, kamar na gina sabbin hanyoyin Jiragen qasa, da kuma sake fasalin tsaffin tsarin da muke da shi na hanyoyin Jiragen na qasa, ga hanyoyi nan ana ta ginawa ko’ina a cikin qasa… Wannan gwamnati ce da ta kashe Naira tiriliyon 1.3 wajen aiwatar da manyan ayyuka, a kasafin kuxin shekarar 2016 kaxai, ta kuma kashe abin da ya yi kama da hakan a kasafin kuxin 2017.
18
A Yau
Muryar Talaka...
Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Tare da Bishir Dauda 08165270879
Mu Tattauna Ranar 24-3-2018 ce ranar da qungiyar Muryar Talaka Reshen Jihar Katsina ta gudanar da taron da ya kunshi masu ruwa da tsaki wadanda suka hada da shugabanni, qungiyoyin farar hula, ‘yan siyasa, ‘yan jarida da daidaikun jama’a. Taken taron shi ne: Tattaunawa game da yadda za a inganta rayuwar talaka. An fitar da fannoni guda uku da akai tattaunawar kansu. Wadannan kuwa sun hada da Kasafin kuxi, kiwon lafiya da kafafen yada labarai. Wannan tattaunawa ta gudana a xakin taro na otel din Katsina Motel, kuma an fara gudanar da taron wajen karfe goma da minitina 40. Dalilin shirya wannan taron kamar yadda shugaban qungiyar Muryar Talaka Reshen Jihar Katsina, Kwamared Kabir Shehu Yandaki ya bayyana shi ne idan akai la’akari da dimbin matsalolin dake fuskantar Talakan Nijeriya, to har yanzu bukatar shirya tarukan nemo mafita ba sui kadan ba. Taron karawa juna sani a kasa kamar Nijeriya inda rashin gaskiya da kokarin boye gaskiya ya kazanta abu ne mai matukar muhimmanci. Har yanzu lokaci bai yi ba da za a daina tara mutane domin a fada ma juna gaskiya, koma ba domin komai ba, kasar kwata-kwata shekarunta 58 da samun ‘yancin kanta. A ma wannan lokaci har yanzu ba a fita daga magagin mulkin mallaka ba. Kai wasu ma na ganin fa har yanzu mulkin mallakar ake yi ma Talaka. Bambancin kawai shi ne, yanzu ‘yan uwanmu baqaqe, wani lokacin ma Allah daya ake bautamawa amma ke mamu mulkin fir’aunanci. Idan aka dubi matsalolin da taron yai bita kan su, abubuwa ne da suka shafi rayuwar talaka kai tsaye. Misali mu dauki kasafin kuxi. Duk wata karya da wani xan siyasa ko wani shugaba zai yi na inganta rayuwar talaka, to dole fa sai an kai abin a cikin kasafin kuxi. Kasafin kuxi doka ce cewa ba a taba kudaden gwamnati haka kawai. Kuma tsari ne dake yi ma gwamnati jagora wajen gudanar da aikace aikacenta. Ayyuka kalilan ne, wadanda basu da muhimmanci za a iya gudanarwa ba tare da an sanya su cikin kasafin kuxi ba. Sai dai kash duk da muhimmancin kasafin kuxin, an maida shi wani abu kamar na wasu ‘yan tsirarru. Mutanen da suke rike kasafin
•A wurin taron na muryar talaka kwanakin baya.
kuxin su yi yadda suka ga dama da shi ba su wace ‘yan majalisu da bangaren zartaswa ba, sai kuma shugabannin hukumomin gwamnati. Sai sun kammala komi, sannan za su kira ‘yan qungiyoyin farar hulal da suke so, su zo taron jin ba’asi inda mafi akasari ba aiki ake da shawarwarin qungiyoyin ba. Idan ma talakan bai cikin qungiyoyin, to bama zai san abin da ake ciki ba. A muqalar da ya gabatar wajen taron Injiniya Muttaka Rabe Darma ya ce duk da kasafin kuxin da ake yi duk shekara, Katsina na cikin jihohin da suke fama da talauci. Ya samo hujjojinsa daga wasu cibiyoyi masu bada alkalumma kan ci gaba. A cikin kasidar kuma ya nuna kasafin kuxin da ake yi a Katsina bai kunshi bukatun talaka wa ba. Komai dai menene a bayyane take cewa ba kasafai ‘yan siyasa ke maida hankali kan abubuwan da suka damu talaka ba. Misali, akwai kauyukanmu dake cikin lunguna inda babu asibitoci, amma sai a dawo cikin birane da manyan garuruwa ana gyaran asibitoci. Wani kauyen, ruwan korama ake sha shekara da shekaru, maimakon a samar da ruwa, sai a dauki kuxin karamar hukuma a gina masu kasuwannin zamani, inda daga qarshe kasuwannin ba zasu inganta tattalin arziki, kauyen ba, sai dai su koma mafaka ta ‘yan shalisha da kodin, da masu lalata kananan yara. Ko kuma matsalar ilimi ta karancin malamai ce a makaranta kaza, amma sai aje ana fenti, a bar makarantar ba mai koyawa. Mafi akasarin ma, makarantun da aka fi gyarawa sune wadanda ke
bakin hanya, amma an bar na cikin lunguna a lalace. Wasu masana, na ganin dalilin da yasa ‘yan siyasa suka fi baiwa gine-gine muhimmanci shi ne, an fi satar kuxi ta nan. Misali nawa za a sata ta hanyar daukar ma’aikata? Kusan ba a bin da ake samu sai ma hidima da zata karu. Maimakon a maida hankali wajen horas da malaman makaranta da na asibiti, ko wurin gina dakunan karatu da na bincike da zuba masu ingantattun kayan aiki, sai a koma wani abu daban. Wannan kwaskwarimar ce ta hana komi ci gaba a Nijeriya. Muqala ta biyu wadda Dokta Abubakar Kurfi ya gabatar, ta maida hankali kan matsalolin kiwon lafiya, musamman Inshorar kiwon lafiya. In ba yanzu ba da aka samu dan arewa na jagorancin NHIS, mu nan Arewa ma ba mu damu da muhimmancin inshora ba. Wasu ma in kai masu maganar Inshora suna iya kafirta ka. Yanzu ne Farfesa Yusuf ke kokarin wayar da kai a Arewa, inda har ta jawo masa bita-da kulli daga ministan shi. Matsalolin kiwon lafiya a Nijeriya yawa gare su. Kullum ana kasafin kuxi akan kiwon lafiya, amma a banza. A cewar Dokta Abubakar Kurfi, talakawan kasashen da suka ci gaba ba su sayen kiwon lafiya. Koda suna saye, to baida wani tsada. Ya ce a inda mutum keda daraja, to duk abin da ya shafi kiwon lafiya, ilimi to gwamnati ce ke bada su.A nan Nijeriya, abun ba haka bane. Masu kuxi ne ke iya samun kulawa mafi inganci , domin idan mutum yana son kada ana magani daban kaba daban, to dole ya tafi asibitin kuxi. A nan Nijeriya babu ma wadatattun cibiyoyin kula da
lafiyar. Indiya da Masar can masu kumbar susa ke zuwa a duba lafiyarsu. A nan sai dai ka je asibiti, inda za ka hadu da wulakancin nas ko likita. Muna jin yadda ake kashe mutane a asibitocinmu. In da sauran shan ruwa, mutum zai fuskanci wulakanci, kusan wasunmu na tunanin ko wulakanta majinyata na cikin kwasa-kwasan da ake koyawa a makarantun horas da malaman asibiti! Wai ga wanda ma keda ikon zuwa asibitin. Wasu ai sai dai asha maganin na wagini baban Ai’sha magananin dake maganin kowace irin cuta. In da sauran jahilci kuma sai dai a tai wurin dan tsibbu, mutum na fama da cutar daji, dan tsibbu na gaya mai sihiri ne. Saboda lalacewa da cin hanci da rashawa da tai ma sashen lafiya dabaibayi, cututtukan da tuni aka magance su a wasu kasashen da suka san ciwon kansu, mu har yanzu kokari ake a magance su da hano da katsari. Allah ya kyauta. Muqala ta qarshe da muka tattauna wajen wannan taro ita ce, wadda Muhammad Bashir Ruwan Godiya yai kan yadda za a inganta aikin jarida. A cewar Dokta Mukhtar El-Kasim malamin koyar da jarida a kwalejin kimiyya ta Hassan Usman Katsina, ‘yan jarida sun zubar da mutuncinsu, inda suke hada baki da barayin gwamnati ana tauye talaka. Ya ce dubi xakin taron nan, dan jarida nawa ya zo? Amma yau da ace taron gwamna ne da ka gansu birjik, saboda nan za a bada kuxi, amma taron Talaka wa zai je?
RAHOTO
A Yau Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
19
Ya Kamata T.Y Xanjuma Ya Nemi Gafarar ’Yan Qasa Da Hukumar Sojoji -Kanal Yombe Dabai Daga: Umar Faruk, Birnin-kebbi
Kanal Samaila Yombe Dabai Mai ritaya ya bayyana takaicinsa da kuma vacin ransa bisa ga kalaman da Janar T.Y Danjuma ya yi a kwanakin baya a yayin da Janar xin ke gabatar da jawabi a wurin taron bukin yaye xaliban Jami’ar Taraba. Kanal Samaila Yombe Dabai ya bayyanawa manema labarai hakan ne a jiya a ofishinsa da ke Birnin Kebbi a lokacin da ya gudanar da taron manema labarai domin nuna rashin jin daxinsa dangane da kalaman na Janar T. Y Danjuma. Ya bayyana wannan rashin jin daxinsa ne a matsayinsa na tsohon kanal xin soja mai ritaya, kuma xaya daga cikin waxanda suka fafata yaqin basasa. Kanal Yombe ya ce; “Kalaman Janar T. Y Danjuma na zargin sojojin qasar nan da haxa kai da ‘yan ta’adda wurin aiwatar da kashe-kashen da ke faruwa a jahohin Arewa maso yamma. Haxi da cewa sun kasa samar da tsaro ga ‘yan qasa ko bada kariya ga rayuwarsu da Kuma dukiyoyin Al’ummar qasa. Wanda haka sam bai dace ba, domin a matsayinsa na wanda yayi yaqin basasa a qasar nan, kuma tsohon hafsan soja a qasar nan, a ce shi ne ke irin wannan kalamai da ke iya jawo rikici a qasa wanda bai dace ba.” Saboda haka, kanal Samaila Yombe Dabai ya nuna rashin jin daxinsa ga waxannan kalaman da Janar T. Y Danjuma ya yi a kan sojojin qasar nan. Idan dai ba a manta ba, kalaman na Janar Danjuma ya xau lokaci yana tayar da qura a ciki da wajen Nijeriya, inda yake cewa; “ku tashi tsaye, ku kare kanku domin jami’an sojoji su ne ke haxa baki da ‘yan ta’ada suna kashe ku “. A nashi hangen, Kanal Yombe ya ce, wannan kalaman sam ba su dace ba, kuma sun yi muni ga irinsa wanda yayi yaqin basasa ya kuma sadaukar da kansa ga qasarsa Nijeriya kan ganin cewa qasar nan ta zama wuri guda, ta kuma samu zaman lafiya. Har ilayau Yombe Dabai ya ce; “Ina xaya daga cikin tsofaffin sojojin qasar nan da suka san wane ne Janar T. Y Danjuma domin na yi aiki
tare da shi. Ya kuma yi zama matsayin shugaba na a wata rundunar Sojoji da ke garin Ibadan, da kuma Okija da ke Enugu a lokacin yaqin basasa a qasar nan. Amma yau an wayi gari Janar Danjuma ne ke faxin wannan munanan kalamai, ya tuna cewa shi ma yayi yaqi ya kuma bar tarihi. “Ko yana nufin tarihin da ya bari kenan na sojoji su riqa haxa kai da ‘yan ta’ada domin su yi ta kashe ‘yan qasa? Kazalika Yombe ya ce; “ina jin vacin rai da kuma baqin ciki a matsayina na tsohon sojan qasar nan wandan ya yi yaqin basasa a qasar nan domin maido da zaman lafiya, kuma wanda ya sadaukar da kansa ga Najeriya, sannan a ce wai yanzu sojojin qasar nan su ne ke kashe mutanensu ko kuma suke haxa baki da ‘yan ta’adda domin su kawo tashin hankali a qasar nan, gaskiya wannan abin yayi muni kwarai da gaske. Saboda haka ni Mai ritaya kanal Samaila Yombe Dabai ban amince da Kalaman Janar Danjuma ba.” Bugu da qari Yombe Dabai ya ce ya fara aikin soja tun yana da shekara tara zuwa goma bayan ya kammala makaranta yaran sojoji. Daga nan ya zarce zuwa makarantar horas da sojoji inda ya kammala makarantar ya fito da muqamin Laftanar wato anini xaya. Daga nan ne aka ba shii shugaban wata rundunar domin ya jagorance su. “Saboda haka bari in bayyana muku yadda na san Janar T. Y Danjuma, na san
shi tun shekara ta 1967 a lokacin na kammala karatu na daga makarantar soji, inda aka kai ni wata runduna da ake kira bataliya ta xaya, bayan hukumar soji ta tura ni makarantar horaswa kan wata bindiga da ake kira 106 wadda ake daurawa kan motar soji da ake cewa LandOver. “Bayan na dawo daga makarantar horaswa sai aka tura ni wurin shugaban qasar nan na soja Ogun-Ironsi a matsayin bodigad na shi, masu ba shi tsaro a lokacin, kuma a lokacin ne muke kai wata ziyara a garin Ibadan a nan ne Janar T. Y. Danjuma da wasu aka shirya cewa a hamvarar da gwamnatin Ogun-Ironsi, wanda ina cikin waxannan mutanen, bayan an hamvarar da gwamnatin, aka canza ni zuwa bataliya ta huxu dake qarQashin runduna ta xaya da ke garin Nsukka kuma lokacin T. Y Danjuma shi ne kwamandan rundunar, kuma shi ne ya jagoranci tawagar rundunar sojojin da suka yi yaqin basasa a garin Okibeh da ke Enugu.” inji shi Bugu da qari, Kanal Yombe ya ce; “saboda haka nake ganin cewa Janar Danjuma soja ne mai ilimi da kuma qwazo ta hanyar tafiyar da aikin soja, ya kuma yi matuqar qoqari a lokacin yaqin basasa da aka yi a qasar nan. “Saboda haka kalamansa sun tava mani hankali sosai game da sojojin Nijeriya masu bada tsaro ga jahohin da ake fama da tashin hankali. Kuma gashi yana xaya daga cikin tsofaffin
sojojin qasar nan da ake girmamawa, ballantana mu da muka yi aikin soja a qarqashinsa, amma gashi yau shi ne ke waxanan miyagun kalamai ga sojojin da ke iya qoqarinsu na ganin sun maido da zaman lafiya a jahohin arewa maso yamma. “Janar Danjuma yana da damar da zai iya ganin shugaban qasa ko kuma shuwagabannin sojojin qasar nan domin ya basu shawara idan har akwai wani abu da ya ga cewa ya kamata a gyara, amma ba ya furta irin waxanda kalamai masu qara kawo tashin hankali a qasa ba.” inji Kanal xin Ya kuma ce da Janar Danjuma ya san abin da ya faxa da ya janye kalaman da ya faxi, ya kuma roqi gafara ga ‘yan Nijeriya kan kalaman da yayi. Ya ce; fuskar da yaqin na yanzu ya ke da shi ne ba ka san ta inda miyagun za su vullo ba, domin suna iya vullo wa ta ko ina. Yau ga shi T. Y Danjuma ne ke nuna yatsa ga sojojin Nijeriya cewa basu san abin da su ke yi ba. Ya manta da irin qoQarin da sojojin nan ke yi na ganin cewa an samar da zaman lafiya a jahohin arewa Maso gabas kuma qasar nan baki xaya. Daga qarshe, Kanal Samaila Yombe Dabai ya yi kira ga Janar Danjuma da ya fito a kafafen watsa labarai ya janye kalamansa da yayi da kuma neman gafara ga ‘yan qasa da kuma hukumomin da abin ya shafa. Saboda a matsayinsa a qasar nan ba shi ne ya dace ya yi wannan kalaman vatanci ba.
20
A Yau
CINIKI
Kasuwanci MASANA’ANTU
INSHORA
HANNUN JARI
Talata 3.4.2018
KASUWAR SHINKU
CBN Da Bankuna Za Su Sanya ‘Yan Nijeriya Miliyan 60 A Harkar Hada-Hadar Kuxi Daga Abubakar Abba
Makon da ya gabata ne Babban Bankin Qasa(CBN) da Bankunan ‘yan kasuwa da masu hada-hadar kuxi ta hanyar zamani dake da lasis da kuma manyan ajent suka qulla yarjejeniya don samar da kuxi da kuma faxaxa ajent don bunqasa hada-hadar kuxi a Nijeriya. Yarjeniyar ta haxa da sanya ajent 500,000 a cikin shekaru biyu masu zuwa don gudanar da hada-hadar kuxi kamar na shigar kuxi da kuma fitar da su da tura kuxi da biyan kuxi da sayen katin hadahadar kuxi da rabarwa da kuma shiga tsarin(BMS) da kuma samar da katin (BVN) na fitar da kuxi daga banki da aka qiyasta kimanin ‘yan Nijeriya su miliyan 50 a yanzu suna amfani da katin na (BVN). A cewar Bankin Duniya, sanya hada-hadar ta kuxi, yana buqatar waxanda suka manyanta da ‘yan kasuwa su samu damar kayan da suke buqata da kuma ayyukan da za’a yi masu daidai da buqataun su kamar na tafiyar da biyan kuxi da ajiyar kuxi da samar da katin xaukar kuxi da karvar bashi da yin inshora ta hanyar data dace. Anyi amannar cewar, It is samun sukunin yin amfani da asusun ajiya na banki, shi ne mataki na farko na inganta hadahadar kuxi ganin cewar, hakan zai baiwa mutane dama su ajiye kuxi da tura su da karva. Hada-hadar ta kuxi, wata hanya ce ga cibiyoyin hada-hadar kuxi wadda kuma za ta baiwa mutane dake faxin duniya samun damar wajen gudanar da hada-hadar kuxi a asusnun ajiyar su kuma wannan shi ne rukunonin Bankin Duniya ya mayar da hankali a ka yi. Manyan jami’an na bankuna dake Nijeriya
sunyi ammana akan cewar samun damar hada-hadar kuxi za ta taimaka wajen gudanar da hada-hadar kuxi da samar da ci gaba. A saboda haka ne, Bankunan dake Nijeriya suka zage wajen shigo da masu samun kuxin shiga ‘yan kaxan da aka bar su a baya ta hanyar zamani don su ma su shiga a dama dasu da kuma yin amfani da hanyar gudanar da hada-hadar kuxi don a sanya ‘yan Nijeriya a cikin harkar a bisa tsarin CBN na samar da kashi 80 ta hada-hadar kuxi kafin shekarar 2020. Sabbin aikin zai nuna wa Babban Bankin Qasa ‘CBN’ da kuma bankunan kasuwanci da manyan ajent da masu hadahadar kuxi dake da lasisi ta hanyar bai wa ajent damar amfana da shirin don sanya Nijeriya a cikin tsarin, musamman saboda samar da sabuwar hanyar bayar da bashi da ajiyar kuxi da inshora da fansho don amfanin waxanda basa mu’amala da bankuna da sanya masu qaramin qarfi a cikin harkar hada-hadar kuxi.
Babban Jami’i na Bankin Guaranty Trust Segun Agbaje shi ma a na shi jawabin ya ce, “banbanci a tsakanin wannan shirin da sauran da aka gudanar a baya shi ne, masana’antu masu zaman kansu da bankuna ne suke jagoranta sabon shirin. Wannan ba tsari bane da gwamnati ke jagoranta ba, musamman ganin cewar a matsayin na bankuna duk abinda muka sanya a gaba, sai munga mun kammala shi kuma wannan bawai anyi bane don sai lallai an samu wata riba ba, sai dai daga baya zamu samu ximbin riba, amma asalin tsarin shi ne don a janyo mutane ajiki akan hadahadar kuxi. Ya ce, kuma kuxaxen da muke yin amfani dasu, kuxaxe ne da tuni an ware su a gefe guda na daga cikin ribar da muka samu. Ya yi nuni da cewar, wannan sabon tsarin don kawai amfanin ‘yan Nijeriya ne musamman don janyo su a cikin harkar kuma tsari ne don a qarfafa harkar hadahadar kuxi. Shi kuwa Babban Jami’I
na Bankin Zenith Peter Amango ya ce, abinda yafi mahimmanci akan tsarin shi ne, don a qarfafa hadahadar kuxi a qasar nan kuma zamu yi dukkan maiyuwa don gudanar da komai a cikin sauqi. Mun sanya masu hadahadar kuxi na zamani da kuma Babban Bankin CBN muna kuma son mu sanya harda waxanda ke a cikin gari dana karkara. Shi ma Babban Jami’in bankin Diamond Uzoma Dozie ya ce, manufar ita ce don janyo waxanda basa yin hada-hadar banki don suma su amfana. A cewar sa, “muna zauba jari ne saboda ga amfanin gaba kuma wannan yana daga xaya abubuwa da zai amfani xaukacin qasar nan. Da yake na shi tsokacin a madadin masu gudanar da hada-hadar kuxi ta zamani, Tayo Oviosu, wanda kuma shi ne ya qirqiro da inuwar da ake kira (Paga) ya yi buni da cewar, don a cimma nasara wajen havaka cibiyoyin hada-hadar kuxi a qasar nan, akwai buqatar samar da tsarin gudanar da hada-
Ci gaba a shafi na
21
KASUWANCI 21
A Yau Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
CBN Da Bankuna Za Su Sanya ‘Yan Nijeriya Miliyan 60 A Harkar Hada-Hadar Kuxi Ci gaba daga shafi na
20
hadar kuxi ta zamani ga dukkan masu gudanar da hada-hadar ta zamani da kuma qara inganta hanyar sadarwa ta zamani a xaukacin faxin qasar nan. Sama da shekaru uku da suka shiga, bankunan Nijeriya suke da nufin sanyawa da kuma qara ‘yan Nijeriya miliyan 60 tunda farko da kuma qara sanya wasu ‘yan Nijeriya miliyan 40 akan tsarin katin (BVN), inda a qalla za su kai yawan miliyan 20 a duk shekara da qara sanya wasu ‘yan Nijeriya miliyan 40 akan tsarin katin (BVN).Don cimma wannan nasarar, bankunan ‘yan kasuwa sunyi la’akari da wasu dalilai da ake dasu a qas da suka shafi sanya Nijeriya a cikin hada - hadar kuxi, waxannan dalilan suna haxa da; ragewar gudanar da hada-hadar kuxi ilimantar da masu ajiyar kuxi a bankuna da wayar masu da kai akan jahilcin da suke dashi na hadahadar kuxi da wayanda basu da ayyukan yi da matsayin talauci. Kamfanonin dake gudanar da hada-hadar kuxi ta zamani dake da lasisi da manyan ajent ana sa ran za su janyo ajent masu gudanar da hadahadar kuxi don su buxe rassa a cikin gaggawa a cikin garuruwa da kuma a cikin karkara dake qasar nan, musamman ta hanyar
mayar da hankali ga a shiyoyin dake Arewacin Nijeriya ganin cewar su an bar su a baya wajen harkar hada-hadar kuxi. Kwamitin da bankin (CBN ya amince dasu sune; shiyyar Arewa Gabas za ta samu kashi 30 bisa xari shiyyar Arewa maso Yamma za ta samu kashi 30 bisa xari shiyyar Arewa maso Tsakiya za ta samu kashi 20 bisa xari shiyyar Kudu maso Kudu za ta samu kashi 7.5 bisa xari shiyyar Kudu maso Yamma za ta samu kashi 7.5 bisa xari,sai kuma shiyyar kudu masu Yamma za ta samu kashi 5 bisa xari. Wasu daga cikin kamfanonin hada-hadar kuxi dake da lasisi da suka tsallake siraxin bankin (CBN) sun haxa da; Capricorn Digital da Cellulant Nigeria da Tranzact da Innovectives da Inlaks da Interswitch da Financial Inclusion Services da Paga Tech da kuma Unified Payments Nigeria. A cewar tsarin na bankin (CBN) da kuma bankunan a Nijeriya sama da ‘yan watanni da suka shige za su fito da sababbin dabaru da kaya da kuma gudanar da ayyuka don qarfafa wa da kuna sanya Nijeriya a cikin hada-hadar kuxi. A saboda hakan za’a mayar da hankali akan samar da rangwame na
samun damar yin amfani da na’urar zamani don inganta yin gangami da wayar da kai akan akan karvar bashi da yin inshora da zuba jari akan kaya don a amfana musamman a tsakain marasa qarfi dake qasar nan. Bankin (CBN) zai kuma jagoranci neman gwamnati ta bayar da xauki da kuma biyan ajent don a sabunta qa’idojin don a cimma nasarar da aka sanya a gaba da kuma samar da jingina daga gwamnatocin jihihin qasar nan yadda zaus tsaya a matsayin masu tsayawa wajen karvar bashi da wayar da kai da samar da hanya mafi sauqi akan samar da katin(BVN) da qarfafa tsarin (KYC) don buxi asusu a bankuna da dukkan cibiyoyin gudanar da hada-hadar kuxi da sake yin dubi akan zuba jari a bisa tsarin hadahadar kuxi ta zamani. Da yake tsokaci akan faxaxa shirin ajent Shugaban jami’an bankuna Mista Herbert Wigwe wanda kuma shi ne Babban Jami’in Bankin Access ya ce, “wannan yarjejiniyar da aka qulla, ta nuna a zahiri akan qoqarin da da Bankin (CBN) yake yi na sanya cibiyoyin hada-hadar kuxi kafin zuwan shekarar 2020. Wannan qirqirar za ta kuma samar da sababbin
ayyukan yi sama da 500,000 sama da shekaru biyu. Ba kawai maganar bayar da basussuka bane, zaka samu komai da kake buqata daga bankunan kuma muna bayar da tabbaci akan cewar, jama’a da za su zo a bisa tsarin da aka gindaya zamu basu damar samun ayyukan banki.” Shirin na faxaxa ajent, zai taimaka wa tsarin mu a cikin sauri a shekara mai zuwa. Sakamakon faxaxa shirin, xaukacin cibiyoyin gudanar da hada-hadar kuxi za su shiga lunguna da saqosaqo don iske miliyoyin ‘yan Nijeriya a cikin sauqi. A bisa binciken da aka gudanar a Nijeriya a shekarar 2016, gudanar da hada-hadar kuxi ta kai kimanin kashi 41.6 bisa xari a tsakanin waxanda suka manyanta waxanda kuma basu samu damar shiga harkar ba, sun kai ywan miliyan 36.9 a shekarar 2014 da zuwa miliyan 40.1 a shekarar 2016. Gwamnan babban bankin Nijeriya ‘CBN’, Mista Godwin Emefiele, yasha yin yin shela a wasu tarurruka a baya akan cewar bankin zai samar da kashi 20 wajen sanya cibiyoyin hada-hadar kuxi a shekarar 2020 mai zuwa.
22
Kiwon Lafiya
A Yau
Talata 3.4.2018
Albasa Da Amfaninta Ga Jikin Xan Adam Daga Idris Aliyu Daudawa
A wannan vangare ko kuma sashe na duniya, an saba da amfani da albasa lokacin da ake dafa abinci, yana kuma da wuya ace har an dafa abinci ba tare da amfani da albasa ba. Ba wani abin mamaki shi yasa ta kasance an saba da ita, ana kuma iya ganin ta ako wane xakin dahuwa , wato kitchen. Koda yakedai amfanin albasa ya wuce maganar tukunyar girki, saboda nazarin da ba a daxe da yin shi ba, ya nuna cewar ‘yar uwar Tafarnuwar ta qunshi sinadaran Vitamin C, Sulphuric compounds, flavonoids, da kuma phytochemicals. Kamar yadda masana kimiyya suka bayyana su sinadaran phytochemical suna amfani ne da wani abu na jikin mutum, domin kare jiki daga wani abin da zai cutar da shi, yayin da su kuma flavonoids, suna rage yiyuwar kamuwa da cutar parkinson’s, cardiovascular, da kuma mutuar vangaren jiki. Saboda dai mu qara gane amfanin albasa a jikinxan Adam, yana da qyau a san al’amarin da ya shafi tarihinta. Tarihin Albasa Albasa ta samo asalinta ne daga nahiyar Asiya ta tsakiya, a zamanance Iran da kuma Pakistan, tana kuma daga cikin daxaxxun kayayyakin amfanin gona da ake haqowa. Tun wajen qarni na shiida B. C. wani jami’in asibiti da ake kira Charaka Sanhita ya yi bikin Albasa a matsayin magani, diuretic, tana da amfani wajen ala’amarin da ya shafi, yadda ake sarrafa abinci, aikin shi da kuma kammala aikin shi, Zuciya, Idanu, da kuma mahaxa ta qashi da tsoka. Yana kuma da qyau a gane cewar an fara noma albasa a qasar Masar tun qarni na 3500 B C, ana amfani da ita ne wajen bauta mata, musamman ma yadda
halittarta take,kamar yadda zane cikin zane abin yana burge su, har suna yi mata wata xauka daban. Fenti na albasa anyi su a bangaye na cikin Pyramids wato dalar qasarMasar da kuma kaburbura, wani lokaci ma har ana rufe waxanda suka mutu da labasa, saboda ana sa ran cewar saboda yadda take da yajin nan mai qarfi, ko kuma qanshinta, da akai wata mu’ujizar da ake ganin tana da ita, wadda ake kuma sa ran shi wanda ya mutun watakila ya yi numfashi. Wannan shi ne yadda wasu ke ganin yadda ita Albasa take, saboda an yi maganar ta a Bible, a namba 11.5 kamar yadda Yahudawa suka yi qorafi akan abin dake gina garkuwar jiki. ‘’Mun tuna da kifi, wanda muka ci a Masar ba tare wata matsala ba, da kukumba, da kuma melon, da leeks, Albasa, da kuma Tafarnuwa.’’ Yadda Albasa ke Taimakawa samar da lafiya ta waxannan cututtuka biyar 1. Tana maganin matsalar da ake samu ta mafitsara Tana da wasu sinadaran diuretic da suka shafi lafiya, albasa tana da matuqar amfani, idan ana fama da matsalar data shafi mafitsara. Shi yasa ma wasu ma’aikatan lafiya ke ba
waxanda suke fama da tsananin zafi lokacin da suke fitsari, cewar su sha ruwan da aka tafasa, da giram 6 zuwa 7 na albasa, saboda tana samar da sauqi na alamun ciwon da shi ciwon. 2.Tana Yaqi Da Cutar Daji (Kansa) Sakamakon da aka samu daga binciken da aka yi, ya nuna cewar,albasa ta kasu daban daban, saboda an sansu da maganin cutar kansa, musamman ma yadda take girma. Bugu da qari duk dai dangane da binciken da ka yi, idan na mafani da ita akai akai, tana rage yiyuwar kamuwa da cutar kansa daban daban, kamar kansa ta colorecta, oral kansa, kansar mqogwaro, kansar ciki, kansar wurin da abinci ke biya wuce zuwa hanji, sai kuma kansar mahaifa. Abin so ne mutum ya yi amfani da labasa xaya ko wacce rana. 3. Albasa na rage sikarin dake cikin jini Jini wanda ya qunshi sikari mai yawa(hyperglycemia) wannan yana kasancewa ne, lokacin da jinin da ke cikin sikari da ake kira (glucose), yayi yawa fiye da yadda jiki ke buqata, domin yin aiki da shi kamar yadda aka saba. Wannan yanayi shi ne ka sani da samar da matsala nan da nan da kuma wadda ke xaukar dogon lokaci.
Amfani da Albasa kusan kullun ya nuna cewar tana sa sikarin da yake cikin jini ya ragu, saboda ta qunshi wani sinadarin allyl prppyl disulfide, wanda yake taimakawa, wajen rage yawan glucose, ya kuma qara yawan sinadaran insulin. 4. Tana Qara Qarfin Sinadaran dake taimakawa wajen yaqar cutar Kamar yadda Anne Maune anda shi qwararre ne danagne da kayayyakin abincin, mai zama a Washington DC, ya bayyana cewar akwai poly phenolds a cikin albasa wanda yake aiki kamar sojojin da ke yaqar cutar cuta da ake kira free radicals. Akwai kuma quercetin a cikin albasa yana kuma taimakawa ne, wajen rage shiga wani hali , ko kuma ji ya nuna alamar tashin hankali, anan yana hana jiki samar da histamines, wannan shi ke sa mutum, ya yi Hamma, kuka, ko kuma jin zafi, idan mutum na yin wani abu, saboda da zarar ya ga wani abu sai jikin shi ya shiga wani hali. 5. Tana taimakawa wajen rashin samun matsala dangane da yadda ake narkar da abinci. Bugu da qari albasa tana tana da wani sinadari na musamman da ake kira fibre oligofructose wanda yake taimakawa qwayar cuta mai qyau a cikin hanci.
KIWON LAFIYA
A Yau Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
23
Zazzavin Lassa: NCDC Ta Tabbatar Da Kamuwar Mutum 394 Da Mutuwar 95 A Shekarar 2018 Daga Idris Aliyu Daudawa
Cibiyar hana yaxuwar cututtuka da kuma maganinsu (NCDC) ta tabbatar da samun mutane waxanda suka kamu da cutar zazzavin Lassa 394, da kuma mutuwar mutane 95, tsakanin watan Janairu da kuma Maris na wannan shekara ta 2018, wannan kuma ya biyo bayan varkewar annobar zazzavin. A wani rahoton da ba a daxe da fitar da shi ba, NCDC ta bayyana cewar an samu ire iren zazzavin har guda goma sha takwas, a qarshe mako na watan Maris. Koda yake dai ita Hukumar ta bayyana cewar an kuma samu wani ci baya, a sabon zazzavi na cutar a makonni biyar da suka wuce. Amma kuma Hukumar ta bayyana cewar a wani qiyasin yadda cutar ta ke yaxuwa, a wasu qarkewar ta annobar, abin ya nuna cewar han yanzu yadda cutar take yaxuwa sosai lokacin bai wuce ba, don haka yana da kyau a ci gaba da sa ido kamar yadda ake yi shekarun baya da suka wuce, da kuma kai xauki wanda ba na vata lokaci ba, da zarar dai an samu bayani akan vullar annobar. ‘’Hukumomin hana yaxuwar cututtuka da kuma ta lafiya da duniya, da kuma sauran duk masu bada gudunmawa, da su ci gaba da zage damtse, na kai xauki wuraren da suka samu
vulluwar cutar. Sai kuma ci gaba da zuwa wuraren, saboda hana yaxuwar cutar zazzavin Lassa da kuma , bayani akan inda aka gano cutar ta vulla’’. Bugu da qari ita Hukumar ta yi kira da ‘yan Nijeriya musamman waxanda suke zama a jihohin Edo,Ondo, da kuma Ebonyi, su ci gaba da mayar da hankalinsu, ta wajen hana yaxuwar cutar. Ya bada shawarar da a riqa sa kayayyakin abinci da suka qunshi hatsi awurin da irin su vera ba zasu samu damar shiga ba, sai kuma ita shara a riqa zubar da ita, inda ya dace, ba kusa da gida ba. ‘’Yadda maganin cutar zazzavin Lassa ya danganta ne akan yadda su al’umma suke wato al’amuran da sukla shafi tsaftace muhalli, domin hana veraye shi ga cikin gidaje. Sauran matakan sun haxa da ajiye hatsi a cikin wurin da vertaye ba zasu iya shiga ba, sai kuma gidaje su kasance ko yaushe a tsaftace. “Dole abinci a tabbatar da an dafa shi ya dahu sosai, sai kuma mutanen gida su yi qoqari su guji yin hulxa da jini, da kuma duk wani abu da yake dangantaka da ruwa ruwa, lokacin da suke kula da wani mara s lafiya wanda kuma ya kamu da cutar zazzavin Lassa.’’ “Shi rahoton ya yi kira dama’aikata masu kula da lafiya da su yi qoqari su lura wajen sa ido sosai, akan duk wurin da suke tsammanin alamun zazzavin Lassa, lokacin da suke tare da
maras lafiya, koda kuwa wane irin hali suke dangane da lafiyar jikinsu’’. “Bugu da qari za a iya tabbatar da cewar shi zazzabin Lassa an kamu da shi lokaci da maras lafiya yake fama da zazzavi, ciwon kai, shi kuma an manta dawata maganar zai iya kamuwa da cutar shawara, musamman idan shi maras lafiya xin bai nuna alamun jin sauqi, nan ya kamata su ma’aikatan lafiya su koma ga dukka yadda qa’idoji
suka shata, wato su riqa sa dukkan abin da masu kula da masu zazzavin Lassa suke sawa.’’ Shi ma shugaban Hukumar hana yaxuwar cututtuka da kuma maganinsu Dokta Chikwe Ihekweazu, ya ce “Hukumar ita da masu taimaka mata, zasu ci gaba da taimakawa jihohi, da qwararru, domin maganin shi zazzavin Lassa.’’ Wakilin Hukumar lafiya da duniya wanda ke
ofishinsu na Nijeriya, ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewar, Hukumar a shirye take, wajen taimakawa ayyuka masu qyau da ake yi a Nijeriya.’’ “Za mu tsaya domin taimakawa Nijeriya, ba wai sai an bari an samu varkewar annobar ba, amma shi darasin da aka koya, ya kamata a yi amfani da shi, domin hana sake aukuwar varkewar annaobar wadda tana niya gagarar mutane Allah ya kiyaye’’.
WHO Za Ta Kashe Dala Miliyan 178 Kan Kiwon Lafiya A Nijeriya Daga Idris Aliyu Daudawa
Ranar Litinin ne Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce zata kashe kuxaxe har dalar Amurka milyan 178 tsakanin shekarun 2018 da kuma 2019, akan al’amuran da suka shafi harkar lafiya a Nijeriya. Wakili mai kulawa da ofishin Nijeriya na Hukumar lafiya ta duniya Dokta Wondimagegnehu Alemu, shi ne ya bayyana haka lokacin ta aka yi taron haxin guiwa na amincewa da kuxaxen da za a kashe a kasafin kuxi na shekarun 2018 da kuma 2019, tare
da Ministan lafiya Farfesa Isaac Adewole a Abuja. Alemu ya ce, dalar Amurka milyan 127 wadda kashi 66 cikin 100 ne na kasafin kuxin, waxanda za a kashe su ne wajen tsare tsaren mganin shan Inna wato polio. Ya qara da cewar dalar Amurka milyan 30 za a kashe kuxaxen wajen maganin zazzavin malaria, tarin fuka, da kuma cutare qanjamau. Ya jaddada cewar dalar Amurka fiye da milyan 8.1 an ware ta ne za akashe wajen kula da lafiya ta hanyar rage mutuwar
qananan yara, da kuma tsarin tazarar haihuwa. Ya yi qarin bayani na cewar sauran kuxaxen za a kashe su ne ta hanyar ta maganar vullar kota kwana, wato annoba ta cututtuka. Wakilin Hukumar wanda ya bayyana ya sa hannu a kasafin kuxina madadin Darektan, ya bayyana cear shi Darektan ya amince da kasafin kuxin. Bugu da qari za ariqa yin taron tuntuva tsakanin masu ruwa da tsaki, domin a tabbatar da ana yin al’amuran kasafin kuxin kamar yadada aka amince.
A nashi jawabin Adewole ya jinjinawa Hukumar lafiya ta duniya, a qoqarin data ke yi na bunqasa harkokin kiwon lafiya a Nijeriya. Ya bayyana Nijeriya ta samu gudunmawa mai yawa da ga Hukumar,don haka sa hannu a kasafin kuxin wani abu ne da ke nuna cewar Hukumar zata ci gaba da taimkawa Nijeriya. Shi ma Ministan lafiya ya jinjinawa ita Hukumar lafiya ta duniya, sabioda taimakon da take ba Nijeriya, musamman ma al’amarin da ya shafi kawar
da cutar polio. Maganar kasafin kuxi na kawar da qwayar cutar polio babban al’amari ne, don haka za ayi amfani da kuxaxen kamar yadda aka baiyana. Ya ce, ‘’Ina farinciki akan kuxaxen da aka ware ma cututtuka masusaurin yaxuwa, saboda yaan kasafin kuxin can zai fi amfani. ‘’A madadin al’ummar Nijeriya da kuma gwamnati, ina mai nuna farin ciki na akan gudunmawar da aka bamu, da kuma wadda muka yi ta masa daga Hukumar’’.
24
TALLA
A Yau Litinin 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
25
A Yau Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Kimiyya
Dala Miliyan 500
ne adadin kuxi Nijeriya ke kashewa duk shekara waurin safarar xanyen man fetur da wasu sinadaran da ake amfani da su a sashen sinadarari da magunguna
Google Zai Tallafa Wa Kafafen Watsa Labarai Da Dala Miliyan 300 Daga Idris Aliyu Daudawa
Ranar Talata ne ta makon daya gabata kamfanin Google ya vullo da wani sabon tsari na taimakawa sababbin mawallafa da taimakon dalar Amurka milyan 300, su samu su biya waxanda suka yi rajista dasu lokacin da suka haxu da wani labarin da babu qanshin gaskiya. Shugaban harkokin yanar gizo ya bayyana cewar tsarinda kamfanin Google ya yi, na tsarin taimakawa saboda labarai wani ‘’Shiri ne taimakawa harkar aikin jarida, a irin wannan yanayi da muke na sabuwar fasahar zamani ta sadarwa.’’ Ita wannan sanarwa wadda aka yi a Newyork ta biyo bayan wasu tarurrukan da aka yi saboda taimakawa kafar samar da labaran, wadda Google ya yi, saboda ana ta guna gunin cewar ana ta cita ceto, da wasu kafafe suka ce ana yi, dangane da yadda ake kaucema magana bada kuxaxen shiga kamar yadda suka dace. Philipp Schindler shi ne jami’in harkokin kasuanci ne na Google, shi cewa ya yi ‘’Ko wanne lokaci ina tunanin cewar abin da zai iya faruwa ga kamafani Google da kuma harkar wallafawa wani al’amari ne da yake buqatar a riqa aiga baya, saboda na iya barin wurin da yake buqatar gyara’’. Don haka idan abokan harka ba su yi nasara ba mu ma ba zamu yi ba’’. Google zai taimaka ma masu amfani da shi da su nemi neman samun labarai, kamar sau biyu, idan suka nema kuma kuxin da za a biya basu taka kara sun qarya ba. Bugu da qari shi kamfanin Google zai taimaka wa masu samar da labaran biyan waxanda suke amfani da labaran. Shi wannan sabon tsari kafafen watsa labarai kamar sittin ne, suka haxa kai wajen kafa shi tsarin, waxanda suka haxa da Washinton Post, Financial Times, da kuma wani kamfani daga qasar Faransa Le Figaro, na Brazil kuma
Grupo Globo, sai kuma na qasar Italiya La Rupublica. Manufofin duka shi tsarin sun haxa da qara martabar aikin jarida, qara samu harkokin bunqasa kasuwanci, sai kuma taimakawa kafafen watsa labarai wajen, su dogara a ko wanne lokaci zasu samu qaruwar sababbin dabaru na fasahar zamani ta sadarwa. Google ya yi aiki da masana’antar sadarwa ta shekaru masu yawa, da niyya wadda ta qunshi, samun shafuka su bayyana , bada vata lokaci ba, akan wayoyin zamani, da kuma sa yadda ake kallon bidiyo ko labarai ta You Tube, saboda masu wallafa labarai, samar da wani xaki na horo akan labarai ta sabuwar hanyar Digital wani tsari daga Yammacin Turai. ‘’Mun zuba jari da kuma qarfinmu danagane da shi wannan sabon tsari, kamar yadda Schindler ya bayyana’’. ‘’Amma kuma maganar gaskiya dukkan waxannan ba dole bane su isa, abin ana qara samun matsala wajen bambanta, abin da yake gaskiya, da kuma wanda baya cikin bisa tsarin’’. Shi sabon tsarin na kamfanin Google shi ne ya
taimaka ta wajen qoqarin da ake yin a, saboda a qara taimakawa da kuma xaukaka aikin jarida, kamar dai yadda Schindler ya yi bayani. Ana qara xaukaka shi al’amarin daya shafi Google, wajen horo domin ya yarda, da irin labaran da xumi xumi, domin bada majiyar labarai, wadda ba za a yi shakkun ta ba. ‘’Masu buqatar rashin rubuta labaran da ba za a yi wasi wasi ba, kamar labaran da xumi xumi ta kafar Googles, wannan shi zai sa ayi tsammanin ana iya samar da labaran da ba cikakku nagartatantu ba’’. Hakanan ma kamfanin Googles ya qaddamar da da wani vangare wanda zai yi qoqari, akan samun hanyoyi waxanda za ayi maganin labarai ko labaran da babau qanshin gaskiya, ko kuma lokacin da ake zavuvvuka, ko kuma labaran da xumi xumi. Bugu da qari Google wanda yake a Carlifornia ya bayyana cewar yana qoqari na haxa kafaxa da, wata cibiya a Poynter, sai kuma jami’ar Standford, da kuma qungiyar kafar watsa labarai da take, da take Amutka, domin a qaddamar da wata kafa ta sadarwa, domin a
taimakawa matasa yadda zasu iya fahimtar abin da labaran da suka karanta ta yanar gizo, ya nufa, ko kuma me yake nufi. Google yana taimakawa wajen sa al’amarin samu labarai ga waxanda, suka nemi damar, sun kuma yin gwaji akan yadda maus wallafa labarai zasu gano, waxanda suke son su riqa amfani da labaran, kamar dai yadda Schindler ya bayyana. Bayan haka ma Google ya qara fito da wani sabon tsari, na wasu abubuwan da kafofin watsa labarai zasu yi amfani da su, wajen samar da haxawa ta yanar gizo, tare da amfani da kafar samar da damar amfani da Network mai zaman kanta. Daga qarshe kamfanin ya bayyana ya na qara qoqari ta hanyar, samar da wasu wurare na yadda za a qara samar da labarai waxanda sune, manya daga cikin buqatun masu amfani da Google. Shi wannan sabon tsarin ya zo dai dai lokacin da Facebook, Google, da kuma Twitter suke matuqr fuskantar takurawa, domin a hana amfani dasu wajen yin ani abin da bai kamata ba, ko kuma su labaran ayi qoqarin canza masu fuska.
26 RAHOTO
A Yau
Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Shahararrun Mata 10 ’Yan Nijeriya Masu Harkar Xaukar Hoto Daga Sulaiman Bala Idris
Kamar sauran vangarorin qwararru, sana’ar xaukan hoto wani fage ne wanda a ka fi danganta shi da maza. Sai dai bincike ya tabbatar da cewa tauraron mata ya fara haskawa a harkar. A wannan rahoton, an tattaro asu shahararrun mata 10 ‘yan Nijeriya waxanda tauraronsu ya ke haskawa a harkar xaukon hoto. TY BELLO
Mace ce wacce ta fara qaurin suna a matsayin mawaqiya kafin daga bisani tauraruwarta ta fara haskawa a fannin xaukan hoto. Har ya kai ta kasance mai hoto ta musamman ga tsohon shugaban qasa Goodluck Ebele Jonathan. Labarin rayuwar TY Bello labari ne na wata matashiya wacce ta faro daga tallan biredi, wacce ta shiga harkar waqa. TY Bello ta kasance ta kan shirya jaular xaukan hoto domin yin amfani da kuxaxen da a ka samu wurin tallafawa marayu. AISHA AUGIE – KUTA
xaukan hoto, ta kasance mai shirya fima fimai da kuma kundin tahiri. Aisha ba ta taqaita xaukan hotonta a kan wani abu guda xaya ba, duk wani abu da Kamararta ta gani sai ta xauka. A yanzu ita ce babbar mataimakiya ga gwamnan Kebbi a kan sabuwar kafar watsa labarai ta yanar gizo. ADEOLA OLAGUNJI
An fi saninta wurin xaukar hotuna masu qarfin nagarta. Yawancin hotunan da Olagunji ta ke xauka su na jan hankalin al’umma, saboda yanayin yadda su ke xaukuwa. Kamar sauran masu xaukan hoto, ba a harkar kawai ta taqaita ba. ta na yin zane, harkar fima fimai, da sauransu. FATIMA ABUBAKAR
Wannan wata mai xaukar hoto ce marar tsoro kuma ta musamman wacce ta fito daga jihar Borno. A kan idanuwanta ‘yan ta’addan Boko Haram su ka tarwatsa garinta, ta hanyar hare haren ta’addancin da su ka yi ta qaddamarwa. Aisha Kuta ta shahara Duk da wannan, Fati ne sakamakon ayyukanta Abubakar ta yi ta xauko a kan jinsi. Baya ga harkar hotunan lamurran da ke
faruwa, ta na watsa duniya domin a san haqiqanin abubuwan da ke damun jihar Borno. Ta kan yi hira da waxanda hare – haren su ka rutsa da su. Hotunanta ba kawai su na nuna qwarewa da hazaqa ba ne, a’a sun a nuna rashin tsoronta ne da kuma son ganin bunqasar yankinta. YETUNDE AYENI – BABAEKO Mafi yawan rayuwar yarintanta ta yi ta ne a qasar Jamus kafin ta dawo gida Nijeriya. Saboda irin shauqin da ta ke da shi ga al’adun Yarabawa, ya sa ta shiga harkar xaukan hoto. Wannan ne ma ya sa hotunanta sun fi nuni ga al’adun Yarabawa da kuma irin rawar mata a qasar ta Yarabawa. Haka kuma ta na amfani da xaukan hotonta wurin yaqi da cutar Kansa. LOLA AKINMADE AKERSTROM Ta kasance mai xaukar hoto wacce ke zirga zirga, mazauniyar qasar Sweden. Tun a farkon rayuwarta Akerstrom ta ke sha’awar zirga zirga, saboda yadda ta ke qaunar ‘Geography’ Hotunan da ta ke xauka su na nuna irin yawon da ta yi zuwa wurare daban daban. Haka kuma ayyukanta an wallafa su a shafuka, mujallu da sama da 60 na duniya. Waxanda su ka haxa da kafafen BBC, CNN, Huffington post, National Geographic, da kuma Time Warner. Haka nan kuma ita ce babbar editan Slow Travel Stockholm, wani shafi wanda ke yiwa maziyarta da matafiya bayanin yadda za su yi zirga zirga a Stockholm. AISHA DAPCHI Ta kasance mai qaunar Kamara tun daga yarinta, wanda hakan ya sa ta ke xaukan hoton duk wani abu da ke gudana a rayuwarta, waxanda su ka haxa da mutane, unguwanni, da kuma yanayi. Ta kasance ta na qauna da shauqin masu xaukar hoto, inda ta ke koyo da kwaikwaiyon yadda su ke gudanar da harkarsu. Bayan digirinta na farko ta shiga kwasa kwasai na
xaukan hoto, wanda bayan kammawalawa kuma ta faxa ma harkar gadan – gadan, lamarin ta ya janyo mata xaukaka a rayuwa. HAYE OKOH Tun ta na yarinya ita ma ta ke qaunar xaukan hoto, duk da kasantuwar mahaifinta shahararren mai xaukan hoto a garin Jos, amma ba a wurinshi ta koyi harkar ba. ta kasance ta kan xauki duk wani abu da ta gani, saboda imanin da ta ke da shin a cewa xaukan hotunan abubuwa a rayuwa ya na sa rayuwa ta yi armashi. Baya ga xaukan hoto, ta kan i fima fimai, sannan ta fara shirin shiga harkar bada umurni a fim. Ya zuwa yanzu ita ce mai hoto ta musamman xin matar shugaban qasa, Aisha Buhari. YAGAZIE EMEZI Ta kasance mai tattara kundin hotunan Afrika, wacce ta kammala digirinta na farko daga sabuwar jami’ar Mexico. Daga nan ta dawo Nijeriya domin yin aiki da wani sabon kamfani wanda ke taimakawa masu hikima da basira wurin bayyana basirarsu. Ayyukanta sun haxa da bankaxo wasu waxanda wani lamarin fargaba ya rutsa da su a nahiyar Afrika, da kuma irin taimakon da al’umma ke yi wa rayuwarsu. Kafafe a faxin duniya su kan buga ayyukanta, irinsu Guardian, Huffington Post, Aljazeera, Union bank,Essence magazine da MTV. SWAT KASHAM AFENGBAI Ta kasance haziqar mai xaukr hoto kuma marubuciya wacce ke zaune a Texas ta qasar Amurka. Qaunarta ga zane ne ya rinjaye ta zuwa ga xaukan hoto. Duk wata dama da ta samu ta kan yi amfani da kamararta wurin xaukan hoton abubuwan da ke gudana a rayuwarta. A fahimtarta, harkar xaukan hoto na iya kawo ‘yanci ga mata da yara a wannan qasa ta mu ta Nijeriya. Kuma wannan na daga cikin dalilinta na yin tsayin daka a harkar ta xaukan hoto.
RAHOTO 27
A Yau Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Qungiyar SERAP Ta Qalubalanci Gwamnatin Tarayya Kan Fitar Da Jadawalin Varayi Daga Bello Hamza
Qungiyar bin diddigin yadda ake kasha kuxaxen gwamnati na “The Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP)” ta buqaci shugaban qasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta janye zavavvun sunayen varayin gwamnati da aka fitar makon day a zuce saboda zavo sunayen ya yi kama da wani biya dakulli ne na siyasa. Qungiyar ta ce, “Irin wannan aikin ya na rage kaifin gwamnati na yaqi da cin hanci da rashawa na gwamnati, ya na kuma rage farin jinin qoqarin gwamnatin yaki da vata gari a cikin gwamnati. Wannna taqaddamar kuma zai bayar da kafarv da varayin dake a cikin jam’iyyra APC da ma waxanda suke cikin jam’iyyar PDP su sulale ba tare da an hukunta sub a, hakan kuma zai yi wa yaqi da cin hanci mummunar zagon qasa” Ministan watsa labarai da al’adu Lai Mohammed, ya bayana sunayen mutanen day a yizaigin su suka kwashe kuxaxen qasar nan daga asusun gwamnatin tarayya. Sunayen ya na qunshen ne da sunayen ‘yan jam’iyyar PDP dake fuskantar shari’u a kotunan daban daban a qasar nan. A nata martanin qungiyar SERAP a sanarwar da shigaban ta Mista Adetokunbo Mumuni, ya sanya wa hanu ranar Lahadi, y ace, “ya kamata gwamnati ta janye waxannan sunayen ta kuma fito da cikakkiyar sunayen varayin qasa kamar dai yadda maishari’a Hadiza Shagari ta bayar da umarni a shekarar day a gabata”. Barin waxannan sunayen zai rage kaifin yaqin da wannan gwamnatin ke yi, zai kumam nuna cewa, wannan gwamnatin ba gasket a ke yi ba wajen zaqulo das ace kuxaxen gwamnatin da aka yi a zamanin mulkin tsohon shugaban qaaa Goodluck Jonathan da kuma ximbin cin hanci da rashawa da ake zargin yana gudana a qarqashin masu gudanar da wannna gwamnatin” Qungiyar ta wara da cewa, “In har da Shugaba Buhari da gaske yake yin a haqi da cin hanci da rashewa da kuma tabbatar da bin doka da oda to day a bi umurnin mai shari’a Shagari inda ta umurci gwamnati da ta bayyana wa ‘yan Nijerisuka saci kuxaxen gwamnati na da dana yanzu, yin haka zai tabbatar da cewa da gaske kuke yi a yaqi da ci hanci da rashawa haka kuma zai qara tabbatar da bin doka da oda” Sanarwa ta ci gaba da cewa,“A siyasantar da sunayen da aka gabatar, hakan kuma yazo ne a lokacin da Nijeriya ke da’awar it ace a kan gaba wajen yaqi da cin hanci da rasahwa a Afirika har
tana buqatar da wasu qasashen Afirika su yi koyi da ita, ya kamata mahunkunta su dai na kauce kauce su fuskanci bin dokar hukuncin da mai shari’a Shagari ta yanke kawai. A bin da ake qasa ba kawai batun bin doka da oda bane kawai hard a maganan ko wannna gwamnatin da gaske take yin a yaqi da cin hanci da rashawa da kuma kaucewa rashin bin doka da oda tare da hukunta duk wani da aka samu laifi ko menene matsayinsa. “Ba zai yiwu gwamnati tar inqa zaven wani hukumci kotu zata bi ba, dole a bi dukkan doka gaba xaya ko da kuwa gwamnati zata hukunta xan siyasa ne daga vangaren APC da PDP” “Danqarqwa ‘yan Nijeriya waxannna sunayen ba tare da bin umurnin mai shari’a Shagari ba karya doka ne kuma cin amanan da ‘yan Nijeriya suka bai wa gwamnatin ne, rashin bin doka ya zama rowan dare a wannna gwamnatin hakan kuma yana iya duqusar da gwamnatin ya haifar da rashin bin doka da oda a tsakanin ‘yan Nijeriya. “In har Shugaba Buhari na son jaddada qudurinsa na yaqi da cin hanci da rashawa daga kowannen xan Nijeriya daga vangaren, yan adawa da na cikin jam’iyya mai mulki ta APC to dole ta yanye waxannna sunayen ta kuma fito da jerin sunayen da zai samu karvuwa a dukka vangarrorin siyasar qasar nan, hakan zai qarfafa wa ‘yan Nijeriya gwiwar cea a na bin doka da oda” “Kotunnan mu ne wurin fassara tsarin mulki da dokokin da ke fitowa daga vangaren majalisun dokokin qasar nan. Amma dagewa a kan rashin bin doka da oda da wannan gwamnatin tayi suna das hi, yana zubar da mutuncin gwamnatin
kuma karan tsaye ne ga tsarin bin doka da oda da kuma mutuncin sashin shari’a na qasaar nan”. Ida za a iya tunawa a shekararv day a gabata ne ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa, shugaban qasa Muhammad Buhari ya umurci a tattara sunayen waxanda suka saci kuxaxen gwamnati da nufin bin umurnun hukuncin kotun tarayya na umurtar gwamnatin tarayya ta bayyana wa mutanen qasa cikakken varayin kuxaxen gwamnati waxanda aka qwato kuxaxe daga hannunsu. I dan za a iya tunawa Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa, shugaban qasa Muhammad Buhari ya bayar da umurni ga hukumomin gwamnati su tattare sunayen waxanda suka saci kuxaxen gwamnati tarayya daga dukkan alamun domin bin umurnin kotun da ta bayar na a bayyana sunayen manyan yan Nijeriyar da suka saci kuxaxen gwamnati da kuma kuxaxen da aka kwato a hannunsu. Mai Shari’a Hadiza Shagari ta yanke Hukuncin ne a watan Yuli bayan Qatar da aka shigar man manba FHC/CS/964/2016 da hukumar SERAP ta nemi gwamnati tarayya ta bayyana wa yan Nijeriya yadda aka gano kuxaxen da ka ce an kwato, ta bayyana ko nawa ne aka kwato daga kowanne maiakacin gwamnatin da aka ce an kwato a hannunsu. Mista Malami ya yi wannan tsokacin ne yayin da tawagar SERAP ta ziyarce shi a watan Oktoba na 2017. In za a qara tunawa, qarar da SERAP ta shigar ya fito bayan bayanin da gwamnatin tarayya ta yi ne na cewa, ta kwato maqiludan kuxaxe daga hannun manyan ma’aikata daga bangare gwamnati
da masu zaman kansu. A cikin Hukuncin nata data zartas ranar 7 ga watan Yuli na shekarar 2017, Maisharia Shagari ta yarda da qungiyar SERAP that “A hukumar dole gwamnatin tarayya ta bayyana wa yan Nijeriya sunayen dukkan yan Nijeriya da suka saci kuxaxen gwamnatin a zamanin wannan gwamnatin da na gwamnaticin da suka gabata. A qarar an haxa da Ministan watsa labarai da aladu Mista Lai Muhammed, alda ma’aikata watsa labarai da aladu. A wannan ranar ne kuma Mista Malami Ya bayyana wa manema labarai cewa, gwamnati ta yarda da hukuncin kuma za ta aiwatar da tanade tanadin hukunxin. Maisharia Shagari ta kuma bayar da waxannan hukuncin, Cewa sashin 4 (a) Na dokan yancin haqqin samun labarai ta tilastawa wanda ake qarar da ya miqa wa wanda ya yi kara waxanda Bayanan. A bayar da sunayen manyan mutanen da aka qwato kuxaxen gwamnati daga hannun su tun daga watan Mayu na shekarar 2015. 2. Hanyar da aka yi wajen qwato kuxaxen. Idan za a iya tunawa ma’aikata watsa labarai ta wallafa bayanan kuxaxen da aka qwato, bayanin Ya nuna cewa gwamnatin Nijeriya ta samun Nasarar Naira 78,325,354,631.82, da Dala 185,119,584.61 da Fan 3,508,355.46 da kuma Fam 11, 250 a tsakanin ranar 29 ga watan Mayu na shekarar ,2015 da ranar 25 fa watan May ,Na shekarar 2016. An kuma bayyana qwato kaddarori a tsakanin wannan lokacin na Naira 126,563,481,095.43, da Dala 9,090,243,920.15, da Fan 2,484,447.55 da kuma Xan 303,399.17.
28
Tauraruwa Mai Wutsiya
A Yau
Talata 3.4.2018 08174743902 wutsiya2019@gmail.com
Masu Harkar Garkuwa Da Mutane 750 Ne Su Ka Tuba A Kaduna Daga Idris Aliyu Daudawa
Mutane 750 ne waxanda suka tuba daga aikata ayyukan ashsha waxanda suka haxa da satar shanu, karguwa da jama’a, a jihar Kaduna suka tuba, suka kuma nemi gafarar mutane, kamar dai yadda suka yi rantsuwa da Alkr’ani da kuma Bible, da cewar ba zasu qara shiga cikin wannan hali ba. Ana iya tunawa da irin bikin da kay i mako biyu ke nan, bayan da wasu mutane 400 ‘yan ta’adda, da suka haxa da masu garkuwa da mutane, suma suka yi rantsuwa, da sun bar aikata waxannan ayyukan ashshan. Da yake yi ma ‘yan jarida bayani a Kaduna bayan da ka kammala bikin, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna Austin Iwar, ya bayyaba cewar, su waxannan da suka tuban, sun yi amfani da wata dama da gwamnati ta bayar da kuma shugaban Rundunar ‘yansanda ta qasa Ibrahim Idris. Iwar ya ci gaba da bayanin baya ga barin aikata duk wasu ayyukan ashsha,
waxanda suka tuba xin zasu miqa dukkan makaman su ga gwamnati. Iwar ya qara bayyana cewar ’’ Nan bada daxewa ba zamu fara amar makaman, tun da yake wasu sun xauki alawarin zasu maido da kayayyakin makaman nasu, amma ba a gaban mutane ba’’. ‘’Xaya daga cikin dabarun da zamu yi amfani dasu shi ne, zamu ga yadda zamu kai ga zuwa wurin shugabannin al’umma, zamu kuma yi amfani ne da yadda ake kare al’umma ta aiki; wanda yayi kama dana ‘yansanda.’’
‘’Idan mutum yana son ya yi maganin wata matsala, ya kamata yayi magana da mutanen da suka samar da ita matsalar, mun yi tarurruka da maharba, wannan kafin a xauki dukkan matakai na kawo qarshen ta’addancin ke nan.’’ ‘’A ce ana da matasa waxanda suke cikin daji, suna aikata dukkan laifukan da basu da qyau, su kuma fto suce sun daina aikata laifukan, har su kai ga rantsuwa da Alkur’ani mai girma, cewar ba zasu sake komawa ga harkar aikata
ta’addanci wannan wani abin farin ciki ne.’’ ‘’Ana iya ganewa abu ne mai wuya a ce nmai aikata laifuka da yawa ya fito gaban mutane, ya bada sanarwar ya daina aikata dukkan ayyukan ashsha, waxanda ya saba yi’’. Shugaban qungiyar ‘yan qungiyar Vigilante na Anchau, ya jinjinawa jami’an tsaro, saboda haxin kan da suka ba, shi tsarin da aka vullo da shi, abin da ya fi bashi mamaki shi ne yadda suka shawo kan su masu aikata laifukan.
kashe wani mutum mai suna John Mogidi, haxa kai domin qaqarin kisan wani mutum da ake kira Innocent Akemu, waxannan laifuka su, suka sa aka gurfanar dasu. Alqalin a hukuncin da ya yanke, ya xaure Agbofodo zuwa shekaru goma sha huxu, a kurkuku, saboda an same shi da laifin haxa kai da niyyar kisan kai, ta ratayewa a laifi na biyu. Bayan haka kuma ta yanke hukunci a laifuka na uku, da kuma huxu,cewar tsohon shugaban al’umma, za a bar shi kurkuku, har shekaru bakwai, sai kuma shekaru 21 wanda hukuncin laifi na huxu ne, wato qoqarin kisa. Shi dai marigayin da kuma wanda aka tabbatar da ya aikata laifin dama can suna zaman manja da doya, a dalilin shugabancin, qungiyar matasa ta al’umma, wanda kuma daga qarshe sai
abin ya kai ga ana tayi ma juna maganganun da basu dace ba, da suka haxa da shi maganar da ya furta cewar sai ya kashe, Mogidi, bayan ‘yuan kwanaki da ikirarin sai yayi kisan, sai aka samu shi marigayin an kashe shi. Xaya daga cikin masu bada shaida Akemu ya shaida ma kotu cewar, shi wanda ake zargin ranar 16 ga watan Mayu ne, yasa matasa bakwai riqe da makamansu, cikin motoci biyu,Prado SUV da kuma Toyota Camry,suka amshe mashin xin da shi , da kuma marigayin, suke kan shi akan hanyar NPA a Akpa, a canne kuma ka kashe marigayin. Mai bada shedar ya qara jaddada cewar da yake su matasan suna amfanine da umarnin wanda aka yanke ma hukuncin, sai suka tilasata ma Mogidi ya shiga motar, amma sai ya qi, daga nan
sai xaya daga cikin matasan wanda ake kira Darlinton ya harbi shi Mogidi ba sau xaya ba, a sanadiyar haka nan take kuma ya faxi ya mutu. Wanda ya aikata laifin a bayanin da yayi ma’yansanda ya qaryata cewar da hannun shi a kisan, amma kuma ya kasa faxawa su ‘yansanda, inda yake lokacin da aka aikata laifin kisan kan. Lokacin da ake shara’ar sai yayi qaryar cewar yana gida, amma kuma ya kasa kiran wani wanda zai ma shi sheda, a qoqarin da yake na, ba kotun hujjar gamsarwa. Agbofodo ya qaryata kiran marigayin ta waya inda yayi ma shi barazanar kashe shi, amma kuma da aka je kamfanin da marigayin ke amfani da layin su, a cikin wayar shi, aka kuma kawo kotu a matsayin sheda, sai abin ya nuna cewar shi dai ba mai gaskiya ba ne.
Kotu Ta Yanke Ma Shugaban Al’umma Na Delta Hukunci Kisa Ta Hanyar Rataya
Daga Idris Aliyu Daudawa
Wata babbar kotu a jihar Delta wadda tayi zama a Asaba ta yanke hukunci akan wani mai sarautar gargajiya na da ake kira Unuewvoro, wanda shi , shugaban al’umma, na Ekpan a gundumar Uvwie, Newton Agbofodoh, zuwa kisa ta hanyar ratayewa. Shugaban al’ummar dai an kama shine ranar 17 ga watan Yuni, na 2016 lokacin da jami’an tsaro da suka haxa da’yansanda da kuma sojoji suka kai hari gidan shi, ana dai zargin shi ne da aikata laifin kisa na Mogidi , da kuma qoqarin kisa, wannan mutumi shi mataimakin shugaba ne na matasan al’ummar Ekpan. Da yake yanke hukuncin ranar Talata, kotun ta gano wanda ake zargi da ikata laifin ne, saboda laifuka huxau da suka haxa da, haxa kai domin ayi kisan kai,
29
A Yau Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
Qasashen Waje Mahamadu Isuhu Ya Bayyana Samun Nasarori A Shekara Ta Biyu
Tare da Rabiu Ali Indabawa 08069824895
Gasar Ajin Qwararru Ta Bana Ta Matasan ‘Yan Wasa Ce – Jamilu Wada Aliyu
Daga Rabiu Ali Indabawa
Yayin da gwamnatin Mahamadu Isuhu na Jamhuriyar Nijar cika shekaru biyu a wa’adinsa na qarshe, jami’an gwamnatin sun ce sun cika wasu daga cikin alqawuran da suka xauka a lokacin yaqin neman zave. Sai dai masu fafutuka na bayyana akasin hakan. Gwamnatin Jamhuriyar Nijar qarqashin jagorancin Mahamadu Isuhu ta ce, ta samar da ci gaba na a-zo-a-gani a qasar a wa’adinta na biyu. A jiya Lahadi shugaba Isuhu ya bayyana a gidan talbijin inda ya
zayyana ire-iren cigaban da qasarsa ta samar yayin da ya cika shekara biyu a wa’adinsu na biyu. “Ga likitoci da aka samar a asibitoci daban-daban, musamman ma a Maraxi, da Yamai, da kayayyakin aiki da aka samar a asibitocin, hakan ya sa a irin kididdigar da ake yi, an sa Nijar a cikin qasashen da ke kiyaye lafiyar al’umarta.” In ji Ministan raya al’adu kuma kakakin gwamnatin ta shugaba Isuhu, Asoumana Malam Isa. Ya qara da cewa an samu ci gaba a fannin ilimi yana mai cewa “Gano matsalolin da malamai ke da su a
fannin na ilimi wannan ma ci gaba ne.” Sai dai gwamnatin ta shugaba Isuhu ta amince da cewa akwai sauran matsaloli da qasar ke fuskanta, kamar na cin hanci da rashawa. Amma kuma qungiyoyin fararen hula na ganin akwai kurakurai da gwamnatin take tafkawa tun bayan da shugaba Isuhu ya samu wa’adi na biyu. “Shi yana murna ya shekara biyu, mutane kuma suna baqin ciki ya yi shekara biyu yana muzguna masu.” Inji Jami’in fafutuka Gamatou Muhammadu.
Shugaba Trump Ya Yi Watsi Da Shirin Kare Yaran Da Aka Shigo Dasu Qasar Tun Suna Qanana
Shugaban Amurka ya yi watsi da shirin da ya kare yara qanana da aka shigo da su ta varauniyar hanya dake da laqabin DACA saboda ba’a sakarwa jami’an shige da fice mara ba, Mexico kuma tana barin mutane na kwararowa cikin qasar. Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Lahadi, yayi kira da a kafa tsauraran dokokin shige da fice, kuma ya lashi takobi cewa zai dakatar da shirin ba matasan da aka shigo da su Amurka tun suna qanana izinin zama a qasar, shirin da ake yi wa laqabin DACA a taqaice. Trump ya xora a shafinsa na Twitter a jiya da safe cewa ba a
sakarwa jami’an tsaro dake sintiri a kan iyaka mara su gudanar da ayyukansu, saboda dokoki da masu sassaucin ra’ayi suka kafa wanda ya ayyana a kama, daga bisani a saki baqin hauren.” Ya ce lamarin na qara zama mai haxari, yanzu ayari- ayari ke shigowa Amurka saboda su amfana qarqashin sabon shirin na DACA. An vullo da shirin ba da matsuguni ga yaran da aka shigo da su Amurka tun suna qanana ko kuma DACA ne loakcin gwamnatin shugaba Obama, kuma shirin ya bai wa yaran da aka shigo da su Amurka ta varauniyar hanya izinin zama da yin aiki a Amurka.
Gwamnatin Trump ta kawo qarshen shirin a cikin watan Satumba, amma kuma ta ba majalisun qasar dama su fito da tsari na dindindin a kan makomar masu amfana da shirin. Tun da farko Trump ya ce zai amince da cigaban shirin DACA ne, in dai majalisun qasar sun tabbatar da kuxaxen da za a aiwatar da gina katanga a kan iyakar kudancin qasar da Mexico. A wani sakon Twitter da ya aike da safiyar jiya Lahadi, Trump ya xora laifi a kan Mexico cewar ba ta yin wani abu domin hana baqin haure kwarara zuwa Amurka, kuma yana barazanar dakatar da yarjejeniyar cinikayya da Mexico, saboda hakan.
Shugaban qungiyar qwallon qafa ta Giodano dake Kano Jamilu Wada Aliyu ya ce, gasar bana za ta sha banban da sauran da aka tava bugawa, duba da qungiyoyin da za su fafata a gasar. A tattaunawarsa da wakilinmu a Kano Jamilu Wada cewa yayi duba da sabbin qungiyoyi da suka shiga gasar ta bana da kuma manyan qungiyoyi da suka faxo daga ajin firimiya ya sanya gasar zama ta musamman, uwa uba da yawa daga cikin qungiyoyin sun rungumi salon bai wa matasan ‘yan wasa dama abin da ya sanya kusan kaso 80 bisa 100 na ‘yan wasan sabbi ne kuma masu qarancin shekaru kamar yadda hukumar wasanni ta qasa ke ta kira, Da yake amsa tambaya kan ranar fara wasan Jamilu Wada cewa yayi, lokacin yayi daidai duk da cewa kamar ya qure, amma daga yadda aka fitar da jadawalin abu ne mai qarfafa gwiwa,
kuma da alamun jinkirin zai zama alheri ga qungiyoyin da za su buga gasar. Dangane da wasanin da qungiyarsa da za ta buga, cewa yayi ba abu ne mai sauqi ba duba da qungiyoyin da za mu fara wasan da su, kuma a gida, amma da qoqarin ’yan wasan da haxin kan magoya baya da adduoi da masoya ke yi mana tun bayan samun nasarar mu, to muna da qarfin gwiwar da za mu samu nasara da ikon Allah. Ya qara da cewa abin alfaharinmu shi ne yadda al’ummar Kano suka karvi wannan qungiya kuma suke yi mana fatan alheri, musanman kuma qarfin gwiwa da shugabannin babbar qungiyar mu ta Kano pillars suke bamu ya qara mana qaimi fatanmu shi ne mu fidda jihar Kano kunya da kyakykyawan wakilcin da kowa zai alfahari da shi. A ranar 31 ga watan Maris ne za a fara gasar ta bana inda Qungiyar Giodano za ta fafata da Bimo FC a Kano.
Wasanni 30
A Yau
Talata 3.4.2018
Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com
Conte Ba Zai Ci Gaba Da Zama A Chelsea Ba, Inji Garry Neville
Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Tsohon xan wasan qungiyar qwallon qafa ta Manchester United Garry Neville ya bayyana cewa mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Chelsea, Antonio Conte ba zai ci gaba da zama a qungiyar ba zuwa kakar wasa mai zuwa. Chelsea dai tayi rashin nasara har gida a hannun qungiyar Tottenham a wasan firimiya daci 3-1 wanda kuma sakamakon hakan ya sa abune mai wahala qungiyar ta Chelsea ta iya kaiwa zuwa mataki na huxu domin wakiltar qasar ingila a gasar cin kofin zakarun turai a kakar wasa mai zuwa. A shekararsa ta farko dai a qungiyar, Conte ya lashe kofin firimiya sai dai Garry Neville ya ce daman haka halin Chelsea yake basa riqe mai koyarwa yayi shekara da shekaru a qungiyar. Yaci gaba da cewa Conte ba zai ci gaba da koyar da Chelsea ba zuwa kakar wasa ta gaba saboda daman ya faxi haka tun farkon fara gasar saboda haka tsarin qungiyar yake idan kana samun nasara zaka ci gaba da zama amma idan kuma ka samu akasin haka to abune mai wahala kaci gaba da zama. Ya qara da cewa koda yaushe Conte yana qorafin cewa qungiyar bata siyo masa yan wasan dayake soba saboda haka yake yawan sukar shugabannin qungiyar idan yana hira da manema labarai a sakamakon haka yajawo rashin jituwa da wasu daga cikin shugabanni a qungiyar. Sai dai ya ce qungiyar ta lashe kofuna kusan 14 cikin shekaru goma saboda haka dole ne ka yabawa qungiyar da kuma duk masu horar da qungiyar amma dai Conte yazo qarshe a qungiyar.
‘Har Yanzu Ba Mu Lashe Kofin Laliga Ba’ Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Mai koyar da ‘yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Barcelona, Enesto Valverde ya bayyana cewa har yanzu qungiyarsa bata lashe kofin Laliga ba saboda akwai ragowar wasanni, sai dai ya ce kawo yanzu sun xauki hanya. Ya bayyana haka ne bayan qungiyarsa ta tashi daga wasa 2-2 da qungiyar qwallon qafa ta Sevilla a wasan Laliga da suka fafata a ranar Asabar xin da ta gabata, bayan Sevilla ta
zura wa Barcelona qwallaye biyu daga baya kuma duk suka farke qwallayensu bayan Messi ya shigo wasan. Barcelona dai tana mataki na farko da maki 12 tsakaninta da Atletico Madrid wadda take mataki na biyu akan teburin, sai dai ya ce dole sai sun sake dagewa a ragowar wasannin da suka rage wa qungiyar idan har suna son lashe gasar ta bana. Ya cigaba da cewa har yanzu ba su lashe Laliga ba amma sun kusa saboda haka za su ci
gaba da neman maki ido rufe har wasan qarshe. Barcelona za ta karvi baquncin qungiyar qwallon qafa ta AS Roma a wasan zakarun turai a ranar Laraba kafin daga baya kuma su karvi baquncin qungiyar Leganese a gida a wasan Laliga.
Mourinho Zai Kashe Fam Miliyan 200 Akan Sababbin ‘Yan Wasa Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban gudanarwar qungiyar qwallon qafa ta Manchester United, Ed-Woodward ya shirya ba wa Mourinho kuxi kusan fam miliyan 200 domin sayo sababbin ‘yan wasan da za su qarawa qungiyar qarfi. Manchester United dai tana son qara qarfin qungiyar domin goga kafaxa da kafaxa da Manchester City a kakar wasa mai zuwa inda tuni mutanen biyu suka fara tattaunawa akan irin ‘yan wasan da ya kamata qungiyar ta nema.
Rahoton ya ce manya-manyan ‘yan wasa da suka haxa da Jorginho da Alex Sandro da Toby Alderweid da Tierney da Danny Rose da Hector Bellerin su ne ake saran qungiyar za ta saka kuxi domin ganin ta same su a kakar wasa mai zuwa. Sai dai wataqila ‘yan wasa irinsu Damian da Blind da Rojo su ma Luke Shaw za’a ba su damar tafiya yayin da kuma Phil Jones da Chris Smalling sunma zansu iya tafiya amma idan har qungiyar ta samu madadinsu. Mourinho dai yayi shirin lashe gasar Firimiya a kakar wasa ta gaba kuma idan
har bai lashe ba wataqila qungiyar za ta iya rabuwa da shi domin neman wanda zai lashe gasar ta firimiya sakamakon rabon qungiyar da gasarFirimiya tun 2013 shekarar da tsohon mai koyarwa Sir Alex Ferguson yana koyar da qungiyar. Manchester United dai kawo yanzu tana mataki na biyu akan teburin firimiya da maki 15 tsakaninta da Manchester City wadda take mataki na xaya, sai dai United xin har yanzu tana fafatawa a gasar cin kofin qalubale na FA inda za ta kara da Tottenham a wasan kusa da na qarshe a qarshen wannan watan a filin wasa na Wembley.
A Yau Talata 3 Ga Afrilu, 2018 (16 Ga Rajab, 1439)
WASANNI 31 Dole Ne Sai Messi Ya Ci Gasar Cin Kofin Duniya Kafin A Haxa Shi Da Maradona Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Salah Da Mane Da Firmino Su Na Da Wahalar Riqewa, Inji Guardiola Mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Manchester City Pep Guardiola ya bayyana cewa abune mai wahala riqe yan wasan gaba na Liverpool guda uku Muhammad Salah da Sadio Mane da Roberto Firmino saboda su na da wahalar sha’ani. Guardiola ya bayyana haka ne a shirye shiryen da qungiyarsa keyi na kai ziyara filin wasa na Anfield domin fafata wasan kusa dana kusa dana qarshe na gasar zakarun turai a ranar Laraba. Yaci gaba da cewa, ba kawai Muhammad Salah bane abin tsoro a Liverpool domin Mane da firmino ma su na da hatsari sosai domin sun basu wahala a wasan da suka dokesu a wasan firimiya a watan janairun daya gabata. Qungiyar qwallon qafa ta Liverpool ce qungiya xaya tilo data doke Manchester City a wannan kakar a gasar firimiya bayan data doke ta daci 4-3 a filin wasa na Anfield wasan da Firmino da Mane da Salah xin duk sun zura qwallo a raga. Yaci gaba da cewa yanzu akwai aiki agabn yan wasansa na baya ta yadda zasuyi qoqarin ganin sun hana waxannan yan wasa yin qoqari saboda idan har zasu samu dama to zasuyi musu illa ba qarama ba. Sai dai Guardiola ya ce wannan lokacin gasar zakarun turai ce kuma ya san suma bazasu saki jiki ba sosai kamar yadda suka buga a wasan firimiya amma kuma ya ce tabbas akwai qalubale da yawa a wasan. Salah dai ya zura qwallaye 37 a wannan kakar yayinda Firmino da Mane kuma suka zura qwallaye 38 jumullar qwallayensu su biyu.
Tsohon mai koyar da ‘yan wasan tawagar qasar Argentina, Carlos Bilardo ya bayyana cewa idan har Messi ya na son a ci gaba da haxa qwarewarsa da ta Maradona dole ne sai ya ci wa qasarsa gasar cin kofin duniya a wannan shekarar. Bilardo, wanda ya jagoranci qasar Argentina a matsayin mai koyarwa a shekarar 1986 tare da xan wasan qasar Maradona suka lashe kofin duniya ya ce kofin duniya ne kawai ya rage wa Messi ya cika duk wani tarihi a rayuwarsa. Messi dai ya kusa lashe gasar cin kofin duniya a qasar Brazil, sai dai qasar Jamus ta doke su a wasan qarshe. Sannan kuma har ila yau sun yi rashin nasara sau biyu a wasan qarshe na cin kofin kudancin Amurka a hannun qasar Chile har sau biyu a jere a shekarar 2015 da kuma 2016. Sai dai xan wasan ya lashe duk wata gasa da ya buga a Barcelona abinda ya sa ake cewa suna matsayi xaya da Maradona, amma Bilardo ya ce dole sai ya lashe kofin duniya sanann zai yarda cewa ya kai matsayin Maradona wanda qasar Argentina ba ta tava yin xan wasa kamarsa ba a duniya. Sannan ya ce Argentina suna da babbar damar lashe kofin a wannan shekarar musamman ma idan suka ba wa Messi damar cin gashin kansa ba tare da yana sakkowa yana taimakawa ‘yan wasan baya ba tabbas zai yi qoqari yadda ya kamata. A qarshe ya ce tawagar qasar har yanzu tana da qarfi kuma za su iya fin shekarar 2014 ma shekarar da suka je wasan qarshe da qasar Jamus domin ya ce qasar Jamus bata fi qarfinsu ba kawai nasara suka samu. Argentina dai za ta fafata wasan rukuni da qasashen Iceland da Nijeriya da kuma qasar Crotia a qasar ta Rasha.
Neymar Ba Zai Bar PSG Ba, Inji Mbappe Daga Abba Ibrahim Wada Gwale
Xan wasan gaban qungiyar qwallon qafa ta PSG, Kylian Mbappe ya bayyana cewa xan wasa Neymar ba zai bar qungiyar ba a qarshen kakar nan da ake ciki duk da raxe-raxin da ake yi na cewa zai koma Real Madrid. Real Madrid dai ita ce qungiyar da aka bayyana ta fara zawarcin xan wasan watanni kaxan bayan ya bar abokiyar hamayyarsu wato Barcelona. Mbappe ya ce yana da yaqinin Neymar zai ci gaba da zama a qungiyar har zuwa wani lokaci mai tsawo, sannan shi ma mai koyar da ‘yan wasan qungiyar ya ce yana sa ran zai ci gaba da zama a qungiyar. Ya cigaba da cewa surutu ne kawai na ‘yan jarida cewa Neymar zai tafi domin suna tattaunawa kuma yana turo masa labarai kuma shi ma ya yi masa fatan alheri, sannan kuma yayi masa fatan buga a gasar cin kofin duniya cikin nasara, amma bai yi masa fatan lashe kofin ba, saboda shi ma yana son lashewa da qasarsa ta Faransa. Ya qara da cewa sun buga kakar wasa mai kyau a PSG duk da cewa basu yi nisa a gasar zakarun turai ba, amma gasar qasar Faransa ta yi armashi kuma daman ba su cancanta da su yi gaba ba a gasar zakarun turai tun da Real Madrid ta fisu buga wasa mai kyau a haxuwarsu. Nan da makonni 2 zuwa 3 ake sa ran Neymar zai dawo domin cigaba da xaukar horo bayan dogon hutu da yayi sakamakon jinya da yayi bayan an yi masa tiyata a qafarsa.
Perez Ya Na Son Zidane Yayi Amfani Da Bale A Farkon Wasa A Karawar Juventus Wasu rahotanni daga qasar sipaniya sun bayyana cewa shugaban gudanarwar qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid Florentino Perez ya buqaci mai koyar da ‘yan wasan qungiyar Zinedine Zidane ya fara wasa da Gareth Bale a ‘yan wasan farko a wasan da qungiyar za ta kara da Juventus. Real Madrid dai za ta kai ziyara Juventus domin fafatawa a wasan kusa da na kusa da na qarshe na gasar cin kofin zakarun turai da aka haxa qungiyoyin biyu a watan da ya gabata. Rahoton ya ce Perez ya na son Bale ya samu dama domin ya nuna kansa don manyan qungiyoyi su neme shi ya tafi sakamakon qungiyar tana son sayar da xan wasan kuma bata son sayar da shi da araha. Qungiyoyin Manchester United da Chelsea da Tottenham ne dai suke zawarcin xan qwallon wanda ya koma Real Madrid daga qungiyar Tottenham akan kuxi fam miliyan 86 wanda hakan ya sa ya fi kowanne xan wasa tsada a duniya a shekarar. Tun bayan komawarsa qungiyar Real Madrid a shekarar 2013 Bale yake fama da ciwo a qungiyar sai dai duk da haka ya buga wasanni 179, sannan kuma ya zura qwallaye 79 a raga sannan kuma ya taimaka an zura qwallaye 58 a raga.
3.4.18
AyAU LEADERSHIP
Talata
Don Allah Da Kishin Qasa
www.leadershipayau.com Leadership A Yau
JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA
LeadershipAyau
No: 113
WASANNI
‘Har Yanzu Ba Mu Lashe Kofin Laliga Ba’
N150
> shafi na 29
Xumama Da Canjin Yanayi Aliyu Dahiru Aliyu
A watan Disambar bara aka samu ruwan sama a wasu daga jihohin Arewa, ciki har da Abuja, savanin yadda aka saba samun bisa tsarin jadawalin ilimin Jugrafi da yake nazartar halayyar kasa. A watan Maris din da ya gabata kuwa aka samu jerin kusan mako guda ana wani irin mai hade da yanayin sanyi tare da zafi-zafi kadan tun daga Abuja har zuwa jihar Kano. Abin ya zo wa kowa da mamaki banda iri na yan kadan da dama mun sha faxar hakan za ta iya faruwa. Lokacin da akai ruwa a watan Disamba, dayawa wasu sun xauka saukar rahama ce, amma ni ina kallon hakan a matsayin wata manuniya da Allah yake so ya nunamana cewa mu shirya ko kuma azabarsa ta isa gare mu baki daya! Kuma dai kun san idan azaba tazo ba ta barin wai wanda zai ce babu ruwansa. Idan ta tashi zuwa to kan mai-uwa-da-wabi take dira. Idan iri na basu yi magana ba to tabbas wata rana dukanmu tare za mu yi gudan hijira ko kuma mu dinga rububin karbar tallafi daga kasashen waje. Wa zai so haka? Allah ya kiyaye. Wannan ruwan da aka samu na nuni da gurvacewar yanayi ne. Mun sassare bishiyoyinmu kuma mun kasa dasa wasu. Zai yi wuya ka ga yanzu, a unguwannin da ba tsarin gwamnati ba, an yi bishiyoyi a qananun gidajen da muke zaune aciki. A wata sabuwar unguwa ko a Kano da aka xauko hotonta daga tagar jirgi, an gano babu alamun kore sai dai ja kawai. Wata alama da take nuni da cewa mun sare bishiyunmu kuma mun kasa dasa wasu. To amma fa Allah ba ya kiyayewa sai mun kiyaye da kanmu. Allah ba ya canjawa mutane komai sai abinda suka fara canjawa da kansu. Lokacin da Allah yace ya sanar da Annabi Adamu sunaye ba wai yana nufin cewa kai ma ka zauna kana rokon Allah ya sanar da kai sunaye bane ba tare da ka yi yunkuri da kanka ba. Allah ya fada cewa shi fa da Alqalami yake sanarwa. Domin ka nemi Allah ya sanar da kai to sai ka dauki kayan karatu, littafi da Alqalami, domin ka cigaba da nazari don ya sanar da kai ilimi. Ta haka Allah yake sanar sa mutum abinda bai sani ba. Da wannan siyaqin za mu gane cewa akan komai da zaka roki Allah to kana buqatar ka yi wani qoqari a matakin farko domin sai ka tashi Allah zai taimakeka. Babu dalilin zama a gida kuma kana cewa Allah ya
dahiraliyualiyu@gmail.com
kaika China ko Amerika kuma kana kwance. Sai ka nufi filin jirgi to kuma sai ka yi addu’ar Allah ya kiyaye hanya kuma ya kaika lafiya domin shi yake da iko da jirgin da kuma mai tukin jirgin. Wannan na fara bayani akai ne don kada wani ya xauka cewa Allah yana abu babu sababi ne. Duk lokacin da aka kaucewa tsarin Allah akan komai to za a haxu da matsaloli. Mutane suna xauka zunubi ne yake janyo gurvacewar muhalli ko saukar azaba. Babban zunubin da yake janyo lalacewa da gurvacewar muhalli shi ne kaucewa tsarin da xabi’a take dashi. Duk wanda ya gurvata ruwan sha to zai samu annobar cutar kwalara. Wanda ya tashi bom xin nukiliya to tabbas zai ruguza gari ne. Duk abinda yake samun mutane na azabar da take fita da musiba to mutanene da kansu suka janyo. Lokacin da mutane suka yanke bishiyu kuma suka fitar da iskar gas mara kyau to tabbas suna rusa muhallinsu da hannunsu ne. Kada musibar tazo kuma mutane su ce Allah ne ya jarrabesu bayan su suka tsoma hannunsu dakansu! Wannan ruwan da aka gani a watan Disamba da kuma hazon da aka gani a watan Maris, alama ce ta cewa akwai barazanar canjin yanayi saboda dumamar yanayi. Yan bishiyun da suke sanyaya muhallin duk an ciresu. An fi bukatar fili ko gawayi fiye da yadda rashin bishiyu suke barazana ga muhallinmu. Bara na gayamaka illar da hakan za ta iya janyowa. Ka dauka kai manomi ne da ka gama
haxa shukarka kana jiran ruwa a watan Yuni. Maimakon kaga ruwan sama a watan sai kawai ka ga sanyi ya buso shukarka duk ta bushe! Idan fa ba kai kaxaine kayi shukarba to duka manoma wannan canjin yanayi zai shafa. Daga nan sai fari saboda canjin yanayi. Wannan shi ne qaramin misali da zan iya baka na matsalar da canjin yanayi za ta iya bayarwa. Me ya kamata mu yi tun kafin wannan matsalar ta yi qarfi? Tun yanzu ya kamata mu yi babban shiri wajen wayar dakan al’ummarmu muhimmancin dasa bishiyu a matakin farko da kuma illar sare bishiyu. Gwamnati na nata kokari wajen ganin an dena amfani da injina masu fitar da hayakin da za su iya lalata sararin sama, saura ga qungiyoyi masu zaman kansu da su dinga bita ta musamman don ilimantar da al’umma kan muhimmanci gyaran muhalli da kuma dasa bishiyu a inda ya dace. Mu dena sare bishiyu ba tare da dasa wasu ba domin hakan babbar illa ce ga rayuwarmu. Malamai ma za su iya taka rawarsu anan. Ni tunda nake karatu ban ga wani addini da ya kai na Musulinci mutunta bishiyu ba. Hatta lokacin yaqi an haramtawa musulmi ya sare bishiya ko da a garin da ba nasa bane. Hadisai masu yawa sun bayyana cewa dasa bishiya haxe yake da babban lada mai yawa don ana lissafa ladan gwargwadon ‘ya’yan bishiyar ne. Dukkaninmu muna da hanyoyin da zamu taimaki duniyarmu. Kuma dai taimakon duniya tamkar taimakon
Muqalar Talata +2349039128220 (Tes Kawai) bayin Allah ne. Shi kam Allah bai da babban abinda yake so mu yi fiye da mu taimakawa bayinsa. Lokacin da yace a rantamasa bashi ma ai bayinsa yace a bawa. Lokacin da ya kira masallaci xakinsa ai bayinsa ne suke shiga. Masallaci kuwa ba iya gurin sallah bane; makaranta ce haxe da gurin zaman bayin Allah. To idan muka taimaki duniya ta hanyar kuvutar da ita daga xumamar yanayi to kamar mun taimaki bayin Allah ne waxanda za su iya salwantar da dukiyarsu da kuma rayuwarsu saboda gurbacewar yanayi. Kowannenmu zai iya dasa bishiya ko a gurin aiki, ko a makaranta ko kuma a wani dajin. Bishiya guda xaya da zaka dasa za ta taimaki duniya. Hausawa ma na cewa : wanda za shi sama ya taka leda ai ya rage hanya. Ina ga wanda zai taimaki duniya kuma ya dasa bishiya ko da guda xaya ce? Ya kamata kuma gwamnati ta dawo da al’adar dasa bishiyu acikin ma’aikatunta da kuma makarantunta. Kai har makarantun da ba na gwamnati ba a sanya su bisa tsarin dasa bishiya. Na je firamaren da na yi na ga duk an sare bishiyun da na sani akwai a lokacin ina xalibin makarantar. Akwai wata firamaren kusa da gidanmu ita ma dai yanzu duk babu bishiyoyin dogon yaro da na sani a makarantar tun ina yaro. A makarantar da na koyar kuwa, wata karamar sakandare ta mata, babu ko da bishiya guda daya balle kuma ciyawa. To idan aka rasa bishiyu a guraren gwamnati a ina kuma za a samu?
Babba Da Jaka An fid da sunayen varayin gwamnati –Labarai
Yaushe za a damqe su?
Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 0703 6666 850; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 01-8963459. E-mel: leadershipayau@yahoo.com