Leadership A Yau 5 Ga Afrilu 2018

Page 1

5.4.18

AyAU Alhamis

LEADERSHIP Don Allah Da Kishin Qasa

JARIDAR HAUSA TA FARKO MAI FITOWA KULLUM A NIJERIYA

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

5 Ga Maris, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

LeadershipAyau

No: 119

N150

Baquwar Cuta Ta Halaka Mutum 10 A Jigawa Daga Munkaila Abdullah, Dutse

Rahotanni sun bayyana cewa, kimanin mutane goma ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu yadda wasu kuma da dama ke kwance a asibiti don karvar magani sakamakon varkewar wata baquwar cuta a qauyukan Baro, Ari, Gamji da Maule dake qaramar hukumar Babura a jihar Jigawa.

Shugaban qaramar hukumar ta Babura Alhaji Muhammed Ibrahim ya tabbatar da afkuwar al’amarin ya yin zantawarsa da ma nema labarai ta wayar salula. Shugaban ya bayyana cewa, zuwa yanzu dai basu sami tabbacin musabbabin cutar ba sakamakon sai ma’aikatar lafiya sun gwada sannan su bada bayanai a matsayinsu na masana fannin lafiya. Rahotanni sun bayyana cewa, baquwar cutar ta

bayyana ne kwatsam a qauyen Baru yadda wasu mutanen suka fara da zazzavi da kuma amai yadda kafin wani qanqanen lokaci sai mutum ya ce ga garin kunan. Haka kuma bayanai sun nuna cewa, a wannan qauye na baru an rasa rayukan mutane matasa maza su huxu. Haka kuma, bayanai sun nuna cewa, sakamakon vullar cutar a garuruwan Ganji da Maule yadda

anan kuma aka rasa rayukan mutane biyar. Shi ma wani mazaunin qauyen Hardo Umar ya bayyanawa majiyarmu cewa,a halin da ake ciki a yanzu akwai mutane uku da ya sani suna can Asibiti suna karvar magani. LEADERSHIP A Yau , ta yi iya bakin qoqarinta domin ganawa da kwamishinan lafiya na jihar Dakta Abba Zakar don jin matakan da suka xauka amma har zuwa loakacin haxa wannan rahoto al’amarin ya ci tura.

Rashawa Ta Fi Cutar –Magu Kansa Illa 4

• Shugaban Hukumar Yaqi Da Cin Hanci Da Rashawa, Ibrahim Magu (a tsakiya); Daraktan Sashe na LEADERSHIP A Yau, Mubarak Umar (na biyu a dama); Editan Jaridar LEADERSHIP A Yau, Sulaiman Bala Idris (na farko a hagu) tare da Editan Jaridar LEADERSHIP A Yau LAHADI, Malam Nasir Gwangwazo (na farko a dama) jiya a yayin wata ziyarar musamman da tawagar LEADERSHIP A Yau ta kai wa Shugaban a hedikwatar EFCC dake Abuja

’Yan Fashi Sun Kai Hari Sanata Mustapha Bukar Ya Rasu Wani Coci A Abuja > Shafi na 5

> Shafi na 14


2 NAZARI

A Yau

Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Xankwambo: Gwarzon Namiji A Shekaru 56 Daga Musa Shua’ibu

Kafar ‘Google’ ya sauqaqa mana lamurra da daman gaske. Bincike kaxan na yi a kafar inda na samu bayanai dangane da Gwamnan Jihar Gombe. Lokacin da nake bankwana da Jami’ar Ahmadu Bello, a daidai wannan lokacin ne wannan matashi kuma zaqaquri aka xauke shi a wannan tsangayar da na bari. Dankwambo tare da taimakon wasu tsoffin xalibai, sun yi qoqari matuqa wurin sanya mu yin alfahari da jami’ar Ahmadu Bello. Daga binciken da na yi ne, na fahimci cewa a yau, wannan bawan Allah, Alhaji Hassan Dankwambo yake cika shekaru 56 da haihuwa. Domin kuwa an haife sa ne a ranar 4 ga watan Afrilun shekara ta 1962, an haifesa ne a unguwar Herwagana da ke cikin jihar Gombe. Ya yi karatun Firamare xinsa ne a Central Primary School Gombe, ya ci gaba da karatunsa ne a sakandarin Government Secondary School da ke Billiri, a jihar Gombe, sannu a hankali ne kuma ya nemi yin jarabawar (JAMB) domin samun zarafin shiga jami’a. Daga nan dai bayan samun nasara ya shiga jami’ar ‘Ahmadu Bello dake Zariya. Ya samu damar yin karatu a fannin ilimin hada-hadar kuxi da lisaffai (Accounting) wanda ya kammala digirinsa da sakamako mai daraja ta biyu. Sakamakon da ya fita da shi a wancan lokacin sai ka tona kafin ka samu wani ya fita da sakamako mai kyau kamar ta sa a jihar Bauchi (lokacin Gombe na haxa a jikin Bauchi). Sakamakon qwazonsa, ya faxaxa karatunsa inda ya tsunduma neman digiri na biyu a jami’ar Legas (UniLag), nan kuma dai ya nutsa ne a fannin ilimin tattalin arziki. Xankwambo na matashin shi, ya ci gaba da faxaxa iliminsa zuwa matakin gaba inda ya samu qarin karatun wata Difloma akan sashin na’ura mai qwaqwalwa ‘Computer Science’ a jami’ar jihar Delta wato Abraka. Daga bisani kuma, ya garzaya zuwa babban jami’ar Okada da ke jihar Edo domin samun shaidar digirin digirgir wato ‘PhD’. Hazaqarsa ta taimaka masa wajen gwanancewa

a fannoni daban-daban har guda bakwai, ya samu shaidun karamci da kuma halartar kwasa-kwasai da dama kan fannonin ilimi, misali, ya samu shaida a (ICAN) wanda har ta kai ya samu kan fannin qididdiga, bayan nan kuma ya kammala jami’a kan wannan kwarewar ta qididdiga. Sannan kuma ya kasance cikakken mamba ‘Institute of Chartered Accountants of Nigeria’ har zuwa yau. Ya kuma zama mamba a cibiyar nazarin aikin banki; mamba a cibiyar amsar haraji, mamba a ‘Nigerian Institute of Management’, mamba a cibiyar ‘yan kasuwa, mamba a cibiyar nazarin tattalin arziki. Har-ila-yau, Gwamna ya samu shaidun karatu a fannoni daban-daban, wanda hakan samar masa da qwarewa matuqa kan sha’anin rayuwar jama’a. Aqalla, ya samu gwanancewa fiye da misali wanda ta kai ya samu ilimi kan hada-hadar kuxi da sarrafawa. Mai girma Gwamna, ya samu shaida a jami’ar Harvard, Cambridge, Boston Massachusetts dukkaninsu ya samu shaidar kwasakwasan ne a kan fannin tsarin kuxi na duniya, matsaloli, inganta wa da kuma hanyoyin shawo kan matsaloli. A jami’ar Duke, DCID, da kuma jami’ar Durham, ya samu wasu kwasa-kwasan kan fannin tsara kasafin kuxi, tsara gudanar da kashe kuxaxen jama’a. Har wa yau, ya kuma ya sake zuwa wata jami’ar ta ‘Stanford University’s Business School’, inda ya samu gwanancewa kan sha’anin tattalin kuxi, sannan kuma a cibiyar nazarin ilimi ta Landan ya karanci sashen ririta kuxaxe da tsarawa gami da ci gabantar da sha’anin. Waxannan zurfafa ilimin na sa, ne ya sanya gwamnan jihar Gombe mai girma, Dakta Ibrahim Dankwambo ya maida sha’anin ilimi wani abu da ya sanya a gaba domin bayar da fifiko gaya, mene ne dalilin hakan? saboda ya san muhimmancin ilimi ga jama’arsa, don haka ne ya xauko ilimi a matsayin wani abu mai matuqar daraja a qarqashin gwamnatinsa. Dakta Dankwambo ya auri matarsa, Hajiya Adama Ibrahim Dankwambo,

•Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo.

wacce Allah ya azurta su da nagartatun ‘ya’ya guda biyar. Kamar uwa da uba, ‘ya’yan nasa sun halarci kwasa-kwasai daban-daban da manyan makarantu daban-daban domin su samu ingantaccen ilimi. Wannan gida mai xumbin albarka, zan iya misalta shi da cewa, gida ne wanda ya himmatu domin samar wa yara mata ilimi mai nagarta, da lafiya musamman tun a lokacin haihuwa domin rage yawaitar asaran jarirai a wajen haihuwa. Gwamnan Gombe, ya samu ilimin addininsa da kuma na zamaninsa, sau tari jama’a da daman gaske sun fi muhimmanta ilimin Nasara fiye da na addini, to shi ya haxa duk biyun ne dominya zama ya samu nagarta. A bisa haka ne ma, matarsa ta dage ka’in da kuma na’in wajen gangamin faxakarwa kan muhimmancin neman ilimi. Gwamna ya yi imanin ilimin iyaye mata da cewar su ne masu gina al’umma tun a matakin farko, mace uwa kenan, idan ta samu ilimin da ya dace za ta yi amfani da shi wajen ilmantar da ‘ya’yanta da kuma samar da nagartaccen tarbiyya a gare su. Ilimantar da mata, zai bayar da dama gina al’umma ta gari da kuma kula da ‘ya’ya yadda ya dace, wannan dalilin ne ya sanya gwamna da iyalansa suka tashi tsaye domin tabbatar da mata a jiharsa sun samu ilimi mai sunan ilimi. A bisa wannan gagarumar

gudummawar da wannan gidan suka bayar wajen ci gaban Gombe, an samu qarin masu cin jarabawa zuwa kashi 62% daga 23% da gwamna ya zo mulki ya samu a shekara ta 2011, a fannin ilimin mata kaxan, an samu gagarumar ci gaba daga matakin babu zuwa kashi 72% na matan da suke jihar. Wannan gagarumar ci gaba ne wajen gina al’umma. Dukkanin mutumin da yake da irin waxannan sanin, la-shakka jama’a za su amfana kwarai da iliminsa da kuma saninsa, a bisa haka ne a kowanne lokaci gwamnan ke qoqarin yin ayyukan da suka dace wa jama’ansa da kuma samar wa jama’an jiharsa hanyoyin samun ilimi, kowani xan jihar Gombe ya gamsu da yadda gwamnan ke tafiyar da mulkin jihar domin ya na da kwarewa matuqa musamman ta fuskacin hada-hadar kuxi da kuma tsara yadda za a kashesu. A yau da gwamnan jihar Gombe, mai daraja, da tarin fa’ida, mutum mai nafarta yake ciki shekaru 56 a duniya, ina da tabbacin gidaje da daman gaske a jihar Gombe suna cike da murna da kuma taya gwamna murna kawo wa yau a duniya, domin jagoran mai kishinsu, mai kuma sonsu na cika wannan shekarun. Ina mai cewa murna da taya murnar kawowa yau a Duniya, Barka da zagayowar ranar haihuwa! Musa Shua’ibu, ya rubutu ne daga jihar Kaduna


3

A Yau Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Ra’ayinmu

Yayin Da Aka Yi Bikin Ranar Mata Ta Duniya… A ranar Alhamis xin da ta gabata 8 ga watan Maris 2018, xaukacin al’ummar duniya suka gudanar da bikin ranar Mata ta duniya. Ranar 8 ga watan Maris, rana ce da aka keve musaamman domin qara sanar da duniya matsayi, qima da kuma darajar da Allah Ya yi wa Mata. Rana ce, da a kan gudanar da taruka domin yayata irin ci gaban da kuma gwagwarmayar da mata suka yi ko kuma ma suke kan yi a dukkanin sassan duniyar nan. Tun a farkon wannan qarnin ne aka keve wannan ranar ta 8 ga kowane watan Maris na kowace shekara domin nu na halin da matan ke ciki a jiya da kuma yau, rana ce da gwamnatoci, Qungiyoyin mata, Kamfanoni da ma sauran xaixaiku sukan yi taruka, shirya wasu bukukuwa na musamman, domin su tattauna halin da matan ke ciki saboda mahimmancinsu, a duk faxin duniyar nan. Ranar mata ta duniya, rana ce da a kan dakatar da komai domin a tsaya a yi dubi da kyau a kan qimar matan, a matsayin su na, Matan aure, Iyaye, manyan ‘yan kasuwa, Shugabanni, ‘yan gwagwarmaya, da makamantan hakan. Taken ranar ta wannan shekarar shi ne, “Lokaci ya yi: da ya kamata a sami canji a rayuwar mata,” a taqaice kenan, da turanci taken ranar matan ta bana shi ne, “Time is Now: Rural and Urban Activists Transforming Women’s Lives”. Bikin na bana, ya yi karo da yunquri kala-kala da matan ke yi a dukkanin sassan duniyar nan,na ganin sun fitar da kansu daga wasu al’adu ko dokokin da suke tawaye ne a cikin darajar da Allah Ya yi masu. Suke kuma gwagwarmayar tabbatar da samun ‘yanci wanda ya yi daidai da na kowane mahaluqi a bisa gaskiya da adalci ba kuma tare da nu na wani bambanci ba. A wasu qasashen kamar qasar Amurka da makamantansu, matan sukan gudanar da jerin gwano ne a bisa tituna da kuma bin gidaje a cikin birane da qauyaku, inda suke tunatar da mutane a kan wasu haqqoqinsu da aka tauye masu, musamman a wuraren da a kan bambanta albashin matan da na maza ko abin da ya shafi matsayin su wajen raba muqamai a siyasa da sauran qungiyoyi. Hakanan kuma sukan yi amfani da wannan ranar domin tunatar da al’umma haxarin da ke tattare da cin mutunci, tsagwama, qoqarin raina matsayi, Fyaxe, da duk da a kan yi wa matan. Mu a nan, muna ganin kamata ya yi Shugabanninmu da sauran masu faxa a ji, su yi amfani da wannan ranar ta wannan shekarar wajen tsayawa tsam da kuma yin dubi bisa hali da kuma yanayin da matan ke ciki musamman

ma matan karkara. Waxanda za mu iya cewa, sune kaso aqalla xaya bisa huxu na al’ummar wannan duniyar tamu. Tare da wannan ximbin yawan na su, da kuma gagarumar gudummawar da suke baiwa al’umma ta dukkanin fannoni, sai kuma sukan zama abin tausayi, domin kuma za ka taras a duk wani sashe na more rayuwar da suka taimaka wajen daxaxa ta, su ne a baya. Akwai bukatar xaukan matakai na gaggawa waxanda za su ciyar da rayuwar matan da muke kira da iyayen

al’umma gaba, tilas ne mu baiwa matan gudummawa ta kowane sashe kuma a birane da karkara da ma dukkanin qauyaku. Tilas ne mu zaqulo matan da suka yi dukkanin abin yabo a cikin al’umma domin mu yaba masu kamar yadda a kan yabawa kowa. Tilas ne mu qarfafi mata ‘yan gwagwarmayar fito da haqqi da qimar mata a duk inda suke. Sannan kuma ya zama wajibi ga gwamnatocinmu da su tabbatar da sun gusar da dukkan wani abu mai qarfafa qyama da kuma nu na bambanci ga

EDITA Sulaiman Bala Idris

MATAIMAKIN SHUGABA (NA MUSAMMAN) Christian Ochiama

MATAIMAKIN EDITA Bello Hamza

DARAKTAN SASHE Mubarak Umar

RUKUNIN KAMFANONIN LEADERSHIP SHUGABA Sam Nda-Isaiah

BABBAN MANAJAN DARAKTA Abdul Gombe BABBAN MANAJAN DARAKTAN KADARORI David Chinda MANYAN DARAKTOCIN KAMFANI Dele Fanimo Felicia Ogbonlaiye DARAKTAN KULA DA MA’AIKATA Solomon Nda-Isaiah DARAKTAN KULA DA KADARORIN KAMFANI Zipporah D. Tanko MANYAN MANAJOJI Ibrahim Halilu Femi Adekunle Ebriku John

manufarmu

LEADERSHIP A Yau jarida ce da ake bugawa a Abuja. Ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da shugabanci da wakilci nagari. Jaridar za ta ci gaba da kare muradun al’umma, ba kare ra’ayi da muradun mahukuntanta kaxai ba. Da waxannan qudirorin ne muke fatan jama’a za su xora mu kan Mizani. Haka kuma duk ra’ayoyin masu karatu da muke bugawa, ba manufar kamfanin LEADERSHIP ba ne, ra’ayin masu karatun ne. Sai dai, ba za mu tava mantawa da dalilin wanzuwarmu a doron qasa ba, wato: Don Allah Da Kishin Qasa!

mata. Kamar yadda ya zama wajibi ga gwamnatocin namu da su yi dukkanin abin da za su iya yi na ganin sun kyautata rayuwar matan, ta hanyar fito da shirye-shirye da kuma wasu ayyukan da za su kyautata rayuwar matan. Kamata ya yi, wannan rana ta kasance ta shekara ce sukutum, ba ranar 8 ga watan Maris ba kaxai, muna ganin lokaci ya yi da dukkanin mutane a xaixaikun su ne ko gwamnatoci, Kamfanoni, Qungiyoyi da sauran dukkanin al’umma za su yi dukkanin abin da ya dace na ganin sun fitar da haqqin matan gami da kyautata rayuwar su ta hanyar samar masu da dukkan abin da zai iya ciyar da rayuwar ta su gaba. Kowace al’umma ya kamata ta duba ta ga hanyar da ya kamata ta taimakawa rayuwar matan ta yadda za su mori rayuwar su daidai da sauran mutane. Mutane da yawa, zaton su shi ne, fifiko yana ga mawadata da kuma masu mulki ne kaxai, wanda lallai ba hakan ne ba. Wannan zamani ne wanda duniya ta kasance tamkar ta taru ne a cikin xaki guda, musamman kasantuwar hanyoyin sadarwa na zamani da ake da su yanzun, ta yadda duk abin da ya faru a nan duk duniya za ta kasance da masaniya a cikin sa. Wannan ya isa ya nu na mana cewa, ya zama tilas mu guji taka haqqin mata da ma sauran marasa qarfi, domin kuwa dukkanin abin da muka yi tabbas duk duniya tana kallonmu. Wannan aiki ne da ya hau kan kowa. Ya wajaba, mata su fito su ma su faxa domin a ji su a kuma saurare su, su kuma yi amfani da hannuwansu wajen yin nu ni da dukkanin halukan da suke ciki ta hanyar rubuce-rubuce, su kuma yi amfani da dubarbarun da Allah Ya huwace masu wajen taimakawa junansu kamar yadda suke taimakawa al’umma bakixayanta. Su kuma ci moriyar dukkanin kafafen sadarwa wajen yayatawa duniya hali da kuma yanayin da ‘yanuwansu na karkaru da qauyaku ke ciki. Ya kuma kamata al’umma da ta baiwa matan sarari domin su nu na irin bajintar da Allah Ya yi masu, a makarantu, wuraren aiki, wajen wasanni da dai sauran su. Dukkanin gwamnatoci ya kamata su samar da hanyoyin kare haqqin mata da mutuncin su, musamman mu a wannan nahiyar matan da rigingimu da yaquka suka xaixaita su, suka raba su da gidajen su da kuma iyalan su. A qarshe muna kira ga gwamnatin tarayya, da ta hanzarta sanyawa a cikin dukkanin tsare-tsaren ta, gami kuma da aiwatar da abubuwan da muka bayar da misalan su dangane da kare haqqi da mutuncin mata.


4 LABARAI

A Yau

Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Rashawa Ta Fi Cutar Kansa Illa – Magu Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Shugaban hukumar yaqi da cin hanci da rashawa ta qasa, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa, illar da rashawa da cin hanci ke da su ga qasa ta fi ta aibun da cutar kansa ke da ita ga jikin xan adam. Magu ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da editocin LEADERSHIP A YAU, Idris Sulaiman Bala da Nasir S. Gwangwazo tare da daraktan sashe, Mubarak Umar, ranar Laraba a ofishinsa da ke hediwatar EFCC xin a Abuja. Mista Magu ya qara da cewa, rashin biyan albashi a wasu jihohi ya na matuqar taimaka wa wajen illata rayuwar talakan Nijeriya, saboda idan ba a biya albashi ba, kuxi ya na yin qaranci a hannun jama’a, wanda hakan ke jefa mutane a matsin da su ke iya sanya su harin abin wani. Malam Ibrahim Magu ya qara da cewa, aikata ayyukan rashawa da cin hanci ya na haifar da lalacewar arzikin qasa da hana komai ya tafi daidai a dukkan sassa da al’amuran qasar, domin duk qasar da rashawa ta yi katutu, ba ta tava iya samun cigaba mai xorewa. Ya jaddada cewa, tamkar yadda cutar daji ko sankara ke ruguza lafiyar xan adam ta kuma hana shi amfanar kansa ballantana ya amfani wani, sannan kuma a qarshe ta halaka shi gabaxaya, haka ita ma rashawa ke yiwa Nijeriya irin wannan mummunar illa. Don haka sai ya yi kira ga al’ummar qasar da su qyamaci duk wani nau’i na cin hanci da rashawa kuma su taimaka wa hukumarsa wajen yaqi da wannan mummunar xabi’a, wacce ita ce ta hana Nijeriya cigaban da ta cancanci ta samu, kuma hakan ne ya hana talakan qasar samun yalwa da arziki mai xorewa a hannunsa, duk da cewa

qasarsa ta na da ximbin albarkatun qasar da bai dace a ce ’ya’yanta su na cikin wannan mawuyacin halin ba. Daga nan sai ya yi kira ga ’yan jarida da su kasance sun shigo cikin rundunar yaqi da cin hanci da rashawa ta hanyar tonawa da fallasa masu irin wannan xabi’a, domin a

cewarsa aikin jarida na da muhimmiyar rawar da zai taka wajen tabbatar da cewa an tsarkake Nijeriya kuma an kakkave hannun maqetatan shugabanni marasa gaskiya daga kan madafun iko; ciki kuwa har da ma’aikatan gwamnatin da ke hana ruwa gudu a kawo qarshen wannan gurvatacciyar xabi’a.

•Magu

Kashe-kashe: An Tura Sojojin Sama Zuwa Zamfara Daga Bello Hamza

Shugaban rudunar sojojin sama Air Marshal Sadique Abubakar ya bayar da umurnin tura runduna na musamman zuwa jiuhar Zamfa domin kawoqarshen kasha-kashen da ‘yan ta’adda suke yi a faxin jihar. Wannan matakin ya biyo bayan hare-haren da aka kai kwanan nan ne a qauyen Bawan Daji dake qaramar hukumar Anka ta jihar in da aka yi asarar rayukar mutane da yawa. Sanarwar da jami’in watsa labarai rundunar Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya ya sanya wa hannu, ya ce, rundunar ta tura runduna na musamman masu horo na musamman a fannin yaqi da bayar da agajin gaggawa an xauke sune daga filin jirgin sama nan Kaduna a jirgin yaqi sanfurin Hercules aircraft mai manba NAF C-130. A na sa ran rundunar zasu

yi aiki kafaxa-kafaxa da sauran jami’an tsaron dake aiki a jihar domin kawo qarshen kashe al’umman da basu ji ba basu gani a faxin jihar. Rundunar zasu yi aiki ne tare da sashin da aka kafa kwanan nan mai suna “207 Quick Response Group” a

garin Gusau, in da zasu haxu da sauran jami’an tsaro wajen shiga gaggarumin shirin da aka yi domij fatattakar ‘yan ta’addan mai suna “Operation SHARAN DAJI”. Da yake jawabi ga jami’an rudunar a Gusau, shugaban su Air Vice Marshal Ismaila

•Shugaban Rundunar Sojin Sama na Nijeriya

Kaita ya ce, za a rarraba jami’an zuwa qananan qauyuka in da zasu haxu da sauran jami’an tsaro wajen gudanar aiyuna kawo qarshen kasha kashen da ake yi a a faxin jihar. Ya buqace su dasu yi amfani da qwarearsu wajen kare rayuka da dukiyoyin alumar jihar Zamfara dama faxin qasar baki xaya. “Bayan kafa rubdunar “Quick Response Groups and Wings: tare da aika rundunar mu nanmusamma a faxin qasar nan, mun kuma kafa irin wannan rundunar na musamman a garuruwan Agatu da Doma da Nguroje a jihar Binuwai da jihar Nasarawa da kuma jihar Taraba domin samar da tsaro a can cikin qauyuka” “Shiri ya yi nisa na kafa “Quick Response Group” a Jalingo a jihar Taraba in da zasu haxa hannu da sauran jami’an tsaro domin samar da zaman lafiya faxin jihohin”

Ofishin Jakadancin Nijeriya A Amurka Ya Bayyana Dalilin Korar Ma’aikata Da Ya Yi Daga Bello Hamza

Ofishin jakadancin Nijeriya a Washington, DC, ya bayyana cewar, an bi cikakken qa’ida wajen korar ma’aikata da aka yi kwanan nan. Wani babban jami’i a ofishin jakadancin ya bayyana wa manema labarai cewa, an kamala shirin biyan kuxaxen salammar ma’aikata 15 da aka kora, kuma kwanan nan za a biya su haqqoqinsu. Ya ce, ma’aikata harkokin qasashen waje ne ta bayar da umurnin sallamar ma’aikatan a sabon shirin sake fasalin aiyukan ma’aikatan ofishin jakadanci da ake yi a halin yanzu. Daga nan jami’in ya qara da cewa, ma’aikatan harkokin qasashen wajen ta bayar da

izinin biyan kuxaxen sallama ga ma’aikatan da aka kora, waxansu daga cikinsu ma sun kai shekara 30 suna aiki a ofishin jakadancin. Wasu da wannan korar ya rutsa dasu sun nuna cewa, ba a bi qa’aidar da dokokin xauka da korar ma’aikata ba wajen korar su daga bakin aikinsu ba, sun kuma ce ofishin jakadancin bai yi wani shirin biyan su kuxaxen sun a sallama aiki ba ya zuwa yanzu. Haka kuma, ma’aikatan sun zargi ofishin jakadancin da korar ma’aikata ‘yan qasa kawai sun bar ‘yan qasashen waje suna ci gaba da gudanar da aiyukansu ba tare da wani tsangwama ba. ofishin jakadanci ta qaryata zargezargen da ma’aikatan suka

yi, in da ta qara da cewa, tun watan Fabrairu na shekarar 2017 a ka bayar da sanarwar za a yi sallamar, sun kuma ce, shirye shiryen biyan su kuxaxen sallamarsu ya kusa kamala, saboda haka su qara haquri kwanan nan zasu su ji “alert” Wani jami’in ofishin ya qara da cewa, “A watan Fabrairu na shekarar 2017 aka yanke shawarar sallamar wasu ma’aikata na cikin gida amma suka bayar da haqurin a xauke su a matsayin ma’aikatan wucin gadi da shekara xaya wanda ya qare a watan fabrairu na wnnan shekarar, ma’aikatanmu ne daga Abuja ta amince da sallamar nasu” “A halin yanzu mun samu amincewa daga Abuja na mu

biya su kuxaxen sallamar su kuma zamu biya su kwanan nan, lallai a kwai waxanda suka yi shekara 30 suna aiki da mu. “an xaue su aikin ne na wucin gadi, kuma shawarar gwamnati ne na ta amince ta qara musu wa;adi ko ta kore su in bata buqatar aiyukansu” Idan za a iya tunawa a shekara 2017 ofoshin jakadancin ta shiga taqaddama tsakainin tad a ma’aikata cikin gida a kan rashin biyan su albashinsu na tsawon watannin abin daya aukar da zanga zanga a lokacin, bayan rikicn daya nemi tsayar da aiyukan ofoshin jakadanci ne a ka bayar da umurmin biyansu albashinsu.


LABARAI 5

A Yau Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

’Yan Ta’adda Sun Yi Ajalin Wani Babban Manomi A Jihar Katsina

Daga Bala Kukkuru

A ranar Laraba da ta gaba ne ‘yan ta’aada suka bindige wani shaharren manomi a yankin qaramar hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina, maonomin mai suna Alhaji Ibrahim Garkuwan Kogon Hakimin Sabuwa, yana kuma xauke ne a qauyen Labbo dake a kan hanyar Sabuwa daga Xandume. Qanin mamacin mai suna Alhaji Qasimu Usman ya bayyana wa wakilinmu cewar, dama mazaje a qauyen Labbo dama sauran qauyukan dake yankin basa kwana a gidajen su saboda fargabar harin da yan ta’aadan ke yawan kawo wa yankin suna kashe mutane tare da kwashe dukiyoyin

jama’a. “A ranar Laraba Alhaji bai fita daji kwana ba kamar yadda ya saba, cikin dare kuwa gungun ‘yanta’adan suka kawo hari gidan inda suka nufi xakinsa kai tsaye suka xirka masa wata bindige mara qara, suka kuma yi awon gaba da kuxaxen da ya zuwa yanzu ba a san ko nawa bane. “Abin mamaki kuwa shi ne yadda ‘yanta’adan suka sami labarin cewa Alhaji bai fita wajen gari ba a ranar, kuma suka nufi xakinsa kai tsaye suka kashe shi” Inji shi. Wakilinmu ya gano cewa, marigayyin shaharren Manomi ne don kuwa ya kan noma buhun hatsi duhu 3 zuwa 4 a duk shekara, duk da kuwa harkokin ta’addacin daya addabi yankin Sabuwa zuwa

Birnin Gwari ya xan kawo wa manoman yankin koma baya a ‘yan shekarun nan. Da yake tattaunawa da wakilinmu a kan rasuwar Alhaji Ibrahim Garkuwan Kogon Katsina, babban xansa mai suna Alhaji Adamu Garkuwa ya ce, marigayyin ya rasu ya bar mata huxu da yaya 37 da kuma jikoki da dama, ya kuma yi alkawarin ci gaba da aiwatar da aiyukan alhairin da marigayyin ya ke yi na taimakon jama’a. Duk qoqarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin Jami’in hulxa da jama’a na rundunar ‘yansanda Jihar Katsina ya ci tura, amma dai kashe kashe da garkuwa da jama’a abu ne daya zama ruwa dare a yankin a ‘yan shekarun nan.

•Alhaji Ibrahim Garkuwa

’Yan Fashi Sun Kai Hari Wani Coci A Abuja Daga Umar A Hunkuyi

Wasu gungun mutanan da ake kyautata zaton ‘yan fashi da makami ne sun kai hari Cocin, New Ona Iwa Mimo Onimajemu Cherubim and Seraphim Church, da ke Anguwan Kwaso, TunganMaje, Zuba, ta babban birnin tarayya Abuja. Shugaban Cocin, Oladejo John, ya shaidawa manema labarai cewa, varayin sun sace kuxaxe da wayoyi, sun kuma jefa firgici a zukatan mutane da harbe-harben da suka riqa yi ranar Talata. Wakilinmu da ya ziyarci

wajen, ya jiyo cewan varayin su huxu ne, suna kuma sanye ne da kakin Sojoji sun kuma rufe fuskokin su. Sun kai hari a Cocin ne da muisalin qarfe 2 na dare a ranar ta Talata, da farko sun fara da sace wasu mata ne guda uku da su ka zo Cocin addu’o’in dare. John ya ce, sai ya xauki kwalba ya jefi varayin da ita a lokacin da ya ga za su ta fi da matan uku. John ya ce, fashewar kwalban, sai suka yi zaton qarar bindiga ce, sai su ma suka yiwo harbi da bindiga kafin su tsere, suka kuma bar matan uku ba su ta fi da

su ba. Wata da lamarin ya faru a kan idon ta, Uwargida Bose Komolafe, cewa ta yi, varayin sun shigo Cocin ne, sai suka umurci kowa da ya kwanta ya kifa fuskarsa qasa, daga nan suka tambayi inda Faston Cocin yake. Bose ta ce, sai John xin ya miqe tsaye ya ce masu shi ne Faston, ta qara da cewa, sun bincike kowa sun qwace wayoyi, kuxaxe da sauran abubuwa masu mahimmanci a Cocin. A cewar ta, sun tambayi John xin, ina bindigarsa take. “Sai Baba (John) ya

bukace su da su gabatar da kansu tukunna. Sai xayansu ya dake shi da sanda. “Wani cikin su kuma ya cakume shi ya dake shi, yana tambayar sa inda yake ajiye kuxi da wayar sa. “Bayan sun gama qwace mana komai ne, sai suka kwashi mata huxu tare da matan Baba, (John), ni da xiyata sun xauke mu, bayan sun fita da mu wajen Cocin ne, sai suka ce ni na koma. “Sun ta fi da xiyata, sun shiga daji da su, sai suka sake cewa xaya daga cikin matan ta koma, sai suka ta fi da sauran ukun. “Sun shaidawa Fasto xin

ya biya milyan biyar domin su saki matan. “Sai ya bi su a baya, yana bin bayan su ne sai ya ga sun sako mace guda,” in ji Komolafe. Wani mazaunin Anguwan, Mista Akinlami Aduragbemi, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta qara sanya tsaro a Anguwar ta hanyar qara yawan ‘yan sandan da ke Anguwar. Kamfanin dillancin labarai na qasa, ya ruwaito cewa, da safiya ne aka kai rahoton faruwar lamarin a Ofishin ‘yan sanda na Zuba, inda suka fara binciken lamarin.

Mu Na Samun Nasara Sosai Wajen Daidaita Tsakanin Al’umma –Hisbah Katsina Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Kungiyar Hisbah a jihar Katsina ta ce tana samun nasarori so sai wajan daidaita matsalolin da ke ta so wa na yau da kullun a tsakanin al’ummomin musamman a yankunan kankara. Babban kwamandan Hisbah na jihar Katsina, Malam Qasim Abubakar Imam ya bayyana haka a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki na kungiyar ta saba yi duk bayan wata uku, domin tattauna irin nasarori da suka samu da kuma lalubu hanyoyi magance matsaloli idan sun ta so. Taron wanda ya gudana a qaramar hukumar Sandamu ta jihar Katsina ya samu halartar wakilai daga qananan hukumomi 29 daga cikin 34 na jijhar Katsina

haka kuma an tattauna qara inganta aikin kungiyar Bayan kammala wannan mahimman batutuwa da Hisbah inda ko a kwanakin mahimmin taro baban suka shafe rayuwar al’umma bayan sun hurras da mata kwamandan Hisbah na da kuma ci gaban kungiyar a qaramar hukumar Mani jihar Katsina, Malam Hisbah a jihar Katsina. domin shiga lungu da saqo Qasim Abubakar Imam tare Haka kuma taron na da nufin na aikin kungiyar Hisbah. da mataimakinsa Malam yin amfani sabbin hanyoyi wajan ganin al’amurra sun ci gaba da daidaituwa a tsakanin al’umma wanda yanzu wannan kungiya ta Hisbah a jihar Katsina tana qara samun ci gaba ta hanyar qara xaukar sabbin mambobinta domin faxaxa wannan aikin. A cewar baban kwamanda yanzu suna qara samun goyan bayan al’ummar gari idan aka yi la’akari da abubuwan da aka tattauna wajan wannan taron, inda yanzu korafe-korafe sun rage so sai a wajan mutanen gari ba kamar a baya ba. Ya kuma qara da cewa suna nan suna wani tunina na •Kwamandan Hisba lokacin da suka kai ziyarar fadar Sarkin Daura

Abdullahi da kuma babban sakatare, Malam Rabi’u Mohammed da sauran tawagar suka kai wata ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruq Umar Tun da farko da yake jawabi a fadar mai martaba Sarkin Daura, kwamandan Hisbah na jihar Katsina, Malam Qasim Abubakar ya bayyana dalilinsu kai wannan ziyara ta ban girma ga iyayan al’umma domin samun albarka da neman shawara ga mai martaba Sarki. Da yake maida jawabi mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar, ya nuna jin daxinsa da wannan ziyara ta kungiyar Hisbah inda ya nuna cewa Hisbah na yin aikin Allah kuma sakamakon aikin da suke yi yana wajan Allah a ranar gobe kiyama.


6 LABARAI

A Yau

Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

’Yan Sandan Kano Na Son Mutane Su Fallasa Masu Riqe Da Makamai Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta yi kira ga jama’ar jihar da su fallasa makaman da ke riqe a hannun mutane, waxanda ba ta kammala amsa daga hannunsu ba. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin kwamishinan ’yan sandan jihar, Alhaji Rabiu Yusuf (psc) a zantawarsa da manema labarai ranar Larabar nan, 4 ga Afrilu, 2018 a hedikwatar rundunar da ke Bompai a birnin Kano. Kwamishina Yusuf, wanda ya baje kolin makaman da rundunar tasa ta amsa a gaban manema labaran, ya bayyana cewa, wannan wani cika umarni ne na babban sufeton ’yan sanda na qasa, Alhaji Ibrahim K. Idris (NPM, mni), wanda tun a ranar 6 ga Maris, 2018, ya umarnin dukkan rundonin ’tan sanda na jihohi da su amshimakaman da ke hannun mutanen gari ba bisa qa’ida ba cikin kwana 21. Rundunar ta jihar Kano ta kira taron manema labaran ne, don ta bayyana duniya yadda ta cika alqawarin cikin qasa da makonni uku kacal, don kada a bar ta a baya tsakanin ’yan uwanta na jihohi. “Kasancewar wa’adin da a ka bayar ya cika, rundunar ’yan sanda ta Kano ta na mai farin cikin bayyana wa jama’a cewa, kwamitin da ta kafa don aiwatar da aikin karvar makaman daga hannun masu aikata laifuka, masu satar mutane ko garkuwa da su, masu satar shanu da kuma waxanda su ka miqa makaman don radin kansu, ya sam nasarar amsar makamai a wannan tsakani,” in ji CP Yusuf cikin takardar yaxa labarai da ya aike wa wakilin LEADERSHIP A YAU ta hannun jami’in

hulxa da jama’a na rundunar SP Magaji Musa Majia. Takardar ta nuna cewa, rundunar ta amshi bindiga qirar AK-47 guda uku, qananan bindigogi 23 da harsashi 37 da magazin 17 da dai sauran makamai daban-daban. Daga nan sai kwamishinan ya qara da cewa, rundunar za ta fara farautar qwace makaman da kanta daga hannun masu kunnen qashi, don su fuskanci fushin hukuma. “Mu na kira ga jama’ar gari da su kai rahoton duk mutumin da su ka gano ya na riqe da wani makami ga caji ofis mafi kusa da su ko kuma hedikwatar rundunar ta jiha,” in ji sanarwar.

• Kwamishina ‘yan sanda na jihar Kano, Rabiu Yusuf, ya na jawabi a lokacin da ya ke bajekolin makaman da rundunarsa ta yi nasarar amshewa. Daga hagu, SP Magaji Majia ne ke taimaka ma sa

NAHCON Ta Yi Amfani Da Ma’uni Wajen Ware Wa Masu Jigilar Maniyyata Masu Zaman Kansu Kujeru 20,000 -Shutti Daga Abubakar Abba

Shugaban sashen yawon buxe ido na hukumar aikin hajji ta qasa (NAHCON), Alhaji Alidu Shutti ya bayyana hanyoyin da hukumar ta bi wajen warewa kujeru aikin hajji ga masu gudanar da jigilar Maniyyata masu zaman kansu dake qasar nan dake da lasisi. Hukumar ta ware kujeru masu 20,000 a aikin hajjin na shekarar 2018 daga cikin kujeru 95,000 da aka bai wa Nijeriya a aikin hajjin na bana. Shutti yace, a al’adar hukumar, shine taje rabbata ba hannu ta (MoU) da ma’aikatar alhazai ta qasar Saudiyya a lokacin gudanar da dukkan aikin hajji. Yaci gaba da cewa, a bisa dokar Majalisar qasa ta shekarar 2006 wadda ta kafa hukumar ta NAHCON, ta baiwa hukumar

qarfin ta bayar da lasisi da sanya ido da kuma duba dukkan hukumomi da gwamnati da kuma masu zaman kansu dake da lasisi da aka sanya yin jigilar Maniyyata ‘yan Nijeriya zuwa qasar Saudiyya yin aikin hajji ko yin Umrah. Shutti ya bayyana cewar yadda aka zavo masu jigilar masu zaman kansu, anyi shine a bisa dokar data kafa hukumar. Ya qara da cewa, tattarawa da miqa takardu, yana xaya daga cikin hanyar da aka yi amfani da ita. Acewar sa, “mun kai ziyara ga ofishoshi don tabbatar da cancanta cewar ko ana haya ne na mallaka ne da kuma duba cancantar ma’aikatan su, musamman akan qwarewa da kuma yadda za’ayi aiki dasu. Acewar Shutti, dukkan waxannan tsare-tsaren an

sanya su akan yadda aka zaqulo kamfanonin. Acewar sa, “mun kuma yi dubi a cikin kudin na qwararru kamar na qungiyar (IATA) don mu tabbatar da cewar, waxannan kamfanonin komai nasu a daidai yake.” Ya qara da cewa, “muna da abin da muke kira tantance masu jijilar, wannan wata hanya ce da hukumar ta samar da kuma warewa masu jigilar.” Shitti ya bayyana cewar, zavowar bai wai tsaye take tsak ba, amma ya danganta da irin zagewar masu jigilar dake da lasisin na qasar nan. Acewar sa, “ a wannan shekarar za’a iya kai ka matsayi na ‘A’ ko kuma a mayar da kai matsayi na ‘C’ abin danganta ce. Ya yi nuni da cewar zavar masu yin jigilar, wata hanya ce wajen ware masu kujerun a cikin

sauqi. Acewar sa, “ ba sai munga ba kafin muce ka cancanta abinda muke dubawa shi ne iya qoqarin ka akan yadda kake samarwa da Maniyyata walwala.” Ya bayyana cewar, wayarwa da Maniyyatatan kai, shima yana taka muhimmiyar rawa da kuma nuna zagewa wajen gudanar da shirye’shiryen. Ya bayyana cewar, kulawar da masu jigilar masu zaman kansu zasu bai wa Maniyyatatan a kafin tashin su daga Nijeriya zuwa qasar Saudiyya, hakan yana da mahimmanci so sai ga hukumar. A qarshe yace, masaukar Maniyyatatan da aka samar a Saudiyya, suma sun haxa da damar da aka yi amfani da ita wajen baiwa masu jigilar masu zaman kansu dake da lasisi dama.”

’Yan Bindiga Sun Kashe ’Yansanda Biyu Bayan Sun Kai Hari Ofishinsu Daga Idris Aliyu Daudawa

‘Yan bindiga daxi sun kashe jami’an ‘yansanda biyu da kuma wani mutum xaya wanda ake tsare da shi, su dai waxannan ‘yan tada zaune tsaye waxanda ba a san ko su wanene ba, sun kai hari ne a ofishin ‘yansand na Gegu Lokoja akan hanyar Abuja ranar Talata. Su dai ‘yan ta’addan da suka

kai biyar suna xauke da bindiga AK47 suka mamaye ofishin misalign qarfe biyu da kwata na dare ranar Talata suka kan mashina. Majiyar ta bayyana cewar zuwansu ke nan ofishin sai suka fara harbe harbe, domin tsorata mutane, daga nan suka shiga cikin ofishin, inada suka harbi ‘yansanda biyu waxanda suke aiki a wannan ranar. Akwai wani wanda ake

zargi da aikata laifi sun kashe shi. Bugu da qari an samu labarin cewar su ‘yan bindigar sun xauke bindigogin ‘yansanda AK 47, suka kuma bincike caji ofiss saboda neman bibdiga da kuma harsasai. Jami’in yxa labarai na rundunar ‘yansanda ta jihar Kogi Mr William Ayah, ya tabbatar da aukuwar kai harin, ya kuma qara bayanin cewar ‘yansanda

biyu sun mutu, yayin da kuma wani wanda ake zargi da aikata laifi ya samu raunuka. Ya kuma ce rundunar ta fara bincike dangane da kai harin. Gawar ‘yansandan biyu an xauke ta an kai ta xain ajiye gawa na Asibitin gwamnatin ytarayya dake Lokoja, wanda kuma Hukumar kiyaye haxura ta qasa, ita ce ta kaisu, yayin da shi kuma wanda ake zargi da aikata laifi, ana kulawa da shi asibiti.


RAHOTO 7

A Yau Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Jokolo Ya Bayyana Yadda Dasuqi Ya Xora Buhari Kan Mulki A 1983 Daga Idris Aliyu Daudawa

Wannan wani rahoto ne wanda Jaridar DAILYNIGERIAN ta wallafa, kuma Umar A. Hunkuyi ya fassaro mana. rahoton yayi cikakken bayani kan yadda Dasuqi ya xaura Buhari a mulki a shekarar 1983. ga cikakken rahoton: Tsohon dogarin Janar Muhammadu Buhari, lokacin da ya Shugabanci qasarnan a mulkin Soja, Mustapha Jokolo, ya fasa qwai kan irin rawar da wani tsohon mai baiwa Shugaban qasa shawara Kanar Sambo Dasuqi mai ritaya, ya taka wajen samun nasarar juyin mulkin da Sojoji suka yi a shekarar 1983, wanda shi ne ya xora Buhari, a matsayin Shugaban qasarnan na mulkin Soja a wancan lokacin. Mustapha Jokolo, wanda tsohon Sarkin Gwandu ne wanda aka tuve, ya yi waxannan bayanan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da wata jarida, a martanin da yake mayar wa kan wani littafi da Sarkin da ya gaje shi a Sarautar ta Gwandu, Janar Muhammadu Iliyasu Bashar mai ritaya, ya rubuta. A cewar tsohon Sarkin Jokolo, Dasuqin ya taka mahimmiyar rawa ta hanyar xaukan nauyin juyin mulkin da kuxin sa da kuma kitsa yadda juyin mulkin wanda a cikin sa ne Muhammadu Buhari ya zama Shugaban qasa, zai yi nasara a 1983. Da yake magana kan wasu bayanai da ke cikin littafin na Janar Bashar, Jokolo, ya nanata maganan na shi inda yake cewa, “A bisa zahirin gaskiya, wannan shi ya sanya nakan ji zafi sosai kan halin da Dasuqin yake ciki a halin yanzun. Na damu sosai da hakan. “Wannan gaskiyan kenan. Baccin na kawo Dasuqi, cikin lamarin juyin mulkin ba, na 1983, da juyin mulkin da Buharin ya zama shugaban qasa a cikin sa bai yi nasara ba. Sambo Dasuqi ne ya shirya mani komai na yadda za a yi juyin mulkin. Ni shawarar juyin mulkin ne kawai na ba shi. “Na rantse da Allah. Duk shi ne ya taro mutanan da aka yi juyin mulkin da su. Duk shi ya tsara komai. Ya taka rawa a juyin mulkin sosai, a zahirin gaskiya….Sai na haxa su da Sambo Dasuqin, sai…kai ko a lokacin da muke shirya yanda juyin mulkin da Buharin ya zama shugaban qasa a cikin sa, zai gudana, Sambo Dasuqin ne yake nemo mana kuxaxen da za a yi komai.

“Shi ya karvo mana kuxi daga wajen Aliyu Gusau, ya kuma gamsar da Kwamandan askarawan Sojin qasa, har ya aminta da shirin juyin mulkin, saboda kwabo xaya ba mu samu a wajen Buhari xin ba. “Ba ma wannan kaxai ba, Sambo Dasuqin ne ya yi amfani da kuxin mahaifin shi, inda ya tura wasu Malamai qasar Saudiyya domin su je su yi addu’o’in samun nasarar juyin mulkin,” in ji Jokolo. Da yake tabbatar da abin da aka rubuta a wani littafi da aka wallafa kwanan nan mai suna, “An Encounter with the Spymaster” wanda wani mai suna, Yushau Shuaib, ya rubuta, Sambo Dasuqi, ya yi bayani filla-filla kan yadda shi da kansa da kuma wasu matasan Jami’an Soji biyu, suka je suka sami Buharin a kan maganan juyin mulkin na 1983. Sambo Dasuqi, ya tabbatar da cewa, “Shi da wasu matasan Jami’an Soji biyu ne (watau Manjo Mustapha Jokolo da kuma Manjo Lawal Gwadabe), suka yi takakkaka har Jos, suka iske Buharin wanda a wancan lokacin shi ne Kwamandan Rundunar Sojin tankokin yaqi ta 3 da ke Jos xin, inda suka yi masa bayani kan juyin mulkin na 1983 da suke shiryawa, wanda Buharin ya ci gajiyarsa inda ya zama Shugaban qasa bayan an kifar da gwamnatin farar hula ta Shehu Shagari.” Sannan kuma, Sambo Dasuqin ya bayyana yadda Buhari xin ya nu na damuwar sa kan sakamakon kasancewar sa jagora a shirin juyin mulkin a wani taro, inda shi Sambo Dasuqin ne ya tabbatar wa da Buharin da ya kwantar

da hankalin sa kan duk wata barazana, inda ya ba shi tabbacin za su karvi mulkin daga hannun ‘yan siyasan.” Da Mista Shuaib, marubucin littafin, ya tambayi Dasuqin, kan to ya aka yi kuma a qasa da shekaru biyu da yin juyin mulkin, sai ga shi kuma, Dasuqin ya sake shiga cikin waxanda suka kitsa juyin mulkin da aka yi wa shi Janar Buharin, sai Dasuqin ya bayar da amsar cewa, “Ai shi Buharin ya san ko wane ne ya kamata a zarga a kan hakan.” Dasuqi ya ce, “Ni a kodayaushe nakan yi biyayya na kuma girmama na gaba da ni, da ma masu mulki duk na kan ga qimar su, lokacin ina aikin Soja da ma bayan nan. Duk da shike a lokacin, kasantuwan ni mai qaramin matsayi ne, ban so a ce an je kamo shi da ni ba. Don haka ba ni cikin waxanda suka kamo shi.” “Na dai je na same shi ne a Barikin Soji na, ‘Bonny Camp,’ ni da Lawal Rafindaxi. ba ta yadda zai yiwu a ce wai na ci masa mutunci kamar yadda wasu ke faxin hakan. Ina farin ciki kasancewar da yawa daga cikin waxanda suka taka rawa a lokacin duk suna raye.” Savanin yadda ake yaxawa a wurare da yawa cewa,Sambo Dasuqin yana cikin Sojojin da suka je suka kamo Buharin a juyin mulkin na 1985, Kanar Abdulmumini Aminu mai ritaya, wanda xan asalin Jihar Katsina ne, ya bayyana ko su waye Manjo-Manjo xin guda uku, a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a cikin jaridar ‘Sunday Trust,’ ta watan Agusta 2015. Mai neman qarin bayanin hakan, sai ya bi ta, (wannan

shafin: https://goo.gl/KEz5nk, https://goo.gl/wirj2T, https:// goo.gl/9vZM5A). Abdulmumini Aminu, ya ce, mutane uku ne waxanda shi da kansa ya jagorance su, suka je suka kamo Shugaban qasan na wancan lokacin, (Janar Muhammadu Buhari), sauran biyun sune, Lawan Gwadabe da kuma John Madaki. Ya ce, “Tilas na bayar da shaidar ni na jagoranci kamo shi. Na ta fi Barikin Dodon Barrack a lokacin, tare da rakiyar Sojoji biyu, Manjo John Madaki da kuma Lawan Gwadabe. Mu uku ne muka je, amma a zahiri, ni na hau sama na kamo Buharin. “Na kamo shi da cikakkiyar girmamawa, na sha karantawa a cikin kafafen yaxa labarai, mutane na cewa, wai mun ci mutuncin sa, mun wulaqanta shi. Sam hakan ba gaskiya ne ba. Ni da Janar Buharin ne kaxai muka san haqiqanin abin da ya gudana a tsakaninmu a saman benen, ba wani abu makamancin hakan da ya faru. “Mun ba shi duk girmamawar da ya kamace shi a matsayin sa na babba gare mu, domin ai ko kafin wannan lokacin, muna ba shi cikakkiyar girmamawa, saboda irin halin sa. Har kawo yau, muna ganin qimarsa, babu kuma wani munafunci a tsakanin mu da shi, shi kuma ya san matsayin bin umurni a aikin Soja, a lokacin da duk na gaba da kai ya sanya ka yin wani aiki. “Ya ma tava faxi mani hakan wani lokaci. Don haka, mu kamar yadda ta faru da shi ne a baya, lokacin da ya karvi shugabanci a juyin mulkin da aka yi wa Shagari. Ina cikin waxanda suka taka mahimmiyar rawa wajen ganin ya zama Shugaban qasa, a shekarar 1983.”


8 TALLA

A Yau Litinin 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Burinmu Shi Ne Mu Sauqaqa Muku

Ba a chaj in kuxin on ka cire d i j a h c a a B saqonnin watin waya kuxi daga ak na wasu banku

Da zaran an buxe asusu da mu, za a morewa rashin chaji idan mutum ya cire kuxi a akwatin wasu bankuna, haka kuma ba za a riqa cire kuxin saqonnin waya ba.

Domin cimma nasara a hada-hadar banki, ka yi mu’amala da bankin Sun Trust a Yau Ziyarci: www.suntrustng.com


A Yau Litinin 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

TALLA 9

Gaba dai! Gaba dai “Super Eagles”

Bankin Zenith na taya ‘yan qwallon Nijeriya “Super Eagles”, murna sakamakon nasarar da suka samu ta kai wa gasar Cin Kofin Duniya wanda za a gudanar a qasar Rasha.


10 LABARAI

A Yau

Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

• Shugaban Qasa Buhari (a tsakiya) bayan ya kamala zantawa da gwamnonin jihohi biyar a fadarsa, gwamnonin su ne: Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje; Gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun; Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong; Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, tare da Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari

Fayose Ya Goyi Bayan Obasanjo Kan Kar Buhari Ya Sake Neman Tsayawa Takara Daga Umar A Hunkuyi

Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce, kiran da Obasanjo ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari, da ya daina kawo uzurin rashin tavuka komai da gwamnatin sa ta yi, a kan gwamnatocin da suka gabace shi. Sannan kuma, “’Yan Nijeriya ka da su sake su sake zavan gwamnatin da ta gaza, da cewa, wannan kiran na Obasanjo daidai ne. A cikin wata sanarwar manema labarai da gwamnan ya fitar a Ado Ekiti, ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaxa labarai, Lere Olayinka, ya ce, gwamnatin ta Shugaba Buhari, ta baiwa waxanda suka zave ta kunya, don ta kasa biyan masu bukatun su, ya ce, wannan yana tabbatar da maganan da ya faxa ne, inda yake cewa, babu wani abin kirki da Buharin zai iya tsinana ma al’ummar qasarnan. Gwamnan ya ce, duk da yake ina da savanin ra’ayi da Obasanjo, amma ba daidai ne ba idan ya faxi wani abin kirki a gaza yaba ma shi, musamman idan aka lura da irin haxarin da qasarnan da mutanan ta za su iya faxawa ciki. “Hukuncin da Obasanjo ya yi kan Buhari, ya gaskata ni ne, inda yake cewa, “Ba

zai iya shugabanci ba.” Abin da Obasanjo ya faxa, ba sabuwar magana ce ba kan wacce na saba faxa, kafin da kuma bayan zaven Buhari. Na sha faxan cewa, Buhari, ba shi da qwazo, hazaqa da kuma qoshin lafiyar da zai iya yin mulkin qasa kamar Nijeriya, yanzun ga waxanda ke kan gaba wajen sanyawa a zave shi suna gaskata magana ta.” “Kamar yadda na faxa ne lokacin da ya rubuta masa waccan wasiqar ta watan Janairu na wannan shekarar, na yarda da sabon matsayin da ya xauka a kan Buharin, ina kuma kira ga sauran ‘yan Nijeriya waxanda suka xora shi kan mulkin Nijeriya, suke kuma kallon abin da ke faruwa a halin yanzun, amma suka yi

gum da bakunan su, da su fito su ma su gaya masa gaskiya, domin qaunar da suke yi wa qasarnan. “A yau baccin Obasanjo da ya fito fili ya faxa, yawancin xaixaikun mutane da qungiyoyin da suka damu da ci gaban qasarnan, duk suna faxi a voye cewa, Buhari ya gaza. “Abin da wannan gwamnatin ke tutiya da yaqar sa, na cin hanci da rashawa da ayyukan da ke karya tattalin arzikin qasa, hatta Qungiyoyin lura da lamarin na cin hanci da rashawa na duniya, sun shelanta cewa, cin hanci da rashawan ya fi qamari a lokacin mulkin wannan gwamnatin a Nijeriya, fiye da shekaru 16 a baya. Bill Gate, cewa ya yi, tanade-tanaden da

gwamnatin Nijeriya ta yi sun kasa biyan bukatun ‘yan Nijeriyan. Janar T.Y. Xanjuma kuwa cewa ya yi, gwamnatin ta kasa samarwa da ‘yan qasa tsaron rayuka da dukiyoyin su. Janar Ibrahim Badamasi Babangida, gayawa Shugaba Buhari a fakaice ya yi, da ya koma gida ya huta ma kansa, ya bar matasa su amshi ragamar mulkin qasarnan. “Kamata ya yi Shugaba Buhari ya karvi waxannan shawarwarin da aka ba shi hannu bibiyu, a matsayin sa na dattijo, ya sauka daga kan mulki domin ya gujewa qasarnan faxawa cikin wasu masifun. Ya dubi qasarnan da kuma wahalar da talakawanta ke ciki, ya manta da masu

kiran sa da ya ci gaba da mulki, ba ma sai bayan wannan shekarar ba, ballantana ma batun wai ya sake neman tsayawa takara a shekara mai zuwa. “’Yan Nijeriya ka da a yaudare ku kamar yadda aka yaudare ku a baya, idan kun yarda an sake yaudarar ku, kun zama wawaye. “Kamar yadda na sha faxi ne a can baya, muna qarqashin mulkin gwamnati ce marar Imani, komai ya birkice. Tsaro ya tavarvare a dukkanin sassan qasar, yanzun ta kai mutane sun fara tunanin samarwa da kansu tsaro. “Don haka ya wajaba ‘yan Nijeriya su takawa wannan gwamnatin marar qibla burki, domin su ceci rayuwar su.”

Wani Yaro Xan Shekara 13 Ya Rataye Kansa A Gombe, Inji ’Yan Sanda Daga Khalid Idris Doya

Wani yaro xan shekaru 13 a duniya wanda kuma xan wani jami’in hukumar ‘yan sanda ne, an yi zargin ya kashe kansa da kansa ta hanyar tarayewa da igiya a jihar Gombe, kamar yanda rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana hakan a ranar Talata. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, DSP Mary Malum, ita ce ta shaida hakan, ta ce yaron da aka tantance sunansa da Muhammadu Al-amin ya

rataye kansace xin ne a cikin xakinsa da igiya. DSP Malum ta ce lamarin ta kuma auku ne a ranar Litinin da misalin qarfe huxu na yammaci “Mahaifin yaron mai suna Insifekta Abdu Manu wanda ke tsaka da aikinsa a ofishinmu da ke Pantami, sai ya amshi qiran waya daga matarsa inda take shaida masa cewar xansa mai shekaru 13 ya rataye kansa a cikin daxinsa,” Ta ce, mahaifin yaron ya samu labarin da ke cewa xansa ya rataye kansa ne

bayan dawowarsa daga makarantar Kur’ani. Malum ta qara da cewa samun labarin ke da wuya ne kuma sai jami’ansu suka himmatu domin jewa wajen domin xauko hoton gawar yaron da kuma bincikar xan bayan da suka samu. Ta ce sun samu nasarar xauko gawarsa da kuma igiyar da yayi amfani da ita wajen rataye kansa, haka kuma sun wuce da gawar zuwa asibitin Gombe sashin adana gawarwaki. DSP ta kuma ce yanzu

haka suna kan gudanar da bincike kan lamarin da zarar suka kammala za su sanar da manema labaru abubuwan da suka naqarto. Makwaftan gidansu yaron, sun shaida wa kamfanin dillacin labarai cewar sun ga yaron na wasa da tsakar rana da shi da abokansa, lokacin da suka samu labarin ya rataye kansu kuma abun ya yi matuqar ranazasu. Duk qoqarin da aka yi don jin ta bakin mahafin yaron ya gagara.


LABARAI 11

A Yau Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Xan Shekara 45 Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 4 Fyaxe A Yobe Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Rundunar tsaron Nijeriya ta NSCDC, a jihar Yobe ta damqe wani mutum xan kimanin shekara 45Shu’ibu Yakubu, wanda take zargi da yiwa yar shekaru huxu (4) a duniya fyaxe, a Damaturu babban birnin jihar. Mista Ayinla Taiye Olowo, shi ne kwamandan rundunar NSCDC kuma ya bayyana cewa, mahaifiyar wannan yarinyar ce ta kawo musu qorafi dangane da al’amarin, ranar 27 ga watan Maris, 2018, inda daga bisani suka cukumo wanda ake zargin domin gudanar da bincike. Kwamandan ya ci gaba da bayyana cewa, binciken su ya gano cewar wanda ake zargin, ya aikata wannan tavargaza ga qaramar yarinyar ne a sa’ilin da take wasar qasa a maqwabta, yayin da ya bata ‘alawar minti’, inda kuma daga bisani ya xauke ta zuwa xakin sa tare da lalata da ita.

“kamar yadda mahaifiyar ke gaya muna yadda lamarin ya afku, ta ce bata ankara da wannan al’amarin ba har sai a lokacin da take yiwa yarinyar wanka, yayin da yarinyar ta nuna mata cewa gaban ta yana yi mata raxaxi. Al’amarin da ya sa mahaifiyar qoqarin gano abinda ya faru, a qarshe yarinyar ta shaida wa mahaifiyar kan cewa wani mutum ne ya gaya mata, idan ta sake ta faxi wanda yayi mata fyaxen, to za ta mutu ne”. “Bugu da qari kuma, mahaifiyar tayi hanzari wajen kai qorafin ta ga jami’an mu, wanda kuma kan ka ce kwabo sun kama shi. Kuma ba tare da vata lokaci ba ya amsa laifin sa, tare da bayyana cewa shima ba a hayyacin sa yake ba a sa’ilin da ya yiwa yarinyar fyaxen”. Ya nanata. Mista Taiye Olowo ya ce, baya ga yadda ya amsa laifin sa ne, sai NSCDC ta tattara mai laifin da

qaramar yarinyar zuwa asibiti domin a gudanar da binciken lafiyar yarinyar tare da girman laifin. “bayan gudanar da gwaje-gwajen likita, an samu dukkan su ba su xauke da Wata cuta wadda take yaxuwa ta hanyar jima’i (STD), sai dai kuma ya yiwa ita yarinyar lahani kuma tuni aka yi mata magani, wanda kuma daga bisani aka sallamo ta zuwa gida”. Yayi qarin haske. A hannu guda kuma, kwamandan ya bayyana matuqar damuwar sa dangane da yadda matsalar yawaitar fyaxen ke neman zama ruwan dare a garuruwan Potiskum da Damaturu dake jihar ta Yobe, inda kuma ya shawarci iyaye da cewa su rinqa yin kaffa-kaffa da yayan su, domin kaucewa faxawa a hannun vata-gari masu qoqarin vata rayuwar qananan yara. “miyagun mutane suna

•Shu’aibu da ake zargi

nan a kowanne lungu da kwararo, kuma su kan yi amfani da kowacce irin dama suka samu wajen

aiwatar da alkaba’in nasu da nufin cimma muradin su- na tsafi ko zina.” Ta bakin shi.

Kalaman T.Y Danjuma Sun Yi Matuqar Ba Ni Mamaki, Inji Sanata Matori Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Har zuwa yanzu dai kalaman TY Danjuma suna ci gaba da samun suka da kuma masu sharhi kan kalaman nasa, na cewar ‘yan qasar nan su xauki matakin kare kansu daga kansu, a cewar TY Danjuma sojojin Nijeriya ba su xauko hanyoyin kare ‘yan qasa ko kuma samar musu da mafita kan rasa rayuwa da ake yi ba. Tsohon Sanata Alhaji Salisu Musa Matoci (Xan Masanin Bauchi) yana xaya daga cikin dattawa ba akwai a jihar Bauchi har ma da Nijeriya baki xaya, a hirarsa da wakilinmu a Bauchi ya bayyana cewar waxannan kamalan sun zo da ban mamaki, la’akari da wanda kalaman suka fito daga bakinsa, a cewarsa basu tsammaci nagartaccen mutum wanda ya yi aikinsa na sadaukar da ransa wajen ci gaban qasa ya zo yana furta irin waxannan kamalan wanda ka iya kawo wa Nijeriya ci gaba ta fuskacin tsaron qasar. Ya bayyana cewar sanin da

ya yi wa TY Danjuma bai tava tsammatar irin waxannan kamalan daga garesa ba, ya kuma nuna takaicinsa kan yanda wasu ke mai da zagi a matsayin hanyar mayar da martani kan wasu lamura. Ya ce, “Ni dai har yanzu a cikin zuciyata, ina xaukan wani abu ne da Hausawa ke cewa zarvaviya, idan mutum magana ta xauko har kan zo ya faxi wasu abubuwan da basu kan hanya, ba zai ankara da abun da ya faxa ba sai bayan ya faxan. Ni ina tunanin irin abun da ya samu Janaral TY Danjuma kenan” Alhaji Salisu Musa Matoci ya xaura da cewa, “Ina xaya daga cikin mutanen da suka tantance Janaral TY Danjuma a zaven da aka yi na 1999. Ina daga cikin Sanatocin da mune aka ajiyemu domin mu tantance shi; mun zauna da TY Danjuma na tsawon awanni, mun yi maganganu tare da shi. To, malam idan aka yi la’akari da irin maganganun da ya gwada mana a wancan lokacin na son da qauna da yake a Nijeriya wanda har

ta kai mun amince masa, sannan kuma idan aka kwatantashi da Xanjuman da ya zo a Jalingo yana wannan jawabin tilas ne kanka ya xaure, musamman idan da kana daga cikin waxanda suka tantance shi da jin kalamansa. a wannan ranar ina nan, Sanata Zongina, Sanata Bala Adamu, Sanata Bala Ibrahim da sauransu mune muka tantance shi

da cewar mun yarda ya zama Ministan tsaro na Nijeriya a bisa jawabai da kuma bayansa da muka ji na son ci gaban Nijeriya daga bakinsa,” Matori ya kuma shida cewar abun mamaki ne kalaman TY, idan aka duba aka ga wanda ya yi kalaman “Sai ga shi kuma mun zo mun ji wannan maganar daga bakinsa ka ga dole ne

•Sanata Matori bayan kammala hirarsa da wakilinmu

kanka ya xaure kuma dole ne ka ce akwai wani abun da ya kifta a tsakani, kuma mene ne wannan? Allah kaxai ya sani,” Matori ya ce kamatuwa ya yi a irin wannan lokacin hukumomi su qirawo TY Danjuma da ya zo ya amsa tambayoyi gami da kuma yin bayanai kan dalilansa na furta irin wannan kamalan alabashi a yi gyara idan da buqatar hakan “Amma abun da duk ya kamata ga duk mai hankali ya yi shine ba zagi ko batanci, suka ko zage-zage ne zai kaimu ga samun wani nasara a wasu al’amuran da muka sanya a gaba ba; abun da muka sanya a gaba shine ne ya faru? Sai ya yi bayani, a zauna da shi teburi ya bayyana abun da ke damunsa,” Daga qarshe dai ya tsaya kan batunsa na cewar zaman lafiya ta fi kowani mataki samar da ababen da ake da buqata, ya qirayi mahukunta da su himmatu don yin ababen da ka iya kawo wa qasar nan ci gaba a kowace marhala.


12 LABARAI

A Yau

Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Rikicin Manoma Da Makiyaya: Shugaba Buhari Ya Umurci A Binciki Yawan Asarar Da Aka Yi A Binuwai Daga Bello Hamza

Shugaba Muhammadu Buhari ya munurci hukumar bayar da ceton gaggawa NEMA da ta fara tattara alqaluman varnar da aka yi sakamakon rikicin daya auku tsakanin makiyaya da manoma a faxin qasar nan, Mataimakin shugaban qasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyanan haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki daya haxa da kwamitin zartasawar hukumar NEMA a fadar shugaban qasa dake Abuja. Kamar yadda wata sanarwar da mataimaki na musamman a kan harkokin watsa labarai ga mataimakin shugaban qasa Mista Laolu Akande ya sanya wa hannu, mataimakinn shugaban qasar ne ya jagoranci taron a matsayinsa na shugaban kwamitin gudanarwa hukumar ta NEMA. Osinbajo ya ce, “Shugaban qasa ya umurci mu yi nazarin varnar da aka yi a garuruwan da al’ummun da rikice rikicen suka rutsa dasu musamman rikicin manoma da makiyaya. “Hukumar NEMA ce zata jagoranci wannan aikin yayin da ofishin shugaban qasa zai bayar da tallafi na

musamman. “Zamu yi aiki ne tare da mutanen da rikincin ya shafa ba wai mu shugo da mutane daga waje ba a qoqarinmu na sake farfaxo da garuruwan. “Zamu yi aiki da mutanen qauyukan, masu akin hannu saboda suma su amfana daga aiki sake gina garruruwa. Jihohin da waxanna rikicin makiyaya da manoma ya fi rutsawa dasu sun haxa da jihar Binuwai da Plateau da Taraba da Zamfara da Oyo da Kogi da Ekiti da kuma Ondo. A ranar 5 ga watan Fabrairu Osinbajo ya bayyana wa majalisar gudanarwar hukumar NEMA cewa, shugaban qasa ya bayar da amincewar kwamitin qasa da zata yi nazarin yadda za a sake gina alummun da rikice rikicen da suka auku na jihohin qasar nan. Ya ce, wannna yana cikin hanyoyin neman maganin matsalar rikicin manoma da makiyaya na dindindin a wasu sassa na qasar nan. A taron da aka gunadar ranar Talata, Osinbajo ya taya manbobin kwamitin murnar naxin da aka yi musu ya buqaci su qara qaimi wajen ganin aiyukan hukumar ya samu ci gaba, ya ce, lallai aiyukan NEMA ya yi

matuqar tasiri a faxin qasar nan. “Hukumar NEMA tana gudanar da aiyuka fiye da abin da aka ayyana mata ahukumance, abin day a kamata mu xauka da mahimmanci kenan” inji shi. Mataimakin shugaban qasar ya kuma buqaci Hukumar ta bayar da qarfi wajen faxakar da mutane a kan lamurorin dake kawo bala’i na gaggawa da kuma abubuwan daya kamata a yi a lokacin da aka samu varkewar wani bala’i. Ya kuma buqaci hukumar NEMA ta haxu da masu ruwa da tsaki wajen gudanar

da aiyukan ta musamman da qungiyouyi masu zaman kansu da kanfanoni masu zaman kansu. Manbobin hukumar ta NEMA sun haxa da Shugaban Hukumar da wakilin ofishin sakataren gwamnatin tarayya da wakilin ma’aikata harkokin cikin gida da na Jiragen Sama dana ma’akatan lafiya da kima ma’akatan ruwa. Sauran sun haxa da wakilan rundunar sojojin qasa dana sama. A wajen taron, shugaban hukumar NEMA Mustapha Maihaja, ya gabatar dac tsarin gudanar da aiyukansu

da kuma matsalolin da suke fuskanta. A wata subuwa, mataimakin shugaban qasa Yemi Osinbajo ya karvi bakoncin tawagar qungiyar “Oxford Business Network for Africa from the Oxford Business School” da ta fito daga Ingila a fadar shugaban qasa Abuja. Mista Bayo Owolabi, ne ya jagoranci tawagar, ya kuma godewa gudummawar Nijeriya a rahoton da aka samu na “World Bank Doing Business Report”. Ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya a qoqarinta na farfaxo da tattalin arziqin qasa.

Mutane Na Ta Yaba Wa Sarkin Gombe Na III Daga Abubakar Abba

Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Dakta Abukakar Shehu Abubakar lll wanda alummar suke yi masa laqabi da mai horon abi Allah ko kuma jarumin wannan lokacin, an haife a ranar 17 ga watan Nuwambar shekarar, 1977 a cikin jihar sa ta Gombe. An sanya shi a makarantar Firamare dake jihar Gombe daga shekarar 1982 zuwa shekarar 1988 daga nan ya wuce zuwa makarantar Sakandare ta kimiyya dake cikin jihar Gombe daga shekarar 1989 zuwa shekarar 1995. Mai martaba Abubakar Shehu ya samu Babban Digiri a fannin nazarin siyasa daga jami’ar Maiduguri, inda yake a matsayin xalibi daga shekarar 2001 ya kuma kammala a shekarar 2005. Kafin a naxa shi Sarki, ya yi aiki a wuri da ban-da-ban ,inda ya riqe muqamin Kansilan sanya

ido a qaramar hukumar Gombe daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2007. Bugu da qari, daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2009, mai marba Dakta Shehu Abubakar ya riqe muqamin mataimaki na musamman na Darakatan gudanar da mulki a Ma’aikatar Tsaro ta qasa dake birnin tarayyar Abuja, inda daga baya kuma, ya zama shugaban Kamfanin Kliptown Lagoon Nigeria, inda daga baya kuma, ya riqe muqamin Babban Darakta na kamfanin Horizon Interlinks Global Resources. Mahaifin sa marigayi Shehu Abubakar shi ne Sarkin Gombe na goma kuma ya rasu yana da shekaru 76, inda kuma bayan rasuwar mahaifin nasa a ranar 27 ga watan Mayu shekarar 2014 sai Alhaji Dakta Abukakar Shehu aka tabbatar masa da sarautar Sarkin Gombe, inda ya zamo Sarkin Gombe na sha xaya.

Mai martaba Abubakar Shuhu na III ya zama magajin mahaifin sa tun daga farkon watan Yunin shekarar 2014. Sakataren Gwamnatin jihar Gombe Abubakar Bage, ya miqawa Dakta Abubakar waqisar tabbatar wa da Dakta

•Sarkin Gombe

Abubakar Sarkin na Gombe Gombe a babban Masallacin Juma’a na jihar a ranar shida ga watan Yunin shekarar 2014. Wani abin sha’awa shi ne, tun daga lokacin da Dakta Abubakar Shuhu ya zama Sarkin na Gombe yau kusan shekaru uku da wani

abu, bai ajiye irin ayyukan alkhairin da mahifin sa yake yiwa alummar jihar ta Gombe ba musamman talakawa, inda ya xora daga inda akan kyawawan ayyukan da mahaifin sa yake yi na gudanar da ayyukan jin qai ga xaukacin alummar jihar. Maimartaba Dakta Abubakar yana jan kowa ajiki baya nuwa kowa qyama, inda hakan ya sanya xaukacin almummar jihar a kullum suke nuna hamdalar su. Bugu da qari, irin wannan tausayawar da yake yiwa alummar jihar ne ya sanya ya samu lambobin yabo iriiri, misali, a kwanan baya ya karrama shi da lambar yabo ta girmamawa daga Kungiyar Ci gaban Matasan Jahar Gombe (GYPN). A kulluma Dakta Abubakar yana da burin yaga ana zaman lafiya a tsakamin alumomin jihar da kuma kiraye-kirayen kowa ya zauna lafiya da juna.


RAHOTO 13

A Yau Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Obasanjo Ba Shi Da Mutumcin Zargin Wani Da Cin Hanci –Ayo Adebanjo Daga Bello Hamza

Xaya daga cikin jagororin qungiyar qabilar Yarbawa ta Afenifere Cif Ayo Adebanjo Ya ce tsohon shugaban qasa Olusegun Obasanjo ba shi da wani Mutumcin da zai zargi wani dan cin hanci da rashawa. Ya ce, har yanzu Obasanjo bai qaryata bayanin cewa Naira 20,000 ne kachal a assusun ajiyarsa na banki a lokacin da ya sake dawowa daga gidan yari ya kuma zama shugaban qasa a shekarar 1999 sannan tsohon mataimakin shugaban qasa Atiku Abubakar da wani xan kasuwa mai suna Oyewole Fasawe ne Suka ceto shi daga talauci. Adebanjo ya qara cewa, in har da Nijeriya qasa ce mai mutunci da mutane kamar su Obasanjo ba zasu iya samun daman tasiri a harkokin jama’a ba har abada, ya ce, yana matuqar mamakin yadda mutane ke mahimmantar da Obasanjo duk da an irin halayyarsa. Ya ce, yana da tabbacin cewar, in har aka samu gwamnati jama’a masu adalci ke mulkin qasar nan da zasu qwace katafaren ginin xakin karatun nan na “Obasanjo’s Presidential Library Complex” dake garin Abeokuta” daga hannunsa. Adebanjo, wanda zai cika shekara 90 a ranar 10 ga watan Afirilu, ya yi bayanin ne a cikin littafin tarihin rayiwarsa da ya rubuta, an gabatar wa jama’a ranar Talata a Legas. Ya qalubalanci tsohon shugaban qasar musamman a fasali na 13 shafi na 233 na littafin a in da ya yi bayanin, ‘Awolowo, Obasanjo and the Yoruba Nation.’ A bikin da tsohon mataimakin shugaban qasa na sojoji Ebitu Ukiwe ya jagoranta, an kuma samu halartar jagoran jam’iyyar APC Bola Tinubu da tsaffin Gwamnonin jihar Ogun Cif Olusegun Osoba da Otunba Gbenga Daniel. Haka kuma taron ya samu halartar tsohon shugaban qungiyar qasashe renon turai Chlif Emeka Anyaoku, da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Cif Olu Falae da tsohon qaramin minista a ma’aikatan tsaro Musiliu Obanikoro da tsohuwar Ministan masa’anatu Misis Nike Akande sai kuma shugaban cocin Latter Rain Assembly, Pasto Tunde Bakare da kuma Cif Albert Horsfall. Haka kuma taron ya samu

halartar shugaban First Bank Nigeria, Misis. Ibukun Awosika da dan kasuwa Cif Rasaq Okoya da Farfesa Pat Utomi da kuma Tony Elumelu. A cikin littafin nasa, Adebanjo ya kwatanta shekaru 8 na mulkin Obasanjo daga 1999 zuwa 2007 a lokacin daya jagorancin kasar a matsayin shugaban farar hula da cewa yana tattare da tashin hankali da bai kuma tsinana wa qasa wani abin alhairi ba. Ya ce, “Mutumin dake tafiya kamar ya fi kowa mahimmanci bai samun nasara a matsayinsa na shugaban qasa ba, shekaru 8 da ya yi (19992007) a matsayin shugaban qasa tashin hankali ne kuma bai tsinana wa qasa komai ba, babu wani abin alhairi daya aikata mana, me ya aikata a shekaru 8 xin da ya yi? Kafin ya zo muna sayan litar mai Naira 20 ana kuma sayar da gangan mai Dala 23. A shekarar 2007 a muna sayen litar mai Naira 75 yayin da gangan mai yake Dala 65 zuwa Dala 75, ko a lokacin Abacha ana sayaen Dala xaya ne a Naira 120 a shekarar 2007” Adebanjo wanda xan gani kasha nin marigayyi Cif Obafemi Awolowo ne, ya ce, Obasanjo ya wulaqanta Awolowo, a lokacin daya ziyarce shi bayan ya zama shugaban qasa na mulkin soja bayan da aka kashe Manjo Janar Murtala Mohammed ranar 13 ga watan Fabrairu na shekarar 1976. Ya qara da cewa,“A kwai alamomin masu yawa dake nuna cewa Obasanjo maqiyin qabilar Yarbawa ne, bashi da tausayi ga muradun yarbawa, muradun kansa ne kawai ke a gaban sa a duk abin daya sa a gaba. Wannan itace matsala ba kuma ina da hujjojin masu yawa da zai tabbatar da abin da nake faxa.” Adebanjo ya kuma xorawa Obasanjo alhakin rushewar jam’iyyar Alliance for Democracy lokacin daya naxa marigayyi Bola Ige, wanda xan jam’iyyar ne a matsayin minista ba tare da amincewar jami’iyyar ba a shekarar 1999. Daga nan kuma ya qara da cewa, “A nawa mahangar tun lokacin da Bola Ige ya shiga gwamnatin Obasanjo bayan ya faxi zaven FIFA gwani da aka gudanar in da ya samu quri’a 6 yayin da Cif Olu Falae ya samu quri’a 17 ne aka kama hanyar rugujewar jam’iyyar, abubuwa da suka faru ne suka kai ga rugujewar jam’iyyar AD. A nasa jawabinya wajen taron, Anyaoku ya bayyana

•Ayo Adebanjo

Adebanjo a matsayin xaya daga cikin waxanda suka kafa sabuwar Nijeriya. Anyaoku ya ce, kamar yadda na faxa Adebanjo ya san lokacin da qasar nan ke mulkin yanki yanki aka kuma samu gaggarumin nasara. Ya ce, “Na rayu a wanna lokacin na kuma tabbatar a cikin zuciya na ana tafi da Nijeriya yadda ya kamata a lokacin a na tafi da qasar ne a bisa tsarin tarayya na gaskiya, kowanne yanki na tafiya a bisa iya qarfinaa Tate da alfaharin kasancewa a cikin tarayya Nijeriya gaba xaya. “Tuni muka rasa wannan kyakyawan tsarin gwamnatin duk lokacin da muke tuna ci gaba sai baya ne aka samu ci gaban. Da farko muxan tuna yankin Yammacin qasar nan qarqashin shugabancin Cif Obafemi Awolowo, a wancan likacin a kwai gada mai ma’ana da yankin Gabashin Nijeriya wanda Dakta Michael Okpara ke shugabanta yana qoqarin kawo ci gaba yankinsa. An samu ci gaba kwarai a fannin aikin noma a gabashin qasar nan. A yankin Arewa kuma inda Sir Ahmadu Bello ke mulki, ya koyan harkar mulki daga takwarorinsa na yanmmaci da gabashin da kuma yakin yamma tatsakiya qasar nan. Anyaoku ya ce, shigowar sojoji harkar mulki ne ya kawo mana matsalar da qasar ne ke fuskanta, domin

bai kamata su jirkita tsarin mulkin qasa na. Ya ce “Na yi imani da sojoji basu yi juyin mulki ba a watan Janairu na shekarar 1966 kumua suka tsaya a kan mulki na tsawon shekaru, sannan da basu jirkita tsarin mulkinmu ba da qasar nan ta samu cikakkiyar ci gaba daya kamata a dukkan fannonin rayuwa. “Ban tava tunanin a kwai wata qasa a duniyan nan da ke da banbance banbance kamar tamu zata iya rayuwa a qarqashin mulkin soja ba. Abin da muke buqatar a Nijeriya shi ne, tsarin trayyata na haqiqa dake tafiya tare da tunanin Cif Obafemi Awolowo, abin kuma daya rayu a kai har ya koma ga Allah”. Shima da yake jawabi, Tinubu ya ce, Adebanjo, mutum ne tsayayye, da ya yi tsayin daka wajen ganin an yi zave cikin adalci a shekarar 1999 lokacin daya tsaya takarar gwamnan Jihar Legas,har Allah ya ba shi nasara. Ya ce “I na matuqar mutunta raayoyonsa a kan abubuwan da suka shafi qasa, Idan baka fahince shi ba sai kayi tunanin yana da ra’ayin riqau a kan wasu harkoki da suka shafi qasa. Tabbas na yarda da shi a kan matsayin sa na sake fasalin qasa ta yadda kowanne yanki zai ci gashin kansa tare da mutunta juna.


14

Aikin Hajjin 2108: NAHCON Ta Qara Ranar Yin Rijista Zuwa 30 Ga Watan Afirilu Daga Abubakar Abba

Hukumar Aikin Alhazai ta Qasa (NAHCON) ta qara ranar yin rijistar maniyya ta aikin hajjin shekarar 2018 zuwa ranar 30 ga watan Afirilu. A sanarwar da hukumar ta fitar ta hannun Shugabar sashen yaxa labarai Hajia Fatima Mustapha Mohammed ta baiwa jaridar LEADERSHIP a Abuja, hukumar tace, ta yi hakan ne saboda kirayekirayen da maniyya tan sukai ta yi a taron bitar data shirya masu a Abuja. Acewar hukumar, zata kuma yi amfani da damar qara ranar don ta kammala sanar da kuxin aikin hajji na bana. Taci gaba da cewa, babu sanar da kuxin aikin hajjin na bai xaya a bana ga mahajjatan, inda tace, kuxin ko wacce jiha itace zata sanar. Hukumar ta yi kira ga maniyyatan dasu tabbatar da sunyi rijistar kafin ranar ta qarshe data ware domin baza ta sake xage ranar ba. Tuni tawagar jihohi dana hukumar suka isa qasar ta Saudiyya don kammala shirye-shirye na qarshe kafin a sanar da kuxin aikin hajjin na bana ga alummar gari.

•Abdullahi Muktar

A Yau

Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Jadawalin Varayin Gwamnati: Tsohon Gwamnan Neja Zai Shigar Da Qara Kotu Daga Idris Aliyu Daudawa

Tsohon gwamnan jihar Niger Babangida Aliyu ya qaryata cewar ya saci kuxaxen jihar, lokacin da ya yi mulkin muqamin gwamna na shekaru takwas, ya kuma yi barazanar shigar qara kotu domin ya qalubalanci zargin da ake yi ma shi. Babangida Aliyu ya qaryata maganar zargin da ake yi ma shi ne, a wata sanarwar da ya sa ma hannu, ranar Litinin, lokacin da yake nuna rashin jin daxin shi, dangane da sunayen varayin da suka saci kuxaxe, wanda gwamnatin tarayya ta

fitar. Ya ci gaba da bayanin cewar ‘’Ni ban ma san dalilin da gwamnatin tarayya ta sa sunana a cikin waxanda suka saci kuxaxe, mutne 24,wanda Ministan watsa labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya fitar. Ya yi barazanar zai shigar da qara har sai ya kai ga qarshen al’amarin, bayanya gama tuntuvar lauyoyin shi. Shi dai gwamnan ya ce, babu wanda ya same shi d wata takarda da take nunaya amshi Naira bilyan xaya da dubu xari shida,daga hannu tsohon mai ba da shawara akan

harkokin taro Sambo Dasuqi,don haka ya buqaci gwamnatin tada nuna alamun cewar ya yi hakan. Ya furta cewar APC duk tana yin abin da ta iya, sai taga ta goga ma shi kashin kaji, sabnoda yaqi ya shiga jam’iyyar. ‘’Gwamnatin APC ta yi shirin sai ta samu damar vata mani rayuwa saboda kawai na qi yarda na shiga jam’iyyar.’’ ‘’Mun san maganar cewar maganar shiga jam’iyyar wata siyasa, ai maganar idan mutum yana so ne, ba wata maganar tilastawa a nan’’. ‘’Da yake suna qoqarin sai sun yi mani sheri,yanzu

ina kotungwamnatin tarayya da kuma babbar kotu Niger, duk asaboda suna neman vata mani suna’’. ‘’Wannan ya nuna ke nan suna qoqarin kai ni har qasa, ammakuma ba zasu yi sa ‘a ba. Mr Aliyu ys qara jaddada cewar shi dai a sanin shi ya yi ma al’ummar jihar Niger kamar yadda ya kamata. ‘’A matsayi na na gwamna, nabar abaubuwanda za ariqa tunawa da ni, donhaka duk wani qoqari na a vata mani suna , abin ba zai yi tasiri ba. Babu wani abin da zai al’umma jihar Niger su manat da ni.’’

Sanata Mustaphar Bukar Ya Rasu, Yana Da Shekaru 63 Daga Khalid Idris Doya, Abuja

Shugaban kwamitin manyan kasuwanni na majilisar Dattawan Nijeriya, Sanata Mustapha Bukar (Na jam’iyyar APC, wanda ke wakiltar mazavar Katsina ta Kudu) mazavar da shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya ke ya rasu. Sanata Bukar wanda kuma shi ne ke riqe da sarautar (Madawakin Daura) ya rasu ne a jiya Laraba da misalin qarfe goma na safiyar jiyan, rasuwarsa na zuwa ne bayan fama da rashin lafiya da ya yi fama da ita. Qanin marigayin, Alhaji Kanta Bukar, ya tabbatar da mutuwar xan uwan nasa, ya ce Bukar ya rasu ne da safiyar jiya Laraba a asibitin Nizamiye da ke Abuja. Ya ce, marigayin ya rasu ne ya bar mata biyu a duniya, ‘ya’ya goma sha biyu, ciki kuwa har da Dakta Ibrahim Bukar wanda yake aiki a ofishin hukumar sadarwa ta qasa ‘Nigerian Communications Commission’. Alhaji Kanta ya bayyana cewar jana’izar marigayin ne a jiya Laraba a garin Daura. Kanta Bukar ya misalta rasuwar marigayin babban yayansa da cewar rashine wanda suka yi gagaruma,

wacce za su jima suna tsaka da tunanin rashinsa, haka kuma ya bayyana cewar rasuwar tasa qasa da jihar Katsina ne suka yi wannan rashin xaya daga cikin masu hidima domin ganin qasar nan ta samu ci gaba. Mai tallafa wa marigayin na qashin kai, Malam Ahmed Abdullahi, ya misalta mai gidansa a matsayin wani mutum mai gudanar da aiki tukuro domin tabbatar da yin aikin da jama’ansa suka turasa zuwa majalisa. Abdullahi ya bayyana cewar za su ci gaba da tunawa da Bukar a cikin nagartattun Sanatocin qasar nan, musamman daga yankin nasu. LEADERSHIP ta labarto cewar Mustapha Bukar ya dawo qasar nan Nijeriya daga UK domin jinyar rashin lafiyar da ta addabesa. Wakilinmu ya labarto cewar an haifi marigayi Sanata Bukar Mustapha ne a ranar 31 ga watan Disamba 1954 a garin Daura, Bukar dai wannan zaman sa Sanatan ita ce ta farko da ya shiga majalisar dattawa a matsayin Sanatan. Mustapha Bukar ya kammala Firamaren sa ne da garin Daura shekara ta 1968, daga bisani kuma ya tafi Sakandarin GSS da ke Katsina, ya kammala ne a shekara ta 1973. Sannan kuma ya tafi School of Basic

• Marigayi Sanata Mustapha Bukar

Studies da ke Zariya a 1975, bayan nan kuma ya samu izinin shiga jami’ar ABU inda ya karanci ilimin Injiniya a shekara ta1978. Bayan da ya yi wa qasa hidima, ya kuma yi aiki a ma’aikatar ruwa na jihar Kaduna a matsayin manajan aikace-aikace, daga bisani ya zama babban Manaja, ya yi ritaya ne a shekara ta 2008 a

matsayin Darakta a ma’aikatar ruwa ta jijar Katsina. Sanata Bukar ya rasu ne a daidai lokacin da majalisar take tsaka da jimamin rasuwar Ali Wakili mai wakiltar Bauchi ta Kudu wanda ya rasu a kwanakin baya a ranar 17 ga watan Maris, Wakili ya rasu yana da shekaru 58 a duniya, ya kuma rasun ne a gidansa da ke Abuja.


A Yau Litinin 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Domin Qarin Bayani A Tuntuvi: • Mubarak Umar – 0703 6905 380 •Sulaiman Bala Idris –0703 6666 850

TALLA 15


16

Siyasa A Yau A Yau

Alhamis 5.4.2018

Mawallafin Jarida Zai Tsaya Takarar Gwamnan Neja Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Rahotanni sun bayyana cewar mawallafin jaridar Nigerwich, Alhaji Yahaya Muhammed Usman yayi nisa akan niyyarsa na tsayawa takarar gwamnan Neja a zaven 2019, mawallafin yana xaya daga cikin ‘yan jarida masu gwagwarmaya ganin gwamnati ta kyautatawa talakawan jihar, an ruwaito cewar ya yanke shawarar tsayawa takarar ne dan ganin yadda har yanzu gwamnati ta kasa samar da natijiyar hanyar da zai taimakawa marasa qarfi. Yahaya Baba wanda matashi ne da aka fi sani da “Sai Baba” yana daga cikin matasa masu azama wanda kuma tsohon mamba a jam’iyyar PDP, duk da cewar

• Yahaya Muhammed Usman

akwai rahotannin da suka nuna cewar tun bayan faxuwar jam’iyyar a zaven 2015 ya fice daga jam’iyyar. Dan gane da jin jam’iyyar

da matashin ya koma, Leadership Ayau tayi qoqarin jin tabakinsa amma hakan ya cutura. Duk qwazo da karvuwansa a wajen matasa ‘yan uwansa, tsarin mulki na karva-karva da jihar ta amince da shi na daga cikin turakun da ake ganin zai iya hana shi samun damar yin takarar duba da irin salon da jam’iyyun adawa ke xauka a jihar na ganin kowa ya tsayar da xan takara daga yankin Neja ta Arewa. Wani makusancinsa ya tabbatar mana cewar yanzu haka matashin xan jaridan ya himmantu ne tattaunawa da magabata akan wannan maganar, lallai takarar kujerar gwamna ta nan kuma akwai muradin hakan amma har yanzu ba mu tsayar da jam’iyya ba, muna dubi da

tsari da dokokin jam’iyyun da ke da rajista ba lallai ba ne mu fito a jam’iyyar da jama’a ke tsammani, muna qoqarin zaqulo jam’iyyar da ke da nagartaccen tsarin da zai taimakawa tattalin arzikin qasar ne wanda zai inganta rayuwar al’ummar jiha. Makusanci ya musanta zargin da ake yaxawa na cewar turo gwanin na sa ake son yi, yace ai Yahaya Muhammed “ Sai Baba” xan jiha ne kuma kar ka manta an yi mulkin baya da shi kuma ya taka rawar gani wajen inganta rayuwar matasa a jihar nan, ko yanzu halin da ya ga matasa a ciki na vata masa rai, tunda yasan wani abu a mulki shi yasa ya ke qoqarin neman goyon bayansu da haxuwa mu ceto jihar nan daga wannan halin da ta ke ciki.

Ba Wani Canji Da APC Ta Kawo A Qasar Nan Sai Qunci A Zamantakewar Al’umma -Dada Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An bayyana cewa ba wani abu da mulkin jam’iyyar APC ta kawowa al’ummar qasar nan na canji illa sasu a cikin quncin rayuwa. Shugaban jam’iyyar PDP na qaramar hukumar Birnin Kano, Alhaji Sabo Ahmad Dada ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai. Ya ce kowa ya kalli yanda al’amura ke tafiya an samu koma bayane a qasar nan komai ya tavarvare mutane suna cikin quncin rayuwa,ba ilimi,ba hanyoyi,ba wuta ba ruwa ba aikinyi komai ya koma baya babu ma alamar sunaso su gyara. Alhaji Ahmad Sabo Dada ya ce takai yanzu al’ummar qasar nan na cewa dama za a dawo da qasar yanda PDP ta basu da ya fi saboda a wannan lokacin akwai walwala da jin daxi. Shugaban na jam’iyyar PDP na qaramar hukumar birni ya ce duk lokacinda

masu mulkinnan suka gaza sa suce haka suka sami qasar,hakan sai ya bashi dariya saboda in aka yi duba da wannan wahala da yan qasa ke ciki me yasa a baya basu shiga ba? Da suke cewa PDP ta kashe qasar da suka karva sun taradda mutane a cikin quncin rayuwane? Sai da suka karveta cikin wata xaya abu ya rikice musu kaya suka riqa tashi. Ya ce an ce, PDP ta shekara 16 tana vata qasa a cikin shekarun nan ba inda aka sai mai Naira 145, ba inda aka sayi buhun shinkafa sama da Naira 10, 000. Wane hikima PDP ta riqa yi mutane suka riqa samun abubuwan masarufin rayuwa cikin sauqi da kwanciyar hankali? Dada ya qara jaddada cewa, “babu wani abu da APC zasu nuna,basuzo da basuzo da tunanin yanda za suyi mulki ba,basu tava zaton xan’Nijeriya zai zavesu ba saboda haka basuda”blueprint”saida

aka karvi mulki aketa kame”kame,wannan shi ne abin da yake faruwa daga sama har qasa na mulkin APC.Saboda haka mutanen qasar nan sun zavi mutane da da ba za su iya mulki dan kyautatawa musu ba.Dan haka ya kamata nan gaba su buxe ido su zavi jam’iyyarda ya kamata. Ahmad Sabo ya ce yasan PDP itace yan qasar nan ya kamata su zava,dan in aka zauna aka natsu za aga mulkinda APC ta kusa shekara uku tana yi da ita ta shekara 16 da PDP ta yi ana cewa ta kashe qasa kuma har yanzu damakwaraxiyya ake.anya ba qasa bane?Yan qasa su zavi mutanen kirki matasa ba wanda suka shekara 70 ko 80 ba.kazo ka zavi mutum mai zaiyi maka? Alhaji Ahmada Sabo Dada ya ce yanzu kamar Gwamnan Kano Ganduje ne,tunda yazo bashida wata magana saita qaqabawa mutane haraji ga wahala ga komai amma

haraji ake nema,talakawa. ma’aikata,yan kasuwa haraji, gashi an qaqabawa wa ma’aikata biyan kuxin inshorar lafiya dole a zaftari kuxi a xan albashinda ake basu wanda baya ma isarsu saboda halin quncin matsi da tsadar rayuwa da APC ta jeja al’umma a qasar nan. Ya qara da cewa ga Asibitoci ba magani,an farke tituna a kano da sunan aiki ba a yi.Ya kamata al’ummar Kano da dukkan yan qasa su gane cewa ana cewa an fta daga matsin tattalin arziqi a qasar nan kamar yadda mataimakin shugaban qasa yake faxa a wani taro saboda sunga zave ya taho zasu baza kuxi domin xan qasa ya manta ya zave su, to yana qara zavensu suka koma matsalarda za a koma ya fi na yanzu dan haka ya zama wajibi mutane su buxe ido PDP itace mafita ita ya kamata a yi domin kowa yanzu a qasar nan ya ga al’qiblar da waxanda suke mulkin qasar a yanzu suka kai ta.


A Yau Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Wakilcin Al’umma Da Ce Ne! Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Wakilcin Al’umma al’amari ne mai sarqaqqiya gaske domin akwai abubuwa masu tsoratarwa da kuma ban sha’awa a cikinsa, saboda haka ne ma ya sa tsarin demokaraxiyya ya mayar da hankali kan baiwa al’umma damar zavar wanda suke ganin kila shi ne zai iya fidda jaki daga duma, ko ace zavarsa Kwalliya na iya biyan kuxin Sabulu. Wasu al’umma sun tsinci kansu cikin dana sanin zavar wasu daga cikin wakilansu a matakai iri daban daban, wasu kuwa baki har baka domin laya tayi kyan rufi. Duk da cewa akwai kujerun da doka ta nuna cewa su waxanann wakilan abin da ake so daga garesu shi ne samar da dokokin da za su inganta rayuwar al’ummar da suke wakilta, ba cewa aka yi dole sai sunzo sun bayar da kuxi ba. Amma a siyasa irin tamu wannan bashi talakawa ke duba wa ba, abin da ake buqata shi ne mene ka bani a matsayi na wanda na zaveka, wannan kuma ba dole ya shafi sauran al’ummar da muka haxu wajen zavar wakilin namu ba. Rt. Honarabul Ado Alhassan Doguwa matashin xan siyasa wanda shekarunsa duka duka basu wuce cikin cokali ba, Mai tsawatarwa a majalisa, ya kafa tarihin da a halin yanzu ba wani wakili a majalisar wakilai ta tarraya da ya kama qafarsa. Da farko dai a halin yanzu shi ne wakili xaya tilo a faxin majalisar wakilan tarayyar Najeriyya da ya zarta sauran daxewa a cikin wannan majalisa, domin ahalin yanzu cikin zango na biyar yake a matsayin wakilin al’umma Doguwa/T/Wada daga Jihar Kano. Wannan ya tabbatar da irin amincewar da al’ummarsa suka yi masa sakamakon irin tagomashin da yake kaiwa yankin da yake wakilta Haka zalika shi ne xan majalisar da ya ciri tutar cewa matuqar yana

cikin qasarnan Najeirya, ya wajabtawa kansa duk makon duniya sai ya koma mazavunsa domin ganawa da al’ummarsa. Sannan kuma idan ana batun samar da ayyukan ci gaba, wannan kuma sai dai ayi addu’a a tashi, domin shi ne wakili da kusan bawai qaramar Hukuma, Mazava ko garin dagaci ba, duk wani akwatu da ake kaxauri’a akansa Alhassan Ado Doguwa ya kai masa aikin raya qasa. Qaramar Hukumar T/ wada na da Akwatu 240 ya yin Doguwa keda a kwatu 116, duk waxanan akwatuna sun rubuta da wani nau’I aikin ci gaba, kama daga rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana, asibiti, hanya, Makaranta da sauran abubuwa more rayuwa. Ayyukan wakilin al’ummar Doguwa/T/ wada sun zama kamar al’amara domin a cikin watanni uku na wannan shekarar Alhassan Ado Doguwa an tabbatar da cewa al’ummar da ya ke wakilta sunyi hafzi da rijiyoyin Burtsatse masu amfani da hasken rana sama da 54, ajujuwa, hanyoyi, asibitoci da kuma taimakon harkokin karatun xalibai ‘yan asalin wannan yanki. Yanzu haka abin da ba’a tava gani ba Alhassan Ado bisa la’akari da yankin da ya fito, yanki ne da ake gudanar da harkokin Noma ka’in da na’in, hakan tasa ya samar da Tirela 30 ta takin zamani wanda kyauta ake rabawa manoman waxannan Qananan Hukumomi biyu da yake wakilta. Haka kuma domin sauqaqa zirga-zirga daga nan zuwa can wakilin al’ummar ta Doguwa/ T/Wada ya samar da babur 1,000 xaya lakadan wanda yanzu haka an gama shirye shiryen rabawa al’ummar da yake wakilta. Matan Karkara a qananan Hukumomin Doguwa/T/ Wada su ne shaida domin aduk shekarar Allah ta’ala wakilin nasu na samar da injunan Malkaxe, Saqa tare bayar da jarin bahunan fulawa domin ci gaba da gudanar sana’u iri daban daban.

SIYASA 17

• Doguwa

Batun injunan ban ruwa ga manoma kuwa an kai matsayin da a halin yanzu gidan kowa akwai, Haka lamarin ya ke ta fuskar tsaro duk wanda ya san yankin Doguwa/T/ Wada yasan sunyi fama da matsalar sace-sacen shanu da garkuwa da mutane, amma yanzu al’amarin ya zama tarihi domin Alhassan Ado Doguwa ya yi duk mai yiwu domin ganin an samar da wata rundunar soja da suke gudanar da atisaye a cikin dajin Falgore wanda hakan ya kawo qarshen waccan matsala. Idan da ace duk sauran wakilan da aka zava haka suke gudanar da ayyukan da aka tura su wakilcin al’umma, ko shakka babu da jama’a basu ci gaba da kokawa a wasu lokuta ma wanda har jin wasu al’umma ake suna qoqarin yin kiranye domin maido da nasu wakilin gida saboda rashin tsinana masu komai. Haka kuma da yawa al’ummar wasu qananan Hukumomin

daga randa aka rantsar da wanda suka zava shi kenan sai zave ya zagayo sanann ake sake ganinsu sun qara lallavowa da qoqon barar quri’ar al’umma. Amma dai al’ummar Doguwa/T/Wada sun nu nawa Duniya hallaci domin ba haka kawai al’umma za su ci gaba da zavar wakili har karo biyar ba tare da gamsuwa da wakilcin da ya ke masu ba, haka ma yanzu duk wanda ke wanann yankin ba’a kai masa maganar wani xan takara, domin dole sai ka faxa masu abin da ka yi wanda ya shafe wanda Alhassan Ado ke yiwa al’ummar Doguwa/T/ Wada har da kake buqatar su aje gwaninsu wanda suka gwada kuma suka tabbatar da nagartarsa. Daman dai kamar yadda bahaushe ke cewa buqatar maje Hajji Sallah, saboda Alhassan Ado ya zarta sa’a kuma ga dukkan alamu shi al’ummarsa suke da yaqinin ci gaba da wakiltarsu.


18 RAHOTON MUSAMMAN

A Yau

Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Sara Suka A Kaduna: Laifin Gwamnanti Ko Na Jami’an Tsaro Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

Kalmar sara suka, ko ‘yan shara, wani suna ne da idan aka kira kan razana zukatan mutane har ta kai su ga sun fita daga hayyacinsu musamman mutanen cikin Garin kaduna inda lamarin yafi yin qamari. Babu ko shakka a halin yanzu ‘yan sara suka ko mu ce ‘yan shara, na ci gaba da cin karansu babu babbaka, musamman a irin yankunan unguwannin da suka haxa da kawo, Badarawa, unguwar shanu, kwaru Malali, unguwar Dosa, Hayin banki, Rafin guza, Barnawa da dai sauran wurare a cikin garin kaduna. Zamu iya cewa, lamarin ya qara qaruwa ne ranar lahadin makon da ya gaba, inda waxannan ‘yan sara suka aqalla su 100 da ‘yan kai, su ka afkama Unguwar Kawo dake Qaramar hukumar kaduna ta Arewa. Na kasance ganau ne ba jiyau ba, domin za a iya cewa kusan lamarin ya afku ne a kan idona, domin na fito zan tafi wajen aiki, ban ankara ba, sai na ga jama’a na ta gudu, ban yi wata wata ba, a matsayina na mai neman Labarai, na koma gefe nayi fakin mota na, na fito domin na shaida abin da yake faruwa, duk da a lokacin kowa na ta kansa, amma nayi sa’a na sami wani mai aikin haya da mashin, wanda ake ce ma ‘Xan acaba, a inda nake tambayarsa dalilin guje gujen da naga a nayi, a nan ne yake shaida min cewa ai ‘yan Sara suka ne suka faxo cikin unguwar kawo. A inda ya qara da bayyana min cewa, “Ranka ya daxe, wallahi masallaci muka shiga har an tayar da hiqama za’ayi sallar la’asar, waxannan ‘yan Sara suka, suka faxo mana dole Limamin ya datse sallar kowa ya fito ya yi ta kansa.” Duk da wannan bayanin da Xan acaba ya yi mani, sai da na roqi alfarmarsa akan ya xauke ni a kan mashin xinsa domin naje na gani da ido na, saboda kullum jin labarin ‘yan Sara suka

nake yi, amma ban tava ganin su da idona ba. Da qyar na shawo kan Xan acaba har ya amince ya xauke ni zuwa cikin unguwar kawo, tabbas a karon farko nayi ido huxu da waxannan Matasa ‘yan Shara ko ‘yan sara suka, waxanda yawancinsu Matasa ne ‘yan qasa da shekaru 19 zuwa 22. Kuma gaba xayansu babu wanda baya xauke da makami a hannunsa. Mun kai dai dai wajen da ake sayar da dabbobi dake kasuwar kawo, muka yi arba da wani Matashi, ya na gudu yana ihu yana kiran ‘wayyo Allah’ ‘wayyo Allah’ da hannunsa a guntule jini na zuwa tamkar an kunna ruwan fanfo. Wannan lamari ya yi matuqar tayarmin da hankali matuqar gaske, domin ban san lokaci da na yi tsalle na sauka a kan mashin ba, na ranta ana kare, domin a lokacin na lura har ‘yan sara sukan sun yi nasarar qone wasu gidaje guda biyu, wato gidan yin biredi mai suna Aminci, da kuma wani gida dake jikinsa. Cikin ikon Allah nayi nasarar shiga cikin makarantar kwana ta ‘yan mata wanda ake kira GGSS Kawo, domin na tsira da raina.

Da misalin qarfe 8 na dare, na sami kiran waya cewa Gwamnan Jihar kaduna, Malam El-Rufai zai ziyarar gani da ido a inda lamarin ya afku. Nan ma ban yi wani qasa a gwiwa ba, na xauki shaidar kati na aikin jarida na, na hau mota na nufi wajen da lamarin ya fi qamari. A lokacin na tarar da jami’an tsaro jibge a unguwar, sannan na lura da wasu gidaje da aka qona, da kuma wasu daga cikin gidajen da akayi ma lambar shaidar cewa cikin dare ‘yan sara suka zasu qona su xaya bayan xaya. Tabbas za mu iya cewa, zuwan gwamnan tayi ma’ana, domin ba domin haka ba, da Allah kaxai yasan yawan gidajen za a qona su, domin kusan gaba xaya rabin unguwar sun tsere daga cikin gidajensu domin gudun abin da zai faru. A lokacin na sami zantawa da wani Matashi mai suna Abdullahi Xan kawo, wanda ya shaida min cewa, “ Sun shigo kawo ne domin xaukar fansa ne akan kashe xaya daga cikinsu da aka yi, wanda ake kira da Mai Kasa. Shi ne suka shigo kawo domin xaukar fansa kan mai uwa da wabi.”

Abdullahi ya qara da bayyana cewa,” Akan idona na naga an sari mutane masu yawan gaske, daga ciki har da wani Dattijo mai kusan shekaru 70, sannan akwai wani mai shayi wanda naga sun sare shi a kai, sannan sun qona shagonsa. Wancan gidan biredi da suka qona, hakan ya faru ne saboda ramuwar fansa domin su na maqwabtaka da xaya daga cikin gidajen ‘yan sara sukar wanda shi ma sun qona shi qurmus.” A cewar Abdullahi Xan kawo. A vangare xaya kuma, haka lamarin ya afku a Unguwar Barnawa dake Qaramar hukumar kaduna ta kudu, a inda Matasan ‘yan sara sukan, suka afkawa wani Matashi mai suna Sani Adamu, wanda shima sun yi nasarar sare masa hannu. GA yadda ya shaida ma wakilinmu kamar haka. “Ina kan hanyata na zuwa shago domin nayi aski, kawai sai naga ana ta gudu nima na ranta a na kare, nima nabi jama’a nayi ta gudu a cikin Unguwarmu ta Barnawa, duk da ina gudu ne amma ban san abin da ke faruwa ba, amma duk da haka ina gudu ina tambaya lafiya? Amma babu wanda ya

Ci gaba a shafi na

26


19

A Yau Litinin 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Adabi

Tare da Dakta Aliyu Ibrahim Qanqara 07030797630 imel: ibrahim@fudutsima.edu.ng

Zuwan Bahaushe Afirka Ta Yamma, Rayuwarsa Da Sana’o’insa (III) Har ya zuwa wannan waqati na qarni na 15 babu wuri ko kuxi na ciniki a wannan zamani sai dai abin da su ka kira ‘ba-ni-in-baka’, wanda Turawa ke ce ma trading by bata. Ma’anar haka shi ne su manoman sai su ba maqeran gero da dawa ko masara, da sauransu. Su kuma maqeran sai su mayar masu da abubuwan da su ka qera. Mahalba kuma sai su ba maqeran xan naman dabbobin da su ka halbo ko wasu abubuwan daban, su kuma su basu kayan halbin da su ka qera. Ko wannensu a cikin ukun ya dogara akan kowanne kan zaman sana’ar sa. A daidai lokacin kuma wannan wuri ya qara bunqasa, domin ana ma tunanin unguwar Ambuttai aka fara kafawa a cikin birnin Katsina, to daganan sai qananan sansani na kewaye da ita su ka tsira. Mahalba na sare itacen su na mayar da su itacen bindigogi. Maqera kuma, waxanda a sa’annan a ka fi kira da ‘yan tama su na saro itace su na qonawa, su na kuma amfani da garwashin wajen gasa qarafa. Cinikin tama fa ya gawurta. Duk wani yunquri na daidaita tarihin Katsina dole sai ya ci karo da ra’ayoyi mabanbanta, na daga bakunan waxanda aka samo labarun. Saidai wasu masana tarihi sun bayyana qarara cewa Barth da Palmer ba su bi diddiqin abinda aka bayyana masu ba, kuma shi kan shi Palmer, ya yada mafi yawancin wasu ra’ayoyi da suka ci karo da juna, ma’ana bai yarda da su ba. Bayan nan, tarihin Katsina ya zama maras yawa saboda masu bincike na farko-farko ba su yawaita binciken akan xabi’o’i da ciniki da kasuwanci da zamantakewar jama’a da har su ka sanya daular ta ci gaba ba, sai dai sun rinjaye akan neman tarihn sarakuna kurum. An riga an tabbatar da hakan. Wani binciken ya nuna cewa muhimmin tarihin da za a samu a Katsina ya fara daga mulkin sarki Korau, kuma ana tunanin a haqiqance ana iya cewa ya yi mulki a tsakiyar Qarni na 15. Abubuwan tarihin sarki Korau su ne wata wuqa ko takobi mai suna ‘gajere’ wadda da ita ne Korau xin ya yanka Sanau da kuma tukunyar qarfe. Haka ma an ce Korau ya na da wani takobi mai suna ‘bebe’ wanda aka qwace daga hannun Sarkin Gobir Yakubu cikin 1795 lokacin yaqin su da Katsinawa. Hatta gidan

sarkin Katsina sunan da aka raxa masa shi ne: ‘gidan Korau’. Sai kuma aka vullo da wata sara idan an naxa Sarki a Katsinar, sai a ce ‘shiga gidan Korau’ Wani kirarin da ke yi wa kowanne sarki na Katsina tun daga wancan lokaci zuwa yau shi ne da ake cewa: Korau Raqasa! Korau xan Korau! Korau jikan Korau! Korau magajin Korau! Raqasa magajin Raqasa! Korau abu gungurun! Korau mai tukunyar qarfe! Korau mayen Samri! Yanka mashidi baqon Sanau! A wasu littattafai an bayyana cewa Korau shi ya fara musuluntar da mutanen Katsina. A wasu kuma an bayyana cewa a lokacin mulkin sa ne aka fara bayyanar da musulunci. A farkon Qarni na 15 jama’a sun fara yaxuwa gari ya kafu har ma ya fara bunqasa. Daga cikin waxannan wurare akwai Durvi-ta-kusheyi ita kanta, da ‘Yanxaka da Birnin Samru da kuma Karofi. Sauran wuraren da fatake ke tsayawa su yada zango da ‘yan mazaunun jama’a da ke gab da birnin Katsina kuma sai cikin lokaci qanqani su ka haxe da Katsinar. Akwai ma wasu wuraren da a yanzu babu su da ke daga gabashin Katsinar, kamar su Dutsin Bamle da birnin Mamman. Tun a daidai lokutan

kuma aka fara naxa masu unguwanni ko masu gari da ke kula da sha’anonin mulki. Akwai kuma masu kula da wuraren bauta, kamar inda ake bautar iskoki da sauran su, kamar su Badawa da Ambuttai. Kafin zuwan zamanin sarki Korau akwai kuma masu kula da sha’anin karofi ko wuraren rini. Akwai kuma magajiyar bori ko mai shugabantar masu bori da masu shugabantar farauta da sarakunan kawunan maqeru. To waxannan su ne ke kula da mulkin mutanen da ke waxannan wurare. A wannan lokaci sana’ar Bahaushe ita ta daxa sanyashi ya shahara matuqa. Cikin waxannan sana’o’I akwai noma da kiwo da fatauci da qira da jima da saqa da rini da dukanci da sassaqa da wanzanci da fawa da xori, to sai kuma sana’o’in mata. Wasu sana’o’in mata sun haxa da saqa da kaxi da yin kitso dad a sauransu. Banda masarautar Katsina, masarautun da ke da qarfi a wannan lokaci na yankin Bilad as Sudan sun haxa da na Kano, Barno, Shongai da Kebbi. Anan, ci gaba na samuwa da sauri na sha’anin sarauta da tattalin arziki. Kai, daga qarshen qarni na 15 da farkon qarni na 16 sarakunan su sun zama masu qarfi da iko, su ne: sarkin Kano

Muhammadu Rumfa (14631499) da Kanta na Kebbi (1513) da Mai Ali Ghazi na Borno (1470-1503) da kuma Askiya Muhammadu Toure na Shongai (1493-1528) Babban batun da ya fi xaukar hankalin masu sarauta da talakawa a lokacin shi ne zancen addinin islama da kuma bautar iskoki da gumakka. Ana cikin wannan yanayi sai ga wani babban malami da ake kyautata zaton ma waliyyi ne, ana ce da shi Sheikh Abu Abdallah Muhammad bin Abd alKarim bin Muhammad al-Maghil wanda ya iso cikin birnin Katsina a shekara ta 1490 wanda kai tsaye da ya zo wa’azi ya yi ta yi, na zuwa ga addinin Allah (SWA) Wasiqar da ya rubuta ma Sarkin Kano Muhammadu Rumfa (1463-1499) mai taken Taj al-din fima yajib ala-l muluk ita ya aiko ma Sarkin Katsina, na ya na ba shi shawara ya sa ido sosai akan masu gudanar da mulkin sa ko masu gari, ya tabbatas da gaskiya ya kuma tabbatas komi an yi shi akan yanda addinin islama ya shimfixa. A cikin takardar, ya ce a tilasta ma kowa ya rungumi addinin musulunci. Ya kuma tsara ma gwamnatin sarki yanda za a amshi zakka da yanda za a bada ta ga mabuqata. Shi kuma ya tsara masu yanda za su gudanar da mulki kamar yanda ya zo a Alqur’ani mai tsarki da Hadisin Manzon Allah (SAW)


A Yau Alhamis 5.4.2018

20

CINIKI

Kasuwanci MASANA’ANTU

INSHORA

HANNUN JARI

KASUWAR SHINKU

Yadda Ake Cin Kasuwar Wayoyin Da Aka Sato Daga Ingila –Rahoto Daga Umar A Hunkuyi

Wasu gaggan varayin qasarnan suna samun milyoyin kuxi daga wayoyin hannun da zaunannun varayin Ingila suka sato suka shigo da su kasuwannin qasarnan. Wayoyin salula na hannu da ake fisgewa daga hannun matafiya a qasar Ingila, sune ake tallata su a matsayin ‘Sakan hand’ musamman a kasuwannin Legas, ana sayar da su a farashi mai sauqin gaske. Nijeriya ba ta sanya hannu kan dokar kasuwanci ta duniya ba, wacce ta haramta yin kasuwancin satattun wayoyin, don haka ne qungiyoyin varayin suke ci gaba da shigowa da dubannin wayoyin ga manyan varayin dilolin na su da ke cikin qasarnan. Wayoyin da ake satowan, varayin sukan yi qoqarin kwashe bayanan da ke cikin su ne da zaran sun sace su, inda sukan yi qoqarin kutsawa cikin ajiyar Bankunan masu wayoyin domin su yi ma su sata. Bayan nan ne sai su yi gwanjon su ga varayin zaunen da ke can, waxanda su kuma suke tura su gabashin Turai, inda wasu qwararrun varayin ke satan bayanan masu wayoyin. Bayan sun gama komai, ne sai su sayar wa da dilolin varayin da ke nan Nijeriya da Aljeriya da kuma indiya. Wani bincike ya nu na, wayar iPhone da aka sato daga Ingila ana sayar da ita a Legas da kewayen Ikeja, kan Fam 560. Wani kanti ma yana sayar da wayar iPhone 6 da aka sato daga Ingila kan Fam 230. Xan Majalisar Jam’iyyar, Conservative’ ta Ingila, ya shaidawa manema labarai cewa, “Gaskiya ne, lamarin da tsoratarwa a ji cewa, hareharen ta’addanci da ake kaiwa a nan Ingila, ana amfani da su ne wajen azurta ‘yan kasuwan bayan fage a wasu sassan duniya.” Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Legas ya ce,

shi ba shi da labarin ana sayar da satattun wayoyin na Ingila a Legas. Wani bayanin da aka gabatar a farkon wannan shekarar, ya nu na yadda varayin ke bugun qirji suna shaidawa wakilin gidan yaxa labarai na BBC, yadda suke sato wayoyi, kwamfutocin Ipad da jakunkuna na dubban famafaman na Ingila, da kuma yadda suke yin fisgi ka ruga, na ababen adon mata na wuya da na hannu a kan titunan biranen qasar ta Ingila. Xaya daga cikin ‘yan qungiyar varayin da ke sanye da fuska biyu, mai shekaru 21 da aka fi sani da Mista X, yana ta burga kan yadda yake iya fisgan wayoyi masu tsada guda uku a cikin sakan 20, inda yake kwatanta sauqin satan wayoyin da, ‘fisge alawa daga hannun jarirai.’ Mista X, wanda ya qware wajen fisgan wayoyin, ya yi iqirarin yana zaune ne a birnin Islington, da ke can Arewacin birnin na London, ya yi burgan ya saci xaruruwan wayoyin a cikin shekaru bakwai da suka shuxe. A cikin bayanin, Mista X, ya kai wa wani varawon zaune abokin burmin sa, wayoyi masu tsada guda huxu, wanda

shi kuma ya saye su a hannun sa tsakanin Fam 70 zuwa Fam 250 kowannen su. Shi kuma nan take ya aike da su Nijeriya, inda ya sayar da su da tsada a can. A shekarar 2016 kaxai, an sami rahotannin satar wayoyin hannun har sau 446,000. A birnin London kaxai, an yi satan wayoyi da kuma fashi da makami har sau 60,000, yawancin wayoyin kuma samfurin iPhone ne. A cikin watanni 12 zuwa watan Yuni 2017, Jami’an ‘yan sanda a yankin Scotland, sun karvi rahotannin aikata laifukan da suka shafi satar wayoyin ninki uku da rahotannin da suka samu a daidai wannan lokacin a 2016. Mafiya yawan wayoyin, zauna gari banzan varayin sun sace su ne ta hanyar yin amfani da ruwan acid, Takubba, adduna da makamantan su a kan masu tafiya a kan hanya. An sami rahotannin satan Babura 23,000, a birnin London kaxai a shekarar da ta shige, kusan a miqidarin satan guda 63 kenan a kowace rana. Aikata laifukan sun qaru sosai da kashi 2,100, a babban titin kasuwancin

nan, Oxford, na cikin birnin na London. A watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, Jami’an tsaron na, Met, sun qaddamar da wani mashin mai xan karen gudu da kuma na’urorin hangen masu aikata laifuka a tattare da shi, domin ganowa da kuma bin sawun masu laifi. Hakanan an qaddamar da hodar da ake fesawa domin gano qwayoyin halittan masu laifi da kuma na’u’rorin nan na ‘stinger’ domin gano masu aikata laifukan. Sabbin mashinan na BMW da aka qaddamar, suna iya bin masu laifin cikin kowane irin lungu da kwararo. Mashinan na, ‘stinger,’ da ba su wuce a sanya su a cikin jaka ba, suna da tayoyi ne kamar na Vespa, ana kuma iya yin amfani da su wajen toshe hanyoyi biyu da za a iya bi a tsere a lokaci guda. Wannan hodar mai ban al’ajabi wacce ake fesawa domin gano masu laifin, idan aka haska ta a qarqashin hasken nan na UV, tana iya nu na alamun masu laifin ko da kuwa an yi makwanni da yawa da aikata laifin a wajen. An gwada ta sau da yawa wajen gano masu laifin.


KASUWANCI 21

A Yau Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Naira Ta Xan Qara Faxuwa A Kan Dala A Kasuwar Bayan Fage Daga Umar A Hunkuyi

A ranar Talata, Naira ta xan faxi qasa a kan dala a kasuwar bayan fage, inda aka riqa canza ta kan Naira 361.20, a kan kowace dala guda. Kamfanin dillancin labarai na qasa, ya kawo rahoton kuxin na Nijeriya ya rasa qimarsa da kwabo 20 kan yanda aka riqa canza shi a 361 kan dala guda kafin a ta fi hutun Easter. Hakanan an canji Naira kan 508 da 444 , da Fam xin Ingila da kuma Yuro bi-dabi. A wajen ‘yan kasuwan canji, an sayar da Naira 362 kan kowace dala guda, ya yin da aka riqa sayar da ita 508 da kuma 444 kan Fam xin Ingila da kuma takardan kuxi na Yuro. An sayar da Nairan ta Nijeriya a wajen masu zuba jari kan 361.35 kan dala guda, sa’ilin da masu cinikin tsakanin Bankuna suka

sayar da ita kan 305.65 kan dalar guda. ‘Yan kasuwar kuxaxen sun nu na damuwar su kan yiwuwar samun xan wani canji kan yadda Babban Bankin qasa, CBN, ke tafiyar da wani taro kan kuxaxen, da

a yanzun haka yake gudana a Abuja. Kamfanin dillancin labarai na qasa, NAN, ya kawo rahoton taron a karo na farko da Babban Bankin ya shirya kan kuxaxen, wanda kuma aka fara yin sa

ranar Talata, za a kammala shi ne a ranar Laraba. Sai dai Nairan tana nan inda take a kasuwar canji ta waje, kan yadda Babban Bankin na qasa ya tsayu wajen ganin havakan kasuwar tamu ta waje.

Gwamnatin Tarayya Ta Buqaci Qasashen Haxakar “Niger Basin” Su Bayar Da Gudummawarsu Daga Bello Hamza

Gwamnatin tarayya ta buqaci manbobin haxakar “Niger Basin Authority” su biya kuxaxen gudummawarsu na gudanarwa domin samun cikakken ci gaba a yankin dake mutane fiye da miliyan 130. Gwamnatin tarayya ta qara da cewa, ci gaba da buqasa yankin Niger Basin ba zai samu ba said a cikkaken kuxaxe rashinsa kuma yana sa rayuwar miliyoyin mazauna yankin cikin garari. Hukumar NBA wani haxakar gwamnatotoci ne a yankin Afrika ta yamma dake da burin sarrafa albarkatun dake a jibge a yanki da cikin kogin Neja. Qasashen 9 ne suka haxu auka kafa qungiyar, sun kuma haxa da qasar Benin da Burkina Faso da Mali da Cameroon da Nijar da Nijeriya da Chad da Guinea da kuma Cote

d’Ivoire. Da yake bayani a madadin gwamnatin Nijeriya a taron hukumar na 36 da minitocin ruwa na qasashen suka gudanar a Abuja. Ministan ruwa na Nijeriya Suleiman Adamu, ya lura da cewa, canjn yanayi ya kawo babban matsala ga harkoki masu yawa a yankin. Ya ce, “Baza mu iya cikakken magana a kan ci gaban tafkin na gofin Neja ba ba tare da bayar da gudummawar kuxi a kan lokaci ba domin gudanar da aiyukan ci gaban al’umma kamar yadda ya kamata. Rashin biyan kuxaxen gudummawar da kuma vata lokaci wajen biyan kuxaxen sun a daga cikin manyan matsalolin dake hana ruwa gudu a qoqarin tafiyar da hukumar” “Dole mu qarfafa wa kwararru masu gudanar da aiyuka ta hanyar

bayar da kuxaxen dake a kanmu, rayuwar jama’ar mu ya dogara ga wannan gudummawa namu” Suleiman dai ya samu wakilcin babban sakatare ne a ma’aikatar ruwa mai suna Alhaji Musa Ibrahim, ya kuma bayana wa mahalarta taron cewa, “Yankin Niger Basin nada yalwataccen arziqi a kwai kuma mutum fiye da Miliyan 130 a yankin ammam arziqin da ake da shi a yankin na fuskantar barazana masu yawa” A nasa jawabin, shugaban hukumar ta Paul Adalikwu, ya yabawa Nijeriya a bisa qoqarinta na taimakawa harkokin ci gaba a yankin iyaka, ya kuma lura cewa Nijeriya ta xauki harkokin zamantakewa a yankin iyakokin qasar nan da matuqar mahimmanci. Ya kuka lura da cewa, yankin kogin Neja ba kawai yana da

mahimmanci ga Nijeriya ne kawai, yana kuma da mahimmanci ga saura manbobin qungiyar wajen dogaro da shi wajen tafiyar da rayuwarsu. Adalikwu ya ce, abin takaici ne a karon farko tun shekarae 185 vangaren kogin Neja na Niamey, a jamhoriyyar Nijar ya qafe baki xaya saboda canjin yanayi dake fuskantar duniya. Babban sakataren NBA, Abderahim Hamid, ya bayyana rashin jin daxinsa ne game da qafewar da kogin na Neja ke ci gaba da yi saboda dalillan canjin yanayi. Ya ce, qarfafa haxin kai tsakanin manbobin hukumar da bayar da gudummawar kuxi a lokacin daya dace shi ne zai tabbatar da ingantuwar rayuwar mutane yankin saboda za a samu hanyar sarrafa rowan kogin domin taimakawa jama’a.


22

Kiwon Lafiya

A Yau Alhamis 5.4.2018

Babban Dalilin Da Zai Sa A Halasta Amfani Da Wiwi Daga Idris Aliyu Daudawa

Masana a qasar Amurka sun samu babban dalilin da zai sa su bari a riqa shan tabar wiwi,sun ci gaba da bayanin cewar tana taimakawa Amurkawa, waxanda suke qoqarin, suka saba da shan opioid, da hakan kuma suke ganin rage wa masu cutar opioid. Kmar yadda wani nazari ya nuna a wata mujalla da ake kira JAMA Intrnational Medicine, ya nuna an samu raguwar shan maganin opioids da milyan 2.11 ko wace shekara, wannan kuma ya nuna, ana samun a qalla daga milyan 23.08 kullun na maganin da ake sha, duk shekara, lokacin da aka amince tabar wiwi a matsayin magani. ‘’Wannan ya nuna ke nan bada dama ta amfani da wiwi saboda

samun lafiya, zai sa a riqa samun qaramin bayani, akan amfani da opiod, zai rage cutarwar akan matsalolin da ake fuskanta na opiod’’ An bayyana cewar al’amarin yana qarfi sosai a jihohin da suka yadda da dokar. Binciken ya nuna yan maganin da ake bisa bayanai na qwararru tsakanin shekarun 2010 da kuma 2015, a qarqashin Medicare Part D, shi zavin da aka bada na bayanai akan maganin da kuma, fa’idar abin zai shafi Amurkawa milyan 42. Yadda ake bayanai akan shan opiod a Amurka ya qaru a cikin shekaru goma sha biyar da suka wuce, kamar yadda masu bayanai akan magana suka bayyana, cewar shi opoid na maganin ciwon, da ya tsanatada kuma

wanda bai kai hakan ba. ‘’Mace mace akan amafani da opiod abinya qarui daga 14,910 a shekarar 2005 zuwa 33,091 a shekarar 2015.’’ ‘’Tsakanin shekar 2000 zuwa 2015 mace macen asanadiyar opiod abin ya qaru da kashi 320’’. Nazarin a sandiyar

binciken ya nuna a kai wata gardamar da ka yi, wadda ta goyi bayan al’amarin maganin daya shafi, cannabis, a matsayin wani tsari na qasa, za ayi amfani da abin domin, hakan ya zama dalilin hana bayanai akan shan opiod. Kusan jihohi 30 ne

suka amince da amfani da marijuana a matsayin magani, don haka jihohi tuni sukaamince ma amfani da tabar wiwi. Amma kuma akwai wasu jihohi da suke ganin amfani da wiwi kamar amfani ne da wasu muggan qwayoyi, kamar su heroin.

Kungiyar KMC Karkashin Mamaye Za Ta Aikin Wayar Da Kan Jama’a Game Da Kiwon Lafiya Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Qungiyar gamayyar qungiyoyin kiwon lafiya da na ‘yan jaridu wanda qungiyar mamaye Evidence for Action ta qaddamar kwanakin baya, za ta fara aikin wayar da kan jama’a a asibitocin yankunana karkara da biranen Jihar Bauchi don ganin an samu nasara kan aikin da qungiyar ta sa a gaba wajen inganta lafiyar mata da qananan yara a jihar Bauchi. Shugaban kwamitin ilmantarwa kan inganta harkokin kiwon lafiyar mata da qananan yara na qungiyar mamaye da aka qaddamar a kwanakin bayar Alhaji Ladan Isa Dalhatu, shine ya bayyana haka cikin ganawar sa da manema labarai a kwanakin baya, inda ya bayyana cewa aikin da aka xora masa

yana da muhimmancin gaske wajen ganin an duqufa don shiga yankunan karkara a ilmantar da mutane don su riqa halartar asibiti a kan lokaci da kuma kai yara ana musu alluran rigakafi yadda ya dace. Don haka ya bayyana cewa wannan qungiya da aka qaddamar wacce ta qunshi ‘yan jarida da ma’aikatan asibiti da shugabannin qungiyoyi masu ruwa da tsaki kan harkokin kiwon lafiya za su ci gaba da aiki tare kamar yadda aka saba don ganin an samun ingancin kiwon lafiya fiye da halin da ake ciki a yanzu. Don haka ya yaba wa jami’in qungiyar Mamaye Evidence for Action Mista Laide Shokunbi, wanda ya qaddamar da qungiyar a gidan Mahwun da ke Bauchi game da irin agajin da Mamaye ke yi

•Alhaji Isah Ladan

game da kiwon lafiya a jihar Bauchi. Don haka ya ja hankalin qungiyar da cewa a shirye dukkan waxanda aka zava suke wajen sun yi aiki don taimakawa kiwon lafiyar mata da qananan yara. bayan haka kuma Ladan Dalhatu ya bayyana cewa qungiyar za ta fara gagarumin aikin jan hankalin gwamnatin Jihar Bauchi wajen ganin ta xauki ma’aikatan asibiti, saboda a ahalin yanzu yawancin asibitocin jihar Bauchi babu wadatattaun ma’aikata sai masu tallafawa da suka fito daga makarantun kiwon lafiya basu da aiki suke agazawa abin da ake qira volontiya, don haka ya ce ya zamo wajibi a tashi tsaye don ganin gwamnati ta zauki ma’aikata don gudanar da ayyukan kiwon lafiyar jama’ar jihar Bauchi.


KIWON LAFIYA

A Yau Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Hattara! Shan Magungunan Da Ke Qara Girman Nono Na Da Hatsari Daga Idris Aliyu Daudawa

Akan wasu dalilai mata suna bada muhimmanci ga nononsu da xuwaiwai ba kawai domin su kaxaiu ne suka fi muhimmanci daga cikin sassan jikin mutum ba, amma sai saboda waxannan abubuwan biyu, sune suka fi jan ra’ayin maza. Koda yake watakila ko don saboda wasu dalilai, suna yin haka ne domin su burge ko kuma, ko kuma suna yin amfani da hanyoyi daban daban saboda su sa su waxannan wuraren biyu, su kasance cikin girma koda yaushe, maganar neman nono ya girma, ko kuma xuwaiwai. Ga matasa idan sun kasance haka toabin ya yi daidai, yayi da kuma ga wasu matan aure, idan waxannan wuraren suka kasance da girma, zai ba mazajensu sha’awar su kasance dasu, musamman ma wasu maza ire iren waxannan wuraren ne suka jan ra’ayinsu. Koda yake dai da akwai waxanda saboda nononsu bai yi girma ba, kamar yadda wani rahoto ya bayyana, amma wannan ba mai rinjaye bane. Amma wasu na samun damar mai da waxannan sassa nasu su girma cikin sa’a, wasu suna yin hakan ne ta hanyar tiyata, wasu kuma ta hanyar shan qwayoyi, amma kuma masana sun ja kunen masu yin hakan,saboda akwai haxari, wajen qoqarin da wasu ke yi na amfani da wuqa domin a qara masu girman nono , ko kuma xuwaiwai. Maganar gaskiya koda yaushe irin waxannan mutanen ana buqatar da su sa hannu a wata takarda mai nuna an yarda, su kuma amince cewar da akwai matsala, tattare da yin tiyatar da suke son ayi masu, wani abu kuma yana iya faruwa. Magana akan nono da farko, baya ga kuxaxe masu yawa da ake kashewa, wasu bincike bincike da ake yi, ya nuna cewar da akwai matsala wacce ake samu bayan an yi ita tiyarar, dalilin haka kuma ana iya samun yin wata tiyatar ta biyu, domin a samu gyara matsalar da aka samu. Akwai hanyoyi biyiu da ake amfani dasu wajen qara girman nono, sun kuma haxa da saline( wand aka sama saline ko kuma ruwan gishiri da kuma wani abin tiyata) da silicone wani sinadari wanda shi maan sa mashi( silicone sell). Amma kuma kamar yadda Farfesan al’amarin tiyata a Jami’ar North western Feinberg sashen makarantar koyon harhaxa magunguna

a Chicago, Laurie Casas, ya bayyana cewar dukkan saline da kuma silicone, wato hanyoyin da ake qara girman nono, basu kaiwa wani lokaci mai tsawo. Saboda wani aikin yana iya buxewa, ko kuma su lalace gaba xaya, sai an canza. ‘’Marasa lafiya ya kamata su fuskanci gaskiya saboda babu abin da yake daxewa har abada’’. Ta bayyanawa WebMD wanda ke samar sahihan labarai na al’amuran da suka shafi harkar lafiya. Wata kuma babbar matsala ita ce yayin da aka yi wannan aikin qari saboda nono ya qara girma, akwai wata cutar Kansa wadda ake kira anaplastic large cell lymphoma. Hukumar kula da abinci, lokacin da suke fitar da wani saqon jan kunne, a shekarar 2017 sun bayyana cewar, ita cutar kansar sanadiyar qarin da aka yi ma nono saboda ya qara girma, ta kashe mata tara tuni, ba tare da la’akarin ko salin bane ko kum silicone. ‘’Dai dai ta 1 ga watan Fabrairu na 2017 FDA ta amshi wasu na’urori 30 waxanda na ala’amarin da ya shafi lafiya ne, akan rahoton waxanda aka qara ma girman mama, ALCL an samu mutuwa 9, dalilin hkan sai ita FDA ta bayyana cewar ya kamata, su masu son a qarawa nononsu girma ta tiyata. Su nemi shawara kafin su yanke shawarar yin hakan. Da take ba mata waxanda suke da niyyar ayi masu aiki domin qara girma shawara Hukumar lafiya ta duniya, ta bayyana cewar ita cutar kansar ta kan xauki shekareu goma, kafi ta kai ga bayyana. Ta qara bayanin cewar kafin ta bayyana kanta, kuma ita kansar ta kan nuna kamaruwar wani abu ne da ake kira, seroma fluid tsakanin abin da aka dasa wa mace a nononta ko kuma kewayen shi. Har ila yauidan aka gano cutar da maganin ta da wuri, na xaukar matakin cire shi qarin da aka yi, shi ne babbar hanyar samun sauqi. ‘’Ko ma menene mata waxanda aka qara masu girman nono ta hanyar tiyata, suna iya kamuwa da cutar kansa ALCL, idan aka haxa da mata waxanda basu qara wa kansu girman nono ba, hadai su ‘’. Dukkan bayanai da suka haxa da yau sunan da muhimmanci, saboda ya nuna cewar mata waxanda suka, qarawa kansu girman nono ta hanyar tiyata, sun fi duk sauran mata yiyuwar kamuwa da kansa, fiye da mata waxanda ba ruwansu da yin hakan.’’ Wani qarin bayani shi ne

ita FDA ta bayyana a kafar sanarwar ta , cewar, alamun kmuwa da cutar kansa , sun haxa da, jin zafi akan nono, canjin wurin, wato da shi nipple, da kuma yadda shi nonon zai riqa yin wani zaf. Sauran matsalolin da kae fuskanta kamar yadda FDA suka bayyana, sun haxa damaganar gaskiya duk da yake wasu suna shayarwa, duk da yake an masu qarin nonon, waxansu ba zasu iya shayarwar ba, saboda su sinadaran da suke kawo ruwan nonon, ana iya rasa su lokacin da ake yin tiyatar. Amma kuma har yanzu ba a tabbatar da watakila ko wasu ‘yan sinadaran silicone, sun wuce ta wani qoqo, zuwa ruwan nono lokacin da ake shayarwa, wannan kuma yana iya kawo ma jariri matsala. Sauran matsalolin sun haxa da quraje da zasu riqa fitowa kusa da nono, sai kuma matsar da silicone, wannan kuma, saboda matsalar da ake fuskanta, bayan nan kuma akwai matsalar rashin lafiya, wadda zata biyo bayan yin ita tiyatar, ta wannan hali kuma zai iya sawa a cire qarin da aka yi. Wurin bazai iya warkewa cikin lokaci ba,saboda fitowar saltwater wanda ke cikin haxin saline, qirgi ko kuma ko kuma wajen haqarqari, wurin zai samu matsala, fata kusa da nono zata fara yin tattarewa, shi kuma nonon zai ragu, wannan kuma yana nuna dole ne sai an yi wata sabuwar tiyatar, saboda a kauce ma shiga babban bala’i.

‘’Yawancin canje canjen da ake samu a nono, bayan an yi tiyatar, idana bin ya xauki lokaci mai tsawo, za a iya samun matsal’’. Wata mata dake zaune a Birmingham mai suna Dennis Lees wadda aka tava yi ma qarin saboda son girman mama, ta kusa rasa rayuwarta a shekarar 2016, ta biya fam dubu biyu da xari uku da saba’in da biyar, lokacin da aka yi mata tiyata ta farko. A rahoton wanda UK Metro ta bayyana cewar al’amarin ya faru ne, ‘yan kwanaki bayan a yi mata tiyata a Belgium, lees tace wata Nurse ta bayyana mata, da ta mutu cikin wannan daren, idan da ta koma asibiti, bayan da ta ji wani ciwo a nononta na hagu, bayan an yi mata tiyata ta biyu. Bayan data masu matsaloli waxanda suke da dangantaka da tiyata, cibiyar bincike akan cutar kansa, a haxaxxiyar daular Turawa, da cewar a daina mafani da da qwayoyi domin samun wani kuzari. ‘’Saboda bamu san wasu bayanai ba dangane da gamsassun ala’amura ba, dangane da sahihancin, magungunan rage zafin ciwo sanadiyar qarin girman mama ba, amma mun bada shawarar kada a yi amfani dasu’’. Ta kuma ja kunnen mata waxanda suke da cutar kansa kada suyi amfani da magungunan, suna qara cewar, magungunan suna iya kawo cikas saboda,. Maganin da ake sha saboda kansa.

23


24

TALLA

A Yau Litinin 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)


25

A Yau Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Kimiyya

Dala Miliyan 500

ne adadin kuxi Nijeriya ke kashewa duk shekara waurin safarar xanyen man fetur da wasu sinadaran da ake amfani da su a sashen sinadarari da magunguna

Yadda Ake Goge Saqonnin Da Aka Aika A Kafar ‘WhatsApp’ Daga Idris Aliyu Daudawa

Ba wani abin mamaki bane wani lokaci akan aika saqo ga mutumin da bai kamata ba, har ma wani lokaci akan yi dana sani, ba ma kamar idan saqon ya nuna ya isa, mutum zai qoqarin hakan , amma ba zai yiyu ba, sai daikuma duk hakan yanzu abin ya zama labari. Ana iya cewa ya zama labari saboda shi kamfanin WhatsApp ya samo wata hanyar da zata arkar da ita matsalar, da kumazata bada damar mutum ya goge saqon daga mallakar mutum, da kuma hirarraki na qungiyar abokai. Abin sau da yawa yana ba mutane matsala, ta yadda za a goige saqo ta ta vangarn mutum na hirar WhasAPP , amma kumaka kasa yin hakan,a vangaren na mutane, alal misali maganar wasu kurakurai na rubuta kalmomi, ko kuma yakasance wasu sun samu damar karanta shi. Sai a bi wasu dokoki nan qasa saboda za akoya yadda za ‘a goge saqokaitsaye daga WhatsApps, ba tare da sai an yi wani aiki mai wuya ba, amma kuma duk da haka akwai wasu muhimman abubuwa da suka kamata a sani, tun daga farko. Duk hanyoyin xaya ne ba wani bambanci, koda kuwa mutum yana da iOS, Windows, ko kuma Android, amma kuma akwai ‘yan abubuwa kaxan da ba a son a zarce su wato a wuce yadda aka ce ayi amfani dasu. Dukkan wand aka aikawa saqo ba lalle bane,dole ya kasance tya mallaki waya wadda bata daxe da shigowa ba, saboda yin Whats App ko kuma shi wani samfuri na shi, idan akwai wani a group xinku wato qungiya ke nan ta hira, wanda baikai samun sabon

samfuri na Application na WhatsApp ba, abibin zai yi wuya a goge shi wancan saqon. Hakanan shi WhatsApp ba zai sanar da mutum ba, idan buqatar gogewar bata samu dama ba, don haka sai mutum ya yi fatar abokn shiko kuma iyalan shi, suna da sabon samfurin na Application na WhatsApp ba. Yadda Mutum Zai Gane Idan Yayi Ma Waya Mugun Sabo Waxannan qa’idoji ba zasu hana mutane ganinsaqon mutum ba kafi ya kai ga goge shi, ya dace mutum yayi tunanin haka a zuciyar shi, cewar watakila ma wani ya riga ya ga shi saqon, kafin ya kai ga goge shi.

Ya dace mutum ya tuna yana mintuna bakwai ne ya goge saqon da ya aika, kafin ya manta ya bar shi . WhatsApp ya ware minti bakwai shi ne ya fi dacewa, a ba mutum domin goge saqonni, don haka da akwai buqatar a lura da waxannan shawarwari, idan mutum yana saongoge wani saqo. Idan mutum yana son goge saqo sai ya fara daga wurin da jka farao ita hirar, don ya san saqon da yake sonya goge. Idan mutum na buqatar xan tsayawa akan wani saqo mutium kuma ya tava alamar (Delete) alamar gogewa, daga cikin abubuwan da zai zava, to akwai zavi na goge ba duka saqonnin ba.

Amma dai da zarar mutum ya danna alamar da take nuna a goge akan ko wanne, wannan yana nufinduk wanda yake cikin wannan hirar ba zai kai ga ganin saqon ba. Daga nan kumamutum zai samu saqo mai nuna ma shi cewar ‘’This message was deleted’’ ‘’An goge wannan saqon, don haka da akwai yiyuwar za a iya tambayar mutum ga wanda aka yi niyyar saqon ya kai ga wurin shi, ya san abin da shi saqon ya qunsa. Wannan kuma yna nufin ko maganar goge shi saqon ya samu matsala daga cikin WhasAPP, amma kuma duk da haka yana da qyau, mutum ya riqa yin haka a matsayin wata makama.

Kamfanin Apple Ya Qaddamar Da Sabuwar Ipad Apple Daga Idris Aliyu Daudawa

Kanfanin Apple ya qaddamar da sabuwar wayar Ipad mai tsawon fiye da inch tara (9.7 inch), a wani taron da ya shafi harkar ilmi, ranar Talata a birnin Chicago. Ita sabuwar wayar Ipad xin ta qunshi, abin tavawa IDcompatible da kuma home button, tare da har ma taimako na Apple Pencil, wanda na kamafanin ne yayi domin taimakawa wanda zai amfani da shi. Sabuwar wayarzata fito da 8megafixel wata camera ta xaukar hoto, wadda kuma zata xauki hoton bidiyo 1080 tare kuma da HD camera ta gaba, wadda zata iya yin har awa goma da cajin farko da kuma tainako na LTE. Tana da gig 32 wanda za a riqa aje wasu abubuwa, bugu da qari kuma tana samun qarin agaji daga Apples’s A10 Fushing chip wanda zai

yi aiki kamar ya dace. Apple tana sayar da sabuwar Ipad xin akan ko wace xaya Dala 329 wannan kuma ya danganta ne akan ko wace iri ce mutum yake so, amma makarantu zasu iya samu akan Dala 229, da kuma fiye da hakan. ‘Yanmakaranta zasu samu gig 200 mai free iCloud na ajiye abubuwa, da farko dai wurin ajiyar bai wuce gig 5 ba. Kamfanin Apple ba ya haxa da Pencil xinta ba, wanda ake sayarwa Dala 99 tare da ita wayar, amma duk da haka shi kamfanin ya xan nuna yadda kayayyakin nata suke saboda masu sha’awar saye, da suka haxa da Logitech Dala 49 da ake kira Crayon. Har ila yau kamfanin ya bada sanarwar sababbin applications nata ita wayar Ipad , da suka haxa da shafuka da kuma keynote, sai kuma taimakawa shi Fensirin, su

applications xin zasu iya alaqa da Ipad a qyauta, sai kuma ita Apple akwai wasu abubuwan da zasu taimaka su yi ingantaccen aiki, a aji wannan kuma ya haxa da, qwazon malamai su lura da ayyukan xalibansu. Bugu da qari kuma Kamfanin na Apple ya qaddamar da wani application da ake kira Schoolaork wato ‘Aikin makaranta’ wanda za a iya mafani da shi fasahar sadarwa ta zamani, na ayyukan aji waxanda malamai ke badawa. Shi wannan application za a same shi cikin watan Yuni ne, zai kuma yi aiki ne kafaxa da kafaxa dawani application da ake kira ClassKit, wannan kuma zai taimakawa malamai ne wajen bayar da ayyuka ta hanyar applications masu yawa. Dukkan waxannan an yi su ne saboda ita sabuwar wayar xin a mayar da ita wadda zata kasance,

wadda za ayi ta rubibinta, a vangaren ilmi wurin da Google, ya daxe yana ta cin Karen shi babu ko babbaka,ya kuma kasance shugaba, saboda yana da wani application na littattafai da ake kira Chromebooks . Shugabannin kamfanin Apple sun xan yi Google habaici lokacin da suke qaddamar da sabuwar ayar Ipad ranar Talata, inda suka ce da akwai applications da waya ( manufa wasu hanyoyi da ake bi domin samun damar yin aiki da wani abu) a wayar Ipad fiye dana Chromebooks, wanda wannan kuma ya danganta ne akan akan applications waxanda suka dogara ne akan wayar gizo (internet). Yanzu Apple tana da applications 200,000 waxanda za a riqa amfani dasu domin vangaren ilmi da kuma tuntuva saboda neman wasu bayanai, a wata ma’ajiya ta application kamar dai yadda kamfanin ya bayyana hakan ranar Talata ta wannan mako.


A Yau

Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

RAHOTON MUSAMMAN 26

Sara Suka A Kaduna: Laifin Gwamnanti Ko Na Jami’an Tsaro Ci gaba daga shafi na

18

amsa min sai daga can gefe wani ya yi qarfin hali ya amsa min da cewa ‘yan Shara ne kayi ta Kanka.” Sani ya qara da cewa, “Ban yi aune ba kawai sai naga wani Matashi ta gabana ya kawo mun Sara kici-kici, muka kama kokuwa ni da shi ina qoqarin qwatar kaina, amma a qarshe suka yi mun yawa sukaci qarfi na har suka sare mun hannu.” A cewarsa, “Ina kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna, da ta kawo qarshen waxannan ‘yan ta’addan da ake kira da suna ‘yan Shara, idan kuma har sunfi qarfin gwamnati ne to, ina kira ga jami’a da mu tashi mu kare kanmu da kanmu, domin banason abin da ya faru da ni, ya sake faruwa da wani na.” Inji Sani Adamu, wanda ya haxu da iftila’in ‘yan sara suka. Haka kuma lamarin ya afku da wani Tsohon Soja mai suna Sani Suleiman, dake zaune a Unguwar Kwaru cikin Garin kaduna. Shi ma ya gamu da illar ‘Yan sara suka inda suka tsinke masa hannu baki xaya. Kamar yadda Sani Suleiman ya shaidawa wakilinmu lokacin da ya ziyarci shi a Asibitin Gwamnati na Barau Dikko dake kaduna. Ya shaida

masa cewa a Daren ranar Asabar da ta gabata ne lamarin ya faru da shi. A inda ya qara da bayyana cewa, “Ranar Asabar da ta gabata ne na fito Gida da misalin qarfe 8:30 na dare zan yi siyayya a shago domin Iyalina muyi amfani da shi idan Gari ya waye, sai kawai naga zugar waxannan Yara sun Kai a qalla su 50, nan take suka yi kai na ban san hawa ba balantana sauka, sai wasu suka kawo mini sara a kai ta wajen idanu na, sai na sa hannu don in kare, sai suka cire mini wuyan hannu baki xaya, kamar yadda kake gani a yanzu sun cire mini hannu gani a kwance a gadon asibiti ina neman lafiya.” Sani Suleiman ya qara da bayyana cewa,” Ni da na kasance Soja amma har na gama aikin soja na ban sami irin wannan matsala ba sai

yanzu da na haxu da iftila’in waxannan Yara ‘Yan sara suka.” A cewar Sani Suleiman Tsohon Soja. Masana al’amuran yau da kullum na Kallon wannan lamari a matsayin wani sakaci daga vangaren gwamnati, domin a cewarsu, gwamnati ita ce wanda haqqin Al’umma ke kanka, wajen ganin ta kare lafiyarsu da kuma dukiyoyinsu. Amma a Jihar kaduna lamarin na naiman ya fi qarfin gwamnati. Duk da wasu na xaura laifin kacokan akan Abokan hamayyar gwamnati, musamman a siyasance, domin an bayyana cewa tun farkon hawan wannan Gwamnanti Jihar kaduna qarqashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed El-rufai, ya yi qoqarin gaske matuqa musamman a lokaci da gwamnatinsa ta shigo ta tarar da waxannan matasa ‘yan sara suka, wanda a lokacin gwamnan da kansa ya baiwa jami’an tsaro umurnin cewa duk wani Matashi da suka kama da hannu a lamarin, to lalle sai dai Iyayensa su haufi wani. Masu kula da al’amuran yau da kullum sun qara da bayyana cewa, daga bisani ne wasu masara kishi daga cikin ‘yan siyasa kan yi amfani da damar su wajen ganin sun shiga sun fita domin ganin sun yi bellin irin waxannan Matasa wai duk da sunan kare haqqin Xan Adam.

Wanda a cewar Masanan hakan shi ne babban umul aba’isin qaruwar wannan lamari na Matasa ‘yan sara suka ko ‘yan shara. A yayin da wasu kuma ke zargin jami’an tsaro da hannu dumu dumu wajen qaruwar lamarin. Domin a cewarsu, shaidu da dama sun nuna cewa, an sha kama irin waxannan Matasa ana damqa su ga jami’an tsaro, amma daga bisani su sake su, ba tare da sun hukunta su ba. Suma a nasu vangaren jami’an tsaro na xaura alhaqin hakan ga su kansu jami’an gwamnati, musamman ‘yan siyasa, wanda suka bayyana cewa sune ke amfani da irin waxannan Matasa domin cinma wani burinsu a siyasance. Wani babban abin da zai baka mamaki da irin waxannan Matasa shi ne, mu kanmu a matsayinmu na ‘yan jarida sau da yawa idan aka gayyace mu taro, muna samun matsalaloli sosai wajen shiga harabar zauren taron duk da kasancewa akwai shaidar katin alamar aikin jarida da kuma katin gayyatan taron. Amma abin mamaki shi ne, yadda da zarar mun shiga muke tarar da irin waxannan Matasa ‘yan sara suka ko muce ‘yan bangan siyasa xauke da makamai a cikin xakin tarukan da ake gayyatarmu. Wani lokaci na taba tambayar wani jami’in tsaro,

akan dalilinsu na barin irin waxannan vatagarin Matasa na shigowa irin wuraren tarukan nan? Amsar da ya bani itace, “ Irin waxannan Matasa da kake gani sun fimu gata a wajen gwamnati, domin sune manyan manyan yaran ‘yan siyasa wanda suke ji da su. Kuma ina mai tabbatar maka da cewa, babu wani Xan siyasa tun daga kan gwamna har zuwa kansila, wanda bai tafiya da irin waxannan Matasa, domin su shane yanzu magani yanzu, amma ai mu jami’an tsaro muna da hankali da ilimi, domin bamu yadda za’ayi wani Xan siyasa yayi amfani da mu domin yace mu kashe wane ko mu sari wane.” A cewar wani jami’in tsaro dana tattauna da shi. Yanzu dai zamu koma gefe mu zura ido domin mu ga irin matakin da gwamnati za ta sake fitowa da shi akan irin waxannan vatagarin Matasa waxanda ake kira da ‘yan sara suka ko kuma ace ‘yan shara. Duk da a halin yanzu jami’an tsaro sun bayyana cewa sun kama

mutum 23 waxannan ake zarginsu da hannu dumu dumu wajen aikata irin waxannan laifi ka. Wannan ba shi ne irin abin da Al’umma suke so ba, abin da Al’umma ke so shi ne, kawar da irin waxannan vatagarin Matasa kwata kwata daga cikin Birni da Qauye na Jihar kaduna.


RAHOTO 27

A Yau Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Nijeriya Ta Samu Canji Qarqashin Mulkin Buhari – Itegboje Daga Idris Aliyu Daudawa

Nijeriya ta samu canji a qarqashin mulkin shugaban qasa Muhammadu Buhari, duk kuwa da yake da akwai matsalolin daya gada, Ambasada Samson Itegboje, wanda shi ne wakilin dindindin daga Nijeriya , wanda ke majalisar xinkin duniya, shi ne ya bayyana hakan. Itegboje ya bayyana hakan ne lokacin da aka yi taron tattaunawa wanda ‘yan Nijeriya mazauna Washington DC suka shirya , ma ‘yan Nijeriya mazauna can. Taken shi taron shi ne ‘’Magana da murya xaya ita ce babban haxin kai’’. Shi jakadan duk da haka ya ce, har yanzu kamar gwamnatun tarayya bata son bayyana ci gaban da, gwamnatin Buhari ya ce, domin su ‘yan qasa su san abin da ake ciki. ‘’Mun san cewar kafin zuwan mulkin shugaban qasa Muhammadu Buhari, tattalin arzikin Nijeriya kamar ya durqushe ne. ‘’Maganar gaskiya shugaban qasa Muhammadu Buhari ya gaji tattalin arziki, wanda ya daxe da shiga halin ni ‘yasu’’ ‘’Ga kuma maganar Boko Haram wadda a lokacin da ya karvi mulki, lokacin tana riqe da Qananan Hukumomi goma sha huxu, na jihara Borno’’ ‘’Amma wannan gwamnati ta ci gaba da aiki ne, kuma maganar gaskiya ita wannan gwamnatin ba mai son ta riqa bayanin duk wasu ci gaba data samu bane’’. Ya bayyana wasu ci gaban daban da aka samu qasa da shekaru uku, na ita gwamnatin, waxanda kuma yace suna buqatar da sai an tantance su. ‘’Qasar Nijeriya ta xauki shekaru uku kafin ta fita daga tavarvarewar tattalin arziki, amma ita gwamnatin, ta xauki shekara xaya da rabi ne, domin fita daga shi tavarvarewar tattalin arzikin. ‘’Asusun ajiya na qasar waje yanzu da akwai dala bilyan 43, babban abin da ka samu ke nan cikin shekaru huxu, wannan kuma dga dala milyan 24 a shekara xaya’’. Ya bayyana cewar gabatar da asusun bai xaya, wanda tsarin wanda ya kawo cikas akan yadda satar kuxaxen shiga da suka kamata su shiga aljihun gwamnatin tarayya, bugu da qari an an samu aje Naira bilyan108, saboda cire wasu kuxaxe na kulawa da ake ba bankuna saboda, kafin bayyanar asusun bai xaya. ‘’Nijeriya ta koma matsayi 24 na asusun duniya akan

matakin samun harkarb kasuwanci a sauqaqe, bayan nan kuma ta samu wuri, na qasashe goma waxanda suka fi iya harka. ‘’Kamar yadda wani rahoto na watanni uku na tsakiyar shekara da suka kai wata tara ke nan na shekara ta 2017, kayayyakin aikin gona da ake fitarwa sun qaru da da kashi 25, yayin da kuma harkar fitar da ma’adinai wannan kuma ya kai kashi 78.’’ ‘’Kayayyakin da ake amfani dasu waxanda ake sayarwa qasashen waje, sun qaru da kashi 70 na shekara zuwa shekara, sai kuma kayayyakin da kayi cikin gida, waxnda ake kaiwa zuwa qasashen waje, sun qaru da kashi 22, na shekara shekara. Yayin da kuma kuxaxen da ake samu, ba daga xanyen mai ba,sun qaru da kashi 40, na asusun qasar waje.’’ ‘’A matsayi na Ya ci gaba da bayanin Hukumomin gwamnati kamar su Hukumar hana fasa qwauri, Hukumar shirya jarabawar shiga jami’oi da sauran manyan makarantu, sun samar da kuxaxen shigar da ba a tava samu ba. Ya tuna cewar bada daxewa bane ita Hukumar JAMB ta samar da Naira bilyan 7.8, idan aka kwatanta Naira bilyan 51 tsakanin shekarun 2010 da kuma 2016. ‘’Manoman shinkafa milya shida a shekarar 2015 yanzu sun kai fiye da milyan 12, wannan kuma shi yasa aka

rage shigowa da shinkafa daga qasar Thailand.’’ ‘’Nijeriya ita ce qasa ta biyu wajen noman dawa bayan qasar Amurka, ta uku kuma a duniya wajen noman gero, bayan qasar Indiya, ita ce kuma ke jagoranci a duniya vangaren noman rogop da kuma doya.’’ ‘ ‘’Gaba xaya babban muradin gwamnatin shi ne vangaren aikin gona zai qaru daga kashi 25 zuwa 40 na GDP, ta hakan kuma ne za ayi maganin fatara.’’ ‘’Maganar samar dawutar lantarki abin an samu ci gaba na megawatt 7,000 yayin da kuma maganar hanyar jirgin qasa, daga Lagos zuwa Kano, Lagos zuwa Ibadan da kuma Kano zuwa Kaduna, za a fara aiki da hakan shekara ta 2019. Bugu da qari hanyoyi 25 waxanda sune manaya ana gyaransu, yayin da kuma hanyar jirginqasa daga Kalaba zuwa Lagos, ana ta yarjejeniyar yin aikin. Kamar yadda Otegboye ya qara yin bayani. Yayin da kuma har yanzu wasu zasu iya cewar, har yanzu basu gamsu ba, amma nan bada daxewa ba’yan Nijeriya zasu shiga wata sabuwar rayuwa. Mr Pierro Tozzi wanda shi darekta ne na ma’aikata a majalisar Amurka akan harkokin qasashen waje, ya bayyana jin daxin shi akan gaggarumin ci gaban ‘yan Nijeriya suka samu a Amurka. Amma kuma Tozzi ya nuna rashin jin daxin shi har ila yau akan matsalolin dake gida Nijeriya.

Ya qara cewar Amurka na ci gaba da taimakawa vangarori da yawa na tattalin arzikin Nijeriya, amma kuma ya ce qasar Amurka ta damu qwarai, dangane da rikicin da ke tsakanin manoma da makiyaya, a sashen Arewa ta tsakiya. Mr Samuel Adewusi shi na darektoci na NIDO USA ya bayayana dokar dake tattare da Hukumar ‘Yan Nijeriya mazauna qasashen waje, zata taimaka wajen ci gaban al’umma da kuma qasa wajen amfani da, kuxaxensu da kuma qwarewarsu wajen ci gaban Nijeriya. Ita dokar kamar yadda Adewusi ya bayyana zata samar da sunayen ‘yan Nijeriya, a fannoni daban daban, zasu yi amfani da qwarewarsu, da kuma kuxaxe domin kare mutuncin Nijeriya. Waxanda suka halarci taron sun qalubalanci yadda ake tafiyar dagwamnati, da kuma su shugabanni, akan gazawarsu a siyasance, sun kuma yi kira gare su da su qara lura da haqqoqin da Allah ya xora masu na waxanda suke shugabanta. Amma duk da haka sun xauki alkawarin ci gaba da taimakawa Nijeriya, da qwarewarsu, domin ci gaban Nijeriya, sun kuma da cewar ‘’ Mun qalubalanci kanmu sosai’’. Shi dai taron wanda ya samu halartar ‘yan Nijeriya daga vangarorin Amurka da dama, ya tattauna akan maganar al’amarin daya shafi shige da fici na qasashen waje, da kuma harkokin ofishin jakadancin Nijeriya.


28 LABARAI

A Yau

Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

NUJ Ta Na Kan Ba Mambobinta 50 Horo Kan Na’ura Mai Kwakwalwa A Bauchi

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A jiya Laraba ne qungiyar ‘yan jarida ta qasa reshen jihar Bauchi ta fara ba da horo kan ilimin na’ura mai kwakwalwa da yanda ake iya sarrafa ta ta hanyoyin da suka shafi xan jarida da kuma aikin na jarida a wannan zamanin. Wannan horon dai haxin guiwa ne a tsakanin qungiyar ‘yan jaridan da kuma kwalejin kimiyya da fasaha na gwamnatin jihar Bauchi wato (Abubakar Tatari Ali Polytechnic, Bauchi). Wannan adadin ‘yan jarida hamsin da suke samu horo a halin yanzu, qari ne kan wasu ‘yan jarida xaya da suka samu horo a karo na farko, da na biyu inda a yanzu haka kuma karo na uku suke kan ci gaba da samun horo kan na’ura mai kwakwalwa da kuma sanin dabarun inganta aikin jarida daidai da zamani, wanda adadin ya kawo ‘yan jarida 150 da NUJ ta tsakulo. Da yake yi wa LEADERSHIP A Yau qarin bayani kan shirin, Kwamared Ibrahim Muhammad Malam Goje wanda shi ne shugaban ‘yan jarida na jihar ya bayyana cewar wannan horon sun himmatu ba da shi ne domin cika alkawuran da suka xauka a ya yin da suke yaqin neman zave a wajen mambobin ‘yan jaridan “wannan dai wani ci gaba ne ta fuskacin horas da ‘yan jarida na jihar Bauchi wanda ita NUJ ta quduri aniyar yi kamar yanda muka shelanta a lokacin yaqin neman zave. Kuma shi wannan horaswar na tsawon kwanaki uku ne kamar yanda aka fara a yau talata 4/4/2018 (jiya kenan) za kuma a kammala a ranar Juma’a 7/4/2018”. Malam Goje ya ci gaba da

cewa abun da wannan tirenin xin ya qunsa dai shi ne ba da horo na musamman kan ilimin amfani da na’ura mai kwakwalwa wato (computer). Ta bakinsa “abun da wannan horaswar ya qunsa dai shi ne mutane hamsin daga cikin ‘yan jaridarmu ne za mu ba su horon nan, kamar yanda muka yi a karo na farko da na biyu, yanzu gamua a karo na uku “Horon nan a kan fannonin da suka shafi aikin jarida kai tsaye ne. na farko akwai abun da ya shafi mu’amala kai tsaye da na’ura mai kwakwalwa ta hanyar shiga yanar gizo (Internet), na biyu kuma akwai horo na sarrafa na’ura mai kwakwalwar wajen yin rubuce-rubuce sai kuma na uku wajen yin amfani da kwamfuta wajen sarrafa hotuna, kwarewa kan amfani da addireshin E-Mail, ilimin xan jarida a kan kafafen sadarwa ‘Social Media and Social Networking’ da kuma yadda xan jarida zai yi aikinsa da waxannan fannoni, da sauran fannonin da ake ba da horon domin inganta aikin namu”. A cewarsa Ya ci gaba da cewa babban abun da suke son cimmawa a irin wannan horo da suke baiwa mambobinsu na ‘yan jarida shi ne domin su laluvo hanyoyin shawo kan matsalolin da suke jibge a aikin na jarida “irin matsalolin da ake samu ka ga wasu ‘yan jarida suna gudanar da aikin ba tare da ilimin da ya dace ba; muna son ganin an kawo qarshen rashin gudanar da aikin nan ba tare da ilimin da ya kamatan ba. za ka samu xan jarida a wannan qarnin na 21 amma bai iya sarrafa kwamfuta ba, wannan

abun kunya ne kuma naqasu ne mai girma ga shi kansa xan jaridan. Muna son su mambobinmu suna da ilimi kan ita na’ura mai kwakwalwa ta yanda za su iya sarrafa ta cikin qanqanin lokaci wannan shi ne abun da muke son mu cimma domin yin aikin da kwamfuta na kawo sauqi sosai wajen tafiyar da aikin jarida”. In ji Goje Da yake bayani kan natijar da horon farko ya jawo kuwa, ya bayyana cewar an samu ci gaba sosai ga waxanda aka basu horon nan a karin farko da na biyu yana mai cewa natijar ba ma ya misaltuwa “hatta shuwagabanin cibiyoyin ‘yan jaridu sun yi ta qiranmu suna bayyana mana cewar a sakamakon wannan horon sun fara ganin canji a wajen wasu daga cikin ma’aikatansu wannan ka ga ci gaba ne. sannan su kuma waxanda aka basu horon nan da dama sun yi ta samun yanda za su yi domin shawo kan matsalolin da suke ciki.

wasu da dama da aka basu horon nan sun iya fahimtar a da suna shan wahala sosai wajen gudanar da aikinsu a sakamakon basu amfani da ita kwamfuta amma yanzu da suka samu ilimi kan kwamfutar sun koma suna amfani da ita wanda mun ga ci gaba sosai ta fuskancin wannan horon”. Ta bakinsa Wannan horaswar dai shi ne karo na uku, inda aka yi wa ‘yan jarida hamsin horo a karin farko da na biyu, yanzu ga wasu hamsin xin suna samun horo kan wannan Ilimin zamanin. Sakatare NUJ na Bauchi Yakubu Lame ya bayyana cewar sun himmatu wajen inganta walwala da kuma jin daxin mambobinsu a bisa haka ne suke samar da shirye-shirye domin inganta aikin jarida da kuma dawo da martabar aikin a idon duniya yana mai shaida cewar za su ci gaba da fitar da tsare-tsare masu fa’ida domin a samu cimma nasarar da aka sanya a gaba.

’Yan Sanda Sun Kama Xan Shekaru 80 Da Ya Yi Qoqarin Yin Garkuwa

Daga Idris Aliyu Daudawa

‘Yansanda metro na dake qarqashin rundunar ‘ynsanda ta Lagos ranar Talata ce ta kama wani mutumi mai shekaru 80, wanfda yayi qoqarin karguwa da yara uku, kusa da kasuwar Oluwale da ke kusa da Waterside Apapa. Shi dai wannan mutumi mai suna Muftahu an kama shi ne, a cikin kwale- kwale akan hanyar zuwa Olodi Apapa, lokacin da yake qoqarin arcewa daga hannun matasa waxanda suka fusata.

Kamar yadda wanda yaga abin da kansa ya bayyana Adetunji, ya bayyana cewar shi wanda ake zargi da qoqarin aikata laifin, saboda ‘’ Yana tava goshinsu da kuxi, da ya fito dasu daga wata farar ambulan.’’ ‘’Lokacin da aka tambaye shi yasa yake tava su, sai nan da nan ya shi ga kwale- kwalen da zai tafi Apapa. Sai muka tsayar da kwale-kwalen a kusa da tsakiyar ruwan, aka jawo shi waje’’. Da aka tambayi wani yaro dangane da al’amarin, sai ya ce shi wanda ake zargin ya goga ma shi kuxi a goshi.

‘’Yaron wanda yayi magan cikin yarbanci, ya same mu ya tambaye mu yadda zai je Olodi Apapa, mun yi ma shi bayani, daga na kuma say a fito da kuxi ya tava mana goshi’’. Amma shi Muftahu ya qaryata sanin su yaran, bare ma yayi qoqarin yin wani abu. Amma kuma wasu’yan kasuwa a kasuwar Oluwole sun ce, sun gan shi yana zagaya kasuwar, sun ma yi tsammanin ko mahaukaci ne, saboda yadda ya kasance sanye da kayan da basu dace ba. Amma sai jami’an ‘yansanda

suka kawo xauki lokacin da taron mutane suke neman tumurmusa shi mutumin, suka xauke shi zuwa ofishin ‘yansanda na Area B, domin su yi ma shi tambayoyi da kuma bincike. Da ka tuntuve shi mai magana da yawun rundunar ‘yansanda ta Lagos Chike Oti, ya bayyana cewar ya ji labari akan al’amarin, amma yar yanzun bai samu cikakkun bayanai ba. ‘’Muna tare da kwamishinan ‘yansanda duk kuma lokacin da muka gama ganawa zan baku cikakkun abubuwan da suka faru.’’


A Yau

29

Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

Qasashen Waje

Tare da Rabiu Ali Indabawa 08069824895

Makwaftan Libiya Sun Yi Taron Qarfafa Tsaro Qasashen Chadi, da Libya, da Nijar, da kuma Sudan na gudanar da taro a Birnin Yamai domin tattaunawa kan hanyoyin qarfafa matakan tsaron iyakokin qasashen huxu. Taron wanda na wuni xaya tak ne na matsayar wata damar chanja yawu tsakanin ministocin dake kula da harkokin cikin gida da takwarorin su na tsaro da masu kula da harkokin

waje ba’idin manyan hafsoshin soja da jami’an samar da bayanan sirri a wani yunqurin zaqulo ingantattun hanyoyin warware matsalolin da ke da nasaba da rikicin qasar Libiya inji mininstan tsaron Nijer Alhaji kalla Muntari, inda yace matsalar da ke cikin Libiya ta fi qarfin qasa guda, kuma matsalar da take kawowa qasashen makwaftan ta ya fi qarfin

qasa guda. Shi ya sa wannan qasashe suka kawo shawara ga Shugaban qasar Nigar akan a yi taro a tattauna a kan wannan batu, ya qara da cewa makamai dake shiga Nijar daga Libiya ake kawowa, da motocin sata da ma muggan kwayoyi, ya ce dole a xau mataki a kai. Sakataren harkokin wajen qasar Sudan Abdulkarim Abdulganiy ya ce mai da hankali ga

musanyar bayanai ita ce hanya mafi a’ala wajen cimma burin da aka sa gaba, inda kuma Ministan cikin gidan qasar Chadi Ahmad Bashir ya shawarci qasashen huxu a kan xaukan muhimmam matakan shige da fice, wato qarfafa tsaro a kan iyakoki da tsananta bincike musamman iyakokin Libiya ta vangaren Gabas da Kudu maso Gabas a sakamakon lura da yanayin da qasar ta Libiya ta haifar a

qasashe makwaftanta ya sa taron bayyana shirin danqa al’amura a hannun qwararru domin jin ta bakinsu a kan abubuwan da suke ganin su ne mafita, sun bayyana cewa taron Ministocin zai ba da sanarwar qarshen taro xauke da alqawuran ko wacce daga cikin qasashen hudu da suka kira kansu qasashe mafi xanxana kuxar tavarvarewar al’amuran hukuma a qasar Libya.

Qasar Mexico Za Ta Ba ‘Yan Gudun Hijira Mazauni ‘Yan gudun hijirar da ke tafiya don neman mafaka sun janyo mai da martani daga Shugaban Amurka Donald Trump. Gwamnatin qasar Mexico ta ce za ta ba da mazaunin ‘yan gudun hijira ga wani ayarin baqin haure daga qasashen yankin Amurka ta tsakiya, waxanda saqonnin shugaban Amurka Donald Trump a shafinsa na tweeter su ka ta da musu hankali kwanan nan, a kan buqatar shugaban ta qarfafa iyakokin qasarsa. A wata sanarwa daga ma’aikatun harkokin cikin gida da na waje na Mexico suka fitar jiya, sun lura cewa ayarin jama’ar waxanda

Wani Harin Jiragen Saman Sojan Afghanistan Ya Hallaka XalibaI Masu Saukar Qur’ani

Mutane da dama ne ke cike da fargaba sakamakon wani harin jiragen sama da jiragen saman sojojin Afghanistan suka kai kan wata makarantar karatun al Qur’ani dake Kunduz, Arewa maso Gabashin qasar, inda aka bai wa xaliban takardar shaidar kammala karatu a gaban wasu shuwagabanin Taliban da xalibai da dama. A cewar shugaban asibitin yankin Dr. Na’im Mangal, mutane da dama sun rasa rayukansu a yayin da wasu sama da 15 suka jikkata, waxanda kuma suka haxa da qananan yaran da aka kwantar a asibitinsa mai tarazar kilo mita 50 daga lardin Dashte Archi inda

harin ya wakana. Majiyoyin tsaro da na shaidun gani da ido sun ce, fararen hula da dama ne dai suka halarci shagululanan saukar karatun kur’anin mai tsarki a lokacin da abin ya faru. Muhammad Is’haq wani ganau ne, ya sanar a tashar TV Tolo News ta qasar Afghanistan cewa, suna cikin masallacin Akundzada inda saukar karatun ta gudana ne, wanda kuma ya samu halartar xalibai da fararen hula da yawa, da kuma wasu mambobin qungiyar ‘yan tawayen Taliban da aka gayyata ne, suka ji qarar jiragen sama nan take kuma ‘yan Taliban suka tsure, hankalinsu ya tashi

kafin ka ce me tuni bamabamai sun fara sauka a ginin wannan masallaci, nan take kuma mutane da dama suka rasa rayukansu da kuma jikkata. Wani mai xaukar Hoton AFP ya ce, ya ganewa idonsa qanqanan yara da matasa da dama daga cikin waxanda suka jikkata kwance a qasa da kuma cikin lungunan da kwanonin asibitin. Sai dai a ta bakin kakakin ma’aikatar tsaron qasar ta Afghanistan, Muhammad Radmanish, ya musanta cewa harin ya rutsa da yara da fararen hula a masalacin, illa shugabanin Taliban a qalla su 20 da suka haxa da kwamandansu, da aka kashe

yawancin daga qasashen Guatemala, da Honduras, da El Salvador suka fito, sun tava yin irin wannan tafiyar ta ayari tun daga shekarar 2010, abinda ke janyo hankali akan ‘yancin ‘yan gudun hijira, musamman waxanda ke guje wa matsanancin yanayin rayuwa a qasashensu don neman mafaka a wasu wuraren. “Manufofi akan baqi na qasar Mexico na da qarfi sosai, da su ke neman tabbatar da doka, da Oda wajen shigowar baqi da kuma mutunta ‘yancin jama’a a cewar sanarwar. Babu yanayin da gwamnatin Mexico ta yarda da shigar baqi ba bisa ka’ida ba a qasar.

Trump Ya Tabbatar Da Janye Sojoji Daga Siriya Duk da shawarar da qwararru ke bashi cewa ISIS na iya komawa Siriya tare da fargabar qawayen qasar, Shugaban Amurka ya haqiqance sai ya janye sojojin qasarsa daga Siriya. Game da batun soji har yanzu, shugaban Amurka Donald Trump, yana nan kan bakarsa na iqirarin da ya yi cewa, lokaci ya yi na janye sojojin Amurka daga Siriya, duk da cewa qawayen Amurka da suke qasar suna kiran da ta sake tunani. “Babban burin mu na zuwa can shi ne ganin mun kawar da ISIS, Mr. Trump ya faxa jiya talata. “kusan mun kammala wannan aiki, kuma za mu yanke shawara nan ba da jimawa ba

tare da shawara da waxansu, kan abinda za mu yi ba,” Shugaban na Amurka ya faxa a wani taro da manema labarai da ya yi tare da shugabannin qasashen yankin Baltic su uku. Sai dai wannan matakin janye sojojin Amurkan qawayen Amurka ba su goyi bayan haka ba, ciki kuwa har da qasar Iraqi da Qurdawa. Da dama suna fargabar hakan zai bar givi da wasu ciki har da ISIS za su cike shi. A halin da ake ciki kuma, wata mata ta buxe wuta a shelkwatar kamfanin Youtube a jihar California ta jikkata kanta da mutum uku kamin ta kashe kanta, kamar yadda hukumomi a yankin suka yi bayani.


Wasanni 30

A Yau

Alhamis 5.4.2018

Tare da Abba Ibrahim Wada Leadership Ayau@yahoo.com

Za Mu Iya Lashe Gasar Zakarun Turai -Zidane Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

An fafata tsakanin Juventus da Real Madrid a matakin wasan dab da na kusa dana qarshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a filin wasa na Allianz,xan wasa Christiano Ronaldo ya taka rawa a nasarar da qungiyar sa ta samu a karawa da Juventus da ci 3 da nema. mai koyar da tawagar Real Madrid, Zinedine Zidane yace wannan nasara na qara bashi damar kare kanbin da qungiyar ke riqe da shi a karo na uku a jere. Juventus za ta yi qoqarin rama abin da Real Madrid ta yi ma ta ranar 11 ga watan Afrilun nan idan sunje qasar sipaniya a wasan da zasu fafata a filin wasa na Santiago Barnabue dake garin na Madrid. Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya buqaci ‘yan wasansa da su maimata rawar da suka taka a filin Allianz inda yace har yanzu akwai sauran aiki a gabansu saboda haka sai sun sake dagewa. Ronaldo mai shekaru 32 ya taimaka inda xan wasan ya zura qwallaye biyu a ragar Juventus, Christiano Ronaldo ya zura qwallaye biyu na Real Madrid a mituna 3 da mituna 64,bayan haka Marcelo ya zura qwallo na uku na Real Madrid a mituna 72 da wasa.

Real Madrid Ta Zura Qwallaye 25 A Ragar Juventus Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

A ranar Talata ne Juventus ta karvi baquncin qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid a wasan gab da na kusa da na qarshe a gasar Zakarun Turai. Qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid ce tasamu nasara daci 3-0 a qasar ta italiya bayan da xan wasa Cristiano Ronaldo ya jefa qwallo biyu sai kuma Marcelo ya jefa qwallo xaya a wasan da aka bawa xan

qwallon Juventus na gaba, Paulo Dybala jan kati. A bara ma dai Madrid ce ta doke qungiyar a wasan qarshe na gasar, abin da ya ba ta damar xaukar kofin gasar a birnin Cardiff na kasar Birtaniya. A kowacce karawa da Madrid ta taba yi da Juventus, Ronaldo yana samun zura qwallo a raga wanda hakan yasa Buffon yace babu xan wasa kamarsa a wannan zamanin. Sau 20 qungiyoyin suna

haxuwa a tarihin gasar Zakarun Turai -Madrid ta yi nasara a wasanni goma, yayin da Juventus ta samu nasara a wasanni takwas, sun kuma yi kunnen doki a wasanni biyu. Hakazalika, duka qungiyoyin biyu kowace ta zura wa abokiyar karawarta kwallaye da dama bayan Real Madrid ta zura qwallaye 25 sai Juventus kuma ta zurawa Madrid qwallaye 22 ne a raga a tarihin karawarsu.

Ba Na Tsoron Chelsea Ta Kore Ni, Inji Conte Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Mai koyar da qungiyarqwallonqafa ta Chelsea, Antonio Conte, dan qasar italiya yace baya tsoron qungiyar ta Chelsea ta koreshi duk da cewa yana cikin matsin lamba a qungiyar. Chelsea dai tasha kasha a hannun Tottenham a filin wasana Stamford Bridge dake birnin landan bayan da qungiyar tasamu nasara daci 3-1. Conte, mai shekaru 48 yace baya damuwa da raxe-raxin da mutane sukeyi na cewa za’a koreshi kawai dai ya mayar da hankali

da aikin sa duk da abinda yafaru a nan gaba yana maraba dashi. Rahotanni sun bayyana cewa shugabannin qungiyar sun bayyana cewa sun fara gajiya da qorafe-qorafen da mai koyarwar yakeyi na cewa wasu daga cikin yan wasansa suna ciwo shine dalilin daya sa baya samun nasara a wasu wasannin da qungiyar tayi rashin nasara. Chelsea dai tayi rashin nasara a wasanni da dama kuma anyi waje daita a gasar zakarun turai a hannun Barcelona. Qungiyar dai tana fama da matsalar ciwon

yan wasa inda a kwanakin baya yan wasa irinsu Morata da Kante da Drinkwater da Cahill sukaji ciwo. Conte yace tabbas yana cikin matsin lamba kuma idan shugabannin qungiyar suka yanke hukuncin korarsa babu yadda zaiyi haka zai karvi qaddara tunda ba akansa aka fara ba. Chelsea dai yanzu itace a matsayi na huxu a kan teburin firimiya da maki 16 cikin wasanni 9 kuma za ta fafata wasan cikin kofin Qalubale na FA da qungiyar Southampton a qarshen wannan watan.


A Yau Alhamis 5 Ga Afrilu, 2018 (18 Ga Rajab, 1439)

WASANNI 31 Mancheter United Za Ta Fara Zawarcin Andre Gomez Na Barcelona Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Ronaldo Ya Kai Matsayin Pele Da Maradona, Inji Buffon Mai tsaron ragar qungiyar qwallon qafa ta Juventus, xan qasar italiya, Gianlugi Buffon ya bayyana cewa kawo yanzu xan wasa Cristiano Ronaldo matsayinsa ya kai a haxashi da manyan yan wasan duniya da suka shahara wato Pele da Maradona. Buffon yaci gaba da cewa dole duniya ta yadda acewa Ronaldo da Messi sun kai matsayin Maradona da Pele saboda yadda suke buga qwallo kuma suke buga wasa yadda yakamata suke qayatar da yan kallo da magoya bayan qungiyoyin da suke bugawa wasanni. Ronaldo dai ya zura qwallo biyu a ragar Buffon a wasan da qungiyar ta lallasa Juventus daci 3-0 har gida a wasan zakarun turai da qungiyoyin suka buga a qasar italiya. Buffon ya bayyana hakane bayan antshi daga wasan sannan kuma yace babu makawa qungiyarsa ta Juventus tafita daga gasar domin rashin nasara a gida daci uku babu ko xaya sannan kuma ya yabawa Ronaldo da ragowar yan wasan qungiyar ta Madrid. Pele yace Ronaldo ne kaxai xan wasan dayake sawa dole sai qungiyarsa tasamu nasara kuma ya cancanta a haxashi da Maradona da Pele idan ana maganar qwallon qafa a duniya domin shima a yanzu babu kamarsa. A qarshe yace yayi danasin wasan domin bai kamata suyi rashin nasara daci 3-0 ba duk da cewa qungiyar Real Madrid ta cancanta data dokesu. Ronaldo dai yazura qwallaye 25 cikin wasanni 13 daya bugawa qungiyarsa da kuma qasarsa ta Portugal.

Chelsea Ta Na Son Asensio A Maimakon Hazard Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Qungiyar qwallon qafa ta Chelsea ta fara zawarcin xan wasan gaba na qungiyar qwallon qafar Real Madrid, Marco Asensio a matsayin vangaren yarjejeniyar da take son cimma tsakaninta da Real Madrid, dangane da saida wa Madrid xin xan wasanta na gaba Eden Hazard. Jaridun labaran wasanni na qasar sipaniya dake wallafa labarai a kullum a Sipaniya sun rawaito cewa Chelsea na qoqarin toshe Baraka ko gazawar da za ta samu ne, muddin Hazard ya sauya sheqa zuwa Real Madrid. Sai dai jaridar Daily Mail ta rawaito cewa qungiyar Chelsea ta ce a shirye ta ke ta sayi Asensio, ko da kuwa dan wasanta Hazard ya zavi ci gaba da zama a cikinta. Chelsea ta amince da biyan Fam miliyan 119 domin sayan Marco Asensio mai shekaru 22 indai Real Madrid xin ta amince za ta rabu da dan wasan. Qungiyar qwallon qafa ta Real Madrid dai tana shirin garanbawul a qungiyar sakamakon rashin buga abin arzqi a wannan kaka kuma ana tunanin har da xan wasan acikin yan wasan da ake zargin zasu bar qungiyar. Itama qungiyar qwallon qafa ta Manchester City tana zawarcin xan wasan wanda ake tunanin zai maye gurbin xan wasa Cristiano Ronaldo.

Qungiyar qwallon qafa ta Manchester United ta shirya tsaf domin taya xan wasan tsakiya na qungiyar qwallon qafa ta Barcelona, Andre Gomez wanda yakoma Barcelona daga Valencia shekaru biyu da suka gabata. Gomez, xan asalin qasar Portugal ya koma Barcelona ne akan kudi fam miliyan 45 bayan ya haska a gasar laliga a shekarar inda ya taimakawa Valencia taje gasar Europa a shekarar. Mai koyar da yan wasan qungiyar qwallon qafa ta Manchester United, Jose Mourinho shine aka bayyana yake zawarcin xan wasan wanda ya nema a Valencia kafin Barcelona su rigashi siyan xan wasan. Rashin buga wasa da xan wasan yake fama dashi a qungiyar yasa Mourinho yake ganin kamar zaisa xan wasan ya canja shawarar zamansa a Barcelona domin ya samu inda zai dinga buga wasa. Xan wasan dai sau uku ana fara wasa dashi acikin yan wasan sha xaya na farko a qungiyar ta Barcelona a dukkan wasannin da qungiyar ta buga sai dai yashigo bayan hutun rabin lokaci har sau goma a gasar zakarun turai dana laliga. Manchester United tana neman dan wasan tsakiya sakamakon rashin buga wasa da xan wasa Machael Carrick sannan kuma xan wasa Maroune Fellani yaqi sake sabon kwantaragi a qungiyar wanda hakan yake nufin zai iya barin qungiyar a qarshen kakar nan. Ana tunanin Manchester United za ta taya xan wasan idan an buxe kasuwar siye da siyar da yan wasa ta watan Janairu a shekara mai kamawa kuma tuni aka bayyana xan wasan zai kai fam miliyan 31 idan har United xin tana son dauka.

Tsohon Xan Wasan Chelsea Da Manchester United Ray Wilkins Ya Mutu

Rahotanni daga qasar ingila sun bayyana cewa tsohon xan wasan Manchester United da Chelsea, Ray Wilkins ya rasu bayan yasha fama da bugawa zuciya. Wilkins, mai shekara 61 ya shafe kusan mako xaya a wani asibiti dake arewacin landan bayan da zuciyarsa ta buga kuma iyalansa suka xaukeshi zuwa asibiti. Marigayin ya buga wasanni a qungiyoyi 12 a tarihinsa kuma ya lashe kofin qalubale na FA da qungiyar qwallon qafa ta Manchester United a shekarar 1983 sannan kuma ya lashe kofin rukuni- rukuni na qasar Scotland a s hekarar 1989 da qungiyar Rangers. Ya kuma bugawa qasar ingila wasanni 84 sannan kuma ya shafe shekaru 6 yana matsayin mataimakin mai koyar da yan wasan qungiyar Chelsea haka kuma ya riqe matsayin mai koyarwa na riqon qwarya a qungiyar ta Chelsea. Kafin mutuwarsa ya koyar da qungiyar qwallon qafa ta Queens Park Rangers da qungiyar Fulham sannan kuma ya koyar da yan wasan tawagar qasar Jordan.


5.4.18

AyAU LEADERSHIP

Alhamis

Don Allah Da Kishin Qasa

www.leadershipayau.com Leadership A Yau

JARIDAR HAUSA MAI FITOWA KULLUM TA FARKO A NIJERIYA

LeadershipAyau

No: 119

QASASHEN WAJE

Trump Ya Tabbatar Da Janye Sojoji Daga Siriya

N150

> Shafi na 29

Sabatta Juyatta A Cikin Jam’iyyar APC Ba Ta Qare Ba Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@gmail.com

A

‘yan kwanakin nan jam’iyyar APC mai mulki na fama da wani abu mai kama da rikicin cikin karkashinkasa. Da farko Gwamnonin jam’iyyar ne suka yi taro suka kuma sahalewa Shugaban jam’iyyar na kasa Cif John Oyegun, da ya ci gaba da jan ragamar jam’iyyar har na tsawon shekara guda ba tare da an gudanar da zaben sabbin Shugabannin jam’iyyar ba. A lokacin da Gwamnonin APC sukai waccan Sahalewa a gaban Shugaban qasa Muhammadu Buhari sukai, bai ce komai ba, suka goyi bayan Shugaban jam’iyyar ya ci gaba da mike kafa a matsayinsa na Shugaba a cikin jam’iyyar. Sun cimma waccan amincewa ne tsakaninsu su Gwamnonin Jam’iyyar na jihohin Najeriya. Bayan da Gwamnonin suka cimma waccan matsaya ne ta karawa Oyegun ladan gaben shekara guda a matsayin Shugaban jam’iyyar na kasa, sai kuma al’amari ya sauya. Domin Jagoran jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yayi tutse akan wancan batu na Gwamnonin jam’iyyar na sahalewa Shugaban jam’iyyar na kasa Oyegun ya ci gaba da jan zarensa na tsawon shekara guda. Tinubu ya ce sam ba zata sabu ba akan abinda Gwamnonin jam’iyyar na kasa suka yi, na amincewa John Oyegun ya ci gaba da jan ragamar jam’iyyar har na tsawon shekara guda. Inda yake kumfar baki yana ikirarin yin hakan, sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ne da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya baki dayansa. Ba’a je ko ina ba, Shugaban qasa Muhammadu Buhari da kansa ya fito fili ya goyi bayan ra’ayin Bola Tinubu akan Shugabancin jam’iyyar, alhali kuwa a gaban Shugaban qasa Gwamnonin jam’iyyar suka sahalewa Oyegun ci gaba da jan ragamar jam’iyyar a matakin shugaba na kasa. Amma tunda Jagoran jam’iyyar, tsohon gwamnan jihar Legas kuma tsohon Sanata, Bola Ahmed Tinubu yaki amincewa da batun, shima Shugaba Buhari ya nuna kin amincewarsa akan wa’adin shekara guda da aka karawa Oyegun da Gwamnonin suka yi. Da farko alamu sun nuna za’a yi baram baram akan batun Shugabancin jam’iyyar na kasa, ina bayan wani zama da aka yi

Muqalar Alhamis

tsakanin gwamnonin jam’iyyar da Shugabankasa, rahotanni sun nuna cewar an rabu gida biyu a majalisar Gwamonin,inda wani sashi suke goyon bayan tsyawa kan batun karin wa’adin shekara guda ga Oyegun, wani bangaren kuma suke goyon bayan ra’ayin Shugaba Muhammadu Buhari da Tinubu na lallai sai Shugaban ya sauka saboda wa’adinsa ya qare. A cewar Tinubu kundin tsarin mulkin jam’iyyar bai tanadi abinda Gwamnonin suka yi ba. A saboda haka dolle Oyegun ya sauka a cewar Tinubu. Sai dai kuma, daman tun ba yau bane ake cewar akwai jikakkiya tsakanin shi Tinubu da kuma shi Shugaban jam’iyyar na kasa, John Oyegun, inda ake ganin Gwamnonin jam’iyyar sun arawa Oyegun din baya. Daga gefe guda shi kuma, Shugaban qasa da wasu Gwamnonin suke ganin zasu makale a bayansa dan su kuma cin zabe, shi kuma yana goyon bayan Tinubu. Kamar dai hakan na nuna akwai yakin basasa na karkashin kasa a tsakanin manyan Shugabannin jam’iyyar da bangaren

Gwamnoni wanda suke yiwa Tinubu gani gani. Idan ba’a manta ba, Shugaban qasa Muhammadu buhari ya amince da nadin Bola Tinubu a matsayin sabon bakaniken jam’iyyar, wanda zai sasanta ‘yan jam’iyyar masu adawa da juna, inda tun bayan nadin nasa ake ganin ba’a sanya kwarya a burminta ba, domin a matsayin Tinubu na mai shiga tsakanin wanda suke adawa da juna a cikin jam’iyyar, shi kansa akwai wanda yake adawa da su a cikin jam’iyyar. Misali shi ne Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, da yawa sun yi amanna ana zaune ne ta ciki na ciki tsakanin Bola Tinubu da kuma Bukola Saraki, tun bayan zaben da ya kai ga Sarakin zama Shugaban majalisar dattawa. Baya ga saraki da ake ganin suna zaman doya da manja da Tinubu, ta kuma bayyana cewar akwai takun saka tsakanin shi Tinubu din da kuma Shugaban jam’iyyar na kasa. Wanda a yanzu shi Tinubu yaci nasarar kai keyar John Oyegun kas a matsayinsa na Shugaban jam’iyyar APC. Da yawa wasu ma ganin shi

+23408099272908

kansa Tinubu akwai bukatar a kafa wai kwamiti da zai sasanta shi tsakanin sa da wasu manya a cikin jam’iyyar da basa ga maciji da juna. Ko dai ya abin yake, zaa’a iya cewar, tsugunne bata qare ba a cikin jam’iyyar ta APC, dominkuwa wannan sabatta juyatta da ake yi zata ci gaba, kan wane zai zama sabon Shugaban jam’iyyar na kasa baki daya, bayan qarewar wa’adin John Oyegun. Wannan ma wani batu ne da ake ganin zai gwara kan Jagoran jam’iyyara na kasa Bola AHmed Tinubu da kuma su gungun Gwamninin jam’iyyar na kasa, kan waye zai gaji Oyegun a matsayin sabon Shugaban jam’iyyar na kasa. Tuni tuni masana da masu sharhi kan aal’amuran siyasa suke hango wannan baraka a cikin jam’iyyar APC kan wanda zai zama Shugaban jam’iyyar bayan Oyegun din da Tinubu ya kafawa kahon zuka. Ko ma dai ya ake ciki, batun sabon Shugaban jam’iyyar na kasa da wuya bai barbaya da kura ba, duba da cewar zaben 2019 na gabatowa, yayin da Gwamnonin jam’iyyar da kuma shi jagoran jam’iyyar na kasa Bola Tinubu suke kokarin gwadawa juna yatsa akan karfin iko mallakar jam’iyyar a mataki na tarayya. Amma shi Tinubu rawa yake namansa na jaka,domin ya kwan da sanin cewar, Shugaban qasa na tare da shi a duk abinda ya shafi SHugabancin jam’iyyar na kasa da sauran kunji kunji dake cikin jama’iyyar.

Babba Da Jaka Magu ya ce; Rashawa ta fi Cutar Kansa Illa –Labarai

Kar ka raga musu, DODON VARAYI!

Ana shiryawa da buga LEADERSHIP A Yau a kamfanin LEADERSHIP GROUP LIMITED, lamba 27, kan Titin Ibrahim Tahir, a Gundumar Utako, Abuja. Tarho: 07036666850; Fax: 09-2345360. P. O. Box 9514, Garki II, Abuja. Ofishin mu a Legas: 34/36 Titin Adegbola, Anifowose, daidai Oba Akran, Ikeja. Tarho: 07036666850. E-mel: leadershipayau@gmail.com, Leadershipayau@yahoo.com


Turn static files into dynamic content formats.

Create a flipbook
Issuu converts static files into: digital portfolios, online yearbooks, online catalogs, digital photo albums and more. Sign up and create your flipbook.